Ad Code

Adamsy Hausa Novel Complete

Adamsy Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ADAMSY*

 

 

 

 

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

*GARGAƊI*

 

Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.

 

 

*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*

 

Ina mai matukar ƙara godiya ga Allah subhanahu wata’ala da ya bani ikon fara wannan sabon littafin nawa *ADAMSY* idan akwai wani sharri wanda zai amfane ku ina roƙon Allah kada ya bani ikon gama rubuta wannan labarin,ina roƙon Allah ya bani ikon rubuta abunda zai amfani al’ummar musulmi. Alkhairin da ke cikin wannan labarin Allah ya sada mu da shi, ina roƙonku kada kuyi amfani da abinda ba alkhairi ba da kuka ci karo da shi a cikin littafin nan, kuyi amfani da darasin da ke ciki, sannan ku tsoraci mai sunan ƙeya (Danasani) dake cikin littafin, ina fatan zaku karɓi wannan littafin na *ADAMSY* kamar yadda kuka karɓi littafin Inteesar koma fiye da yadda kuka karɓi Inteesar.

Yan Biyu Maciza Hausa Novel Complete

 

Page0️⃣1️⃣

 

Aguje ta fito daga cikin ɗakinta tana ihun naman taimako,mayafinta ne ya faɗi ya harɗe ƙafarta wanda hakan yasa ta faɗi ƙasa.

 

Fitowa yayi daga ɗakinta yana ƙwala mata kira.

 

“Husnah! Husnah!! Husnah!!!”

 

Tana ganinsa ta rintse idanunta tare ƙwalla ƙara, kanta ta cusa a tsakanin gwuiwarta. Amina ce ta fito daga ɗakinta sakamakon jin ihun Husnah ke yi, cewa kin mamaki ta kalle su tare da furta cewa

 

“Lafiya kuwa amaryar da aka kawo daddaren nan waɗanda suka kawo ki ma ko awa ɗaya basu yi da tafiya ba ki fito kina ihu me ke faruwa?”

 

Jin muryar Amina ce yasa ta Husnah ta miƙa da sauri ta nufi bayanta, ɓoyewa take a bayanta kamar wacce za’a kama.

 

“Adams wai me ke faruwa ne? Naji ihunta ne yasa na fito cikin tashin hankali dan ganin me ke faruwa, amma abin mamaki sai naganku ku biyu akwai abinda ka mata ne?”

 

Girgiza kansa yayi cikin damuwa ya ce,

 

“Nima abinda ke bani mamaki kenan, lokacin da muka shigo da abokina tana tare da ƙawayenta, bayan anyi siyen baki sun tafi sai na bisu na raka su, kuma iyakar ƙofar falon nan na tsaya suna fita na rufe ƙofar, dawowa ta yanzun nan ina ina shiga naga ta kalle ni ta ƙwalla ƙara.”

 

Amina ce ta janyo Husnah daga gefenta, zuba mata ido tayi tare da cewa

 

“Husnah me ke damunki ne?”

 

Kuka kawai take mara sauti, idanunta kuwa kamar an buɗe fanfon ruwa. Ganin bata da niyyar yin magana ne yasa Amina ta kalli Adamsy tare da cewa

 

“Ko dai tana da wata larurura ce?”

 

Girgiza kai yayi tare da cewa

 

“Bana tunanin akwai wata larura a tattare da ita, dan da akwai da Ummanta ta sanar da ni”

 

Kallon Husnah Amina tayi tare da cewa

 

“Kinga yanzun dare yayi ƙarfe goma sha biyu saura kwata, ki je ku kwanta.”

 

Ba musu ta nufi ɗakinta yayin da shi kuma ya sunkuya ya ɗauki mayafinta yabi bayanta suka wuce.

 

Tura ƙofar ɗakin ta yi ya shiga yana biye da ita a bayanta, bakin gadon ta zauna kanta a sunkuye, jin muryarsa tayi ya kira sunanta a hankali.

 

“Husnah”

 

A hankali ta ɗago kai ta kalle shi, gangar jikinsa ne kawai nasa amma kansa sam baiyi kama da na mutane ba, dan ƙaho ne ta gani a kansa ga fuskarsa buzu-buzu da gashi, idanunsa kuwa jazir, wani irin ƙara ta sake saki wanda ya fi na ɗazu a guje ta ruga sai da ta ci karo da ƙofa kafin ta fita.

