Ad Code

A Jini Take Hausa Novel Complete

A Jini Take Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

A JINI TAKE

*(IZZATA)*

 

By

_*Zarah Maitama (Mhiz Innocent)*_

 

 

 

_Bismillahir rahmanir raheem_

 

 

_*CHAPTER ONE*_

Page _01

 

 

 

__La’asar ce sakaliya dan kuwa rana ma ta kusa faÉ—uwa. Babu laifi akwai iska, irin iskar nan me daÉ—i, duk da ba lokacin sanyi bane, se dai yanayin garin sosai yayi kyau da kuma daÉ—i. ‘Yan mata ne guda biyu ke tafiya sanye cikin hijab dogo har Æ™asa kala É—aya. ÆŠayar da niÆ™ab a fuskarta ta saÆ™ala jaka a kafaÉ—arta, yayin da É—ayar ke sanye da hijab kawai. Hannun wadda ke sanye da niÆ™ab riÆ™e yake da wani Æ™aramin kyakkyawan yaro, fari Æ™all da shi, wanda ba ze wuce 5years ba sanye cikin uniform, wanda hakan ya alamta min cewar daga Islamiyya suka dawo. A hankali na kai dubana zuwa fuskar wadda babu niÆ™ab a fuskarta, kwata_kwata kyakkyawar fuskarta ta babu annuri, da alama wani abun ne ya É“ata mata rai ko kuma akayi mata. Se dai duk da yadda fuskarta ta ke a haÉ—e hakan be hanani ganin tsagwaron kyawun fuskarta ba, wadda idan ba dan shigar da ke jikinta ba da kai tsaye zan iya kiranta da balarabiya, dan kuwa komai na ta yayi kama da nasu, dara_daran idanu masu É—auke da baÆ™ar Æ™wayar ido me matuÆ™ar É—aukar hankali da wani irin Æ™yalli, dogon siririn hancinta da ke zaune É—ass akan fuskarta kamar an zama, se kuma É—an Æ™aramin red lips É—inta me matuÆ™ar kyau wanda shi ne yafi komai Æ™awata fuskarta. Har suka Æ™arasa gida babu wadda tace da er uwarta komai.

 

Babban gida ne me kyau sosai, duk da ba wani ƙyale ƙyale ne a gidan ba amma kasancewarsa me girma da kuma yanayin ginin gidan na zamani ne yasa ya ƙawatu matuƙa. Tun a parlour AFAAF ta jefar da jakar hannunta da tun da suka fito daga makaranta ta kasa maƙalata a kafaɗa se riƙeta tayi a hannu, wucewa ɗaki tayi kamar wadda aka kora. Ammi ta bi ta da kallo kafin ta dawo da kallan nata kan AFRAH dake kwance niƙab ɗinta tace

 

“Ke lafiya kuwa? Yau kuma me aka yiwa Afaaf?” Dariya wadda aka kira da Afrah tayi daidai lokacin da ta ida kwance niÆ™ab É—in fuskarta, wanda hakan ya bani damar ganin kyakkyawar farar fuskarta wadda kallo É—aya na mata na gane ita É—in er biyun Afaaf ce, dan kuwa kamarsu É—aya sak, kamar yadda Afaaf ke da manyan idanu haka Afrah ke dasu, dogon hanci da Æ™aramin baki me kyawun gaske haka Afrah ke da shi, ba dan tsayawa nayi ina kwatanta muku kamanninta ba da bazan iya gano wani banbanci a tsakaninsu ba, saboda kamarta su ta É“aci, banbancin da zan ce na gano guda É—aya ne shi ne, saÉ“anin Afaaf da ke É—auke da baÆ™ar Æ™wayar ido ita Afrah brown ne da ita me maiÆ™o.

 

“Tubarkallah Masha Allah!” Shi ne abin da na faÉ—a sanda na sake tabbatar da lallae waÉ—annan en biyun irin waÉ—annan da ake kira da identical twins ne, se dai su waÉ—annan nin sun fita daban ta hanyoyi da dama, a Æ™iyasce ba zasu wuce 17 years ba, kowaccensu na da kyawun jiki me kyau, hatta kuma da jikinsu ba zaka iya banbance wani banbanci ba dan kuwa dukansu basu da Æ™iba.

 

“Ammi ita da Gwani ne..” Afrah ta faÉ—a da siririyar muryarta me daÉ—i wadda ke É—an rawa a duk sa’ilin da take magana, zaka É—auka tsoro ko wani abun makamancinsa ke sanya muryarta ta rawa, se dai ba haka bane, haka muryarta ta take a halitta, hakan kuma shi ke Æ™ara Æ™awata muryarta ta ta sake zama ta daban.

 

“Gwani kuma? Me ya faru? Wani abun ta sake yi?” Ammi tayi tambayar a jere. Girgiza kai Afrah tayi kafin tace

 

“A’ah Ammi, kawai dai an chanja mana malami ne, yanzu Gwani AFFAN ne malamin ajinmu.”

