Sanadiyar ta Hausa Novel Complete
SANADIYYAR TA
Zainab (Indian Girl)
Mikiya Writer’s Association
_Bis-millahir-rahmanir-raheem_
*NOTE*
Dan Allah dan Annabi Muhammad s.a.w duk wanda ya iya gyara whatsapp idan ya samu matsala kowacce iri ce dan Allah yai min magana privet ya gyara min amma dan Allah a taimaka
Page 1&2
Tsaye take a É—akin tana É—aÉ—É—aga hiniform É—in makarantarta da suka kasance ash da baÆ™i duk sun koÉ—e sun yayyage, kwallace ta zubo daga idanunta ya yin da a zuciyarta take cewa “yanzu saboda Allah a haka zan din ga tafiya makaranta da wannan yagaggun hiniform É—in sai kace wata mara hankali” kuka ne ya suÉ“ce mata.
Cuta Ta Dau Cuta Hausa Novel Complete
Kiran da Ummanta ta kwalla mata yasa ta aje hiniform É—in ta fito zuwa tsakar gida tana ta goge hawaye, Umma dake Æ™oÆ™arin raba kunun data dama ta É—aga kai ta kalle ta kafin Ta ce”A’a Kubra lafiya me kuma ya same ki kike kuka?” “Yanzu Umma saboda Allah kamar ni ace na din ga zuwa makaranta da yagaggun kaya sai kace wata mara hankali ko mara gata” Kubra ta faÉ—a tana fashewa da wani kukan.
Umma ta saki baki tana kallon Kubra kafin Ta ce”Tofa! Yanzu Kubra dama ke me gatace? Ai na zata gatanki Allah ne tun da kin san ba mu da halin hakan” Kubra ta goge hawayan fuskarta kafin Ta ce”Eh na san ban da gata; amma wallahi ba zai yiwu na cigaba da zuwa makaranta da wanna yagaggun kayan ba idan za’a canza min a canza idan kuma na zauna ba ilmin shikenan” Tana gama faÉ—ar haka ta koma É—akin.
Mamaki Umma ta shiga amma ko da yake ba abin mamaki bane tun da ai ta san halin Kubra sa rai na kai kanta in da Allah bai kaita ba. Haka ba yadda ta iya ta saka hiniform É—in domin ta na son zuwa makarantar ba zata iya fushi taÆ™i zuwa ba, haka ta fito ta sunkuya ta É—auko kofin da aka zu ba kununta a ciki ta kafa kai tana sha; sai da tasha sosai sannan ta ajiye kofin tana yatsina fuska tana Ce wa”Kunun ma babu sugar idan naje makaranta na san Rahma ta zo mana da lafiyayyan break fast sai na ci amma wannan kunu haka sai kace kayi amai” Umma dai tana É—aki tana jinta bata tanka mata ba har ta fice.
Misalin Æ™arfe 8:00am kowane aji babu abinda kake ji sai muryar malami yana karatu, haka ajin su Kubra ma wanda ya kasance aji 6; kowa yayi shiru ana sauraran malamin dake gaban allo yana rubutu. Kubra ta dubi Æ™awayanta Rahma da Waleeda kafin Ta ce”Rahma,Waleeda!” Duk suka amsa suna kallonta don jin me zata ce musu. Kubra Ta ce”Ku saurara da kyau kuji abinda zan faÉ—a muku kuma wallahi idan kuka É“ata min bajet wallahi! wallahi!! wallahi!!! kun dai san halina ai” Rahma Ta ce”Ke ma kin san ai ba za mu baki kunya ba” Waleeda Ta ce”Duk yadda kika ce haka za ai” Kubra tai murmushi kafin Ta ce”Yawwa to ku saurara ku ji abinda zan faÉ—a muku” A hankali ta faÉ—a masu abinda za su aikata yau a makarantar wanda sai ya tashi hankalin kowa, shewa suka saka jin abinda Kubra ta faÉ—a musu. Da sauri É—aliban ajin dashi kansa malamin suka juyo dan ganin masu yin dariyar amma sai suka maze tamkar ba su bane suka yi dariyar wanda aka rasa wanda yai amma su Æ´an ajin sun sani amma tsoran halin Kubra yasa su ku shiru. Cikin É“acin rai malamin yake tambayar Æ´an ajin su wane suke masa dariya a aji yana karatu amma babu wanda ta tanka shi, ganin sun Æ™i bashi amsa yasa ransa a É“ace Ya ce”Ok, ba za ku fito da su ba to wallahi yau kowacce sai taci ubanta” bai Æ™ara cewa komai ba ya juya ya fice daga ajin rai É“ace. Ai yana fita aji ya hargitse da hayaniya ana Ce wa”Wallahi ku su Waleeda kawai ku fito karku ja mana tun da dai kune ku kai dariyar nan” wata tsawa Kubra ta dakawa Æ´an ajin wanda yasa duk su kai shiru domin suna bala’in jin tsoranta gata ita ba Æ™atuwa ba amma sai sharri dan ita ba Æ™aramin aikinta bane yanzu tajawa mutum a kore shi dag makatantar. Cikin bala’i Ta ce”Wallahi duk Æ´ar iskar data sake ta faÉ—awa malamin nan cewar mune mu kai dariyar nan wallahi sai ta gwammacewa wahalar da zata sha a wajansa fiye da abinda ni zan mata” Jin abinda Kubra ta faÉ—a yasa kowacce taja bakinta tai shiru.
