Ad Code

Jahilci Ko Al'ada Hausa Novel Complete

Jahilci Ko Al’ada Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

‘𝗗𝗔𝗡’𝗗𝗔𝗡𝗢 𝗗𝗔𝗚𝗔 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡

𝗡𝗔

𝗛𝗔𝗥𝗜𝗥𝗔 𝗦𝗔𝗟𝗜𝗛𝗨 𝗜𝗦𝗔𝗛

̶U̶W̶A̶R ̶B̶A̶T̶O̶O̶R̶L

 

𝗠𝗔𝗥𝗨𝗕𝗨𝗖𝗜𝗬𝗔𝗥

 

MAFARKI NAH

&

◦’YAR SARKI CEE

 

𝗛𝗔𝗣𝗣𝗬 𝗠𝗔𝗨𝗟𝗨𝗗𝗨𝗡 𝗡𝗔𝗕𝗘𝗘𝗬 𝗦𝗔𝗟𝗟𝗔𝗟𝗟𝗔𝗛𝗨 𝗔𝗟𝗔𝗜𝗛𝗜 𝗪𝗔 𝗦𝗔𝗟𝗟𝗔𝗠 𝗧𝗢 𝗔𝗟𝗟 𝗠𝗨𝗦𝗟𝗜𝗠 𝗨𝗠𝗠𝗔𝗛

𝙰𝙻𝙻𝙰𝙷𝚄𝙼𝙼𝙰𝙷 𝚂𝙰𝙻𝙻𝙸 𝚆𝙰 𝚂𝙰𝙻𝙻𝙸𝙼 𝙰𝙻𝙰 𝚂𝙰𝚈𝚈𝙸𝙳𝙸𝙽𝙰 𝚁𝙰𝚂𝚄𝙻𝚄𝙻𝙻𝙰𝙷𝙸 𝚆𝙰 𝙰𝙻𝙰 𝙰𝙻𝙸𝙷𝙸 𝚆𝙰 𝚂𝙰𝙻𝙻𝙰𝙼

 

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله 𝚂𝙰𝚆

 

𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠

 

 

Baabaa tace “Indo wai har halin naki ya balaga ya kai haka? Indo rashin storon Allahn ma ya girmama ya wuce misali? Ina magana kina zaune wato ta mutu? Kai subhanallahi tirr da wannan tambaɗewan rayuwa wai AL’ADA, Indo Sallahn ki ma ba karɓuwa zai yi ba dan alhaqin baiwar Allah dake kanki, ni Meramu wannan JAHILCI KO AL’ADAH za’a qira sa? Mutum na da iliminsa dai-dai gwargwado amma sai ya cika carbin burbushin tunaninsa tsaɓ da JAHILCI, to Allah ya kyauta miki” Baabaa Mero na gama magana ta fice rai a ɓace.

Sanadin Mijina Hausa Novel Complete

“Magaji ɗauka mun yarinyar nan mu tafi gida na” cewar Baabaa Mero.

Magaji miqewa yayi ya ɗauke ta a kafaɗa suka fice tare da Baffai sai gidan Baabaa Mero.

 

Suna shiga gidan tasa Magaji ya ajeta akan tabarman da dama take zaune a kai kamun Baffai yazo qiranta, mafifici ta shiga ɗaki ta dauko Baffai ya karɓa yana fifita Innai Magaji kuwa kanta na cinyansa.

Baabaa tagumi kawai ta zuba tana ganin ikon Allah dan duk iya sanin ta ko wani irin maciji ne ya ciji mutum muddin ta basa wannan magani ta manna masa gadalin shikkenan sai ya amar da dafin, dan a wajan mijinta ta gaji duka magungunan.

Miqewa baabaa tayi ta shiga ɗaki can ta fito da wani qullin magani da qwai da kofi, tana zama ta fasa qwan sannan ta sanya maganin ta kaɗa, Magaji ta miqawa ya karɓa ya buɗe bakin Innai yana sa mata, sai ta kuma buɗe ido tana haɗiya kaɗan-kaɗan, yana gama bata ta wara ido tana ya tsine fiska sai lokacin ta fara jin tashin zuciya, in tayi kaman zata rufe ido sai taji amai na taso mata tana buɗe ido ya kwanta.

