Ad Code

Bita Da Kulli Hausa Novel Complete

Bita Da Kulli Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

BITA DA KULLI

 

*NA*

 

*HASSANA Y.IYAYI*

 

*MAMAN NOOR*

 

 

 

 

 

 

 

1

Misalin karfe 6:30 na safiyar litinin ya gama shirin tafiya kasuwa kasancewarsa irin mutanan nan abota sammako wani lokacin ma acan yake samun koko da kosai yayi kalacin safe. Har ya kai tsakiyar zauren nan yayi tozali da katon kwalli an dan bude bakinsa kadan, mamaki ya cika shi, tun yaushe kwallin yake a gurin, iya saninsa lokacin da ya fita sallar asubahi bai ga komai ba, cikin mutuwar jiki hadi da tsoro wanda lokaci guda sukayi masa dirar mikiya yake ayyanwa a rainsa kar dai wani mugun abun aka kunso aka ajiye masa a hankali ya motsa bakinsa da miyan bakin ya kafe tsoronsa Allah tsoronsa *bita da kullin*

mutanan unguwar a hankali ya furta.

Inda Rai Hausa Novel Complete

” Innallilahi ! me idona yake gani na shiga uku ” kirjinsa yayi nauyi hadi da wani irin lugude tamkar an daka da tabare da hanzari ya karasa gurin babu inda baya rawa a jikinsa tsoro mai tsanani ya kama shi tamkar ya bude kwalli nan yayi ta maza ya ja da baya murja ido yayi hadi da karasawa gaban kwallin,babu ko tantama biyo shi akayi bayan ya dawo salla aka ajiye bai rufe kofar ba saya kofar yayi ya wuce ka sa kunne yayi, ai kuwa ya fara jin kukan jariri na tashi kasa_kasa ga dukan alamu ya dade ya na kukan har muryansa ta dan dakushe dafe kirjinsa yayi tamkar kafarsa bazata iya daukarsa ba ya jingina da bangon zaure yana fadin.

 

” Na shiga uku na lalace ni Mansur me zan gani da asubahin nan jariri wallahi jariri ne kai jama’a” dan matsawa yayi a rude kusa da inda kwalli yake nan a ya she, ya kara bude idon dan dai ya tabbatar ba gizo idonsa ke yi ba cikin hanzari hadi jan kafa ya koma baya, cike da tashin hankali ko ganin gabansa ba yayi ya kada baki ya shiga kiran Ramma dake kwarya daki kwance tana bacci kira

 

“Ramma!Ramma yi da jiki dan Allah ki tashi daga wannan baccin asarar da ya zame miki jiki, da jijjiya ki fito masifa ta same mu zo ki ta ya ni gani masifa da asubahin fari fito mana Ramma ”

 

A sukwane Rahmatu ta fito ta saki hamma hadi da murza ido ga dukan alamu baccin bai isheta ba dan ga yawun bacci nan da shatti tabarma rudu -rudu a gefen fuskarta, cikin muryan wanda ya tashi a bacci take fadin.

 

“Allah ya raba mu da masifa malam me ya faru ne duk ka rude haka yi min bayani da manyan baki in tsaka da mafarkin an kawo min zakkar yan dubu -dubu ka ka tse min wannan daddan bacci”

 

 

Cikin sarkewar murya hadi da inda-inda ya fara magana

 

” Dan Allah kiyi min shiru ana ga yaki kina ga kura ba ki da zance sai na maganar da bata da amfani kudi dai kudai kamar kiyi sata mu je zaure ki gani lallai mutanan unguwar nan har yanzu sunan da mugun nufin su akan mu basu daina bin mu da Bita da kulli ba …” kafin ya kai ga rufe baki kukan jaririn har tsakar gidan dafe kirji Ramma tayi ta kankace ido ta ce

 

” A’a dakata min kamar kukan jariri kune na ke jiyo min ko dai jin kunne ne? ya illahi malam! ‘yar wa ka haikewa ni Ramma! wannan abi kunya da yawa yake na banu na lalace ” cike da tsoro hadi da far gaba Malam Mansur ya ce

 

“Shiga hankalinki ma na haba Ramma ! ni kike jifa da wannan mummunar kalmar, wallahi tallahi kin ji rantsuwar dan musulumi yanzu nan fitar da zanyi na ci karo da kwallin kar ki sa jama’a su dauka da gaske ne kiyi kasa da murya dan Allah “. Takamar wanda aka tankada a haukace tayi zauren daurin zani na ballewa jikinta har tsuma yake.

