Ad Code

Ameer and Adam Hausa Novel Complete

Ameer and Adam Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

*AMEERA & ADAM*

 

_*( By S-REZA

 

*First class writers asoo…*

 

*(Writer of Uwata ce sila. Meera & Nusee* )

 

_Sadaukarwa ga marubuciyar arziƙi. Yau na cika alƙawarin da na ɗauka. Wannan page ɗin naki ne ke ɗaya (Kahdija Candy)_

 

 

*Bismillahi Rahamanin Rahim!*

 

*PAGE 1️⃣*

 

Ƙarar homm É—in mutar da ta Æ™ara ji a karo na babu adadi ne ya sa ta bar naiman abun da da take yi ta nufo hanyar waje har ta na haÉ—awa da sassarfa. Zaune ta same shi a cikin motar ya na kallon hanyar fitowa da ga cikin gidan ya cika ya yi fam kamar zai fashe. Fuskarsa ta Æ™ara kalla a karo na biyu taga yanda ya haÉ—a rai kaman haÉ—uwar gaggarumin hadari a cikin watan ogosta. Da sauri ta buÉ—e Æ™ofar mai zaman banza ta shiga tana cigaba da satar kallonsa. “I’m sorry honey wayata na ke ta naima tun É—azu bansan inda na jefata ba ne shi yasa na daÉ—e. Ameera ta faÉ—a ta na gyara zamanta a cikin motar. Ko kallonta bai yi ba yaja mota mai gadi ya buÉ—e musu get suka É—auki hanya. Har suka iso babban asbintin babu wanda ya Æ™ara magana acikinsu. Kallonta ya yi a karon farko tun bayan shigarta cikin motar ya ce “Shiga ki fito ina jiranki idan kinje ki tsaya naiman wayarki karki fito da wuri.Ya faÉ—a ya na kawar da kansa daga gareta ganin ta kafeshi da banyan idanunta. Kallonsa ta yi ganin har yanzu fuskarsa a haÉ—e ta ke da ga É—an abun da ya faru. “Wai wannan haÉ—e fuskar na meye dan Allah? Na baka uzuri nafa, please dan Allah muje tare wallhi ni kunya zuwa ni É—aya nake yi please honey. Ta faÉ—a ta na kamo hannun angon nata cikin shagwaÉ“e murya. Kallonta ya yi ganin yanda ta Æ™ara haske ga y’ar rama da yagani a jikinta. Sosai ya ke lura da yanayinta kwana biyu ganin duk ta canja, hakan ne ya sa ya ce dole sai sunzo asibiti domin yanayin nata ya na bashi mamaki. Yana son matarsa sosai kaman yadda yasan itama tana sonsa, sai dai ya lura saboda zuwa asbintin nan da bata so ne yasa take son É“ata masa rai! Badan shine ya matsu da zuwa asbintin nan ba da ba zai shiga ciki ba. Kuma yasan tunda har ta fara haka tofa ko ya barta ita kaÉ—ai ba zuwa zatayi ba. “Fito muje” shine abun da ya ce ya na cire hannunta a jikinsa sannan ya fita itama ta fito suka jera izuwa cikin asbintin.

 