Baabaa tace “kai Magaji yanzukam ɗago ta kar ta ɓata maka jiki” sai ya ɗago kanta ya zaunar da ita amma yana riqe da ita.

Sai lokacin Baffai ya tuna da maganan tofi, nan take ya ɗau kofi da ruwa ya fara addu’a yana tofawa sannan ya sa mata a bakin ta sha, tana gama sha ko kofin bai gama barin bakinta ba sai amai, sosai take amai kaman zata harar da kayan cikin ta, ganin haka sai duk suka yi hamdala suna aikin jera mata sannu.

Sosai tayi amai ta galabaita, tayi luuuu zata faɗi Magaji yayi saurin taro ta, nan baabaa ta miqe ta ɗauko roba da ruwa sannan ta sanya Magaji ya gogewa Innai jikinta ta kawo wani riga tace ya saka mata.

kallon Baabaa yayi jin abinda tace na ya sawa Innai riga, duk da dai qanwar sa ce kuma yarinya ce tunda shekarunta sha-huɗu 14 kuma ba komai qirjinta amma baya jin zai iya sa mata rigan dan gudun mastala shi shaiɗan ba’a iya masa.

Ganin ya tsaya da riga a hannu sai ta harare sa ta karɓa zata sa mata shi kuma Magaji kau da idonsa yayi sai da ta gama saka mata ya juyo, Baabaa ta sanya shi ɗaukan Innai ya kaita ɗaki.

Ya ɗauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar da ita akan gadon ta ya juyo ya fito.

Duk suna zaune zugum-zugum kowa yayi shiru ko wannensu da abinda yake tunawa a ransa yayinda shi kuma Magaji tunani yake wannan yarinya ko kaɗan bata da nauyi kullum ka ɗaga ta kaman ka ɗaga stinke.

Baabaa Mero tace “mai sunan Malam kana ji na? Baffai ɗaga kai yayi alaman yana sauraranra, sai ta numfasa tace “mai sunan Malam abun ya isa haka yau shekara ɗai-ɗai shekaru sha-huɗu kenan da haihuwan takwara sannan tun randa aka haifeta har yau ba abinda ya sanja na daga AL’ADAN da uwarta ta ɗaura wa kanta, abun ya isheni yau an qureni na tabbata nan gaba ko ba rai aka kawo takwara indo ba zata kalli gawanta ba balle batun ta mata addu’a ko ta wanke ta dan haka zan ɗau mummunan mataki a kanku duka abun ya ishe ni, ku tashi ku bani waje” ta faɗa tana kallon Baffai da Magaji.

Magaji kallon baabaa yayi yace “baabaa kiyi haquri amma ni na tabbata Inna na son Innai irin matsanancin soyayyan nan ma, dan Allah kuyi haquri ku mata uzuri” harara baabaa Mero ta aika masa da shi tace “kai dan ubanka tunda ba kai ake azabtarwa ba dole kace haka, bayan AL’ADA ta kunyan ɗan fari kasan akwai AL’ADAH ta SHA’DI kamun aure ko? To tunda kace haka ka tabbatar sai an maka za’a baka matan aure jarababben mara tausayi har za kayi magana ni da nasan ba dan an daina sha’di ba sai dai ka mutu ba aure, to ciwon da ake ji a shaɗi na ɗan awanni ko mintuna ka isa ka haɗa shi da irin ciwon da ake ji na rashin kulawa daga mahaifiya? Anbar duk waɗan nan AL’ADUN saboda zamani yayi kowa ya fahimci yawancin AL’ADU ba komai bane face JAHILCI da kuma ɗaukan alhaqin bayin Allah a banza da wofi abu ba ayan Qur’ani ba bare Hadisi kuma dai ba Mustahabbi ba ko Sunna balle a qira sa Farilla kaman yacce mutane ke jahiltan kan su suka aza a gaban goshi, ciwon da takwara ke ji ba ko wanne mai laga-lagan zuciya bane zai iya ɗauka ka godewa Allah uwarka Habiba ba ruwanta da wannan JAHILALLEN AL’ADA dan da kai ne na tabbata sai ka shiga duniya dan jaraba”.

