Ad Code

Littafin Balaguro A Isra'ila Da Falasɗinu

Balaguro A Isra’ila Da Falasɗinu

 

 

 

 

 

 

Littafi: Ilmi Mabuɗin Tafiya: Balaguro a Isra’ila da Falasɗinu

Marubuci: Ibrahim Sheme

Kamfani: Informart, Kaduna

Shekara: 2005

Shafuka: 112

 

Jiya a Facebook na ga shugabar ƙungiyar mu ta marubuta, Alƙalam, Hajiya Halima K Mashi , ta saka hoton bangon wani littafi da na rubuta mai suna ‘Ilmi Mabuɗin Tafiya: Balaguro A Isra’ila Da Falasɗinu’.

 

Wannan littafi an buga shi da Hausa a cikin 2005, to amma sai da aka fara wallafa shi da Turanci, mako-mako, a cikin jaridar New Nigerian Weekly a farkon shekara ta 1999.

 

Ya na ɗauke da labarin ziyarar da na kai ƙasar Isra’ila da yankunan Falasɗinawa waɗanda Yahudawa su ka danne da nufin ƙwace su baki ɗaya. Na kai ziyarar ne a cikin Disamba 1998 tare da wasu editocin jaridun Nijeriya guda shida da wani jami’in Ofishin Jakadancin Isra’ila a Legas (mu biyu ne Musulmi).

Mahaifina ne Hausa Novel Complete

A balaguron, mun je wuraren tarihi waɗanda ban taɓa tunanin ƙafa ta za ta iya takawa ba, mun ga abubuwan mamaki, kuma mun tattauna da manyan jami’an gwamnati na ɓangarorin Isra’ila da Falasɗinu, da ‘yan kasuwa, ‘yan jarida, sojoji, ɗalibai, malaman addini, malaman jami’a, ‘yan siyasa, masu harkar nishaɗantarwa, da sauran su.

 

Wuraren da mu ka je sun haɗa da Masallacin Al-Aƙsa (wanda shi ne wuri na uku mafi tsarki a Musulunci); da ɗakin da aka haifi Annabi Isa (a.s.) da inda ya fara wa’azi da kotun da aka yi masa shari’a da inda Kiristoci ke cewa an gicciye shi (Calvary Hill / Golgotha) da kogon da su ka yi amanna da cewa ya tashi daga matacce (Stone of Anointment); da tsibirin Masada, da tekun Dead Sea, da Jami’ar Hebrew, da gidajen jama’a a ƙauyuka, da birane irin su Ƙudus (Jerusalem), Tel Aviv, Haifa, Nazareth, Canaan, Tiberias, Tabgha, da Capharnaum; da Ma’aikatar Tsaro, ma’aikatun gwamnati, Kotun Ƙoli, Tsaunin Hertz (inda aka yi maƙabartar manyan Yahudawa), da gidan tarihin kisan kiyashi na Holocaust (wato Yad Vashem), da wuri mafi tsarki a addinin Yahudawa (wato Wailing Wall), da hedikwatar addinin Baha’iyanci ta duniya, da babbar majalisar ƙasa, wato Knesset, da tsaunukan Golan Heights, da Ofishin Jakadancin Nijeriya, da dai sauran su. Mun je ofishin tsohon Firayim Minista Shimon Perez, mun gana da shi. Shi ma mugun nan, Firayim Minista Benjamin Netanyahu (wanda a yanzu ma shi ke riƙe da muƙamin), mun je ofishin sa domin mu gaisa da shi, to amma sai ya sulale ta wata ƙofa ya bar mu ya tafi Majalisar Dattawa inda ake turka-turkar tsige shi saboda wata kwaɓa da ya tafka. Can mu ka je mu ka same shi, mu ka sha kallo.

 

Wannan littafi, mai shafi 112, ya ƙunshi bayani kan asalin rikicin Falasɗinawa da Yahudawa wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, da al’amurra masu tarin yawa. A yau da azzaluman Isra’ila a ƙarƙashin Netanyahu su ke aiwatar da kisan kiyashi kan Falasɗinawa da ragargaza Birnin Gaza da wasu sassa na Falasɗinu da Lebanon, a kullum ina tuno da waɗannan wurare da na ziyarta, ina ganin su a rai na kamar jiya na je cikin su, da abubuwan da na ji daga bakin jama’ar ɓangarorin biyu.

 

Littafin ya shiga kasuwa a lokacin da ya fito shekaru 18 da su ka shuɗe (bayan an buga shi wata-wata a cikin mujallar Fim).

 

Idan mutum na buƙata, zai iya samun shi a waɗannan kantina:

1. Arewa House Bookshop a Kaduna

2. Chapter One Bookshop da ke Gwammaja, Kano

3. Booksellers da ke Garki, Abuja

 

Wanda ya ci sa’a kuma, zan ba shi kwafe kyauta!

Close Menu