Ad Code

Nisan Kiwo Hausa Novel Complete

Nisan Kiwo Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Nisan Kiwo Hausa Novel Complete

_Mom Islam_

 

 

Domin samun more pages kuyi following É—ina arewabook

 

 

Page1

 

“Shin kinsan da cewar ciwon mahaifiyarki baya buÆ™atar damuwa akan me zaki dinga kusantar ta bayan tace babu abinda ta tsana kamar ta buÉ—e ido ta ganki?”

Cikin shesheÆ™ar kuka Anum tace “akan me zata dinga furta min irin waÉ—annan kalaman kodan saboda taga Allah yayini da Halitta ba irin taku ba?”

Tai maganar tana toshe bakinta da hannu saboda kuka yaci Æ™arfinta. cike da tsananin damuwa gami da tsantsar tausayi Jannat ta kamo hannun Anum suka fito daga É—akin da Ummu take, a parking space suka tsaya, inda jerin danÆ™ara-danÆ™aran motocin masu gidan ke a parke, “Anum nasani abin da ciwo ace mahaifiyarka wace ta É—auki cikinka tun yana watanni É—ai-É—ai har tara da kwanaki yau a wayi gari tace bata Æ™aunarka duk inda zakaje kaje wannan sam ba É—abi’a bace, sannan gaskiya anyiwa Allah butulci”

Kyandir Romantic Love Story Hausa Novel

Jannat ta faÉ—a tana dafa kafaÉ—ar Anum, magana take son yiwa Jannat É—in amma ina bakinta da zuciyarta gabaki É—aya rawa sukeyi yayinda takejin kanta nayi mata matsanancin ciwo kamar zai tsage, cikin Æ™arfin hali tana dafe da kanta tace “anty Jannat Ummu fa musamman ta baro gidanmu saboda ni, ta dawo gidan mutanen da ba danginta ba ta tare, tace inci gaba da zama acan, nikam bazan iya zama ni kaÉ—ai a gidan ba duk da akwai Arshi”

“Haba Anum ya ya inason kawo miki ingantacciyar shawara kina kawomin wani zaman gidanku, ki nutsu ki saurareni, duk da cewar Allah yayi miki Halitta guda biyu, mace da namiji kinga mudai ba wani hali ne damu da zamu iya taimakawa ayi miki aiki ba, tabbas Arshi tana bani tausayi kodan Lalurar juyewar Æ™waÆ™walwa da take tare dashi, amma wlhi nafi tausaya miki, dama shawarar da zan baki itace..”

Kiran Ummu ya katse Jannat, ta amsa tare rugawa a guje.

Anum ta durƙushe a gurin zuciyarta na faman yi mata zafi, ta kalli takalmin mazan dake a ƙafarta sannan ta shafi gashin bakin da ko ta aske gurin a baƙi yake zama, sannan ta kalli nonuwanta da suke a tsaye ƙyam kafin ta taɓo gabanta da ya kasance akwai na maza a jiki, ta ɗaga idanunta sama tare da dawo dasu ƙara hawaye na zuba sharr kamar an buɗe famfo,

“Jannat wlhi tallahi idan kika Æ™ara dawomin da Anum cikin gidannan mai rabani dake sai Allah tunda na gaya miki bana sonta bana sonta ko ana dole ne? inace ni na haifeta sannan nace bana Æ™aunarta?”

Ummu tai maganar tana nuna Jannat dake tsaye a bakin Æ™ofa bata ma samu damar Æ™arasa shigowa ba, a hankali ta tako tare da zama gefen Ummu cikin tausasa murya tace Ummu mai yasa kikeyin abu sai kace ba musulma ba, karki manta idan har kina tunanin kin gujeta ne, nan gidan da kike gadara dashi wlhi masu gidan suna iya dawowa a koda wane lokaci sannan sai sun tozartaki dan ba isasshen mutunci ne dasu ba”

Ummu ta miÆ™e kamar mai shirin yin tafiya, sai ta dawo da baya ta watsawa Jannat mari tana hoci tace “kar Allah yasa su bari inkai safiya, gidane nazo bazan fita ba tunda dai kema bana ubanki bane ai saiki barni da masu gidan ko?”

