Ad Code

Yaushe Matar da ta Haihu ya kamata ta fara Kusantar Mijinta?


 Daga Maigari Abdulrahman


Wata likita kuma kwarrarra a fannin sha’anin lafiyar mata da ungozoma da ke aiki babbar asibiin Ebute, ta yi bayani tare da bayyana dacewar hutun saduwa ga mace har zuwa akalla tsawon mako 6 bayan haihuwa.

Ta bayyana cewar wahalhalun haihuwa tare da yanayin haihuwa da su ka hada da zafin haihuwa, dinkewar aiki, karancin karfi da kuzarin jiki, tiyata (wasu lokuttan) da kuma karancin shaáwar saduwa daga bangaren mata na daga cikin abubuwan da ke sanya bukatar jinkirta saduwa har sai bayan mako 6 din.

‘’Yayin da aka samu tsaguwa a gaban mace yayin haihuwa, to wannan tana bukatar hutu mai tsawo domin warkewa kafin ta koma kwanciya, ba ma iya mako 6 kadai ba; ya danganta,’’ in ji ta.

Likitar ta yi gargadi da cewar, ci gaba da saduwa kasa ga mako 6 bayan haihuwa, musamman ga macen da aka yi wa aiki yayin haihuwar, kan iya janyo kamu da da cutar yoyon fitsari.

“Mahifiya na bukatar hutu domin warkewa daga zafi da radadin haihuwa na dan wani lokaci kafin komawa cigaba da saduwa.” in ji ta
Likitar ta kara da cewar, mace na bukatar ya zama ta dawo da karfinta da kuzarinta daidai kafin ta koma saduwa da mijinta.
“Mafiya yawan lokutta mukan ce mako 6, amman shawarar mu a kullum ita ce, a jinkirta komama saduwa har sai karfin matar da kuzarinta sun dawo daidai har ma da sha’awarta kuma”.

Ta ci gaba da cewa, “wasu matan su kan warke da wuri fiye da wasu, to kuma ba abinda za a iya tilastawa ba ne ko a kara masa sauri ba. Kawai dai idan sun warke shikenan, idan kuma da saura to sai a jira har sai sun kammala warkewar.”

A bayanin ta, likitar ta yi nuni da cewar, dalilin da ke sa wani lokacin mata kan ji tsoro ko dari-darin komawa kusantar miji bayan haihuwa, har da tunanin abinda su ka fuskanta yayin haihuwar.

Amman zuwa mako 6 bayan haihuwa, zai zama ta samu cikakkar lafiya da ake bukata tare da dinkewar fata idan ma an fasa ta kafin haihuwar. To sai dai, ta yi nuni da cewar, akwai banbancin halitta a tsakanin mutane.

Komawa jimaíi kafin lokacin ba tare da matar ta samu cikakkar lafiya ba kan iya jefa matar cikin wani ciwo ko kamuwa da cutar yoyon fitsari ko wata cutar daban, in ji ta.

“Idan ko hakan ta faru, to matar za ta koma zuwa asibiti lokaci bayan lokaci, hakan na nufin za ta iya dadewa ba a sallameta ba lokacin da ya kamata.
Likitar ta kammala da cewa, “Amman madamar matar ta warke tare da samun cikakkar lafiya, to za ta iya ci gaba da kusantar mijinta.”

Wasu masanan ma, sun yi nuni kan muhimmancin hutun bayan haihuwa na akalla mako 4 zuwa 6, akalla. Inda su ka yi bayanin yiyuwar kamuwa da cuta bayan haihuwa yayin saduwa a makonnin biyu na farko, haihuwar ta kasance an yi tiyata ne ko akasin haka, ko ma ya haihuwar ta kasance dai, akwai bukatar hutun, a bayanin su.
Close Menu