Ad Code

Da Ciwo A Rayuwata Hausa Novel Complete

Da Ciwo A Rayuwata Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

DA CIWO A RAYUWATA_*

 

Page A

 

Na Wawa shi ke fadin abin da zai aikata, mai kuri shi ke bayyana abinda ya aikata. mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa.

 

*

*

 

Mai_Dambu

Wattpad:Mai_Dambu

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

 

Adamawa State….

 

Jumeta, kwance yake a cikin lambu kanshi akan cinyata wanda yake lulluɓe da mayafi so yake yasaka hannunshi cikin ya yayye mayafin dake masa shamaki da ni, abin mamaki sai yaga hannunshi yaki kaiwa dole ya ɗago daga cinyarta gani yayi wani mutum da wasu yan mata uku da yar karamarsu suna janta koda ya mike take yaji tana cewa.

“Kazo ka taimakeni  Sadeeq kchvvvvarka bari su tafi dani Sadeeeeeeeeeeeeeeq..”

 

A firgice ya farka daga mugun mafarkin da yake akaina wanda inda sabo yasaba ganin dattijon dake kusada shi yasa ya gyara zamanshi addu’a yayi sannan yacigaba da kallon kasa kamar mai nazari,

“Assalamun Alaikumun” akayi sallama a bakin kofar ɗakin, sanin wanda yayi sallama ba bakonsu bane yasa Dattijon yace.

“Waalaikumun Salam, Imran kashigo mana ai gidan ba bakonka bane kota jikin bango zaka iya shigowa balle kuma ta koina nagidan.”

 

Bayyana yayi a gabansu cikin jin kunya ya dukar da kanshi yace.

“Malam jauro ina wuni, dukda

Karfe sha biyu saura na rana,”

 

“Lafiya lau Imran ya gida ya iyayenka, da sauran mutanenku.” Inji Malam jauro yace masa.

Murmusawa yayi kafin yace.

“Suna lafiya, kakatace ma ta aiko ni gurin wanca miskili bansan yanda zai ɗauki maganar ba dan nasan a halin ynx tsoron mutane yake, taya kuma zai iya kawo karshen wasu matsalolin.”

Nahuce Part 4 Hausa Novel Complete

Shirune ya gifta tsakanin duk maganar da suke baisa ya ɗago ya kallesu ba, yasan daga Imran har kakanshi bazasu taɓa cutar da shi ba, sake cusa kanshi yayi cikin tsakankanin cinyoyinshi ya rufe idanunshi bayan ya zagaye hannunwanshi akafarshi, yayi musu shiru

 

Gyara zama  malam jauro yayi kafin yace.

“Malam Imran da fatan lafiya dai wannan aikan.”

 

Girgizai kai yayi kafin yace.

“Nidai tace min nazo na ɗaukeshi zuwa bauchi yayi wani aiki na taimako bayan haka bansan mi take nufi ba, naso nasan mi yasa ta turashi can sai tace min yaje zai ga abinda idanunshi”

 

Bai ɗago ba kuma basuyi tsamanin zai ce wani abu ba yace.

“Kaka yau ma nasake tana ihu da niman taimakona Ya Allah kusani a addu’arku mana.”

A raunane ya kai ayar maganarshi, kusadashi Imrah ya isa ya dafashi kafin yace.

“Babu lokaci kazo muje ana jiranmu fa, sai dai kayi hakuri dan zaka zama bawa a wani gurine dan bayan bukatar wasu,”

 

D’ago kanshi yayi cike ds ɓaccin rai ya ture hannun imrah sannan ya zabga masa harara kaman bazai magana ba nan kuwa a hasale yake da masifa.

Yace

“Wato ku aljannu kuna da matsala tunda kuka taimakeni shi knn kuka mai dani bawanku wallahi zan iya zabga maka naushi sannan naje har inda Kak…..”

 

Ji yayi a rike masa wuyarshi  ba tare da ya karasa batunsa ba, murmushi Imrah yayi sannan yace.

“Kaine kake da matsala bamu ba. Inda zaka domin kanka aka tura ka, matukar kace baxaka ba toh tabbas akwai matsala akan rayuwarku malam tashi muje babu lokaci.”

 

Sake masa wuya akayi  jikinshi ba kwari ya mike ya shiga haɗa kayanshi bawai baida yanda zaiyi bane sai dai bazai iya bijirewa ImraN da Family shi ba, sun gama masa kome a rayuwa sunyiwa Rayuwarsa hidima musamam Imran da Kakarsa mace.

 

Yana gama haɗa kayanshi Imran ya kalli Malam jauro yace.

“Duk halin da yake ciki zai faɗa maka zamu haɗa karfi da karfe mu taimaka musu, amma dole sai yaje Bauchi tukun yaga muna maka sallama irinta addinin musulunci.”

 

Jinjina kai Malam jauro yayi sannan ya mika masa hannun sukayi musabaha, haka ma Sadeeq ɗin suna fitowa tsakar gida sukayi kiciɓis da Innawuro kallonta Sadeeq yayi sannan yace.

“Tsohuwar karfena zanyi balaguro nawani lokaci.”

 

Tsaki tayi ciki ciki, sannan ta kunce goron bakinta ta ɓantara cike da masifa take taunawa sannan ta ɗago manyan idanunta ta banka masa harara tace.

“Wallahi ka kwalta tuzurun banza tuzurun wofi a haka dai zaka zauna kana bacci a ɗaki idan ka isheni auro maka Bintalo zanyi.”

Murmushi yayi ya juya suka bar cikin gidan har yakai bakin kofa ta kwala masa kira dole ya tsaya cak tana zuwa ta mika masa farin langa bokiti tace.

“Gashi nan sadiquna dambu zabine.” karɓa yayi sannan ya mata godiya, juyawa tayi tana shafce hawayenta cike da bakin ciki komawar jikarta haka, koda suka shiga mota basu ɓata lokacu ba dan motar Imran ce.

 

*Bauchi State*

 

At A.T.B.U……

 

A hankali nafito daga cikin aji ina tafiya a gajiye sabida tsayuwar danayi na koyar da ɗalibaina yan matakin masters duk jikina yaga mutuwa gida kawai nake bukatar zuwa, ofishina naje nagama abinda zanyi nasa kai nafito ko bakin kofan ban bari naji suna min dariya ɗaya daga cikinsu nace.

“Eh nafaɗa maku budurwace bata taɓa aure ba, wallahi.”

 

Can wani a cikinsu yace.

“Ina budurwa a talatin da ɗaya budurci yayi gaba abinshi yaushe zata zauna babu namiji bazawara dai ko,”

 

Haka sukayita faɗar maganganu akaina, da sauri na isa gurin motata na tada ita a guje ina tuki amma zuciyata cike yake da kunci haka nafigi motata raina a ɓace wai shin nizan iya sauya kaddarata ce, da mutane suke kalubalantata, dakyar Allah ya nufa na isa gida, ko parking me kyau banyi ba na fita daga motar aguje ina kuka, yana zaune shida Baba maigadi, wanda yq buɗe min kofa, da kishiyar Inna nafara cin karo inda na zube a jikinta tare da fashewa da wani irin kuka, jikina na rawa na ɗago kai ina kallonta cikin kuka nace.

” Nenne shin laifina ne da banyi aure ba, ko wani yana wucce kaddaransane.”

Girgiza kai tayi a tsanake sannan tayi murmushi sannan tace.

“Kome yayi farko zaiyi karshe Amrahtu hakuri da kikayi na shekaru yakusan zuwa karshe kiyi hakuri kinji”

 

“Nenne Da ciwo a rayuwata fa, tun kuruciya nake kuka Nenne har yau kuka nake, duk wanda yazo gurina yau gobe bazai sake dawowa ba idan kuma ya dage da  niman aurena karshe mutuwa yake.”

 

Shafa kaina tayi tana kallon fuskana da yayi ja, itama goge kwallarta tayi sannan tace.

