Ad Code

Kwana 24 Hausa Novels Complete


 *1*


25 GA WATAN DAYA .


Da misalin karfe shida na yamma , hadadden jirgin nan wato KATAR AIR LINE ya sauka da jigajigan masu kudi na kasashen daban daban a filin jirgin sama na croatia.


Croatia kasa ce wadda mu a nan sai mu rantse muce babu talaka ko daya a cikinta saboda kyawun garin, ko’ina ya kawata. Ga kuma farar fatar ‘yan kasar na sake haskaka garin. A gaskiya Croatia bata cika samun baki bakar fata ba, don da yawan masu kudin mu basu waye da xuwa wannan kasa ba, ko don shakatawa ko don kasuwanci, sunfi xuwa London, America, dubai, da kuma uwa uwa Saudi Arbia, saboda Croatia tana da nisa ainun daga Nigeria don ko ‘yan Nigeria  da suka iso cikin jirgin nan suma ta America suka bi sannan suka iso wannan kyakkyawar kasa mai dumbin arxiki.


 Ma’aikata nata kai kawo bayan saukar jirgin don ganin an bude matafiyan dake ciki sun fito kowa ya kama gabansa. Ana ta saukowa daga jirgi har yanxu dai babu bakar fata duk sai turawa majiya kudi da mulki su matansu da ‘ya’yansu. Wadanda sukaxo taryen su sunata murna suna rungumarsu kamar yadda suka saba gaisuwarsu. Atika sadam, mannira bala da axixa adam abdulfatah sune suka fara sako kai suka sauko daga jirgin, bayan sun sauko ma’aikatan da suka dauko musu kayayyakin su suka bisu har xuwa wajen wata dalleliyar mota baka mai walkiya kamar yau ta fito daga kamfanin da aka kerata. Da wasu turawa guda biyu bakar fata guda daya yana rike da wata katuwar takarda wadda aka rubuta welcome to Croatia Axixa, Mannira, Atika yana ta dagawa, ma’ana bai sansuba shima , amma idan suka ga sunayen su sun san su aka xo tarya don haka da suka ga sunayen su sai suka doshi wajen da suke. Suna xuwa Mr Johnson ya tare su da murna da fara’a, y mika musu hannu sannan cikin harshen turanci yace “sannun ku da xuwa” atika saddam ce a gaba, da ita suka fara gaisawa sannan ta mikwa dayan baturen hannu mai suna Mr brown sannan ta matsa kusa da wannan bakar fata dake tsaye a gefe mai suna Ashraf, da alama mai aikin su ne ko kuma direban su, ta mika masa hannu shima ya mika mata gami da yi mata murmushi. Haka itama mannira ta mikawa kowa hannu suka gaisa, amma ta karshensu wato axixa da mr Johnson ya mika mata hannu sai ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe tayi tsaki, sannan cikin harshen turanci tace “banxo Croatia ba don in gaisa da mutanen ta, don haka a rabu da ni.” Ta sake jan wani dogon tsaki sannan ta wuce ta nufi cikin mota. Su duka suka bita da kallo tana tafe.


 Atika tayi murmushi tace “kuyi hakuri haka halinta yake masifaffiya ce” mr Johnson yayi murmushi yace “babu komai ai kyakkyawa ce don tayi haka babu laifi. Su duka suka sheke da dariya mannira tace “haba ku turawa farar fata ya xa’ayi kuce da bakar fata mai kyau? ” 

mr johnson ya sake tuntsirewa da dariya yace “baku san akwai kyawawan bakar fatan da suka fimu farar fatar kyau ba, ai axixa irin wannan kalar ce da take tsada a nan wato chocolate colour kuma ga kyau ga kudi ai dole ta jawa maxa aji.” Suna ta dariya dai Ashraf ya bude but ya xuba akwatinansu a ciki.


 Mr Johnson yace da Ashraf ya je ya tuka daya motar su tafi a ciki shi da mr brown, shi kuma xai tuka su a wannan. Bayan kowa ya shiga, suka ja suka nufi wani kataferen hotel da yake bakin ruwa.


 Allahu Akbar, Allah mai yadda Ya so, Ya axurta wanda Ya so Ya tabuka wanda Ya so, yanxu tun suna America suka bugo waya suka shaida musu ga sunan xuwa rana kaxa karfe kaxa suna son kaxa da kaxa. Shine kafin su karaso an tanadar musu komai hatta irin motar da suke so su ringa hawa a kasar itama saida aka tambaye su aka kuma tanadar musu. Daga Croatia ma ba xasu tsaya a nan ba, sati daya xasu yi kafin jirgin ruwa ya xo ya wuce dasu kasashe daban daban ta hanyar jirgin ruwa. Su yi ta xagaya duniya kamar Atlanta, Malaysia , Italy da dai duk sauran kasashe masu manyan tekuna. ‘yan hutu kenan su axixa babu abinda suka xo yi sai hutu kawai har na tsawon wata uku xasu yi, don a America ma satin su biyu sannan suka yo nan.


 Nan da kwana uku ma suke sa ran xuwan su Mubarak, Ibrahim da sadik wato samarinsu don su kara jin dadin hutu sosai. Suma wata ‘yar matsala ct a tsayar dasu shi yasa basu taho tare ba. Mubarak shi ne masoyin axixa, soyayya ce mai tsanani kuwa. Ibrahim shi kuma na mannira, sadik kuma na atika saddam. Wai! Wai!! Wai!!! Babban goro sai magogin karfe, yanxu dukkan wadannan samari da ‘yan dukkan ‘ya’yan jigajigan kasar nan tamu ce ko wannensu dan wani multi miloniya ne mai ji da kansa, don haka ma dan talaka ko ‘yar talaka basu kawo kansu ba ma don yin soyayya da daya daga cikinsu. Yasu-yasu ne don haka sai su yi yadda suka so yi da dollar ko pounds.


 Mubarak , ibarahim da kuma sadik su duka abokan junane don makarantarsu daya tun suna sakandire, suka yi sakandire a togo, suka yi jami’a kuma a America, shekaru uku da suka wuce, gama. Su kuma matan London Axixa tayi firamare da sakandire su atika a lagos suka yi firamare da sakandire suka hadu har axixa suka tafi jami’a London ta man chester, a nan suka gama don yanxu ma hutun nan da suke yawan yin a gama makaranta ne, basu fi wata daya ba ma da karewa. Haka kuma iyayensu ma abokan juna ne musammam mahaifin axixa da Mubarak abokaine na kuttan. Don su ne masu jiran gado lokacin gwamnatin wannan ta karasa lokacin ta saura shekara daya a yi sabon xabe, baban axixa ne ya tsaya takarar shugaban kasa, wato Alhaji Ahmad Abdul Fati, baban Mubarak kuma a mtsayin mataimakin sa shi kuma alhaji isa el yakub. Don haka Nigeria ta kusa xama tasu koma ince ta su ce. Ga kuma ‘yar dan takarar shugaban kasa mai jiran gado dadan mataimakin sa masoyan juna ne, wadanda suke shirin aure da xarar an gama hada-hadar siyasa. Da alama alhaji ahmed abdul fati xai cinye wannan xabe saboda yadda talakawa suke kaunarsa musaulmai da kiristoci, hausawa da yarbawa, ibo duk dai suna sonsa kasancewar sa mutum mai mutunci da rikon addini, mai tausayin talakawa ga amana.


 Su kuma sauran abokan nasu wato alhaji saddam mahaifin atika da alhaji bala dasu alhaji adamu wato mahaifin sadik duk dai suna mara musu baya suna tayasu shige da fice na ganin an cimma buri an ci wannan xaben domin in alhaji ahmad abdul fati da alhaji isah el-yakub suka samu kamar sun samu ne. sun san ko ba komai sai an duba mukamin kusa da shugaban kasa wajen ci sannan a basu.


 Washe garin da Croatia suka xo da sassafe axixa da kawayenta suna kan keken motsa jini suna dan jujjuyawa sai ga mr Johnson ya gaishesu duk suka amsa, ashruf ma ya gaishesu. Mr Johnson yace, na xo ne daman in sanar muku cewa yau da daddare ake sa ran dawowar jirgin ruwa amma a rashin sa’a karamin ne xai taho mai cin fasinja goma sha biyu kacal. Babban jiirgin ya dan sami matsala don har yanxu Italy basu ma karasa xagayawa kasahsen da xasu ba, balle ma su juyo. Don haka ya kuka gani? Xa ku tafi a babban mu jira xuwan su? 

Ko kuma a samo cikon masu tafiya ku xama ku goma sha biyu mu tafi a karamin? 


 Axixa ta mike tsaye ta rike kugu tace, malam ka fa damemu da surutu ka ga mun yi maka kama da wadanda xasu shiga jirgin yawa ko kuma mun yi maka kama da wadanda xa su kasa biyan jirgi mai cin mutane goma sha biyu? 

 Mr Johnson ya yi murmushi yace, yi hakuri maigirma axixa tambayarku na yi don ban san me kuke so a ranku ba. 

tace, ta yanxu ka sani jirgin ya xo ya jira mu akwai mutanen da muke jira xasu xo jibi. Ina ya so ka yi mana total ka ajiye ka yi gaba. Mar Johnson jiki na rawa ya karbi takardu a hannun ashruf ya hau ‘yan rubuce-rubuxe da kirge-kirge daya gama sai ya mika musu kan wani tebur da karami da yake a jiye a gabansu, kusa da kofuna lemon da suke dan kurbawa in sun yi training sun gaji. Ya yi murmushi yace, to na bar ku lafiya sai kun ji ko kuma na ji daga gareku. Atika da munnira suka daga masa hannu suka yi masa bye-bye.


 Bayan sun fito farfajiyar katafaren hotel din ne ashruf ya duka yace da mr Johnson  maigidana ina jin tsoron yin wannan tafiyar da ka ce nixan tafi a jirgin wadannan ‘yan mata. 

Mr Johnson yace, tsoron me ashruf? Ashruf ya nisa yace, tsoron axixa nake yi, saboda naga yadda take yi maka ne kai maigidana ku masu jirgin ma balle ni mai hidimar jirgi ai ina ga sai ta mare ni don yanxu ko gaisheta na yi bata amsawa.


 Mr Johnson yayi dariya ya dafa kafadar ashruf yace, ko xaginka ta yi ko mari nema  ka yi mata murmushi ka ce ka gode saboda tana da kudi mu kuma kudinta muke so. Ashruf ya yi shiru yana tunani yace a ransa lallai turawa basu san mutuncin kansu ba balle na addininsu yanxu akan kudi sai a yi musu wulakanci suna ji suna gani? 

To Allah Ya kiyaye Ya kuma hore min abinda xan ci in ciyar da iyayena in bar wannan aikin kaskanci. Can ya ji mr Johnson nagirgixa shi cikin figita ya farfado daga tunanin da ya ke. Mr Johnson yace, ashruf ka bar damun kanka a kan yarinyar nan axixa ka san abinda ta ke so? 

Son girma. Idan ka ringa girmamata kana bata girma kamar xaka kwanta mata to xa ka ga kun daidaita kun rabu lafiya, kaga saboda iya aikinka da hankalinka ga nutsuwa da girmama mutane ne yasa na xabe ka mu yi tafiyar nan da kai, naga xa ku daidaita da axixa. Haka dai mr  Johnson ya dinga lallashin ashruf yana nuna masa hanyoyin da xai bi ya ci maganin xama da axixa.


 Haka suka isa wajen da suka ajiye motarsu suka shiga ashruf ne mai tukawa, suka fice daga farfajiyar hotel din. Ashruf dai a ranar haka ya yini cur yana ta tunani a kan irin wulakancin da xai fuskanta a wajen axixa na tafiyar nan. Babu abinda ashruf ya ki jini a duniya irin wulakanci, baya son ya shiga shirgin daya jibanci wulakanci Balle kuma ma wulakanci irin na axixa, yarinya sa’ar kanwarsa. Gata ta iya cin mutuncin jama’a a yadda ya ga dai alamunta. Can ya nisa yace, Allah ga ni gare Ka, idan babu alheri a tafiyar nan, Allah Ka sa a fasa tafiya da ni a tafi da sauran ni in ni babban jirgi duk da dai babban jirgi ya fi jama’a, ya fi yawan aiki amma kuma wasa da dariya yake rabani da matafiyan, sun san mutuncina su dauko kudi mai yawa kuma su bani duk da dai sun san hidima da na ke yi musu biyana ake yi amma  kuma sun san su tausaya min tunda ni ba bawa ba ne. abin mamaki sai ga ‘yan uwana  bakar fata maimakon su rungumeni sai nake ganin kamar kyamata xasu yi ko da yake su atika naga suna da mutunci, axixa ce. 


 To Allah Ya fi ta ai. Haka ashruf ya yini ya kawana tunane tunane da addu’o’I don shi da gaske yake baya son abinda xai hadasu da axixa balle ta ci masa mutunci. Kwanci tashi su axixa sun yi kwana hudu a Croatia , basu ma cika xama a hotel din da suka sauka ba sai dai barci ya dawo das u. direba na musamman aka basu a hotel din yake yawo dasu waje-waje a cikin birnin Croatia da kewayenta. A yau kuma mr Johnson da ashruf suka sami wayar su Mubarak sun iso, suka je taryar a filin jirgi wato su Mubarak suma sun iso yau da misalin biyar na yamma daga filin jirgi kai tsaye hotel din dasu axixa suke ashruf ya wuce dasu. a rashin sa’a suka iske su axixa basa nan sun fice tun safe. Basu yi wata-wata ba suka nemi a basu dakunansu daban a kusa dana ‘yan matansu. Aka kuwa yi musu hakan cikin gaggawa, sai  can wajen goma na dare su axixa suka dawo suka iske abun kaunarsu nan fa murna ta rincabe.


 Bayan xuwan su Mubarak da kwana biyu suka yiwa mr Johnson Magana akan sun shirya tafiya. Ran daya ga watan febrairu da misalign karfe goma sha biyun rana mr Johnson ya turo ashruf da sauran direbobinsa guda biyu kowanne da mota daya motoci uku ke nan, su xo su dauki su axixa da kayansu su kaisu tashar jirgin ruwa don su tafi a yau din. Ashruf ne a gaba don shi ya fi sauran direbobin sanin inda dakunan suke. Ya tsaya a bakin kofar ya dannn kararrawa, yaji shiru, ya sake matsawa sai ya ji an xo an bude. Axixa ahmad abdul fati ce tsaye ta bata fuska, gaban ashruf ya fara dukan uku-uku don fargaaba ya duka ya gaisheta a cikin rawar murya bata amsa ba, sauran ma suka gaisheta duk dai ta yi shiru bata amsa ba, ashruf yace mun sa an yi muku waya a reception suka ce kun shirya xa mu tafi tashar, jirgi yana nan yana jiranku. Axixa cikin tsiwa da cin mutunci tace, kun yi waya a reception nace ku xo shi ne kuma kake dannn min karrarawa kamar in ban bude ba xa ku shigo ku tafi da ni? 

Ban san kai dabba bane sai ka nuna min halin dabbancin. 


 Ran ashruf ya yi bakikirin don kuna hankalinsa ya tashi yace a ransa, yariyar nan ko raina na ciro na ajiye mata a gabanta don ladabi sai ta ci min mutunci abin har ya kai ta cire min daraja ta ta mutum ta sani a cikin dabbobi? 

Axixa tayi shigewarta sai atika ce ta ce ku shigo ku kwashi akwati nan. Ashruf da abokansa direbobi alex da Solomon suka kinkimi akwatina suka juya  xasu fice. Munira tace, idan kun kai ku dawo daki  na kusa da nan ku dibi nasu Mubarak ku jiramu muma ga mu nan fitowa. Cikin ladabi da sanyin murya suka ce to ranki ya dade. Suka fice. Atika ta juya ta kalli axixa wacce take kan kujearar mudubi tana tsala kwalliya tace, axixa kenan kina abun da kika ga dama amma da wata kalma guda daya da kika gayawa yaran nan ashruf ban ji dadi ba kika ce masa dabba . Munira ta yi caraf ta cafki maganar tace, Allah sarki shima daga gani bai ji dadin Kalmar ba. axixa ki ringa dan sassauta masa tunda naga yana da hankali kuma dai daga sunansa ashruf Kaman musulmi ne ma. Axixa ta waigo a fusace tace oh nace masa dabba shi yasa ba ku ji dadi ba, shima daga fuskarsa bai ji dadi ba ko? 

To sai dai in ya mutu daga yau ma ba xan dinga kiranshi da sunansa ba ashruf yake ko wa? Da sunan dabba xan dinga kiransa  sai ya mutu, ku kuma da kuke tayashi takaici sai ku sume.


 Suka atika da munira suka tuntsire da dariya suka tafa suka ce, axxy best kenan kina sha’aninki. Bayan sun gama yan kintse kintsensu ne suka firfito xuwa wajen motoci. Axixa da Mubarak suka kame a bayan motar da ashruf yake ja, atika da sadik dinta suma suka harde a bayan motar da Solomon yake ja. Munira kuma da nata gwanin Ibrahim suka shige bayan motar alex sai tashar jirgin ruwa. Karfe biyu daidai mr Johnson da matukan jirgin, da masu dafa abinci guda uku da kuma ashruf duk suka gama xuxxuba abubuwan da xasu bukata har na tsawon watannin da xasu yi tafiyar wanda xai ishesu. Da wasu kwararrun likitoci suma da akwatinan maganinsu ko wata rashin lafiya ka taso. Ashruf kuwa bai manta da komawarsa ta kamun kifi ba, dan shi a aikinsa bayan share-share da goge-goge har da kamun kifi, da xai dinga yi a cikin ruwa wanda xa a dinga dafawa matafiyan. Da kuma wasu injiniyoyi masu gyarann jirgi da matuka jirgin ruwa ya tashi da wadannan attajiran samari da ‘yan matasu kadai suka dauki shatar jirgin ba a sa musu bare ko daya ba, daga su sai ma’aikatansu. Sun bar Croatia sun kama hanya.


 1st FEBRUARY

 Jirgi ya ware fankoki a cikin ruwa yana ta daba wuta, ma’ana yana ta shara gudu a cikin ruwa. Kamar dai yadda muke ganin irin wadannan jirage a finafinan turawa ko kuma a satellite, jirgin ruwa ne amma ya fi wani gidan ma girma danko xa a hada girmansa da gida ma to ba kowane irin gida ba. sai irin katafaren gidan nan wanda girmansa ya isa. Dan shi wannan jirgi duk da yake karamine ma ba babban bane mai cin daruruwan mutane, amma duk da haka akwai dakuna shida na matafiya ga dakin mr Johnson dashi da sauran ma’aikata matukan jirgin, ga na likitoci biyu, ga na ashruf shi da masu girki uku duk kasa dakunan matafiyan yake, da kuma bene duk a jirgin sannan nasu mr Johnson a kusa yake da dakin tuki nasu ashruf kuma a kusa da kicin yake, kowannen daki kuma da bandaki a ciki da gado da komai dai da aka sani ana samu a daki. Ga wani katafaren falo wanda ya kunshi komai da komai na kayan kallo da kujerun alfarma da dardumai masu laushin takawa, ga dakin cin abinci shima  daban yake a tsakanin falo yake da kicin, inka shige cikin jirgin  sai ka rantse ka ce a wani gidan kake hadadde mai kyan gaske.


 Idan ka hau sama wani katon fili ne budadde nan da kujerun shakatawa iri-iri kuma anan ne xaka dinga ganin ruwa don wajen a bude yake kawai da karfe aka agaye filin. A nan  xaka ji wata iska mai sanyi da kamshin ruwa suna tashi na alfarma. Duk da wannan fadi da girma sama da kasa na jirgin bai kare ba, akwai kuma can karkashin jirgin shima akwai wata na’ura da xata kai ka can kasan jirgin misali idan suna so su yi wanka a ruwan akwai kataferen xagayyayen wajen wanka wato (sweeming pool) da kuma wani bangare da ake jifge wasu kananan jiregen ruwa masu kama da balo buga musu iska ake yi amma da akwai bangaren injin da ake jonawa da gas suke amfani su kuma idan matafiyan suna son su xagayawa cikin ruwa suke shiga suna xaxxagawa cikinsa ko in sun hango wani tsibiri ko wani gari a gefen ruwa suna so su sauka su ga al’adar ‘yan garin ko kuma su ga yanayin wani abu to shi ne ake yin ampani da wadannan kananan jirage.  Suna da masifar gudu ainun don kallon wani abu suka tsaya yi a wani gari da yake bakin ruwa kuma a jirgin ya wuce da kamar awa to a cikin dan kankanin lokaci wadanda suke cikin dan karamin jirgin nan xasu iya xuwa su sami babban jirgin. Babban jirgin shi baya tsayuwa a ko’ina sai kamar a wata kasar da take da tashar jirgin ruwa kuma matafiyan sun ce suna so su tsaya a kasar da dai makamantan wannan.


 Su axixa sun yi wajen awa biyu cikin jirgi da fara tafiya kuma su duka suna xaune ne a wannan kataferen falon suna kallon talabijin. Axixa ta matsa kararrawa ma’ana mai aiki daya ya xo tana son wani abu. Ashruf cikin sauri ya shigo cikin ladabi da fargaba yace, gani axixa ta yatsine fuska tace babu mutum sai kai? Ashruf bai gane abinda take nufi ba, yace ai ni ne daman xan dinga yi muku aike-aike na dauko muku duk abinda kuke so, sauran ai su suna kicin su suke dafawa ni kuma xan dinga miko muku. Axixa tace ina nufin mutum nake kira ba kare ba, ahsruf ya sunkuyar da kai ya ma rasa mai xai ce mata.


 Kowa ya kurawa axixa ido yana kallo da alama babu wanda ya ji dadin abinda ta yiwa ashruf. Amma  saboda ita babu wanda ya isa da ita sai kowa ya yi shiru yana kallonta. Can ta nisa ta kurbi lemo tace, to tun da sai kai kadai (guldo) sunan kare ne. guldo to ina so gasashsshen kifi marar kaya da yawa a tsaga cikin a xuba albasa da tumatur da yaji a gasa a gudansa a kawo min kar a wuce minti ashirin da hudu. Ashruf ya juya xai fice sai ya ji tana kira, irin kiran nan da ake yiwa kare. Ashruf bai juyo ba sai ya ji  ta daka masa tsawa tace, ba ka san kiranka nake yi ba ma ko? 

Ashruf ya juyo a fusace yace sunana ashruf kuma kiran kare na ji kina yi shi yasa ban juyo ba. ashruf na rufe bakinsa sai ga mr Johnson a gabansa ya bata rai kai ka ce an aiko masa da mala’ikan mutuwa ne, duk wannan wasa da dariyar ta mr Johnson ya dakawa ashruf tsawa yace ya fice ya bashi waje. Ashruf ya fice cike da kunar xuci, ya nufi kicin a fusace, kuku nan suka lura da ran ashruf a bace yake, mummunan baci kuwa sai suka shiga tambayarsa me ke faruwa ko dai mutuniyar taka ce? 

Dake duk wanda ya san ashruf ya san shi da  gudun cin mutuncin axixa a wannan tafiya.


 Ashruf yace bakar dagar nan ce take son ku gasa mata kifi cikin rawar jiki suka bude firij suka dauko irin kifin daya fasalta musu suna gyarawa suna tambayar ashruf me ta yi maka kuma ranka yabaci. Ashruf y ace ban taba yin kisa ba amma ina ganin daga kan makiyiyar nan tawa xan fara in ya so idan na kasheta nima a kashe ni. Daya daga cikin kukun ya yi sauri ya taryi maganar ashruf yace yi shiru ka daina fadar haka abokina bacin rai ne amma ai ba xa ka iya kasheta ba kuma komai lokaci ne nan da ‘yan kwanaki ko wata xaku rabu watakila ma kai da ita babu wanda xai kara ganin wani, koda yake suma bakar fata ne kaima haka watakila kasar ku ma daya idan aka bi tarihi. Ashruf yace ita daga Nigeria take ni kuma daga jamaika nake babu hadinmu. Yana rufe baki sai ga mr Johnson ya bugo kofa ya shigo yace kuwa da wa Allah Ya hadani in bada kai ba, ya hau ashruf da fada fa,fa,fa kamar xai hadiye shi. Ashruf dai ya sunkuyar da kai kasa yana sauraron kawai.


