Ad Code

𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡 𝗭𝗨𝗖𝗜𝗬𝗔 Hausa Novel

𝗠𝗨𝗥𝗔𝗗𝗜𝗡 𝗭𝗨𝗖𝗜𝗬𝗔 Hausa Novel

















𝙸𝙳𝙰𝙽 𝙺𝙸𝙽𝚂𝙰𝙽 𝙱𝙰𝚉𝙰𝙺𝙸 𝙺𝙰𝚁𝙰𝙽𝚃𝙰 𝙱𝙰 𝙺𝙰𝙳𝙰 𝙺𝙸𝚂𝙷𝙸𝙶𝙰 𝙸𝙽𝙳𝙰𝙸 𝙱𝙰 𝙺𝙰𝚁𝙰𝚃𝚄𝙽𝙴 𝙽𝙰 𝙼𝚄𝚁𝙰𝙳𝙸𝙽 𝚉𝚄𝙲𝙸𝚈𝙰 𝚉𝙰𝙸 𝙺𝙰𝚆𝙾𝙺𝙸 𝙱𝙰 𝙺𝙰𝙳𝙰 𝙺𝙸 𝚂𝙷𝙸𝙶𝙰 .𝙸𝙳𝙰𝙽 𝙺𝙾 𝙱𝙰 𝙷𝙰𝙺𝙰 𝙱𝙰 𝚉𝙰𝙺𝙸 𝙹𝙸𝙺𝙸 𝙰 𝚆𝙰𝙹𝙴 .



𝗖𝗢𝗠𝗠𝗘𝗡𝗧 𝘋𝘐𝘓𝘌.....


@𝘉𝘖𝘖𝘒1


𝘗𝘌𝘎𝘌 1/2


𝘣𝘪𝘴𝘴𝘪𝘮𝘪𝘭𝘭𝘢𝘩𝘪𝘳 𝘳𝘢𝘩𝘢𝘮𝘢𝘯𝘪𝘳 𝘳𝘢𝘩𝘪𝘮.







001








Tuƙi yake ranshi a bace matashin saurayine wanda a shekaru bazai wuce talatin da shida ba fari ne sol kyakkyawa dashi dogo mai yalwataccen gashin kai gashi baki idanunsh arsh irin na mage,gudu yake sosai yana bugun stiyarin motar kamar zai ɓallata sosai ranshi ya ɓaci gashi kuma ya nada lecture a makaranta Ringing din wayar sa ce ta dawo dashi duniyar tunanin da ya lula ya kalli screen din wayar yaga Ammiey ce ke kiransa tsaida motar yayi ya amshi kiran dama Bluetooth ne a kunnensa shiru yayi yana sauraren Mey zatace masa "Son sai raina ya ɓaci hankalin ka zai kwanta ko yanzu fisabilillah koda ace ba sbd Ni ba zaka wulakanta yarinyar mutane exam fah take ta bari tazo amma ka wani ce kai bakada lokaci haba Son pls" ta karasa cikin sanyi dan tasan halin ɗan'nata, ajiyar zuciya yayi sannan daga kyar ya buɗe baki yace"Ammiey exam nakeda ga meeting abubuwa sunmin yawa amma in sha Allah ko zuwa dare ne zanje gidan nasu ba'a sameta yanzu haka wlh na makara" ya fada yana lallashin uwar tasa"Tau shikenan tunda kace zakaje bari taje itama exam takeda da niyata ka wuce da ita school dinsu" "Ammiey pls" 

"Tau shikenan Son saika dawo Allah ya kiyaye ka kula da kanka pls" 

"Ok in sha Allah I love you"

"Love u too baby bye" 

Ya kashe wayar yana murmushi shidai a duniyar nan yana tsananin son mahaifiyar'sa gashi su biyu Allah ya ba iyayensu.

Koda ya isa school din saura minti goma su fara exam kai tsaye office dinshi ya nufah koda ya buɗe kamar wani gida haka office din yake da falo da dani komai dai ganin haka yasa nasan cewa lalle wannan matashin Malami mai hannu da shuni ne.

Kai tsaye kaya kawai ya sauya ya dau face glass dinsa ya saka ya fito ya rufe office din,kam hanya ya haɗu da Amininsa suka gaisa yace masa ya bari su fito sbd dukansu sunada class kowa kai tsaye class ɗinsa ya nufa yana shiga yaga har kowa ya hallara kasancewar sunsan halinsa daya shiga ba wanda zai sake shiga "Morning sir?" 

"Morning how was your night?"