“Tashi ki shiga ciki,”

 

Haka na mike jikina bakwari na shige ɗakina da aka ware min, sai da nayi kuka mai isata sannan na rage kayan jikina na ɗaura towel na shiga wanka, ina fitowa nayi sallar la’asar na dan kishingiɗa sai barci  sosai nayi, sai gurin karfe biyar da kwata na mike shima sabida mafarkin da nayine wanda ina tashi na manta kome wanka nashiga da alola sannan nasaka doguwar riga mai karamin hannun nafito zuwa falo, muryan Ya Abbas da Baffanmu yasa na karaso fuska ɗauke da murmushi na zauna a cikinsu, nan kuwa hira yasake ɓarkewa har muka gangaro maganar, ɗaukar min drive da akayi shiru nayi kaman ruwa ya cinyenk, kiran sunana Baffanmu yayi.

“Amratuuuuu, shin drvn bai miki bane naga kinyi jum.”

Girgiza kai nayi cikin sanyi jiki nace.

“Baffa ba haka bane kawai gani nayi ai nima zan kula da kaina ko?.”

Kaina a sunkuye na bashi amsa

“A’a Amrahtu ina gudun kar wani ya sake yunkurin cutar dake ne, shi yasa na daukar miki shi kuma naganshi yana da kamala da nutsuwa!!!” nufashinsa ya sauke kafin ya cigaba da cewa.

“Gashi yana da ɗan ilimi dan har N.c.e yayi zanga takardunsa sai na nima masa aiki kinga bazai kare a tukaki ba kafin Allah ya kawo miki miji na gari, yawwa ɗazun suwaye suka saki kuka.”

 

Murmushi nayi sannan nace.

“Ai ya wucce a manta dasu kawai.”

 

Sai naji zaman falon ya gundireni, dan bana son tukani da wani zaiyi, koda yake banga laifin Baffa kwana uku da suka wucce ina fitowa daga yelwa zan yanko kwanar governmen house wasu yan dabba suka tare ni har suka fasa min glass ɗin motata,  dakyar Yan sanda da suke gurin suka koresu parking nayi na kira Ya Abbas wanda yake aikin a Cid office yazo ya daukeni cike da tsoro anyi bincike ba agano ko suwaye ba shi yasa aka ɗan saka min matakan tsaro wanda Aikin Ya Abbas ne,

 

Dakina na koma cike da jin haushi, buɗe wayata nayi na duba naga babu data, tsaki nayi na ɗauki gyalena zuwa waje kafana sanye da yar silifas taroba mai pink da blue, a hankali na fito harabar gidan suna zaune da ma’aikatan gidan, idan suke hira cikin nishaɗi shi kuwa yana zaune murmushine kawai akan fuskarshi, kallo ɗaya nayi musu na kauda kaina Nura me yiwa flower gidanmu ban ruwa nakira na bashi 3k nace ya sayo min da sauri yafita, ina tsaye a gurin ina kallon motata da naga an gyara mata zama, tunawa nayi da akwai abubuwa a cikin motar, a hankali na isa gurin motar nasa hannuna na buɗe, ban lura ba sabida hankalina na kan Nura da ya shigo cikin gidan nakai hannuna knn zan ɗauki kayana, kamar ance kalle, hmmm macizai guda huɗu nagani a cikin motar tsananin tsoro da firgici bansan lokacin da na daka tsalle ba, sannan na akwala ihu tare da rufe motar zaman dirshan nayi a can gefe guda jikina na rawa,

 

Kafin ace wani abu duk masu aikin gidanmu da Baffanmu da Ya Abbas haɗi da Iyayena mata son kawo min ɗauki har da shi a ciki suka iso kaina kowa na tambayana lfy kamar wacce ta tashi daga barci na mike zubur jikina na rawa nace musu.

“Wallahi wasu irin macizai nagani a cikin motata, ni na hakura da motar,”

 

Buɗe motar sukayi aka duba ba’aga kome ba yana jingine da motar Ya Abbas.

 

Haka sukai ta niman macizan nan babu su babu dalilinsu, asalima kamar babu alamarsu, haka suka hakura suka ɗibo min kayana zuwa cikin gida jikina a sanyayye na shige ɗakina ina jinjina wannan al’amarin

 

***

Washi gari…..

 

Karfe goma da rabi nafito ina fitowa nasame shi a cikin motar, taɓe nayi sannan na shiga motar a hankali yaja motar, wayarshi ya ciro ya duba map ɗin bauchi A.t.b.u yayi searche nan hanyan ya fito masa, jinjina girman kanshi nayi ace mutum ga wanda zaka tambaya, hmm.

 

Har cikin makrnt ya shiga dani nan ne kuma yayi parking yana kallon wayar can yasake figar motar har department ɗinmu ko cikan ka bance ba nafita tare da ɗibar kayana zuwa ciki, bai tambaye ni yaushe zai dawo ba nima ban damu da na faɗa masa ba……

 

#Fiction

#Spirits

#Jinn

#Amsad……By Mai_Dambu

 

*_DA CIWO A RAYUWATA_*

 

Page B

 

Na

Mai_Dambu

Wattpad:Mai_Dambu

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

 

Karfe ɗaya narana ina fita anan na same shi yana jirana, buɗewa nayi na zuba kayana na zauna sannan muka bar makrnt a gajiye liɓis sai ajiyar zuciya nake sabida gajiya,

 

A titin Ahamdu bello way muka tsaya gurin traffic muna jira wasu yan mata guda huɗu suka zo ta inda nake kaina a sunkuye, ina duba wayata, dukda glass ɗin a rufe yake amma abin mamaki sai jin muryansu nayi suna cewa.

“Umma abamu sadaka sabida Allah”

 

Cike da mamaki na ɗago kaina ashe a waje suke, kallonsu nayi kafin na shiga kiciniyar zuge glass ɗin yaki buɗuwa daga gaban motar yace.

“Koda wasa karki basu kome na faɗa miki.”

 

Mamakine ya sake turnike ni na zuge glass ɗin motar na mika musu 1k kuwa garin kiciniyar karɓa naji sun karceni da wani abu kamar farce da sauri na maida hannuna ina yarfewa, ɗago kaina nayi da niyyar kallonsu wayam nagani babu su babu dalilinsu, sake duba hannun nawa nayi naga yayi wani irin ja…..

 

Inda babu ciwon na fitar da wani irin zufa, shiru nayi har muka bar gurin jikina yayi sanyi  koda muka isa gida yana fakin na kwashi kayana zuwa cikin gida abin mamaki hannuna kara kumburi yake, har na shige ɗakina babu kowa ina shiga  zubar da kayan nayi na faɗa ban ɗaki ina kwara ruwa ko kayan jikina banyi ba sabida mugun zafin da nake ji, ina fitowa na yanki jiki na faɗi…..

 

****

“Koma Yaya ne dole kasaka ido akanta dan sabida ita kazo gidan nan kayi kokarin gano inda matsalar take, ynx haka tana can ɗakinta ta suma sabida gubar macijin da ke jikinta, kasan abinyi kafin lkc ya kure maka.” Inji Imran knn,

“Toh ya kake so nayi mata sam babu ɗa’a afuskarta mutanen gidan basu da matsala amna ita tana da matsala dan na lura  bata da kunya kodan kananun kuɗin da take ɗaukane suka ɗaga mata hankali shi yasa take hura hanci ranar da ta ɗauki manyan kuɗi ai ba’a magana ni babu abinda zan iya mata.”

 

Da imran yaga bashi da niyyar zuwa sai ya ɓace a ɗakin ya rikiɗe zuwa sufar Sadeeq ya shiga cikin gidanmu yayi sallama a kofr falo Badi’atu ta amsa masa sallqmar, tare da ɗaga labule “sannu dai kana son wani abune?”

Ta tambayeshi tare da kafa masa idanu, girgixa mata kai yayi sannan ya mika mata wayata, yace.

“Hmm ɗazun nazo karkaɗe motar naga ashe Hajiya ta manta wayarta a motar.”

 

Karɓa tayi tare da sake masa murmushi dan sadeeq Allah yayi masa baiwar kyau kamar mace, fari tasss.

 

Kaman yash, haka yake kunga dole badi’atu ta sussuce, niko a jikina dan kyanshi bai burgeni ba asalima ni baka ce  dan duk yan gidanmu farare ne nice baƙa , yana mika mata ya juya da sauri yabar kofar falon,

 

Itama kuma ta komo ciki ɗakina halin da tasame ina kwance malala akasa, kamar mara numfashi, ihu ta fasa sannan tafita da mugun gudu tayi ɗakin Nenne ta faɗa mata kasancewar Innarmu ta rasu, nenne ita ta zame mana uwa, kuma,da itace uwar gidan baffa. Tun auren saurayi da budurwa, ita tahaifi Ya Abbas sai aunty Mariya sai….