Dafe da kumatu ta miƙe daga zaman da tayi akan gado, kana ta miƙe jiki a sanyaye ta raɓa ta gefen Ummu ta fice, tana fitowa harabar gidan ta hango Anum na a durƙushe a gurin da ta barta ga uban rana da akeyi mai zafi, da sauri ta karasa gurin Anum ɗin tare da kamo hannunta, sukayi hanyar fita bakin get.

Jiki a sanyaye Jannat ta buÉ—e get É—in suka fice, duk da shirun da ya ratsa anguwar bai hanasu samun wani dakali a Æ™ofar gidan dake a kusa da wanda suka fito suka zauna ba, har yanzu Anum kuka takeyi, Jannat ta sanya hannu ta buÉ—e kan Anum, da sauri ta fashe da kuka tare da rungume Anum, cikin kukan take cewa “Anum akwai matsaloli a tare dake masu tarin yawa, gashin kanki irin na maza ga gemu sannan kuma ga nono bayan nan..”

“Anty Jannat ki sanar dani abinda kikeson gayamin lokacin da Ummu ta kiraki”

Anum ta faɗa sbda wannan dogon lissafin da sukeyi ba wani ƙarewa zeyi ba,

Jannat ta mammatsa hannayenta kafin ta shafi gefen fuskarta da yayi jajir sannan tace “naji kafin nan gayamin nan gurin ya tashi ko?” Kallon kumatun nata Anum tayi cikin raunatacciyar murya tace “Ummu ce ta mareki ko?”

Jannat ta gyaÉ—a kai kana tace “karki damu idan Ummu ce zatayimin abinda yafi haka tunda yanzu ina tare dake, amma bata tunanin rayuwar Hajna?”

Sosai takaici ya kama Anum sbda a halin yanzu zuciyarta ta fara bushewa sam bata tunanin wata Hajna tunda dukkansu abin a taimaka musu ne, amma yanzu kam kanta take tunani, “ki mance da Hajna”

 

Anum ta faÉ—a.

“Toh shikenan, dama shawarar itace kinga yau baki da gurin kwana, sannan a gidanmu ma ba lallai su yarda mu kwana a tare dake ba, amma da zaki yarda da nayiwa Æ™anwar momyna magana ta É—aukeki aiki duk wata kina turomin da kuÉ—in cikin account É—ina, sai mu dinga tarawa har ya isa wanda za’ayi miki aiki, wlhi har makaranta zata saki, matsalar É—aya ce dole ki kasance a suffar mace saboda wlhi mijinta baya Æ™aunar namiji a gidansa, akan hakan matarsa ta tsayar da aihuwa, yaransu biyu Jumayma da Arshi, hamshaÆ™in mai kuÉ—i ne sannan kuma dole Æ´an aiki tare da yaransa suke kwana, amma fa ansha kawo masa Æ´an aiki wlhi yana korarsu dan ranar da naji Æ™anwar momyn tana faÉ—a Æ´an aikin da aka yi musu korar kare sunkai su ashirin”

Anum ta zaro ido kafin tace “Anty Jannat gaskiya bazan iya ba, saboda daga lokacin da suka tabbatar da ni MATA MAZA ce kinsan na shiga uku, inaga nikam kasheni zeyi kamar inda Ummu take buÆ™ata”

Jannat ta toshe mata baki, tare da cewa “haba kisa, shidai ya kasance mai baÆ™ar zuciya ne, dan wlhi nima nan da kika ganni ko gidan bana zuwa saboda akwai ranar da Arshi tayimin leifi na duketa bakiga É—an dukan ba wlhi yana shigowa ya tambayeta tace nice, kawai sai nayi tsuru-tsuru, gashi sangameme ya tako har inda nake zaune saman kujera ya shaÆ™emin wuya, yace min, wai su biyun sune rayuwarsa zai iya kashe kowa a kansu in kiyaye,

