Ad Code

Hauwau Kulu Yar Cikin Badala Hausa Novel

Hauwau Kulu Yar Cikin Badala Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*YAR CIKIN BADALA*

 

~(HAUWA-KULU)~

 

 

(PAID BOOK)

 

 

*SUMAYYAH ABDULKADIR*

07030137870

(whtsp only)*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

(1) SHIMFIDAR LABARIN

 

 

 

 

*NIGERIAN BAR ASSOCIATION CONFERENCE HALL*

 

Wani irin cika dakin taron yayi, da manya da kananan lauyoyi wasu tareda iyalansu, a gefe kuma wakilan kungiyoyi ne masu zaman kan su (NGOs).

 

Duk da cewa dakin taron bai cika girma ba, amma ya hadiye mutane da yawa da suka halarta. Wasu da yawa ba don taya ta murnar mukamin da aka bata yau suka zo ba, sun zo ne musamman don ganinta ido da ido (to quench their curiosity), da son tabbatar da jita-jitar da suke ji akan cikar lafiyarta, a matsayin ta na celebrity din Najeriya ga masu nakasa, wadda sunanta ya watsu, a kafafen yada labarai.

 

 

Wasu kuwa don farin jininta ne kawai suke son ganinta sabida yadda sunanta ya fantsama a duniya akan kare hakkin nakasassu a arewa.

Tuzuru Hausa Novel Wattpad

Kungiyoyin kare hakkin masu bukata ta musamman, su suka hada mata wannan taron na Gani da ido (meet and greet), domin taya ta murnar karbar shugabancin kungiyar gamayyar lauyoyin kasa da aka fi sani da suna *”Nigerian Bar Association”.*

 

Wadannan kungiyoyin sun tsaya mata ne a dalilin tsayuwar ta tsayin daka wajen kare hakkin nakasassun arewa, da tsayawa cigabansu da ilmin ‘ya’yansu, karkashin hadin guiwarta da *Sustainable Development Goals* da kuma aikin da ta zaba na zama lauyar marasa ‘yanci.

 

Bayan kasancewarta ‘ *SDG ADVOCATE* ‘ har ila yau, lauya ce ita mai zaman kanta, wadda aikinta yafi karkata ga tsayawa *less-privileged* da wadanda basu da halin daukar lauya ko akaci zarafinsu adalilin nakasa ko aka take hakkinsu na ‘yan kasa, itace kan gaba wajen kare hakkin nakasassu a duk fadin arewa.

 

Lokacin data durkako dakin taron, wato (ta doso) cikin shiga ta kamala da kwarjini, hannunta yana makale cikin nasa, suna taku a hankali zuwa inda aka tanadar musu don tsayuwa tare. Sai aka mike don nuna girmamawa a gareta, da yawa yau da suka samu ganinta a zahiri sun ce a zukatansu “hakika *HAUWA* ganin ki ya fi jin ki!”

 

Duk da cewa wannan karon ma da bakin gilashin nata a idanunta. Hakan bai boye zahirin cikar zatinta da cikar kamalarta da iya adonta ba.

 

Bayan an zauna an nutsu, ta karbi lasifika ta fara da rero godiya ga duk mahalarta taron, da sauran zaqaquran lauyoyi ‘yan uwanta, da kungiyoyin da suka hada mata wannan muhimmin taron gani da ido da gaisawa, kungiyoyin ne masu tabbatar da cewa, mutane masu bukata ta musamman sun samu rabauta daga duk wani matsatsi na rayuwa karkashin tallafin *Sustainable Development Goals* da take yi wa aiki, ta sake godewa kungiyoyin nan da suka roki ta fito yau, duniya ta ganta, kasancewar muryarta kadai aka sani a kafafan sadarwa, sun roki ta baiwa al’umma labarin ta, maiyuwuwa ya zamo *inspiration* ga al’ummar da suka samu kansu cikin kwatankwacin irin *situation* dinta.