 

Da sauri mutanen gidanmu suka shigo ɗakina suna zuwa suka shiga kiciniyar ɗaukata basu ajiye ni a ko ina ba sai asibitin  City clinic dake titin bank road da gaggawa aka amshe ni kusan babu bincike da basu yi ba haka suka cigaba da zuba min allura har bayan kwana uku,

 

Karshe wancan yaron dasuka kawo a drv na shi yakawo maganin da aka shiga bani ina sha, sai gashi nayi aman wani farin ruwa kamar madara mai shegen wari. Kwana shida aka sallameni.

 

***

Abinda na lura yaron yana da girman kai, dan dakyar ya shigo gaishe ni ko kallon inda yake banyi ba nace lafiya.

Daga haka ban kuma kallon inda yake ba, asalima ɗan banzan yaro kwarjini yake min bansan dalili ba…

 

****

Kusan satina biyu a gidan na fara zuwa a.t.b.u. ranar da zan fara zuwa ban faɗa masa ba sai ganina yayi a shirye aikuwa ya taso yazo ya buɗe motan ya shiga abinshi yusha’u ne yazo da sauri ya buɗe min kofa motar nasaka kayana raina aɓace nacewa.

“Yusha’u nagode sosai.”

 

Tsaki nayi kasa kasa nace.

“Yaro karami sai tsabar iskanci da rashin kunya idan mutum bazai iya aikin ba ya bari mana.”

 

Murmushi yayi da gefen baki yaja motar zuwa makaranta.

 

Ina gama koyarwa na shigo officer din sai ga H.O.D mun ya shigo nan muka gaisa dashi hankalina na kan aiki ashe shi nashi hankalin akaina yake ban ji haka nayi a jikina ana kallona ina dago kai sai ya shiga sosa kanshi yace.

“Dama ina son magana dake maybe zan shigo unguwarku da yamma.”

 

A hankali na saci kallon yan ofishinmu sai naga kowa harkan gabanshi yake dan haka na gyaɗa masa kai kawai dan babban mutune ya manyanta sosai dan haka da girmamawa a tsakaninmu.

 

Ina tashi nafito har gurin parking nazo babu yaron nan babu dalilinshi haushine ya kamani na tsaya jiranshi can sai gashi yana zuwa na buɗe nasaka kayana na shiga ciki na zauna.

Nace.

“Wannan wani iskanci ne daza tafi yawon banzan ka, ko kamanta da ina jiranka ne, eyye ni bana son shashancinku irin na yaran nan.”

 

Juyowa yayi ya kalle ni sosai kafin ya juya ya fara tafiya ranshi ya ɓaci sai tauna bakinshi yake har muka isa gida.

 

Bayan sallar magarib sai ga h.o.d mu yazo iso nayi masa har falon baki anan dai muka gaisa na ajiye masa abin taɓawa, yasha ruwa sannan ya zuba min ido kafin yace.

“Amrah dama nazo ne ina niman damar aurenki da fatan ba matsala kinga dai mu ba yara bane ya kamata mu tsayi da magana ko ya kika ce, dan nasan akalla shekarunki bazasu haura talatin da ɗaya zuwa dabiyu kinga ni kuma next month nake da hamsin da huɗu da fatan ban tsofa miki ba”

 

Kunya ce tasa na rufe fuskana ina dariya tare da gyaɗa masa kai mun dan zanta kaɗan sannan muka rabu jibi zai turo magabatanshi,

 

Ko Nenne ban fadawa ba sabida nasan ba lallai bane yasake dawowa, washi gari har ofishina ya biyo ni inda muka ɗan taɓa hira har yake tambayata a ina nayi master da phd nace masa a Canada munyi hira sosai sannan muka rabu abinka da jami’a sai gashi ana gulmarmu..

 

Kaman yanda yace haka kuwa takasance sai ga manyanshi sukazo har gida, dake sun shirya har da sadaki suka bada,

Sati uku tsakanin sai ga kayan aurenshi soyayya ba kama hannun yaro, sai wani rawan kai nake amma duk da haka lokaci zuwa lokaci jikina na sanyi da al’amarin,

 

Ansa bikin wata biyu masu zuwa dan haka kowani shashi shiri ake sosai musaman ta shashinmu anfi shi,

 

Lokaci na tafiya yanayi nakara kitsu kai har binki ya rage saura satittika a hankali ya sauko yan kwana ki.

 

Ana saura kwana biyu anyi kamu washi gari juma’a akayi walima, bayan an watse yazo gidanmu nafito har motanshi na shiga muka gaisa, fitar da ɗaya kafarshi yayi waje mukq cigaba da hira can yaji kamar cizon kwaro yana dubawa yaga babu kome dan haka ya share muka cigaba da hiranmu can yaji kafar tadameshi dan haka mukayi sallama, ya tafi yana isa gida yasa kai zai cire kafar sai yaji tayi masa wani irin nauyi kamar dutse tayi fari fat, ga wani irin farin ruwa na zuba ,

 

Dakyar ya shiga cikin gida dake gidansu family house ne amma kowa da side ɗinshi,

 

Dakyar ya shga babban falo yana,zuwa ya yanki jiki yana zubda wani farin ruwa irin wanda yake fita akafarshi…….

 

Toh fa

 

#Fiction

#Spirits

#Jinn

#Amsad……By Mai_Dambu

Pls share nd Comments

 

*_DA CIWO A RAYUWATA_*

 

Page C

 

Na

Mai_Dambu

Wattpad:Mai_Dambu

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

 

Page C.

 

Salati duk matan falon suka saka tare da mikewa suna kiran sunanshi “Alhaji Yusif”

Yaranshi kuwa har sun fara kuka shigowar ɗaya daga cikin Yaranshi da gudu ta zuɓe a gurin tace.

“Ku kyale min Babana karku kuskura musa kafar wando ɗaya daku ku kyale shi naceeee”

 

“Hahaha Zabba’u kenn zamu kyale shi sai ya janye daga niman auren Uwarmu in ba haka ba sai dai ya mutu dan alkawari muka ɗaukawa Babanmu sai mun kashe duk wanda yace zai aureta kuma duk kashedin da muka…”

 

“Keee Fauzn ban tambayeki ba ku fita min a jikin babana” Zabba’u ta buga mata tsawa,

 

Abin kamar almara haka idanunshi suka koma fari fat kamar yanda jikinshi ya koma dan har gashin kansa yayi kaman hazo.

 

Tun goma na dare ake abu ɗaya har karfe biyar na asuba a dare aka nemo wni malamin yazo suka sakasu a gaba ana abu ɗaya sun kafe sai ya fasa auren matukar aka fasa ko hanyar da yake bi bazasu sake bi ba.

 

Suka je masalaci suka dawo da kanenshi maza da wasu yan uwan babanshi da Mahaifiyarshi suka tsayida magana a janye auren an fasa sun tsayida shawara misalin goma nasafe,   gurinshi suka zo sukayi sallama dakyar suka amsa,

“Toh mun janye auren ya fasa Insha Allah ya rabu da ita knn.”

 

Kafin malamin ya gama magana har sun fita abinsu kafar dake ruwa ya koma kamar bashi ba dama ta nan suka shigeshi, ya jima yana bacci kafin ya farka nan mahaifiyarshi tace.

“Toh dama ai ba yau akafaɗa min kome akan yarinyar da kake nima ba dan haka indai nice na haifeka na haramta maka aurenta har duniya ta tashi.”

 

Shiru yayi yana kallon mahaifiyarshi kafin ya gyaɗa kai, nan aka shiga niman mutanen da zasu gidanmu suce an janye aurena.

 

:::

Yana kwance tun da nayi sallar asuba zazzaɓi ya rufe nu,dakyar nasamu nayi wanka nasha farfesun da aka haɗa min waina gyara, ina sha ina sake murmushi sabida son da nake alhji a shirye nake na bada kome nawa kuma ai dama ni nafi son auren babba wanda ya manyanta zaifi sanin darajata akan na auri sa’ana ko wanda bai fini ba, ko wanda yafini da kaɗan dan dukkanmu sai a hankali.

