Akanshi Hausa Novel Complete
AKANSHI
BY
*KADIDJA BASHIR*
daga alqalamin
*Maman Abdallah*
Marubuciyar Littafin
*MUGUNTA FITSARIN FAKO*
And new
*AKANSHI*
PAID BOOK
*PERFECT ESSENTIAL WRITER’S ASSOCIATION*
*P.E.W.A*
*Home of perfect writer’s* *together we stand
*ESSENTIAL WRITER’S*
*Pen is mightier than* *the sword*
_Bismillahir rahamanir rahim
Pree
Page *1&2*
Shuru kake ji kamar babu wani mai rai a cikin wajan, baka jin komai sai Saukar Nunfashin Mutanan dake zaune .
Yadda tsarin wajan yake shi ya tabbatar mini da kotu ne , gyara tsayuwa ta nayi na fuskanci inda nake Tunanin nan ne aka tanada dan zaman Alƙali, wani Babban mutun nagani mai cikar kamala da haiba, sanye da Manyan Kaya na Alfarma, da Hirami akan shi, ya sanya farin glass a Idanunsa, wanda yake ƙara masa ƙarfin gani, Sakamakon yana fama da lalurar Idanu, ga kuma Shekaru da suka fara ja.
Dattijo dan kimanin shekaru sattin da uku Duniya, Malam Inuwa Masa’ud kenan, AlÆ™ali mai Gaskiya a cikin jerin AlÆ™alan da da jama’a suke alfaharin dasu.a wannan Gari, É—an gani Kashenin Gaskiya ne komai ÆŠacinta, akan riÆ™on Gaskiyar sa, dayin Hukunci kamar yadda ya sauka daga sama , aka yi masa sanadin duka Iyalan sa har lahira.
Matar Musaki Hausa Novel Complete
Ameen ameen naji suna faÉ—a duka wajan , sai yanzu na lura ashe tun Shigowa ta wajan adu’ar buÉ—e taro ake, tare da yin salati ga Ma’aikin Allah .
yana daga cikin Æ™a’idar Malam Inuwa komai ayi shi akan sunnar Ma’aiki s.a.w , shi ya Umar cemu da mu Æ™awata wajan zaman mu , da yin Salati a gareshi, dan haskene a garemu ranar tashin AlÆ™iyama.
Ubangiji da kansa yayi alƙawarin duk wani abun da aka ɓudasa da sunan Habibin sa, to yanajin ƙunya maido da wannan abu ba tare da an duba kuma an karɓe sa ba.
Jama’a nace Annabi Muhammadu ………..
Duk wanda bai ce S.A.W ba to shine babban marowaci a wannan Duniyar, haka ya faÉ—a s.a.w.
Wajan zama nima na nema na zauna a kusa da wata Mata, kukan da take ne a hankali yasa na kalli sashen da take zaune, Farar Mace ce amma ba fara cancan ba, tanada tsago guda biyu a gefe da gefen Fuskar ta, Fuskar nan duk ta Kumbura alamar kodai tasha kuka ko kuma batada Cikakkiyar Lafiya, Atamfa ce a jikin ta mai Mafaidaitan kuÉ—i wajan saya, da alama matar tana da tsabta sosai dan ko takalman da ke Æ™at’farta a wanke yake tas kamar ba Æ™asa ta tako kafin ta iso kotun ba.
Juyowa tayi Sashen da nake, ganin zata kamani ina kallon ta yasa na maida Hankali na wajan Alƙali.
Gam, gam, gam ya buga Teburin da yake gabansa da Gudumar Hannun sa, nan waje ya sake yin tsit kamar ba kowa, cikin DaddaÉ—an Muryar shi mai Cikar kamala yace ” maga takarda muna sauraron ka” , wani dan Matashi ya mike daga inda yake a Zaune, ya miÆ™a wa alÆ™ali takardun da yake Hannunsa ta Æ´ar kantar da take tsakanin su kafin ya daidaita tsayuwar sa yace ” yau muna biyar ga watan Rabi’ul Auwal , wanda yayi daidai da Bakwai ga september, ya dauko wata Takardar da take ajiye akan sauran takardun da yake gaban sa , ya cigaba da cewa yau za’aci gaba da sauran Shari’ar da ake yiwa Hasiya Ibrahim, ana zargin ta kashe Mijin Auren ta Mukhtar, bayan basu fi watanni Biyu da Kasancewa Ma’aurata ba ” yana faÉ—in hakan ya zauna a Mazaunin sa .