Sosai hantar cikin Anum ta kaÉ—a, cikin karyar zuciya Anum tace “tunda kince yaran basu da kunya aiko dai bazamu shirya ba, Gara na shimfiÉ—a kwali na nemi gurin kwana ko a gefen titi”

 

“No ki bari muje a gyara miki gashin bakinnan, saboda nikam bazan iya ganinki cikin damuwa ba”

Jannat ta faÉ—a tana rausayar da kanta.

Sosai tausayin Anum É—in ya kama Jannat,

Shiru ne ya biyo baya na Æ´an wasu lokuta kafin Jannat tace “bazaki kwana akan titi ba, zan tafi dake gidanmu zuwa gobe da Asbha kafin su momy su fito sai muyi shawarar abinda ya dace”

Tabbas Anum tana jinjina tausayi tare da jarumtaka irin na Jannat sbda tasan idan har iyayen Jannat É—in suka samu labarin Jannat É—in ta kwana tare da Anum tabbas zata fuskanci mummunan hukunci, domin mutane da yawa suna suffantata da namiji, ita kuma Anum É—in abinda bata taÉ“a kawowa kanta ba kenan, tana sawa a ranta koda yaushe ita mace ce, “toh” Anum tace dan itama kanta ta fara tsoron kwana a titin.

“Inda abin zai kasance, tunda tsakaninki da gidanku akwai nisa sosai gashi har an fara kiran sallah, zan fara shiga gidanmu, sannan da zarar na shiga zan yaudare mai gadi akan yazo ya dubamin wani abu acan baya, kinaji nace “subahanallah sai ki shigo a hankali ki É“uya gurin motocin Dady, nikuma zan zo sai muyi shawarar inda za’ayi ki shiga ciki”

Anum ta kalli Jannnat dake ta faman kawo musu mafita, kafin tace “Nagode anty Jannat Ubangiji ya saka miki da alkairi”

Jannat É—in ta miÆ™e tana cewa “karki damu fatan nasara zakiyi mana”

Suka fara tafiya riÆ™e da hannun juna, koda suka fito bakin titi da yake gidansu Jannat É—in dole sai sun tsallaka titi, mutane sai kallon Anum sukeyi, wasu na tsokanarta wasu na nunata da yatsa, daga Anum É—in har Jannat É—in sunji zafin hakan, musamman ma wacce abin yake a kanta, cikin tausasa murya Jannat tace “Anum daga yau karki sake yawo babu hijabi kinji?”

Anum ta zura hannayenta cikin aljihun wandonta kamar dai inda maza sukeyi kafin tace, “anty Jannat tun ina Æ™arama Ummu ta sabarmin da rayuwa a haka, wlhi rannan da na kwatanta sanya hijabi jinayi ya shaÆ™emin wuya sai naji sam babu daÉ—i dole na cire”

Jannat ta zaro ido tare da cewa “aiko inhar bazaki dinga saka hijabi ba wlhi duk gidan aikin da za’a kaiki matsala zaki samu indai ba aikin gida kamar mai gadi da dai sauransu zaki samu ba”

 

“Anty Jannat wlhi dan kawai kar inyi miki musu ne, amma duk sanda na kalli kaina a mirror sai tausayin kaina ya kamani, duk da nasan saÉ“o nakeyi nakance, mai yasa Allah bai dauki rayuwata ba tun inda jaririya, dan bana raye babu wani Æ™alubale da zan fuskanta musamman ma ga mutane uwa uba harda mahaifiyata”

 

Jannat ta dafe kanta, kana tace “idan har bazaki godewa Allah da baiwar da yayi miki ba wlhi bazaki godewa azabarsa ba, inaso ki sani kefa da ranki da lafiyarki sannan zaki iya yin komai na aiyuka banbancin halittace ce dake, Æ´ar uwarki fa? da yanzu zakiga ana wasa da dariya da ita yanzu zata juye kamar ba ita ba?”