Key motata ce faɗo min arai na mike da sauri ina jin hayaniyar yan shirin ɗaurin auren karfe sha ɗaya sai kaiwa da komowa suke,   ta kofar kitchen na bi naje har inda wanca yaron yake yana ɗakinsu ganin Yusha’u nace.

“Yusha’u ina wannan yaron yake?”

 

Kallona yayi da mamaki yace.

“Wani yaro hajiya kuma.”

Taɓe baki nayi nace.

“Sabon drvn nan mana”

“Ai Sadeeq”

Nayi masa shiru nuna min ɗakinsu yayi yace.

“Yana jinki ai dan yana ciki.”

 

Haushine ya kamani na bankaɗe labule, yana sanye da farar dakakkiyar shadda kamar shine angon. Tsaki nayi a madadin sallama na mika masa hannuna nace.

“Bani key”

 

Kamar da dutse nake magana idan kuka ganni dashi sai kun jinjina min rashin kunyata Eh nasan na girmeshi but baxai wucce irin 2yr to 3yr bafa amma ji nake kaman na haifeshi, sabida ina koyarda wanda suka fishi da sa’o’inshi a jami’a gani yar karama dan idan ban faɗa maka shekaruna ba bazaka yarda ba,sabida ni yar mitsila ce, kome nawa karamine shi yasa mutane suke raina girmana, amma duk da haka inada cikar halitta daga sama har kasa, sake nanata masa nayi nace.

“Ɓazaka bani key ɗin bane ko sai na maka ihun ɓarawo ishashe mara kunya”

 

Ɗago idonshi ɗaya yayi ya kalleni daga haka bai kuma cewa kome ba, fusata nayi na shigo ɗakin na tsaya masa kerere a tsakar kanshi ina masa rashin mutunci.

Mikewa yayi tsaye Wallahi basan lokacin da na ɗaga kaina ina kallon basumudan gaba ba, kutt nace a raina, dama haka yake da tsawo sai gani a gabanshi kamar lomar tuwo, saka hannunshi yayi a aljuhunshi ya wurga min key ɗin, tsabar raine kin ɗauka nayi nace.

“Zaka ɗauko kabani ko sai na falla maka mari”

Zama zaiyi amna baisan lokacin da dariya ta,suɓuce masa ba,

Gyara zama yayi irin bismillah nan haushi yasa na ɗauki key na nayi gaba ina masa gorin yazo cin arziki yanawa mutane gadara. Bai damu kallon Imran yayi yace.

“Kaii Wannan matar akwai masifa na tausayawa mijinta.”

 

Dariya imran ɗin yayi yace.

“Idan kuma Allah ya nufa kaine mijin fa”

 

“Tir Allah ya sauwaka ba daini ba ina zankai wannan tsohuwar nifa burina na auri yarinya yar sha bakwai wacce zan moreta ta moreni ina zan kai guzuma irin wannan wllhi na aureta toh na shiga uku.”

 

Shi dai Imaran baice kome ba har suka fito waje.

Tunda na shiga cikin gida gabana ke faɗuwa dan saura mintuna goma idanuna akan agogo har lokacin yayi.

 

A falon baki yan uwan H.O.D ɗinmu ne suka zo akan an fasa tashin hankali bayqn sun gama bada hakuri sun fitane Ya Abbas ya fito sallamar mutane anan yake faɗawa ma’aikatan gidan haka kawai sadeeq yaji sun bashi tausayi riko hannun Ya Abbas Sadeeq yayi suka koma ciki, ya zuɓe a gabansu shiru yayi kafin yace.

“Idan bazaku damu ba a maida auren kaina da matukar nauyi a sallame mutanen da sukayi dogon tafiya haka dan shaida auren.”

 

Gyaɗa kai sukayi da yan uwan baffa sun amince fita akayi gurin ɗaurin auren aka ɗaura da Sadeeq Mustapha, abin yabawa mutane mamaki yanda al’amarin ya sauya farat ɗaya.

 

Lokacin da labarin auren yaje mana cikin gida babu wanda yafl faɗa min sai wata kawatq takirani tana tambayata waye kuma sadeeq aka ɗaura aurena da shi.

Fitowa nayi naji wasu nacewa.

“Allah ya biyashi yafitar damu kunya ai tunda ya aureta Allah sarki yayi kokari koma dan waye mutumin kirkine.”

 

Hannuwana nasaka akai na fasa ihu sosai kafin na zuɓe sumammiya, ruwa aka ɗauko ana zuba min amma ban farka ba, ɗakina aka maidani ana min fifita, har natashi da gudu na sauka agadon nafito waje falon Baffanmu ina kuka, nace.

“Baffa ka rufa min asiri karabani da wannan yaron mi zancewa kawayena kanin bayana nake aure don Allah ku sa shi ya sake ni.”

 

“Shiru yayi na kallona kafin yace.

” Amratu kiyi hakuri kuma kiyiwa mijinki biyayya shine fatana dake yaron nan ya fiddamu kunya a gaban dubannin mutane karki zama mai butulcewa Ubangiji mana.”

 

Bansan mi yake faɗa ba anan dai na zuɓe asume, akayi asibiti dani ban farka ba sai dare duk yan uwana suna zaune ganin na farka suka yo kaina daka musu tsawa nayi nace.

“Wallahi karku zo kusadani indau bazaku rabani da wancan yaron ba.”

 

Take na shiga fisge fisge ina cire robar ruwan kowa yazo kusadani duka nakai masa,  har likitan tsoron taɓani suke, shigowarshi yasa yayuna suka fita takowa yayi har inda nake ya kama hannuwana ya murɗasu sannan ya haɗini da kirjinshi ya matseni a hankali yacewa likitan.

“Zo kuyi mata dress ɗin”

 

Cikin hanzari suka shiga maida min abinda na cire sannan aka saka min alluran bacci, a hankali na shiga cewq.

“Wallahi sai ka rabu dani bana son wannan kaddararren auren naka mugu ɗan iska kacikani ni bana son ka kara taɓa ni banxa ɗan kauye.”

 

Bacci mai karfine yayi gaba dani, ban farka ba sai washi gari,

 

Ina tashi aka cire min ruwqn naje nayi alola da wnka sannan nazo na gabatar da sallolina inayi ina kuka, shigowa yayi tare da sallama shida kanina mubarak, sai hira suke nan ya durkusa ya gaida Nenne sannan ta mike mubarak zai maida ita gida.

Suna fita na ɗago idanuna nace.

“Mara zuciya kawai inka isa ɗan halak kasake ni nace inba haka sai nayi maka wulakanci a garin nan”

 

Murmushi yayi yana gyara tsayuwarsa yace.

“Haka ko?”

 

A fusace nace.

“Wallahi kanemi raina min hankali zan baka mamaki yaushe aka gama maka wanka da zaka fara tunanin aure, waton tashen balagarka ta motsa shine bari kanemi auren sa’ar yayarka ko, dubeka kai har kakai cikakken namijine a gurin”

 

Tsura min ido yayi inata zaginshi da kiranshi yaro babu abinda ke ɓata masa rai kamar kalmar yaron nan.

 

Da yagaji da rashin kunyanta zuwa yayi gabana ya tsaya, take na haɗiye bala’in da nake sakamakon make min baki da yayi aikuwa na fashe da kuka, sosai ko a jikinshi zama yayi a chair yana kallona nu kuwa tsakanina da Allah nake kuka na tare da cewa.

“Wallahi sai ka rabu dani.”

#Fiction

#Spirits

#Jinn

#Amsad……By Mai_Dambu

 

*_DA CIWO A RAYUWATA_*

 

 

 

Na

Mai_Dambu

Wattpad:Mai_Dambu

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

 

 

 

 

Page D.

 

“Wallahi sai ka sake ni dubaka yaushe ka girma da har zaka iya rike mace guda nawa kake mi zaka iya bani dame zan kiraka mijina kana karamin yaro sai tsabar jaraba tsiya wallahi sai kasake ni.”

 

Lumshe idanunshi yayi yana mai jin zafin maganata, dariyar Imran ce tasake harzuka shi ya kifa hannunshi akan fuskarshi imran yace.

“Zan baka guri ka nuna mata girmanka da irin darajarka don Allah ko sau ɗaya ne.”

 

Tsaki yayi cikin ɗaga murya yace.