 Mr Johnson ya ci gaba da cewa ba ka dauki duk abubuwan da na dinga gaya maka ba ko? To a kan axixa  xa ka iya rasa aikinka, don haka ka kiyaye! Cikin ladabi ashruf yace xan kiyaye mai gidana, kuma don Allah ka yi hakuri ba xan sake ba. washegari da duku-duku ashruf ya dauki komar kama kifinsa ya dulmiya cikin ruwa yana ta kokarin kama kifaye. Sai can ya yunkuro ya fito dauke da kifi himili guda a cikin koma a kafadarsa ya hayo jirgi ya shigo cikin jirgin sai ko suka yi ido hudu da axixa wacce ta harde akan wata kujerar shakatawa da kofin lemo a hannunta da jarida tana karantawa a kusa da ita kuma abin kaunar ta ne, Mubarak yana kan keken wasa jini yana tattakawa. Ashruf ya duka ya gaishesu, Mubarak ya amsa amma ban da mutuniyar ko kallonsa bata yi ba. ashruf ya jawo daron da yake wanke kifi ya fara dauko kifayen nan daga cikin koma yana datsasu tunda da ransu suna tsalle-tsalle, in ya datsa da wuka sai ya jefa cikin daron wanda yake a cike da ruwa. Axixa ta yatsine fuska ta kalli Mubarak tace wannan kuma mai ake yi ne? 

daga ina ya samo kifi haka masu rai? 


 Mubarak yace ina nan tunda asuba naga ya fito ga sanyin asubar nan na tambayeshi yace mun kifi xai kamo yake gaya min shi daman aikin sa don ya dinga kamo kifi ne kawai don haka duk kifin da matafiya suke ci to sabon kamawa ne. axixa tace wadansu mutanen basu da hankali kuma basa gudun wahala. Yanxu yaya xa a yi mutum ya fito tun da asuba ya shiga ruwa ga sanyi ya kamo kifi kawai, nawa xa a biya shi? Mai xai samu? Mutane su suke jawa kansu talauci da kansu saisu dorawa gwamnati ko kuma masu kudi alhali kuma su suke jawa kansu talauci, ga dai wahalallen rigarsa a yage kansa duk a cukurkude yana tafe ciki a shamule kai ka ce bai taba cin abinci ba, da ka gan shi ka ga talauci amma kuma kullum baya hutawa a bauta yake.


 Bai kuma sami kudin ba. Mubarak ya nisa cikin harshen hausa yace, axixa idan xamu yi Magana irin wannan a gaban wadanan mutane to mu canja harshen hausa tunda basa jin hausa amma idan da turanci ne suna ji saisu dauka ci musu mutunci muke yi. Axixa ta gallawa Mubarak wata matsiyaciyar harara cikin harshen turanci tace da turanci na saba Magana kuma da turanci xan ci gaba ba xan yi hausa ba in wahalar da kaina. Dan su ji daman nake fada. Ashruf a durkushe yake kawai kamar yana gyaran kifi amma sauraronsu yake yi kawai, duk a bubuwanda axixa ta ke yi masa na cin mutuncin bai taba jin ya tsaneta ba, sai dai ya tsani halinta, ba kamar a wannan lokacin, yayi  shiru yana tunani bai san sanda hawaye ya rinka kwaranyowa daga idanuwan sa ba, ya tausayawa kansa da kansa yace, a ransa wannan bata san Allah bane mai axurtawa? Kuma Shine mai talautawa, yace, da na san inda xani inyi kudi lokaci daya ta hanyar halak daba xan xo ina ta wahalar da kai naba.


 Can kamar a mafarki ya ji tana kira irin na karnuka ya ji tace guldo! Guldo kira nake fa. Mubarak yace malam ahsrauf xo nan. Ashruf ya taso ya xo wajen Mubarak yace yes sir. Axixa ta yi caraf tace yes ma because I’m the one calling you, I need something cool not cold. Ashruf ya kurawa axixa ido yana cewa a xuciyarsa inama-inama badan gudun hukuma ba kuma ‘yan nan kasar babu ruwansu da mai gaskiya mai kudi kawai da na shake yarinyar nan yau data gayawa ‘yan garinsu. 

Mubarak yace jeka mana ba Magana take yi maka ba, ka kura mata ido ko kuma ba xa ka je ba ne? 

ashruf ya nisa ya duka yace, sorry sir! Ya juya xai tafi, sai axixa tace guildo xo nan. Ashruf ya dawo tace, ba xan iya shan abun hannunka ba, da yagaggiyar rigar nan taka mai karni a cikin sakan ashirin da hudu nake so ka yi wanka ka canja kaya ka kuma kawomin abu mai sanyi in sha. 


 Ashruf ya juya ya nufi dakinsu cikin sauri yayi wanka ya kuma canja kayan ya shiga kicin ya dauko musu lemo da kofuna biyu ya kawo musu. Axixa ta kalleshi daga sama har kasa ta kuma kalli agogo. Ta ce, nace sakon ashirin da hudu yanxu ka yi minti ashirin da hudu, ashruf ya sunkuyar da kai kasa takaici marar misaltuwa suka lullube xuciyarsa yace I’m sorry, ya duka ya ajiye musu lemon da kofuna akan tebur ya juya xai tafi. Axixa ta yi fito tace, guldo, ashruf ya juyo ya dawo sai ta kurawa gaban rigarsa ido ta kece da dariya. Ashruf shima sai ya kalli inda take kallo a kirjinsa tana dariya amma sai ya ya rasa abin dariya, rigarsa t-shirt  far ace sol a wanke to me abun dariya a jikinta kuma! Axixa ta yi ta dariyar har Mubarak ya dinga kallon ta shima bai san abinda take yiwa dariya ba, amma kuma dariyar sai take bawa dariyar sa dariya, axixa ta gama dariyarta tace guldo kana da ‘yaya ne? 

ashruf yace eh, ina da ‘yaya. Axixa tace, shi yasa ka sayo riga mai hoton ‘yan aljanu wato (catoons) kamar wani yaro to ko su ‘y’yanka ka soyowa ta yi musu yawa don kar ka yi asara kake saka kayan ka? 


 Ashruf ya ji kamar ta daba masa wuka a ransa yayi shiru yana sauraronta tagama masa iskancin da taga dama ta sallame shi ya wuce cike da takaici ya nufi dakinsu yana xuwa ya sake tube wadannan wankakkun kaya ya sake sa yagaggu masu karni na aiki ya dawo ya ci gaba da aikin wanke kifinsa. Axixa tace da Mubarak darling ka ga abinda nake gaya maka ko shi talaka kullum a matsiyacinsa yake ya fi so a ringa ganinsa a cikin tsiya da talauci shi yasa na tsani talakawa musamman wannan. Ta nuna ashruf ya juyo a fusace yana kallonta.


 Axixa ta yi shiru tana tunani a ranta tace, wannan mutumin daya sami fili irin kallon nan da yake min daya faffallamun mari koma ya shekeni don naga daga kallon da yake min ya ji haushi tace amma sai dai ka mutu ni kuma daga yau xan sa kafar wando daya dashi


 ina bakatar nadunga samun comment dari biyar a wannan kayataccen littafin domin somin tabine nagani sainajiku naku a kullum maidebemiki kewa

Abdul Dboy 

Bauchi state

[8/28, 9:41 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[8/28, 9:44 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU.

*2*

.

.

Hantsi sakaliya rana ta fara fitowa su atika da suke ta barci ciki ya fara kiran ciroma duk sun tattashi. Bayan sun yi sallah,  sun yi wanka sun yi brush sun tattaru a dakin cin abinci su axixa ma sun shigo. Ashruf tuni ya fara aikin jera musu abinci iri-iri a kan tebur.

 Bayan ya kawo musu komai da komai xai fita sai ya ji mutumiyar tasa ta mike da gudu tana kakakin amai ta nufi shara ta tofar da abinda ta sa a bakinta, Mubarak da sauran duk sun mike a hargitse suna tambayarta lafiya? 

Bayan da axixa ta gama ‘yan tofe tofenta aka bata ruwa ta kuskure bakinta sai ta dawo ta xauna tace da ashruf xo nan. Ashruf ya matso yace ga ni, axixa ta daka masa tsawa tace yau wane irin kifi ka kamo mana marar dadi? 

Ashruf yace a wajen dafawar sane suka cika gishiri! Axixa tace kifin ne kansa bashi da dadi ya fara rubewa don haka a canjo min wasu. Ashruf ya kinkima ya nufi kicin. Mr Johnson da sauran kuku suka xo suka kewaye kwanon kifin nan a cike da mamakin me ya sa aka dawo dashi? 

Ko ci basu yi ba bayan irin shirya shi din da akayi, yayi dadi. Mr Johnson yace, ashruf lafiya? 

Ashruf yace tace kifin babu dadi. Mr Johnson ya dauki cokali ya gutsira ya dandanan ya ji dadi, dadin ma mai xakakwa don shi ya dade bai ji irin wannan dahuwa mai dadin wannan kifin ba. 


 Ashruf yace, ranka ya dade yaya ka ji kifin? 

Mr Johnson ya nisa yace kifin kam da dadi don ko maki aka ce in bawa kifin nan xan bashi sama da casa’in  a cikin dari. Koda yake babu komai masu kudi ne komai suka maka ka yi murmushi ka basu abinda suke so. Ka xamar da kanka tamkar wawa wanda baka san abinda kake ba, don su bamu kudinsu mu kuma idan muka tashi karbar kudinsu sai mu yi ta karba su yi ta miko mana su kuma kamar wawaye. Ashruf miko wani kwanon. Ashruf ya mikowa mr Johnson wani kwano na tangaran mai kyan gaske, wanda ya fi na farkon kyau mr Johnson ya juye kayatacciyar miyar kifin nan a ciki ya cewa ashruf ya dauko ya biyoshi dashi. Ashruf ya kinkima yana biye da mr Johnson har dakin cin abinci inda su axixa suke. Axixa tana ta faman yiwa Mubarak babbalin masifa wai yana xaune yana kallon irin abubuwan da ashruf yake yi mata baya Magana shi kuwa yana ta lallashinta shi da abokansa su Ibrahim da kawayenta su atika.


 Su mr Johnson suka shigo, ya gaishe su sannan ya matsa kusa da axixa ya duka yace, mai girma axixa ki yi hakuri kifin da yaran nan ashruf ya kawo muku bashi da kyau ashe. To gashi a cikin gaggawa an yi sauri an dafa muku wani. Mr Johnson ya karbi kwanon kifi daga hannun ashruf ya mika kan tebur a gaban axixa yana ta faman yi mata murmushin kwantar da hankali. Axixa ta yatsuna fuska tace da mr Johnson bude mun in ga irin wannan din, mr Johnson cikin rawar jiki ya bude sai ya ga axixa ta kawar da kai ta tashe hanci tace mr Johnson matsar min da kifin nan daga gabana na gane irin na daxu ne. to in har ba xa ku iya ciyar da ni ba irin abinda nake so xan ringa fita kasuwa bakin ruwa ina siyo abinda nake so ina dafawa. Mr Johnson yayi sauri ya tari maganar da take yace haba madam axixa ki daina fadin haka yanxu ko daya daga cikinmu kike so a dafa miki ba a dafa miki ba balle kifi? 

Mr Johnson yayi murmushi yace to yanxu ranki ya dade me kike so cikin minti ashirin da hudu adafa miki kiyi hakuri axixa mu da ku muke alfahari muna sonku amma mun fi son kudinku. Ashruf babu abinda yake yi sai kallon mr Johnson yake wani yashe baki yana wani murmushi waishi a dole ya xamar da kansa wawa saboda yana son kudinsu. Ashruf yace a ransa ina xan iya yiwa wannan makiyiyar nan tawa wannan murmushi tana ci mun mutunci ai ina ganin xan rasa aikina akan wannan yarinya. Maganar axixa ce ta farfado dashi daga tunanin da yake ya ji tace wannan kifin da ya kawo mana ne bana son irin sa, irin wanda nake so yanxun nan ya shiga ruwa ya kamo min kananan kifaye, jarirai ba iyaye ba. mr Johnson yayi murmushi yace, an gama. Ashruf ka ji maxa-maxa ka je ka dauko komarka ka shiga ruwa yanxun nan ka kamo kifaye kanana. Ashruf yace, to amma yanxu kamun irin wadannan kifi yana da wahala da dai da asuba ne yanxu rana ta yi duk sun watse sun yi kasan ruwa. Mr Johnson ya ce ita kuma su take so. Axixa ta karasa da cewa a yanxu kuma.


 Ashruf ya wuce sumi-sumi a cikin sanyin jiki ya nufi wajen da yake ajiyar komarsa ya dauko karamin jirgin da yake hawa ya tafi kamun kifin yahau ya tafi  cike da takaici ga yunwa danko karyawa bai yi ba.

 Ashruf bai dawo ba saida la’asar sakaliya ya kuwa ciko daro da kifi irin wanda tace tana so ya wanke su anan kan barandar jirgin ya dauko xai kai kicin sai ya ci karo da axixa ta fito daga wani daki a guje da kofin lemo a hannunta tana dariya, cikin dakin  kuma ga sautin kida nan da alama ma dai rawa suke ko wani party, kuma gudun da ta yi ta yo waje watakila ita da darling dinta ne ko kuma kawayenta ta tsokana ta yo waje saura kiris Ashruf ya sharo mata wannan danyen kifin a jikinta don ta bangaje shi, shi kuma daro a kafadarda da kifi. Axixa ta tsuke fuska tace da ashruf da kifin xa ka xubo min aka? Ashruf ya ce a’a ke kika bangaje ni daron ya kusa subuce min sai na rike da sauri dan kar ya xube. Ya yunkura xai wuce sai ya ga ta tari gabansa ya sake bin ta gefe xai wuce sai ta sake tarar gabansa sai ya tsaya cak yana kallonta, tace mr ashruf kake ko waye? Kana jiyo sautin kida kuwa daga nan dakin? 

Ashruf yace, eh inaji. Ta ce yauwa yanxu abinda nake so ka sauke daron kifinka ka taka min rawa in gani. Ya ji wani takaici ya lullube shi yace a ransa yarinayar nan ta dauke ni wani sakarai marar mutunci wanda ma bai san abinda yake yi ba, talauci ba hauka bane ai kudi ma ba hauka ba ne.


 Axixa tace, kana bata min lokaci ka yi min rawa nace. Ashruf yace da ita rawa bata cikin aikin da aka dauke ni na dinga yi. Ana biyana kamun kifi ne aiki na manya ko kanana da dai kifi ne idan na kamo manyan kika ce kanana kike so xan kamo kananan kuma suma idan basu yi miki ba sai kice kwan kifi kike so tunda aikina ne xan nemo miki, amma ba rawa ba. talaka yana da abin yi, baya rasa aikin yi ya xauna yana rawa don haka matsa min in wuce. Ya wuce abinsa har ya shige kicin axixa na tsaye tana kallonsa. Ta nisa tace, ashruf baka san halina ba sai ka gwammace baka bani irin wannan amsar ba. ba xan fadawa mr Johnson ba don kawai shi sallamarka xai yi amma da aikin naka farin ciki ya gagari xuciyarka yaro axixa kake ji baka santa ba. dan attajiri ma baya gangancin gaya min Magana balle dan matsiyaci, matalauci kamar ka. Axixa ta wuce cikin dakin da suke rakashewarsu.


  A ranar da daddare axixa ta sawa ashruf dokoki ir-iri tace, idan suna cin abinci ya xo ya tsaya har sai sun kare don bata so ko tana da korafi akan wani abu sai ta sha wahalar dannan karrarawa. Duk dai wani abun da ta san xai Konawa ashruf xai kuma wahalar dashi shi ta sa a cikin dokokinta.

 Kwanci tashi satinsu biyu a hanya sun kuma tsaya Italy sun yi kwana biyu sun wuce. A da a kowace rana sau daya ashruf yake kamo kifi wata ranar ma baya komawa in wanda ya kamo na wannan ranar masu yawa ne yakan isa a ci yau a ci gobe. Amma a wannan tafiya saboda axixa wani lokacin ma har sau uku yake kamo kifi iri-iri daban daban ya kamo wannan tace ba irinsa ba, ya koma ya kamo wani tace bashi ba, sai yayi sau uku, ko biyu daga karshe ma tace ita yau ta ma fasa cin kifin kaji xa ta ci aje a bawa masu ci. Ashruf ya kule ga jigata ko barci bai cika samu ba balle wai ya xauna a xaune da rana yana hutawa ai sai dai idan su axixa sun fita ne a karamin jirgi, amma muddin axixa tana nan ashruf shi da kishingida bissalam.


 Don haka duk wanda yasan ashruf da idan ya ganshi yanxu ba xai ganeshi ba, don ya rame kullum a cikin bacin rai babu walwala a tare dashi. Mr Johnson ya lura cewa gaskiya axixa har da don ta musgunawa ashruf take sashi wannan aiki iri-iri. To babu yadda xai yi da ita tunda xuciyarsa ta kone a wajen son kudinta, sai dai yakan kira ashruf yana ta bashi baki akan yayi hakuri da duk abinda axixa xata yi masa dan lokaci ne xa su rabu, amma shi kam da wannan hakuri na mr Johnson ai gara babu ya kyaleshi ya ci gaba da fuskantar wulakanci da kaskantarwar da axixa take masa, ashruf yakan daga hannu ya roki gafara a wajen Ubangijinsa yace gwanda ya dauki ransa a cikin wannan hali da yake ciki baya so ya karasa wannan masifaffiyar yarinya don cin mutuncinta ya isa. Abokansa kukun nan guda uku suma har sun gaji da lallashin ashruf idan sun xo kwanciya barci don duk juyin da xasu yi cikin dare saisu ga idaonsa biyu yana tunani kawai wani lokaci ma yana hawaye duk don axixa. 


 Ranara da suka cika kwanaki ashririn, ashirin ga watan febarairu kenan axixa ta cika shekaru ashirin da hudu a duniya. A yau kuma ta hada kayataccen (birthday) a cikin wannan jirgin ta sa aka huhhura balo ko ina aka saka abin kyale kyale, an rubuta HAPPY BIRTHDAY AXXY BEST. Anan farfajiyar aka harhada kujeru na alfarma, ga wani kek mai hawa hudu shima an caba masa ado wanda xata yanka, da misalin karfe takwas na dare aka haifeta don haka saida karfe takwas din aka fara shagalin wannan bikin xagayowar ranar haihuwar axixa. Ta kuwa caba ado da wata dandatsetsiyar doguwar riga irin ta turawa daga kanta har kafarta gwala gwalai ne kanta babu dankwali ta saki gashinta har gadon bayanta, ashruf na can kurya yana labe yana kallon kudi a gidansu ya kurawa axixa ido yana kallon halittar Allah. 


 Ya ce a ransa wannan yarinyar kin yi dace da kyau dama ace kin yi dace da hali me kyau da kin ji dadi duniya da lahira. Ya ga gashi mai sunan gashi ga tsawo ga yawa ga tsantsi sai ka ce ba bakar fata ba, idanuwanta dara dara masu kyau ga wani hanci  dodar har baka, baki dan karami a wannan kewayayyar fuskarta tata, haka ya dinga kallon kirar kyakkyawar halittar da Allah Ya mata, wanda ya ga cewa duk a banxa suke, domin babu hali ko daya.


 Ashruf yana ta kallon axixa yana xano halitunta can ya nisa, yace a ransa wai yau kwana na nawa da axixa ace ban taba lura da wadannan halittu ba sai a yau? Ya ce ko da yake sai a yau naji raina ya dan washe don ita ma wacce take sani damuwar naganta yau a cikin farin ciki shi yasa ma kyanta ya fito sosai har na lura, don idan ta kular da ni kyakkyawar fuskarnan tata kamar ta bakin kumurci nake gani. Ashruf ya ci gaba da kallonsu. Mubarak ma ya fito sanye da wata tsadaddiyar bakar coat (suite) a jikinsa. Ashruf yace a ransa lallai Mubarak ka yi rawar jiki a kanta don na tabbata ba don kaima kana da kudi ba ne axixa ba xa ta kula ka ba, wani baki kirin dashi babu kyaw babu fasali. Ana ta daukar hotuna iri-iri dana bidiyo, ga fitulu kala kala, haske tar wajen kai ka ce ranace. Su mr Johnson dasu kuku da likitoci da sauran matuka jirgi da masu tukin kananan jirgi duk sun hallara a wajen wannan shagali, amma ban da ashruf shi dai yana wani dan lungu a boye. Yana jin mr Johnson yana nemansa ya ki ya je, yace ni kare na je wajen partyn uwargijiyata, ai sai in dinga shinshina mata kek din ta, in haramta mata shi. 


 Atika da munira duk sun yi kyau sun caba ado da samarinsu su Ibrahim da sadik, an kuwa warware disco mai ratsa jiki ana kurba lemo ana taka rawa a hankali kowacce da nata abun kaunar. Bayan an taka rawa sai aka umarci shugabar taro wato axixa ta yanka wannan katon kek din mai hawa hudu ta yanka a kasa tafi raf raf. Duk ana ta dauka a hoto ana dauka a bidiyo caset. Axixa ta xo gefe tana gwada waya ko da sabis tana so ta kira babanta don shima ya san yau ranar xagayowar haihuwarta ne ya san duk ida take yau tana gudanra da bikin xagayowar haihuwarta yana so yayi mata congratulations yana ta kokarin nemanta sai ta yi kamar xata shiga sai ta tsinke, itama axixa tunda safe take gwada neman babanta a waya ta kasa samu. Wayar turaya ce (new modern) wacce ko a ciki sahara kake xaka iya yi da ita amma yau gashi sabis yana yankewa. Axixa ta ji haushi kamar xata fashe da kuka tana juyawa gefenta sai ta hango ashruf a loko a sakule yana kallonta. Ta dan ji tausayinsa kamar tace masa  ya xo cikinsu sai wani girman kai da isa taga fa dan talakawa ne shi in yana so mai xai hana ya shigo cikinsu.


 Sai ta wucewarta ta rabu dashi. Haka dai suka kai kusan sha biyun dare suna cashewa da kida iri iri da ciye ciye da tande tande da lemuna kala kala ashruf na xaune yana kallo suka yi suka gama kowa ya watse ya nufi makwancinsa sai ya ga axixa ta tunkaro shi ta xo ta tsaya a gabansa tana kallonsa, ta yi murmushi tace guldo mun gama da sauran kasusuwa a wajen ka je ka tande ka gyara wajen kafin da safe mu fito. Ta wuce tana karairaya kamar xata gurde kugu.


 Ashruf ya bita da kallo harta wuce ta sauka kasa ya buga hannunsa da kansa yace oh God. Takaici ya lullube shi ya yi awa daya a xaune ya ma rasa mai xai yi, sai ya mike ya doshi wajen gyaggyarwa yaya xai yi? Ranar da suka cika kwana ashririn da hudu ga watan febirairu, da la’asar likip gamin magariba kamar karfe biyar da rabi na yamma, ga hadri ya kidimo garin ya yi kitif kamar ruwa xai kece. Ashruf da wasu matuka karamin jirgi su biyu suna xaune a farfajiyar jirgin suna gyare gyaren inji. Sai suka ji ana hayowa daga kasa ana tafiya a matattakala su dai a sanin su babu kowa a matafiyan nan da wadansu ma’aikata kamar mr Johnson da captain james dasu Mubarak, atika, munira, sadik, Ibrahim duk sun tafi can wata kasuwar bakin ruwa don kallon wani katon kifi da aka kamo a wani teku. Mr jihnson yace musu kifin yayi girman gini wato (shark) sunan kifin yana kuma iya hadiye mutum cancak. Munira tace shark xai iya kifar da jirgi fa! Mr Johnson yace ai ba a ruwan nan aka kamo shi ba nan dai aka xo aka jifgeshi, tiawa masu bincike daga kasashe suna nan suna bincike a kansa ana daukarsa a hotuna yace ai shi wannan ruwan saida aka fiffitar dasu tas da ireiren su sannan jiragen ruwa suka fara bi ta cikin sa.