AlÆ™ali inuwa ya kalli securityn da yake kusa da kanshi a tsaye yace ”a shigo da wacce ake zargi ” , cikin Girmamawa ya Amsa tare da barin wajan.
Wannan tsarin Malam Inuwa ne , killace wanda ake kan Shari’a dashi daga wajan Mutane, dan kar yawan zantuttukansu ya giÉ“i tashi ya kasa bada Amsar Tambaya yayin da ake masa, Æ™arfe bakwai daidai Motar Æ´an’sanda ta kawo ta Kotun tare da Rakiyar jami’an da zasu tsare ta har a gama Shari’ar a ga Sakamakon da ta bada, shine aka fice da ita can Cikin kafin lokacin Shari’a yayi.
Shigowa akayi da ita kanta a kasa , Matashiyar da za’a iya kiranta Budurwa a inda ba’asan anyi mata Aure ba, sanye take da baÆ™ar abata ajikinta, da kuma baÆ™in hijaÉ“i, Hannun ta a cikin ancor haka securitys guda biyu mata suka shigo da ita, bisa jagorancin wannan securityn É—an aike.
Har wajan da aka saba sakata ta tsaya suka kaita, kafin daya ta tsaya daga dama É—aya kuma daga hagu, har yanzu kanta a kasa .
Gyaran murya Malam Inuwa yayi yace ” Masha Allah, Allah ya kuma nuna mana yau a Matsayin Rana ta Æ™arshe da za’a gama wannan Shari’a, Hasiya ” ya ambaci sunan ta .
ÆŠago da kanta ta tayi , masha Allah babu wanda zai ga Fuskar Hasiya bai yaba da kyawun ta, ba fata bace, ba kuma za’a kirata da baÆ™a ba, rashin walwalar da yake kan Fuskar ta shi ya bayyanar da Tsananin Tashin Hankalin da take ciki, a da yarinya ce mai yawon raha , amma yanzu Æ™unci shine abokin rayuwar ta.
Sashen da mutane suke zaune ta kallo, karaf suka haɗa ido da Mahaifiyar ta, wacce har ta sauya kamanni a kamar data santa a da, da sauri ta kauda kanta zuwa wani gefen, dan bata san ɗan ƙwarin gwiwar data samu ya ƙoranye Sanadiyar ganin rauni a tare da Mahaifiyar Tata.
” Hasiya ” ya kuma kiranta a karo na biyu, cikin Muryar ta data gaji da kuka har ta dashe ta amsa da ” na’am ” , ” yau ne rana ta Æ™arshe dan gane da zaman da muke akan Mutuwar mai gidan ki Mukhtar, shin sami lauyan da zai kare ki ” alÆ™ali ya tambaye ta cikin Mutuntawa. ” a’a Ni har yanzu banida lauya ” ta faÉ—i kanta a Æ™asa , ”shin Lauyan wa’yanda suke Æ™ara yana kusa ?” yayi Tambaya yana kallon sashen da Lauyoyi suke zaune, ” eh ina nan Allah ya Gafarta Malam ” cewar Barister Lawali ÆŠalha tare da mekewa daga inda yake zaune , ya fito dan filin dakeTsakanin su da inda Hasiya take , ya kuma cewa ” Allah ya Gafarta Malam wannan abu a bayyane yake cewa Hasiya ita ta kashe Mukhtar bisa La’akari da Hujjoji dana bayar tun a Zaman farko, saboda haka ina neman Alfarmar wannan kotun Muslunci mai albarka data Hukunta wannan baiwar Allah daidai da Hukuncin da Ubangiji ya zartas akan duk wanda ya kashe rai ba akan hakkin Shari’a ba ” ya kara da cewa idan har ba ita ta kashe shiba ai da tuni sun nemi Lauyan da zai kare ta, ranka ya daÉ—e tsawan lokaci ana ta É—aga wannan Shari’ar a wannan karon ina neman Alfarma da ayi Gaggawar yanke Hukunci Nagode ” ya karasa maganar da risinawa alamar Girmamawa kafin ya komawa wajan zaman sa ya zauna.
