Ad Code

Baqeer Hausa Novel Complete

Baqeer Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BAQEER

NA

AYUSHER MUHD

DA

UMM ASGHAR

 

DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ÆŠAYA

 

*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*

*TAFIYAR BIYU TAFI ÆŠAYA*

 

*KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?*

*INA KUKE MANYAN MATA? WAÆŠANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?”

*KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.*

Mun gwada mun gani 💯

Mun gani mun shaida 💯

Anyi mun gani 💯

MAGANIN SANYI

MAGANIN NONO

MAGANIN HIPS

MAGANIN SLIMMING

MAGANIN NANKARWA

GYARAN AMARE

GYARAN MAIJEGO

MALLAKAR MIJI KO MATA

SUBULU DA SCRUB

MAYUKA NA GYARAN JIKI

TURAREN WUTA

MATSI

MAGANIN NI’IMA

MAGANIN TSUMI

INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯

 

08142800199

07068558096

 

 

 

[1]

 

Tafe yake a gefen titi hannunshi na dama na riƙe da waya wacce ke saitin kunenshi, yanayin shi kaɗai zaka kalla kasan yana cikin ɓacin rai wanda ke nuni da abinda ake faɗa a cikin wayar ba abu ne mai daɗi ba. Magana yake yi a nutse sai dai kuma ranshi a ɓace yake matuƙa saboda rainin hankalin da mutumin yazo mishi dashi, taya zai sa yayi mishi aiki akan bayan kwana biyu zai biya shi kuɗin aikin shi amma gashi har yanzu da ake neman yin watanni biyar bai gama biyanshi kuɗin shi ba? Sai ma tsitsinka mishi kuɗin da yayi ta yadda babu wani ƙwaƙƙwaran abu da zai iya yi da kuɗin tunda ba a dunƙule ya bashi ba. Cike da takaicin abinda yake ji ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin yin magana, abinda yaji ne yasa ya kasa tantance a wace duniyar yake, wani abu yaji yayi sama dashi, idanunshi ne suka sauka akan sararin samaniya yaji kwakwalwarshi ta ɗauke dif na wucin gadi, sam ya kasa gane abinda ke faruwa dashi, kafin yai auni ya dawo da kwakwalwarshi tai wani aiki yaji ya faɗo kan wani abu, kanshi ne ya ji ya bugi gaban mota sannan ya sulale ya faɗi ƙasa, dishi-dishi ya shiga gani a hankali yake ƙoƙarin buɗe idanunshi yana son sanin meke faruwa dashi, sai dai idanunshi mai makon su buɗe sai ma kullewa da suke, karar kiɗa kawai yake ji a kunuwanshi, nan idanunshi suka rufe wanda daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba.

 

Daga cikin motar kuwa wani saurayi ne wanda kallo É—aya zaka yi mishi kasan É—an gayu ne wanda ke ji da kanshi. “Goddamn it! This bastard is gonna make me late.” MatuÆ™in motar ya faÉ—a haÉ—e da dukan stearing wheel na motar da É—an Æ™arfi, burki ya taka sannan ya rage sautin kiÉ—an dake tashi cikin motarshi, bai ko kashe motar ba ya fito a fusace yana duba gaban motar, ganin da yayi babu abinda ya sameta yasa shi komawa cikin motar yayi reverse ya kaucewa saurayin dake yashe a Æ™asa wanda kana ganinshi zaka ga babu alamun rai a tattare dashi, yaja motarshi da wani irin mugun gudu ya bar wurin yana mitar ‘duk Daddy ne ya janyo musu ya rasa unguwar da zai yi gini sai cikin talakawa wai shi a dole yana protecting political image É—in shi, gashi nan abinda ya janyo musu mingling da Æ´aÆ´an matsiyata da basu san komai ba sai gidadanci.’

Akwai Sirri Hausa Novel Complete

Majalisar samari ce zaune a kan kujerar dake Æ™arÆ™ashin bishiyar darbejiya, daga gefensu kuma mai shago ne yana ta saye da sayarwar shi, idan ka kalli can nesa dasu kuma zaka ga gungu-gungu ne na yara suna wasanni kowanne na daidai shekarun su. Idan ka buÉ—e ido ka kalli yanayin gidajen unguwar sosai zaka gane cewa kowa ta haÉ—a wato daga masu hannu da shuni har zuwa matsakaita masu rufin asiri bakin gwargwado da kuma talakawa, a taÆ™aice dai unguwa ce ta kowa da kowa. Musu ne ya kaure a wannan majalisar inda samarin unguwa ke taruwa su zauna yawanci da yamma bayan sun taso daga wuraren sana’o’in su ko makaranta. Musu ne akan siyasar Æ™asar nan don haka wurin ya kaure da hayaniya har wani baya jin abinda É—an uwanshi yake cewa, wani daga cikin samarin ne idanunsa suka kai kan abinda ya faru daga gaba dasu kaÉ—an, ihu ya saki da Æ™arfi wanda ya sakasu kallon wurin suma, hankali a tashe suka rugo inda saurayin nan yake a yashe.

