Ad Code

Tsananin Rayuwa Hausa Novel Complete

Tsananin Rayuwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

TSANANIN RAYUWA

 

 

 

*NA*

*MARUBUCIYA (A’ISHA YAHAYA TANKO)*

 

 

 

*AMINCI STAR🌟 WRITER’S ASSOCIATION*

 

(A.W.A)

 

 

 

K’ungiyace ta amin tattaun marubuta wanda suka k’ware wajan kawo muku litattafai na hausa masu ma’ana wa inda zasu nisha d’antar daku gamida fad’akar daku wa’azantar daku da zakulo muku abubuwanda zasu amfanemu musamman mumata aminci da aminci sed’an halali.

 

*ALKALAMI✍🏾YAFI TAKOBI🗡️*

 

 

_Wannan littafi yana ɗauke da abubuwan daban-daban na tausayi da Al’ajabi nasan idan ki/ka karanta sai ka zubar da hawaye_

 

*PAGE. 1*

 

Fatima da Sadiya ne zaune a ƙofar wani katafaren gida, kallo ɗaya zakai musu kasan suna neman taimako.

Gidan Aunty Hausa Novel Complete

Na taka burki ina ƙoƙarin fitowa daga cikin motar naji sautin muryar ɗaya daga cikin su tana cewa.

 

“Ke Sadiya mu gudu kar ya sace mu”.

 

Turus nayi jikina a sanyaye na jingina a jikin murfin k’ofar,ina saƙa abubuwa a zuciyata har na dena kallonsu saboda irin gudun da suke yi.”

 

_”Wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu, da kun tsaya zan taimake ku, amma rashin sanin waye ni yasa kun yiwa kanku, in sha Allah nayi alƙawarin zan taimake ku aduk inda kuke.”_

 

Inji Yusuf lokacin da yake furta wannan kalaman a cikin zuciyarsa.

 

Yana gama faɗa ya shigewarsa mota ya tada, ya fara tafiya a nutse yake toƙi har ya isa cikin gida.

a falo ya tarar da Amina tana kwance tana danna waya.

 

“Sannu sarauniyar mata,ana sana’anarne?, baki san bama nazo bare kizo ki tare ni, ina yaran ne banji motsin su ba,ko basa nan ne?”.

 

 

Ta ɗago kai cikin sauri tace.

 

“Sannu da zuwa Hubbi sun gama cin abinci, su kai bacci nima kai nake jira.

to ya hanya?, ko duk gajiyar ce tasa na ganka haka ko yunwa ce?”.

 

Inji Amina.

 

“Duk abinda kika faɗa akwai a tare dani, yanzu inaso kafin ki kawo min abinci ki haɗa min ruwan dumi nayi wanka”.

 

“To Hubby duk abinda kakeso yanzu za’ai maka shi”.

 

kaci gaban Tsakanin Rayuwa

 

 

Ta k’arashe Maganar tare da mik’ewa tsaye ta nuni bayan gida tana k’oka’rin haɗa masa ruwan.

 

Tunanin yaran nan ne ya dawo masa, ji yai hankalinsa Yayi mutuƙar tashi saboda ganin k’arancin shekarun su, shin ta ina zai sami mafitar da abinda ya ƙudura acikin zuciyarsa? ji yai an tsaya akansa ana magana da cewa.

 

“Dama ni nasan akwai wani abun da kake shirin ɓoye min, ga shi yanzu alamu sun fara nunawa tun ɗazu na jima akanka amma baka sani ba,to bama wannan ba yanzu ka tashi muje na gama haɗama ruwan wankan”.

 

 

Cewar Amina.

 

 

Tashi yayi a sanyeye ba tare da yace uffan ba, bakinsa ya gaza cewa komai Toilet ya dosa cikin ƙank’anin lokaci ya kammala komai.

 

 

Haka ya iske ta afalo ta haɗa masa abinci kala-kala nan ya kwasa.

 

A can riga kuwa Fatima ne da Sadiya zaune cikin yana yin damuwa.

 

Inna tace

 

“Nifa bana san irin wannan shirman naku ai gashi nan kun dawo baku samo mana ko kanzo ba, ga kawunku tunda ya fice har yanzu ba’aji duriyarsa ba ko yana raye ko yana mace Allah ne masani, ni dai zan tsunduma cikin birni, don na samo mana mafita, wannan rigar tamu ba’a taimakon mu sai mun fito a dinga zunbe mu, wai harɗo ya tafi ya bar mu cikin kunci da wahala”.

 

 

“Nifa Inna nayi alƙawarin a wannan lokacin zan samar miki da farin ciki, amma inaso ki bari na dinga fita ni kaɗai saboda ki gane irin kwazo nah”.

 

 

Inji Sadiya.

 

“Bana san rawar kai kinsan mutanen burni basu da kirki, kar su sace ki kamar yanda suka sace kawunku harɗo, ku dai yi haƙuri wata rana sai labari”.

 

A can gidan Yusuf kuwa yana kwance a falon Amina ta fito daga cikin ɗaki

” wai ka fasa zuwa rigar ne?”.