 

Amina da ke ƙoƙarin shiga ɗakinta ne ta jiyo ihun Husnah, dakatawa ta yi tare da juya bayant, idanunta suka sauka a kan Husnah da ta fito a guje kafin ta ankare har Husnah ta rungume ta tana kuka, cikin mamaki ta ce,

 

“Husnah me ya ke damunki ne haka? Kina ta ihu baki ga dare yayi ba ko so kike ki tara mana jama’a a daren nan dan Allah ki je ki kwanta.”

 

Girgiza kai tayi tare da cewa

 

“Wallahi bazan bishi ba tsoro yake bani”

 

“Ban gane tsoro yake baki ba, ba mijinki bane?”

 

Shiru tayi bata sake magana ba, Amina ce ta maida dubanta ga Adamsy dake tsaye yana kallonsu ta ce,

 

“Wai me ke faruwa ne? Ya daga kawo maka amarya yau sai matsaloli ke ta kunnowa tunda jama’a suka watse?”

 

“Amina bani da amsar tambayar da kika mani, dan nima haka naganta tunda na shiga ta kalle ni take ta ihu.”

 

Jinjina kai tayi tare da cewa

 

“Kodai tana da taɓin hankali ne?”

 

Girgiza kai yayi tare da cewa

 

“Bana tunanin haka, sai dai idan wani abin ne daban, amma Husnah bata da kowane taɓin hankali.”

 

Amina ce ta janyo hannun Husnah suka ƙarasa jikin kujera, zaunar da ita tayi akan kujera tare da cewa

 

“Husnah me ke damunki? Dama kina irin haka ne?”

 

Kai ta girgiza tare da cewa

 

“Bana komai shine ya ke canza siffarsa idan muka shiga ɗaki, yake firgita ni”

 

Kallon juna sukayi Adamsy da Amina suna mamakin jin kalamanta, inda ta cigaba da cewa.

 

“Ke Aunty bai taɓa canza maki siffarsa ba, idan kina tare da shi?”

 

Kai Amin ta girgiza mata tare da cewa

 

“Mijina ba wata siffa da yake da shi ko yake canza mani, ke dai sai dai kina da wata larura ne da yasa hakan take faruwa da ke, to wane irin canza siffa kamar wani aljani?”

 

Da sauri ta kalli Amina tare da cewa

 

“Eh wallahi Aunty ai kamar alhani haka nake ganinsa.”

 

Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

 

“Ke kin isa kiga aljani da ido ko?”

 

Amina ce tayi mata maganar tana nuna ta da yatsarta manuniya, inda ta cigaba da cewa.

 

“Kinga ki kwantar da hankalinki ta yiwu ma mafarki kikayi kike tsorata, idan kuma ba haka ba tabbas kina da ciwon hauka.”

 

“Wallahi gaskiya nake faɗa maki ki yarda da magana ta, ni bani da ciwon hauka lafiya ta ƙalau, ni da ido na na ganshi bayan ya raka abokansa ya dawo yana shie ya fara tsoratar da ni. Amma lokacin da suke nan bai yi komai ba ya tsaya a yadda yake, bayan tafiyarsu ne sai ya fara canza siffa kamar na aljani.”

 

Adamsy kam zuba mata ido yayi yana kallonta, ya ma rasa abin faɗa, kai tsaye ya koma ɗakin zuciyarsa a cunkushe.

 

Amina ta dinga rarrashin Husnah tare da bata haƙuri kam ta tashi da daure ta bi mijinta, sai da ta tabbatar ta ɗan saki jiki sannan ta raka ta har bakin ƙofar ta tura mata ƙofar, ta shiga sannan ta janyo masu ƙofar ta wuce zuwa ɗakinta.

 

A hankali cikin tsoro Husnah ta ɗago idanunta ta kalli Adamsy, sai ta nufi ƙofar fita a guje, biyo bayanta yayi shima cikin hanzari yasha gabanta, wanda hakan yasa ta kalle shi tsabar tsorata yasa ta zube wajen ƙasa sumammiya.

 

Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerar dake falon tare da yin tagumi yana faɗin

 

“Na shiga uku”

 

Ruwa ya ɗuko a fridge, ya ɓalle marfin robar tare da yayyafa mata a jiki, a jiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, tare sakin kuka, a hankali ya kira sunanta.