Kasancewar likitan abokinsane ya sa tun kafin su isa cikin asbintin ya kirasa ya na sanar da shi isowarsu. Koda suka isa gaban likitan bayan sun gaisa Adam ya fara masa maganar abun da ya kawo su. “Ta yi fari ga wani irin taurin kai da takeyi yanzu ga rama idan na tambayeta ta ce wai ita lafiya ta ke, abun da yafi bani mamaki ma shine yanzu abu kad’an za’a mata ta fara masifa, Æ™unci kamar ba itaba, to tun ba yau ba nake mata maganar muzu asibiti taÆ™i, sai yanzu na samu ta yarda, inaso a dubata idan ma ta kama gado za’a bamu to. Likitan yayi dariya ya na faÉ—in babu batun bada gado in sha Allah abun arziÆ™i ne. Koda likitan ya sa tayi fitsari domin ya gwada ko ciki ne gareta domin abun da ya fara zuwar masa kenan lokacin da ya haÉ—a ido da ita. Ita kuwa Ameera tashi ta yi ta nufi toilet É—in dake cikin ofecc É—in domin kuwo fitsarin. Gwajin farko ya nuna tana É—auki da ciki. Tsabar murna Adam bai san lokacin da ya rungume likintan ba. Ita kanta Ameera abun yazo mata a bazata domin bata taÉ“a kawo ciki gareta ba. Sosai farincikin ta ya fito fili ta na kallon Adam kamar wanda ya fita daga haiyacinsa tsabar farin ciki. Kamota yayi a gaban likitan ya fara surfa mata addu’a ya na shafa cikin kamar ya samu kan motarsa. Sosai yake cikin farin ciki kana ganinsa zaka gane hakan. RiÆ™o hannuta ya yi suka fito bayan likitan ya gama sanar dasu yanda zasu kula da cikin É—an wata guda, harda sanar da Adam cewa har yanzu cikin bai bar lokacin laulayi ba sai yayi haÆ™uri . Adam kuwa ji yake ba ma laulayi ba koma me ye zai jure a kan wannan cikin.

Hauwau Kulu Yar Cikin Badala Hausa Novel

A cikin motama dai da hannu É—aya yake tuÆ™i hannu É—aya kuma ya rike hannunta kamar wacce zata gudu. Saida suka tsaya suka sayi magani kafin suka wuce gida. Suna isa gida ya fito da sauri ya buÉ—e mata Æ™ofa ta fito ta na jinta kamar wata sarauniya, ga mukuma yanayin Æ™uncin da take yawan tsintar kanta a cikin kwana biyun nan. Haka ya rike hannunta suna tafiya a hankali har suka isa cikin Æ™aton falon nasu. Zaunar da ita ya yi a kan kujera sannan ya nufi kicin ya É—auko rowa mai sanyi ya buÉ—e ya kafa mata tana sha ya na kallon yanda ruwan ke shigewa ta maÆ™ogaronta, yana ji a ransa yanzu wannan ruwan zai dangana ga yaronsa dake wannan cikin, sosai murmushi ya samu mahalli a kan fuskarsa. Bayan ta gama sha ya zauna kusa da ita ya ce “Jikina yana faÉ—a mini ba lafiya kike ba ashe dai rabone mai girma a tere da ke. Dariya ta yi tana jin barci na son kamata. Wayarsa ya ciro ya fara kiran Æ™anwarsa kasancewar mahaifiyarsu ta rasu daga shi sai Æ™anwar tasa ka É—ai suka rage, mahaifinsu kuwa tun Æ™anwar tasa na Æ™arama ya rasu. Ta na É—agawa ya ce

 

“Kadija albishirin ki?

 

“Goro fari tas-tas” ta faÉ—a cike da zumud’in son jin mai yayan nata zai ce mata domin tasan da jin haka to abune mai daÉ—i. ”

 

Ameera na dau’ke da ciki har na wata guda.

 

Da Æ™karfi kadija ta kwaÉ—a wani uban ihu ta na cewa “Da gaske Yaya?

 

Bai ko bata amsa ba ya kashe wayar yana kallon Ameera da har barci ya fara tafiya da ita. Afili ya ce “A she ba a banza ba wannan saurin fushin naki da kikeyi na kwana biyu. Ganin haka yasa ya É—auketa gaba É—aya ya nufi kicin É—aki da ita ya kwantar da ita sannan ya fita yana mai ci gaba da kiran Æ´an uwa da abokan arziÆ™i.