A fuce malamin ya dawo ajin da bulala a hannunsa murtukekiya fuskarsa a É—aure tam yaja ya tsaya gaban allo kafin Ya ce”Dan ubanku tun da ba zaku faÉ—a ba yanzu jikinku zai gaya muku” Take kowacce idanunta ya sake raina fata gashi ana tsoran a faÉ—i su waye ana tsoran abinda zai biyo baya. Malamin ya nuna site É—in farko yace su fara fitowa, haka ba yadda suka iya suka fito. Sai da ya zane kowa na ajin amma ban da su Kubra dan tace wallahi babu mai dukan su, ai tana ganin saura su uku ta daddage ta kwalla wata uwar Æ™ara kafin ta zube Æ™asa babu alamar numfashi a tare da ita. Ai su Waleeda suna ganin haka sun san da cewa shirin Kubra zai fara aiki ne dan haka a fakaice su kai dariya. Ƙarar da Kubra ta kwallace ta janyo hankulan jama’ar dake makaranta aka rankayo zuwa cikin ajin. Shi kuwa Malamin mamaki ne ya kama shi ganin ko taÉ“a ta shi bai ma yi ba amma gashi kamar ma ta mutu, a hankali ya taka zuwa in da take a kwance su kuma su Rahma suna kuka suna mata fifita da gefan hijabin su. A hankali ya sunkuya dan ya duba yaga ko da numfashi a jikinta amma me abinda ya faru ne yasa duk É—alibai saurin kaucewa daga wajan ciki kuwa har da su Rahma cike da firgici, ai malamin yana sunkuyowa ta danÆ™i wuyansa tana zazzare ido tana wasu muzurai. ƘoÆ™arin kwatar kansa ya shiga yi amma ya kasa domin ba Æ™aramin riÆ™o tai masa ba, da sauri wata É—aliba tai office É—in malamai ta kira su suna zuwa suka shiga Æ™oÆ™arin kwatar malamin wanda da kyar suka kwace shi. Buge-buge da duka Kubra ta shiga yi tana wasu maganganu irin na wanda yake iska ganin haka yasa jikin kowa yai sanyi su kuwa su Rahma kuka suke sosai sai kace gaske nan kuwa idan suka haÉ—a ido da Kubra dariya suke. Karatun alqur’anin da aka kunna a waya ne yasa ta dena buge-bugen ta kom ta kwant lakwas, a hankali wani malami yai Æ™arfin halin Æ™arasawa in da take yana addu’a ya durÆ™usa gabanta kafin Ya ce”Bayin Allah kuyi haÆ™uri kun san fa cewa Allah ne ya halicce mu kuma ya halicce ku amma kuke son cutar da wannan Æ™aramar yarinyar?” Cikin wata kalar murya Kubra ta fara magana “Dakata! Nace dakata bil’adama, mu ba masu cutarwa bane an taÉ“a mana jaririyar mu ana Æ™oÆ™arin cutar da ita” Malamin ya sake Ce wa”Kenan ku mutanan jikinta ne?” Tsawa ta daka masa kafin Ta ce”Dalla rufe min baki kana tantama ne?” “A’a wallahi! Wallahi ban tan tama” “To kui mana abinda muke so mu tafi mu barta ta huta” aka faÉ—a cikin tsawa. Malamin Ya ce”Muna jinku me kuke so ai muku” “KuÉ—i, kuÉ—i muke so a ba mu domin gyara É“arnan da akai mata” Malaman suka kalli juna kafin malamin Ya ce”To nawa kuke buÆ™ata?” “Dubu 10 muke da buÆ™ata” Rahma da Waleeda suka kalli juna suka Æ™unshe dariya. Su kuwa malamai mamaki suka shiga yi jin aljanu masu son kuÉ—i, “Ba damar yin tunani na baku ba umarni nake so a cika yanzun nan ko yanzu kowannan ku ya fita babu ido” kallon-kallo malamai da É—aliban dake cikin