Malam Inuwa ya fara wasu Æ´an rubuce rubuce a takardar dake gaban sa.
Kukan Maman Hasiya ne ya cika ilahirin kotun , da gudu tazo wajan da tarin Lauyoyin da zasu kai takwas wasunsu suna jiran lokacin da za’a gabatar da Shari’ar da suke Jagoranta, kusa da Æ™afafuwan su ta zube tana kuka mai tsuma rai, Nunfashin kamar zai bar Gangar jikin ta, tabbas wannan Jarabawar Hasiya ce amma ita tafi ta jin zafi da raÉ—aÉ—in wannan Intila’in daya tunkaro su Bagtatan ba Tsammani, cikin kuka mai Tsuma rai tace ” dan Allah ku taimaka mana , kamar yadda Allah ya taimake ku ya baku dama, wallahi bata aikata abinda ake zargin ta dashi ba, ta Æ™aÆ™a zata kashe mutumin datafi so sama da Rayuwar ta, *AKANSHI* bata ji , kuma bata gani, wallahi ba ita bace, dan Allah ka taimake Ni ka tsaya wa Æ´ata dan Allah” Mama Kuburah ta Æ™arasa Maganar leka riÆ™e Æ™afar Lauya Lawali wanda ya gama zuba zance da bada Hujjoji akan Lallai Hasiyar ita ta kashe Mijin ta Mukhtar, cike da Dubara ya janye Æ™afar sa daga riÆ™on da tayi masa, yayi wani Murmushi mai sauti, wanda sai da ya Hankalin jama’ar dake Kotun, wanda kowa yake faÉ—in albarkacin bakin sa game da Shari’ar .
Cikin Kissa, Makirci da iya É—aure Mutun yayi kalar tausayi yace ” haba Mama wannan ai ba Girman ki bane, koma miye ai bai kai har ki dafa Ƙafafuwa naba, wannan abu dai anriga da anyi shi, ina mai baki Shawara É—azu maiÆ™a wuya ku faÉ—i Gaskiya, ta yiyu ta sami Sassauci wajan yanke mata Hukunci, koda dai kowa yasan Hukuncin wanda ya kashe Mutun a Shari’ar Muslunci ” ya ci gaba da cewa nidai abinda nake gani kenan, amma idan har kina Tunanin zaki samu wanda zai kare ta shikenan, sai Ku Gabatar dashi a Matsayin Lauyan da zai kare ta , wannan Shawara ce ” ya faÉ—a yana É—aga kafaÉ—a alamar ya rage nata.
Malam Inuwa ya kuma buga Guduma a karo na uku, jin duka kotun ta Hargice da Cecekucen jama’a , nan kuwa waje yayi tsit , kowa ya haÉ—i sauran zancen da yake bakin sa, bakajin komai sai kukan Mama da Ajiyar Zuciyar Hasiya, cikin É—aga Murya AlÆ™ali yace ” Malama Kuburah a karo na karshe zan É—aga wannan Shari’a a karo na huÉ—u kenan, jiya iyau, babu abinda ya canja a Tsakanin kwanakin da muka baku akan ku sami Lauyan da zai kare ku, baki shike yanka wuya, idan zaki tuna akwai Lokacin da ita kanta Hasiyar ta amsa cewa *AKANSHI* ne , bazamu san ma’anar wannan kalma ba , sai dai idan ita ce ta faÉ—a da bakin ta, ko kuma munji daga bakin Lauyan ta, saboda haka , na daga wannan Shari’ar har zuwa Ashirin ga wata, zuwa wannan Lokaci ina fatan zaku sami Mafita da yardar Ubangiji, sannan kuma za’a cigaba da tsare Hasiya a Gidan Yari har Lokacin da muka É—auka ya Æ™araso, abu na biyu a wannan karon za’a iya Ziyartar ta, kama daga Iyayenta, kodai wasu Makusantan ta” Malam Inuwa ya faÉ—a haka tare da yin Rubutu a Takardar dake gaban sa .
” Ninan zan Tsaya mata ” suka ji Magana daga Bakin Æ™ofar shigowa Kotun…………….
Ayi Haƙuri ba yawa.