Anum tace “inayiwa Allah godiya, kinsan sharrin zuciya babu abinda bata aiyyanowa É—an adam musamman ma idan yana fuskantar tsangwama da tsana..”

Isowarsu bakin get É—in gidansu Jannat ne yasa dukkansu yin shiru tare da kallon juna,

Jannat takai bakinta dai-dai saitin kunnen Anum, kome ta gaya mata oho naji Anum É—in tace “toh”

Anum ta koma can baya Jannat É—in taje kusa da get tayi nocking lokacin har an fito sallahar magriba, “waye” mai gadi ya faÉ—a, “Nice haba malam Lado ka buÉ—emin mana”

Ƙaramar Æ™ofar ya buÉ—e kafin ya washe haÆ™ora yana cewa “aiko Hajiya jannatu ki shirya karÉ“ar faÉ—a daga gurin Hajiya domin kuwa tun tuni take sababi” ya Æ™are maganar yana tafa hannu, taÉ“e baki tayi tare da nuna shi da yatsanta kafin tace “ni dan Allah karka dameni ka matsamin in wuce”

Tai maganar tana gyara É—an siririn mayafin dake a kafaÉ—arta, da sauri ya bata guri ta wuce, da sauri ta nufi can bayan É—akin mai gadin gurin ya kasance da kyawawan flowers masu kyau da ban sha’awa, tsala ihu tayi tana cewa “Lado dan Allah zoka taimaka min Please bansan meye a gurin ba” yana tafe yana jin radio yana cewa “kedai Hajiya wani lokacin idan kina abu sai kace Æ´ar yaye, ke da zaki wuce É“angarenku mai ya kawoki É“angare na, koda ya iso gurin tana tsugunne kanta a Æ™asa, Æ™arar horn É—in motar dadynta da ta karaÉ—e musu kunnuwa ne yasa tai saurin dafe Æ™irji tare da waro ido sbda gabaki É—aya zuciyarta ta tsinke ta riga ta gama rayawa a zuciyarta Dady yaga Anum angama shikenan kashinta ya bushe….!

 

Mai kuke tunani Anum zata samu damar shiga gidansu Jannat kuwa?

Idan masu gidan da Ummu take suka dawo ya zatayi?

Ya kuke tunanin Arshi zatayi bayan babu kowa a gidan sai ita kaÉ—ai?

 

Amsarku tana cikin littafin NISAN KIWO

 

Drop your comments saboda ku samu update akan lokaci, and then karku manta kuyi following account É—ina a arewabook

 

Mom Islam 08141799224

NISAN KIWO

 

Chapter 2🫰

 

https://arewabooks.com/chapter?id=652a963c3827a31172060506

 

cikin É—aga murya akace “hahahaha bazakuje ku shirya ba, gashi Aljani É—an Æ™arami harya shirya?” Momy da Dady suka ruga da uban gudu, kai tsaye É—akin farko na momy suka shiga, sukayi tsuru-tsuru, ko wanne da abinda yake saÆ™awa a ransa, Muryar Anum ta katsesu, dan sun haÉ—a baki da Jannat tace “ta rama mata dukan da Dady yayi mata ta hanyar firgitasu” aiko Jannat taje window É—in momy ta sake sauya murya tace “hahahaha ku kaÉ—ai muke jira saboda Aljanu sun taru a can inda kuke cin abinci bil adama ne kawai babu, ado zakuyi irin na bikin bil adama saboda muma munsha kwalliya” cikin sauri Dady da momy sukayi zigidir kafin…!

 

Please kuyi following account É—ina arewabook domin samun new update

 

Close Menu