Suna Æ™arasowa hankalinsu ya sake tashi ganin halin da yake ciki. A guje Bello É—aya daga cikinsu ya Æ™arasa wurin hankalinshi a mugun tashe, jiki na rawa ya kai hannu saitin hancin saurayin dake kwance akasa dan ya tabbatar yana numfashi, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauÆ™e jin yana numfashi a hankali, kafin ya nemi taimakon sauran jama’ar da ke wurin akan su taimaka akai shi asibiti. CicciÉ“arshi aka yi za’a saka shi cikin motar É—aya daga cikin mutanen da suka taru a wurin, hankalinsu ya sake tashi ne ganin jini ta bayan inda aka É—aga shi, haka su Bello da wani daga cikin abokansu suka sakashi a mota, duba wayarshi Bello yayi sai dai sam babu alamar ta, ya sani sarai a cikin mutanen wurin ne wani har ya sace dan yanzu in aka yi hatsari wasu sata ce kawai a gabansu ba wai ceton rai ba.

Accident and emergency (A&E) na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano suka isa dashi, a gaggauce aka karɓeshi aka yi ciki dashi domin kuwa ba ƙaramin jigata yayi ba, kuma har yanzu bai san inda kanshi yake ba, sai numfashi da yake fitarwa shima a hankali.

Nurse ce ta kawo musu takarda akan su cike sannan tace “Ya sunanshi?”

Bello cikin sanyin jiki yace “Muhammad Baqeer!”

“Kai ne guardian É—inshi?” Kalaman da yaji nurse É—in tayi mishi kenan, kafin yayi magana tace “In kasan ba kai bane please ka Æ™ira su yanzu dan muna son su saka hannu cikin gaggawa.” Tana kaiwa nan ta juya ciki da alama sauri take yi, Bello idanunshi duk sun yi jaaa, wayarshi ya É—auko yana Æ™oÆ™arin Æ™iran mahaifin Baqeer, mamaki ne ya kamashi ganin Æ™iran wayar mahaifin nashi, nan ya daure ya É—auka “Aka ce Baqeer yayi hatsari?” Kalaman da yaji ya dake shi da ita kenan, cikin rawar murya yace “Eh muna asibitin Aminu Kano!”

“Ni nasan wannan abotar taku ba abinda zata jawo mana sai É“acin rai, don na sha faÉ—a maka ka daina zuwa kana kiranshi in yana aiki amma da yake kai ba mai jin magana bane kai kenan da ziryar janshi ku tafi majalisa.”

A hankali Bello yace “Wallahi yau Baba bama ni na Æ™irashi ba sannan yana zuwa ko zama bai yi ba ya tafi.”

Jin alamun an kashe wayar yasa ya shafi saman goshinshi yana sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya.

Baba daga can É“angaren ranshi ne ya sake tunzura a fusace ya fara Æ™oÆ™arin fitowa daga gidan, hannu tasa ta rikeshi tace “Kai ma Alhaji ka kwantar da hankalinka, na tabbatar ba sosai bane da sukace yaji ciwo sosai, kasan zancen yara su dama sun iya zuzuta abu.”

Hannunshi ya fincike daga hannun matar dake tausasar sa da kalaman nan, yana ji kamar zuciyarshi zata fito, yana fitowa daga É—akin yaga Fatima wacce itace mahaifiya ga Baqeer É—in, tana Æ™oÆ™arin shiga da kwanukan da ta wanke cikin É—akin ta, fita kawai yayi ranshi na sake É“aci, da gudu kanin Baqeer wanda saurayi ne bai wuce shekaru 24 ba shine ya fito daga ciki gidan ya biyoshi tare da buÉ—e Æ™ofar mota ya shiga gefenshi ya zauna.

Baba bai musa ba ya ja motar don ko magana baya son yi.