 

Hannu na rawa ta bude kwallin yayin da idon ya fada kan jaririyar da ke kwance tana canyara kuka yarinya kyakyawar gaske an shiryata cikin tsadaddun kayan jarirai masu taushi kasa dauke ido ta yi daga kanta lokaci guda kaunar jaririyar ta tsirga mata har rainta.

 

 

 

Cikin kidima ta dora hannu aka ta shiga kururuwa.

 

 

“Wayyo Allah mun bani mun lala ce! ke duniya ina zaki damu dauki jama’a an ajiye ma na jaririya a tsaure wannan masifa har ina wacce bakar dagar ce ta haife cikin shege ta zo ta ajiye mana a soro ”

 

Kafin ka ce meye wannan kofar gidan Malam Mansur ya dinke da jama’a tuni masu recording suka shiga dauka ana salati dan yanzu kiris ake jira a samu na watsa a social media

 

” Duniya ina zaki da mu tubarkallah! ku kalli jaririyar nan jawur da ita san kuwa kin wanda ya rasa yanzu uwar ‘yar nan bata ji kunyar goyon cikin ba, sai kunyar raino kai wannan rayuwa Allah ya saka miki duniya gidan banza inda ranka ka sha kallo muna jin wai-wai a gari ga shi ya ishe mu har cikin unguwa”

 

Mutane kowa sai tofa albarkar cin bakinsa yake nan masu watsawa a media kuma suka shiga yadawa harda karin kanzan kurege wasu ma cewa suke a buhu aka kulle jaririya ko yanke mata cibi ba’ayi ba kamar jira ake mutane suka shiga ruwan comments.

 

“Yanzu dai gidan mai unguwa ya kamata mu fara kai yarinyar nan sannan mu wuce gurin yan sanda ko? “Malam Mansur ya fada yana dauke kwallin da aka sanya jaririyar a ciki kallon kasan kwalli yayi nan idonsa ya fada kan wata farar takarda dake shinfide a kasan kwallin …….

BITA DA KULLI

 

*NA*

 

*HASSANA Y.IYAYI*

*MAMAN NOOR*

 

 

 

 

 

2

 

Hankulan jama’ar gurin baki daya yayi kan takarda da hanzari Malam Mansur ya kai hannu ya dauka hadi da warware ta ya fara karantawa kamar haka:

 

Alamun hawaye ya fara cin karo da su.

 

 

Na rubuta wannan takarda ne ina mai cike da bakin cikin rabowa da gudan jinina! saidai hakan shine mafita a gare ni, tabbas Halima ba shegiya bace da ubanta!sarkakkiyar da ta sarke rayuwarmu.tasa dole na ajiye ta akwai tarkonan dake farautar rayuwarta a halin yanzu dan Allah ku kular min da Halima ! yayin da alamon hawaye suka cigaba har i zuwa karshen takardar.

 

“mtsss aiki banza in ba shegiya ba ce to wacece ita ki din? ki barta a hannunki ku sha wahalar gami da azabar da zaku sha tare da ita ma na ka ji min zance banza zance wofi ji wani ihu bayan hari in ce babu rami ba abinda yake kawo da ramin malam Mansur mu je dan Allah ” cikin sanyin jikin Malam Mansur ya tura kafa rungume da Halima har izuwa ofishin yan sanda an shigar da bayanan kowa sannan Ramma ta roki alfarmar abar mata rikon jaririyar har lokaci da uwarta zata waiwaye su, cikin kankanin lokaci Allah ya zuba mata tsantsan kaunarta. Babu wani jin kiri su cike takardu aka mikawa mata ita, cikin dan lokaci ta nemo kaikayi tayi wanka ta dama kunun kanwa ruwan nono yazo ta ci ga da sharyar da Halima wanda tafara tashi a sake uwa babu kwaba kaka ba harara

 

 

Bayan Halima ta fara tasawa sai Allah ya zuba mata shegen rashin jin magana tamkar wadda aljannu suka shafa, dukda da farko -farko ta taso shiru-shiru rana tsaka halayayyar ta fara canzawa da Halimarta zuwa sabuwar Halima.