 

Da misalin Æ™arfe biyar na yamma Amerra ta faraka, ko da ta farka sai ta farka da wani irin ciwon kai, ga kuma wani É“acin rai da mai barci ke tashi da shi musamman barcin yamma. Ta na fitowa falo ta ganshi sanye da kananan kaya na adides masu ruwa kore sosai kayan suka zauna a jikinsa, kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki, ga kuma falon wani Æ™amshine ke tashi shima dai a’lamar ya gyara ko ina. Ya na ganinta ya nufo gurin yana sakin murmushi haÉ—i da kiran sunanta. “Honey kin tashi? Muje ki yi wanka kafin a fara kiran salla saura kaÉ—an na gama abinci, ina fatan barccin ya isheki ko? Tun lokacin da ya fara magana take jin É“acinran da ta tashi dashi yana Æ™aruwa, haka kawai taji bata son yin mgn, sosai take daurewa karta ce komai domin tasan ba magana mai daÉ—i zatayi ba, hakan ya sa ta kasa cewa komai sai yatsine fuska da takeyi. Shi kuwa ganin haka yasa ya nufota yana dariya.

 

Bakinsa ya kai da niyar sakar mata kiss a kuncinta amma ta ja fuskarta ta na had’e fuskar harda tsartar da yawun bakita kamar wanda yayi mata kiss É—in. Da mamaki Adam yake kallonta ganin abun da ta yi. “Lafiya kuwa kike honey? Ya faÉ—a ya na kallonta domin yasan abun da tafi so kenan a duk lokacin da zai fita daga gida ko idan ya dawo Koda ya dawo da É“acin rai ne to ita zata masa, amma yanzu tun kafin yai mata tana kawar da kai. Bata ce komai ba ta nufi É—akin ta domin É—azu a É—akinsa ya kwantar da ita, tana shiga ta faÉ—a toilet ta yi buroshe sannan ta yi wanka tana jin har lokacin É“acin ran bai bar kantaba. Shikowa Adam uzuri ya yi mata ganin daga barci ta tashi gashi Kuma bata da lafiya. Sauri ya yi ya gama gyara komai kafin shima ya sake wanka sannan ya É—aura alaula ya fito sanye da jallabiya. ‘Dakinta ya nufa ganin bai ganta a Palo ba. Yana shiga ya ganta a kwance tana kallon sama ba barci take ba. Kallonta ya keyi yana jin tausayinta sosai ganin yanda ramarta ke sake fitowa fili.

 

“Honey kiyi alaula kiyi salla kafin na dawo na yi mana girki mai daÉ—i yau na hutar dake Kuma…Tun kafin ya Æ™arasa ta tsayar dashi domin ya kaita bango, shi bai san bata son yin magana bane. Cikin É—an É“acin rai ta ce “Dan Allah ya isa! ni nace maka yinwa nake ji ne? Fisabililahi kazo sai surutu kake mini wai kayi girki, to ni nasakaka, ko nace Adam kayi kirki ne, dan Allah kaje Kaci kayanka ni bama abinci zanci ba yau a Æ™oshe nake. Ta na gama faÉ—a ta bar masa É—akin ta fito Palo ta zauna tana jin wani haushi wanda bata san daga ina yake zuwa ba. Adam kuwa mutuwar tsaye ya yi ya saki baki da hanci yana kallonta har ta bar palon. Shi dai baiga abun da yayi ba, kuma Ameera da ko musu bata iya masa idan ya yi maga amma take masa irin wannan magana da ihu harda kiransa da Adam!. Shima fitowa yayi daga É—akin domin an fara kiran sallah. Kallonta yayi ganin yanda ta haÉ—e rai ka rantse wani abu a kai mata. Ita kuwa ta na ganinsa ta kawar da kai ta tashi domin barin gurin. Adam kuwa bai karaya ba ya ce “Sorry honey nasan duk barcin yamma ne, dama ana magar cewar babu kyau barcin yamma, yanzu dai ki daure kiyi alaula kiyi sallah kinji. Kallonsa tayi tana jin magana a bakinta amma ta daure har ya fita daga gidan.