 

“Auu shi ne take fushi saboda makarantarta ce ko kuwa me?” Ammi ta faÉ—a a É—an zafafe. Se da Afrah ta É—an yi kalar tausayi da fuskarta gudun kada Ammin ta fusata sosai sannan tace

 

“A’ah fa Ammi, ita abin da ya É“ata mata rai yadda ya aiko wai a faÉ—a gobe ze fara da karÉ“ar hadda.” Tsaki Ammi ta ja tana girgiza kai, wannan hali na Afaaf na Æ™ona mata rai wani lokacin, kamar ba za tace komai ba se kuma tace

 

“Idan ta so kada tayi, zata haÉ—u da ni ko da Abbanku.” Daga haka ta miÆ™e ta bar parlourn. Bin ta da kallo Afrah tayi ba tace komai ba se dauke ajiyar zuciya da tayi sannan ta dawo da dubanta cikin É—akin kana ta miÆ™e ta wuce É—akinsu.

 

 

.. Se da Afrah ta gama komai sannan ta koma kan gado, ta É—auko Qur’an É—inta dake cikin jaka ta buÉ—e ta soma karantawa. Tana cikin yin karatun Afaaf ta fito daga toilet da alama wanka tayi, ta Æ™arasa ta shirya cikin kayan bacci sannan ta dawo kan gadon tana Æ™oÆ™arin kwanciya. Rufe Qur’an É—in Afrah tayi sannan tace

 

“Me za ki yi?” Se da ta harari gefe sannan tace

 

“Bacci zan yi.” Karo na farko kenan da na fara jin muryar Afaaf wadda itama cikin ikon Allah muryarta su iri É—aya ce, dan idan wata a cikinsu ma tayi magana ko da ka sansu ba zaka banbance ba se dai idan ka ga fuskarsu.

 

“Malama ki É—auki Qur’an ki yi karatu, kin san dai halin Gwani.” Se da ta tura baki sannan tace

 

“Ai yau so nake na Æ™ure shi wallahi, mutum se faÉ—in rai da nuna shi wani ne bayan ba kowa bane. Ban da tsabar iyayi meye na wani cewa ze karÉ“i hadda a ranarsa ta farko a ajinmu? Ni babu haddar da zan yi.” Ta faÉ—a tana neman waje zata kwanta. Da sauri Afrah ta riÆ™ota tace bayan ta haÉ—e rai

 

“Lulu ki fita a idona wallahi. Gwanin kike faÉ—a wa haka? Ki tashi malama ki yi karatu kin san dai ba É—aukar iskancinki ze yi ba.”

 

“Don Allah Didi ki Æ™yaleni.” Afaaf (Lulu) ta faÉ—a a ranta tana sake tuna wannan Æ™arfa_Æ™arfar da Gwanin ke Æ™oÆ™arin yi. Cika hannunta Didi tayi kana ta haÉ—e fuskarta waje É—aya ta cigaba da haddarta a zuciya. Ita kuwa Lulu kwanciyarta tayi, se dai yanayin yadda ta ga fuskar Didin ya hanata yin baccin. Tsaki ta ja a hankali ta miÆ™e zaune tana tura baki. Ita kuwa Didi ko kallanta ba tayi ba, duk da dama ta san Lulun ba zata iya kwanciya tana fushi da ita ba. Sauka Lulu tayi ta É—auko Qur’an É—inta ta koma kan gadon itama, bata kalli Didi ba ta soma karatunta a zuci, se dai ba haddar take yi ba, dan kuwa ta riga ta Æ™udurcewa kanta ba za tayi haddar ba, se dai kawai ta shiga muraja’a hankalinta kwance. Ta riga Didin idarwa, da ta ga har lokacin bata kalleta ba se ta É—ora kanta akan kafaÉ—ar Didin da itama take kan aya ta Æ™arshe a maimaita haddar da take yi. Se da ta idar sannan ta saka hannunta ta buge kan Lulun. Tura baki Lulu tayi kafin tace

 

“Kai Didi, nayi karatun fa. Kiyi haÆ™uri.” Murmushi Didi tayi dan itama ba wai tana fushi da Lulun bane kawai dai ta É“ata ranta ne dan tayi karatun, dan haka tace

 

“Toh na ji, amma dai ki dena abin da kike yi musamman akan Gwani Affan, ni ban san me ya tare miki ba!” TaÉ“e baki Lulu tayi dan ita sam bata da buÆ™atar jin magana akan Gwanin, ko a makaranta ne kuwa ballantana a gida.

 

“Haka kawai fa Didi, É—aga kansa yayi yawa kuma..!”

 

“Ni kam ya isheni haka nan Afaaf, ke kodayaushe zancenki kenan!” RiÆ™o hannun Didi Lulu tayi kafin tace

 

“Pls Didi mu bar maganar nan, Allah kuwa raena É“aci yake yi.”

 

“Naa ji.” Didi ta faÉ—a tana Æ™oÆ™arin miÆ™ewa. LangaÉ“ar da kai Lulu tayi kafin tace

 

“A’ah fa Didi, ta yaya zan san kin haÆ™ura.. Smile..” ta faÉ—a tana murmushin da ya sake fiddo da ainahin kyawunta. Itama Didin murmushin tayi wanda hakan ya sake ruÉ—ani akan tsananin kamarsu da ta sake fitowa fili, dan komai na su iri É—aya ne hatta da murmushin kuwa.