ajin suka shiga yi kowanne cikinsa ya É—uri ruwa, kafin kace me tuni aka shiga haÉ—a kuÉ—i a cikin malamai har aka haÉ—a dubu goban. Tambayar in da za su ajiye kuÉ—in su kai cikin tsawa tace a je wajan bishiyar kuka dake kusa da ajin a ajiye, haka kuwa akai ana kai kuÉ—in ba a É—aÉ—e ba Kubra ta dawo hayyacinta amma tayi wujiga-wujiga da ita. Da ido taiwa Waleeda alama da taje ta É—auko kuÉ—in idan ta É—auka kuma karta dawo ajin, haka komai ya tafi yadda ta tsara. Bayan an tashi daga makaranta ta ba su naira dubu É—aya tace su raba ita kuma zata siyo hiniform da sauran kayan karatu da bata da su, haka kowa ya koma gida.
Washe gari ya kama weekend ne babu makaranta dan haka bayan Kubra ta gama karyawa dake dama bata komai na aikin gida, rana tana É—an dagawa ta shirya domin zuwa kasuwa ta yankowa kayan makaranta. Bayan ta gama shiryawa ta fito tace da Umma sai ta dawo, Umma ta tambayeta ina zuwa?. Kubra Ta ce”Haba Umma sai kace É“ata zanyi ko kuma baki yarda dani bane?” Umma ta girgiza kai Ta ce”Ba wai ban yar da dake bane Kubra amma ai naga ni ban aike ki ba sannan naga babu makaranta” Kubra ta sauke ajiyar zuciya sannan Ta ce”To Umman su Waleeda ce zata aiketa shine tace na zo na rakata” Umma Ta ce”To a dawo lafiya Allah ya tsare” Kubra ta fice ba tare data amsa ba. Bayan ta dawo daga kasuwar bata Æ™araso gida ba sai da ta biya ta kai É—inki sannan ta nufo gida, tafi take abinta hankalinta kwance burinta ya cika zata sake hinform. Wata Æ™atuwar baÆ™ar mota ce ta shigo layin a guje wanda hakan yai dai-dai da Æ™arasowarta in da Kubra take aikwa ji kake facal motar ta fallatsata da ruwan Æ™asa irin wanda yake taruwa a kan hanyar nan, zafafe Kubra ta bi motar wadda taja burki ta tsaya da kallo sannan ta Æ™arewa kanta da yadda duk jikinta da kayanta suka É“aci ji tai kamar ta saka kuka dan takaici. A hankali motar ta fara dawowa baya har ta dawo dai-dai in da Kubra take ta kasa cewa komai tsabar takaici. A hankali aka buÉ—e murfin motar kafin wata kyakykyawar Æ™afa wadda ke sanye da safa cikin takalmi baki sau ciki kafin kuma ya zuro duka jikinsa ya fito, cikin rashin son magana Ya ce”Please dan Allah kiyi haÆ™uri ina sauri ne shine yasa ban ganki ba har na É“a…” Wani lafiyayyan mari Kubra ta wanke kumatunsa duka biyun dashi wanda ita kanta da tai marin ta san yayi wuta da yawa, cikin bala’i ta fara magana “Dabbane kai? Ko kuwa baka da hankali? Mahaukacine kai ko kuwa wawane kai? To wallahi kaje Allah ya isa ban yafe ba É—an iska É—an tasha kawai” masifa take ko ta ina wanda ko tsayawa ta kalli fuskarsa ma ba tai ba, tana gama faÉ—an tai tafiyarta. Tsintar kansa yai da binta da kallo ya rasa dalilin da ya sa ya kasa É—aukan mataki akanta da har ya iya tsayawa tai masa wannan cin mutuncin, ta san kuwa wane shi da zata kira shi É—an iska É—an tasha?. Kwafa yai ya koma mota ya zauna ya tayar ya bar wajan kalmomin na masa ciwo a rai.
