Daga Aliyu Samba
A ƙasa da shekara guda da rantsar da shi a matsayin Shugaban ƙasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi ayyukan da tasirin su ya amfani ƴan Najeriya ta fuskoki daban-daban na rayuwa.
Duk da baza a bugi ƙirjin cewa an shawo kan duk wata matsala da ta addabi ƙasar nan ba, amma cikin ƙasa da shekara guda, an ɗau saitin da ya warware matsaloli da yawa da aka haifa a shekaru takwas ko sama da haka wanda suka cigaba da wanzuwa tsawon lokaci.
Mafi girman matsalar da ta addabi ƙasar nan kuma ta shafi kusan kowanne ɗan ƙasa ita ce batun karyewar darajar Naira, da ta sanya kayan masarufi tashin gauron zabi a faɗin ƙasar. Yanayi ne da ƙwararru a fannin tattalin arziƙi suka jima suna jan hankalin gwamnatocin baya dan su gujewa jefa ƙasar cikin halin da aka tsinci kai a ciki.
Rashin ɗaukar matakin da ya dace ya sanya Darajar Naira tayi ƙasa a duniya, musamman in aka kwatanta da Dalar Amurka, wanda kusan da ita ne ake hada-hadar kudi yayin shigo da kayayyakin bukatar al'umma na yau da kullum.
Matakin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta É—auka ya saita darajar Naira zuwa kaiwa ga tudumin tsira, wanda a yanzu haka farashin yana ₦1,117 akan kowacce Dalar Amurka 1,wanda in aka kwatanta da tashin da Dalar Amurka tayi a baya, sai da ta kai har ₦2,000 kan kowacce Dala 1.
Abinda yan Najeriya ke ta tambaya yanzu shine, yaushe farashin kayayyakin masarufi zasu sauka tun da an É—auki matakin da a kullum zai É—aga darajar Naira ya karya Dalar Amurka?
Amsar a bayyane take, kamar yadds ya faÉ—a yayin shan ruwa da sashen yan jam'iyyar APC a fadar gwamnati dake Aso Villa, ya karfafa gwiwar yan Najeriya da cewa tabbas za a samu sauki da sauyi kan farashin kayayyakin masarufi.
Mu cigaba da kyakkyawan fata, da kuma bawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu dukkan goyon baya da zai tabbatar da mu zuwa ga ƙudirin sa na ''Sabuwar Najeriya'' don inganta tattalin arziƙi da kuma wadata ƴan Najeriya da dukkan ababen more rayuwa.
Allah ya taimaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Allah ya taimaki Najeriya.