 

 

 

… Washegari wajen Æ™arfe 2 da rabi Didi ta gama shirin Islamiyya, tana kallan Lulu da tun dawowarsu daga boko ta kwanta a kan gado ita a lallai bata da lafiya. Kasancewar sun makara ne ya sanyata saurin É—aura niÆ™ab É—inta a jikin Æ™aton mudubinsu me kyau sannan ta É—auki jakarta ta fito. Kallanta Ammi tayi tace

 

“Har kun shirya? Ba zaki tsaya ki ci abinci ba?”

 

“A’ah Ammi sauri nake yi, kada na makara. Idan na dawo zan ci..”

 

“Toh Allah ya tsare..” ta Æ™are maganar tana kallan hanyar É—akinsu

 

“Ina Afaaf É—in?” Kallan É—akin tayi sannan tace

 

“Ammi wai bata da lafiya..” Kafin Ammin ta sake cewa komai Abba ya shigo cikin É—akin da sallama. Dogon babban mutum wanda kallo É—aya zaka masa ka san twins É—in nan shi suka biyo, dan kuwa shi ma a kallan farko zaka gano kyawun da yake da shi. Dukkansu suka amsa masa sallamar kafin Little ya tafi ya rungume shi.

 

“Abba sannu da zuwa.” Afrah ta faÉ—a.

 

“Yawwah Didi an shirya ne?” Ya faÉ—a mata sunan da yawanci en gidan ke kiranta da shi, wanda har shi É—in ma wani sa’in ya kan kirata da shi.

 

“Ehh Abba..”

 

“Toh Allah ya bada sa’a.. A’ah ina Afaaf?” Ya tambaya shi ma. A wannan karon ma se da ta sake kallan Æ™ofar É—akin nata sannan tace

 

“Abba wai bata da lafiya.”

 

“Ji min ja’irar yarinya, sauÆ™in ze sameta ne tana daga kwance.. Kai Little maza je ka tasota ta sha magani sauÆ™in ze sameta acan.” Babu musu kuwa Little ya zura da gudu zuwa cikin É—akin. Da Æ™arfi ya soma kiran

 

“Lulu! Lulu!!” Yana saka hannu ya soma yaye Æ™aton blanket É—in da ta rufa da shi. Duka ta kai masa sanda ya sake buÉ—e murya ya kira sunanta. Be kuma saurara ba ya É—ora da

 

“Abba yace ki fito mu tafi makaranta.” Ya faÉ—a da muryarsa me daÉ—i duk da akwai É—an tsami kaÉ—an a cikinta. Dukan da ta masa ne ya sanya shi kai hannu ya riÆ™e wajen yana kwaÉ“e fuska

 

“Allah se na faÉ—a wa Abba..” ya faÉ—a yana shirin yin gaba.Da sauri ta riÆ™o shi ta É—an sassauta fuskarta kaÉ—an kafin tace

 

“Ka je kace bani da lafiya..” maÆ™e kafaÉ—a yayi yana faÉ—in

 

“A’ah..” Tsaki ta ja dan ta san in dae ta biyewa wannan yaron se dai faÉ—an da Abban ze nata ya Æ™aru, hakan ne ya sanyata sakinsa kawai ta shiga shiryawa tana sake cika tana batsewa. Ta san halin Abba sarai, gudun kada ya gane ciwon ba na gaske bane ya sanya ta yin kalar tausayi da fuskarta hadda aro Æ™wallar Æ™arya cikin idanunta sannan ta fito, a hankali tace

 

“Abba sannu da zuwa” ta faÉ—a da muryarta da ta sake yin rawa fiye da yadda take. Cikin tausayawa yace

 

“Yawwah. Bari na É—akko miki magani ki sha se ku wuce” Tun da dai ta san makaranta ce dole se taje tun da Abba ya saka baki ya sanyata faÉ—in

 

“A’ah Abba ai na sha, ciwon kai ne dama kuma ya warke”

 

“Toh madallah. Se kun dawo Allah ya tsare.” Didi da Little kaÉ—ai suka iya amsawa ita kuwa Lulu ta kasa faÉ—in komai dan gaba É—aya hankalinta ya tafi kan yadda zasu Æ™arke ne da Gwani bayan ba tayi hadda ba, duk da yadda hankalinta ke a kwance da rashin yin haddarta ta amma yanzu se da ta ji wani tsoro tsoro na neman kamata tayi saurin basarwa tana sake cika tana batsewa. Ita kuwa Didi dariya kawai take yi a É“oye dan kada Lulun ta gani yanzu se ta sake fusata.

 

“Yau ba zaki biyawa Masoyiyarta ki ba?” Didi ta faÉ—a tana kallan Lulu sanda suke dab da wuce gidansu Æ™awar Lulun. Hararar gidan tayi kamar shi ne ya mata laifi sannan tace

 

“Ehh É—in..” ta faÉ—a tana wuce gidan ma da sauri. Ba tace komai ba Didi se bin bayanta da tayi suka cigaba da tafiya. Sakin hannun Didi Little yayi ya koma kusa da Lulu yace

 

“Ki riÆ™eni kin ji!”

