Gawurtattu Uku Magana Zarar Bunu Ce
*_U M M
20 July 2023
*ÆŠANÆŠANO.*
*1*
_Magana, zarar bunu ce._
Da gudu na fito daga bedroom ɗin ina mai take mi shi baya ganin saurin da yake. Gadan-gadan ya doshi ƙofa ba ko waiwaye. Bin kololin abincin da ke jere nayi da kallo, kafin namujiyata ya koma kan hanyar da ya dosa.
"Yaya Mudassir (Md) abincinka fa?" Na furta da sauri ganin yana niyyar fita daga parlourn. Bai juyo ba, hakan ne yasa nayi azamar cimmasa.
"Magana fa nake Yaya." Na kuma furtawa daidai lokacin da na ƙarasa kusa da shi yana dab da buɗe ƙofar parlourn. Screen ɗin wayarsa ya duba kafin ya ce, "Am very sorry Nihlah. Bana so na makara." Furucin da ya iya fitowa daga fatar bakinsa kenan a hankali tamkar wanda maƙogaronsa ke ciwo. 'Maƙol!' Na haɗiye wani yawu mai ɗaci kafin Na bishi da kallo har ya ƙarasa, madaidaicin tsakar harabar gidan. Ban iya barin gurin ba har zuwa lokacin da ya hau mashin ɗinsa roba-roba da samari ke kira (Wayyo kuɗina) ya fita daga cikin gidan.
Gauron numfashi na sauke ina niyyar rufe ƙofar naji alamar ana turowa sai sake danno ƙofar ake ana son shugowa. Bin ta nayi da kallo har lokacin da tayi kamar ta bige ni ta wuce.
"Wallahi Nihla kina da matsala, da rufewa zakiyi ko me?" Sam na manta da fitar da tayi banɗakin tsakar gida, duk kuwa da ko wacce tana da toilet a bedroom. "Yi haƙuri Amal" Na furta tare da gaggawar barin gurin. Hakan bai hanani jin sautin dogon tsakin da ta ja mini ba, girgiza kai kawai nayi tare da nufar ɗakin baccina. Saman godona na faɗa zuciyata na bugawa da sauri-da-sauri. Na ɗauki tsawan awa guda cikin wani irin yanayi kafin na tashi ganin saƙa da warwarar da nake bazata amfane ni da komi ba. Parlour na dawo ɗauke da littafin addu'o'i a hannuna domin zaman kawai ban saba da shi ba, shine ma dalilin da yasa zaman da nayi naji ya gundure ni, nafi so na ganni ina aiki ko kuma wani abu mai muhimmanci, ko sabo da yi ne oho! Bana cikin matan dake ƙare lokacinsu a banza ba tare da samun wani abin yi ba...
"Don Allah Amal ki daina ɗaga mini murya haka, bayan kin san bamu kaɗai ba ne a gidan nan." Maganar Muzammeel (Mz) ce ta daki masarrafar saurarona, inda kawai Amal ta fito parlour tana wani ciccin magani, shima yana biye da ita. Gani na a parloun ne yasa ka Yaya Muzammeel ƙirƙirar dariyar tilas.
"Nihla kina zaune kenan?" Gyaran murya kawai na iya mishi sai da nakai aya kafin na ce. "Eh ina zaune" Duƙawa nayi har ƙasa ina gaishe shi ya amsa cike da fara'a kafin ya ce"Bari na wuce kar na makara." Taɓe baki Amal tayi, da sauri na ce"Yaya Muzammeel Mz ga abinci na shirya idan zaka ci." Ɗan jim yayi idanuwansa akan Amal wacce ta miƙe da sauri ta nufi wajen daddumar da kulolin abincin ke kai, shima bin bayanta yayi tare suka ci abincin ina zaune kan kujera ina karanta addu'o'i.
"Amal zan wuce." Bata É—ago kai ba balle yasa ran zata amsa, juyawa yayi yasa kai ya fice.
"Amma abin da kike sam bakya ƙyautawa Amal, Yaya Mazammeel fa mijinki ne, kuma...." Jan numfashi nayi sakamakon hannun da ta ɗaga mini, alamar na dakata! Sai da taja dogon tsaki kafin ta ce"So kike na dinga bauta mishi tamkar ke a gari? Ke da kike bautawa mijin naki da me ya ƙare ki da shi? Ai gara na gasaka nasan gasa ka nake, wallahi ba a haifi namijin da sai gasa ni tamkar tukubar tsire ba." Girgiza kai Nayi idanuwana zube a fuskar Amal kafin naja wani murmushin yaƙe da yafi kuka ciwo.
"Karki duba wannan, ke dai duk abin da zaki yi ki tuna Allah shine daidai." Ina gama faÉ—a nayi hanyar É—akin baccina, kasantuwar gini ne na zaman mutum É—aya amma haka suka haÉ—a mu ciki parlour ne madaidaici da É—akunan bacci guda biyu ko wannensu da toilet a ciki, hausawa na kiran irin tsarin gidan wato mu haÉ—u a parlour. A waje akwai banÉ—aki guda biyu na bahaya da na wanka, sannan muna da kitchen a parlour haka akwai wani a tsakar gida. Har na shiga É—akina ban daina jiyo surutun Amal ba.