 

Ba domin maganarsa ba itama ta nufi toilet ta É—aura alaula ta fara gabatar da sallar la’asar (Asar) kafin ta fara gabatar da magrib. Tana idarwa ta koma É—aki ta sake kwantawa domin wani sabon barcin take ji. Adam kuwa yana dawowa ya nufi kicin saida ya gama fitowa da komai kafin ya shiga

É—akinta domin kiranta suci abinci. Cikin mamaki yake kallonta ganin tayi shigar barci ta kwanta abunta harma barci ya fara mata nisa. Cikin kwantar da murya ya fara kiran sunanta haÉ—i da bubbuga mata gadon duk dan karya É“ata mata rai. “Honey honey honey hone…”Inna’ilai wa inna’ilaihi raju’un! Wannan wani irin masifane, yanzu dan Allah barcin ma bazaka barni nayi ba fisabililahi, wannan wani irin shiga haƙƙin mutum ne, ko ka manta zunubin da mutum yake samu idan ya tashi wani yana barcci ne, ni nace maka yau bazanci abinci ba, ko ana dole ne cin abincin. Cikin sanyi murya ya ce “Haba honey ya za’ayi ki kwanta bakici abinci ba Kuma gashi ba kya da lafiya, ai ko kaÉ—an kici sai kisha magani ko?

“To wallhi bazanci ba idan kuma dolene sai naga wanda zai sakani na ci, na ce maka na Æ™oshi-naÆ™oshi ko dolene. Ta Æ™arasa tana fashewa da kukan takaici Kai ka rantse da Allah dukanta a kayi. Sosai take jin barcin kuma harga Allah bata jin yunwa hasalima bata son ganin kowa a kusa da ita, yanzu haka ji take kamar dukanta ya keyi. Shi kuwa Adam gurin yin gwaninta zai rarrasheta harda kamota zai kwantar da ita a jikinsa amma ta wani Æ™wace jikinta ta miÆ™e tsaye ta Æ™ara fashewa da wani sabon kukan ta na kiran sunan Umma tana ihu! “Wai ni dolene sai mutum yaci abincin ne? na ce maka na Æ™oshi-naÆ™oshi Kuma barci nake ji dan Allah ka rabu dani waiyoo Umma! Ta na faÉ—a ta yi waje tana cigaba da kukan kamar wacce a ka sanar mata cewar unman ce ta mutu. Shima bayan ta yabi yana kallon wani sabon salo daga wajan matar tasa. Wai to mai ya ke damunta ko dai har yanzu barcin yamman ne bai saketa ba. Ganin ta zauna a palon ne yasa ya É—auko kulan abinci gaba É—aya ya nufo gurin ta ya na faÉ—in “kinga ko cokali uku kikayi sai kisha magani ki kwanta in ba hakaba zakisha wahala kodan cikin dake jikinki please honey ki daure.

Yana ajiye abincin Ameera da har yanzu bata daina kukanba ta É—aga kulan abincin ta buga da Æ™asa tayi booll da kulan ta na faÉ—in. “Idan ma wannan abincin na maitane to wallhi bazanci ba,ni barci nake ji na ce maka na koshi bazan ci ba. Ta na faÉ—a ta koma gurin daining tebul É—in ta kwaso sauran abincin da abun sha da ya haÉ—a musu suma tayi watsi da su tana gamawa ta koma É—aki tayi kwanciyarta abunta, cikin minti kaÉ—an barci yayi awun gaba da ita.