"Alhmdllh" suka faɗa "sit down pls"

Yace dasu kasancewar sunsan halinsa yasa suka zauna har ya dau chock zai fara rubuta musu question yaji takun mutum a bayansa fasawa yayi ya juya, yarinya ce matashiya bazata wuce 19 ba kyakkyawa wace ajin ƙarshe ga diri ga shape ita ba doguwar mace ba ita ba gajera ba fara ce tass daga gani bafulatana ce tasa doguwar rigar Atamfa, captan ce aka mata ta yafa gyalenta saman kai saidai ɗan karami ne wayarta cikin aljihu handout dinta a hannu da makullan motarta, kallon'ta yayi sama da ƙasa yace "get out" kyaleshi tayi kamar bata jishiba saida ya sake faɗa in shout voice sannan ta juya tana hun-guni "ga wannan lakaƙƙen aure ga wannan malami da wane zanji mitzzz nonsense kawai" ta faɗa tana tsayawa bakin class din ganin yarinyar batajin magana yasa ya rabu da ita bai ce mata ƙala ba nan dai ya fara rubutunsa saida ya gama sannan yace su fara bakin kofar ta zauna tana kwashewa juyawa yayi yana kallon ta juyawa yayi ya kyaleta, duk da ta gaji amma haka takeci gaba da rubutun ta ,agogon hannunsa ya kalla yace "lokaci ya kusa" nan kaga kowa na wiƙi wiƙi da idanu shi abin ma mamaki ya bashi yaga dai abinda ya tambaye su ya musu shi lokacin har iyayi suke masa amma yanzu gashi suna kallon kallo kamar ba'a taɓa yi musu shiba,mamaki fal ranshi yace "kuyi somithing hakanan in bakuda abinda zaku rubuta" wannan yarinyar ce first da miƙa tata can cikin ranshi murmushin mugunta kawai yake yasan bata rubuta komai ba dan da yasan ta rubuta bazai ƙarɓa ba "wai Allah ya rufamin asiri ya ƙarɓa dana shiga uku da Abiey dan wlh tsaf zai zaneni" sai kuma tayi murmushi tunawa da tayi da iyayenta, gama ƙarɓa yayi yayi ficewarsa wasu ƴammata ne su huɗu suka fiti suna hararar ta ke "wlh kin iya wulakanci kinsan bamu iya uwar kowa ba shine kikaje kika makara baibari kika shigoba bare mu samu ko 10 ne ynz ƙila ko 0 ya bamu ya taimaka mun" daya gada cikin su ce ke wannan maganar "Tau yy nidai dan Allah ku kyaleni naji da wannan auren dazasu likamin amma ba komai sbd naga suna farin ciki hakanan zanyi hakuri,yauma mahaifiyarsa ce ta aika gida aka daukoni mukaje dan ya rainamin da hankali wai lecture gareshi bazai samu damar zuwa ba amma zaije gida anjima wlh nima saina rama baccin ƙarya zanyi" duk kansu shewa suka yi lokaci ɗaya fiddo ce tace toke ƙawata kenan shima lectura ne tab Allah yasa kar yayi halin sir wlh inyayi halinsa wuya zakici wannan mai baƙin ran tsiya" Hauwa ce ta karɓe da cewa "lalle kam ku Bama kusani ba wai khausar keson sir amma ko kallon'ta bayayi har sawa yake a zaneta ya kesa get man yayi" dariya suka kwashe da ita nan Rheeya ta buɗe baki tace "wlh da in auri wannan dodon gwamma banyi aure ba"

Fiddo ce tace" to kinsan wanda aka zaɓa miji ne kilama sir dinmmu ya fishi kyau" nan dai suka cigaba da hira abinsu wayar tace tayi kara koda ta duba Bala driver ne "Hajiya Rheeya yallabai ne yace nazo daukarki "

Kallonsa Rheeya tayi tace to shikenan Baba amma zamu sauke ƙawayena kafin mu wuce gida" 

"Tau Hajiya ba damuwa"

"Kai Baba Dan Allah kadaina cemin Hajiya ƴar'ka nake fah dan Allah kadaina"

Murmushi kwance a fuskarsa yace "yauwa ƴata Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari" 

"Amin ya Allah Baba nagode sosai"

Ƙawayenta ne suka kada baki sukace "Baba mufa Mey ake nufi damu?" cikin nishadi suke faɗa waisu ba'a saka musu albarka ba ,"Allah yayi muku albarka baki daya Zee ce tace "Baba wannan addu'ar bada Rheeya ba tasamu ta farko mukuma wannan "

Rheeya tace "wlh dani" dariya suke sosai suka shige motar Leema aka fara ajewa sannan Zee sannan Fiddo ta karshe kuma khausar ce.