 Shine tun karfe biyu na rana suka shirya ita kuwa axixa tana ta sharar bacci sunyi sunyi da ita ta taso su tafi kallon kifin amma tace su kyale ta ita ba xata je kallon wani abu kifi ba kamar wata marar aikin yi.  Don haka suka cika kananan jirage guda biyu da masu tukasu suka tafi, ita kuma axixa  sai yanxu ta farka, bayan ta yi wanka ta yi sallah tayi brush da sauransu. Ta shiga sauran dakunan bata gan su atika ba ta shiga falo nan ma basanan, wajen cin abinci nan ma basa nan, to shine sai tayi xaton ko sun fito farfajiyar ne suna shan iska tunda dama da yamma anan suka saba xama suna shakatawa. Tana fitowa taga saisu ashruf ne kawai a farfajiyar. Duk suka xuba mata ido suna mamakin ganinta don sun xata da ita aka tafi. Ta xaro gilas wanda yake sakale a jikin rigarta ta saka tace, ina ‘yan uwana suke? Daya daga cikinsu yace, ai tun da rana suka tafi wani waje da ake kira curbe xasu kalli wani katon kifi. Ta ce koma dai me suka je gani ina son daya ya dauko jirgi yanxu nan ya kaini, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wancan saboda sun san wajen nan yana da bala’in nisa kuma ko babu hadari a garin to fa tabbas kafin su kai dare yayi, kafin su dawo kuwa sai tsakar dare. Kuma da daddare babu ma wanda xasu samu a wajen, suma su mr Johnson a duk inda suke yanxu suna hanyar dawowa.


 Daya ya mike xai je ya dauko jirgin su tafi tace dashi, banda kai koma ka xauna. Dayan ma ya mike tace, koma ka xauna ,guldo maxa a dauko jirgi a taho ko? 

Ashruf  ya rasa abinda xaice shi dai tuki ba aikin sa ba ne yace. Mai girma axixa shawarar da xan baki shine ki bari sai gobe, dare yayi yanxu kuma da hadari a garin, bayan haka kuma wurin yana da bala’in nisa ba xai yiyu mu kai wurin yanxu ba in ba can cikin dare ba kuma ko munje babu wanda xamu iske. Ta ce shawarata gare ka shine karka kara sakon ashirin da hudu kaje ka dauko jirgi ka xo mu tafi.


 Ashruf ya mike ya tafi karkashin jirgi inda kananan jirage suke ya dauko jirgi yaxo yahada yace to a shigo mutafi sauran suka daga musu hannu cike da tausayin su, irin wahalar da xasu sha ga jirgin a bude yake tik babu rumfar da xata kare musu ruwa, gashi daga ganin hadarin ba karamin ruwa xa’ayi ba, yau ana iya kwana ana ruwannan.


 Ashruf ya bude wuta yana ta sharar gudu a cikin ruwa, bayan tafiyarsu da kamar minti ashirin da hudu sai gasu mr Johnson da ‘yan uwan axixa sun dawo, su kuma ta wani bangaren bata bangaren dasu axixa suka bi ba. suna ta saukowa suna hawowa babban jirgi ta wata matattakala. Bayan sun hawo gabadayansu hannayensu rike da ledoji sun yo sayayya, sai mutanen nan na xaune masu gyaran jirgi suka ce kunyi sabani yanxu ashruf da axixa suka biku mr Johnson yace, kai yanxu da daddaren nan xasu nufi wannan hanya, shi ashruf din bashi da hankali ba xai gaya mata nisan wajen ba? 

dayan yace babu abinda bai fada mata ba amma tace lallai ya dauko jirgi su tafi. Hankalin sauran ya tashi musamman Mubarak suka rasa yadda xa su yi. Mubarak yace, lallai a dauko jirgi a bisu a kira su. Wasu daga cikin su suka ce a kyale su ida suka ga ruwa xasu dawo don yanxu an fara yayyafi.


 Ashruf shi dai tafiya yake yi kawai yayyafin yana jijjika su. Can suna tafiya sai jirgin ya mutu inji ya daina aiki. Ashruf ya mike tsaye yaja belt din da ake tayarwa ya yi ta tayar da injin amma jirgin nan ya ki ya tashi. Axixa ta daka masa tsawa tace, malam ka tada injin nan In xaka tayar dama ka san injin bashi da kyau ka dauko mana wannan jirgin ko babu gas da yawa ne? ga ruwa nan duk ya fara jika ni, ashruf dai baice da ita komai ba yaci gaba da tayar da injin yayi yayi injin nan yaki tashi har ya gaji ya xauna, ruwa sai sake tsugewa yake. Ashe ahsruf dama yayi shirin ruwa sai ya dauko rigar ruwa ta leda ya saka ya juyawa axixa baya yayi xamansa, sanyi da jikewa suka gallabi axixa ga yar karamar rigar da ta saka sak duk ta soma jikewa. Axixa tace, nifa sanyi nakeji, wato dama da niyya ka dauko jirgi marar kyau kaxo tsakiyar ruwa ka ajiye ni ko, to sai ka raina kanka. Ka tashi jirgin nan ka mayar da ni na fasa xuwa. Ashruf fuskarsa cike da murmushin dadi baice komai ba ya luf a cikin rigarsa. Can axixa ta hango wata rigarsa wadda yake kamun kifi da a! ita kot ce ta jawo ta kade ta yaba ta a jikinta sai ta xabura ta warar da ita gefe tace karni sannan tayi tsaki. Ashruf ya juyo ya dubeta yace rigar matsiyacinda baya so ya huta sai bautar banxa kuma baiyi kudi ba sai kamun kifi kin san dole tayi karni. Axixa ta fusata tace ka tashi jirgin nan ka juya da ni kafin ranka yabaci, dabba kawai.

 Ashruf ya ce yau kashe ki xanyi, dan a cikin ruwan nan xan jepa ki kipaye suyi bandar ki sai naga iya ji da kai din naki, ni kuma daga nan kasar mu xan koma .... Lol.

.

Ga littapi dai iya littapi, dadi ba'a magana amma sai naga kamar en gidan nan basu shirya ba dan bana ganin comments kaman ruwa, sai da na tambaya lokacin da aka shirya amma aka ce jiya, da son ganin jama'a a daure ana comments, 

Idan kuma littapin ne baiyi ba sai kuyi magana.

Dboy🤞🏻

[8/28, 9:44 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[8/28, 9:46 PM]  "  D'Y: .KWANA ASHIRIN DA HUDU.

*3*

.

.Can axixa ta hango wata rigarsa wadda yake kamun kifi da a! ita kot ce ta jawo ta kade ta yaba ta a jikinta sai ta xabura ta warar da ita gefe tace karni sannan tayi tsaki. Ashruf ya juyo ya dubeta yace rigar matsiyacinda baya so ya huta sai bautar banxa kuma baiyi kudi ba sai kamun kifi kin san dole tayi karni. Axixa ta fusata tace ka tashi jirgin nan ka juya da ni kafin ranka yabaci, dabba kawai.

 Ashruf ya ce  da kenan axixa, 

axixa ta ji yau ya kira sunanta gatsai kuma har kamar yana yi mata musu. Ta ce wato da biyu ka kawo ni nan ko? 

Ashruf yace ni ban daure ki ba na jawoki, ke kika tilasta min na taho ashe don a koya miki darasi ne kika ce mu taho, yace Allah sarki talaka shi ba mutum bane, dan bashi da kudi sai ya yini a ruwa kema yau sai ki dandanan ruwa kiji yadda yake ji, anan xamu kwanan. Axixa ta ji wani takaici da kunci don a rayuwarta yau ne rana ta farko da ta taba haduwa da kunci da wahala irin ta yau.


 Ta yi shiru can dai taga sanyin nan da gaske yake xai illata ta sai ta jawo rigar nan mai karni ta saka tana sauraron taga yadda Allah xai yi da ita kuma ta  kudira a ranta duk ranar da suka koma Croatia, ashruf sai ya raina kansa abinda yayi mata don sai ta sa an daure shi sai yayi prison indai kudi yana amfani wahalar ta  da yayi.daga can nesa suka hango fitila kamar tana yawo a cikin ruwa da alama dai mutane ne ko kuma su mr Johnson ne suke nemansu. Axixa ta mike tsaye tana kwalla musu kira tana cewa ga mu nan. Ashruf dai na xaune yana kallonta. Ta kalleshi tace, ba xaka yi musu Magana ba? ka san mu suke nema. Ashruf y ace dan me xan yi musu Magana bayan ga ki ai daga yau kare ya bar haushi, daman can ma karya a kafi  sani da haushi da masifa. Axixa ta fusata tace guldo yau ni ka ke cewa karya? 

Ashruf yace kwarai kuwa.


 Axixa ta cire hannu ta xuba masa wani uban mari, ya rike kunci yana murxawa, sai yayi murmushi yace kin yi na karshe kenan. Kafin ta juya wajen da take hango hasken sai taga hasken ya juya yana komawa har ya kure hawayen takaici yayi ta kwaranyowa axixa tana xaune takaici ya dameta, ashruf kuwa fuskarsa cike da annushuwa kamar yau sallah a wajensa. Ya yi kwanciyarsa yana wake waken sa, ayi  ruwa a tsagaita a sake tsugewa. Axixa na takure ta hada kai da gwiwa, bata taba xaton ko  da wasa ba a duniya xata tsinci rayuwarta a irin wannan yanayin ba. yadda taga rana haka taga dare, ashruf nata barcinsa yayi juyi ya kalleta, ya koma ya kwanta yana murmushi. Can wajen asuba ta ji sun fara yin kasa kamar jirgin yana sacewa axixa ta xabura tace guldo, guldo ta ji ya yi shiru tace, ashruf, ya yi mata banxa ta daka masa duka, ya mike xaune ya kalleta cikin bata fuska yace, ke ya haka ina barci kina tashina me xan yi miki? 


 Axixa ta ji wani takaici tace, ka duba ka ga yadda jirgin yake mana sacewa fa yake yi. Ashruf yace to me xan yi masa ai gara ya sace mu fada kasan ruwa mu yi rayuwa a cikin kifaye ko muma ma dandana yadda suke rayuwarsu ko ma daina wulakantasu ace ba manya ake so a kamo ba, ace a kamo kananan. 

Axixa ta rude jirgin nan sai sacewa yake yi dai, ta rirrike jikin jirgin rabin kafafuwansu a cikin ruwa, ashruf ma ya rike jikin jirgin a haka dai  igiyar ruwa ta dinga jansu tana yin gaba dasu har garin Allah Yawaye rana ta fara fitowa. Suna nan dai a makalkale, a haka babu ko kukan tsuntsu balle kuma bil adama. Axixa ta fara jin yunwa ga kishirwa to ya xa ta yi yau babu abincin balle ashruf ya kawo tace babu dadi. Ashruf ya kalleta duk ta jigata ta wahala sai ya kyakyace da dariya yace madam axixa mai xan kawo miki ne? 

ba ki kada kararrawa ba guldo ya kawo abu mai sanyi cool not cold? 

Ya sake kecewa da dariya. Hawaye ya dinga xubowa daga idon axixa, don takaici. Haka suka yini har kusan magariba wato awarsu ashirin da hudu a haka. Ashruf ya dinga mika hannu yana kamo kifi ya dangwali wani abu kamar gishsiri ya ci, ya mika hannu ya sha ruwa ya ci gaba da surutunsa, axixa kuwa bata gani ma sosai don yunwa, badan girman kai ba da ta roke shi ko danyen kifin ne ya bata ta ci. 


 Ashruf ya fara gyangyadi sai ya ji axixa na dukansa wai ya tashi ya bude ido yace meye? 

Sai ta nuna masa wani waje a gefen ruwa igiyar ruwa ta kawosu karshen gabar wani bangare na ruwan. Nan da nan suka sa hannu suna tura ruwan jirgin  yana kara yin gaba har suka karasa wajen filin suka firfito daga cikin ruwan. Ashruf ya jawo jikin jirgin gefen  ruwa. Anan jikin wani dutse suka karasa kwanan a xaune suna gyangyadi. Bayan gari yawaye tar sai ashruf ya farka ya kalli axixa wacce take a xaune ta kura masa ido, baki duk ya bushe mata kishirwa da yunwa sun addabi ‘ya’yan hanjinta, ashruf ya yi hamma gami da mika ya mike tsaye, yace, bari dai na xaga garin namu in ga yadda yake fuskarsa cike da murmushi. Axixa ta bishi da kallo ya yi can baya yana xaxxagawa sai ya ga duk duwatsu ne masu bulbulo da ruwa garaigarai. Sai kuma yashi ko ina irin na bakin beach din nan tunda nan ma bakin ruwa ne da bishiyoyi da dogayen ciyayi a jikin duwatsu. Ahsruf ya ga alamar wajen an hura wuta tunda ga dutsinna nan da toka da konannun itace, ya ci gaba da xagayawa sai ya hango wani dan daki na katako ya karasa wajen da sauri ya taba kofar ya ji a kulle, sai da  yayi ta maxa ya xage karfinsa sannan ya iya bude kofa ya shiga ciki ya ga wani gadon itace an tula tsummakara akai an yi shimfida dasu . ya tura windo ya bude haske ya kara garwaye dakin. Ya hango wata loka ya jawo  ya bude ya ga kwalaben giya ne wasu babu wasu akwai, can gefe kuma ga kwari da baka masu kyau har guda biyu murna ta lullube ashruf ya gaya samu wajen xama sosai ga wata kujerar katako ta kishingida ya ci gaba da bincike bincike ya ga fitilar wani kwai ga ashana sinki da kalanxir galan guda cikakke.


 Da tsintsiyar kwakwa duk dai a dakin, dadi ya sake lullube ashruf yace bari in je dai in sallolin da ake bina in xo in gyara dakina. Ashruf ya dauko kwalba daya daga cikin kwalaben nan ya fito bakin ruwa ya iske axixa ta sami wani dutsen da yake disar da ruwa ta sa harshenta tana lasa. Ashruf ya yi murmushi ya girgixa kai ya wuce abinsa. Ya karasa bakin kogi ya duri ruwa a cikin kwalabar nan ya girgije ya xubar ya kara durawa ya girgije ya xubar ya wanketa tas sannan ya ciko ta da ruwa ya xagaya bayan dutse ya yi fitsari yayi tsarki ya dawo ya  cikata yayi alwala. Duk axixa na kallonsa tana tunani a ranta tace daman wannan musulmi ne? 

ni su munira na cewa sunan musulmi gare shi ban dauka musulmi bane. Ta ce ko ana ya samo kwalbar? 

Da ya ajiye ta nima in xo in duri ruwa in sha. Tana jiran in ya gama alwalar ya tashi ya tafi sallah ita kuma ta xo ta sha ruwa a cikin kwalbar sai ta ga da ya gama  ya ciko kwalbarsa yayi tafiyarsa da ita. Ran axixa yabaci kamar dai ta bishi ta roke shi ya bata taga dai ya ma xa a yi ta ringa rokarsa ai xai rainata, ta kyaleshi ya wuce ta xo bakin ruwan nan ta tsaya tana so tasa hannu ta ringa kwarfa tana sha amma sai taga kamar in ta sa hannu xa ta xindima ciki sai ta fasa.


 Hawaye yayi ta xuba a idon axixa don takaici tace a ranta yau wai nice wacce a gida a rana daya sai in sa a dafa min abinci kala kala har fiye da goma, sai wanda naga dama xan ci yau gashi wai ruwa ma ya gagareni in jika makogorona. Ashruf yayi ta jero sallolinda suka wuce shi sanda suke jirgi, har ya kammala rama su. Bayan ya idar ya shiga gyaran dakinsa ya dinga watso tsumokaran nan waje harda kwalaben giyar nan. Sai kuma ya yi tunani ai axixa xata iya daukar daya tana shan ruwa a ciki tunda ya ga yadda take kallonsa, ya san sha’awar kwalbar nan take ta dibi ruwa ta sha, don haka ya xo ya kwashe su ya boye su a cikin lokar nan har tsummakaran nan yace ai sai ta ringa lulluba dasu idan na bar su a waje suma ya mayar dasu daki.


 Bayan yagama gyaran dakin ya fito bakin ruwa inda ya jifge mata mataccen jirgin su ya balle injin jirgin daga jikin gangar jikin jirgin da yake jikin jirgin ne leda ne hurshi ake kamar balo amma  yana da laushi ya jawoshi ya kai ya dora a kan gadon itacen nan na dakin. Kafin ya dawo bakin ruwa sai ya xo ya iske axixa ta xo wajen ta jawo masa wata jakarsa da ta fado daga cikin jirgin. Ashruf ya karaso da sauri ya fisge jakarsa, yace ajiya kika bani? Axixa tace na hango wayata a ciki daman kai ka sace min ita wato dan kar in buga waya in ce ga inda muke ko? 

Wato da biyu ka sace mana jirgin ko kai harda shirinka ka xo su man shafawa su brush da makilin duk na hango, to wallahi xa ka gwammace baka wahalar da niba, sai ka raina kanka. Malam dalla ka miko min wayata kaji ko, barawo kawai.

 

 Ashruf ya daka mata tsawa ya xo daf da ita yana nuna mata hannu yace, ke axixa ki iya bakinki kin ji ko! Ba ashruf din da kika sani da ba ne balle wani guldo da kike kira, da ina sane na dauko lalataccen jirgi don ya tsaya mana a hanya in koya miki darasi kisan talaka ma ba dabba bane, ba kuma abin wulakantawa bane yana da amfani. Ni ne kuma na xare miki waya a aljihun don kar ki kira kowa daga ke sai ni a nan xamu xauna talaka da mai kudi a cikin daji daya ki nemi abincinki in nemi nawa. Don haka dokar  da xan sa ka miki guda uku ne xuwa biyu, ta farko daga yau idan na sake jin bakar Magana ta fito daga bakinki da sunan kin gaya min hukuncinki marine .


 Axixa ta fusata ta tunkude yatsan da yake nuna mata tace baka isa ba kai waye da xaka mare ni ka kwana lafiya? Ashruf ya bude jakarsa ya dauko brush ya matsi makilin ya ciko kwalabrsa da ruwa ya tafi gafe daya yana wanke bakinsa. Haushi da takaici ya lullube axixa tace dashi ashruf karya kake ke ce ka kawo ni nan don ka wulakanta ni ko kuma ka rama abinda na yi maka, ai ko a ina muke da bambanci nib! a sa’ar yinka b! ace kuma ina kara shaida maka sai ka raina kanka, ashruf xaka yi da na sani, dan talakwa…. Kafin ta cigaba da fadar abubuwanda xata fada sai ta ji saukar wani gwauron mari a fuskarta saida ta durkushe abinka da ‘yar hutu ga babu karfi jiki, kishirwa da yunwa sun fara lahantata. 

Ashruf yace kar ki mance da dokata ta farko duk sanda kika gaya min bakar Magana mari ne hukuncinki, doka ta biyu kuma daga yau kar ki kara ce min ashruf balle wane guldo sai dai kice min master, ta ukun kuma itace duk wani aikena da aikace aikace ba sai na saki ba, ke xaki dinga yi min. axixa dai na durkushe ta rike kunci, radadi da xogi yana ratsa mata kunci. Ashruf ya juya xai tafi ya ji axixa ta mike tsaye a fusace tace karya kake matsiyaci baka isa ba, ba a haifi uban da xai sani aiki ba. Karen daya yiwa uwargijiyarsa tawaye ya tafi ya bar ta, tana rufe bakinta asruf ya juyo a fusace ya sakar mata mari mai radadi fiye da na farko yace kar dai ki mance da dokar farko, wallahi wallahi idan baki gaji da fada min bakar Magana ba, ba xan gaji da marinki ba. yayi tafiyarsa ya bar ta a nan a durkushe tana kuka.


 Ya je ya tube kayansa ya saka dan gajeren wando ya dauko kwari da bakarsa ya shiga cikin ruwa ya kamo kifaye manya manya ya xo ya wuce axixa anan a xaune ta yi lamo, da kyar take daga ido ma ta kalleshi.ya wuce abinsa can axixa ta ji kaurin itace da kamshin abinci. Ta ji yawunta na tsinkewa kamar da ta ke ji. Ta lallaba ta hau kan wani dutse ta leka sai ta hango ashruf a xaune akan wata kujera ga wuta a gabansa yana gasa kifinsa a kofar wani daki. Mamaki ya kama axixa tace a ranta yanxu daman ashruf ya san wajenan harda gina daki ga itace gasu brush dinsa duk daman ya tanada ya xo da ni nan ya xauna don ya wulakanta ni.? 

Tana ta liken ashruf har kifinsa ya gasu taga ya sauke akan wani kwali yana gutsira yana ci ga ruwa a kwalba ya tara a jikin wani dutse da yake bulbulo da ruwa, yana cin kifi yana korawa da ruwa. Yawunta ya tsinke ta tuna wannan ta ware ta saka wannan ta ware akan yadda xa a yi ta ci kifin nan.


 Daga karshe dai ta tsaida shawarar ta je ta rokeshi ya bata kifin ta ci, tana tafe tana layi harta kai wajen da ashruf yake xaune, ta tsaya a gabansa tana kallonsa batace komai ba. ya daga kai ya kalleta yayi murmushi yace ke lafiya? Axixa tace ina jin yunwa ka bani kifin in ci. Ashruf yace a’a ba yadda xa a yi ki xo ki same ni haka kawai kice in ba ki kifi ki ci a wane dalili? 

Ko ni bawanki ne? 

axixa tace to nawa xaka siyar min? 

da kudi a jikina ta xaro kudi daloli cunkus tace na saya dollar hamsin.

 Ashruf ya harareta tace to dollar dari. Duk dai bai ce mata komai bata ce to dala dari biyu. Ya kawar da kai ya ci gaba da wurga lomar bakinsa. Axixa ta sake matsowa kusa tace to ga dollar dubu ta mika masa kudin duka. Ashruf ya kadar da kudin suka xube, axixa ta ciro sarkarta dankareriya ta daimon bama gwal bace da abin hannun sarkar tace, gashi duk ka hada ka bani kifin nan in ci yunwa nake ji. Ashruf yace bana son kudinki balle wani banxar gwal dinki idan kudinki yana da amfani ki dauka ki je ki sayo kifi, kin ga kuwa talaucina yayi min amfani tunda kamo kifin da nake yi ya amfana min a ko ina nake xan ci xan sha xan kuma sayar in sami kudi. Kin ga kuwa da nake tashi da asuba in shiga ruwa ba kamo kifi ba rashin hankali ba ne ba rashin aikin yi bane. Saboda haka kowa ya ci abinda yake dashi.


 Ke kuwa kudi kike dashi kici kudinki inci kifina. Gashi ma kifin manya na kamo ban kamo kanana ba ke kuma ba kya cin manyan kifi. A kamomin kanana. Ya ringa gwada yadda take yi masa yana shake murya yana rangwada wai yadda take yi. Axixa ta rushe da kuka ta durkusa a gaban ashruf tana kallonsa yana loma da kifin sa yana ta kwaikwayonta yana tsokana. Axixa ta mika hannu xata  gutsira don ita bata ma damu da abinda yake yi mata ba, don tasan ta musguna masa yanxu kuma lokacinsa ne. ita dai fatanta ya bata kifi taci don ta rayu kwanabiyu babu ci babu sha. Ya tare hannunta ya wurgar gefe gami da daka mata tsawa ya bata fuska yace ke ni nasan ki ne!? 

tashi daga nan ki bani wuri. Axixa tace ashruf ka bani kifin yunwa nake ji. Ashrfu yace meye dokata ta biyu, me nace ki ringa kirana dashi? 

Axixa tayi shiru can tace to master bani inci. Ashruf yace ya xa’ayi ga aikin master ke kuma ki xauna kina cin abinci, ki gamamin ayyukana mana, shiga dakin nan ki dauko kayana suna nan akan gado kixo ki wanke min. idan kin gama sai kixo in dan xuba miki kayoyi irin naku na karnuka ki kuma gyaramin wajen girkin. Kamar yadda tace masa ranar bikin xagayowar shekararta. Axixa tace master ka bani abinci inci sannan in wanke. Ya ce ai nima bakya bari na ina gama cin abinci kafin inyi miki hidimarki, don haka yanxu nan nake so karki kara sakon ASHIRIN DA HUDU .


 Axixa tana tafe tana tangadi kamar wadda ta sha giya ta nufi cikin daki, tayi mamaki da ta iske dakin tas ashruf ya tanadi komai nasa kamar a cikin gidansu. Ta kwaso kayan daya umurceta da ta wanke, ta fito ta nufi wajen ruwa ta wanke duk da dai babu omo taxo ta yayyaba su a jikin dutse. Tana tafe tana tuntube ta karaso wajen da ashruf yake a kishingide akan kujerarsa ta itace yana hutawa ya ci ya koshi. Ta xube sharaf ta xauna. Ahsruf ya dago ya kalleta yace, ke tashi ki koma daga can ki tube takalman ki kiyi min sallama ki shigo, yaya xa’ayi ki shigo min fada da takalmi ki xube min a gaba haka, babu na gama babu godiya babu komai? . 

Axixa ta mike da kyar ta koma baya ta tube takalmanta tayi sallama ta karaso xata xauna yace, a’a baki gama ba, banji kinyi godiya ba da na saki wanki. 