 

Shiru Adam yayi yana kallon ta batare da ya hanta komai ba har ta maba zubar da komai na abincin, shi kan Adam izuwa yanzu yasan ba wai barcin yamma bane yasa ta wannan haukan, anya kuwa Ameera ƙalau take, daga yau ɗaya kawai ta canja daga Ameeran da yasani izuwa zuwa wata aba da ban. Shi yanzu damuwarsa rashin cin abinci da batayi ba ne, rabonta da cin wani abun tun rana kafin su fita asibiti. Haka ya zauna saida ya gyara ko ina da ta ɓata kafin ya shiga ɗakin ganin har tayi barci yasa ya ja mata bargo ya fita izuwa masallaci domin yin sallar isha. Zuciyarsa yana jin izuwa gobe in sha Allah zata daina wannan ƙuncin. Har ya dawo daga masallaci barci takeyi, yaso ya koma ɗakinsa ya kwanta amma yayi tunanin kar Kuma ta tashi cikin dare tana neman abinci. Hakan yasa ya kwanta yana buƙatarta amma yana tsoran masifa, haka ya kwanta yana ta tunanin kyautar da Ubangi yayi musu a wannan lokacin da suke buƙata, kaman ya rungumota amma ya haƙura har shima barci ya ɗaukeshi. Da asuba shine ya fara tashi tun kafin yayi mata magana motsin sa ya tasheta, domin dama wani lokaci ma ita ke tashin su sallar Asubahi. Ko kallonsa batayi ba ta shiga toilet ta ɗaura alaula Koda ta fito bata ganshi ba, ta hau kan dadduma ta tada sallah. Tana idarwa ta koma barci ba tare da ta cire hijab ɗin jikinta bama,ga yunwa ta na ji amma barci ya hanata tashi.

 

Haka tana kwance har ya dawo. Ganin ko daddumar bata naÉ—e bane yasa ya naÉ—e yana kallon irin kwanciyar da tayi. “Good morning honey” ya faÉ—a yana hawa kan gadon domin komawa barcin. Jin shiru yasa ya kai kallonsa fuskarta ya ga ashe har ta koma barci. Da mamaki yake kallonta , iKon Allah wannan barcin dai anya kuwa na lafiya ne Ameera. Kasancewar safiyar litinin ce yasa bai so komawa barci ba amma baccin ya sa ce shi.

 

Misalin karfe shida daidai na safe Ameera ta farka tana jin wata a zababbiyar yunwa kaman an mata sata a cikinta,É“angare É—aya kuma ga wani irin Æ™unci da yafi na jiya da ta tashi da shi! Kallon gurin da yake kwance tayi sai taji bata son ganinsa a kwance, haka kawai taji barcin da yakeyi É“ata mata rai yake. Wayarsa ta É—auko ta duba lokaci ganin shida saura yasa ta ajiye wayar ta na tunani. Tashi ta yi ta na kallonsa kamar ta rufeshi da duka ganin yana barci. Kicin ta shiga ta haÉ—a tii (shayi) mai kauri da zafi ta É—auki kick ta fito falo ta zauna tana ci. Zumbur ta miÆ™e kamar wacce aka tsurkula ta shiga d’akin domin ita har yanzu barcin da yakeyi ya tsaya mata a rai haka kawai. Ta na shiga ta nufi gurin da yake, ta É—auki filo ta fara buga masa ta na cewa “Malam ka tashi ka tafi aiki, ko wani Namiji yana gurin aiki amma kai sai barcin a sara kakeyi tun jiya dadadare kake barci kamar wani mace malam wallahi sai ka tashi ka tafi aiki, yana Æ™okarin tashi amma taÆ™i ba shi damar hakan sai cigaba da buga masa fulo takeyi. Shi kuwa Adam cikin barci yaji ana dukansa yana son tashi amma sai Æ™ara danneshi a keyi Kuma ba’a daina dukansa ba. Da Æ™yar ya iya tashi zaune yana kallonta sai ajiyar zuciya takeyi kamar wacce tayi gudu. Sosai yake kallonta ganin ta kafeshi da ido tana jiran yace wani abu. Wayarsa ya lalubo ya duba lokaci ganin shida da minti biyu ne yasa ya d’ago kai ya kalleta ya ce “Yanzu Æ™arfe shida shine kike cewa kowani Namijin arziÆ™i yana gurin aiki? Ƙarfe shida fa Ameera? wai lafiya kike kuwa. Cikin masifa dake cinta ta fara magana bilhaƙƙi da gaskiyarta “Eh wallahi sai ka tashi, wani irin barcine haka tun dare har yanzu ana yinsa sai kace barcin a sara, ni dai wallhi sai ka tashi ka tafi aiki yanzu nake so kuma. Adam ya ce “Wai honey me ke damunki ne, yanzu ko mai gadin gurin aikin namu bai tashi ba amma ni zan tafi gurin aiki, Ko wanka banyi ba banci abinciba haka kikeso na tafi gurin aikin?