 

“Ba za a riÆ™e ba” ta faÉ—a tana maka masa wata uwar harara, dan yau É—in gaba É—aya haushin kowa take ji, musamman ma Little É—in da kamar shi ne ya janyo mata, da yace bacci take da yanzu tana can a matsayin mara lafiya tana bacci hankalinta kwance. A yanzu kam dariya Didi tayi sosai ta cikin niÆ™ab É—inta, ta janyo hannun Little suka cigaba da tafiya. A haka har suka Æ™arasa makarantar..

 

 

 

*** ***

Gida ne da ya amsa sunansa gida, ƙato wanda idan baka sani ba daga kallan farko zaka iya kiransa da ƙatuwar plaza. Haɗaɗɗen gida ne wanda tsayawa faɗar irin haɗuwar da yayi ɓata baki ne, dan kuwa anyi ɓarin kuɗi kamar me, an gina shi cikin tsari da ƙwarewa kamar ba a Nigeria ba. Ko daga Compound ɗin gidan kaɗai se an tashi kanka saboda yadda ta matuƙar ƙawatu da abubuwa kala kala se dai marasa hayaniya. Idan kuwa tun farko dama a cikin Compound ɗin ka tsinci kanka to fa ba zaka taɓa cewa a Nigeria kake ba. Ƙaton parlour ne da ya lamushe kujeru saiti uku a gefe guda na cikinsa, wanda anan ne aka zuba kayan ado da ƙawa aka ƙawata haɗaɗɗen parlourn da ko na shugaban ƙasa albarka, parlour ne da ya amsa sunansa parlour, parlour ne da a karan farko zaka iya kiransa da aljannar duniya saboda matuƙar haɗuwar da yayi. Akan ƙaramar kujera wani kyakkyawan babban mutum ne dake sanye cikin wata dakakkiyar shadda da kallan farko zaka mata ka san ta lamushe kuɗi na musamman, fuskarsa kuwa a kallan farko baka isa ka ƙayyade adadin shekarunsa ba, saboda yadda jin daɗi da kuma hutu suka lamushe kaso masu yawa daga cikin shekarunsa. Kyakkyawan babban mutum wanda aƙalla ya bawa 50 baya, idanunsa saye suke cikin glass me matuƙar kyau da tsada, wanda yake amfani da shi idan ze yi wani aikin da ya shafi Computer ko waya. A yanzu ma idanunsa na kan hamshaƙiyar waya ne yana dannawa cikin ƙwarewa. A nutse take takowa cikin parlourn, duk da yanayin shekarunta da suka tura hakan be hanata cin kwalliya kamar yarinya er shekara 20 ba, ƙafarta saye cikin wani hill shoe, sanye kuma cikin rantststiyar atamfa me shegen kyau da tsada, ta sha ɗauri irin wanda ake kira da ture kaga tsiya. A haka take takowa zuwa cikin ƙaton parlourn da kafin ƙarasowarta inda mutumin nan ke zaune ta ɗauki sakanni masu yawa. A nutse ta nemi waje ta zauna cikin kissa da kisisina tace

 

“Barka da wannan lokaci YallaÉ“ai.” Se da ya Æ™arasa abin da yake yi cikin waya kamin ya É—ago ya kalleta bayan ya É—an zame glass É—in fuskarsa yace

 

“Barka kadai..”

 

“Aiki ake yi ne?” Ta tambaya tana gyara zama akan haÉ—aÉ—É—iyar kujerar da ke kusa da tasa.

 

“Ƙwarae kuwa. Kin je kin duba abokiyar zaman naki? Bata ji daÉ—i ba.” Se da ta taÉ“e baki sannan tace bayan ta yamutsa fuska

 

“Zan dai shiga, amma yanzu magana ce ta kawoni akan Boy.” Ƙarasa cire glass É—in yayi ya ajje a gefe kamin ya juya ya kalleta sannan yace

 

“Yaya muka yi da ke?” Girgiza kai Hajiya Salma tayi kana tace

 

“A’ah fa YallaÉ“ae, ka sake kwantar da hankalinka ba wani abun yayi ba. Akwai manufofi da dama da suka saka na takura se ya tafi Æ™asar waje karatu, misali raba shi da Abokansa na nan É—in waÉ—anda yake biye musu, acan kuwa idan babu su na san dole ze rage wasu abubuwan. Kawai dai zuwa nayi in ji ko zaka tura a É—akko shi ne?” Sauke ajiyar zuciya yayi, bayan yayi murmushi sannan yace

 

“Kamar na faÉ—a miki zan cire hannuna daga wannan maganar koh? Babu yanda ban yi dake akan fitar AREEF Æ™asar waje ba kika dage, yanzu ma se kiyi komai da kanki.”

 

“Haba kai kuwa me yasa za kace haka? Ta yaya zan yadda Boy yayi karatu anan bayan ga ‘ya’yan manyan mutane na ta fita waje suna karatu wasu ma sun koma da zama acan. Se nawa É—an Æ™walli É—aya takk, ace yayi karatu a cikin Æ™asar nan. Yanzu yallaÉ“ae mu ba abin kunya ba ne a garemu ace É—an gidan ALHAJI MATAWALLE guda yana karatu a cikin Æ™asar nan bayan babu sa’anninsa? Wannan ma ai salon raini ya shiga tsakaninsa da ‘ya’yan talakawa ne.!” Ta Æ™are tana yatsina fuska kamar wadda ta ga kashi..

