Ad Code

Mutallab Asad Muttalab Hausa Novel Complete

Mutallab Asad Muttalab Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*MUTALLAB ASAD MUTALLAB*

(MAM)

 

NA

 

BILLY S FARI &

NANA DISO

 

*SHAFI NA DAYA.*

 

 

_RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU._

_TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA_

 

 

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*

*INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”

*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*

Mun gwada mun gani 💯

Mun gani mun shaida 💯

Anyi mun gani 💯

MAGANIN SANYI

MAGANIN NONO

MAGANIN HIPS

MAGANIN SLIMMING

MAGANIN NANKARWA

GYARAN AMARE

GYARAN MAIJEGO

MALLAKAR MIJI KO MATA

SUBULU DA SCRUB

MAYUKA NA GYARAN JIKI

TURAREN WUTA

MATSI

MAGANIN NI’IMA

MAGANIN TSUMI

INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

Yankan Karfe Hausa Novel Complete

08142800199

07068558096

 

 

 

Garin a lullume yake da hazo, ga wani irin iska dake kaɗawa, wasu na tafiya aƙasa yayin da wasu suke tafiya akan keke mai ƙafa biyu da uku wasu kuma suna tafiya ne da ainahin ƙafafuwan da Allah ya halittawa kowane cikakken mutum, yayin da iskar dake kaɗawa sai manne musu tufafi takeyi duk da yalwar sutura dake sanye da jikunkunansu, haka yasa wasu suka sake ƙawata saman jikinsu da rigunan sanyi don samun cikakkiyar kariya daga bayyanar sauyin yanayin garin da aka samu da muke kira bazara ko kuma hunturu dake ɗauke da wani irin matsanancin sanyi da kowanne mutum ke ƙoƙarin bawa gangar jikinsa da kuma lafiyarsa kyakkyawar kulawa da zata iya bashi kariya daga wannan Sanyin da akeyi mai tsanani. sai dai duk da hakan kamar yanda kowa ya sani tsanantar yanayin da ake ciki bai hana mutane Yin wani kai da kawo na yau da kullum ba da ke tsakankanin rayuwa da kuma mutuwa a kowace safiya.

 

*ALHAJI ASAD MUTALLAB STREET*

 

Abunda aka rubuta kenan a jikin wani ƙarfe dake bakin wani babban layi. Ko ba’a sanarmaka ba kasan gidaje ne na masu faɗa aji a gomnati ko kuma manyan-manyan ƴan kasuwa da sukayi fice da kuma zarra akaf faɗin garin, daga gefen hannun hagu a jerin ƙayatattun gidajen wani babban gidane da kallo ɗaya zai tabbatar maka da cewa mamallakin wannan gidan na ɗaya daga cikin waɗanda Allah yayiwa ni’ima da saukar tarin arziki mai yawa a tattare dasu, duba da yanayin tsaruwarsa, tsananin girmansa da kuma yanda aka ƙawatasa tun daga kan tsarin ginin har zuwa abubuwan da aka ƙawatasa dasu aciki, gidane dake ɗauke da rassa daban-daban wanda hakan ke tabbatar maka da yalwatuwar iyali da kuma zuri’a kamar yanda tarin arziƙi ya yalwata acikinsa, budurwa ce da bazata haura shekaru goma sha biyar zuwa sha shidda ba tafe cikin  uniform ɗinta na makaranta da duka-duka sket ɗin kayan kaɗan ya rufe guiwowin ƙafafuwanta, sai doguwar safar kafa dake cikin takalman makaranta dake jikinta, a samanta kuwa ɗan mitsitsin hijab ne dako ƙirjinta bai ƙarasa rufe wa ba duk da zunzurutun sanyi da kuma iska dake faman kaɗawa, school bag ɗin ta kuma na rataye akan kafaɗarta  ta nufo ɗaya daga cikin jerin danƙara-danƙaran motocin da kowace ke zaune a muhallin da aka tanadar mata acikin farfajiyar gidan ta ƙaraso da sauri saboda ganin suna ƙoƙarin makara, dai-dai lokacin da takai hannunta a jikin marfin motar tana ƙoƙarin buɗewa taji saukar muryarsa cikin wani irin coolness  yana cewa,

“Ina ƴar uwarki ne Jiddah naga driver na ƙoƙarin tayar da motar banga tafito ba?”

