Ad Code

Matan Ramadan Hausa Novel Complete

Matan Ramadan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

MATAN RAMADAN

 

 

DAGA ALƘALAMIN

 

*FATIMA ABDULLAHI SHADAI*

 

*( ZAHRA T.FRESH)*

 

 

 

 

*DASHEN ALLAH WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

 

 

*INA ROƘON ALLAH WANDA YA BANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI,YASA NA KAMMALA SHI A SA’AH. YA ALLAH INA ROƘONKA WANNAN LABARI YAJE WAJEN WAÆŠANDA AKE SO SU AMFANA DA SHI, DON SU GYARA*

 

 

 

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

 

*PAGE 1&2*

 

*Ranar farko*

 

 

Zaune yake a tsakar gidan yaci uban tagumi da hannayensa duka biyu, Ruƙayya ce ta fito daga cikin ɗaki tana dubansa ta ce

 

 

* Ba zama zaka yi ba fa, ta shi zaka yi kaje ka nemo abinda zamu ci dana sahur amma na rantse bazan yi sahur da tuwon dawa ba”

 

 

ÆŠago jajayen idanuwansa ya yi yana dubanta cike da takaici yake ce wa

 

 

Binta kiji tsoron Ubangijin ki, yanzu tuwon dawan kike ce wa bazaka yi sahur da shi ba?

 

Kisani mu Allah ya rufa mana asiri tunda har muna da abinda zamu yi sahur É—in da shi, amma wasu fa sai dai su sha ruwa kawai suyi haÆ™uri kuma su É—auki azumi; amma ke gaba É—aya kinÆ™i godewa Allah”.

 

Banbanci Tsakanin Matsi da Cikowa

Wani dogon tsaki ta ja sanan ta ce

 

 

Kai ya dama amma wallahi bazanyi sahur da tuwon dawa ba, ko sata ce ka je ka yi ka kawo mana abinda zamu yi sahur da shi”.

 

Ganin Binta tana ƙara ɓata masa raine yasa shi fita ya bar mata gidan tana ta faman mita ita kaɗai acikin gidan.

 

 

*****. ******

 

“Zuhriyya tun É—azu kin barni a zaune ina faman jiranki, ki zo ki faÉ—amin me kike buÆ™ata asiyo…

 

 

Fitowa daga cikin kitchen Zuhriyya ta yi tana ce wa

 

” Yi haÆ™uri mana yallaÉ“ai naje na Æ™ara duba store ne naga abinda muke da shi da kuma abinda za’a Æ™aro da wanda kuma yaÆ™are sai an siyo”………….. MiÆ™a masa takaddar hannunta ta yi tana ce wa duk abinda ake buÆ™ata na rubuta shi a cikin takaddarnan”.

 

 

 

Karɓa ya yi yana murmushi ya fice daga cikin gidan.

 

Zama ta yi akan kujera tana murmushi tana tunanin kala – kalan girke – girkenda zata gwangwaje mai gidanta da su… MiÆ™ewa ta yi sakamakon duba agogo da ta yi inda taga Æ™arfe 5:00pm , inda ta tuna yau suka ce zasu fara koyar da girki, dan asamu na yi wa maigida na sahur ….

 

 

*(ZAHRA T.FRESH)*

[23/03, 10:54 pm] +234 704 626 3141: *MATAN RAMADAN*

 

 

DAGA ALƘALAMIN

 

 

*FATIMA ABDULLAHI SHADAI*

 

 

*( ZAHRA T.FRESH)*

 

 

*DASHEN ALLAH WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

*PAGE:- 3&4*

 

 

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

*RANAR FARKO*

 

 

 

Tunda sahabi ya fice daga cikin gidansa, ya samu inuwar bishiyar darbejiya ya zauna zuciyarsa tana yi masa Æ™una, “yanzu dame zanji rashin kuÉ—i da nake fama da shi ko kuwa da Bala’in Binta, girgiza kansa ya shiga yana tunanin inda shima yana da arziÆ™i da ya gwangwaje gidansa da kayan abinci kala – kala.

Amma yanzu da yake da rufi asiri mai sai ya yi da iya abinda Allah ya hore masa kawai…….,

 

 

Jifa – jifa take jan tsaki tana mitar ce wa

 

 

” Na gaji da wannan rayuwar wallahi, mune muka kawo talauci duniya,

 

 

yanzu azuminnan sai dai na dinga jiyo Æ™amshi daga maÆ™ota ina haÉ—iyar wayu, amma agidana sai dai warin miyar kuka, wallahi bazai iyu ba yadda kowacce mace zata ci abinda take so a watannan nima haka dole na girka abinda nake so, ga shi a fara koyar da girki ta online sai dai na zama abar kallo kawai acikin group – group É—inda nake dasu”

 

 

wani irin tsaki ta ƙara ja, sanan ta miƙe dan ɗauko dawar da sahabi ya ajiye mata..

 

****. ****

 

 

 

Alarm É—in wayar sa ne ya fara kaÉ—awa,a hankali ya buÉ—e idanuwansa yana duba lokaci tashin Binta ya yi yana ce wa

 

 

” Binta tashi lokacin sahur ya yi, tsaki Binta taja sannan ta miÆ™e da kwanciyar da ta yi duban Sahabi ta yi tana ce wa

 

 

” Da ka tashe ni to faÉ—a min dame zamu yi sahur to?”