“Hmm daɗin abun rufa miki asiri nayi guzama dake wacce ko abinda yan mata suke takama dashi baki dasu shine zaki takura kanki ni sabida Mahaifinki na karɓr aurenki inba haka ba ɗan 28 zai auri guzuma mai shekaru kusa da kabari 30 da ɗauri fa gaskiya na cutar da kaina”

 

Mikewa yayi yazo har dai dai fuskana yace.

“Ni budurwa yar karama nike nima wacce kirjinta ke cike da ɗanyen yan matanci, kuma wacce kofarta yake tsuke babu alamar girma sun dafar da kofar ko daɗewar shekaru, kinga nifa wacce zan shafa kirjinta nasan na ɓata mace ba wacce zan shafa kamar na shafa kirjin kadangariya ba.”

 

D’aga min gira yayi tare da kashe min idonshi ɗaya, tureshi nayi cikin ɗaga murya nace.

“D’an iska kawai mara mutunci.”

 

Shiru yayi ya zuba min ido cike da mamaki dama zan iya zaginshi.

“Ni kika zaga? Kin manta da igiyar aurenki dake kaina ok ba dmw bari na nuna miki yanda ake rashin mutunci na kuma tabbatar miki ni ɗin ɗan iskane bugun farko.”

 

Ya faɗa min,

Komawa yayi ya rufe kofar shigowa, jikina ne ya ɗauki rawa ina niman hanyar sauka a gadon gadangadan yayi kaina ihu da na fasa aikuwa ya saka hannunshi ya toshe min bakina, yana kallona sam bayi da niyyar min kome barazana ne kawai.

 

Matse ni yayi ya finciko ni daga gadon na sauko kasa, har ina bugewa, ya kalleni sama da kasa, yace.

“Nan kike zagina ashe bakin duk na bugine ki godewa Allah ni bani da ra’ayi akan mace irinki da yaƴ kinga shagali.”

 

Shiru nayi cikin wani irin tsoro wallahi duk rashin kunyar da nake masa duk a bakine dan nasan loma ɗaya zaiyi dani takare min. Amma dukda haka bai hanani gunaguni ba inda nake cewa.

“Ni dai ka rabu dani kawai dan ba zan zauna dakai ba.”

 

“Matsalarki ce ki zauna dani ko karki zauna dani amma kafin nan kije ki nemi izinin rabuwa dani a gurin Alhajinku sai idan yace na rabu dake shi knn dama nima inda wacce zan aura, yarinya karama wacce ko bata saka bra me soso ba akwai su ba karya.

 

Jan tsuka nayi na kuma ce masa.

“Ɓanxa mayen mata.”

 

Wannan karan kan bakina ya murɗe da hannunshi har sai da yaga bakina ya fashe ya kyale ni, yana murmushin mugunta.

 

Wasa wasa sai gashi da zaran na zageshi zai buge min bakina har sai yayi jini, kuma yana kallona zanta kuka wallahi ko damuwa baya yi, sai dai yayi ta murmushi, sabida ganin ina kuka kwanana uku a asibitin city aka sallame ni nayi mamakin yands suka mike wani unguwa daban ba gida ba kusan mota huɗu suka rakoni, can madina quarts, inda wani katon gida mai ɗauke da gids Estate har guda takwas muna shiga yara suka taso suna masa Oyoyo Uncle sadeeq.

 

Fitowa yayi ya shiga ɗaga yaran ɗaya bayan ɗaya, sannan ya komo cikin motar ya mika musu, wata katuwar laida sai ihu suke da godiya,

 

Su Aunty Mom da su Aunty salma suka fito a hankali nafito nima, nabi bayansu sai Hajja kakarmu da Su Safina da fatima, da wasu daga cikin yan uwanmu muka shiga gidan,

 

A raina nace wow sabida haɗuwar falon nasan kusan zaɓina ne kayan ciki but yanayi tsarin falone ba ra’ayina bane dan har da gurin ajiye books kome na gidan ya haɗu,

 

Kallon Aunty mom nayi sannan nayi mata magana kasa kasa nace .

“Aunty Mom waye ya kama mishi wannan gidan dan naga bai da arzikin kama gida irin wannan? Allah yasa ba baffa bane”

 

Wani kallon banza tayi min kafin tace.

“Ki tambayeshi mana hm baki san waye kike tare dashi ba ko, wawuya kawai kibi a hankali dai.”

 

Tura mata baki nayi sabida naji haushin maganar da tayi min,

. Haka suka gama ganin gidan sannan sukayi mana fatan alkhairi suka tafi, suna tafiya sai ga yaran gidansun shigo nan suka cika ni da surutu har ya shigo suka koma kanshi buɗe frij ɗin falon yayi ya ciro musu ice cream aikuwa suna amsa sukayi godiya suka fita a guje.

Tashi yayi ya shiga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan wanda nag mubarak ya hanasu shiga ashe ɗakinshine shiga yayi ni kuwa kamar wacce aka dasani, a gurin bansan ta inda zanfara ba,

 

 

Bayan kusan minti talatin sai gashi ya fito sanye da kananun kaya, kallona yayi alamun mamaki sai ya basar ya ce.

“Daga wanca ɗaki zuwa wanca duk nakine wanca ɗayar kuma zaki iya ajiye yar aiki.”

 

Tsaki nayi na mike nace.

“Dake kuma ance maka zaman gidanka nazoyi”

nabar masa falon zuwa ciki, ina shiga naga yanda aka narka min kaya a ciki kome na a haɗe yake, wanka na shiga nayi sannan na fito nayi sallah na saka riga da skirt na atamfa, dake rigar akwai bras cop ban saka bra ta ciki ba nafito abuna na shige kitchen.

 

Kayan abinci nagani ba kayan miya, tsaki nayi na daga indomie da bashashen kifin dake cikin kwalin da nagani,

 

Tun dana fito ban ganshi ba har dare sai gashi da nikiniki kayan danginsu kayan miya, ɗanyen namar saniya da na kaji, da wasu abubuwan bukata ya zuba min a kicin ya fito ya kalle ni, cikin sanyi murya yace.

“Don Allah taso ki ajiye kayan nan inda suka dace karsu lalace.”

 

Shekeke na kalloshi kafin na mike naje kome na kintsa inda ys dace sannan na fito daga kitchen ɗin take away na gani da Habib yohgort ɗauka nayi na shige dasu ki cin na saka a freeza nafito abuna shi kuwa yana zaune ya juye tuwon dawa miyar kuka, da manshanu sai kamshi yake kallon abinci nayi nace a raina girkin Nenne ne wannan kwaɗayayye ya amso.

 

Haka muka cigaba da rayuwa a cikin gidan ni dashi kowa harkan gabanshi yake, idan ya gaji da sayan abinci sai yazo ya dafa da kanshi ana haka ranar sai ga mubarak yazo bansan yana falon ba Sadeeq ya shiga ɗakina daga bakin kofa yashiga bugawa, haushi da ya kamani na fito nace.

“Uwar me zan maka da kake buga min kofar ɗaki, ko ance maka naxo zamane da kai toh malam tun wuri ka juya.”

 

“Kiyi hakuri abinci nake so nayi bakone” ya faɗa min cikin saukar da kai.

“Bazan girka ba kashiga ka girka muku ni ba baiwarku bace mara kunya kawai.”

 

Karasowa mubarak yayi har inda nake ya zuba min ido cikin kaɗuwa yace.

“Adda Amrah ke ce kike wannan rashin hankali idan wani ya faɗa min bazan yarda ba. Mijinki kike faɗawa maganar banza haka toh Wallahi a kunnen baffa.”

Rai aɓace ya bar gidan hararar sadeeq nayi kafin nace.

“Munafuki hankalinka ya kwanta ka shiga tsakanina da Yan uwana da iyayena.”

 

Juyawa yayi jikikshi a sanyayye nima kirjina bugawa yake cikin damuwa amna can da natuna ba lallai bane Mubarak ya faɗa sai na cigaba da tsabgata karshe sadeeq waje ya fita yaje yaci abinci da ya tashi dawowa haka ya dawo dasu fresh milk da duk kayan ciye ciye, ya zuba a frij ɗinsa na ɗaki.

 

Bayan kwana biyu kwats sai ga Nenne da wasu daga cikin yan gidanmu har ɗaki ya bini ya faɗa min amma na tsagalgale shi da masifa har suna jiyo mu.