 

Kungiyoyin sun hada da kungiyar ‘ *AGILE* ‘, da kungiyar ‘ *Sightsavers* ‘, sannan kungiyar ‘ *Action Against Hunger’* da ‘ *PERL* ‘.

 

Ta kuma godewa manema labarai daga gidan rediyon *BBC* , karkashin jagorancin wakilin yada labarai na Kano, da gidan rediyon *VOA* karkashin jagorancin *HAMZA MUSTAPHA MAWONMASE*.

 

Sama da kowa, above all, and above all, tace tana godewa uban ya’yanta, wanda ta kira da suna “ *my PACE-SETTER….”.*

 

 

Zazzakar muryarta ta cigaba da karade dakin taron ta cikin bututun lasifika,wadda murya ce da dama take familiar ga kowa tun kafin zuwan ranar yau, a daidai sanda take cewa;

 

 

 

**TAKORI’S LOUNGE*

[19/10, 8:32 pm] +218 92-2035171: ~HAUWA-KULU~

 

(2) “Kamar yadda kowa ya sani sunana na yanka Hauwa-Kulu”. Hauwa shine sunan da aka yankamin rago dashi. Sau-tari idan na bushi iska musamman a lokutan nishadi na da son baiwa kaina farin ciki na kan bugi kirji in gayawa kaina da kaina, “babu wanda ya kaini samun yin kuruciya mai dadi!

Na kan yi tunanin ai nafi duk tsararrakina jin dadin dabdalar kuruciya, dalilina na fadar haka shine nayi kuruciyata ne a zamanin da hankulan kasarmu da jihohin arewa bakidaya suke a kwance, sannan kuma dukkan iyayena Uwa da Uba suke a raye tare, ina jingine jikin su musamman Innata, ina rabar ni’imar dake tattare da kulawar uwa da ta uba a tare, cikin rayuwar rufin asiri irin ta kowanne talakkan Bakano.

 

Nayi yarintata a sa’ilin da muke cikin shekarar nan mai tarin abubuwan bada labari a kasarmu ta Najeriya, zamanin da sojoji suka kwace mulki daga hannun sibiliyan koko in ce musu (farar hula) cikin shekarun (late 80s), wanda lokacin da wayona mulkin Najeriya ya koma hannun mulkin soja, bayan mulkin (Alhaji Shehu Shagari).

 

Hauwa ta cigaba da cewa “a lokacin ana gudanar da wata irin rayuwa ne mai matukar sauki da hadin kai a tsakanin alummar jihar Kano, har ma da daukacin kasar Najeriya gabadaya irin wanda yayi karanci ko kuma ace babu shi sam! A halin da muke ciki a yanzu.

 

Ni Hauwa-Kulu nayi ‘yammatancina a zamanin mulkin Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

 

A wancan lokacin da muke zance, kwanciyar hankali shine babban arzikin da al’umma suka mallaka, suka Kuma wadatu da shi ba tarin dukiya ta yaki-halak yaki-haram ba.

 

Koko ince a lokacin Ubangiji yayi mana ludufin arzikin kwanciyar hankali da wadatar zuciya sama dana komai, wanda yafi tarin dukiyar yanzu alfanu ga dan adam alhalin babu kwanciyar hankali, godiyar Ubangiji ya wadaci zukatan al’ummar BADALAR Kano da kewayenta, saboda kowanne talakkan birni a zamanin, in kayi duba na tsanaki zaka ga cewa ya iyawa talaucin sa, dai-dai gwargwado kuma daidai misali jama’a basa cikin halin wahala da kaka-ni-kayi; tunda kowa yafi karfin hatsi, wato duk tsananin talauci ba zai sa a kwana da yunwa ba, saboda ba’a damu da cewa lallai sai an ci mai dadi ba, ko sai an sha koko da sukari, ko sai an ci abinci mai maiko da nama, gidan talakka da gidan mai kudi kusan duk irin rayuwa daya ake yi babu banbanci, abinci iri daya ake ci, babu yi wa juna rowa, haka suttura kusan iri daya ake daurawa tsakanin matayen cikin badala duka, daga na masu kudi har na talakkawa.