 

 

 

Mamaki ne ya kama sahibi dubanta ya yi ya ce ” bana kawo dawa ba?”

 

 

 

Wani irin kallo ta jefe shi da shi sannan ta miƙe tana mita, tana fita tsakar gida taji wani daddaɗan ƙamshi ya daki hancinta, wani mayen yawu ta haɗiye afili take ce wa

 

” Dama ni ce mai mutum zai yi da auran talaka idan ba masifa ba”. Tana shaÆ™ar da warwararta taga haÉ—a wuta ta É—ora É—umaman tuwon, amma Æ™amshinnan yaÆ™i barin hancinta.

 

 

 

Miƙewa ta yi ta ɗauki kwano, tasa mayafi ta nufi hanyar waje, da sauri sahabi yaje ya tare ƙoƙarin gidan ya dubeta yana ce wa

 

” Me kike so ki yi ne Binta?”

 

 

 

Tsaki Binta taja sannan ta ce ” zan je na samo abinda zanci ne, baka ji Æ™amari yana tashi a gidan masu hannu da shuni ba?”

 

 

 

Girgiza kansa Sahabi ya yi yana ce wa kiji tsoron Ubangijin ki Binta kada ki manta a watan azumi da muke bazaki yi wa mijinki biyayya ba awannan watan mai albarka ba, kisani komai kika yi awatannan ninka miki shi za’ayi walau na lada walau na zunubi”

 

 

 

Tsaki taja tace ” na ji to ka yi min shiru kuma ka bani hanya, kiyi haÆ™uri Binta yanzu mu yi sahur da abinda muke da shi, idan lokacin shan ruwa ya yi zaki yi mamakin kayansa zan siyo mana da kuma kalar girkin da zaki yi mana kinji”.

 

*( ZAHRA T. FRESH)*

[25/03, 11:01 am] +234 704 626 3141: *MATAN RAMADAN*

 

 

*PAGE:- 5&6*

 

 

DAGA ALƘALAMIN

 

 

*FATIMA ABDULLAHI SHADAI*

 

*( ZAHRA T. FRESH)*

 

 

*DASHEN ALLAH WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

*TAKUN FARKO*

 

Shiru ta yi na ɗan wani ta ƙaitatcen lokaci kafin ta ce

 

 

” Shi ke nan zan iya haÆ™ura, amma iya yau dan bazai iyu na dinga jiyo tashin Æ™amshi a gidajen maÆ™ota ba “.

 

 

Shi dai sahabi hamdala ya yi acikin zuciyarsa yana godiya ga Allah da Binta ta yi saurin saukowa haka, Æ™arÉ“ar kwanan hannunta ya yi, sannan ya kamo hannunta suka shigo cikin gidan, gudun rigimar ta ne yasa Sahabi zama ya Æ™arasa É—umaman tuwon da kansa ya zubo ya kawo mata…

 

 

Duk loma É—aya sai ta yi tsaki, wani lokacin sai ta yarfa hannu tana haÉ—awa da mita.

 

Shi dai Sahabi ido ya zuba mata yana mamaki sabon halinda ta É—auka take yin sa, “ko haka matan suke idan azumin ya zo ?” Tambayar da yake yi wa kansa kenan wacce ba shi da amsar ta kuma babu mai amsa masa akusa….

 

 

Bayan sun gama sahur ɗin ne Sahabi ya miƙe yaje ya ɗauro alwala, duban Binta ya yi ya ce

 

” Ki tashi kije kiyi alwala kizo muyi nafula kafin akira sallah kuma”

 

“Nafull me ? Haba Sahabi ka barni kawai zanyi wacce ta wajabta akaina amma nafila ba yanzu ba kuwa”

 

 

Ido Sahabi ya zaro yana dubanta ya ce “Binta kina da hankali kuwa? Idan baki tashi tsaye ba kina yi mana addu’ar Allah ya yanke mana wannan halinda muke ciki ba to sai yaushe, kada fa ki mance da watan azumi wata ne mai falalar gaske kuma watane da ake amsar addu’armu cikin sauri kuma fa kada ki………

 

 

“Dakata Sahabi me kake nufi da ni jahila ce kenan bansan abinda nake yi ba ko me? ”

 

ÆŠorawa ta yi da ce wa ” kaima kasan ina da ilimi dai – dai gwargwado, dan haka kaje ka yi sallarka ni kwanciya zanyi dan inajin bacci sosai ma kuwa”

 

 

Mamakin ta ne ya hanashi yi mata magana inda afili yake ce wa “Allah ya kyauta ya ganar da ke Binta “.

 

 

****. *****

 

 

Tunda ta zauna ba’abinda take yi sai faman chatting inda wani lokacin take duba group na girke – girke tana faman haÉ—iyar yawu tana ce wa

 

” Kai duniya gidan daÉ—i wani girkin idan ka ganshi sai ka rantse ba abincin mutane ba ne gaskiya dole a dama dani wannan shekarar sai naci irin abincin masu kuÉ—innan, shiyasa lokacin azumi sai ka gansu kamar ba azumin suke yi ba”..

 

Nan ta ci gaba da duba tarin saƙonnin da suke shigowa ta group ɗin.

 

 

*09070918434*

*MY WHATSAPP NUMBER*

 

*GA MASU SON BADA SHAWARA, KO ƘARIN HASKE, KO KUMA GYARA*

 

*( ZAHRA T. FRESH)*

Close Menu