 

 

 

A JINI TAKE

*(IZZATA)*

 

 

By

_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

 

 

*CHAPTER ONE*

 

Page_02

 

__Kallanta Alhaji Matawalle ke yi har ta ƙare zancenta. Ya girgiza kai yana ɗaukar juice me sanyi cikin tambulan ya kai bakinsa ya ɗan kurɓa kana ya sauke. Baya son zancen nasu yayi nisa dan be ƙarasa aikin da yake yi ba, ya kuma san idan har be amsa mata ba ba zata tafi ta bar maganar ba, shi kuma ya riga da ya tsara mutanen da zasu je taho da Areef ɗin. Se dai a kodayaushe baya nuna mata yana bin bayan yadda take shagwaɓa Areef ɗin, take so ta dinga nuna yafi kowa a cikin garin saboda kasancewarsa ɗan wanda yafi kowa kuɗi a garin a wannan lokacin.

Gawurtattu Uku 2024 Hausa Novel

“Ki je zamu yi maganar.!” Ya faÉ—a bayan ya kalleta fuskarsa a É—an cunkushe, baya ma so yayi mata magana akan irin maganganunta marasa daÉ—i da kullum basa Æ™arewa alan talaka, yayi maganar, yayi faÉ—an har ya gaji.

 

“Amma YallaÉ“ae da gaske ka damÆ™a komai a hannuna?” Girgiza kai yayi kafin yace

 

“Na É—auki wannan aikin, ke dai kawai ki shiryawa dawowarsa.” Murmushi me Æ™ayatarwa ta saki har cikin ranta tana jin daÉ—i, musamman idan ta tuna yadda tilon É—an nata ze dawo bayan tsawon shekarun da ya É—auka a harvey Mudd College da ke California U.S. Ba ta kai ga cewa komai ba Alhaji Matawallen ya sake faÉ—in

 

“Ki saka a gyara masa part É—insa.” Da sauri ta soma faÉ—in

 

“YallaÉ“ae halin Boy É—in ka manta? Ni da kaina zan gyara masa, idan ba haka ba yanzu zaka ji yace É—akin yana warin ‘yan aiki.” A wannan karon ma se ta Æ™are maganar tana yamutsa fuska.

 

“Allah ya taimaka” yayi gaggawar katseta.

 

“Ameen. A huta lafiya.” Tayi maganar tana miÆ™ewa ta fice daga É—akin. Bin ta da kallo yayi kafin ya dawo da dubansa cikin É—akin yana girgiza kai, a kodayaushe al’amuran Hajiya Salman Æ™ara Æ™aimi suke yi, shi har mamaki take ba shi da ta yadda ya cire hannunsa akan tafiyar Areef Æ™asar waje. Bayan ta manta waye shi wajen kula da tarbiyyar Areef É—in, shi ne take tunanin ze bar shi sakaka haka a can wata Æ™asar ba tare da yana sakawa ana duba shi ba? Ya sake girgiza kai kawai yana maida glass É—insa ya cigaba da abin da yake yi cikin wayar.

 

.. Wayarta da tayi ƙara ta kalla, ganin kiran wadda ya shigo wayar ya sanyata ɗagawa tana cigaba da taku ɗai_ɗai.

 

“Hello Auntyn Areef” shi ne abin da Hajiya Salma ta faÉ—a. Murmushi wadda aka kira da Auntyn Areef tayi kana tace

 

“Na’am, toh ya ake ciki?”

 

“Cikin satin nan Boy ze dawo!”

 

“Woww!! Amma gaskiya na ji daÉ—i ki ce na kira a daidai.”

 

“Aikam dai. Bari zan kiraki akwai abin da zan yi yanzun.” Babu É“ata lokaci suka yi sallama da Æ™anwarta ta daidai lokacin da ta Æ™araso bakin Æ™aton part É—in abokiyar zamanta. Se da ta É—an tsaya kamar me son ganin wani abu, se kuma ta É—an saki Æ™aramin tsaki kana ta cigaba da takawa zuwa cikin É—akin. HaÉ—aÉ—É—en É—aki ne da ya Æ™awatu da Furniture masu kyau da tsada, komai kuma na cikin É—akin milk da coffee ne irin masu É—aukar idon nan. Ƙaton parlour ne se dai duk girmansa be kai na Alhaji Matawalle ba. Daidai lokacin da ta shiga É—akin ta tsinci muryar Atine (Er aikin kishiyarta) na faÉ—in

 

“Ranki ya daÉ—e cikin satin nan YallaÉ“ae Areef ze dawo.” Kafin Hajiya Sa’adah ta bada amsa, Atine suka yi 4 eyes da Hajiya Salma, duk se ta duburburce, ta miÆ™e a sukwane, a hankali ta zo ta gifta ta gefen Hajiya Salman ta fice daga É—akin. Wata banzar harara Hajiya Salman ta bita da shi kafin ta ja Æ™wafa ta Æ™arasa shigowa É—akin. Kyakkyawar farar bafulatanar da ke zaune kan kujera sanye cikin wata haÉ—aÉ—É—iyar atamfa me mugun kyau É—inkin doguwar riga, ta juya ta kalli inda Hajiya Salma ke tsaye dan ganin abin da ya saka Atine fita haka babu faÉ—ar dalili, se taga Hajiya Salma na cigaba da takowa zuwa cikin É—akin. Murmushi ta saki duk da na Æ™arfin hali ne kasancewar ta É—an kwana biyu bata ji daÉ—i ba.