Ita kuwa Kubra a fusace ta shiga gida babu ko sallama ta shiga gidan ba tare da ta kula kowa ba ta É—ebi ruwa ta shiga wanke jikinta tana cigaba da zagin mutumin, zage-zagen da take ne yasa Umma fitowa daga É—aki ta tsaya tana kallonta kafin ta tambayeta. “Wani É—an iska na haÉ—u dashi yai min haka ko dan yana taÆ™amar shi É—an mash kuÉ—i ne to ni wallahi babu ruwa na da kuÉ—in su shiyasa na zage shi na ci masa mutunci” Kubra ta faÉ—a cikin takaici. Umma Ta ce”To Allah ta kyauta” Tai komawarta É—aki domin itama kanta Kubran ba kyaleta tai ba. Haka Kubra ta gama wanke duk in da ruwan ya É“ata ta tana ta sababi sannan ta koma É—aki domin cire kayan jikinta.
****
Ransa duk a jagule ya isa gida kai tsaye É“angaransa ya nufa domin maganganun yarinyar nan sun taÉ“a masa zuciya ba ka É—an ba, wai har shi zata duba ta cewa É—an iska É—an tasha; kalarsa ce ta nuna haka ko kuwa shigar jikinsa? Shi ba shigar ban za yai ba amma yau shi aka gayawa magana maganar ma daga Æ™azama kucaka. A haka dai ya samu ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin yadi mai matuÆ™ar kyau da tsada sannan ya nufi part É—in iyayansa domin yunwar da take Æ™oÆ™arin hana shi kuzari, da sallama ya shiga falon farko har zuwa falon da zao sa da shi da É—akin Mammynshi. Da sallama ya shiga falon Hajiya Aisha tana zaune akan É—aya daga cikin kyawawan kuma tsadaddun kujerun dake cikin falon, tana sanye cikin shiga ta alfarma tayi matuÆ™ar kyau; hannunta riÆ™e da waya da alamar wani take son ta kira. Sallamar da yai yasa ta É—aga kai ta kalle shi da Æ´ar damuwa akan fuskarta, Æ™arasowa in da take yai ya zauna kusa da ita kafin Ya ce”Mammy sannu da hutawa” “Ina ka shiga kasani a damuwa sannan wayarka busy?” Hajiya Aisha ta faÉ—a ba dariya. Ya ce”Sorry Mammyna wallahi naje ball ne kuma a hanyar dawowata na haÉ—u da…” nan ya kwashe duk abinda ya faru ya faÉ—awa Mammy. Hajiya Aisha macece mai tsauri sannan kuma bata Æ™aunar talaka ko da da misÆ™alan zarati amma yau wai ace talaka ne yaiwa jininta wulaÆ™anci irin wannan ai ba ma zai yiwu ba dole a É—au mataki, cikin zafi Ta ce”Amma My Son me ka tsayayi da har ta faÉ—a maka wannan baka É—au mataki ba? An ya Afdal zuciyarka irin tawa ce kuwa?” Cikin kwantar da hankali Afdal Ya ce”Kiyi haÆ™uri Mammyna kinji ki kwantar da hankalinki” Hajiya Aisha Ta ce”In kwantar da hankali na fa kace? To idan kai baka kishin kanka ni ina yin kishinka dan haka dole na É—au mataki” tana gama faÉ—ar haka ta É—auki wayarta ba tare da ta jira mai zai ce ba ta shige ciki da matsanancin É“acin rai a fuskarta. Dafe kai Afdal yai ya san sarai halin Mammy babu abinda ba zata iya aikatawa ba akansa duk wanda yace zai wulaÆ™anta shi; gashi yanzu ta É—au zafi wanda Allah ka É—ai ya san abinda zata aikata.