Tambaya: Miye Hukuncin Masu Karatun Hausa Novels
*_HUKUNCIN MASU KARATUN NOVELS_*
*_TAMBAYA (89)❓_*
*_As salami Alaikum, malam tambayata itace mutum xai iya karanta littafin novel kokuma babu kyau_*
*_AMSA❗_*
*_Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuhu_*
*_Alhamdulillah_*
*_Novel, kamar yanda turawa suka fada a dictionary, shine abinda suke kira da kirkirarren labari wanda tsayinsa yafi gajerun labarai_*
*_Ma'ana: shi novel karyace (fictional story) da ake kirkira don a tsara labarin da zai ja hankalin mai karatu_*
*_Yawancin malamai sunce karanta Novel bata lokaci ne musamman la'akari da cewar labaran karya ne a ciki kuma bai dace ga cikakken musulmi mai imani ya kyale Qur'ani da sauran littattafan addini a gefe guda sannan ya shagala da karatun da bazai amfanar dashi ba_*
*_Idan labari kike son ji to ki karanta Qur'ani domin kuwa kashi daya Tauhidi ne, kashi daya Shari'ah ce sannan kuma daya kason labarai ne don su zamo darasi a garemu_*
*_Ga ladan karatu (na kowanne harafi lada 10 ga kuma sanin ilimin dake cikinsa - wanda kowanne ilimi akwai shi a cikin Qur'ani)_*
*_A shawarce; ki maida hankali wajen karatu, fahimta da tadabburi a cikin ayoyin Qur'ani mai girma, ki duba hadisai, ki karanta littattafan hukunce hukuncen jinin mata (Haila, Istihada, Nifas), ki gyara yanda zaki bautawa Ubangijinki ta hanyar karantar Siffofin yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yake sallah (Sifatus Salatin Naby na marigayi Nasiriddin al-Albany), ki karanta littafin aqidah, ki duba littafin Hisnul Muslim domin fa'idantuwa da addu'o'in yau da gobe_*
*_Amman yawancin Novels idan kina karantasu babu abinda zasu kara miki sai buri da son cimma matsayin wata da ta burge ki a cikin labarin, hakan kuma zai iya kaiwa ga rashin godewa ni'imar da Allah ya baki, kuma yawancin littattafan Novels akwai kalaman batsa a ciki wadanda bai kamata ace musulma tana karantawa ba tunda shi ji, gani da zuciya duk ababen tambaya ne a ranar Alqiyama kamar yanda Allah Azzawajallah ya fada;_*
(إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا )
الإسراء (36) Al-Israa
*_"...Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya."_*
*_Akwai wata daliba ta da na ga tana karanta Hausa Novel, ina musu lecture ita kuma Novel yana koyar da ita, kanta a sunkuye a kasan benci, naje na amshe littafin, na ga duk kalamai ne wadanda bai dace ta bata lokaci tana karanta su ba. Don na nunawa sauran daliban maza da mata illar karanta Novel din sai na ce ta fito ta karanta, kasawa tayi. Nace, wannan shine illar karanta Novel, iyayenki sun turo ki don ki karanta Chemistry, Physics, Biology amman kin bige da karanta Kishi kumallon mata kashi na 1, na 2 da na 3_*
*_To kema irin dai shawarar da na bawa dalibar can ta wa, ita zan baki: kada ki kuskura ki karanta abinda zai sa kiyi da na sani a rayuwarki. Shi lokaci tsada ne dashi_*
*_Wannan shine shawarar da zan baki a matsayinki na yar uwa ta musulma_*
*_Wallahu ta'ala a'alam_*