 

“Ki Æ™araso mana” Ƙarasawar tayi ciki se dai bata nemi waje ta zauna ba, ta É—an ajje numfashi kafin tace.

 

“Har an kawo miki gulmar yarona ze dawo kenan?” Ta tambaya tana kallanta. ÆŠan murmushi Hajiya Sa’adah tayi kana tace

 

“Ba gulma ba ce, kawai dai ta faÉ—a min ne ko da ban sani ba” Jinjina kai Hajiya Salma tayi tana É—an taÉ“e baki

 

“Eyyah, don Allah Sa’adah ki fita a harkar É—ana, ban san wannan É—in wane irin abu ne ba. Ka da kice zaki shirya masa wani abu, dan yana da uwar da zata shirya masa, baya buÆ™atar na shishshigi. Don Allah ki kama kanki ki bari idan kika haifa se kiyi rawar kan akansa.” Tun da ta soma magana Hajiya Sa’adah ke kallanta, ba tayi mamakin soma maganar da tayi ba dan dama ba yau ne karon farko da ta ke faÉ—a mata makamancin waÉ—annan maganganun ba, se dai yau É—in mamakin yafi kamata sosai musamman da har se da ta shigo É—akinta sannan take jifanta da waÉ—annan kalaman. A nutse ta buÉ—e baki duk da yadda take jin wani irin É—aci a cikin bakinta, maganganun Hajiya Salman tabbas sun daketa sun kuma taÉ“ata sosai

 

“In Sha Allah.” Shi ne abin da ta iya furta wa sannan ta É—auki wayarta tayi stairs É—in da ke cikin É—akin nata. Tsaki Hajiya Salma ta ja tana bin ta da kallo, a ranta tana fata da addu’ar Allah yasa ta bar mata É—anta, ta dena wannan shishshigin ta bari idan ta haifi na ta se ta yi duk abin da za ta yi.

 

 

 

 

… A É“angaren Twins kuwa ko da suka isa makaranta kai tsaye aji suka nufa, lokacin babu wanda ya shigo ajin, da yake ajin ba baya ba wajen sanin ya kamata se kowaccensu ta É—auki Qur’an ta soma bitar haddar da za a karÉ“a yau É—in. Kallan Lulu Didi tayi tace a hankali saboda karatun da ake yi

 

“Ki maimaita karatun mana” ta faÉ—a ganin ta É—auki wani hadith tana dubawa.

 

“Didi na iya fa, ba se na maimaita ba.” Sanin Lulun na da kaifin hadda ne ya sanyata yadda da hakan, ta rabu da ita, ita kuma ta cigaba da karatunta. Duk da yadda idanun Lulu ke kan hadith É—in da take karantawa amma gaba É—aya hankalinta ba ya kai, duk taurin kanta se take ji kamar ta É—auki Qur’an ta yi haddar, amma se ta ji zuciyarta ta Æ™eÆ™ashe, hakan ne ya sanyata jan tsaki da siririyar muryarta ta cigaba da karatunta. Dukan da aka É—aka mata a kafaÉ—arta ne ya sanyata saurin juyawa bayan ta É—an saki Æ™ara saboda yadda dukan ya shigeta.

 

“Masoyiya!” Ta faÉ—a tana buÉ—a baki. Galla mata harara wadda ta kira da Masoyiyar tayi kana tace

 

“Ni zaki wa rashin mutunci koh? Ya miki kyau” ta faÉ—a tana neman waje ta zauna kusa da ita ta haÉ—e rai.

 

“Ke dallah makara fa muka yi, na É—auka kin tafi” Lulu ta faÉ—a tana kallan Fateema Kabeer wadda ta kasance babbar Æ™awarta a Islamiyyar ta su.

 