 

“Su sauran ma’aikatan an faÉ—a maka abinci sukeci suke zuwa? ko wankanma dolene sai kayi, Malam wallahi ka tashi ka fita dun kafin raina ya Æ™ara baci.

 

Cikin karaya ya ce “To kisamamin wani abun kafin nayi wanka. “Babu abunda zan girka kuma bazakayi wankan ba,ni dai kawai kabar gidan koma ina zakaje kaje bana son ganinka ne a gidan gaba É—aya.

 

Haka Adam ya miÆ™e ya É—auki doguwar rigarsa ya saka, ita Kuma ta na biye dashi a baya riÆ™e da filo ta na cigaba da maganganu “Ni bana son Namiji rago kullum barci-barci sai kace mace, kawai ka fita gurin aiki. Sai da ta kaishi har Æ™ofar falon fita kafin ya ce “Kinci abincin ne ke? Cikin tsiwa da matsuwa da ganin yabar gidan ta ce “Ina ruwanka da naci ko banci ba. Tana faÉ—a ta tura shi waje ta rufe gidan tana Jan tsaki.

 

Tsaye Adam yayi a waje daga shi sai doguwar riga sai yanzu ya kula da ko takalmi ma babu a Æ™afarsa wayarsa ma a ciki ya baro ta, afili ya ce “Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raju’un! Wai me ke damun honey ne, anya kuwa ba sauyamin ita a kayi a asibiti ba, to idan ba haka ba menene matsalar daga jiya zuwa yau na kasa sakewa a gidana babu damar nayi gwaninta. Ya na laluba aljihunsa yaji babu makullin mota, sannan babu ko sisi da zai hau mashi izuwa gidan Æ™kanwar sa, kasancewar babban abokinsa take aure. Ko da yazo mai gadi barci yake yi abunshi haka ya buÉ—e get É—in ya fita yana kallon titin tsit sai É—ai-É—aikun mutane masu tafiya a Æ™asa. Sai da ya daÉ—e kafin ya samu mai mashi ya hau izuwa gidan su Najib. Koda suka isa ya tsaya a bakin get d’in gidan yana bugawa, amma sun kai minti biyar babu wanda ya amsa harma mai mashin É—in ya fara magana, suna cikin haka mai gadi ya buÉ—e get É—in da masifar katse masa barci da a kayi, domin yasan dai masu gidan suna ciki. Amma ganin Adam yasa ya saki fara’a yana masa barka da safiya.

 

Cikin jin kunyar ganinsa a haka da mai gadin yayi ya ce “Kamin mgn da Najib yanzu please. Ko da Najib yaji cewar Adam ne da sauri ya fito yana mamakin zuwansa da sassafennan dama jiya kadija ke sanar masa da cewar Ameera tanada ciki kodai ba lafiya bane. Kafin Najib yace komai Adam ya ce “Please sallami mai mashin É—in nan yana faÉ—a ya shige gidan ya bar Najib da mamaki ganinsa a birkice.

 

Ameera kuwa bayan fitan Adam palo ta koma ta zauna ta É—auki shayinta ta fara sha, jin yayi sanyi yasa ta koma kicin É—in, ta Æ™ara haÉ—a wani, zata É—auki keck amma taga ya Æ™are, ita kaÉ—ai sai kumbure-kumbure takeyi, tana jin haushin komai ma shi kanshi gurin da a ke ajiye Keck É—in ganin babu saida ta rufe gurin da Æ™arfi har yana tsagewa. Firiza ta buÉ—e ko zata samu super commando domin shine drink dinta shima ganin babu yasa ta ture firiza É—in da Æ™arfi har yana faÉ—uwa ko ta kansa bata biba ta duba bredi shi Kuma taga saura kaÉ—an Kuma ya d’an bushe hakan yasa tayi wurgi dashi ta shiga É—aki ta É—auko kuÉ—i ta nufo gurin mai gadi.