 

Ɓata rai tayi tare da sakin murfin motar tana turo baki gaba sannan ta juyo haɗe da cewa, “Ya MUTALLAB bata tashi ba kuma mun makara”. Ba tare daya kalleta ba ya nufi sashensu yace, “Ki koma ki tasheta ta shirya sannan kufito kuwuce”. Sanin baya magana biyu yasa ta fashe da kuka tana bubbuga ƙafafuwa haɗe da ƙunƙuni ita baza taje ba kuma ba zasu tsaya jiranta ba wallahi. yaran dake cikin motar tun ɗazu su biyu ƴan maza suna zaman jiran yayun nasu suka fito suma daga cikin motar suna kallon sashen da ya’yan nasu ya nufa, ɗaya zai kai shekaru goma sha biyu ɗaya kuma bazai wuce shekara bakwai ba, tamkar wasu manya suka bishi da banzar kallo sai kace ba yayansu ba kafin Khalil da shine mai shekaru sha biyu ya maido kallonsa gareta yana gyara stocking ɗin wandonsa cikin ɓaci rai yace

 

“Aunty Jiddah gaskiya idan muka makara aka dakeni Allah ya isana bazan yafe ba tunda da gangan kuka ki shiryawa da wuri”. A hasale ta juyo tayo kansa zata kai masa duka ya goce ya balla mata harara, dai-dai lokacin mahaifiyarta mai suna Hajiya Zainab tafito daga sashen daya kasance mallakin mahaifinsu tana cewa, “A.a.a.a meye haka Jiddah wai har yanzu baku tafi ba? Kun san ƙarfe nawa kuwa yanzu?”

 

“To Ummah ba ya Mutallab ne ya hanamu tafiya ba wai sai mun jira Afrah kuma ko tashi daga bacci batayi ba”.

 

“Me ne? Yau she yasamu wannan matsayin acikin gidan nan, ita Afrah ɗin waye ya hanata tashi ta shirya da wuri? Ai kuwa bai isa ba maza ku shiga a kaiku, idan taga dama ta fito sai ta nemi abun hawa ya sauke ta, dama meye haɗin tsintsiya da ragga in ba dole ba”. Ta ƙarashe maganar cikin ɓacin rai tana rufe masu motar bayan sun shiga tare da dallawa sashen su Mutallab ɗin harara, wanda hakan yayi dai-dai da fitowarsa zai shiga sashen mahaifin nasu gaishesu, duk da yana jin maganganun da take yi bai tanka mata ba sai ma gaisheta da yayi cikin girmamawa ya wuce gaba abunsa ba tare daya tsaya saurarar amsar da zata fito daga bakinta ba, wata uwar hararar ta sake dalla masa haɗe da cewa,”munafurcin banza munafurcin wofi da ban tashi ba zaka ganni ne”. Sannan tabi bayansa tana ci gaba da yaɓa masa maganganu don tuni driver yaja motar ya wuce.

 

Cikin girmamawa ya gaida mahaifin nasa dake kishin giɗe akan wata lallausar darduma dake cikin falon nasa daya gama tsaruwa ya amsa masa ba yabo ba fallasa, miƙewa yayi da zimmar fita Ummah dake tsaye gefe cike da takaicinsa na rashin tankata tace,

 

“Alhaji ka jamasa kunne akan yaran mu tunda baya ƙaunar a zauna lafiya kullum burinsa ya raba ɗaya biyu”. Ɗan ɗauke fuska mahaifin nasa yayi kafin ya kallesa tare da dakatar dashi daga ƙoƙarin ficewarsa da yake shirin yi, maido kallonsa ga Ummah yayi sannan yace, “Me yake faruwa?”

 

“Ai kasan halinsa da nuna banbanci tsakanin yaran nan Alhaji sai kace duka ba ƙannensa bane, idan ba haka ba akan me ƴar uwarsa zata je tayi kwanciyar bayan tasan suna zuwa makaranta har lokaci ya ƙure kuma yace dole sai Jiddah ta koma ciki ta jirata bayan makara zasuyi? To nidai gaskiya bazan lamunci a takurawa Jiddah ba tana jamata duka a banza a makaranta, ban sani ba ko ita Amarya zata iya haƙura aci gaba da dukar mata yara a banza saboda laifin ƴar uwarsa, don haka kama canza masu wajen karatu tunda bazata iya tashi tana shiryawa da wuri ba ka kaita inda za’a ɗauki wannan shashancin nata”.

 

Ga mamakin Mutallab mahaifin nasu bai tsaya yin binciken komai ba kawai  yace, “Shikenan, yanzu ina yaran suke su suje a saukesu?”