.. Sanye cikin wata lallausar brown É—in jallabiya, sumar kansa saye cikin irin wannan naÉ—in da larabawa ke yi a wajen goshi zuwa bayan kansu. Kyakkyawa ajin farko, fari me É—auke da wasu idanu masu mugun kyau, manya masu É—auke da baÆ™ar Æ™wayar ido me shegen kyau, wata irin gira ce da shi wadda take a jere kamar wadda aka saita ta ta zauna akan fuskarsa ta matuÆ™ar Æ™awata ta, hakan ya sa har haÉ—ewa da junansu se da suka yi, saboda se da suka bada wani irin shahararren kyau a tsakiyar goshinsa. Bakinsa É—an Æ™arami ne kamar na mace, kuma ja kamar wanda yake shafawa jan baki ko wani abun makamancinsa, se dai sam ba haka bane. Hannunsa É—auke da wasu littattafai na Addini kasancewarsa É—aya daga cikin manyan Malaman Addini a makarantar, ba ma a makarantar kaÉ—ai ba hatta a yankin yana É—aya daga cikin manyan Malamai, duk da Æ™arancin shekarunsa da ba zasu wuce 25 ba amma da yake gada yayi daga wajen mahaifinsa da ya kasance Babban Malamin Addini a garin. Se hakan ya sake siyo masa soyayya daga wajen mutane da dama, ba ga mata ba ba ga maza ba, kowa Æ™aunarsa yake. Se dai kuma shi É—in mutum ne me matuÆ™ar bauÉ—aÉ—É—en hali, idan dai har ka fahimce shi a bai_bai ba zaku taÉ“a zauna wa lafiya ba, zamanku baze taÉ“a daÉ—i ba, se dai kuma idan har ka fahimce shi shi É—in mutum ne me matuÆ™ar kirki da sanin darajar É—an adam. Abu É—aya ne yake sakawa a kasa fahimtar inda ya dosa kasancewarsa miskili na Æ™in Æ™arawa, hatta da magana bata dame shi ba, za a iya masa wani abun ko kuma ayi abu a gabansa amma ba ze ta tanka ba. Sam baya É—aukar raini, ba ya ma bada fuskar da za a raina shin shi yasa ba a taÉ“a jinsa da wata É—aliba ko É—alibi ba, dan idan dai har ze shiga aji abin da ya kai shi ne kaÉ—ai yake yi, daga nan ba lallai ma wata magana ta shiga tsakaninsa da wani ba. Sallamarsa da muryarsa me amo da daÉ—in sauraro yayi cikin ajin, se dai kasancewarsa mutum mara fara’a a halitta ya sa fuskarsa a cunkushe take, dan kuwa za a iya kiran Gwani Affan da “Sad Man” Gaba É—aya ajin suka haÉ—a baki wajen amsawa, se ya sako kansa cikin ajin cikin nutsuwarsa da tayi matuÆ™ar haÉ—uwa da tsarin halittarsa. ÆŠan lumshe manyan idanunta Lulu tayi tana jin yanda Æ™irjinta ya buga sanda ya shigo cikin ajin, tsoron da ya lafa mata tun É—azun yanzu ya dawo sabo, amma saboda Æ™eÆ™ashashshiyar zuciya irinta ta se ta sauke ajiyar zuciyar tana tsara abin da zata faÉ—a idan ya zo kanta a karÉ“ar haddar.

 

Tsayawa nayi ina kallan ikon Allah sanda na ji bakinsa ya furta

 

“Ina Hafsa Abba?” Dan ban taÉ“a tunanin za a iya yi masa Hausa ya ji ba ballantana ya furta da bakinsa saboda daga yanayin halittarsa har shigarsa da larabawa yayi kama, se dai maganar da yayi ce ta sanyani fahimtar tabbas bahaushe ne, se dai a cikin hausawan irin na daban É—in nan ne, wanda za a iya cewa sun samu komai, musamman ma dai a wajen Gwani Affan da aka ba shi kyau, da kuma ilimin Addini, se dai kamar kowanne É—an adam ba za a rasa wani abun da ya rasa ba, ban san a wajen Gwani Affan ko akwai abin da ya rasa ba dan ni dai a fili ban gan shi ba. Zumbur Hafsa Abba ta tashi bayan maganar da Gwani yayi, tace a hankali

 

“Malam ga ni!” Ba tare da ya kalleta ba ya jinjina kai sannan ya fita daga ajin, bin bayansa tayi zuwa wajen tana É—an gyara tsayuwarta.

 

“Se gobe idan Allah ya kai mu zan kar6i hadda! Ki sanar da en ajin”

 

“Toh Malam” Daga haka ya juya ya soma takawa dan barin wajen cike da nutsuwa, se da ya É“acewa ganinta sannan ta juya ta koma ajin ta sanar da su saÆ™on shi. Lulu kaÉ—ai tayi farin ciki da hakan, dan kuwa gaba É—aya en ajin farin ciki suke da dawowar Gwanin ajinsu. Haka dai ba dan sun so ba suka haÆ™ura. Yau É—in sosai take cikin farin cikin tun da suka fito daga makarantar murmushi yaÆ™i barin baby face É—inta. Didi na lura da ita kuma ta san dalili amma bata kulata ba. Maganar da Fatima Kabeer ta yi ne ya sanyata kallanta

 

“Masoyiya baÆ™uwa na miki magana tun É—azu.” Juyawa Lulu tayi ta kalli wadda Masoyiyar ke magana a kanta, itama ita take kalla tana murmushi, yaÆ™e tayi kana tace

 

“Sannu!” Daga haka bata sake cewa komai ba. Daidai lokacin da suka zo zasu rabu, se suka yi sallama da yake ita baÆ™uwar zuwan makociyarsu Fatima Kabeer ne ya sa suka yi hanyarsu.