 

Tsabar masifa na cinta ma ko sallama bata yi ba ta fara buga Æ™ofar É—akin kamar É—akin ne yayi mata laifi. “Baba mai gad…Baba mai gadi!… Da sauri baba mai gadi ya fito yana amsawa domin ya gane muryarta.

 

“Na’am hajiya lafiya dai ko?

 

“Saboda nazo kiranka shine kake tambayar lafiya? Ok idan da lafiya ban isa kiranka ba kenan ko? Na ce ban isa kiranka ba kenan ko?

 

Jin yayi shiru yasa ta harareshi sannan ta ce “Aikenka zanyi kuma saura kamin shirme kuma wallahi ka dawo yanzu! Tabna faÉ—a ta jefa masa dubu É—aya ta ce “Abu mai laushi zaka sayomin yanzunan karka É“ata mini lokaci. Ta na faÉ—a ta juya ta fara tafiya ta bar baba mai gadi da buÉ—e bakin ganin sabon lamari daga matar gidan nasu. Matar da ko É—aga ido ta kalleshi bata yi, bare har tai masa ihu barema aike, shi dai tun da yake a gidannan bata taÉ“a zuwa ta aikeshi ba, wani lokacin dai Adam ke turota ta ce inji Adam ka sayo abu kaza. Ganin zata shige be kuma gane aiken ba ne ya ce

 

“Hajiya wani abune mai laushi bansan wanda zan sayoba?

 

Tun daga gurin da take ta nufoshi cikin masifa kai ka rantse zaginta yayi, har tana haÉ—awa da gudu ta iso gurinsa ta ce “Kai baka da ilimi ne baka san abu mai laushi ba har sai ka tambaya to kaje ka sayo goriba ko rake tunda baka da lissafi, yanzu abu mai laushi har sai an faÉ—a maka in banda samun guri, to wallhi kaje ka sayo min yanzu ina jiranka. Ta na faÉ—a ta juya fuuu ta nufi ciki ta bar baba mai gadi tsaye yana juya kuÉ—in yana nazari to meye abu mai laushi! Kuma da sassafe haka, anya kuwa hajiya lafiya taka. Haka dai ya fita badan yasan me zai sayo É—in ba.

 

Ita kuwa Ameera bayan ta koma ta nufi gurin da firizan da tafaÉ—ar tana son ta É—aga amma ta kasa, tati-tayi amma ko motsashi ta kasa, haka ta dawo ta zauna tana jiran baba mai gadi domin taga mai zai kawo mata, domin ita kanta bata san me takeson ci ba, ita dai tasan Abu mai laushi take marmari, idan da za’a yankata bata san me take son ci ba, kuma bata son cin bredi hakan yasa bata ce masa bredi ba.

 

Najib da kadija cikin mamaki suke tambayar Adam lafiya dai yazo a haka. Cikin rashin sanin abun yi ya ce “Wallahi babu lafiya gidana tun jiya ba lafiya. Da sauri kadija ta ce “Mai ya samu Ameera É—in Yaya? Wani abun ne ya samu cikin nata?

 

Shi Adam har ga Allah harma ya manta da cewar cikene gareta. Cikin su’butar baki ya ce “Au wai dama ciki gare ta?

 

Da mamaki Najib da kadija suka Kalli juna jin abun da ya ce.

 

“Yaya ina ce kai da kanka jiya ka kirani kace Ameera nada ciki ko dama tsokana ta ka keyi? Kallonsu yayi ganin sun kafeshi da ido sai ya sunkuyarda kai ya ce

 

“Eh gaskene kawai sha’afa na yi.