 

“Sun wuce Alhaji ita kuma har yanzu ina tunaninma bata fito ba saboda tsabar lalaci dake damunta”. Jinjina kai yayi haɗe da cewa “Shikenan ki ƙyaleta zan kaita inda ya dace da ita don bazai yiyu na riƙa banzatar da kuɗina a banza ba”. Da sauri Mutallab ya ɗago kai jin abinda mahaifin nasu ya faɗa, ko kaɗan bai yi tsammanin wannan makircin na Ummah zai sa yayi saurin yanke hukunci haka ba, “To mara kunya kallon me kake yimani? Ina Ni na haifesu duka kuma zan iya yanke duk hukuncin da naga dama akan kowanensu”. Alhajin ya faɗa cikin ɓaci rai yana kallon Mutallab dake ƙoƙarin buɗe baki yayi magana, wata uwar tsawa ya daka masa tare da nuna masa ƙofa yana faɗin yabar masa ɗaki, ɗago kai yayi ya kalli Ummah ta sakar masa wani irin malalacin murmushi dake tattare da kalar ma’anoni daban-daban. Maida kansa ƙasa yayi yaba mahaifin nasu haƙuri sannan ya juya yabar falon gangar jikinsa a mace zuciyarsa cike da ƙunci da kuma samuwar wannan mummunan hukunci da mahaifin nasu ke shirin yanke wa, kai tsaye cikin gidan ya nufa ya samu Aunty amarya na zaune a falo, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa haɗe da danne duk wani abu da yake ji na ɓacin rai a ƙasan zuciyarsa ya gaisheta tare da wucewa kai tsaye ɗakin daya kasance mallakin ƴar uwar tasa dake can sama jere dana Jiddah, Aunty amarya kuwa da harara ta rakasa har ya janye saman sannan tayi wani mugun tsaki tana jin tsanarsa sosai a ranta.

 

Bakin ƙofar ɗakin ya tsaya ya ɗan bubbuga ƙofar tare da kiran sunanta, jin ba’a amsa ba ya sashi ɗan ɗaya Muryar tasa cikin zafin rai yana cewa, “Afrah..Afrah”. Daƙyar ta iya motsa bakinta daga cikin duvet ɗin data tattake aciki tana rawar sanyi tace, “yaya..” sai ta kasa ƙarasawa sakamakon aman da taji ya taso mata wanda ya sata yin wani irin yunƙuri da ƙarfi cike da kakari, jin sautin aman yasa Mutallab tura ƙofar da ƙarfi ashe ma bata saka key ba a buɗe take, cikin tashin hankali ya kutsa kansa cikin daƙin hangota tana ƙoƙarin saukowa kan gadon cikin wani irin yananyi dake tabbatar masa da raunatar gangar jikinta sakamakon rashin lafiyar da take ciki ya tallabota, take tafara kwara amai ga jikinta ya dau zafi sosai tamkar ba a yanayin sanyi ake ciki ba, taimaka mata yayi bayan ta gama aman ya kaita toilet ɗin dake cikin ɗakin nata ya wanko mata bakinta sannan ya fito da ita ya mayar da ita akan gadon tare da Jan duvet ya lulluɓa mata sannan ya cire mata hijab ɗin dake jikinta daya ɗan jike da ruwan data wanko bakinta, idanuwanta a lumshe tace, “yaya..” bata ƙarara ba yace, “ya isa Afrah tun yaushe kike cikin wannan yanayin baki kirani kika sanar dani ba? Sannu meke damunki?”

 

Kanta ta nuna masa da ƙafafuwan ta sai sanyi data sake tabbatar masa da tana ji sosai, wanda hakan ke nuni da zazzaɓine mai tsanani ke damunta. “Ina zuwa”. Ya faɗa tare da miƙewa ya fice daga ɗakin, ba’a jima ba sai gashi ya dawo, sai dai a wannan karon su biyu ne, Cikin sanyin Muryar ya kalli wanda suka shigo taren daya ɗan girmesa yace, “Jalil ka gyara wajen nan, bari naje na samo mata abinda zata ci tasha magani”. Ya ƙare zancen yana nuna masa gun da Afrah tayi amai shi kuma ya fice.