Koda suka isa gida a gajiye Rheeya take,Baba ne ya gyra parking dinsa ya fice ita kuma gidan ta shiga tsayawa faɗin haduwar gidan da tsaruwarsa ɓata bakine sbd sunada kuɗi sosai, "oyoyo yaya Rheeya" Farrah ce Mey maganar dama su biyu ne ga iyayensu kuma baki daya mata,"ouhc wayyo Allah Ummiey Autarki zata ɓallani wlh" 

Kyakkyawar mata ce fara ƙal da ita daga gani kasan itace mahaifiyar yarannnan sbd kamarsu ɗaya saidai ban bancin shekaru.

"Aifah nasan kice kika dawo da kin dawo saiki nemi ɗaga min hankalin yarinya" Rheeya tace "kai Ummiey nice ma mai rigima ƴarki ce fah ina dawowa ta nemi kadani ga gajiya na kwaso dama nasan kinfi son ta Dani"ta faɗa tana hararar auta, gwalo ta mata tana shigewa bayan Ummiey,sallamar mahaifinsu ne ta katse Rheeya da maganar da tasoyi, "Abba sannu da zuwa" Rheeya da Farrah suka faɗa tare " yauwa yan albarka yakuke" "lafiya ƙalau Alhmdllh Abba" juyawa yayi yana kallon Ammiey "ke bazakimun sannu da zuwa ba" su Rheeya ko gefe suka ratsa sukayi tafiyar su ɗakin su,"my love Ina jira ka gama da yara ne sannu da zuwa ya gajiya" Murmushi yayi yanajin ƙaunarta na ninkuwa a cikin zuciyarsa "Alhmdllh kefah ya gidan ya fama da yara"

"Alhmdllh sai rashin ji da neman magana kasan halin auta " dariya yayi yace barsu inaga in basuyi wasa ba tare zan hadesu na wanke" dariya Ammiey tayi wlh kuwa da ka kyauta ma samu muci soyayyar mu hankali kwance" "kedai kam Allah ya shirya mun ke ai yanzu mun wuce soyayya saidai yara" "

kai haba Alhaji dena maidamu tsofaffin dole wlh yi musu aure muma mu shaƙata" ganin firarsu ba mai ƙarewa bace yasa na jawo jikina na fice don ganin wancan bangare ya ake ciki.




Bayan ya kammala aikinsa suka tsaya da lukman abokinsa sukayi yar fira sannan kowa ya kama gabansa, gida ya nufa kai tsaye horn yayi aka bude masa gidane amma kamar gari guda haduwa iya haɗuwa gidan ya haɗu duk da tsaruwar gidansu Rheeya Amma wannan ya damesa ya shanye, bayan anbude masa get ya shiga yayi parking kasancewar sa baida wulakanta babba cikin ladabi ya gaida mai musu gadi da yaronsa malam idi da kamal dan gurinsa bayan sun gaisa ya shiga gida koda yayi sallama a babban parlong gidan yaji kamar hayaniya ɓangaren Mommy'nsa kai tsaye can ya nufa koda ya isa bai tsaya nocking ba kawai ya bude kofar Jamal ya gani da Aneesa autar su da kaninsa kenan suna faɗa wai saiya bata taf dinta shiko yace bazai bayar ba, itako Mommy'nsu na can saman gado tana rike da Husnil Muslim a hannunta tana karatu abinta kamar ma bata ɗakin Jamal ne ya lura da Abheer Aneesa sai kuka take takowa Abheer yayi Jamal ya saki tap din ya arce yana dariya dama so yake yasata kuka kuma yayi "wlh Jamal ka kiyayi haɗuwa ta da kai wannan wane irin sha-shancine " ya faɗa yana karasawa kusa da Anee "my baby boo sorry bro Jamal yayi laifi a yafe masa pls kinji autar mommy da daddy oya smile na baki chocolate" nan da nan Anee ta washe baki taji batun chocolate "anyafe ma bro amma karya sake" kunnensa ya riƙe yace "Tau Yy rankishidaɗe baza'a sakeba" tare da sakar mata murmushi, Mommy kallonsu take tundazu tana matuƙar ƙaunar ya'yanta sosai,Anee tunda aka haife ta take fama da ciwon zuciya haka Abheer da Jamal ke kula da ita komai takeso shi suke mata musamman daddy yafi tausayinta kasancewar ta ƴa mace tilo da yake da hakama su Abheer suke tausaya mata ba ruwanta ko a school bata ƙawance da kowa.




Share & comment fisabilillahi....

Close Menu