Axixa tace thank you master for honoring me with washing your clothes. Ta xauna ya miko mata kifin ta fara ci hannu baka hannu kwarya, ashruf na kallonta kawai ya ji wani sanyi a ransa, yace a ransa wannan ta fara sanin duniya kenan, sai ka bautu kafin ka samu abinda xaka ci ita aida daga sama take gani, tun daga kudin da xata kashe da suturar da xata sa har xuwa cinta da shanta. Shi yasa take daukar talaka marar hankali shi yaso yayi bauta kafin ya samu kudi.


 Bayan ta gama ci ta dauki kwalbar ashruf xata sha ruwa Ashruf ya kwace ya tuttular da sauran ruwan dake ciki yace, je ki debo naki. Axixa ta karba cikin sauri taje ta taro ruwa tayi ta moda saboda irin axababbiyar  kishirwar dake addabarta. Taji kifin nan kamar tunda Allah Ya halicceta bata taba cin abinci mai dadin haka ba, sannan ta farfado daga dishi-dishin  da take gani. 

Ashruf yace maxa tashi ki bar wajen nan kije ki kama bangaren ki don dakin kare  daban da na mutane. Axixa ta gallawa ashruf harara tace kai dai da kake kaine Karen ka fita ka kwana a waje, ni in kwana a daki. Mari ne hukuncin dokarsa ta farko, saukarsa ta ji a fuskarta.


 Axixa ta rike kunci ta tashi a sanyaye ba tare da tace masa komai ba, da kwalba a hannunta ta nufi wajen ruwa, ta duri ruwa a ciki ta xagaya bayan dutsen ta kama ruwa ta xo ta yi alwala ta jawo rigar sa da ta wanke ta yaba a jikinta ta harhada dai ta rufe gashin kanta ta tayar da ikamar salla ba tare da ta tantance ina ne gabas take ba, ta dai kintata. Haka axixa ta yi ta jero sallolin  da bata yi ba, sanda suke jirgi, harta idar. Ta daga hannu sama tana rokar Allah subhanahu wata’ala ya fitar da ita daga cikin wannan kangi, ya raba ta da sharrin ashruf.


 Ta rushe da kuka tace nasan na wulakanta ashruf na kaskantar dashi amma ni kuma kasa ya sassauta min. haka axixa ta yini tana a nan cikin yashi a xaune sai dai idan ta kintaci lokacin sallah ya yi sai ta tashi ta yi, la’asr haka magriba ma haka. Da taga gari ya fara duhu sai ta fara jin tsoro ta karaso wajen ashruf yake xaune. Shima yana jiran lokacin isha ta yi. Rigar ledannan ta ruwa ya yaba a jikinsa akan gajeren wandon da yake jikinsa don ya leka xai dauki kayansa ya sa ya iske tana sallah da su don babu yadda ya iya ya kyaleta ta ci darajar sallah, da yau ta gaya wa aya xakinta. saboda xureren sanyin da yake surarowa daga cikin barkaken tekunan ga duwatsu masu fitar da ruwa, sanyi wajen kamar kankara sai karkarwa sanyi suke. Can ba tare da kowa yace da kowa komai ba, ashruf ya mike ya fara sallar isha, yayi ya idar ya kawo shafa’I da wutirinsa a lokacin itama axixa tana yin sallar isha tana cikin yin shafa’I da wutiri ne taga ashruf yana hade kujerarsa da sauran karikacen sa yana mikawa cikin daki. Axixa tayi ta sauri kar ashruf ya shige ya barta, sai kuwa taga mutumin da gaske yake shigewarsa xaiyi ya dauki fitila. Axixa ta mike a guje tace jirani kar ka barni, ashruf yayi mata banxa ya shige daki ya banko kofa da karfi. Axixa ta rusa ihu mai firgitarwa tace yanxu anan dajin xaka shige ka barni? Cikin sanyin nan kuma gashi ina jin tsoro. Wayyo ina ‘yan uwana ne yau, ina dady na? kuxo ku ganni a cikin wannan hali. Ta fada jikin kofar tana kuka.


  Ta ji ashruf bai ce komai ba. ta tashi a fusace ta ringa fisgar kyaren kofar nan amma ina ta kasa budewa. Ta ce kai matsiyaci marar imani, dan talaka da bai iya samun waje ba, ka bude min kofa. Ashruf ya turo kofa ya bude, axixa ta ji dadi a ranta, ta dauka ya bude mata ne don ta shiga. Bata Ankara ba sai jin mari tayi tas! A kuncinta. Ya ce doka ta ta farko kenan kuma ba xan bude miki ba tunda ke ba muharramata bace. Yaya  xa’ayi ni da ke mu kwana a daki daya? 

Ko kina so ki kwana a shimfida ta  ne? 

axixa ta fusata tace Allah Ya kiyaye in hada jiki ko shimfida da alade. Ya sake miko hannu xai mare ta ta goce, yaja kofarsa ya kulle, ta fada a jikin kofar a tattakure tana ta sharbar kuka tana sake jin sabon imani a xuciyarta, tayi tunanin ashe masu gadi haka suke ji take wulakantasu, ya xamanto ko a barandarta suka xauna sai ta kore su. Ta tuna fulanin daji da suke cikin daji duk sanyi duk damuna.haka ta kasance. Ta ringa ganin kamar wani abu ne mai fararen kaya yake tunkarota. Sai ta rufe ido ta kankame tayi ta karanto addu’o’in da suka xo bakinta, harta fara gyangyadi harma dai ta bingire da a bakin kofa tayi ta barci saboda gajiyar da tayi. Bata farka ba saida taji ashruf na bude kofa, ya hankadata can gefe tayi firgigit ta tashi xaune taga ashruf ne ashe yake bude kofa, ya jefa mata kwalba yace ruwa nake so karki wuce sakon ASHIRIN DA HUDU .


 

 Axixa ta dauki kwalba ta nufi wajen wani dutse ta taro masa ruwan ta kawo. Ya kalleta yace ba kice ba. tace nagode master daka aike ni. Asruf ya yi murmushin jin dadi ya xaga bayan daki ya kama ruwa yayi alwala. Da ya shige daki sai ta dauki kwalbar ta je ta ciko ta d la ruwa, itama ta xagaya baya ta kama ruwa, ta xo ta yi alwala ta yi sallah anan kofar daki. Tana ganin ashruf ya fito da gajeren wando da kwari da baka ya nufi cikin ruwa. Axixa ta xo bakin ruwa ta tsaya tana kallonsa tana tunanin yau kuma wane irin aiki xai sa ta kafin ta ci kifin nan. Can ta ganshi da wani gundumemen kifi mai girman gaske. Ya xo ya wuceta, tana biye dashi a baya har suka je bakin kofar daki, wajen murhu. Ya harareta yace ba ki san dokata ta uku bane? 

Me nace miki? 


 Axixa tace, babu itacen da xan hura wuta, ashruf yace kije ki tsinto a can. Ya nuna mata wani waje. Ya ce da busassun itace. Axixa tace, duk jikin su kaya, ni kuma ba xan soke hannuna ba. ashruf ya daka mata tsawa yace maxa ta je ta yiyo itacen a minti ASHIRIN DA HUDU kafin ya kwada mata mari.  Axixa ta nufi wajen itacen tana hawaye. Ta sha wuya ainun kafin ta iya karyo itatuwan nan.

.

Comment da sharhi su suke kara mani karfin guiwar yimuku nagode

[8/28, 9:46 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[8/28, 9:48 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU 

*4*

.

.

 Nan duk ta caccake hnnunta. Ta tuna kauyawa matan da take gani da himilin itace sun karyo, kuma su xo su dafa abinci, yau itama gata ta gamu da irin wannan rayuwa. ta kawo ta jifge a gaban ashruf wanda yake a kishingide a nan  kan kujera yana jiran dawowarta, yace ta dauki kifin nan ta je wajen ruwa ta wanke shi tas, ta ciccire bawo-bawon bayan. Da kyar axixa ta kinkimi kifin nan ta wanki ta xo ta hura wuta ta dora. Ya ce ta dauki kwalbarsa ta je ta ciko masa, ta dauka da sauri ta ciko. Ta dawo, ta xauna, ashruf  yace tashi ai ba ki gama ba. axixa ta mike tsaye tana kallon ashruf xuciyarta cike da tsanar sa, yace ina so ki dan taka mun rawa ina kallonki ina kallon kifina yana gasuwa. Axixa ta yi shiru ba tace komai ba tana dai tsaye. Ashruf yace kina bata min lokaci ki yi min rawa malama. Axixa tace, ashruf baka isa ka wulakanta niba, kar ka ga tun jiya kake marina kana sani aiki duk don ka ga ina yi shi ne xaka ce in yi maka rawa ko, to ko xa ka kashe ni ba xan yi maka rawa ba. kai har mutumin da ka isa  ka yi min Magana ne balle ma ka dake ni. To ina mai sanar da kai ashruf jaki ko alade sai sun fika daraja ka kuskura muka fita daga wajen nan, idan ba ikon Allah ba da ya rubuto min kaddara, da ko akan tamarma daya xa mu xauna ne? balle daki daya ka kulle kofa dan rashin imani da rashin ilimi ka bar ni a waje kana ciki harda cewa ko shimfidar ka nake so in kwana,? Allah Ya yi min sutura ai, ni in hada hannu da kai balle jiki ai gara na kwana da alade ko jaki.


 Ashruf ya mike a fusace ya kai mata mari sai ta goce, ta kwada masa mari, ya fusata ya kai hannu xai rarumota, ta sa kafa ta dake shi a ciki ta xura da gudu tana cewa na fi so ka kasheni a dajin nan daga kai sai ni ko gawata ma ka jefa a ruwa kar iyaye na su ga gawar.

 Ashruf ma na bin ta guje yana cewa tun da mutuwar kike so ki tsaya mana, ya kike gudu? Kuma yau ba xa ki hada jiki da alade ba da nixa ki hada yau, sai na nuna miki karshen iskanci. Suka yi ta tsere a cikin yashi tulus, can ashruf ya sa kafa ya fyade ta ta fadi fuk! Ya damke ta yace da ki hada jiki da ni gara ki hada da alade ko? to yau xa ki gani. Axixa na dukansa tana xagi, tana ihu. Ashruf ya fisge mata kaya da damban tsiya tun tana kokarin fixgewa ta gudu, ta ji ya shaketa da wannan karfaffan hannayen nan nasa. Tun tana da karfin ihu harta kasa ihu, ya danneta yagama biyan bukatar sa da ita sannan ya dagata. (KALU INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN)


 Abin tausayi axixa cikin jini dan yayi mata jina-jina, ya yi tafiyarsa ya nufi wajen murhu ya manta da kifin da yake gasuwa, wanda tuni ya xama gawayi ya kone kurmus. Ya kashe wutar ya shigewar sa daki, axixa na nan kwance ta kasa kuka ta kasa ihu. Addu’a kawai take Allah Ya dauki ranta a inda take karta kara sakan daya don bata da amfani a duniya kwata-kwata. Can bayan rana ta kwalle xafin rana yana dukanta, ta kokarta da kyar ta mike, ta sassaka kayanta tana rarrafawa harta karaso kofar dakin ta leka cikin dakin bata ga ashruf ba. ta leka bayan dakin baya nan, ta xaga bayan dutsinan nan duk babu ashruf . ta rusa kuka tace, daman ya kawoni nan don ya yi lalata da ni ya gudu, ya bar ni a dajin nan? Ta yi kuka harta godewa Allah. ga yunwa ga kishirwa don rabonta da abinci tun na jiya da safe, wata yunwar ce kuma ta addabeta ga uwa uba tsananin bakin cikin abinda ashruf yayi mata, xuciyarta na kuna gashi duk ya ji mata ciwo, sai radadi. Axixa bata taba ji gara ace tana kabarinta da rayuwar duniya ba sai yau.


 Ta ce a ranta ta san har abada ta yiwa farin cikin rayuwa bankwana ta san ba ita babu wani sabon jin dadin duniya. Tun daga inda Allah Ya kawota. Da kyar ta mike ta sake tube kayanta ta shiga ruwan daya ke bulbulowa a jikin wani dutse, ta yi niyyar yin wankan janaba, ta wanke ko ina. Ta gama ta dauro alwala, sannan ta xo ta saka kayanta, tana ta leke-leke dai ko ta hango ashruf amma bata ganshi ba. ta shiga daki, ta xauna ta takure babu abinda take sai tunani da hawaye ta tuna abubuwa da yawa wanda take jin sa wai, wai a gari, yau gashi duk sun faru a kanta. Ta kintaci axahar ta yi ta tashi, ta yi sallah, ta idar ta koma ta xauna, yunwa da kishirwa sun addabe ta ta dauko wannan kwalbar da suke shan ruwa ta lallabo a hankali don kamar ta fadi take ji, saboda jiri.  Taje wajen dutsen ta tari ruwa, ta yi ta modar ruwan nan ta ciko ta shanye ta sake cikowa ta shanye, har sau uku sannan ta koma daki ta xauna. Ta ji cikinta nata murdawa don bata ci komai ba, ta modi ruwa. Abu dai kamar wasa cikinta ya ci gaba da ciwo, sai aman ruwa tayi ta kwara amai a tsakiyar dakin nan, kamar xata mutu, abin tausayi. Ta ji kamar daga sama an ce sannu. Ita ai a xatonta nesa ce ta xo kusa ko mutua ce ta xo an xo daukar ranta. Ta daga kai a hankali ta kalli dogon mutumin da yake tsaye a bakin kofa, sai taga ashruf tsaye rike da wani gasashen kifi a kan kwali a hannunsa.


 Ta sunkuyar da kai ba tare da ta amsa ba, hawaye na xuba daga idanunta. Ya karaso inda take, ya ajiye kifin a gefenta ya dauki kwalba ya fita. Can da aka jima sai gashi ya ciko kwalbar nan da ruwa, ya xo ya ajiye a kusa da kifin, ya debo yashi ya xuba akan aman nan da ta sharara, ya dauko tsintsiya da wani kwali ya kwashe, ya fita ya xubar. Sama da minti goma axixa taga ashruf bai dawo ba, ta mike da kyar ta leka waje taga baya nan, ta fito sosai ta yi ta lellekawa ko ina bata ga ashruf ba. ta dawo ta xauna a gaban kifinta, amma kanta ya daure tana tantama ma ko kifin ba ita ya kawowa ba, karta ci ya xo ya mareta, ko ba nata bane. Can wata xuciyar tace ke naki ne. ke ya kawo wa gashi harda ruwa ya debo miki. Sai ta tsayar da shawara kawai ta ce kifin nata ne. ta fara gutsirar kifin nan tana wulka loma kamar ta hada da yatsanta ta hadiye. Axixa ta yi ta cin kifin nan ba kakkautawa saida ta ji, ta yin at! Ta kora ruwa. Ta tura sauran kifi gefe, sannan ta tashi ta yi sallar la’asar, ta ci gaba da laximi tana tunanin duniya. Ta ji tunda take da ashruf bata taba jin ta tsaneshi ba irin ta yau, tsana mai tsanani akan abinda yayi mata. Kuma bai taba yi mata abinda taga ya taimaketa taji dadin taimakon da yayi mata ba irin nayau, don ya bata abinci ta ci a lokacinda take tsananin bukatarsa. Haka dai axixa tayi ta tunani, ita tada, da ta yanxu. Halinda take ciki ta daga hannu ta roki Ubangijinta madaukakin Sarki ya sawwake ya yassare mata ya fitar da ita daga wannan kangi da take ciki. Har duhu ya fara ketowa wato magariba tayi, taje ta kama ruwa, ta dauro alwala. Nan ma tayi ta leke-leke ko xata hango ashruf amma bata ganshi ba, ta shiga daki ta yi sallar magariba da aka jima ta tashi tayi sallar isha’I, ta yi shafa’I da wutiri ta xauna tana jiran ashruf ya xo ya kwanta waje in xai kwanta. Don haka ne ma yau ta yi shigar sanyi sosai fiye da jiya don ta sha wuyar sanyi jiya. Ta loda tsummokarai a jikinta wai ita idan an kwanta a waje ta samu saukin sanyin. Ta yi ta sauraron xuwan ashruf shiru bai xo ba, harta fara gyangaydi a xaune, ta yi kamar xa ta fadi ta bude ido taga bbu kowa, har dai ta mike ta laluba saboda dakin duhu ta leka waje da ke da hasken wuta ta hanhanga babu ashruf babu motsinsa. Ta yi tunani da tambayoyi a ranta ina ashruf kuma yayi? Ko me yake nufi da yake tafiyarsa wani waje? Kar dai ya hada baki da wasu ya tafi ya bar ni su xo su kasheni, ko kuma su saceni ma kwata-kwata.


 Ta ji jikinta na karkarwa wani tsoro mai tsanani ya lullube ta fiye da na sanda ta kwana a waje ma. Ta jawo kyauren kofar dakin ta rufe gam, ta sa tsumma ta daure ta rufe windon dakin, ta bi ta tottofa addu’o’I a kowace kusurwa. Ta jawo sauran kifinta da ta rage da rana ta ci, don yunwa kuma ta kara kamata ta kora ruwa, ta laluba ta hau gado. Ai sai ta ji gadon nan kamar wanda aka saka masa katifar auduga don laushi, kan ka ce kwabo barci mai dadi ya saceta, ga dumi ta kudindine da tsummokarai, dumin rus. Rabonta da ta ji dadin barci irn na wannan ranar tun da ta baro jirginsu, yau kwana uku kenan. Babu yunwa ba kishirwa, babu sanyi ai ita ko a maparki ma bata tuna ma a cikin kungurmin daji nan take ba. ta dauka a gida take, duk gabobinta ciwo suke ga ayyukan da ta ringa yi bata saba ba, ga kuma murkushewar da ashruf yayi mata, cinyoyinta sai sara mata suke don xugin radadin ciwo ta yi ta mika tana juyi cikin barci. Bata ma san gari yawaye ba, har rana ta fito ral ta kawalle. Can ta yi juyi xata koma barci, sai taga haske ya gauraye dakin, tayi firgigit ta farka, ta tashi xaune sai taga ashe har gari yawaye, bata sani ba, tayi salati ta yunkura xata mike sai ta ji ta kasa saboda ciwon da jikinta yake yi mata. Ta sake cije baki ta yunkura, ina ta kasa duk jikinta yayi tsami, sai ta fashe da kuka, kuka mai tsanani tana cewa ashruf ka cuce ni ka cuci rayuwata, ka yi min fyade ka ruguxa min rayuwata.


 Tayi kuka harta gaji. Sannan ta sulalo ta sauko gada kan gado, tana rarrafe ta karaso jikin kofa, ta kama ta mike tsaye, ta kwance tsumman da ta daura kofar ta ture kofar ta leko, bata ga kowa ba. ta fito waje bata ga kowa ba, ta waiga ko ina sai ta hango wani abu an kife da kwali a bakin kofar dakin, ta karasa wajen ta bude sai taga gasashen kifine da gasassun tsuntsaye guda biyu. Sai kamshi, ga maiko nasha-nasha ya tsatso a jikin tsuntsayen, a wannan karon har da gishiri a gefe. Abin ya bawa axixa mamaki, musamman ma gishirin nan da ta gani, da tsuntsayen. Ta kinkima xuciyarta cike da farin ciki ta mike daki ta fito ta kama ruwa da kyar ta tsugunna da kyar ta mike tayi alwala, ta shiga daki ta yi sallah. Bayan ta idar ta yi addu’o’inta, ta jawo gasassun tsuntsayen nan da kifin nan tana dangwala gishiri, ba lami shataf din da suka saba sinkimar kifinsu a haka ba, gashi yau ta sami canjin gasassun tsuntsaye . Ta ci ta koshi, harta rage ta ture gefe guda, ta rufe ta sha ruwa, ta koma gefe ta xauna, ta yi ta godewa Allah, don ta fara ganin canji a rayuwarta tanan. Haka aixa ta kasance a jima ta tashi ta lelleka ta hau kan dutse ta leka ko ta hango ashruf ko wani ma amma babu kowa sai tsuntsaye da suke shawagi a sararin samaniya wasu kuma sun sauko suna shan ruwa. Lokacin sallah yayi ta yi alwala ta koma daki ta yi salla ta fito ta sake dubawa taga babu kowa har dai dare ya yi ta ci sauran kaifinta da tsuntsayenta tayi sallahr isha ta kwanta.


Washe gari da sassafe tana fitowa ta sake yin ido hudu da gasashen kifi da gasassun tsuntsaye da gishiri a gefe, irin na jiya. Abin yakara daurewa axixa kai, tace a ranta to ko ba mutum bane yake xuwa ya ajiye min abincin nan? Ta ce in jiya na makara ban tashi da wuri ba, yau ai da wuri na farka yaushe aka kama kifi da tsuntsaye har aka gasa? Tayi ta yiwa kanta da kanta tambayoyi, daga karshe ta kinkimi kwalin da aka dora mata kifin da gasasun tsuntsaye da gishirin a gefe ta shigar daki, ta yi alwala ta yi salla, ta yi Karin kumallo da abincinta, ta rage na rana da dare. Kwanci tashi yau kwanan su axixa tara da baro jirginsu suna wannan dajin, kuma tun san da ashruf ya kwashe wannan aman da ta yi rabonta da ganin shi kenan, ko motsin sa bata ji kuma kullum da safe idan ta bude kofa sai taga gasassun tsuntsaye da kifi dadan gishiri a gefe an kawo an ajiye mata. A yau axixa ta kudiri niyyar ita kuwa yau ba xa ta yi barci ba kuma a waje xata labe ta kwana taga mai kawo mata abincin nan. Don haka ne ma ta yini cur tana sharar barci, da rana don da dare kar barci ya hanata labewa. Can bayan ta dade da yin sallar isha, misalin biyu na dare axixa ta bude kofar dakin ta leko waje ta kalli inda ake ajiye mata abinci, taga ba a kawo ba sai ta fito waje ta tura kofar dakinta ta rufe ta koma bayan dakin ta xauna, ta kudindine ga sanyi yana xurarta tana karkarwa, amma ta daure ta ci gaba da xaman jira. Can bayan fitowarta da kamar awa uku wato misalin karfe biyar na asuba.


 Ta fara jin motsin wani yana tahowa ta mike a hankali tana sauraron daga inda take jin motsin tahowar. Can ta hango wani mutum rike da wani abu a hannunsa ya doso wajen dakin ta yi saurinta xata daya gefen don kar ya hangota, ya xo ya wuce, ta sake matsawa wani gefe kar dai ya ganta, sai taga ya xo bakin kofar dakin ya ajiye abinda ke hannunsa, ya juya ya tafi da sauri. Axixa na kallonsa bata gane dai ko waye ba. kamar ashruf kamar kuma bashi ba, taga ashruf ya fi wannan ‘yar kiba kadan kuma bai kai wannan tsawo ba, kuma yana yi mata kama da mace don lullubi yayi ya rufe kansa kiruf da mayafi. Don haka dai bata gane mai kawo mata abincin ba, sai ta tsayar da shawarar ta bishi a baya ko ta bi ta a baya taga ko waye, ko kuma ko wa cece, daga ina kuma? Sai da ta bari yayi ko ta yi nisa, sannan ta fara bin sa, ko binta a baya suka yi ta tafiya a cikin yashi, taga mutumin ko mutuniyar bai daina tafiya ba, ta ji kamar ta koma kada fa ba mutum ba ne. wata xuciyar tace to me nene ma in kin bi shi kin mutu daman me yayi saura a rayuwar ki? Ai da wannan kuncin da kike ciki gara ki mutu ki huta, ta ci gaba da bin mutumin nan. Sai ya yi kamar xai juyo ya ji motsi a bayansa sai ta yi sauri ta tsugunna ya ga babu kowa, ya juya ya ci gaba da tafiya, tana biye dashi harta ga ya tsaya a gindin wata katuwar bishiya mai girman gaske , itama ta sami bayan wani dutse ta labe, gari yana dada washewa. Mutumin nan yayi alwala  daya tada ikamar sallah, sai ta lallabo bayan bishiyar da yake yin sallar ta tsaya, taga murhunsa da yake gasa kifi ga kwari da bakarsa ga tarkacen kayansa nan da tsummokarai a lubge dasu yake shinfida. 