Baffai kansa a qasa ya kasa cewa komai shi kaɗai yasan ne yake kissinawa a ransa.

Baabaa masifa take kaman zata ari baki barin dai in ta tuno rashin kunyan da Inna ta mata, cewa su Baffai tayi su tafi dare nayi tunda qarfe ɗaya na dare har ya gota, ficewa suka yi suka tafi gida, Magaji yawa Baffai sai da safe ya wuce ɗakin sa.

Baffai yana shiga ɗakin ya samu Inna a kwance da alama tayi bacci ma, qaramin tsaki yaja ya shumfiɗa sallaya ya kwanta a nan qasa..

 

⭐⭐⭐

Jay taɓe baki yayi yace “kaman dai a Jss 1 take ne ko SS 1 tsakanin biyun dai”

 

“Ai kuwa in SS 1 take to a ajina take dan yanzu presently ni ne form-mastern su, amma me sunan ta?

 

Hararansa Jay yayi yace “za kace baka san sunan Hajja Afrah take da shi ba ko kuwa sunan Daddy ne baka sani ba?

 

Farooq na dariya yace “sorry freind na tuna FATIMA NURA right? Amma ba mai sunan sai dai wata me suna FATIMA NURA MUHAMMAD”.

 

“ɗan renin hankali ita ce to tunda baka san tana aiki da sunan Alhaji ba”.

 

“Ai kuwa sai yanzu ma ta faɗo mun kasan ba cika kallon students nake ba yanzu ɗalibai renine da su in ka sake kaɗan su renaka wasu suce suna sonka wasu kuma su maka sharri a wajan qawayensu akan kace kana sonsu alhali ba haka bane”

 

Murmushi Jay yayi yace “kai dai faɗa gaskiya kasan dai na sani wannan AL’ADA ce ta malamai soyayya da ɗaliban su to kai faɗamun akwai wacce ta maka a students naka?

 

Farooq hararan Jay yayi yace “taɓɓ JAHILCI KO AL’ADAH? Kana Malami kayi soyayya da ɗalibar ka ba dai AL’ADA ba sai dai ko JAHILCI dan reni ne zalla gwanda ma in ɗalibai suka gama ka bi yarinya har gida in ta maka, though akwai wacce suke zama da ita Afrah a class ina tunanin qawarta ce yarinyar nistuwan ta da hazaqanta na burge ni amma ba ina nufin wani abu ba dan duk ajin qwailaye ne irin nata ma yayi muni don ko Afrah ta fita cika ido”

 

Dariya Jay ya saka har da kama ciki yace “kaji ɗan iskan malami ba, wai qwailaye wato ido kake sawa ɗaliban ka?

 

Hararansa Farooq yayi yace “in nasa musu ido in kalli me? Ko ita ma wannan yaarinyar ba wai sonta nake ba dan karkaji nayi magananta”.

 

“To in ba sonta kake ba me kake? Kaga in ta maka kawai faɗamun muje har gidan su in yaso sai ka rene ta kar ka damu da rashin girman ta, kawai ta girma a hannunka in kana zuba mata takin asali (sperm) tun yaushe zata girma kaman kazar gona”.

 

“Kai dai ɗan iska ne Jay Allah kawo maka sauqi dan fa baka ga yarinyar ba ta haɗu kam amma ba komai a wajan ni kuma tsakani da Allah yacce na balaga na balagen nan ai duk wacce na samu kasan ba aikin wasa zan mata ba balle akai ga maganan reno, sai dai ko in kai zaka iya haqura kayi renon tunda ɗaliba ta ce sai ka fara kamun qafa”

 

Jay ya buɗe baki zai yi magana sai qiran da ya shigo wayansa ya kaste sa, ganin mai qiransa DMD sai ya ɗauka ya kara a kunne yana cewa “hello dude an tashi baccin ne?