 

Sanin kowa ne a lokacin babu ta’addancin ‘yan kasa da zaluncin shuwagabanni sosai, shiyasa ake cikin kwanciyar hankali da koshin ciki, wato babu masifar talauci da yunwar da har zata tunzura matasa sana’ar nan ta satar mutane da yin garkuwa dasu, sannan babu hadama da gasar rayuwa tsakanin mazauna badalolin Kano, kamar gasar motocin hawa, dana dogayen gine-gine, ko gasar sanya suttura mai tsada a tsakanin matan badala. Wannan a takaice shine misalin irin zamanin da ni Hauwa na taso a cikin sa, wato zamanin da duniya take a kwance lumui.

 

Babban kwanciyar hankalin da ake ciki a lokacin shine; al’ummar 70s da 80s basa cin bashin bankuna don su rayu, irin yadda ake ci a zamanin yanzu kamar yadda ake cin dussa, wai don biyan bukatun yau da kullum wadanda ba masu karewa bane. Ga daukar zunubin kudin ruwa.

Shiyasa zaka ga duk tsananin talauci a lokacin iyayenmu basa cikin fargaba da zullumi, irin wanda tunanin bashi ke haddasawa magidantan yanzu, mai haifar da cututtukan kwakwalwa irin na zamanin yanzu da yake yiwa magidanta illa.

 

Hakan ya faru ne sakamakon cewa kowa yana da abin yi daga (sana’ar data karbe shi), ta kuma ishe shi rufawa kansa asiri, da biyan bukatun sa na yau da kullum batare da ya ci bashi ba. Kuma ba tareda yayi rayuwar dage ba.

 

Kusan kowanne mutum a cikin Badalar birnin Kano da kewaye (kauyuka da kananan hukumomi) yana rayuwa ne daidai shi kuma cikin farin ciki, yalwa da wadatar zucci, domin kullum cikin sa a koshe yake da *Gurasa* , Tuwo, Dumame, Kunu, da Koko da Kosai (manyan abincin *Kanawa* ).

 

A takaice, ko da a ce kai ne beran masallaci sabida talauci a zamanin can da nake yarintata a gaban Innata da Babana, zuwa balaga ta (yammatancina) nayi rantsuwa bazaka rasa abincin da zaka ci sau uku a rana ba”.

 

A kullum ranar Allah tunanin Babana wanda anan unguwarmu ake kira “Baban Hauwa”, dama na kowanne magidanci kamarsa na jama’ar dake zaune cikin kwaryar gidajen ‘Badala’ da ‘ganuwoyin’ garin Kano, shine; na yadda gobe idan garin Allah ya waye, karfe nawa zai yi sammako ya fita kasuwa ko wajen sanaar sa??

 

Ba kuma don komai ba sai don samowa cikin sa dana iyalin sa abincin da zasu ci a yinin ranar.

 

Kowa ya san a lokacin fiye da rabin Kanawa yan kasuwar saye da sayarwa ne. Wannan ne yasa ba’a kwana ana jin yunwa, sannan za’a wuni a koshe. Kuma ba’a tara komai a banki ba, sannan hakan baisa sai an ci bashin kowa ba. Duk da hakan kuma ana zaune lafiya cikin farin ciki. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ake yi a gidanmu.

 

 

 

Na fara da baku labarina ni *~HAUWA_KULU~* tun daga tushe, ta hanyar dora shi akan katangar zamantakewar gidajenmu na Kanawa, wadanda aka fi sani da ‘yan kwaryar BADALA, yanayin rayuwar iyayenmu na cikin Badala wata irin rayuwa ce irin mai ban ban sha’awa ga wanda ba Bakano ba.

 

Rayuwa ce wadda bako *zai tafi gaba ya bada labari* tunda an ce wai Allah daya gari ban-ban.

****

Close Menu