Ta ji yayi sallama ya idar da sallah yana ta laxumi yana istigifari, can taji yayi firgita ya mike yana cewa subhan Allahi yana karkade jikinsa. Axixa ta ji gabanta ya fadi ta sake makalkalewa a jikin bishiya a tunaninta ko ya hango inuwarta ne. ta ji ya dauki itace yana ta bugun kasa sai ta ji shiru kuma kamar babu kowa, ta lallabo ta leko sai taga  mutumin ya sunkuyar da kai kasa ya rike yatsan kafarsa. Ta yi ta kallon mutumin taga dai bai dago ba, ta sake lekowa saosai tana kallonsa harda tsugunnawa da leka fuskarsa sai kuwa ta gane ko wa nene, ashruf ne. tafito daga laben da take ta matso kusa dashi ta tsaya, ya dago kai da sauri ya kalleta sai ya mike tsaye a sanyaye cike da mamakin yadda aka yi ta xo inda yake, suka kurawa juna ido ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba. can axixa ta sunkuyar da kai kasa, ta kalli kafarsa sai taga jini yana xuba ta babban dan yatsansa can gefe kuma gawar wata katuwar kunama ce baki kirin mai girman gaske, tace ashruf daman kana nan, nan ka dawo? 


Yace ina nan axixa, ya aka yi kika san ina nan? 

Axixa ta yi shiru ba tare da ta bashi amsa ba, sai hawaye ne ke xubowa daga idanuwanta ta koma gefe jikin wani dutse ta xauna takifa kai a gwiwa ta yi ta sharbar kuka. Ashruf na tsaye yana kallonta shima abin duniya ya isheshi, yana dingishi ya karaso wajen da take xaune. Ya ce axixa ki yi hakuri kuma ki yafe min na san na cuce ki na kuma fi cutar kaina ba ke kadai na batawa ba na sabawa mahaliccina. 

Axixa ta dago ta dube shi haushinsa ya sake kamata tace yanxu me wannan rayuwa ta kara mana? Dube ka ga yadda ka xama, kafar ka jini hannunka ciwo a daure ka rame ka yi baki ka fita hayyacinka, balle kuma ni kalleni mun xama marayu marasa gata mun ma fita daga cikin jinsin bil’adama mun koma jinsin dabbobi koma ince aljanu. Da ka yi min haka dame ka karu yanxu? Ka cuce ni ashruf babu mai yi mana wannan hisabi sai Allah.

 ashruf yana tsaye yana kallonta, can ya nisa ya  sunkuyar da kai kasa, yace, na ji na kuma yarda ni na saki a cikin wannan hali. Amma kar ki manta ke kika fara sani a halin da na tsani kaina da kaina kuma na tsani rayuwar duniyar kwata-kwata ki ci min mutunci ki yi min wulakancin ma harta kai ta kawo na fita daga sahun mutane na koma kare, kin xamar da ni jaki aiki na ke miki kina xagina.


Ni a wajena wannan rayuwar da muke ciki ta fi min rayuwar da na tsinci kaina tare da ke a cikin jirgi, abu daya na yi miki wanda ban ji dadi ba kuma ba yin kaina bane shi ne dana yi miki fyade. A matsayina na dan musulmi na sabawa Allah na kuma xalunce ki ban kawoki nan don in yi amfani da ke ba, wallahi ko a mafarki ban taba sha’awar in taba jikin wata mace ba da sunan xina, arna ma ba musulma er uwata ba. don haka ne ma na kauro nan ina ta yin istigifari akan mummunan laifin da nayi, kuma ke ma ina niyyar in xo in sameki in nemi gafararki ki yafe min. amma na kasa ina jin kunyarki axixa.


Ta goge hawayen da yake xubo mata tace, haka ne ashruf, na bata maka watakila ma fiye da yadda ka yi min na kuma gane kuskure na, abin kuma da ka yi min tunda ba da niyya ba haushin Magana tace dan nace da in hada jiki da kai gara na hada da alade shi yasa ka yi min haka, na yafe maka. Allah Ya yafe mana mu duka. Ashruf yace amen. Ya durkusa yace, nagode. Axixa ta ci gaba da cewa abu daya kuma ya rage da xaka yi min, shine ka mayar da ni wajen en uwana ka fitar da ni daga rayuwar dajin nan. Ashruf yayi shiru can ya nisa yace to axixa abu daya xamu yi shi ne addu’a Allah Ya kawo masu nemanmu  su ganmu su tafi da mu don ba ni da wata hanyar fita daga nan, kin ga jirgin nan daya kawo mu ya farfashe, injin ya daina aiki, ya ma gutsure a cikin ruwa babu yadda xa a yi ya gyaru. Axixa ta fashe da kuka tace yanxu shi kenan rayuwar mu a nan xata kare? Ashruf ya durkusa a gabanta yana rokarta ta yi shiru komai xai daidaita da ikon Allah, haka axixa ta dauki lokaci mai tsawo tana kuka ashruf na lallashinta, yana bata baki.


A ranar axixa tace ashruf ya kwashi kayansa daga nan suka tafi wajen da suke, sabo da nan inda ashruf yake kusan kullum sai kunama ta cije shi harda gawarwakin macixaan da suke sulalowa xasu sare shi ya gansu ya kashe su.  Don haka ko dogon brci baya yi. Haka axixa ta yini cur a daki tana tunani ta tuna wannan ta tuna wancan hankalinta ya dan kwanta ganin sun shirya da ashruf babu xancen mari da bautar da ya ke ta sata, amma kuma hankalinta yayi mummunan tashi daya ce shima bashi da wata dabara da xai iya yi jirgin nan ya tashi, su bi ‘yan uwansu. Ko su bulla wata kasa ta kusa da inda suke. Hawaye yayi ta xuba daga idanuwan axixa harda shishshikar kuka, ashruf yana kofar dakin yana jiyota hankalinsa ya yi mummunar tashi fiye da na axixar don shi ma yanxu abun ya sha masa kai. Can la’asar sakali, axixa ta fito daga daki, tana so ta dan watsa ruwa a jikinta amma sai ta iske ashruf xaune a kofar dakin. Nan dai ta yi dan xagaye tana lelleka ina ne xata iya xuwa ta yi wanka bai hangota ba. shi dai yana xaune yana kallonta, ita kuma ta rasa yadda xata ce masa, ya tashi xata yi wanka. Da kyar tace dashi jakar  taka ko da sabulun wanka? Don naga harda guxirin makilin ka yi.ya yi murmushi ya jawo jakar da take gefensa ya xaro wayar tafi da gidanka ya mika mata yace axixa ki yafe ni ga wayar ki har caji ta kare , kiyi hakuri. Ta karba ya xaro sabulun wanka, ya dauki makilin da sabon burushi ya mika mata, mamaki ya rife axixa don ita bata taba xaton da sabulu a wajensa ba, ta dai tambaya ne kawai don ya gane ya tashi xata yi wanka, sai gashi harda sabon burush da makilin duk ya taho dasu, maimakon haushinsa ya kamata da ya miko mata wadannan abubuwan musamman…..

.

Allah sarki masoyiya ta....

Yanzu wasu zasu ce ina kallon ta wani kare yana bautar da ita na kasa komai, kuma alhali sadin Maa tace wai kada na neme ta, matan ma gaba daya tace wai na daina kulawa,

Ya kuke gani?

Na bi maganar ta ko na yi watsi da maganar ta na ceto masoyiya ta?

Comment da sharhi su suke karamana karfin guiwa na gode

[8/28, 9:48 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/1, 6:10 PM]  "  D'Y: KWANA ASIRIN DA HUDU

*5*

.

.

 Maimakon haushinsa ya kamata daya miko mata wadannan abubuwan musamman ma wayar sai da caji yakare sannan ya bata, sai aka sami akasin haka ita faranta mata rai yayi ta yi masa lallausan murmushinda koda wasa bata taba yi masa ba, tace nagode. 

Ashruf dai kawai ya bude baki yana kallonta don a gaskiya ba karamin kyawunta ya gani ba da ta yi masa wannan lallausan murmushi da wani kallon faranta rai, tace xan yi wanka. Ya jawo jakarsa ya rataya ya mike tsaye, shima ya sakar mata wani hadadden murmushi yace to uwargijiyata axixa bari in baki waje. Ya juya ya nufi bayan daki, tace a’a ina xaka kuma ka yi can? 

Shiga daki man ka jira na gama.

 Ashruf ya dawo ya shiga daki kamar yadda ta umurceshi, ko wannensu fuskarsa cike da annuri da yiwa juna lallausan murmushi, sai bayan da ashruf ya shiga daki ne ya dinga mamakin irin wannan murmushi da suka dinga yiwa junansu yana cewa to koma ba dashi ta ke ba.


 Da daddare bayan sun yi sallar isha’I sun idar sai axixa ta dauki mayafin lullubarta xata fita waje ta kwanta, ashruf yana kallonta ya ga dai da gaske take fitar xata yi, yace, wai shirin me kike yi ne ? axixa ta sunkuyar da kai kasa tace xan fita bakin kofar dana ke kwana. 

Ashruf ya yi murushi yace axixa kenan yaya xa a yi ni ina daki ke kina waje? 

Da din ma da kika kwana a waje ai rashin fahimtar juna ne, ina ganin yanxu mun koma da, ni mai aikin ke uwar dakina. Don haka yi kwanciyarki a daki nixan fita. Ta yi kasake tana kallonsa ya juya xai fice sai ta mika masa tsummokaran da ta diba na lulluba ya karba, sai ya rage ya dauki guda biyu ya mika mata biyu yace ai dakin ma da sanyi ki rufa da wannan. Axixa ta karba a sanyaye tana kallonsa har ya fice ya tura mata kofa ya rufe. Ta koma ta xauna a gefen gado tana tunani mai rikitarwa, ma’ana ta tsinci kanta a cikin tunanin ashruf game da tausayin sa da nadama a kan abinda ta yi masa a baya, da tsananin son ta ji labarinsa ko shi wa nene, ta dauki tsawon awa guda xaune ta yi tagumi ta tsunduma tsundum cikin tunani, sai ta ji wata murya wacce ta yi mata kama da muryar wanda take muradi. Ya ce madam axixa ba ki kwanta bane nake hango fitila a kunne? 


 Ta yisauri ta daga ido ta kalli wajen da take jiyo sautin maganar, sai taga ashruf tsaye a jikin windo ashe ma windon a bude ta bar shi. Ta yi murmushi tace ba mu kwanta ba dai don kaima gaka a tsaye . Murmushi yayi, yace gadin ki nake uwar gidata, mai gadi kuwa ai ba a sanshi da barci ba. tace ni kuwa bana son irin wadannan kalamai su dinga fitowa daga bakinka kai da ni duk mun xama daya, sai dai ni in ce nice mai aikinka kaine master. Ashruf yayi shiru ba tare daya san amsar da xai bata ba. yayi murmushi yace good night. Ya rufe mata windo ya tafi, itama ta kashe fitila ta hau gado ta kwanta.


 Da asubar fari ashruf ya fita kamun kifi da sassafe ya harbor tsuntsaye guda uku, ya xo ya hada wuta ya fara gasawa.duk hada-hadar na da ashruf yake, axixa bata farka ba, tana sharar barci abinta. Sai can rana ta fara fitowa kamar wajen karfe takwas na safe sannan ta farka, ta yi salati ta yi mika gami da saukowa daga kan gado da sauri ta bude kofa, tana budewa ta yi ido hudu da Ashruf akan kujerarsa a xaune yana murmushi ya ce barka da tashi. Axixa ta Harare shi ta ce ka san gari ya dade da wayewa amma ka ki ka kwankwasa min kofa, in tashi in yi sallah.? 

Ashruf yace baki bani ixinin in yi miki haka ba, amma gobe da asuba xan tashe ki, ki yi hakuri. 

Ta yi murmushi tace ko xa ka kara bani aron brush din jiya da makilin? 

Ashruf yace ga su can a gaban duten can na kai miki, ya nuna mata dutsen. Ta je ta iske ya cika mata kwalba ga brush da makilin a kan wani  kwali ya ajiye da sabulu a gefe.


 Da ya ga ta nupi wajen saiya dauki abincinta ya shigar mata daki, can da aka jima axixa ta shigo sai ashruf ya mike xai fita, axixa tace, ya haka ina xaka je ne?  me ya sa kake gudu na ne? idan na fita ka shigo idan na shigo ka fice baka kaunar ka ganni a kusa da kai ne!? 

asruf ya girgixa kai yace, ba haka bane. Axixa tace to me nene? , 

y ace haka kawai. 

Ta ce to in haka kawai ne ba hujja bace ka dawo ka xauna. Ashruf ya yi murmushi ya dawo ya xauna ta ajiye brush da makilin akan loka tadau wani mayafi ta yafa ta tada ikamar sallah. Bayan ta idar ta shafa addu’o’inta, sai ta juya ta kalli ashruf tace good morning. Ashruf yace assalamu alaikum. Axixa ta yi dariya ta ce assalamu alaikum ya kamata musulmai su rinka cewa ‘yan uwansu musulmai ko? 

Ashruf yace shi ne lada ba good morning ba. ashruf ya jawo gasassun kifi da tsuntsaye ya tura gabanta. Axixa ta yi murmushi tace yaushe kake tashi ne har ka kamo kifi da tsuntsaye ka gasa? Ga sunan da dumi daga gani yanxu aka gasa. Ashruf yace mutum da aikinsa kuma sana’arsa. Axixa ta gutsira ta ji yau gashin da gishirinsa aka gasa shi yasa taga babu gishiri a gefe. Ta kalli ashruf tace yau kuma wata sabuwar dabara ce da gishirin ka hada ka gasa? 

Ashruf yace ina fatan dai ba santi kike yi ba.? 

axixa tayi dariya tace yanxu dai xan yi tambayar santin, na dade ina tunanin inda kake samo gishirin nan don naga farkon da muka xo ba ma ci da gishiri sai daga baya,


 Dashi ka xo ko kuma akwai bishiyar gishirin anan ne? 

su duka suka tintsire da dariya, ashruf yace bishiyar gishiri kuma daman  gishiri bishiya ce? Ai a cikin ruwa nake samu, shi gishiri ai ruwa ne ko wane taku mai girma akwai dandanon gishiri da xaki ji ruwan ma yana yi, to idan kika debo ruwan kika yi ta dafawa har ruwan yakone, to sai ki ga gishiri a kasan. A nan na sami gishiri da yawa muke tsakura  muke cin abinci. Axixa tace to na tuna mun yi a chemistry. Ta ce sauko mu ci. Ashruf yace ai ni tunda sassafe na karya wannan naki ne duka kiyi ta ci. Axixa tace ni ya min yawa. Ashruf yace ki ci ki rage na rana da na dare kuma xan gasa. Ya mike ya fice ba tare daya ce mata komai ba. shiru bai dawo ba, harta gama cin abincinta bai dawo ba. ta fito ta leka ko ina baya nan. Sai ta shiga tunani tana cewa ina wannan yayi kuma? Kamar aljan a ganshi kuma a rasa shi. Ta hau kan kujera ta xauna tana waige waige ko daga ina xata ga bullowarsa? Sai can ta hangoshi da himilin itace a kafadarsa, ta tareshi da sauri ta kama masa suka sauke. Ya yi wani gwauron numfashi gami da ajiyar xuciya. 


 Ta kalle shi ta yi murmushi tace, sannu da kokari. Ashruf yace yauwa. Suka dunguma xuwa gindin wata bishiya mai sanyi don rana ta fara takewa suka xauna. Axixa na xaune kan kujera ashruf na xaune a kasa kan yashi nan fa suka fara taba hira. Axixa ta kalli ashruf tace ashruf ba ni labari . Yayi murmushi yace labari yana wajenku mai girma axixa. Axixa ta lumshe ido tace labarin rayuwarka da masoyiyarka ta kasarku. Ashruf ya tunstire da dariya harda buga kafa a kasa, tace ai dariya ma naba ka? 

Ashruf yace muguwar dariya ma, ina kika taba ganin talaka da soyayya? 

Ta ce talaka baya soyayya? 

Ya ce ni dai bana yi, duk inda kika ganni aike na je yi in samu na cin abinci. Ta ce wato  kai ne ina xaka? Aiki ina ka fito aiki. Ashruf yace kwarai kuwa. Ta ce yanxu ko da wasa babu wata daka taba gani a duniya ka ji kana sonta tun farkon rayuwarka har yau? 

Ya ce na taba yi kuma ban taba yi ba. ta Harare shi ta ce, me kenan kake nupi? 

Ya ce ke dai ban taba yi ba. axixa ta tsuke fuska ta mike a fusace tace bari ma in bar maka wajen nan tunda baka so muyi hira. 


 Ya mike da sauri ya tari gabanta yana cewa yi hakuri ki dawo ki xauna xan fada miki. Irin dan jan lokacin nan nake kada hirar ta mu ta kare da wuri. Ya bata dariya sai ta tustire da dariya tace, to xan dawo bari dai in sha ruwa, cikin sauri yace koma ki xauna in je in debo miki. Ta koma ta xauna amma sai  ta xauna a kasa, ta mike kafa. Tun da ga nesa yake cewa ya kika xauna a kasa? Ya karaso ya mika mata ruwa a kwalba tace thank you, ta karba ta sha shi dai yana tsaye a kanta, ta ce xauna akan kujerar ba komai na fi son xaman kasar. Bayan ya xauna ta kalleshi ta yi musrmushi tace na fa gode.

 Ashruf yace ni fa bana son yawan godiarnan da kike yi min ai aiki nane. Can dan da aka jima ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba, axixa ta nisa tace nikuwa ashruf ina da tambaya ko xa ka bani amsa? ashruf ya tsareta da wadannan kwaxa-kwaxan idanuwansa yace, me xai hana in baki amsa uwargidana axixa. Ta yi dan murmushi ta sunkuyar da kai kasa tana dan xane-xane da tsinke a kasa ta dago tace ashruf wai don Allah me ya sa mutum yake jin ya tsani mutum ne? 

ahsruf yace  ban gane tambayar ba. axixa tace xaka ga wani lokaci idan  xama ko tafiya ta hada ku da wani mutum sai ka ga jinin ku bai hadu dashi ba, kawai ka tsaneshi shima ya tsane ka.

 Ashruf yace ba yadda xa a yi mutum ya tsani mutum haka kawai sai dai idan da dalili, kin ga na farko watakila daya yana yiwa dayan mummunan hali yana uxxura masa baya kyautata masa don haka sai tsana ta shigo.


 Ta yi shiru tana dan tunani can ta nisa tace haka ne, to me kuma yake sawa, daga baya mutum ya ji yana son mutumin daya tsana? 

Ashruf yace kyautatawa ce kuma take sa soyayya. Ta ce mu a can kasar mu a yarenmu na hausa, hausawa suna cewa kiyayya bata xama soyayya, wai babu yadda xa a yi kana kin mutum daga baya kuma ka xo ka ce kana sonsa. Ashruf yace in dai hausawa ne ba haka suka ce ba, hausawa sun ce soyayya bata xama kiyayya sai dai kiyayya ta xamo soyayya. Axixa ta xaxxaro ido tace ashruf ina ka san hausawa balle ka san me suka ce? 

Ashruf yace kika sani ko ni bahaushe ne? 

tace babu abinda ya hada ka da hausa ko xo baka sani ba. ashruf yayi ‘yar siririyar dariya yace axixa kenan, ba don in kin yi yaranki na hausa ba bakinki ciwo yake da daga yau mun daina Magana da turanci da hausa xamu dinga yi. Ta ce waye yace maka haka? 

Ya ce axixa ce ta ke fadawa Mubarak daya ce ku dinga yarenku kar mu ji in xaku yi maganarmu kika ce ba xa ki bata bakinki ba, keda turanci kika saba Magana dashi xa ki ci gaba. Ta yi shiru ta sunkuyar da kai kasa tace, wannan ya wuce. Ya kalleta yace tun daxu kike tambaya ta labarina, me ya sa kike so ki ji labarina ne? 

tace haka kawai ashruf ba don komai ba sai don mutumin da  kake tare dashi xaka so ka san ko shi wa nene.  Ko ba haka ba? ashruf ya nisa ya yi musrmushi ya kalleta, kallo ido da ido yace kina so ki ji labari na ko? To xa ki sha labari yanxu kuwa amma fa sai kin yi hakuri saboda labarina yana cike da abin ban tausayi mai tsanani don duk rashin imanin mutum ya ji labarin nan xai tausaya min, ba kuma kullum nake so in dinga tuna abinda suka faru baya ba, saboda bacin rai. 

Axixa ta dafe kirji tace ashruf iyayenka ne suka rasu? 

Ya ce ina da uwa ina da uba duk suna nan . axixa tace na dauka ma sun rasu ne tun kana karami. Ya ce ai ba sai yaro ya rasa mahaifansa bane maraya ko marar gata ke dai gyara xama ki sha labari ashruf ya kaikaice cikin harshen hausa wanda axixa ta ji kamar a mafarki yana ta kwaranyo yaran hausa kamar jakin kano. Don tun haduwarta dashi ko xo bai taba fada da hausa ba sai gashi yau hausa harda Karin Magana.


LABARIN ASHRUF

 Ya ce sunana Ashruf El-mustapha (ja) sunan mahaifina ne el mustapa(ja) saboda mahaifina fari ne tas shi yasa ake kiransa ja, mahaifiyata kuwa sunanta Fatima. Allah Ya yiwa mahaifina arxiki tun yana matashi bai yi auren fari ba, ya gada a wajen mahaifinsa ne. wanda ya rasu ya bar shi shi kadai, kasancewarsa kwararren dan kasuwa mai ilimi yakan je kasashe daban-daban domin kasuwancinsa kamar kasar larabawa, turawa har ma da china. Wata rana ya baro garin mahaifarsa wato jahar katsina, wani garine a Nigeria shi dan asalin babban birnin garin ne, ya tafi Libya don wasu harkokinsa sai ya hadu da Fatima wato mahaifiyata tana yarinya matashiya bata wuce shekaru goma sha hudu ba. ya nuna yana sonta, to kasancewarsa bakar fata dan wata kasa sai suka hanashi aurenta da kyar dai da Allah Ya yi matarsa ce ya aure ta abin ya xama abin surutu. Balarabiya ta auri bakar fata . ya taho da ita Nigeria gida duk danginsa suka ganta bayan xuwansu Nigeria da kamar wata bakwai mahaifina ya ga dai kasuwancinsa ya fi ci a kasar turawa wato America, ga mahassada sundame shi, sai yakaura shi da amaryar sa xuwa America , gaba daya da xama a babban birnin wato Washington, a nan ne Allah Y basu haihuwa suka haifi xubaida yayata kenan bayan an haifeta, da shekaru uku sai aka haife ni. Mu biyu muka taso a gaban iyayen mu masu matukar son junansu, xaman lafiya da kwanciyar hankali ga wadata an yi mana tarbiyya a bisa shari’ar musulunci, an kuma ba mu ilimin  islama da na boko, tun muna ‘yan kanana kuma komai uba yake sayowa ‘ya’yansa na jin dadin yaro duk mahaifinmu ya dau nauyin komai kika sani.


 In muka gani muke so na ci ko na sawa, ko na wasan yaro mahaifinmu da mahaifiyarmu xasu bamu. Wata rana da yamma muna xaxxaune a farfajiyar gidan ni da yaya xubaida muna hawa keke, momi kuma tana xaune akan wata kujera tana karanta Alkur’ani sai ga daddy mu ya dawo, muka tafi da gudu muka taryeshi a bakin motarsa, direban sa ma ya fito daga motar sai muka ga wani mutum shima ya fito daga motar bakikirin dashi gajere mai jajayen idanu don lokacin shekarata bakwai, ina kallon horror film, amma saida mutumin nan ya  bani tsoro, muka kankame daddy muna jin tsoron wannan bakon. Dady y ace mu daina jin tsoronsa sabon direba ne aka kawo masa ofis daxu, dan uwansa ne dan Nigeria, saboda shi taufik tsohon direban sa tafiya xai yi kasarsu dan Malaysia ne, shi ne aka samo masa wannan xai dinga kai mu makaranta da sauran aike-aiken gida. A matsayin  mahaifiyarmu mai tsananin addini da gudun xargin mutum akan abin da bai yi ba saida ta ji wannan bakin direban bai kwanta mata ba ta ce a sallameshi kawai bata sonsa. Amma dadynmu yace siffarsa ce a haka bashi da fara’a, amma yana da hankali.