 

Guntun tsaki DMD yaja yana driving, a taqaice yace “kana can har yanzu?

 

“Eh inanan amma bana gidan Hajja naje wajan freind”.

 

Da yake DMD yasan wanda Jay ke qira freind sai ya kaste qiran ba tare da yace komai ba ya ci-gaba da driving da gudu, ba jimawa suka isa.

Gidan ba za’a ce masa babba har can ba amma duba da ba’a cikin gari yake ba to zai iya amsa sunan babba kuma stararre wanda a kaf anguwan babu irin sa.

Bai ko shiga gidan ba ya tsaya a bakin gate ya juyo ya kallesu yace “ku sauqa ku shiga kuma kar naji kar na gani fatan kuna ji na?

 

Duk amsa masa suka yi sannan suka sauqa, sanda yaga shigansu kamun nan yaja motan sa yayi gaba.

Layin Jay ya qira ya masa kwatancen inda suke, yana shiga makarantar ya tarar da su suna jiransa, dan sanin halin DMD basu bari ya iso ya qirasu ba suka fito jiransa.

 

DMD kallon Farooq yayi yace “yanzu kai a nan kake rayuwa? Service ɗin nan dole ne?

 

“DMD ba zaka gane bane”

 

Taɓe baki yayi ya shige cikin ɗakin ya ɗauro alwala ya dawo palourn ya same su suna hira sai ya shumfiɗa darduma ya ta da sallah.

Yana idarwa ya kallesu kaman wanda aka sa dole ko aka shaqe yace “kunyi sallan ne ko kun tsaya hiran mata?

 

Jay hararansa yayi cikin wasa yace “ba zancen mata ba cin mata muke ɗan renin hankali mutum sai kace mata-maza nikam anya dude lafiyan ka? Anyama kana jin feelings?

 

Ko kallo Jay bai ishe sa ba balle ya tanka ya juya yaci gaba da qirga countern sa.

 

Farooq dariya yayi har da kama ciki yace “kai fa Jay shahararren ɗan iska ne baka da magana sai na mata ai kam matarka ta shige su, yanzu angaya maka su mata-mazan basa jin feelings ne? Suma feelings gare su mai qarfi ma dan kaji kuma DMD irin su da kake ga suke shirun nan kaman abun bai damesu ba to sune oganni in suka kama mace sai sun sumar irinka kuma kuna good 5mints kun gama”

 

Wani kallon banza kallon bakasan me kake faɗa ba Jay yayi wa Farooq yace “amma tabbas in nace baka ci tuwo akaina ba to nayi qarya dan tsaban renin hankali ka dubeni jibgege da ni kana qiran 5mints ai wallahi yanda nake ji na ɗin nan in mace ta shiga hannuna sai an ɗinka ta kai dai kawai ayi shiru, ɗazu Afrah ke ban labarin wata qawarta Inaga ma ita kake nufi Afrah yarinyar nan dan staɓar tana ji ta fara girma har da cemun wai na auri qawarta tana da hankali amma kuma na kawo kunne ta faɗamun wata magana, duk ɗauka na wata serious magana ne ashe yarinyar nan cewa za tayi qawar tata bata da ko nono, to sai ka tuno mun da Afrah nima kaman DMD nake da ra’ayi sai qosashshiyar mace kuma nunanniya wacce tasan ta amsa suna budurwa”

 

“Hhhhh! Jay Allah kawo maka sauqi ” faɗin Farooq yana miqewa.

 

DMD kallon Jay yayi ya aika masa da harara dan maganganun nasu sosai ya cika sa fam da haushi amma rashin son hayaniya yasa baiyi magana”.

Close Menu