 

“Wallahi Æ™awar nan ta ki ta min Fatima, kyakkyawa da ita kamar ita tayi kanta” Murmushi Fatima tayi tace

 

“Allah koh?” Ba tare da tunanin komai ba Abida tace

 

“Wallahi kuwa dama zaki haÉ—ani da ita!” Kallanta Fatima tayi cikin er rashin fahimta da maganar ta ta sannan tace

 

“Ban gane ba?” Dariya Abida tayi kana tace

 

“Mu yi Æ™awance mana”

 

“Uhmm ai ga ki ga ta, dan in dai Masoyiya ce wallahi dizgaki za ta yi” Se da Abida ta tsaya ta kalli Fatima har se da Fatiman ta tsargu sannan tace

 

“Shi kenan!” Daga haka babu wadda ta sake cewa komai suka cigaba da tafiya.

 

 

 

_Claremont California U.S

Tunnel Rd Berkeley

East Bay Hotel_

 

 

.. HaÉ—aÉ—É—en É—aki ne da ke cikin East Bay Hotel wanda ya amsa sunansa É—aki me kyau, ado da Æ™awa, ya matuÆ™ar Æ™awatu da wasu Furniture ‘yan ubansu. KiÉ—a ke ta shi a cikin É—akin cikin wata Æ™atuwar speaker da ke gefe guda, sosai waÆ™ar ke tashi da Æ™arfi kamar ba mutum É—aya ke ji ba. Babu kowa cikin É—akin bayan speaker da ke cigaba da aikinta. TaÉ“a Æ™ofar toilet da na ji anyi ne ya sanyani saurin kai idona wajen. Farar Æ™afarsa da ke cikin wani takalmin wanka itace na fara hangowa lokacin da yake zame takalmin kafin ya kai ga fitowa gaba É—ayansa. Singlet ce a jikinsa se towel É—in da ke É—aure daga Æ™ugunsa yayin da ya É—ora wani akan kafaÉ—arsa. Yanayin rigar da ke jikinsa itace ta fallasa halittar Æ™aƙƙarfan jikinsa da ke É—auke da wasu lafiyayyun kwantattun gargasa baÆ™a wuluk, wadda ta zauna É—ass akan farar fatarsa da ta gaji da gyara, hutu gami da jin daÉ—i. Ƙarasawa yayi gaban mudubi yana É—an kaÉ—a kansa dake É—auke da tulin suma wadda aka yiwa gyara na musamman, hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawar fuskarsa da ke É—auke da wasu shu’uman idanu, wanda kallo É—aya idan yayi wa mutum ze iya rikicewa, ba ga mace ba hatta ga maza idanunsa kan firgita wasu mazan, idan kuwa mace ta bari ya É—ora shu’uman idanunsa akanta idan dai har bata rikice ta faÉ—a Æ™aunarsa ba toh ba za ta bari ta sake iya haÉ—a idanu da shi ba saboda yadda idanun nasa suke kamar suna É—auke da wani maganaÉ—isu ne, a iya idanunsa kaÉ—ae an Æ™ure kyau, dan kuwa idanunsa na É—aya daga cikin abin da ya kwashe kaso masu yawa daga cikin kyawun da Allah ya bashi, se kuma dogon siririn hanci da ke zaune akan fuskarsa kamar an zana. Duk da yanayin yadda kiÉ—an ke tashi da Æ™arfi hakan be hana shi rage sautin ba se ma buÉ—e baki da yayi ya shiga bin sautin waÆ™ar da se ka rantse shi yayi ta saboda yanda yake bin kowanne waje cike da Æ™warewa da muryarsa me daÉ—in sauraro. Ya É—auki wajen rabin awa yana shiryawa sannan ya gama cikin wata haÉ—aÉ—É—iyar riga da crazy jeans da suka matuÆ™ar yi masa kyau. Wata er Æ™aramar abin hannu me kyau da tsada ya É—auka ya saka a hannunsa da shi kansa yake É—auke da kwantacciyar suma me matuÆ™ar kyau. Wayarsa da ke ajje kan gado ta shiga ruri, se a lokacin ya Æ™arasa ya rage sautin kiÉ—an da ke tashi, wanda da alama ba dan kiran da aka masa ba ba ze rage sautin ba. A nutse ya koma ya jingina da jikin mirror shu’uman idanunsa a É—an lumshe kamar yadda suke a halitta, shi ba irin manyan idanun nan gare shi ba, basu da girma can kuma ba Æ™anana ba ne se dai tasirinsu da kuma kyansu na musamman ne kamar yadda shi É—in ya kasance na musamman.

 

“Bad!” Shi ne abin da Lucky da ya kira wayar ya faÉ—a bayan É—aga kiran da Areef yayi.

 

“Yeah Lucky, What’s going on?” Yayi maganar da muryarsa da ita kanta ta daban ce, me daÉ—in sauraro gami da wani amo da ke É—auke da ita.

 

“Amm ka jirani harkar nan ta samu zan kawo maka har É—aki.”

 

“Nop, Let’s meet at school couz mutanen Dad na nan.” Da mamaki Lucky yace

 

“A’ah Bad kada kace min tsoro kake ji?” Ya tambaya dan ya san halin Bad boy É—in. Wani murmushi Areef ya saki kamar ba zece komai ba se kuma yace

 

“Lucky! Just let’s meet there” ya faÉ—a yana taune lips É—insa na Æ™asa idanunsa a lumshe..

 

 

 

 

 

Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har Æ™arshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra’u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.

Close Menu