 Kuma yana bukatar a taimaka masa kasancewar bako a wannan kasa, bai san kowa ba, bashi da komai, tunda ya iya tuki mu ringa nuna masa gari a hankali xai san  ko ina. Aka bar shi a gidanmu aka bashi dakinsa a boys quarters yake xaune, yace sunansa yakubu(takaka) don haka takaka muke ce masa musamman daddy ya iya kiran takaka kamar shi ya rada masa sunan. Muna nan da takaka yana tukamu sai muka ga ashe mutum ne mai kirkin gaske yana da hankali don haka har cikin gida dady yake kiransa, ya bashi kudi su kirga tare ya kai masa banki, duk huldodin kasuwancinsa yana aiken takaka ko ina da takardunsa da komai, takaka ya san kansu.


 Bayan xuwan takaka da shekaru biyu, wata rana daddy yace tunda mun yi hutu mu xo muje wani gari da ake kira texas  anan America ne mu xuyarci abokinsa. Wani bature, suna yawan xuwa gidanmu shi da iyalansa mu ba ma xuwa. Muka gama shirinmu tsaf da sassafe muka fita muka nufi gari a can muka yini bamu bar taxas ba saida la’asar likis don haka har dare ya fara yi mana a hanya kamar magariba haka muna tafiya sai muka ga takaka ya tafi gefen hanya sosai yana dan shiga daji daidai da wani katon rami ya tsaya, ya kashe mota abu ya bawa daddy mamaki, yana xaune a gaban motar, yana karatun jarida, sai ya ajiye jaridar yace da takaka lafiya ka xo  nan bakin rami ka tsaya? 

Takaka yace fitsari ne yayi bala’in matsa ta. Daddy yace ai kanka tsaya xaka gaya mana ba kawai ina karatu ba kan in dago in ga ka xo nan ka tsaya ban da abinka kuma tsayawa ko daga can gefen titi ne ma ai ya isa a tsaya ba sai ka xo nan daf da rami ba ka tsaya. Ka je ka yi da sauri ka xo mu tafi. 


 Takaka ya fia yana dan xuge-xugen taxuge sai muka ga yana fitowa yana kallon wani gefe. Ashe ya hada baki ne da wani mai  tirela idan ya ga fitarsa ya taho da gudu ya daki motarmu mu gangara shi kenan mu mutu, can gida kuma ashe ya gama kammala takardun daddy na kudaden sa da kamfanoninsa da yake da hannun jari takardun  gidaje da motoci duk ya kwashe idan ya kashe mu sai ya kwashe kudi ya gudu. Ai kuwa hakan aka yi da mai tirela ya hankada motarmu cikin wannan gundumemen ramin mai girman gaske, ga xurfi. Suka yi tafiyar su, gashi dare ne babu wanda ya ganmu. Ashruf ya sharbe hawaye ya ci gaba da cewa a haka muka kasance har gari yawaye wasu sun cika a cikinmu wasu sun jirkinta. 

Axixa ta goge hawayen dake xubo mata tace, waye ya rasu a cikin ku? 

Ashruf yace ‘yar uwata yayata xubaida ko motsawa bata yi ba motar ta danne mata wuya yayi kwatsa=-kwatsa mahaifiyata kuwa wurgi aka yi da ita gefe ta buga kanta da wani dutse ta yi doguwar suma da a sati ma bata farka ba, dady kuwa a lokacin kafarsa ta hagu ta fincike ita daban shi daban. Axixa ta rafsa salati tana fadin wannan rashin imani da yawa yake. Waye ya fito daku? 

Ya ce kwananmu biyu anan sai ga ‘yan wata jami’a ‘yan geography masu bincike binciken yanayin kasa, Allah Ya kawo su nan, to a nan fa suka ganmu cikin wannan mawuyacin hali, ni kadai ne ido na biyu ko kwarxane ban yi ba, ina ta xagaya su ina  tattabasu shiru, daddy ne ma ya farfado idan na kira sunansa yakan amsa amma yaya xubaida da mommy ko motsi basa yi. Nan da nan suka kwashe mu sai asibitin wani kauye don mun yi nisa da garin da muka je. Mun kuma yi nisa da Washington . aka bawa mommy gado ita da daddy don an aunata tana da rai, yaya xubaida kuwa harta fara kumbura ta rasu kin san turawa basu binneta ba sun dai saka mata chemicals don ta daina warin har sai iyayenmu sun farfado sun ga gawar ‘yar su sannan a binne ta.


  Ni dai lafiyata kalau daya daga cikin likitocin ya dauke ni ya kaini gidansa, muna xuwa asibitin in ga iyayena mu koma har dai daddy ya farfado sosai ana hira dashi. Mommy kuwa ta farfado amma bata Magana sai kallo, wai ashe kwakwalwarta ta tabu, sun yi sun yi ina babu yadda xa a yi ta yi hankali. Daddy kuwa sai keken guragu aka bashi, babu kafa daya ta cuxge. Daga karshe bayan daddy ya ga gawar yaya xubaida sai ya yi mata addu’a yace su binne ta.


 Momy kuwa sai kallon gawar take batace komai ba aka binne yaya xubaida. Bayan asibiti sun gama damu suka fara tambayar daddy yaya? 

Me ya faru? 

Ya ce shi dai ya san ya taho texas shi da direbansa da iyalansa, sai direban ya xo ya tsaya a daidai wajen da aka ganmu yace xai yi fitsari, to bayan ya fita ne sai muka ji yayi fito ni dai ban juya ba saida na hango wata katuwar tirela ta nufomu a guje bamu Ankara ba sai ji muka yi anan ta kulikulin kubura damu har haka ta faru.


 Duk suka tausaya mana kuma kowa ma yana xargin babu tantama da hadin bakin direba takaka wajen faruwar wannan al’amarin, gashi sama da satinmu uku a asibiti bamu ganshi ba. nan dai suka kwashemu muka nufi gidanmu, abin mamaki takaka ya hada komai ya sayar hatta gidanmu ya sayarwa wani dan uwansa dan damfara wani bature, ya ringa dauko lauyoyi da shaidun cewa gidansa ne ya saya ga takardun gidan. Kudi a banki babu, kamfanoni babu, takardu gashi a lokacin kai be waye ba babu dokoki da ake bi a kwatarwa mai gaskiya hakkinsa musamman bakar fata a can bamu da hujjar da xamu ce kayanmu ne ko ba mu muka sayar ba, kiri kiri komai namu ya gagare mu. Daga karshe wani makwabcinmu ne dan kasar jamaika shi ya taimaka mana da muhalli, ya kuma je wajen manyan gwamnati ya fadi halin da muke ciki, ake taimaka wa mommy da magani da take sha take samun barci, don barcin ne saukinta idan bata sha maganin ba babu barci sai ta yi ta kuka tana kiran yaya xubaida ko takaka tana kokarin ta fita da gudu amma idan tasha maganin lafiyar ta lau sai dai babu Magana sai kallo.


 Muna nan dai a gidan bawan Allah nan dan jamaika mai suna david ba musulmi bane ina xuwa makaranta duk da dai ba tamu tada bace mai tsada ta yaku bayi ce. Ina aji biyar na firamare david da iyalansa suka fara shirye shiryen komawa kasarsu jamaika kasancewar ya yi ritaya, hankalinmu yayi mummunan tashi saboda babu inda xamu je mu ci abinci mu kuma xauna. Don a lokacin ma gwamnati ta daina biyawa mahaifiyata kudin magani shi David din ne yake saya mata. Uncle david ya bawa mahaifina shawarar ya koma kasarsu mana sai mahaifina yace ba xai iya komawa Nigeria ba don xai wulakanta ya toxarta fiye da yadda yake a nan, yace shi daman mahaifansa sun rasu bashi da wa babu kani ko kanwa sai ‘yan uwan uwa da uba. Ya ce hassada da bakin cikin da suke nuna masa shine ummul aba’isin barinsa garin.


  Ya ce yanxu daya xama haka idan ya je dariya xasu yi masa ba xa kuma su taimaka mana ba karshen ta mu yi bara, mahaifiyata kuwa da wannan ciwon nata karshe sai dai ta baxama dawa tunda babu maganin da take samu tana sha. Ya ce can libiya kuwa idan ta koma shi ma babu mai kula da ita don daman mahaifiyarta ta rasu tuntuni, mahaifinta ma ya rasu tana cikin jinyar nan bata da wani da xai rike ta. Don haka dai mahaifina ya sake rokar david yadda Allah Ya rufa masa asiri ya rufa mana muma mu bi shi kasarsu jamaika din mu xauna. Sai ya yarda muka koma jamaika dasu, na ci gaba da xuwa makaranta har na gama firamare na fara sakandire, dady yana daga xaune yake tufka igiya idan na dawo daga makaranta in dauka in je in sayar mu biya kudin makaranta ta mu sayawa mommy magani. Saboda ko uwar da ta haife ka ce wata rana ta gaji da miko maka tace ka je ka nemo naka. Mr david yana bamu wani abinda muke bukata, amma ba duka ba. ina aji hudu na sakandire mr david ya rasu, komai ya xamo mu xamu nema da kanmu, hatta gidan david din da muke xaune magada da ‘yan uwansa suka mana caa aka ce wai mu tashi da kyar suka yarda suka ba mu wata hudu mu nemi gida mu tashi. To babu irin sana’ar da ban gwada ba amma babu wani kudin kirki da nake samu da xai ishemu ci da sha mu kuma tara kudin haya, dady yace xai je yayi bara na hanashi nace ko xan mutu saboda aiki da wahala xan samo abinda xamu ci ba xai yi bara ba. daga karshe na je na sami wani tsoho mai kamun kifi ina kuka ina rokon ya koya min sana’arsa, yace ba xan iya ba. nace xan iya, daya koya min kuwa saida yayi mamaki na kan ka ce kwabo na kware wajen iya kamawa, ina taimakawa tsohon nan wajen kamun kifi yana biyana.


 Dana gaya masa matsalata ya tausaya min ya kuma taimaka min sosai da dabarunsu irin na tsofaffin dan kamun kifi. Ya ce ya bar mun in dinga kamun kifina ina sayarwa ba sai na kawo masa kudin ba, in je in kula da iyayena. Wata hudu na yi iyayen mr david suka yi mana Magana akan mu tashi hankalin daddy ya kara  tashi, abin mamaki sai daddy ya ganni da motar haya nace su xo mu tafi gidan da na kama mana haya, muka hada yan komatsanmu muka koma gidanmu mu kadai. To a daddafe dai da kyar nagama sakandire. Ina gamawa har gida masu jirgin ruwa su mr Johnson suka sami labarina wajen iya kamun kifi suka xo suka ce idan na yadda xasu yi aiki dani ina kamo musu kifi suna biyana. Da farko daddy ya ki yarda don shi burinsa na yi karatu mai tsawo na sami babban aiki. Sai na nuna masa sana’ar ta fi don idan na fara karatun wa xai biya min kudin makaranta kasancewar da tsada tunda niba dan kasar bane?

 Wa xai sayawa mommy magani? 

Waye xai bamu abinci? 

Amma tunda da albashi mai tsoka da xai isa mu sayi abincin mu ajiye na tsawon wata daya na sayawa mommy maganin wata mu biya haya a shekara nace ya mance da jami’ar nan kawai wata rana na yi. Ya amince, amma abinda yasa bana son aikin nan saboda sai na yi wata biyu ban je gida ba, muna ta bin kasashe a jirgin ruwa bana ganin iyayena, sai dai aike shi ne shi kawai yake damuna. Amma AlhamduLillahi ina samun kudin da xan yi komai da komai.


 Ashruf ya sunkuyar da kai sai hawaye yaketa xuba daga idanuwansa, axixa ma ta goge  hawayen da yake xubo mata dan tausayin ashruf da iyayensa. Ta nisa tace Allah sarki na yi dana sani, yau ne rana ta farko da na fara yin nadama a rayuwata. Ashruf nice ta biyu bayan takaka da na musguna wa rayuwarka, na yi nadama ashruf kai abin tausayi ne, kuma ko waye ya ji labarinka ko bashi da imani xai tausaya maka. Allah  Ya yafe mana gaba daya, Ya kuma fidda bayinSa daga cikin ukuba. A da na dauka babu wanda ya kai ni abin tausayi a rayuwata, kafin in ji labarinka amma yanxu naga labarina ba abin tausayi bane idan na hada da naka ashruf ni din nan nima na tashi da maraici domin na rasa mahaifiyata ina da shekaru shida ni kadai ta Haifa. Ammam ban toxarta ba kasancewa mahaifina a tsaye yake a kaina ya ga nayi rayuwa cikin farin ciki, don haka ne ma baya xama da matan daya ke aure, da xarar ya ga xasu musguna mun to fa sai dai su rabu a kaina. Suna bala’in kishi da ni wai ya fi sona fiye dasu matansa.


 Bashi da lokacinsu sai nawa, don baya fita kowace kasa ya bar ni a hannun wata matarsa dani yake tafiya, haka daga wajen aiki duk yawan aikin daya ke yi xai xo gida ya ganni ya koma, idan kuwa aikin ya masa yawa yadda ba xai iya fitowa ba ya xo, to sai ya kirani a waya da matarsa ta dauka sun gaisa xai ce ba wa axxyna kan wayar. Don haka kishi da bakin ciki yake hanasu xama, a yanxu xancen nan da nake maka bashi da aure ni da abokansa nema muke lallabashi yayi aure tunda shi ne dan takarar shugaban kasar Nigeria mai jiran gado ka ga ya xa a yi shugaban kasa bashi da mata? Amma yace idan sun gama hada-hadar xabe xai yi auren.


 Ashruf yayi murmushin karfin hali don idonsa yayi jajur saboda tuna tashin hankalin daya faru dasu a da. Axixa ta kalleshi xuciyarta cike da tausayinsa tace ashruf lallai xan tafi da tunanin rayuwarka na dinga tunanin ko ya kake kai da mahaifanka musamman mommy. Ashruf na yi nisan da bana jin kira a game  da kai (OOPS! NI KAM BAKI NA RUPE, NA CE BAN JI BA.) 


 Ashruf ya dago da sauri ya kura mata ido alamar tambayar me take nufi bai gane ba? sai ta yi murmushi ta mike xata shiga daki, ashruf ya jawo hannunta ya xaunar da ita yace ban gane ba. ta sunkuyar da kai tace babu komai. Ashruf yace kar kice min abinda nake ji a xuciya shi kike ji? 


 Axixa dai bata dago ba, kanta a sunkuye ta ji duk kunyarsa ta rufeta. To me ya sa take jin kunyar sa? 

Musamman ma yau? 

Da dalili, axixa ta kasance tana tsananin son Ashraf da begensa a xuciyarta, irin wanda bata taba yiwa wani da namiji ba. shima kuwa ashruf ya dade da tsunduma da tsananin kaunarta amma me? Yana ganin axixa ta fi karfinsa ina ma xai taryeta da wannan xancen bashi da budurwa bai taba yi ba bashi da ra’ayin yi kuma. Amma sai ga axixa ta yi masa katutu, sonta ya mamaye masa xuciya, suka yi shiru kowa kansa a sunkuye a kasa yana tunanin ta ina xai fara gayawa dan uwansa wannan maganar. A karshe dai axixa ta dago ta kalleshi, ta yi masa wani lallausan murmushi ta mike ta nufi daki, ya bi ta da kallo harta shige sannan yayi wata doguwar ajiyar xuciya yayi tagumi yana tambayar kansa da kansa waishi me ke damunsa ne ya dorawa xuciyar sa wannan abu marar yiwuwa, wato son axixa da tunanin begenta.

.

Anan muka kawo karshen KWANA ASHIRIN DA HUDU kashi na daya, sai naga yanxu haka kamar littapin bai muku ba, da haka nake son dakatar da typing, har sai nan da KWANA ASHIRIN DA HUDU, bayan kun antayo mana likes, comments da shares har sau DUBU ASHIRIN DA HUDU.

.

.

Tamabaya gare ku masoya, shin ya halatta kan addinin musulunci soyayya ta shiga tsakanin AXIXA da ASHRUF?

.

Comment da sharhi sune suke karamana karfin guiwa ina sanar daku cewa shahararriyar marubuciyannan Aisha muhammad sani zatafa littafi mesuna jarmeel nafseen zamu fara kawoshi group dinnan nagode.

[9/1, 6:10 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/1, 6:11 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PART 2

*6*

.

.

 Can acikin daki axixa ke kwance kan gadon su, ta yi ruf da ciki akan luntsumemen gadon nan nasu na itace da katifar leda da filon tsummakarai, ta fada cikin rijiyar tunanin ashruf. Bayan shigowarta daki da kamar awa sai ta ji kicif an xubar da wani abu a kasa. Da alama ashruf ne yayo itacen abincin rana dana daren da xa su ci. Ta mike da sauri ta fito waje sai ta iske ashruf har ya kamo wasu manyan kifaye guda hudu yana dauka yana kaisu bakin wani dutse mai bulbulo da ruwa xai wanke, ta kalle shi tayi fari da ido ta ce yanxu ashruf maimakon ka kirani na xo in wanke kifin shi ne xaka wanke kifin shine xaka wanke,? ka kamo kifi ka yo itace ka xo kuma ka dafa ai abun yayi yawa ni me ye amfanina a matsayina na mace? 

Ashruf yayi murmushin da har hakoransa suka fito yace axixa kenan bana so naga kina wahala ai ni bana damuwa da ko me xanyi miki ni dai burina in faranta miki. Ta xo ta ciccibi kifi daya ta nufi wajen da suke wankewa ta dawo ta dauki wani ashruf ma ya biyo ta da dayan. Suka tsugunna suna ta dirxar kifinsu suna kankare kaushi-kaushin jiki. ashruf yana yi yana satar kallon axixa harta lura da kallon da yake yi mata, ta tsaya da wankin kifin tayi murmushi tace malam kallon me kake mun? 


 Ahruf yayi dariya yace, gani nayi aiki bai dace dake ba shine nake kallonki, naga wankin kifi kamar an baki wankin jirgi sai xufa kike da garin babu xafi. Su duka suka tuntsire da daiya, axixa tace kana fa yi min tsiya ashruf ko me ka gani kowa yana yi ai koya yayi nima xan koya ne, kuma in saba xa ka ga wata rana na kware. 

Ashruf yace haka ne, hausawa na cewa da koyo akan iya. Suka ci gaba da wanke kifinsu. Can axixa ta dago tace, da gaske ne wai da matan hausawa suke cewa mace tana xaune kuku yayi wa mijinta abinci da sauran aikace aikacensa yana rage soyayyar su? 

Amma idan ita take dafa masa ko me, xai ci ya sha, makwancinsa kayan sawarsa ta gyara wai soyayyarsu tana kara danko da shakuwa? 

Ashruf yace haka ne maganarki. Don naga ni mahaifiyata tana yiwa mahaifina komai da kika sani da ta ke da lafiya ko tsinke bata barinsa ya dauke.

 Axixa ta gyara xama ta ce Allah Sarki yaya yake yi yanxu da haka ta same ta? Ashruf yace yana missing dinta yana kuma tuna da yayi mata addu’ar Allah Ya bata sauki. Ta ce Allah sarki, Allah Ya bata lafiya yace amen.


 Bayan sun gama wankin kifayen sai suka jijjinginesu dan su dan tsane. Axixa ta yi wajen murhu ta saka itace ta hura wuta, ashruf na miko mata kifayen tana jerasu akan wayar gashi dake kan murhun. Suka wanke hannayensu da sabulu saboda  karni. Bayan kifinsu ya gasu suka xuba suka ci tare. Haka axixa da ashruf suka kasance a koda yaushe suna tare suna hira. Haka axixa take sa ashruf a gaba tana yi masa tambayoyi iri-iri akan xamantakewar aure. Me mace xata yi ta farantawa mijinta, daga karshe ta harhada amsoshin da ashruf ya bata suka bata amsar cewa lallai da yawa matan talakwa sun fi yiwa maxajensu biyayyar aure, bayan haka sun fi shakuwa. Saboda yana da cikakken lokacinta, koda yaushe suna tare wani ma ya taya ta aiki kamar dai yadda suke yi da ashruf, kuma uwa uba sun fi son junansu da yin soyayya saboda Allah. bata ga kudinsa ba shima ba don kudinta ba ko na iyayenta, tsantsar soyayya ce saboda Allah, don haka aurensu xaifi karko.


 Axixa tayi tsaye tana tunani a ranta ta ji ita sam yanxu bata son rayuwarta da Mubarak, saboda Mubarak masu kudi ne haka kuma yana da harkokin da suka sha masa gaba. Don baya cikakken wata daya a gida sai ya fita wata kasar. Don haka ba xai bata bikakkiyar kulawa ba kamar yadda ashruf yake yi mata anan. Itama kuma yadda take hango rayuwar aurenta da Mubarak shine kuku  na mai dafa musu abinci masu goge goge da share sharensu daban, mai gyara dakunansu da share sharensu daban, mai gyara dakunansu da bandakunansu daban don haka ita babu wani abu da xata yiwa mijinta na wata kulawa. Wata rana itama ta kama gabanta ta tafi wata kasar, mijinta kuma yana wata kasar sai dai idan sun dan sami lokaci ne xa su fita yawon shakatawar tare. Gaskiya talakawa sun fi sanin hakkunan junansu da aiki da fadar da Annabi Muhammad (SAW) ya fada mana. Mace bata jin girman kai ta yiwa mijinta biyayya idan ta yi masa laifi ta nemi gafararsa. Amma macen mai kudi fa tana ganin ubanta ya fi ubansa kudi ko ita tafi mijinta kudi yaya xa a yi ta rinka wani bashi hakuri tana bashi girma. Shima kuma mijinta haka yake gani ina da kudin da xan auri mata goma ko in nemi matan waje ya xan tsaya akan wannan ta tafi me ye xan tsaya akan wannan ta tafi mana.


 Shi kuwa talaka wani har ‘yar gonar daya gada xai sayar sannan yayi aure, tabbas xai rike ta kamar kwai don idan ta tafi kafin ya sake nemo kudin wani auren xai wahala. Axixa tace kai talaka ya fi soyayya tsakani da Allah. xuciyar axixa cike da tunani ta koma ta xauna a gefen wani dutse ta tara kafarta a cikin ruwan dake bulbulowa tana wasa dashi tana kallon wasu tsuntsaye masu kyau da suka sauko shan ruwa miji da mata ne.


 Bayan sun sha ruwa suka fara wasanninsu suna sumbatar junansu. Abin ya bawa axixa matukar mamaki tace a ranta tsuntsaye suma sun san soyayya? Tabbas ba son Mubarak nake yi ba ni dai kawai naga Mubarak a matsayin saurayina ina kulashi amma ban taba jin wani so a raina ba. tabbas ashruf ya shiga xuciyata daga kansa na fara jin dandanon xakin soyayya, amma ina tsoron son maso wani don ma bai san me nake yi ba. ta ji an sa hannu an kare mata ido ta bayanta ta juyo da sauri sai taga ashruf ne ta yi murmushi shima yayi mata lallausan murmushi ya xo kusa da ita ya xauna. Ta ce tun daxu ban ganka ba.


 Ashruf yace wanka na je yi, ke kuma tun daxu kina nan sai tunani kike yi. Wai tunanin me kike yawan yi ne kwanakin nan? 

Axixa ta nisa ta yi murmushi tace kallon wasu tsuntsaye nake yi suna bani mamaki. Wai har sun san soyayya. Ashruf ya tunstire da dariya yace waye bai san soyayya ba? duk inda miji yake yana lallaba matarsa kamar kwai. Axixa tace ka ce kaima xaka lallaba matar ka? 

Ashruf yace nixan fi kowa ma, ba xan so ta shiga damuwa ba ko wahala daidai da sakon daya, musamman ma idan tana da ciki ai ko bandaki xata je sai na kaita, don karta sha wuyar tafiya dan cikin ya wahla. Suka tutsire da dariya su duka. Axixa tace ah, kai kafi kowa ma.


 Yau kwanansu axixa goma sha tara a wannan kungurmin dajin. Ashruf tun safe ya kutsa cikin daji nemo busashen itacen da xasu yi girki saboda a daren yiya kwana aka yi ana tafka ruwa babu busassun itace anan kusa. Axixa kuwa da tagama wankin kifayen da xasu gasa ta sha xaman jiran xuwan ashruf ya kawo itace, ta ji shiru babu amo ba labarinsa, sai kawai ta je ta harhado kayansu na sakawa danan shimfida saboda duk sun yi datti ta tafi jikin wani dutse mai bulbulo da ruwa ta yanki dan sabulun wankansu ta fara wankewa. Ta wanke tsaf, tana yin shanya ne ta hango wani abin mamaki, mai firgitarwa, abin farin ciki na bakin ciki kuma. Jirgin ruwa ta hango wani daban ba nasu ba, da alama su ake nema. Jirgin yana ta yawo a ruwa. Axixa na tsaye tana kallon jirgin nan gadan gadan ya tunkaro inda suke, abin mamaki axixa ta tsinci kanta cikin tsananin bakin cikin rabuwa da ashruf, ta gwammace gara wannan rayuwar da suke ciki da a koma gida wajen da ake yi mata gata kamar sarauniya. Ga hadaddun abinci, abin sha, suttura mai kyau, wajen kwanciyarta abun ba a Magana, anan fa? Kullum cikin tsumma, gadon itace abincinsu gasashen kifi ne, wata rana babu ko dan gishiri ma. Tabbas axixa ta san wannan jirgin su yake nema, ko tantama babu gunsu ya tunkaro kuma ta san rabuwarta da ashruf ta xo wata kila ma har abada. Ta ce a ranta muddin na rabu da ashruf na rabu da namijin da na ji na taba so da kauna a rayuwata, namijin da xan iya xama dashi har abada a cikin farin ciki.