 

Aunty Mom ce ta mike tazo ɗakin tace.

“Sadeeq jeka abinka,”

 

Fita yayi ni kuwa kirjina ya shiga bugawa tana zuwa gabana ta kwasheni da mari sannan ta finciko hannuna tafito dani falon ta rufe ni da duka, wallahi babu wanda ya amshe ni sai shi da yake saka kaya zai fita nima musu abinda zasu taɓa kafin nagama girki, da sauri ya fito yazo ya kwace ni kamar zaiyi kuka ganin yanda take kifeni da mari, yace.

“Yanxun saboda Allah wannan dukar sai kace wata karamar yarinya kika samu ayya.”

. Jana yayi ya kaini ɗakinshi dukda kukan da nake sai da nayabawa haɗuwarshi…..

🌺🌷🌷

*_DA CIWO A RAYUWATA_*

🌹🌸🌸

 

Na

Mai_Dambu

Wattpad:Mai_Dambu

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

 

Page E.

 

Ture shi nayi sannan na cigaba da kukana, hmm munafuki ko inda nake bai sake kallo ba yafita yabarni a ɗakin hakuri ya basu suma shi suka bawa hakuri  suka ce zasu tafi, har gurin motarsu ya rakasu ina hangosu ta cikin ɗakinshi juyawa nayi ina kallon ɗakin, cike da mamaki yanda ɗakin yake kome a nutse yake a ciki gadon ɗakine yayi bala’in mun kyau, kafin ya shigo nafita.

 

Yana shigowa na tsaya tare da rike kuguna cikin masifa nace. “wani munafikin ne ya kai musu gulma”

 

“Ga zahiri tunda kinyi akan idanunsu.”

Wnnar maganan da yayi ba karamin bani haushi yayi ba dan haka dayazo wuccewa ta gabana, nasa hannuna na finciko masa rigarshi har sai da ta yage, raina ya ɓaci dan haka bana jin zan iya kyaleshi.

 

Shima da yake namiji ya gaza hakuri, juyowa yayi ya rike min wuyar rigana, inda ya caccumeni har da boons ɗina, ya kama rigar sai da ya kaita kasa, dan tsananin mugunta kuwa ya riko hannuna ya murɗa min shi baya har sai da na fasa ihu,  murmushi yayi yace.

“Ke nifa bani da, damuwa dake kece kika dami kanki nan da wata biyar aurena,zanyi bani da lokacin fitinarki.”

 

Sakeni yayi ya shige ɗaki sai lokacin na kalli ɓarnan da yayi min a raina nace *munafuki ya tqɓa min nono da wayo dama abinda yake sha’awar taɓawa kenan tir yaran ynzu da rashin kamun kai*

 

Haka zamanmu ya cigaba da tafiya sam ba daɗi nina kafe sai ya sakeni ga rashin kunyar da nake masa shi kuma hidimar gabanshi ya isheshi

 

Satina biyu da aure hutana ya kare, dan haka monday inada aiki da wuri na gama kome har miya nayi nasaka afirij abincine har dai banayi dashi dan babu wanda zai min dole idan nayi bakine nake bashi dake bai saba ba, sai yace shi ba ynx zai ciba.

Haka na min dadi wallahi da mijin da nake sone da tuni yaga madaran luv.

Hmm ina ruwan madam Amrah ranar monday na shirya  tsaf yana zaune a falo yana shan tea, sai gani nafito gyale na yafa akan doguwar rigar jikina,  ko inda yake ban kalla ba na wucce manta key motana nayi na ajiye kayana na koma kafin nashiga har yasa Imran ya ɗauko masa yakawo ya ajiye masa shi kuma ya saka a gaban remoteɗin tv nagama duba ɗakina babu keybabu dalilinshi,  fitowa nayi aikuwa idanuna ya sauka akan key ɗin bansan lokacin da bala’i ya ciyoni ba nazo kanshi na tsaya, zan ɗauka key ɗin yayi baya haka key ɗin yayita matsawa har kan cinyar Sadeeq sake ina cike da masifa sam banyi alakari da abinda ke faruwa ba sai naji ni a jikin mutum ko kallona baiyi ba, ina son mikewa amma kamar an danne ni, a jikinshi ɗaga kai nayi cike da masifa na nazubawa idanunshi ido, da hanzari nayi kasa da kaina wallahi tun da nake ban taɓa ganin, kwayar idanun ɗan naija ashe colour ba sai sadeeq cikin idanun kuwa har wani diz aka musu, sai kwayar tsakiyar itace mai ɗigon baki, kamar muna fuka na ɗaga kai da niyyar sake gani haka ne dai da sauri na mike tare da jan tsaki nace.

” Dan iska.”

 

Kasa kasa sarai ya ji,ni kawai baida niyyr magane ne,

 

Daukar key ɗin nayi zan fita sai dana kai bakin kofa cikin isa da iko yace.

“Idan kika kuskura kika fita a gidan abakin…”

 

“Yo banda abinka aina jima ina son gutsere auren karasa sai nafita daga nan nayi gidanmu”

Nace masa,

 

Dariya yayi yace.

“Ai ba gidanku zaki ba aikinki zaki rasa har abada, sai kinsan yanda ake niman izinin miji idan mace zatayi abu.”

 

“Wallahi kayi karya Sadeeq aikin kan sai naje, banza malalaci mara zuciyar niman na kanshi idan… ”

 

Ban kai aya ba naji an finciko ni aka yi sama dani sai dakinshi, ban taɓa tunanin zai iya min wannan rashin mutunci ba koda ya jefani a gado fita yayi yabar ni a ɗakin. Har na awa uku kafin ya dawo ya buɗe ni sai gashi wani mugun tsoronshi ya kamani dan dole na sunkuyar da kaina.

 

Tsawa ya buga min cike da ɓacin rai yace.

” Fitan min a ɗaki kafin na sauya miki halitta.” tsabar tsoro a ɗakina nagama jin sauran maganarshi.

 

***

Kwana uku tsakani sai gashi yayi shirin tafiya, ban san inda zai je ba dan haka ban damu ba, yafito yace.

“Zanyi tafiya kwana uku zanyi kawai.”

 

Kuɗi ya ajiye min dubu talatin, cikin kunkuni nace..

“Ni me ya dame ni da tafiyarka aikina zan koma.”

 

“Allah ya baki sa’a da alamun kin kusan barin aikin knn”.

Ya faɗa min sannan yasa kai zai fita.

Aikuwa nace.

“Mugu Allah ya isa min.”

 

Bai damu ba, yayi tafiyarsa  sai zaman gidan ya isheni, haka na share wuni guda ina bacci da aiki. Har dare sannan na kuna tv na fara kallon Mbc 2 dama su ɗin mayun saka horror fim ne, dan haka idanuna yaki bacci,

 

Zama nayi da niyyar kallon wani fim me suna the ring, a hankali aka fara fim ɗin babu tsoro can da fim ɗin yayi nisa aka fara wajen tsoro tuni na kashe tv na kashe wutar falon na koma ɗakina na kwanta, baccine ya fara ɗauka na sai naji karan tv a falo tashi nayi naje na kashe na cire socket ɗin,

 

Na dawo na kwanta can har baccina yayi nisa sai naji tv nayi take tsoro ya kamani a hankali na,sauko da kafafuna nafito zuwa falon wasu irin fararen macizai nagani, a zaune a kujeran falon ina son yin addu’a amma na kasa, sai ma kasalar da ya sauko min da wani irin feelings a hankali idanuna ya shiga rufewa kamar zan zuɓe a gurin wani guguwa yayi sama dani sai ɗakina.

 

Ina jin guguwar ta rikiɗe zuwa sufar maciji mutun, a hankali yake bin jikina yana faɗin.

“Amrahtuna da yardanki aka ci amanata, mi yasa kika amince da wannan auren kinsan yanda nake sonki kuwa mi zancewa Yaranki, Amrah karki tafi kibarmu muna bukatarki a rayuwarmu kinji.”