TuÆ™i kawai yake yi amma gabaki É—aya ya rasa nutsuwarshi, hukuncin Allah ne kawai ya kai su asibitin lafiya amma ba don yayi nutsatsen tuÆ™i ba. Suna shiga accident and emergency Bello wanda dukkanin nutsuwarahi tana wajen Æ™ofar da aka shiga dashi ya taso ya taresu. DurÆ™usawa yayi yana gaida mahaifin Baqeer sai dai bai iya ya amsa shi ba saboda halin da yake ciki sai ma tambayar shi da yake yi yanayin jikin na Baqeer É—in “Tunda muka zo aka shiga dashi ciki basu fito ba sai dai an buÆ™aci sa hannu wanda ganin baku zo ba yasa nayi, sun bukaci za’a Æ™ara mishi jini nida Salim daya kawo mu mun je an gwada namu ko yazo É—aya da nashi sai dai anyi rashin sa’a basu yi matching ba, to bayan nan dai har yanzu basu Æ™ara fitowa ba sai dai ko muje mu tuntuÉ“i waÉ—ancan nurses É—in muji yadda ake ciki.”

Hannu Baba ya É—aga mishi alamun ya kyaleshi sannan ya nufi wurin Nurses É—in, Salim dake fitowa yana gaisheshi ko amsa wa baiba saboda hankalinshi baya jikinshi, Nurses É—in har sun fara tafiya sai ga É—aya daga cikin likitocin da suka karÉ“e shi nan ya fito hakan yasa Bello dake biye dasu a baya ya nunawa Baban Dr É—in yace “Yauwa gama likitan dake duba shi nan ya fito” Baba yi yayi kamar bai jishi ba har suka Æ™arasa wurin shi.

“Sannu likita.”

 

“Yauwa sannu Baba,” yace yana mai gyara tsayuwarshi.

 

“Yarona ne aka kawo mota ta buge shi ance ku kuka dubashi, ya jikin nashi dai? Ina fatan babu wata matsala?”

“Hmm..” kawai kanin Baqeer yace yana taÉ“e baki don a ganinshi da ace É—aya daga cikin shi ko Æ´an uwanshi ne hakan ta faru dasu ba lallai ne ya nuna damuwarshi har haka ba amma da yake É—an gwal ne baya da lafiya duk yabi ya ruÉ—e tun ma bai ga a halin da yake ciki ba,”Allah yasa ma kada ya tashi” ya samu kanshi da yiwa É—an uwan nashi mummunar addu’a babu tausayin halin da ya samu kanshi a ciki.

 

ÆŠan kallon shi likitan yayi yana tunanin ta yadda zai fara faÉ—a mishi halin da É—an nashi yake ciki ganin yadda hankalinshi yake a tashe “A yanzu dai ba zance komai ba, sai abinda gwaje-gwajen da aka yi mishi suka nuna, mun dai yi Æ™oÆ™arin tsayar da zubar jinin da yake yi sai dai muna buÆ™atar wanda za’a Æ™ara mishi ina fata kun zo da wanda zai bashi jinin, sannan akwai karaya a hannunshi na dama da Æ™afarshi ta hagu”.

 

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlif li khairan minha” Kawai Baba ke nanatawa. Cikin wata irin kasalalliyar murya irinta wanda abun duniya ya taru yayi wa yawa yace “Ko nawa jinin za’a iya É—iba matukar jininmu É—aya ai, Allah ya sauÆ™aÆ™a mishi ya tashi kafaÉ—unshi.” Ya Æ™arasa maganar cikin murya mai karkarwa.

Dukkansu suka amsa da ‘Ameen’ banda kaninshi da yake tsaye a gefe sai faman cika yake yi yana batsewa shi a dole bai so zuwa asibitin ba ya biyoshi ne kawai dan mahaifiyarshi ta turo shi akan yazo yaga meke faruwa ya kai mata labari.

Jikin Baba a mugun sanyaye ya shiga cikin É—akin, ja yayi ya tsaya yana jin kafafuwanshi nayi mishi nauyi ganin É—an lelen É—an nashi a kwance wanda duk wani mai imani in ya ganshi sai ya zubar mishi da Æ™walla saboda gaba É—aya kamanninshi sun sauya don ba Æ™aramin buguwa yayi ba, Bello da Salim a gefe suka tsaya kawai dukansu hawaye sukeyi shi da Salim, don abun akwai ban tausayi ace awa biyu baya kana cikin koshin lafiya yanzu banda numfashi ba abinda kakeyi, hancinsa É—auke yake da na’urar taimakawa gun yin numfashi na oxygen, a hankali Baba ya Æ™arasa wurin har a lokacin bai dawo hayacinsa ba ya kalli Bello cike da tausayin É—an nashi yace “Garin yaya hakan ta kasance?” Jiki a sanyaye Bello yake faÉ—a mishi iya abinda ya sani sannan yaran daya mai motar a yanda ya musu kwatance suna zargin yaran gidan Alhaji Sunusi Karaye ne shine wanda ya bugeshi, da yadda yaja motarshi ya bar wurin ba tare da yabi takan Baqeer É—in ba wanda hakan yasa basu gane ko tabbas shi É—in bane.