 

Cewar Amina.

 

“Zanje, hutawa nake ne Musa ne nake jira ya fini sanin ta kan rigar.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Taku har kullum

 

 

 

*A’ISHA YAHAYA TANKO*

*TSANANIN RAYUWA

 

 

 

 

 

 

*NA MARUBUCIYA❤️A’ISHA YAHAYA TANKO*

 

 

 

 

 

 

*PAGE 2*

 

 

 

Jin ƙarar wayar Musa ce ta katse su daga maganar da suke yi.

 

“Ok tohm gani nan fitowa”.

 

Ya ajiye wayar tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye yana gyara hular sa yace.

 

“Duk nonon dake cikin garin nan amma kice sai na cikin riga zaki sha?”.

 

Cewar Yusuf.

 

“Haba Hubby ai ko bayan duniya nace kaje ka nemo min abinda nake buƙata sai kaje”.

 

 

“Wannan haka yake uwar gidana duk abinda kike buƙata shi za’ayi”.

 

 

Yana gama faɗa ya nufi hanyar fita waje ya iske Musa a jingine a jikin murfin motar hannu ya bashi suka gaisa.

 

Tafiya suke cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yusif ya nunfasa yace da Musa.

 

“Kasan wani abu abokina?”.

 

 

Musa yace.

 

“Sai ka faɗa ina sauraronka”.

 

Ya faɗa yana dariya.

 

“Wallahi jiya wasu yara na gani a ƙofar gidan Alhaji me rumbun Allah ya isa, har na tsaya da zummar zan taimaka musu naga sun gudu, ko tsoro suke ji nikam abin ya bani mamaki kwarai da gaske saboda karancin shekarunsu,amma naci alwashin duk inda suke Allah zai haɗa ni dasu”.

 

 

Cewar Yusuf.

 

Dariya Musa yayi yace.

 

” Nasan dai unguwa bata jewar banza nasan halinka abokina kai mugun kwaro ne,idan har ka hango abu sai ka cake shi sannan zaka ji dadi”.

 

Gaba ɗaya suka yi dariya a haka har suka karaso cikin rigar fulanin nan suka iske masu sai da nono kala-kala.

 

Sadiya tace.

 

“Haba Inna ai ba maganar rawar kai,ke dai ki zuba ido ki gani wata rana ma sai mun bar rigar nan da zama,mun koma cikin birni mun gina gidan mu”.

 

“Tab amma sadiya baki da hankali waye zai bamu kuɗin da zamu gida a burni?, ko kin manta mu ɗin su waye sai dai ke ki koma amma mu ba inda zamu koma muna nan,ki dai yi hankali da mutanen cikin birni basu da imani sace mutum a wajen su tamkar ɓatan kwabo ne a wajen yaro”.

 

Duk maganar da suke Inna tana jinsu.

 

Can tace.

 

“Kefa Sadiya kina da matsala na kasa gane inda kika dosa,wa muka bawa ajiye balle mu karɓa da har zaki ce zamu koma cikin birni da zama,mu da ko abincin kirki bama samo mu ci,bari komawa birni da zama,ni dai ki rufa min asiri kar a sace min ke na shiga uku”.

 

Cewar Inna.

 

“Ke dai Innar mu ki kwantar da hankalinki ki kuma zuba min ido kiga aiki da cikawa”.

 

 

Cikin riga kuwa Yusuf ne da Musa suka gama cinikin nono aka fara jera musu a cikin mota, Yusif ya zubawa wata kyakkyawar yarinyar ido wadda take shirin tun karar inda suke,can tunaninsa ya tuno masa inda ya taɓa ganin wannan fuskar ji yai ana kiranta da Sadiya nan ya tuno ɗaya daga cikin yaran daya gani jiya kenan ,a cikin gari ashe dama zai kara ganinsu a kusa kenan amma yaji daɗi ya faɗa a ransa ji yai Musa ya dafa kafadarsa yace.

 

“To Abokina idan ka gama tunanin ka sameni a cikin mota ni dai kaga tafiyata”.

 

 

A firgice ya juyowa wajen Musa yace.

 

” Tsaya mana abokina kaji ina labarin dana ke baka a hanyar mu ta zuwa nan,to wannan yarinyar da ka ke gani itace Bbnga ɗayar ba, amma kaga yanzu dole duk sati mu dinga kawo ziyara nan har sai na sami amincewar ta”.

 

Gaba ɗayansu suka sa dariya tare da shigewa cikin motar da gudu Musa ya tada motar kamar zai tashi sama kowa ya bi motar da kallo suna ganin Mamakin irin wannan gudu,tafiya suke suna tattaunawa akan lamarin yaran nan Musa yace.

 

 

“Amma fa kana ganin wannan yarinyar baka ɗauko ruwan dahuwar kanka ba, saboda naga dudu bata wuce shekara goma sha uku ba, kawai dai tana da ɗan’girman jiki ne”.

 

Cewar Musa.

 

 

“Abokina kenan kadai ka zuba ido kaga inda wasan zai fara”.

Close Menu