 

Gyaɗa kai nayi masa sannu a hankali ya shiga lasar jikina da harshensa guda biyu yana bin ko ina najikina yana motsawa, ji nayi abinda yake min yafi min daɗi akan kome mika nayi yasaka hannunshi duk biyu ya rungume hakarkarina tare da saka kanshi tsakiyar kirjina,  rawan da jikina keyi yasa ya cigaba da bin jikina yana lasa, buɗe ido nake sonyi amma na gaza dan dole na maida kai na kwanta bai fasa bin jikina ba, ni ma ban daina jin haka a jikina ba sai can naji yayi wani irin Ihu dakyar idanuna ya buɗo wani farin mutum na gani da fararen kaya ya kama macijin nan ya shakeshi, wura min isa mutum yayi bacci mai nauyi yayi gaba dani.

 

Ban sake farkawa ba sai da na share kwana uku ina bacci ina farkawa da ihu nake tashi shafa min habbatul saudat da wasu haɗi ake sai na koma, bacci ina haka har nafarka ban tashi da ihu ko kuka ba, sai dai na tashi da sabon tsanar Sadeeq ne a raina, a hankali na fahimci a gida nake, gidan iyayena sosai naji daɗin haka,

 

Tashi nayi na shiga ban daki nayi wanka da alola sannan nazo nasaka kayana, sallar dake kaina na sauke tare da addu’a jin muryan sadeeq yasa jikina ya soma rawa, kafin wani lokaci fatar jikina yayi fari sol,

 

Kifawa nayi a gurin ina gurnani, yana shigowa ɗakin nayi wani irin tsalle na kai masa duka kafin na isa Imaran ya kare masa, yayi wani majjajwa dani ya makani da katifar ɗakin, take suka shiga shafa min magani.

 

Ihu na fasa wanda yayi sanadin wautsina kome na ɗakin sai da suka gama shafa min magani sannan jikina ya fara dawowa normal,

 

Baccine yasake gaba dani.

 

A bakin rafin dunduma ta xube tana ihu da birgima sauran yan uwanta suka fito daga cikin kogon ramin da suke cikin tashin hankali Zarina tace.

“Fauzan mi yasa kika je gurin Umma a wannan lokaci ko baki ji Abbu yace kar wata taje ba  ya shiga tsakanin wanca mutumin da Umma ba, kina ci da zuci”

 

” Hmm ” Fatahiyya tace kafin ta juya ranta a ɓace,

Rusaila ce tayi maza tasha gabanta cikin tashin hankali tace..

“Fatahiyya karki je kibar Abbu ya huta shima jikinshi akwai ciwo muyi hakuri Umma zata dawo garemu dukkanmu muna sonta dan haka kucire damuwar kome ai ynx babu wani shiri a tsakaninsu tunda Abbu ya zuba mata kiyayyar wancan bil adam ɗin umma zata dawo garemu.”

 

Kama fauzan sukayi suka sakata a cikin wani ruwa mai ɗauke da wasu irin jijjiyoyin da saiwowwen bishiya a ciki ta rikiɗe zuwa sufarta ta Whiter sneak.

 

Sauran kuma kogonsu suka shiga cike da ɓaccin rai…..

***

Kwana na uku kafin na warware, sai dai ina jin kewar wasu yara wanda bansan su ba, ko bacci nake sai nayi mafarkin gani da yarana har su huɗu duk mata,  nashafa kan wannan na rungume wannan ina tsaka da mafarkin, ko mahaifin yaran wani kyakyawan mijina yazo gareni, sai na farka toh idan na tashi bana sakewa wani magana a gidan sai anyi awa huɗu, ranar da abin yafi muni ne ina cikin mafarkin mun faɗa shafin ma’aurata saura kiris mu zama daya sai ji nayi ana shafa min magani a jikina ɓat na nemi mijin mafsrkina da yarana, ina buɗe ido naga sadeeq.

 

Bansan lokacin da na fashe da kuka ba, ina ture hannunshi a jikina, ya shigo ɗakin da niyyar ajiye min xuma wanda aka zuba, magani  a ciki sai ya samu ina tura kirjina tare da kamkame jikina, cikin wani irin yanayi shine ya fara shafa min magani dama malamin da yazo dubani ya faɗa masa dole yasaka ido akaina, gefe ɗaya ma abokinshi Imran yana kokarin haɗa min magugguna ina sha ina shafawa ga na wanka nidai nazama Allah sarki.

 

Satina uku akace za’a mai dani gidana aikuwa kuka nasaka musu bori,  anyi fama dani kafin na amince dan sai da Baffa ya nuna baccin ranshi na dawo gidan ynx babu tsiwa dan bana kaunar masa magana, dan ina kallonshi kaman yaso kanshi gurin rabani da farin cikina….

 

#Fiction

#Spirits

#Jinn

#Amsad……Follower Mai_Damb

🌺🌷🌷

*_DA CIWO A RAYUWATA_*

🌹🌸🌸

 

Na

Mai_Dambu

Wattpad:Mai_Dambu

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

 

*Nagode masu comments Yaseen masu min thnks ɗin nan kuwa da sticks ban gane muku ba*😛🤒🥰

 

 

Page F.

Sam shi bai damu da sauyin da yaga nayi ba sabida ba damuwarsa bace abinda yasani shine nasha magani, kwana na biyu da dawowa yasani agaba nasha magani amma naki, ko kallonshi balle yasa ran zan sha aikina nake a computer tunda ba makaranta nake zuwa ba,

Da yagaji da ganin kayan haushi mikewa yayi yazo ya murɗeni har hannunshi na gogan kirjina, ya cusa min magani na shanye sannan ya sake ni ya mika min nashafawa a jiki naki karɓa, mikewa yayi ya shiga kwaɓemin kayan jikina dama ban saka bra ba sai gani tunbur🙈 haka ya gama shafa min magani, cike da masifa nace masa.

“Mara kunya wanda bai san darajar mace ba ince dan ka kalleni ka kirkiro shafa min magani a jikina gashi ba kallo ba har taɓa min boons kanayi wanda bai san ciwon kanshi ba, wawa kawa….”

 

Wallahi wani irin mari naji saukarsaa fuskana cike da bacin rai ya matsa min boons ɗin yace.

“Dubesu fa ko cika min hannu basuyi ba har ana cewa sabida su nake kula da jinyarki mi zanyi da kananun nonuwarki wanda ko tokareni min kirji basu isa yi ba, kika kara zagi sai na yagaki gida biyu naga abinda kike takama dashi wacce bata san darajar aurenta ba.”

 

Tashi yayi ya barni ina kuka sosai fa, kuma naji haushin maganar da yafaɗa min.

 

Tun danaji mari sai nake gudun abinda zai haɗani dashi har ya mareni,

 

Kwatsam wata monday yace na fara zuwa aiki kaman zanyi ihu dan murna haka na fara zuwa aiki abokan aikina maza da mata suka shiga zuwa suna tayani murna.

 

Wasu ma yan gulma zuwa suke su ganni, ko a jikina class ɗina naje na gabatar da abinda zan musu sannan na koma office nasaka kai zan shiga naji hiran yan office ɗinmu suna cewa

“Eh ina faɗa muku wanda ya aureta yarone sosai , kuma naji ance baya sonta kawai dai cusa masa ita akayi wallahi dakyar H.O.D yasha dan aljanu take dasu saura kiris sukashe shi.”

 

Cikin tashin hankali najuya xan bar gurin kawai muka cikaro dashi yazo ɗauka na, dan jimawa zanyi a makarantar ba nuna min gurin mota yayi ba musu na wucce shiga yayi cikin officer ɗin da sallama suka gaisa, sannan ya isa table ɗina ya ɗauki kayana ya zuba a jaka, duk sunyi tsuru tsuru, dakyar wanda yake basu labarin yace.

“Malam lafiya kayan dr Amrah ne kuma ka shigo baka nemi izin kowa ba kana tattara kayan.”

 

Wani shegen murmushi yayi wanda suka karawa fuskashi haiba da zatti haɗi da kwarjini da muryanshi irinta yara yace.

“Kayan Mata ta nake ɗiba ko akwai matsala ne malam.kaji da rayuwarka karka shiga rayuwar wata yau ya zama na karshe da zanji kana maganar Mata ta idan na kama ka, next hmm zaka iya rasa inda zaka ci abinci kana masinja amma zuciyarka cike ɗa kyashi da hassada,”

 

Yana gama faɗan haka ya kwashi kayan yafito ya zuba a bayan mota, ina zaune a gaba kuka nake  kaman idanuna zasu fita taɓe baki yayi dan bai ga abin kuka ba, da zanyiwa kuka.