 

 

 

Sanin bala i Ramma ya sanya mutan unguwar suka shafa mata lafiya babu damar yaro ya fita wasa Halima zata sanya hannu ta kwade shi ko a aiki yaro da kudi haka zata tare shi ta kwace ta koro maka shi ta ce uwarsa ko ubansa su zo su ansa in sun isa haka dai suke zaune dasu babu dadi dama-damar wajen Malam Mansur shine mai tsawartarwa gami da ban baki ga wanda tsautsayin tsokar ya hada da shi in kuma ta kama ya jibgeta yana dukan Ramma na matsifa da balbalin balai.

 

Malam Bala makocin Malam Mansur ne ga gida ga gida Halima ta raina gidan kasancewar gidan zagaye yake da langa -langa babu fargaba zata d’are katangar ta rika leka masu bandaki ta na dariya cikin wannan yanayin ne wani lokaci Malam Bala yana tsaka da gurje fuskarsa da soso ta leka shi tsugunawa tayi ta tsinci duwatsu ta jifa ma sa, ta sunkuya sau uku tana jifa masa duntsen tana dukawa hadi da kwashewa da dariya irin ta ifirtai.

 

Jikinsa ya dauki rawa dan ga zatonsa ko cikin irin aljanu da yake aiki dasu ne yayi masu ba daidai ba suke masa hukunci yana dagowa suka yi kallon kuda da Halima wadda ta tsare shi da manyan idannuwata tamkar mayya. Salati m. Bala ya saki rainsa in yayi dubu ya baci ba karamin munzanta yayi ba yarinya sa’ar jikansa na karewa tsaraicinsa kallo, da sauri ya wulga mata warin takalminsa ta dire tana masa dakuwa hannu biyu.

 

Da hanzari ya zira rigarsa ya nufi gidan Ramma ko iya ganin gabansa ba yayi domin ko matarsa ya tsani ta ga tsaraicinsa bale wata shegiya daban, kai wannan abu yayi muni domin yasan Halima ta tabo tsuliyar dodo, babu shamki ya fada gidan Ramma.

 

” Gafara dai Ramma! na ratse kotu ce zata rabani da mitsiyaciyar yarinyar nan, shegiya ni zata leka ina wanka ”

 

” Halima dake bayan Ramma ta kyabe baki ta ce ” karya yake ni ban leka shi ba, a hanya na hango shi ya tsuguna yana bayan gari shine yace na leka shi” salati malam Bala ya saki hadi da tafa hannu yana kallo Ramma dake jiffansa da matsiyacin kallo ta dago hadi da turo kallabin gaban goshi ta nuna shi da ya tsa ta ce.

 

” An ji jikin Bala na ce an ji jiki yanzu dan Allah baka ji kunya ba, da rana gatsau kake bayan gari a bainar nasi! ai wallahi Halima da kin sani ruwan duwarwatsu kika yiwa almuri kana ji na Bala kake kowa Lado? Alkur an hawainiyarka ta kiyayi ramar Halima ba kotu ba, ka kaita gaba da kotu na ce mutumin banza kawai, Ubangiji ma yace ku guji gurare uku da suke jawo tsinuwa wannan da suke biyan butakarsu akan hanya ko inuwar da mutane suke hutawa to kai yanzu kana daya daga cikinsu tunda har ka kwance zariyar wando kana bayan gari a hanyar da mutane suke wucewa meye laifin Halima dan tayi maka raddi laifi ta yi ko kuwa….” Baki sake M. Bala ke duban Ramma da bacin rai yayi kwafa ya ce.

” Haka ki ka ce, Ramma! babu komai duniya ce zaki ga ni mu zuba ni daku aga wanda zai fado shegiyar yarinya laanana mara tartibin asali ” ya ja kafa da kunan rai ya fice.

” To fa ka ce dama Bala da biyu ka to mu zuba din kurwarmu kur ”

yana fita Ramma ta haw Sababbi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba akan me yan unguwa za su dinga bin diyarta da bita da kwalli duk wanda ta kara gani yana ba daidai ba to da cewarta ce ta gyara masa zama kowa ye shi.

 

To ban garen malam Bala yana fita cikin bakin cikin maganganun da Ramma ta jefe shi da shi da mugun kulli a zuciyarsa ya shige dan luko da yake yawan zama hannu ya daga sama ya sauke fuska Halima ta bayyana ya sakin wani dan guntin murmushin mugunta kwan jimina ya dako ya zana taswirar Halima a jiki a hankali ya sanya kwai acikin wata ragaya ya rataye ya babbake da dariya a ranar ya tattara komatsensa suka tashi daga gidan …….

Close Menu