Amal Pov.
"Aikin baza aikin wofi taka wuƙar zakara, ni ance miki irinki ce, jininmu ne guda amma wallahi halina da naki da banbanci. Ni ba asararriya ba ce da zan yi zama irin naki." Tashi tayi ta shiga ɗakinta tare da ɗauko wayarta ta dawo parlour. Doguwar kujera three siter ta kwanta tare da kunna data ta faɗa group ɗinsu na whatsApp aka hau chafta tana kece dariya, haka ta reƙa facebook tana chating da abokananta maza da mata, anan gurin ta wuni kwance da waya.
Nihlah pov.
Ina shiga toilet na faɗa tare da ɗauro alwala na fara nafilfilu. Na daɗe ina sallah kafin na ɗauko Qur'ani na fara tulawa. Sai da aka kira sallar azahar na tashi nayi, bayan na idar wanka naje nayi saboda zafin da naji a jikina kafin na fito parlourn, kwance na iske Amal sai mutsu-mutsu take hannunta ɗauke da waya tayi kwance rashe-rashe kan kujera. Girgiza kai kawai nayi na wuceta, kololin da suka ci abinci na kwashe tas takai kitchen sannan na wanke su. Indomie ɗaya na dafa tare da soya ƙwai biyu, sannan na haɗa tea mai kauri na jera a ƙaramin tire na dawo parlour na zauna domin ban karya ba tun safe, kuma naji bana sha'awar komi sai indomie ɗin. Ina zama Amal ta ajiye wayar gefenta, ganin yadda idanuwanta suka kaɗa jawur nace "Lafiyarki kuwa?" Hamma ta zuba tare da matsowa kusa da ni. "Tun ɗazu ƙamshin indomie ya cika parlourn shiyasa kika tada mini da ƙwantacciyar yunwata" Bance mata komi ba naga ta tashi sai gata da chokali haka tasa hannu muka fara ci, banci chokali uku ba ta ɗauke plate ɗin wai ta fini jin yunwa, kofin tea ɗina na ɗauka ina kurɓa a hankali ina kallon yadda ƙiri-ƙiri ta cinye mini ita tana jin ƙyiwar tashi ta dafawa cikinta hatta mijinta idan sai yaci abincinta zai ƙoshi to fa haka zai dunga kwana da wuni da yunwa. Amal tana matuƙar bani mamaki yadda bata iya komi, girki, gyaran gida da sauran aiyukan mata, sai dai tayi wanka a dafa taci ta kwanta tana chating.
Ban tanka ta ba don naga kusan kullum sai mun yi ta nanata magana guda akwai gundura tun ba yanzu ba tun muna gida, dole abin ya gundureka. Tsakar gida na fita na gyara ko ina duk da rana ce lokacin kafin na shugo ciki, parlourn ba wani datti sosai domin kullum sai na share na goge haka na kuma sharewa kafin na koma É—akina na gyara fes, wayata na zaro bayan na zauna kan kujerar dake É—akin na danna kiran Yaya Mudasseer, kira har biyu tana yankewa bai É—auka ba, har na fara rubuta masa test sai ga kiranshi ya shugo, murmushi nayi tare É—aukar kiran.
"Yaya barka da rana ya ƙoƙari ya aiki?"
"Alhamdulillah." Ya furta sai kuma yayi shuru, ganin bashi da niyyar magana sai na karya muryata a hankali. "Yaya me kaci bayan fitarka?" Shuru yayi kamar baya son magana sai kuma ya ce"Nihlatulkhair lafiya kika kira ni yanzu." Daram naji ƙirjina ya buga jin yadda ya ambaci sunan nawa har dire. "La..la..fi..ya ƙalau...daman wai inji lafiyarka." Na furta muryata na rawa. "To ina lafiya." Ya faɗa yana niyyar katse kiran nayi saurin cewa "Yaya anjima me zan dafa maka?" "Duk abin da ya miki kiyi.' Yana idawa ya kashe kiran. Ƙurawa wayar ido nayi tamkar ita ce ta mini laifin, kafin na iya ajiyeta jikina a sanyaye lokacin da na tuno irin fara'a da dariyar da Yaya yake mini a gida, kafin aurenmu.
Bazan ce auren so ne tsakani na da Mudasseer ba kuma bazan kira shi auren ƙi ba, domin kafin a ɗaura sai da aka sanar damu kai tsaye zan iya bashi auren haɗi. Yaya Madasseer yana matuƙar ji da ni ko me nake so shi zai mini a baya, haka hira kala da kala ba wacce baya ba ni, amma tun bayan aurenmu watanni na huɗu kenan ya sauya kullum fuskarsa a haɗe tamkar hudowar duhun magriba.