 

Tun daga ranar yan officer ɗinmu suka shiga hankalinsu suna ganinmu zasu nutsu yanzun ya shiga yi min hidima sosai amma a gida kuwa kaman zamu cinye juna dan masifa, wani lokacin idan ina da class 8 – 10/11-1 abinci kake kawo min,  har cikin aji ya katse min karatu yasani a gaba har cikin motarshi sai ya kunna Ac ni kuma, haka ba karamin haushi yake bani ba, dan ko kallon banza nayi masa da murmushi zai mayar min.

 

Ranar da nagaji tun amota nake masifa ya dameni sai gulmata ake kowa har son gani na ake suna cewa mijina yarone amma sai rawan kai yake akaina.

 

Ina gama fadar haka bai kalle ni ba ya cigaba da tuki, can nace.

“Nidai daga yau na yafe,”

Dariya yayi kafin nan yace.

“Allah ya baki baiwar rashin kunya da zagi amma baki iya kwatar kanki a gaban mutane ba nonsense kawai.”

 

“Nice mara hankali.” na tambayeshi a harzuke.

Murmushi yayi sannan ya ɗaga min kafaɗa alamun Eh.

 

Aikuwa na zauna nayita masifa, *A ranshi cewa yayi abinda ta iya kenan* har muka isa gida ban daina ba sai sa yaranshi suka zo nayi shiru na shige dan haushi ko girki banyi ba,

 

Washi gari da zamu fito ya kalle ni yace.

“Saura muje wata mace ta faɗa miki magana kiyi min shiru Wallahi sai na baki mamaki.”

 

Koda muka isa department ɗinmu shi ya ɗauka min kayana ina gaba yana take min baya sai magana yake faɗa min sabida kayan da nasaka. Yake nake kawai dan wani zai zata hiran luv ake nan kuwwa magana yake yaɓamin.

 

Muna shiga matan gurin suka shiga cewa.

“Eyye Dr kina sha’aninki a tukoki akawoki ɗauko kayan sai ya miki kina shagali fa.”

 

Satar kallonshi nayi naga shima kallona yake da wutsiyar ido wani kwarin gwiwa naji nasake murmushi kafin nace.

“Eh mana ba dole ba nayi sha’anina Allah ya bani mijin nunawa sa’a ga so ga kulawa, uwa uba hidima yake min kamar dan ni akayi shi, toh duk cikinku wacece ta taki sa’ar dana taka ne, abinfa rabone wai ɗan fari ya koma,”

 

Juyawa nayi gurin table ɗina sai jin bakinshi nayi a goshina ya sumbace ni sannan yace.

“Gimbiyata sarauniyata ke ɗaya kike mulkar birnin zuciyata sai nazo ɗaukarki, faɗa min wani abu mana.”

 

Duk sai na diriri ce murmushi nayi sannan nace.

“Adawo lafiya Half.”

 

Fita yayi tun daga ranar nasami nutsuwa basu sake min maganar banza ba,

 

Nafito daga class kenan na gaji bacci nake ji mata nagani cike a office ɗinmu nan na kutsa kai na shiga, ashe me kayan matace sister Fannah gaisawa mukayi cikin mutunci na nime kujera n zauna na kifa kaina tuni bacci yayi gaba dani, taɓa table ɗin Fannah tayi na farka cikin raha tace.

“Sai kiyi aure ba sanarwa toh ga kayan gyaran gado nan ko zaki ɗiba ga tsumin karya dawo gumbar saki kishiya kuka, turaren Yar gata, ga kuma bani ba kishiya , ga gida ko mota, ga zumar goran tula sa mai gida ihu kenan yashiga ya jiki kamar korama tsabar ni’ima ga daɗin harka, ga matsin gigita mai gida wannan kika saka Hq ai kuka zaki ji yallaɓai na rusawa.”

 

Tarkace gasu nan kaman hauka, dariya nayi kawai na amshi zumar goran tula ina kallonshi buɗe wani gora tayi ta zuba min wai na gwada naji hmmm karɓa nayi nasha, yayi min daɗi tamvayar kuɗin nayi tace..

“5k take sayrwa.”

 

Karɓan nomber acc ɗinta nayi na tura mata wallahi nasaya ne kawai sabida yanda abokan aikina suke ta cusa min baki amna sam ban yarda da irin maganin nan ba, haka tayi ciniki a office dinmu dan har bashi tana badawa,

 

Lokacin zuwansa nayi sai gashi yazo kayana na haɗa  sannan nayi musu sallama muka fito bayana suka kafa gulma wai da alamun Sadeeq jarababbe ne gashi yana manne dani ba mamaki nima hakan ce,

 

Tun a mota naji marana na sukana, can kaman ya kulle sai can ya sake sai naji kaman zuban abune a kasana dan haka muna isa falo na,zube akan kujera tuni jikina ya mutu dakyar na shige ɗakina nayi wanka na duba na zata circle ɗina ne sai ruwa kawai, ban ɗauka wani abu bane ina fitowa wanka nabi gado ina lumshe idanuna,

 

Wani irin ciwon mara da bayane ya rufe ni haka nayita juyu dakyar nayi sallah na kwanta,  har dare ban fito ba ganin haka sai gashi ya tawo gurina,  yana shigowa yaga halin da nake ciki take ya ruɗe ya shiga niman magani na, yana fitowa Imran yayi masa sallama, yana murmushi yace.

“Bawan Allah ba ciwonta bane, kawai kaje ku raya daren shine gaskiya dan tasha wani abune ya dameta.”

 

Kallon banza yayi masa sannan yace.

“Taɓ Allah ya tsare ni da yin aikin danasani kawai faɗa min abinda zan bata.”

“Toh ba damuwa kasami jar kanwa ka saka a ruwan ɗumi kaba tasha sai kuma.”

 

Shiru yayi ya zuba masa ido yana nazarin abinda zai faɗa masa.

“Sai me kuma?”

Ta tambayeshi, cikin inda inda yace.

“Hmm dama zaka je ne ka tamvayeta inda ke mata ciwo sai kana matsawa Insha Allah zata ji sauki.”

 

Dakinshi ya shiga yaje ya duba jarkanwa yazo ya jika sai gashi ya shigo tallafe min kai yayi ya bani nasha, sannan ya jingina ni yace min..

“Sannu ko! Ina ke miki ciwo.”

Cizon lips ɗina nayi da hakori na nuna masa marana, kaman wanda na aikeshi kawai sai jin hannunshi nayi yana matsa min gurin yana min tausar gurin katuwar ajiyar zuciya na sauke, a hankali yake murza min gurin, can bayan wani lokaci sai naji saukar abu, a jikina,  ajiyar zuciya na sauke tare da lumshe idanuna kallona yayi, sannan yace.

“Sannu ya kike jin gurin har ynx akwai ciwo ne.”..

 

Hararanshi nayi cikn borin kunya nace..

“Ka buɗe ni ka duba mana, idan ka damu.”

 

Aikuwa cike da ɗanye kai ya saka hannunshi tsakanin cinyoyina wai zai buɗe ni, ai bansan lokacin da na hantsilo ba, naga rashin kai da gaske kuma dubani zaiyi dan bai da kunya mikewa nayi naje nayi wanka na haɗa da alola nafito  sallar la’asar na gabatar lokacin yar yayi waje abinshi,

 

Bai ce min kome ba sai ranar ina shirin ɗaura nikkaf ɗina yace.

“Wallahi kika kuskura kika shawo wata damu ki nemi mi sauke miki ban da ɗangidan mustapha Lamiɗo.”

 

Shiru nayi na wucce abuna har  offices ya rakani,.

 

***

 

Watanmu uku cur da aure ina kwance sai gashi ya shigi zama akan stool yace.

“Zanyi baki Kanen Mamana da kanen Babana sai matar kawuna wacce zan auri yarta nan da wata biyu zuwa Uku, ina bukatar a mutuntasu ai ashe na manta da matar karfe kakata wacce ta haifi  Mamana Hajiyata Innawuro.”

 

Shiru nayi na kyaleshi, kwana uku tsakani yasani na kwashe komi nawa nakai dakinshi rana na huɗu sai gasu nan, sun iso ranar tare muka wuni a kicin sai karfe huɗu muka fito amma munyi faɗa yafi sau goma har aka gama girkin.

Close Menu