 

“Husnah”

 

Buɗe ido tayi tare da sauke shi akansa, take ta fashe da kuka tana ja da baya cikin tsoro. Ganin haka yasa shi miƙewa ya nufi ɗakinsa, tare da faɗin.

 

“Ki tashi kije ɗakinki ki kwanta, sai da safe.”

 

Daga nan bai sake wata magana ba, ɗakinsa ya shige yana magana shi kaɗai

 

“Wai wannan wane irin daren farko ne? Ace kayi aure ranar da aka kawo maka mata ta dinga gudunka tana tsoronka kamar taga wani dodo? Daren da yakamata ace nayi kwanan farin ciki sai gashi na yi kwanan baƙin ciki?”

 

Babbar rigarsa ya cire ya nufi toilet zuciyarsa cike da saƙe-saƙe iri-iri .

 

Ɓangaren Husnah kuwa tana ganin ya shiga ɗakinsa sai ta miƙe tsaye, a guje ta nufi ɗalibta tana shiga tayi saurin murza key tare da durƙushewa a wajen, ta jingina bayanta da ƙofar ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

 

Kallon agogon bangon da ke ɗakin tayi, ganin ƙarfe ɗaya na dare yasa ta sakin kuka, dan ba zata iya fita a wannan lokacin da da ta fita, amma ina dare ne a tsorace ta ke , ba zata iya fita ba, Nan ta cigaba da kukanta ita kaɗai ba mai rarrashinta.

 

Misalin ƙarfe biyu da rabi na daren ne ta ji barci ya ci ƙarfinta, duk da cewar ita batayi niyyar barci ba amma kuma barci ɓarawo ne lokacin da zai sace ka ma ba zaka sani ba, tashi tayi a hankali ta nufi bakin gadon ta kwanta, ko hasken ɗakin bata rage ba haka ta kwanta dan a tsorace ta ke.

 

Adamsy ma a ɓangaren sa ma bai samu barcin kirki ba, dan tunda ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da ɗauro alwala ya fito, jallabiya ya saka sannan ya shimfiɗa sallaya, sallar nafila ya gabatar raka’a huɗu, ya dinga jera addu’a akan wannan matsalar da ta tunkaro masa, ya daɗe yana addu’a kafin ya shafa, ƙarfe biyu ya kwanta.

 

Misalin ƙarfe biyar na asuba ya farka, ganin ya kusa makara ne ma yasa ya nufi toilet ya ɗauro alwala, shiri zuwa Masallaci yayi inda ya fito dan zuwa sallar asuba.

 

Sai da ya tsaya ƙofar ɗakin Amina yayi mata knocking dan ta farka lokacin sallah yayi, jin motsi alamar ta tashi ne yasa shi tafiya, ya tsaya ƙofar ɗakin Husnah da niyyar buga mata ƙofar, amma tuna cewa zata iya rikece mashi da asubar nan yasa shi fasawa, yayi ficewarsa dan zuwa masallaci.

 

Sai ƙarfe shida Husnah ta farka daga barci, ganin ta makara ne yasa ty tayi gaggawa ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallar asuba.

 

Tana idar da sallar ta miƙa tsaye ta ɗauke sallayar ta ajiye, bata cire hijabin jikinta ba ta nufi ƙofa, a hankali ta buɗe ƙofar ta leƙo da kanta, ganin ba kowa a falon yasa ta koma ciki da sauri ta ɗauko hand bag ɗin ta da wayarta ta fito zuwa falon cikin sanɗa take tafiyarta dan kada a ji motsinta, kai tsaye ta nufi harabar gidan sauri-sauri gudu-gudu haka ta ƙarasa bakin gate ɗin, mai gadin da yaga zata fita ne yayi saurin buɗe mata ƙaramar ƙofar ta fice.

 

Ajiyar zuciya ta saki ganin ba wanda ya gabata har ta fice, da sauri ta dinga tafiya dan barin layin kada ma Adamsy ya ganta.

 

Bai dawo daga masallaci ba har ƙarfe bakwai yayi sannan ya dawo gidan, ɗakinta ya nufa har ya kai hannu zai murɗa handle ɗin ƙofar yana tsoron abinda zai biyo baya dan haka sai ya fasa, ɗakin Amina ya nufa inda ya same ta zaune tayi tagumi.