"Yaya Mudasseer ina so na auri miji mai sona sosai wanda zai kula da rayuwata ya bani dukkan wani farin ciki da na rasa shi a yanzu, kuma bana son mai mata." Zaro ido yayi da sauri "Amma me yasa baki son mai mata?" Ɗan turo bakina nayi gaba kafin na iya furta "Saboda bana so ta cutar da ni tamkar yadda aka cutar da Mamana, ance wasu matan hatsabibai ne zasu iya komi muddin aka aurar musu miji, shiyasa nake so na auri saurayi wanda bai taɓa aure ba." Fuskarshi ɗauke da murmushi kaɗan ya ce"Nihla kenan yaro man kaza, ai ba anan gizo ke saƙar ba, kuma ko wanne bawa baya haurewa ƙaddararsa ina so kisa a zuciyarki ba Umma ba ce ke cutar da Mama ko wacce haka Allah ya tsara mata." Hirar da muka taɓayi da Yaya na tuno lokacin muna gida. Ranar kuwa nasha duka gurin Umma saboda ta ce na daina shigewa maza wai a cewarta ni ɗin na lalace bani da abokanan hira sai maza. Duk da cewa Mudasseer ɗin gida ɗaya muke domin duka iyayenmu a tare suke da mahaifinsu da mahaifinmu yaya da ƙani ne. A tare suka taso haka gida ɗaya suke zaune har da mahaifiyarsu wato Kakarmu Hajja, wacce ko sunanta naji sai hantar cikina ta kaɗa saboda tsoro, domin na shaida duk a cikin jikokinta babu wacce ta tsana sama da ni Nihla...
Banyi zuciya akan maganar da ya faɗa mini ba, na koyi hakanne a gurin mahaifiyata wacce take iya tsallake komi da fawwalawa Allah saboda tsantsar biyayya da haƙurinta ga zurfin ciki. Ina idar da sallar la'asar na shiga kitchen na shiryawa Yaya abinci shinkafa ce jellop da waƙe tasha albasa sai ƙamshi ke tashi sannan na haɗa mishi zobo, na saka a cikin frigde don ya ɗauki sanyi. Saman dadduma da na shimfiɗa na shirya mishi abincin a tsakar parlour sannan na shiga wanka nayi tare da ɗauro alwala jin an fara kiran sallar magrib. Yaya Muzammeel ya riga Yaya shugowa domin shi ana idar da isha'i takwas ya shugo. Ina jin shi da Amal suna cin abinci da na girka hankalinsu kwance.
Sai goma da rabi Yaya ya shugo ina parlourn sai zuba hamma nake domin sosai nake jin bacci har gangaɗi nake. Kallo ɗaya ya mini ya watsar ya nufi ciki. Jiki a sanyaye nabi bayansa, takalci ya cire tare da ɗaukar fillow ya yadda ƙasan carpet kamar kullum yana shirin kwanciya nace"Haba Yaya ido fa ba mudu ba amma yasan kima, yanzu ka dawo kayi dare ko abinci baka ci ba zaka kwanta."
"Wai ina ruwanki da ni ne Nihla?"
"Akwai ruwana kuwa har ma da tsakina, Yaya kar ka manta kaifa mijina ne na aure."
"Mijinki?" Ya tambaya cike da dariyar shaƙiyanci. Kafin ya ɗaura da cewa, "Har kin mance sharaɗin da ke tsakani na da ke?" Gabana ya buga da mugun ƙarfi tunowar da nayi Yaya ya ce auren shekara guda ne tsakani na da shi, maganarsa ta katse mini hanzari. "Sharaɗi muka ƙulla dake ko kin manta ne?" Tuni hawaye suka cika mini kurmin ido girgiza kaina na fara bakina na rawa nace"Yaya don Allah mu manta da baya mu fuskanci gabanmu."
"Sai da safe" Abin da ya furta kenan tare da juya mini baya ya kwanta ko kayan jikinsa bai rage ba.
Bakin gado na faɗa tare da riƙe kumatukana da hannuwana duka biyu.
"Nihla da gaske shi kike so? Shi ne kika so ki aura ba ni ba?" Cike da yarinta na gyaɗa kaina "Ƙwarai shi nake so Yaya, ai na faɗa maka ni bana son mai mata." Fuskarsa cike da gumi yayin da idanuwansa kamar garwashi saboda ja ya ce"Na miki alkhawari zaki sami abin da kike so Nihla don haka akwai wani sharaɗi da zamu ƙulla idan har kin amince aurenmu ya zamo AUREN SHEKARA GUDA na miki alƙawari shekarar nan na cika zan sake ki, ki auri muradinki. amma fa sai kin yadda da duk abin da zan ce, kin yadda." Da sauri na fara girgiza kai hawaye na zuba kamar ruwan fanfo tunowa da amsar da na bashi a wata huɗu baya kafin yau. Bayanshi nabi da kallo da alama shi ya daɗe da fara baccinsa, haka na kwanta a ɗarare jikina ya fara rawar sanyi sakamakon yunwar dake cina don ko abincin dare ban ci ba gashi da rana ma ruwan tea ne kawai a cikina....
*FATIMA SUNUSI RABIU*