Ad Code

Mutum Ko Zaki Hausa Novel Complete

Mutum Ko Zaki Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MUTUM KO ZAKI

 

*NA*

 

*A’ISHATULHUMAIRA*

 

*~Mikiya writer’s Association~*

 

*Page 1&2*

 

Gajeran labari ne.

 

Bismillahir Rahmanir Rahim.

 

 

______ Ni’imantacciyar iskar dake kaɗa korayen itatuwan da suke kewaye da manya manyan tsaunikan wajen sune suka bada wani kalar launi da tsari me matuƙar kyawun gaske, tsaunika ne manya manya guda biyu masu fuskantar juna kowane da irin tsarin da ubangiji yayi shi, yanayin su ya matuƙar ƙayatarwa kamar ginin manyan masarautu na ƙarnin baya. Ruwa ne me gudana babba tar-tar me kyan gaske da ďaukar hankali a tsakanin waďannan tsaunika wanda shine iyaka dake tsakanin su.

Jahilci Ko Al’ada Hausa Novel Complete

Kyawun ruwan da furannin dake kewaye dashi kaďai abin shagala ne wajen kallo, daga tsakiyar ruwan wani babban dutse ne a ciki wanda ya kasance hanya ta wucewa zuwa ko wane tsauni hakan ya kara kawata wajen sosai.

Ɓangaren dama shine ke ɗauke da korayen ciyayi da flowers red da yellow masu kyau da tsari wanda suka kewaye dukkan tsaunin da ɓangaren nasu baki ɗaya. Cikin tsaunin kuwa wanda girman shi da faďin shi ya wuce tunanin me tunani yake ɗauke da part-part ma banbanta da unguwan ni wanda mutanen dake rayuwa wajen ne suka sassaƙa shi suka yi muhallin zama a ciki.

Kasancewar basu da wani yawa domin ba zasu wuce mutane ɗari biyu ba hakan ya taimaka masu wajen kayata wajen ainun . Irin bishiyu da furanni dake wajejen ya ƙara ƙawata tsaunin wanda in ka shiga ba zaka taɓa cewa a cikin tsauni ka ke ba saboda tsananin kyansa, ɓangaren shakatawa da wajen swimming pool ɗin su kuwa yayi bala’in haɗuwa ga wasu kalan furanni da suke kewaye da ruwan baka taɓa cewa a cikin tsaunin yake.

Yayin da ɓangaren haggu kuma yake ɗauke da ciyawo da red din flowers gaba ɗaya masu kyau da ɗaukar hankali, cikin tsaunin babban fili wanda yake kamar babban falo ko masarauta ɗauke da wasu irin ciyawu masu laushi sai gefe manyan kofofi ne da ƙanana masu wani irin ado me daukar ido har zuwa can saman tsaunin. Tsarin cikin yayi matuƙar kyau da tsari bazaka taɓa tunanin manyan Dabbobi ne ke rayuwa a

Ciki ba.

Ta kowane ɓangare suna zaman lafiya da juna sai dai wani babban al’amari daya gifta tsakanin su na neman kawo masu ƙalubale babba wanda hakan ne ke assasa lamarin, sai dai kuma alƙawarin dake tsakanin su na neman dakatar da komai dake shirin faruwa.

 

Asalin labarin……..

Garin kathub babban ƙauye ne wanda usulin larabawa matafiya da dabbobin su suke zaune a cikinsa, cikin daji ne sosai hakan yasa rayuwarsu su kaɗai suke yinta babu me zuwa inda suke sai masu fita karatu duk Wanda ya taso in bai son fita karatu anan zai rayuwarsa har aure. Suna noma amma basa siyar wa babu abinda basa nomawa tunda ga kan kayan marmari har zuwa hatsi komai suna dashi na more rayuwa ɓangaren cima, abubuwan zamani basu damu dasu ba domin kuwa ko ƴaƴan su suka fita karatu anan suke dawowa domin amfanar da sauran yan uwansu ilmin su, da haka ne har da yawansu suka zama wasu a cikin ƙauyen suka buɗe makarantu da asibiti da masallaci basa zuwa ko ina, babu irin karatun da basu dashi domin kuwa zakayi mamaki idan kaje ƙauyen . Sun samu cigaba sosai inda har suka fi wasu state din kasashen dake makwabta ka dasu.

Akwai yan ƙasar Egypt sune suka haɗu dana Saudi Arabia suna ta tafiya har suka yada zango a ƙurmin dajin da su kansu basu san wace ƙasa bace domin ko turawa masu zuwa yawon buɗe ido basa shiga wannan daji .

Rayuwa suke tamkar yan uwan juna sun haɗe sun zama tsintsiya ma ɗaurinki daya, kansu haɗe yake haka ma kan yaransu haɗe yake babu banbanci, kwatsam wata rana aka yo masu turen sojoji suka buɗe masu wuta ta ko ina ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba sai dai abin yazo masu da sauƙi kasancewar sun ma garin kafi sosai ta yadda babu me iya shiga ciki sai ɗan garin. Ganin da gaske ba kyale su za’a yi ba yasa yah Kathub haɗa zama da manyan garin. Kathub ya kasance shi yafi kowa shekaru a cikin manyan garin kuma yafi kowa manyan yaya shiyasa suke girmama shi da maganar sa shine shugaba a wannan ƙauye mafarin da suka saka ma garin *KATHUB* . Bayan kowa ya hallara ne ya fara masu bayanin abinda ke shirin faruwa dasu duk da sun sani, mafita suka fara nema ma kansu sai dai sun fara tunanin tunda aka san dasu a wajen baza’a barsu su zauna lafiya ba dan haka suka yanke shawarar ƙara ma garin kafi sosai ta yadda har su gama shirin su na tashi baza a cin masu ba . Haka Kuwa akayi nan da nan aka sanar da kowa suka fara shiri tafiya manyan gari kuma suka cigaba da sa kafi gaba daya kewayen garin.

Watan su ďaya suka kammala duk wani shiri nasu suka fara shirin tafiya, can cikin dajin suka kara nutsawa mai makon su fito, sunyi shiri sosai na shiga babban dajin dan haka komai nasu na tare dasu saboda ba ƙaramin hatsari dajin keda shi ba, akwai manyan namun daji bila adadin da aljannu shiyasa shirin su ya kasance na musamman. Sunyi tafiya ta kwana biyu kafin suka fara hango wasu manyan tsaunika guda biyu masu girman gaske, tunda suka fara kusanto wannan tsaunika suka fuskanci tashin hankali na gaba domin kuwa wasu manya manyan halittun dabbobi ne suke tunkaro su gadan gadan

Gaba ɗaya sun kasa cigaba da tunkarar wajen sun tsaya kawai suna jiran ikon Allah……

 

Toh meke faruwa ne haka nace meke faruwa?

Nace kin taɓa jin irin wannan salon kuwa?

Meke shirin faruwa tsakanin waɗannan Manyan Dabbobi da kuma waɗannan mutane ?.

Shin wai wane ma irin mutane ne ma haka?

Waɗanne kalar Manyan Dabbobi ke rayuwa kusa da mutane?.

A wace duniya ce wannan abu ke faruwa?.

Shin wane alƙawari ne tsakanin su

?.

Chakwakiyar dake ciki hasashe ko dogon tunani bazai taɓa hango wa ba har sai an karanta.

Kudai ku biyo alƙalamina don jin labarin da yadda zai kasance .

 

 

 

Banyi alkawarin posting kullum ba saboda Ina zuwa makaranta.

 

A’ISHATULHUMAIRA

Close Menu