 

Sallama yayi ta amsa masa sallamar tare da cewa

 

“Barka da safiya”

 

“Yauwa kin tashi lafiya?”

 

Murmushi tayi masa tare da cewa

 

“Lafiya ƙalau wallahi, ya kwanan amarya? Fatan kun tashi cikin ƙoshin lafiya”

 

Shiru yayi yana tunani wato ita a tunaninta ɗaki ɗaya suka kwana shi da Husnah, murmushin takaici yayi tare da cewa

 

“Lafiya lau”

 

“Masha Allahu, ina dai fatan bata sake irin abunda ta aikata jiya ba?”

 

Shiru yayi yana nazari, sannan ya bata labarin abinda ya fsru, na bayan ta raka Husnah ɗauki ta tafi.

 

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, akwai babban matsala, wani irin masifa ce wannan, nifa ina kyautata zaton cewa yarinyar nan tana da taɓin hankali ne”

 

“Ki daina wannan tunanin Husnah bata da taɓin hankali, bari na je na duba ta.”

 

Daga nan ya nufi ƙofar fita ya fice

 

Kai tsaye ɗakin Husnah ya nufa, murɗa handle ɗin ƙofar yayi ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, ganin bata nan ne yasa yayi tunanin tana cikin toilet, dan haka sai ya zauna a bakin gadon yana jiran fitowarta.

 

Tsawon mintuna goma yana zaune baiji alamar motsin mutum a cikin banɗaki ba, dan haka sai ya karasa jikin ƙofar toilet ɗin tare da ƙwanƙwasawa, jin shiru yasa shi cewa

 

“Husnah kina ciki ne?”

 

Jin shiru yasa shi tura ƙofar tare da kutsa kai ciki, watan ba ita ba alamarta, cikin hanzari ya fito yana ƙwala mata kira.

 

“Husnah! Husnah!!!”

 

Kitcheen ya nufa bata nan yana dawowa falon sukayi kiciɓis da Amina ta tace ,

 

“Naji kana ta ihun kiran Husnah ina ta shiga ne?”

 

Cikin yanayin damuwa da yake ciki tun jiya ya ce,

 

“Da alama ta fita baya gidan nan.”

 

“Subhanallahi bata gidan nan? To ina ta tafi?”

 

“Baice komai ba ya nufi ƙofar fita, tun kafin ya ƙarasa bakin gate yake ƙwaƙwalwa mai gadinsa kira.

 

“Mudi! Mudi!! Mudi!!!

 

Aguje Mudi ya karaso tare da durƙusawa ya ce,

 

“Yallaɓai gani”

 

“Baka ga Amaryar da aka kawo ya fita ba?”

 

“To ai ni bansan wace ce Amarya ba, wata dai ta fita da safen nan tun gari bai gama haske ba, dan lokacin ma kana masallaci baka dawo daga sallar asuba ba.”

 

“Kai nagaukacin ina ne zaka barta ta tafi bayan jiya aka kawo ta?”

 

“To ni ina zansan ko wace ce kawai zata fita na buɗe mata gate, dan tafi awa ɗaya da…”

 

Tasawa ya daka masa

 

Shut off! banga amfaninka ba sha sha sha kawai a kawo yarinya jiya kabbarta ta fita.”

 

Ya ƙarasa maganar yana komawa cikin gidan.

 

“Anya Alhaji wannan wace irin Amarya ce da za’a kawo ta jiya daddare tayi asubancin fira anya tana da hankali kuwa? Dan na ganta wata firgitacciya da ita.”

 

Komawa yayi da hanzari ya nufi ɗakinsa, key motarsa ya ɗauka, yana shirin fita yayi kiciɓis da Amina da ke ƙoƙarin shigowa.

 

“To yanzu ina ta tafi?”

 

Ta ƙarasa maganar cikin yanayin damuwa

 

“Bari dai na fita nemanta”

 

Daga nan ya fita da hanzari tun kafin ya ƙarasa wajen motar yake cewa mai gadi ya buɗe masa gate.

 

“Dalla buɗe mani ƙofa da sauri sha sha sha da baisan aikinsa ba.”

 

Mudi ya miƙe da sauri yana wangale masa gate yana magana

 

“Allah ya huci zuciyarka ba ni nakai zomon ba rataya aka bani.”

 

A guje Adamsy ya fita da motar daga gidan ya ɗauki hanyar fita daga layin.”

 

Close Menu