Nan da nan Baba ya sake fusata, yana ji ranshi na sake soyuwa, tabbas zai je har gida ya samu ubanshi don ba zai yarda da ganganci a cutar mishi da yaro ba. Baba ne ya fito aka gwada jininshi ganin girma ya kamashi suka bukaci a gwada na kanin nashi, kallan Bashir yayi yace “Wuce a gwadaka.” Ji yayi kamar zai yi ihu haka ya wuce dan tabbas suna tsoron mahaifinsu sosai, dawowa yayi É—akin yana jin kwalla na sake taso ma idanunsa, zubawa Baqeer ido yayi kaf cikin Æ´aÆ´anshi yafi ji da Baqeer sannan ya kwallafa rai a kank Baqeer É—in ne zai samu abinda shi bai samu ba.

Hannunsa yasa ya riÆ™o hannunshi yana sake bin fuskarshi da jikinshi da kallo zuciyarsa na sake karyewa, ya daÉ—e riÆ™e dashi kafin yace “Allah ka dubeni ka tashi kafaÉ—n yaran nan, Allah ka dube ni da idan rahama….” nurse ce ta shigo ta Æ™ara sa mishi wani jinin wanda aka É—ebe daga jikin Bashir.

Baba kallon Salim yayi shida Bello da suke tsaye carlo-carko a gefe yace “Please ku tafi mun gode da kulawa.”

Jiki a sanyaye suka juya, Baba ya saÆ™e riÆ™e Baqeer bayan fitarsu kawai hawaye ne yaji sun zubo mishi, tabbas in har wani abu ya samu Baqeer ba zai yafema Alhaji Sunusi Karaye ba, idanunshi ne suka sauka kan bandage É—in da ke naÉ—e a wutsiyar hannunshi na dama, hankali a tashe ya Æ™arasa É“angaren daman ya É—an É—aga hannun, nan danan ya fito cikin sauri yana neman nurse É—in data fito daga É—akin, a gaban wani É—akin ya hangota cikin sauri ya Æ™arasa yace “Nurse me ya samu hannun daman yarona?”

Kallonshi tayi sannan tace “Muje na duba.” Tare suka shigo ta nufi É“angaren dama tana dubawa ta kalleshi tace “Karaya ce a wurin…….”

“Karaya? Kinsan me yake yi da hanun da zaku ce karaya?”

Cike da rashin fahimta tace “An mai É—ori insha Allahu zai warke.”

Cike da faÉ—a yace “Kina tunanin dan kun mai É—ori hanunshi zai dawo yanda yake ne? In ya kasa amfani da hannun fa ko ya kasa yin aikin painting É—in da ya saba? Gasar da zai shiga ta zane da za ayi a karshen watan nan fa?”

Bashir ne ya Æ™ara so da sauri dan ance ma ya kwanta ya huta yace a’a ahi gida zaije, nan ya wa nurse alamar ta tafi, tana fita ya zabgawa Bashir wani kallo yace “Baka da hankali ne? Ko ka É—auka ban ganka bane?”

“Baba ita me nene laifinta? Kula dashi fa kawai suka yi? Sannan shi me yasa kowa na zaune agida amma shi yana yawo a titi da majalisa?”

“Kana sake magana zaka ga É“acin raina, shashashan banza kawai.”

Bashir bakinshi yaja yayi shiru, Baba kallon hannun yayi yana ji ya zai yi idan yaron nan bai warke ba? Shikenan rayuwarshi ta shiga garari, duk wani buri nashi ya tarwatse.

 

Hmmmm…

 

 

 

#Baqeer

#Shalele

# RayuwadaKaddara

#Hawayena

#UMMASGHAR

#AYUSHERMUHD

 

*BAQEER*

Ayusher Muhd

Umm Asghar

 

*KURMAN ALLO*

Asmy b Aliyu

Jidda Aliyu

 

*AKWAI SIRRI*

Zee Bawa

Hajja ce

 

*MUTALLAB ASAD*

Nana Diso

Billy S Fari

 

*KULUWA*

Zee yabour

Sadiya Dan

 

Duka Biyar É—in akan 2k

Hudu 1600

Uku 1200

Biyu 800

ÆŠaya 500

 

Close Menu