 

“Ban gane ka sha’afa ne ba, wai wani abu ne yake faruwa ka fito ko takalmi babu ga shi ko kayan arziÆ™i babu a jikin ka, yanzu kuma wai kace ka sha’afa ne lafiya kuwa? Najib ya faÉ—a yana Æ™ara nazarin abokin nasa.

 

Cikin murya tausayi Adam ya fara cewa “Wallhi tun jiya da muka dawo daga asibiti Amerra ta sauya, dana tun kafin jiyan ta zama abu kaÉ—an fushi da masifa, to daga jiya kuma abun ya Æ™aru komai nayi masifa, idan nace taci abinci masifa,idan na tasheta a barci faÉ—a, yanzu haka itace tace wai na tashi na tafi gurin aiki, nace mata lokaci baiyi ba wai wallhi sai na fita, ta barni na sake kaya ko naci abinci ma wallhi taÆ™i, harfa waje ta rakoni tana dukana da filo. Ya Æ™arasa kamar zaiyi kuka.

 

Dariya kadija ta yi tana cewa “IKon Allah ita Ameeran ce harda dukanka? To ko dai nata cikin ne yazo mata da Æ™unci da É“acin rai?

 

“To Kuma sai tayi É“acin ran harda ni mijinta? Adam ya tambaya cikin rashin yarda.

 

Kadija ta ce “Ta to wallhi yaya in dai irin wannan cikin ne to mutum koma waye sai ta masa, wani lokaci ma idan bata samu abokin yi ba to kuka zata fara ita kaÉ—ai ko kuma ta samu wani abu a gidan ta huce a kansa, irin wannan yanayin mata da yawa na shiga irin sa, Kuma suna shan wahala sosai dole sai kayi haÆ™uri, dama ai Yaya ka sha faÉ—in cewar idan Ameera ta samu ciki zaka tarairayeta kamar Æ™wai, to kaga haka zaka daure.

 

Cikin mamaki Adam ya ce “Wai dama cikinne yasa wannan abun? Nifa duk inace barcin yamma da tayi ne yasa ta haka, yanzu dan mace nada ciki sai ta fara masifa Fisabililahi! Najib ya ce

 

“Ai kawai abokina haka zaka daure, yanzu dai ka shiga kayi wanka ka fito muci abinci anjima kadija sai taje gurinta kar a barta ita É—aya a gida kaga babu daÉ—i. Adam ya tashi ya tafi É—akin da suka nuna masa yana tafiya yana mamakin wannan lamari, yanzu kawai sai mace ta fara masifa saboda ciki, shi bai ta’ba jin wannan labarin ba.

 

Tana zaune idonta Æ™urr a Æ™ofar falon Mai gadi ya turo Æ™ofar falon hannusa riÆ™e da leda, idonta a kan ledar domin ganin mai ya kwaso mata. Shi kuwa baba mai gadi jikinsa har rawa yake domin yasan dole sai ya she masifa barin ma yanzu da ya Æ™ara haÉ—a ido da ita ganin yadda ta kafe ledar da ido. A zuciyarsa ya ce “Yanzu fisabililahi ki aiki mutum ba tare da kin sanar da shi abun da zai sayoba, fatan kawai ki wahalar dani, yanzu nasan dole sai na koma. Jin tsawar da ta daka masa ne yasa shi saurin Æ™arasawa gabanta ya miÆ™a mata ledar kamar zai faÉ—i. KarÉ“ar ledar ta yi ta na Æ™oÆ™arin buÉ—ewa, ganin ledar na mata gardama ne yasa ta yaga ledar tana jin Æ™amshin abun da ke cikin ledar, cikin mamaki take kallon abun da ke ciki. ÆŠagowa tayi ta kalleshi kafin ta Kara kallon abin da ke ciki ta ce…

 

 

 

Kubi S-REZA a hankali kusan bai saba baku kunya ba.

Close Menu