 Wanda yake wanke mun duk wani wata damuwata dana ke ciki. Wanda murmushinsa yake faranta min rai nake ganin fuskarsa tamkar farin wata. Dariyarsa take sani in yi dariya, wanda bana son naga bacin ransa, wanda ya sakani a hanya mai kyau, na san mai arxiki da talaka duk daya ne a wajen Ubangiji. Na san darajar mutum ko yaya yake. Kalamansa yake wanke mun bakin cikin raina, wanda rabuwa dashi ba karamar ukuba bace a rayuwat. Mutumin daya ke cikin bala’I shi da iyayensa suke matukar son taimako, ina son ashruf so mai tsanani wanda shi kansa bai san ina muradin kaunar sa haka ba, idan na rasa shi nixan cutu.


 Hawaye yayi ta xuba daga idanunta, can ta  tuna a yadda daddy yake matukar sonta da duk abinda take so me ye take damun kanta idan tace ta fasa auren Mubarak, ashruf take so ta san daddy ba xai hanata ba. amma kuma wani hanxari ba gudd ba duk son da daddy yake yi mata ba xai taba amincewa ta auri ashruf ba, bayan ga dan amininsa na kut da kut har sun kawo kudin aurensu kuma ya karba har ma an sa rana shekara daya mai xuwa, daddy ba xai yadda ba. koma bahaka ba saboda son da daddy yake yi mata ba xai taba yarda ta auri wani can da bai san asalinsa ba, ba ma dan kasar bane, marar takamammiyar madafa, ke ma axixa xance kike yi. Inji xuciyarta.


 Da wane ido kuma xaki kalli Mubarak ki kalli mahaifinsa Alhaji isah kice ba kya son auren nan kin fasa? A yadda alhaji isah ya ci burin bikin babban dansa na gaban goshinsa Mubarak ai idan aka ce an fasa auren nan duk Nigeria sai kowa ya ji saboda babatunsa. Fasa auren nan xai jawo hatta siyasar da suka tsaya takara da kyar in bata ruguje ba, don dole a bata shi da baban axixa, kuma dan takarar shugaban kasa da mataimaki an bata ai mabiya baya duk saisu kama gabansu, haka axixa ta kame a tsaye tana tunani kala-kala. Har dai ta fara hango surar jirgin sosai, ma’ana ya matso kusa da inda take, tuni xuciyarta ta yanke mata hukuncin ta gudu ta buya ta hakura da ganin daddy data rabu da ashruf din ta, ta kwashe kayan shanyar ta cusa a lungu, ta bi ta cikin duwatsu tana tsugunawa don kar su hangota ta tafi kofar dakinsu duk ta harhada kayan dake wajen su kujera ce su kwalbar da suke shan ruwa, da murhu da kifin da xasu gasa, duk ta tura cikin dakin. Ta tura kofar da karfi ta bame ta sake bin cikin dutsen ta shiga daji a guje.


 Ta yi ta gudu a daji ba tare da ta damu da kayoyin da take takawa ba. har saida ta tabbatar ta yi nisa da bakin ruwa sannan ta sami gindin wata bishiya ta xauna tana ta huci, tana shashekar gajiya. Ta kalli kafarta taga duk kayoyi ne suka caccaketa sai jini yake xuba, axixa ta rushe da kuka tace a ranta me yake faruwa da ni ne haka? 

Wane irin bala’I ne ya afka min haka? 

Kalli halin da na ke ciki yanxu kafa ta farfashe, hannuna ya farfashe saboda wankin da ban saba ba, da hura wuta, kanta  ya cuccure babu tajewa, babu kayan sawar kirki sai riga daya da xannuwan gado tsummokare. Ta rushe da kuka. Ta ce “SO” wannan itace dammar soyayyar? 

Tabbas idan haka ne soyayya to talakawa sun fi masu kudi yin soyayyar gaskiya da shakuwa. Don xaman tare da a koda yaushe muna tare da ashruf shi yasa muka kara shakuwa. 


  Ta ce a ranta ina son ashruf ba xan iya rabuwa dashi ba, ina tausayin mahaifina saboda na san ko a ina yake yanxu duniyar nan ta yi masa xafi saboda rashina. Na san ba a canja uba amma ana canja miji don haka xan xauna da sabon masoyina har muga yadda Allah Ubangiji xai yi da mu, sannan in je in ga mahaifina. Daddy ka gafarce ni, ka yafe min ba yin kaina bane xuciyata ceta kamu da son wani wanda idan ta rasa shi xa ta shiga wani hali, ka gafarce ni, you will miss me, but its just for some time. Ta sake rushewa da kuka ta dora kanta a gwiwar kafarta sai kuka take kamar ranta xai fita.


 Tafiyar da ta ji ana yi a kusa kusa da ita shi ya sa ta katse kukan da take ta mike a firgice ta kankame bishiya, ta gama saddakarwa masu nemanta sun ganta sun gama. Amma me!? 

Comment sharhi da like su suke kara karfin guiwa kuyi hakuri jiya nayi mantuwane nasaka muku 

Duk kyentakalmi maimakon kwana Ashirin da hudu

Auwal Aliyu muhammad 

Kano state

[9/1, 6:11 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/1, 6:15 PM]  "  D'Y: 👫KWANA ASHIRIN DA HUDU PT2

*8*

.

.

Bayan  sun shiga duk sun xaxxauna harda mr Johnson sai alhaji ahmad yace ina sake mika godiyata dai ga wannan yaro ashruf sannan a matsayinka na mai share-share a jirgin na san baka da wani cikakken albashi don haka na yi alkawarin xan baka kudin da xai isheka ka ja jari naka na kanka wanda xaka iya xuwa kowace kasa ka yi saye da sayarwa, in har baka da gida xai isheka ka gina gida, idan baka da aure xai ishe ka yi aure. 

Duk suka dauki tafi raf raf su Mubarak, sadik, ibarhim, atika. Balle kuma mr Johnson ya ji kudi bakin nan har kunne yana dafa ashruf yana wani cire masa ciyawa a gashi kai kace shi aka bawa kudin ma. Ashruf kuwa murmushi yake yaxo gaban alhaji ahmad ya durkusa yayi ta godiya, ya koma kujerar da yake ya xauna. Axixa kuwa tafi kowa jin dadi ta rungume babanta ta yi masa godiya. Daga karshe alhaji ahmad yace duk su shiga ciki su barshi da ashruf. Bayan kowa ya tashi harda mr Johnson sai alhaji ahmad ya ce da ashruf ya matso kusa dashi suyi Magana. Bayan ya matso alhaji ahmad ya nemi ashruf daya bashi tarihin rayuwarsa, ashruf ya gyara xama ya bashi labarinsa kakaf kamar yadda ya bawa axixa. Alhaji ahmad ya tausayawa ashruf matuka ya kuma sake dada kudin kan na da da yayi niyyyar bashi.


 Can acikin daki kuwa axixa na can tana faman sallar wanka ta yi sabi yayi sau goma, kanta datti kai kace ruwan kwata ne don bakar kumfar data ke fita daga  kanta ta wanke ko ina ta fito. Munnira ce take taje mata gashin tana sa hand drayer tana busarwa, atika kuwa da abin yankan farce take yanka mata xaro-xaron farcen hannun da na kafa. Bayan sun gama  mata an mulke kanta da hadadun mayukan gashi tasa ribbon mai kyau ta tufke ta mulke jikinta da mai mai kamshi ta feshe jikinta da hadaddun turaruka  ta caba ado da wani dandatsetsen leshi ja. Kai baka ce axixar daxu bace a daji. Kyanta ya sake fitowa har kamar tafi da, wayar Mubarak ceta ishesu da shigowa yana ta faman dokin ganin axixa yana wani falo ta fito yana jiranta. Ran axixa yayi baki kirin ita ba abun tace xata fita ba to tana so ta je taga ashruf dinta, atika da munnira sai axalxalarta suke suna cewa ke kuwa axixa ki yi sauri ki je gun Mubarak mana, baki ga ba fa halin daya shiga sanda ba kya nan dare da rana, maganar ki ko abincin kirki baya ci. Axixa ta fito daga daki sai  ta ci karo da sadik da Ibrahim suma sun fito daga dakinsu nan fa suka yi ta tsokanarta suna cewa kema mun san kin kagu ki ga Mubarak watakila ma fiye da yadda ya kagu ba dare ba rana xancenki ke harda kuka yake yi cikin dare. 


 Ga shi nan a wannan karamin falon yana jiranki tun daxu shiga mana muje. Axixa ta ji kamar sun daba mata wuka dan takaici da kyar ta yi murmushin dole tace ina xuwa me kuke ci na baka na xuba Mubarak ai muna tare. Suka shige falon da Mubarak yake jiranta ita kuma ta wuce babban falon da ashruf yake, tana dosar falon idanun ashruf ne kyam a kanta yana kallonta. Ta ci sa’a kuwa babanta dam r Johnson sun fita can farfajiyar hotel suna lissafin nawa ne xa a bashi kudin jirginsu saboda xirgaxirgar da suka yi ta yi, sannan cek din kudin da xai bawa ashruf na kudin Jamaica xai bashi ko kuma dollar xai bashi suna dai ta tattaunawa da mr Johnson. 

Axixa ta yi masa lallausan murmushi gami da yin fari da ido ta karaso kujerar da yake xaune tace. Ashruf yana ganka baka walwala jikinka duk sanyi? 

Ya nisa yace, dole jikina ya yi sanyi axixa ina tunanin yaya xanyi idan kika tafi kika barni. Axixa ta xauna kujerar kusa dashi, tace ka kwantar da hankalinka tunda komai ya fara xuwa mana da sauki to ba xa mu rabu ba in sha Allahu, kamshin jikinta ne yake dukan hancin ashruf ya ga ta sake yi masa kyau kamar ya dauketa ya hadiye yake ji, ya kura mata ido kyam baya kiftawa. Ya ce aransa, anya kuwa wannan xukekiyar yarinyar bata fi karfina ba kuwa? 

To amma itama tace na yi mata, Allah Ka taimake ni. Can yace axixa mr Johnson fa na ji yana cewa daddy jibi xamu tafi ku kuma daddy yace gobe xaku tafi. Gaban axixa ya fadi ras ta dafe kirji tace gobe!? Ashruf yace gobe… kafin tace wani abu sai ga Mubarak ya tunkaro inda suke ya xo gaban axixa ya tsaya yana kallonta, ba tace dashi komai ba can ya nisa yace baby ina can ina jiranki na yi waya kicin an hado miki abinci ki xo muje ki ci abinci mana. Axixa ta yatsune fuska tace bana jin cin abinci yanxu.


 Mubarak ya yi shiru ya kalleta ya kalli ashruf ya ga irin xaman da suka yi kujera gaf da gaf sai xuciyarsa ta fara xargin cewa anya kuwa ashruf bai sami ci gaba ba a wajen axixa harta xauna daf da daf dashi haka? Wata xuciyar tace haba Mubarak kamar baka san axixa ba da kyamar talaka kaima mai kudin da yaya take kula ka, ai lallai axixa ko ta sha giyar wake ba xa ta so ashruf ba, ajinta da ya xube idan ta yi soyayya da mai goge goge kawai dai dan sabawar da suka yi ne xaman da suka yi shi ya kawo haka. Mubarak ya kalli ashruf yace malam ashruf shiga nan, ya nuna wani waje, ka yi musu Magana ka ce a account dinmu a baka abincin da kake so ka je ka ci. Ashruf yace nagode, a koshe nake. Ashruf ya fahimci Mubarak dai so yake ya tashi ya bashi waje, sai ya mike yace bari in jira a waje. Ya nufi kofar fita. Axixa ta bishi da kallo, xuciyarta na bata shawarar ta bi shi kawai in ya so Mubarak ya gane din, sai wata xuciyar tace kar ki bishi. Ashruf ya fice saida ya kai waje sannan ya juyo suka yi ido hudu da axixa ya ga ta kura masa ido kawai wani kishi da takaici ne ya lullube shi, ya juya ya tafi don kawai babu yadda xai yi.


 Mubarak ya xo ya xauna a kan hannun kujerar da axixa ke xaune ya sa hanu yadafa kafadarta yace babyna kin canxa kamar ba ke ba kina bata rai ko duk gajiyar ce ko kuma bakunta kikeyi mana ne? 

axixa ta fixge kafadarta ta mike tsaye, ta juya masa baya ta tsaya ta bata fuska kai kace kashi ya shafa mata. Mubarak dai bai yi fushi ba, ya mike tsaye yace muje ki ci abincin kin ji baby. Haushi ya kamata kamar ta buge bakinsa ta yi tsaki ta fara tafiya, yana biye da ita, har xuwa kan teburin da aka shirya mata abincin. Ta jawo kujera ta xauna ya xo kujeran setinta ya xauna, sai wani murmushin banxa yake yi mata, tana tsaki tana kawar da kai tana dan caccakular abincin, ta taba wannan ta bari ta taba wancan. 

Al’amarin ashruf kuwa daya fito waje mr Johnson kadai ya hango akan wata mota yana xaune. Ya karasa wajensa, mr Johnson yana ganinsa sai ya hau washe baki yana cewa ashruf ka yi wannan tafiyar da kafar dama kai ai ka so ka fini kudi. Kaga yawan kudin da mahaifin axixa yace xai baka? An jima xai sauko don yanxu ya hau sama xai danyi barci don ya dade bai yi barci ba saboda rashin yarsa. Idan ya tashi xamu je ya yi waya bankin America, account daya bude a nan Italy, haka xai miko maka kudin a daloli tsirararsu, kar fa ka manta ni ne oganka ni na yi maka sanadiyar samun kudin nan don haka in ji bayani. Ashruf yayi tsaki ya kawar da kai yace ni oga ba wannan maganar nake so ba babu abinda yace maka game da axixa? Mr Johnson yace ban gane game da axixa ba? mun yi dai maganar aurenta. Ashruf ya matso kusa da mr Johnson ya  ce me kuka tattauna? 

Mr Johnson yace  cewa yayi ni da kai mun xama abokansa, saura shekara daya in Allah Ya yarda xai xama shugaban kasarsu, baban Mubarak mataimakinsa xasu hadasu aure da xarar sun hau, xai yi mana waya mu je mu taya su murna. Ashruf ya daki tayar mota da kafarsa ya yi tsaki.


  Gami da dukan kansa da hannu ya juya yana tafiya, xuciyarsa kamar xata fice dan haushi. Mr Johnson yayi dariya ya sake tistsirewa da dariya yace kai yaro ne ashruf dan banxa talauci yayi maka yawa kana tafe a tsumma an baka kudi kana wani xancen soyayya, soyayyar banxa babu kudi. Ashruf bai ce komai ba shi dai tunaninsa ya isheshi, sai xagaye xagaye yake ya rasa ina xai shiga ya ji dadi. Axixa na jikin taga dakinsu a sama tana hango ashruf taga sai xagaye yake da alama dai yana cikin damuwa. Ta tsayar da shawarar bari ta sauka wajensa taji me ke damunsa.


 Atika ta kalli axixa taga takalmi take sawa shirin fita take yi. Atika tace axxy ki xauna mana mu dan taba hira sai bin ki muke mu yi dan labari kin ki duk kin canja ba kya cikin hayyacinki kamar ba ke ba. ba tare da ta amsa ba ta sa kai ta fice abinta. Atika ta kalli munnira, munnira tace axxy ko ta fara xautuwa ne? 

atika tace xama a daji ne yasa take gudun mutane yanxu suka tintsire da dariya. Fitarta keda wuya sai ga mutumin nata shima ya fito daga dakinsu wato Mubarak . Ta yi kasake a tsaye , yayi murmushin dadi yace kamar yadda kika kasa sukuni sai kin ganni haka nima na kasa xama ni dai in ganki. Amma sai mun hadu in ga kamar wani abu yana damunki, haba baby ki saki jikinki ni ne fa Mubarak. Mu shiga falo ne ko kuma mu fita gari mu shakata da direba a waje? .

 Axixa ta bata rai tace babu daya kai dai ka tafi xaka nima in tafi inda xani. Mubarak yace ni babu inda xani sai wajenki, don haka muje in rakaki. Axixa ta yi gaba yana biye da ita har suka fita farfajiyar hotel din. Ashruf na tsaye yana kallonsu suka xo suka wuce shi sai kallon kallo suke shi da axixa, suka karasa wajen mr Johnson yanxu a cikin wani lambu yake a xaune akan kujera yana kora ruwan barasarsa. Axixa tace mr Johnson wayar tafi da gidanka nake so (handset) guda biyu da layi guda biyu yanxun nan. 


 Mubarak yayi caraf yace har guda biyu ke kadai? 

Ta ce ina ruwan ka? 

Guda biyu nake so yanxu kuma, mr Johnson  yace babu komai mu ai mune Italy harkar dai ta kudi ce, isashshen kudi waya ba bata lokaci. Mubarak ya tintsire da dariya suka tafa da  mr Johnson. Mubarak yace kudi yana tsoronka mr Johnson saboda ba kai musu rikon wasa. Ya ciro kudi wanda ya fi kudin waya biyar ma ya bawa mr Johnson. Mr Johnson ya karba yace an yi an gama da kaina xan tafi, da ashruf xan aika naga kamar ya fara xautuwa batan nan da suka yi. Mubarak yace  bashi kadai ba ma har axixa duk ta canja. Ita dai tafiyarta kawai take batace musu komai ba, ta xo ta wuce ashruf yana kallonta tana kallonsa. Mubarak ya xo ya wuce yana cewa malam ashruf ka fa rame kuma kaki cin abinci. Ashruf na jinsa bai ce ta tafasa ba balle a sauke..


.

Auwal Aliyu muhammad

Kano state

KWANA ASHIRIN DA HUDU PT2

*9*                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                    

.

.                                                                                                                                                                                                                                      

Ba dadewa mr Johnson ya aiko ashruf da kan wayoyi guda biyu da layukansu. Ya iske axixa da munnira a farfajiyar hotel amma daga can baya wajen swimming pool ya yi musu sallama suka amsa, ya mikawa   axixa  wayoyin  kallon     kallon  da  ake  idanuwansu  cike  ba  shaukin  soyayya  shi  ne ya  yi  matukar    daurewa   munnira   kai, ta kalli axixa ta kalli  Ashruf ta  sake dubansu sai ta fara tambayar kanta da kanta me ya haka ? kamar a mafarki Axixa da Ashruf masoya ne ko kuma idonta ne? 

axixa ta nisa ta ce ka rike dayar taka ce kayi amfani da ita ko dan yan gidanku ko xaka yi musu waya, yace na gode ya juya ya tafi yana juyawa sai ga su Mubarak sun bullo ta dayan bangaren suka xo suka xaxxauna, ana ta ciye ciye da makulashe da nishadi amma banda axixa har wani katon kek Mubarak ya sa aka yi mata na sannu da xuwa amma a yatsune ta yanka ba walwala. Basu bar wajen nan ba saida magaruba suka koma cikin dakunan su na hotel. Bayan duk sun shiga dakunansu sun yi alwala sunyi sallar magariba sun idar axixa ce bata bar kan abin sallar ta ba ta daga hannu tana ta kwararo addu’o’I tana hawaye . atika da munnira sai xare ido suke sun fa kasa gane halin da axixa take ciki, don tabbas tana cikin damuwa. Bayan ta shafa atika ta xo kusa da ita ta dafa kafadarta tace axxy ki yiwa Allah ki fada mana abinda ke damunki, in ba ki gaya mana ba wa xaki fadawa? 

Idan kuwa kin ki to yanxu xani dakin dady in gaya masa kin san dole ya takura miki sai kin fada. Tayi shiru kamar bada ita ake Magana ba, atika ta dauko hijabi ta saka tace da munnira kar ki bani hakuri ba ma xan dawo ba sai na je na fadawa daddy halin da axixa take ciki. Munira tace ina fa xan baki hakuri je ki ki fada.


 Atika ta fice amma ita bada niyyar ta je wajen daddy bane ta dai fita don ta tsorata axixa ko ta riketa  tace karta je xata fada musu, amma farantakau babu wanda ya biyota harta sauka kasa babu wanda ya rikota. Bayan ta fita axixa ta cire hijabin da ta yi sallah ta fada kan gado ta yi ruf da ciki, tana tunani. Munnira ta matso kusa da ita ta dafa bayanta tace, axixa na fara fahimtar abinda yake damunki da ashruf tabbas naga irin kallon da kuke yiwa junanku, haka ne? 

tana rufe bakinta sai ga atika ta shigo tace axxy kije inji daddy… munnira tace da gaske kin gaya masa? 

Atika  tace ban je ba ni kasa na sauka amma Ibrahim da Mubarak sun je sun gayawa daddy, ni ina kasa ina kallon ikon Allah kin san makudan kudin da daddy yace xai baiwa ashruf daxu? , to fitar da daddy da mr Johnson sukayi da yamma banki suka je aka karbo masa kudin cikin ‘yar akwati cike da daloli shi ne mr Johnson ya bashi yanxu a kasa…. Munnira tace haba har an bashi kudin? Wannan mutum wacce irin murna xai yi yau? Allah sarki. Atika tace ai shine nake so in gaya muku maimakon murna da farin ciki, ya fita daga sahun talakwa  sai ya dauki akwatin ya rada da kasa da kyar mr Johnson ya dauke kudin ya sa a mota ya ja shi gefe yana lallashinsa.


 Munnira tayi salati ta sallance tace daddy yana wajen kuma? 

Atika tace haba aida ba xai ji dadi ba babu kowa ni kadai ce nake kasa. To ina hawowa ne na gamu da su Mubarak suna saukowa daga saman daddy xasu shigo nan dakin sai suka ce in ce axxy ta xo daddy na kiranta wai sun gaya masa halin da take ciki. Munnira ta yi ajiyar xuciya tace ina jin sun yi gamo a dajin da suke sai an yi musu rukiyya. Axixa na jinsu sai yanxu ta motsa ta tashi xaune ta sauko daga kan gadon ta ciro wayarta, ta saka a caji ta saka hijab dinta ta fice, ba tare da ta cewa kowa komai ba. bata xarce ko ina ba sai can sama hawa na uku dakin daddyn ta. Ta tura kofa ta shiga gami da yin sallama, suka amsa ta iske su a falon, daddy yana xaune a kan doguwar kujera, Mubarak da Ibrahim a xaune a kasa tace ga ni daddy. Ya ce yauwa dama yanxu Mubarak da Ibrahim suke shaida mun tunda kika dawo duk kin canja, babu walwala. Ko wani abu ne yake damun ki?. 

Idan baki da lafiya ki yi Magana a kaiki asibisti. Axixa ta girgixa kai tace babu komai. Daddy yace bahaka kike da ba axixa nima na lura dake kin canja.


 Ta rushe da kuka ta fada kan cinyarsa yayi ya yi, ta yi shiru ta yi Magana ta ki, sai yace dasu Mubarak su tafi xai kirasu. Bayan sun fice alhaji ahmad ya ci gaba da lallashin axixa da kyar ta yi shiru, yace karta cuci kanta ta fada masa me ke damunta. Axixa taga dai gara ta fada don idan bashi ba waye xai yi mata maganin cutar dake damunsu, sai ta goge hawayen dake kwaranyo mata ta gyara xama tace daddy ka gafarceni na san ba xaka ji dadin maganar nan tawa ba amma Allah ne Ya kaddara min Ya kuma sani cikin wannan hali. Yanxu Allah Ya dora mana son junanmu ni da ashruf, yanxu ba xan iya auren Mubarak ba ashruf nake so. Bata rufe bakinta ba sai ta ji ya daka mata tsawa yace, yi min shiru shashasha! Yau ne ranar farko da daddy ya taba xagin axixa haka da irin wannan kalma. Ta yi shiru jikinta ya dau rawa yace bada ni ba wannan rashin hankalin wasan da nake yi dake shi ne yasa kika fara xamar dani kakanki? 

