Abinda ya kamata ku sani akan Cutar Herpes Simplex Virus
Cutar Herpes Simplex Virus
Kamar yadda na fadamuku a wasu cikin rubututtukana na baya cewa akwai tarin cuttuka masu hatsari da muni da ake iya dauka ta hanyar saduwa wadanda in aka kallesu da kyau suma ya dace a tsoracesu kamar yadda ake shakkar cutar kanjamau.
Munde ji illar Human papillomavirus daka iya haddasa cutar cancer mazakuta da kuma cancer bakin mahaifa wacce kuma ta hanyar saduwa itama ke yaduwa.
Toh shima Herpes simplex larura da virus ke haddasawa. Wanda virus din ya kasu gida biyu; HSV type 1 da kuma HSV type 2.
Hsv 1 shi baki yake kamawa wanda yawanci idan kaima meshi kiss ko oral sex idan yana ko tana da Hsv 2 toh shikenan anan ake diba.
Hsv 2 kuwa wanda ke shafar farji shi kai tsaye ta hanyar saduwa ake dauka... Dukkan su suna da illa toh ammafa HSV 2 din na yafi muni.... wanda da yawa cikin matasan mu maza da mata ke fama ayau saboda muggan dabi'un su.
Wannan tasa ko yaushe ake jan hankali mutane musamman matasa akan ire iren wadannan risky behavior din.
Abun tsoron shine kafin bayyanar kurjin abaki ko kuwa kuraje ajikin azzakari ko farji a wasu yana daukar lokaci... kuma ahaka zasuje suita yadawa tunda yawancin wadanda ke kamuwa mutane ne marasa kamun kai.
Babban abun karin tsoron shine gaskiya wannan larurar BATA da MAGANI.... duk wanda ya kamu tohfa har tsawon rayuwa ce... zaike fama da kuraje masu tsananin kaikayi tare da ruwa wani lokacin me karnin tsiya... baya ga hatsarin saurin kamuwa da kanjamau da kuma Human papillomavirus da mutum ke ciki wanda akarshe ana iya samun mutum da cutar cancer
Sannan koda aure mutum yai wajibi yake amfani da condom domin duk wanda ya sadu da ita zata dauka... kai inde da kurajen toh ko rungumarta yai sakamakon ruwan da kurajen ke fitarwa nan ma zata iya ta dauka....
Ina dadi ace ka dauma ahaka kaida matarka mutum ace saida condom...
Sannan karin hatsarin in matar ta kamu tohfa nan ma jaririn da zata haifa saide ai aiki a cirosa in haihuwa taxo inba haka ba matukar aka bari ya fito ta farji toh zai kamu kuma idanunsa na iya fuskantar matsalar gani...Don haka ba karamin abune ba.
Manyan likitoci suke iya ganosa su bambancesa da sauran kuraje bama tare da ansa mutum wasu gwaje gwaje ba... rashin zuwa babban asibiti tare da tsayawa kananun asibitoci... inda basu fahimci kan matsalar ba shikesa wani kaji yaje yaita kar6ar magunguna da allurai antibiotics dana rage zogi yana sha amma abanza bai warke ba. Domin baxasu ta6a warkewa ba tunda Herpes virus ne ba bacteria ba.
Don haka magunguna dangin antiviral drugs shi likitoci ke ba mai dauke da ciwon... domin rage radadi da kiyaye nacin kurarrajin... tare da takaita hatsarin yada ciwon daga macen zuwa ga mijinta ko kuma daga miji manemin mata zuwa iyalinsa
Inba haka ba aka barshi toh mutum fa na iya haduwa da cancer. Kuma mu tuna de babu magani babu kuma allurar rigakafinsa.
Magani daya ne: Kowa ya tsaya ga muharraminsa.