 

Dukkansu kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci  jini ɗaya ne da suka fito daga ciki ɗaya saboda tsananin kamar da sukeyi da juna, musamman Afrah da Mutallab da yanayin hasken fatarsu take iri ɗaya, haka ma zayyanuwar kyakkyawar surar dake shimfiɗe akan fuskokin nasu iri ɗaya ne tamkar an tsaga kara, kawai shekaru da kuma bayyanar jinsin kowanensu zaisa ka iya banbance tsakaninsu, Jalil kuwa duk da suna kama yanayin surar fuskarsa yafi bayyana dana mahaifinsa saboda hatta duhun fatarsa duka nashi ne ya ɗebo, gaba ɗaya shekarunsa basu wuce ashirin ba a duniya, sai Mutallab dake da shekara ashirin da biyar, Afrah kuma tana da shekara sha biyar da watanni don kusan Sa’anni suke da Jiddah, gaba ɗaya baifi wata uku zuwa wata huɗu bane da Jiddah ɗin ta bata.

 

Sai da Jalil ya gama gyara wajen sannan ya dawo gefen gadon ya zauna tare da dafa goshin Afrah ɗin yace, “Sannu tsunkui, Ashe bakida lafiya”. Sunan da yake kiranta dashi kenan saboda ba tada wata cikakkiyar lafiya ko yaushe yau ciwo gobe lafiya, hakan yasa ba tada ƙiba sam shi kuma sai yake kiranta da wannan sunan musamman daya fahimci bata so suyita rigima kamar dai yanda kowa yasan yanda saƙo da saƙo suke basa rabo dayin faɗa. Yanzu ma haka ne, duk da tana ciwo hakan bai hanata maka masa harara ba tare da Turi baki tana duvet ɗin har fuskarta ta rufe.

 

“Sorry” ya faɗa yana dariya sai ga Mutallab ya turo ƙofa hannunsa riƙe da cup daya haɗo mata tea a ɗakinsa,

 

“Afrah tashi kisha wannan sai kisha magani”. Ya miƙawa Jalil daya tashi ya bashi wurin cup ɗin sannan ya zauna tare da janye duvet ɗin a fuskarta ya taimaka mata ta tashi ta jingina da gado, idanuwa suka haɗa da Jalil ta sake harararsa haɗe da kallon Mutallab tace, “Yaya ka ganshi ko”. Ɗago kai Mutallab yayi fuskarsa ba wasa suka haɗa ido da Jalil yayi saurin sadda kansa ƙasa, “me yasa kai babban kwabo ne, tana ciwon ma sai ka tsokaneta?”

 

Zai yi magana Mutallab ya miƙa masa hannu yana cewa, “Ya isa haka, bani”. Jalil ya miƙa masa ruwan cup ɗin ruwan tea ɗin ya riƙa bata a hankali tana sha har sai data shanye tas sannan ya ajiye cup ɗin gefe yasa Jalil ya sauka ya kawo masa ruwa ya ɓalle mata maganin ya bata tasha, sannan ta koma ta kwanta ya gyara mata duvet ɗin yana yimata sannu, hannunsa ta riƙe tana kallonsa idanuwanta cike tab da kwalla tace, “Yaya na..” bata ƙarasa ba tayi saurin jan bakinta tayi shiru ganin yanda ya sauya mata fuska nan take saboda godiyar da take ƙoƙarin yimasa. A hankali hawayenn da suka cika mata idanuwa suka fara kokarin saukowa akan kyakkyawar fuskar tata tana jin wata irin soyayya da ƙaunar ƴan uwan nata na yawo a dukkanin magudanar jini da kuma lungu da saƙo na zuciyarta, duk duniya ba tada gata sama dasu, sun zame mata uwa mahaifiya data rasa tun tana ƙarama kuma suka cike mata gurbin mahaifi a tawata fuskar duk da yana a raye shi….

 

 

*BAQEER*

Ayusher Muhd

Umm Asghar

 

*KURMAN ALLO*

Asmy b Aliyu

Jidda Aliyu

 

*AKWAI SIRRI*

Zee Bawa

Hajja ce

 

*MUTALLAB ASAD*

Nana Diso

Billy S Fari

 

*KULUWA*

Zee yabour

Sadiya Dan

 

Duka Biyar ɗin akan 2k

Hudu 1600

Uku 1200

Biyu 800

Ɗaya 500

 

VIP💕🔥

Duk guda ɗaya 1k

 

KATIN MTN Ta👇

07043079282

Shaidar biya

 

#Tafiyar samo

#Tagwaye biyar

#Billy S fari

#Nana Diso.

Close Menu