Dan da bashi da asali bamu san shi ba, idan baki bar maganar nan ba sai na sa an daure shi ma, tashi ki fita ki bani waje, kin auri Mubarak kin gama. Sum sum ta fice tana rusa kuka kamar ranta xai fita. Tana fita bata xarce ko ina ba sai reception tace a bata daki a can sama kololuwa, aka bata daki a hawa na takwas ta karbi mukullin dakin.


 Ta shiga dakinsu ta iske su atika basa nan wata kila suna dinning room suna cin abinci. Ta dauki wayarta da sauran takarkacenta ta fice ta hau sabon dakinta. Tana shiga ta mayar da kofa ta rufe ta sa mukulli ta datse.. wayar ashruf ceta shigo mata tun kafin ta xauna ta matsa ta ji muryar da take muradi ce cikin sanyin murya tace ashruf ya aka yi ka san lambata? 

Ya ce ai kwalin layin naki yana hannuna na manta ban baki ba, a jiki naga lambar layinki. Ta ce yanxu kana ina? Ya ce ni da mr Johnson mun taho wani hotel dake bakin ruwa na saukar matuka jirgin ruwa yana nan bakin teku. Ke kuma fa kina ina naji duk  muryarki ta canja? Ta ce ina dakina a hotel din da muke. Ashruf ya xauna a bakin gadon dakinsa don fitowarsa daga wanka kenan yace axixa ya ya xamu yi? 


 Axixa ta rushe da kuka tace babu yadda xamu yi ashruf ni nan daka ganni komai ya rincabe min. 

ya xabura yace kamar yaya? 

Tace ba ni da mai share min hawaye kamar dady na har na sanar masa abinda ke faruwa amma da ka ga yadda ya sabar min baka ce shi ne mai son nawa ba. ashruf yace kar ki damu axixa yanxu xanxo yanxu mu hadu a reception din hotel dinku. Axixa tace ashruf dady ba xai sa ido a kanmu ba kuwa? Idan ya ganni da kai laifinka xai gani. Ashruf yace na godewa Allah da laifina xai gani ba naki ba, kuma ko me xa a yi min na yarda ba xan iya rabuwa da ke ba. gobe fada sassafe xaku tafi, yanxu ina gani ki tafi ki barni axixa, na yi rayuwa da wa? Axixa ta yi ruf da ciki akan gado sai kuka take ta kasa Magana, ta ji ya kashe wayar. Ita tunanin kada ya xo daddy yasa a daureshi tunda har ya furta daurin nan, ta san kadan daga aikin babanta in dai ransa ya baci to xai iya yin kome yace xai yi.


 Kwankwasa kofarta da ake ita ta katse kukan da take ta tashi xaune, tana tunanin wane ne ya san tana nan ya xo? Ta ji ana ta dannan kararrawa ta mike a sanyayye ta karasa bakin kofa ta daga wani dan karamin labule a jikin kofar da wata ‘yar huda ta leka sai ta hango atika da munnira tayi tsaki sannan ta bude suka shigo suna mata tsiya suna cewa to mun ji me ke damunki. Gaban axixa ya fadi wato daddy gaya musu yayi abinda ta fada masa? Sai ta jib a gaskiya ya fada musu ba cewa yayi xama a dajin ne ya sa bata jin dadin jikinta bata son yin Magana bata iya cin abinci saboda rashin barcin da ta dade bata yi don haka hutu take bukata, kuma bata son kasar nan Nigeria take so su tafi. Suna ta surutunsu ta koma kan gado ta kwanta tana kallonsu daga karshe suka ce kar mu cika ki da surutu tunda kin gaji mun barki lafiya. Mubarak ma yace yana miki sannu saida safe. Axixa tace waye yace muku ina nan kuma? Suka ce sadik yace ya ga sanda kika je reception kina kuka kika karbi makulli shi ne ya je ya tambayesu suka ce daki kika ce kina so a hawa na takwas lamba 500 shi ne muka xo. Axixa tace saida safe. Suka ce Allah Ya kaimu. Suka fice ta mayar da kofa ta bame.


Bayan ta yi sallar isha’I da dadewa babu ashruf babu wayarsa, sha dayan dare babu ashruf sai ta shiga tunanin kar fa ya xo sun hadu da daddy ya sa an kamashi. Nan da nan hankalinta ya tashi, ta hau leke-leken taga babu kowa, can sai wayar dake ajiye a dakin ta hau kara ta kalli agogo karfe goma sha daya da rabi na dare. Ta mika hannu a sanyaye ta dauka sai ta ji muryar baturiyar da take reception din hotel din ce. Axixa ga wani bako yana son Magana da ke, ya ya a bashi dama xaki amsa? 

Cikin sauri tace a bashi mu yi Magana. Ashruf na karba yace axixa ni ne ki sauko mu hadu a reception. Ta ce to gani nan. Tana ajiye wayar ta saka takalminta ta fito duk jikinta rawa yake don fargaba. Ta hau na’urar da ke hawowa da saukar ‘yan sama cikin sauki wato lift, ta sauko kasa. Tana saukowa babu wanda ta fara hada ido dashi sai dadynta, alhaji ahmad ya kalleta fuskarta murtik kamar xai fashe yace ina xaki? 

Nan fa ta hau gargadar magana tana kame kame. Ya nuna mata hannu alamar ta koma inda ta fito. Jikinta na karkarwa ta hau lift ta koma sama. Ya je reception ya duba ko ina bai ga shruf ba, amma kuma ga ashruf din nan xaune bai ganeshi ba. saboda ashruf din daya sani daxu da yagulallun kaya ya sanshi ga wata kasumba, yanxu ya aske ya kuma sha wani tsadadden kaya tsadadden takalma, hadadden wandon jeans baki da wata hula baka, bakin gilashin ido ya xama jajur dashi kamar bature yayi aski don haka alhaji ahmad bai ma kawo ashruf bane, daya ga bai ga ashruf ba a nan sai ya yi xaton to yana waje yana jiranta, ya koma karamin falon da yake bakin matattakalr da dole dai in axixa xa ta fito ya ganta ya xauna. 


 Wato yau xai ga yadda xa a yi ta sauko. Axixa ta koma daki sai wayar ashruf ta sake shigowa ta dauka yace axixa naga daddy a reception yanxu yana dube-dube ke yake nema? Ta ce na hadu dashi ya koro ni ina jin kai yake nima, don haka don Allah tun da bai ganka ba, kar ka bari ya ganka yayi mun rantsuwa idan ban rabu da kai ba ba sai ya sa an daureka. Ashruf ya kama kai don takaici yace axixa na so ki yi dabara ki fito da wallahi a daren nan xamu bar kasar nan a rasa mu kwata kwata mu yi wajen china ko india koma wasu kasashen afrika inda ba xa a taba tunanin muna can ba in ya so idan an kamamu a kashe ni na yarda da in rasa ki ko ba xa ki bi niba? 

axixa ta sharbe hawaye tace me xai hana ashruf? Nima abinda na yanke shawara kenan koda kuwa ajalina ne binka din da xan yi. Ya ce abinda ya sa na dade ban karaso ba filin jirgi naje na yi cuku cukun duk jirgin da xai tashi a tsakar daren yau ya tashi damu koma ina xai je ga kudina da daddy ya bani xai ishe mu mu je ko ina ne a duniyar nan ga mai tsai a waje yanxu fitowarki ne wahala. Axixa tace kar ka damu kai dai fita daga reception din ka jirani a wajen get din hotel xan fito. Ya ce daman bana reception ina waje sai kin fito.


 Suka kashe waya, axixa ta binciko biro da takarda a cikin lokar gado ta rubutawa mahaifinta doguwar wasika, ta neman gafara da kuma bankwana Allah Ya kaddara saduwarsu ita da masoyinta sun shiga mai fadi don su raya sunnar Manxo (SAW) saboda sun xurfafa, sun yi nisa a fagen kaunar junansu, baxa su iya hakura da juna ba. tana hawaye tana rubutawa harta gama ta bar wasikar a bude a kan gado. Ta harhada ‘yan kayayyakin ta a cikin Jakarta kamar wayarta makilin da brush da comb da dai sauransu ta rataya jakar ta  fito. Sai ta ki biyowa ta lift ta bi ta matattakala tana sauka a hankali harta sauko takalminta a hannu. Kicibis ta yi da alhaji ahmad babanta a nan karamin falon dake karkashin matattakala, yana xaune da remote din talabijin a hannunsa yana kallo, ta sankare a tsaye har saida jakar da ke rataye a kafadarta da takalman dake hannunta suka sulalo suka fado don tsorata da tashin hankali. 


 Alhaji ahmad yace dauki jakar xo ki fita ki gudu wajen masoyinki ki bar mhaifinki axixa. Ni in ce kar ki yi, kice sai kin yi duniya da fadi sai kin gwammace baki tafi ba kin bi maganar maharfini ki saboda bala’I xaki tarar a gaba. Sai kin yi dana sani akwai abinda ni na hango miki wanda ke ba xaki hangoshi ba. na gode da bijirewa maganata. Ba ni da ‘da ko ‘ya sai ke kadai ina rainon ki har kika girma yau kin girma ban isa in ce kar ki yi abu ba ki bari kin fi so ki xauna da wani ni ku barni. Axixa ta ji tunda take a duniya bata taba jin tashin hankali ba irin na yau. Musamman kalaman mahaifinta sai ta rushe da kuka ta durkusa a gabansa tana neman gafarar ya yafe mata, in Allah Ya yarda daga yau ta hakura da ashruf. Alhaji ahmad yace ya yafe mata ya jawo hannunta yace ta xauna kan kujera kusa dashi bayan ta xauna kukan da take ya lafa ya ci gaba da yi mata nasihohi masu ratsa jiki yana nuna mata illolin da xasu afku muddin ta auri ashruf.


 Ya kuma nuna mata illar rashin auren Mubarak da halin da alhaji isa xai shiga mahaifin Mubarak babban tashin hankali ne, ya dauki lokaci mai tsawo yana yi mata nasihohi wanda duk ya sa ta yi nadama. Waya a cikin Jakarta tafara kara, kunya da nauyi ya sa ta kasa tashi ta dauko saida alhaji ahmad yace ta je ta dauka ya san ashruf ne ta yi masa bayani yayi hakuri, daga nan ta wuce dakinta ta kwanta. Tayi godiya ta mike ta dauki Jakarta ta nufi daki a sanyaye, tana shiga ta rufe kofa ta hau gado ta rungume filo tana mai tsananin rudadden tunani. Wayar ashruf ceta sake shigowa, ta dauka ta amsa cikin sanyin murya tace hello ashruf ma muryarsa na rawa yace axixa  daddy ya hana ki ko? 


 Ta ce yana bakin matattakala a xaune. Kan ya sake cewa wani abu sai computer ta fara Magana kudinsa yakare, yayi saurin rubuta mata message yace na san na rasaki axixa, amma bana rasaki ba ne har abada don haka ki yi min alkawarin ba xa ki yi aure ba ni ashruf ni ne mijinki ki karbi sako a wajen ma’aikatan da ke reception, gobe idan kun fito xaku tafi ki gudu gurina mu gudu ina nan a filin jirgin daga jikin wata waya xan dinga hango ku. Ya turo mata message din na xuwa wayar axixa sai kuma cajin wayarsa yakare, wayar tayi kara ta mutu. bakin ciki goma da ashirin ya tarar wa ashruf inda xuciya ta dauke shi ya wurgar da wayar cikin ruwa don takaici. Axixa ta karanta sakon ashruf sai ta yi shiru tana tunani tace a ranta xancen guduwa dai yakau saboda nasihar da daddy yayi min na tsorata, amma xancen kin yin aure na amince na yi alkawari in ya so xan iya rayuwa babu aure har sai Allah Ya kara hadamu.ta rushe da kuka tayi kuka ta gaji har idanuwanta suka kankance kamar ‘yar japan. Daga karshe ta dauko wayarta tace bari na buga masa tunda shi kudinsa yakare kuma dare yayi ba inda xai sayi kati.


 Tana bugawa sai ta ji wayarsa a kashe , ta yi ta yi ta ji a kashe sai ta hakura tana xaune ko gyangyadi babu a idonta balle barci, sai tunani iri iri. Ashruf kuwa nan bakin ruwa ya kwana a xaune yana tunani ya fi kaunar mutuwarsa da ci gaba da rayuwarsa a duniya tunda babu axixa. Washe gari da sassafe axixa ta ji motsin mutane………

.

Comment da sharhi su suke kara karfin guiwa gashinan yau har da biyan bashi na shekaranjiya

[9/1, 6:15 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/1, 6:17 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT2

*10*

.

.

 Washe gari da sassafe axixa ta ji motsin mutane   da motoci ta tashi ta leka sai ta ga su mubarak ne suke xuba akwatina a mota wai tun karfe shida jirgi ya kamata ya tashi amma jama,a da yawa sun makara yanxu karfe bakwai na safiyar yau xai tashi don haka har motoci sun xo daukarsu ,ta yi sauri ta fada wanka tana brush ne ta ji ana kwankwasa ,mata kofa .ta gama ,ta fito ta bude ta ga atika dauke da kayan sawarta a hannunta ta ce ashe kin tashi? 

axixa tace eh, na tashi. Atika tace yi sauri ki shirya kowa ya fito xamu tafi yau dai sai najeriya inda kike son xuwa. bata ce da ita komai ba don takaici, tace a ranta ai ni yanxu na fi tsanar Nigeria ma da ko’ina, saboda anan ne xa’a aura min mubarak. 


 Bayan ta kintsa daman tun asuba ta yi sallah sai ta hada komatsanta suka yo kasa. A hanyarsu ta saukowa kasa tana kokarin gwada wayar ashruf amma shiru a kulle, hankalinta ya yi kan sakonta da xata karba a reception da ashruf ya bayar a ajiye mata, amma babu hali duk inda ta yi sai taga su atika da munnira makale da ita mubarak  ma ya hangota ya xo ya isheta da sannu yaya jikin ki? Me ya sameki a ido? Ciwo yake? 

Haka ta hakura suka shiga mota ita da atika da munnira ne kadai a motarsu su mubarak ma motarsu daban daddy da jama’arsa suma motarsu daban. Bayan kowa ya shiga motar xuciyar axixa ta dinga xullumin bata karbi sakonta ba, sai ta yanke shawarar taje kawai ta karbo koma me xa a xarga a xarga. Har an bude get xa su fita tace da direba ya tsaya ta yi mantuwa aka tsaya ta fito da sauri ta shiga reception. Matar da aka bawa sakon na ganin axixa sai tace yauwa tun jiya ya bani sako in baki yace… 


 Sai ga muryar alhaji ahmad yace yace me? Suka juya da sauri sai axixa taga babanta. Nan fa matar ta yi sauri ta canja xancen tace yace ya kai abinci ya jere akan tebur. Dake tun jiya matar ta fuskanci soyayyar da ke tsakanin axixa da ashruf sannan alhaji ahmad baban axixa baya son abin don haka ta san mai jera musu abinci namiji ne sai tace yace ya jera abinci, axixa ta yi ajiyar xuciya ta ji dadi ainun da wannan dabarar da matar nan ta yi tace ai mu har mun fito xamu tafi xamu ci a jirgi mukullin dakinku ne na manta ban baku ba gashi. Ta mikawa matar ta dauko kudi mai yawa ta bata. Axixa ta mika mata hannu suka gaisa ta yi mata godiya suka yi sallama.


 Hawaye ne yake xuba daga idanun matar don tausayin masoyan nan axixa na gaba babanta na biye da ita harta shiga mota, xuciyar ta cike da bakin cikin bata karbi sakon ba, bata san me ye ba kuma. Suka isa filin jirgi suka tsaya a inda motoci ke tsayawa, ma’aikata suka dinga dibar akwatinansu suna shiga  wajen da matafiya ne kawai xasu shiga inda daga nan sai cikin jirgin wato (screening) axixa sai hange hange take yi ko ta hango ashruf, har jikin wayar daya ce su hadu ta waiga baya nan sai hawaye ya yi ta xubo mata tana cewa a ranta ashruf sai a Darussalam kenan rabuwarmu ta xo rabon da in ga kyakkyawar fuskarka tun jiya da yamma da daddare bamu hadu ba. ta hango su mubarak har sun fara shiga screening ta juya bayan ta ta ga babanta na biye da ita sai ta saduda ta hakura ta nufi dakin screening. Kamar daga sama ta ji an kwala mata kira. Ta juya da sauri don taga mai kiranta. Babanta ma ya  juya da saurinsa harda tsayawa cak kamar shi aka kira. Matar ta karaso wajen da axixa da mahaifinta suke tsaye tana hucin gudun da ta sha ta ce, axixa gashi kin yi mantuwa a reception da kuka tsaya. Allah sarki wannan matar ce ta reception din hotel taga ba xa ta iya barin axixa ta tafi ba tare da ta san me ashruf ya rubuta a jikin wasikar nan ba. alhaji ahmad sai gwale ido yake  ya ga me ta ba wa axixa amma axixa ta damke kam a hannunta, ta mikawa matar hannu suka gaisa sannan ta rungume ta dan farin ciki, suka yi sallama su axixa suka shige matar ta juya ta tafi. 


 Alhaji ahmad yace da axixa duk kin rikice kin dagule gashi er tsayuwar da kika yi saida kika yi mantuwa, me nene da kika manta? 

Axixa tace waya tace na mance. Bayan sun shiga an gama binciken passport dinsu da komai da komai sai aka umurce su da su yi sauri su wuce jirgi ya kusa tashi. Suna tafiya xuwa wajen jirgin ne axixa ta samu ta kutsa can gefe, gefen da babu wani a cikin abokan tafiyarta, sai turawa, su kuwa babu ruwansu da leke-leke, ta ware wasikar da sauri sai taga wani gallelen xoben diamond wanda in har xa a kiyasta da kudin Nigeria xai yi dubu dari uku. Ta juya xoben ta sake jujjuyawa sannan ta karanta wasikar kamar haka.


 Axixa.

 Kar ki yi aure ni ne mijinki wannan xoben kuma ki karbeshi a matsayin sadakinki, xan xo Nigeria in taho dake, ga sadakinki! Sadakinki!! Sadakinki!!!


 Har sau uku, axixa ta cukwikwiye wasikar ta hada da xoben ta danke a hannunta ta runtse ido ji take dama kasa ta bude ta tafka ciki ta fada ta mutu ta huta. Sannan ta saka xoben a hannunta tana jujjuyashi, kamar dan ita aka kera xoben nan sai walkiya yake yi. Can a karkashin xuciyarta ta ji maganar babanta ta fado xiciyarta daya ce “kin auri mubarak kin gama” ta yi tsai tana tunanin tabbas babu yadda xa a yi a barni a xaune haka babu aure dole xan yi aure idan kuma na cewa ashruf na karbi sadakinsa na yi karya dole xa a yi min aure. Sai taxare xoben ta nufi tebur din wani ma’aikaci  da yake rubuce rubuce. Ta ce ya bata takarda da biro da sauri don ta hango daddynta na nemanta har su atika sun shige jirgi, cikin sauri ta rubuta “no” ma’ana a’a sai ta nade xoben a cikin takardar tace da ma’aikacin ka kaiwa ashruf don Allah. mamaki ya rufe ma’aikacin nan yace mata wane ne Ashruf? 


 Agigice take ga abbanta nan yana dube dube, yana tambaya shi da ‘yan korensa a bayansa. Hayaniya ta ji a bayanta tana juyawa sai ta hango ashruf ne da ma’aikata ya shigo screening room bashi da passport ba tikitin shiga jirgi suka tarashi. Shi kuma a gigce yake yana hango axixa xata tafi, shi ne ya shigo a guje. Axixa tace da ma’aikacin wancan da aka rike shi ne ashruf ka bashi don Allah. ta dauko kudi ta bawa dan aiken. Ai yana jin dumus a hannunsa sai ya mike ba tare daya kara sakon daya ba, da sauri ya bi ashruf don ‘yan sanda sun kamashi xasu yi waje dashi. Axixa na waiwaye tana ganin wanda ta aika ya mika masa sai ta juya da sauri  tana hawaye ta nufi jirgi. Tana jin muryar ashruf yana kiran sunanta. 


 Daddy ya tafi nemanta shi kuma an tafi nemansa saboda axixa harta rigashi shiga jirgi saida ibrahim ya fito ya kira su yace ai axixa tuni ta shiga jirgi, sannan ya dawo suka shiga. Axixa a kusa da wata karamar yarinya ta xauna ‘yar turawa don bata son ta xauna kusa da daya daga cikin abokan tafiyarta a dameta da tambayoyi don haka ta tafi can baya ta xauna kusa da wata ‘yar yarinya. An rufe kofar jirgi, jirgi yayi haramar tashi, kuka mai tsanani ya keto mata marar kakkautawa, xuciyarta sai fat fat take kamar xata fado, yawun bakinta ya kame. Radadi da xogi a kwayar idonta, farin ciki ya gushe mata, ji take kamar tunda take a duniya bata taba yin dariyar farin ciki ba. wani sabon son ashruf ya sake sarketa, tsanar Nigeria ta shiga xuciyarta.


 Sai  da ta fara karanto inna lillahi wa’inna ilaihi ra ji’un da sauran addu’o’I sannan ta fara jin wasai hawayen ne dai bai daina xuba ba. ‘yar karamar yarinyar nan na kallonta itama sai ta fara hawaye don ta san idan taga babba yana kuka to  tabaci ne. ta ringa gitsuro tissue tana mikawa axixa tana karba tana share hawaye, har dai kukan ya tsaya mata jirgi kuwa ya lula yaketa gajimare ya bude wuta sai gudu yake a sararin samaniya ba kakatawa. 

Al’amarin ashruf kuwa bayan ‘yan sanda sun kamashi suka yi waje dashi da ma’akacin da axixa ta aiko ya xo ya mika masa sako, ya juyo ya kalleta ta kalleshi kana ta juya da sauri ta tafi sai hankalinsa ya tashi bai ma damu da ina ‘yan sandan nan xasu kaishi ba suka nufi motarsu xasu sashi a mota su je osfishinsu ya yi bayani me ya shigo da shi screening room tunda shi ba matafiyi bane, sai dai ko in sata ya xo yi. Sai ga mr Johnson nan, nan fa suka yi ta dogon turanci yace a shaukin so yake har ya fara xautuwa budurwarsa yake bi. Dake ‘yan sandan turai ne da bayanin mr Johnson ya gamsar dasu sai suka sake shi.


  basu ce sai sun tafi dashi ba, sun dai lalubi na goro kawai. Mr Johnson ya sa ashruf a gaba suka doshi wajen daya ajiye mota, a lokacin ne ashruf ya bude jukukkuyar takardar da axixa ta aiko masa. Yana budewa yaga xobensa bata karba ba, yayi sauri ya duba jikin takardar ya gata rubuta no. wato ba xai yiwu  ba ta karbi sadakinsa ta ki yin aure. Nan fa ashruf ya tsugunna ya rike kai wani hawaye mai wuyar fita ne yake keto masa kai kace ruwan hawayen da barkono aka dama don radadin fitarsa. Nan  kuwa tsabar tashin hankali ne. kara yake yana cewa axixa ba kya so na daman kika dawo min da sadakina dana ba ki? 

Mr Johnson ya ji haushin ashruf ya kamashi ya ma rasa me xai ce masa, shi a wajensa soyayya bata lokaci ce, idan ba kudinsa aka taba bame xai sa shi ya shiga tashin hankali irin na  ashruf haka? 


 Mr Johnson ya fusata yace da ashruf na fa gaji da irin wannan rashin hankalin, ka yinan in bi ka, ka yinan in kamo ka, sai in hada ka da en sandan can su tafi da kai, gobe mu yi tafiyar mu Croatia , ba xamu jiraka ba, kuma da kudin ka xan tafi babu wanda xai bar maka kudin jirgi. Soyayyar banxa an baka kudi an baka farin ciki. Ka tashi mu ta fi na ce maka. Yayi yayi ashruf ya ki tashi daga tsugunan nan. Sai daya shiga lallashi yana yi masa dabaru kai ka ce yaro ya samu dan shekara bakawai wai ashruf ka yi hakuri xan kaika Nigeria da kaina ka ga axixa. Ashruf dai na jin sa yana fadin yaro xaka yiwa wannan wayon, a ransa. Daga karshe dai ya goge hawayen sa ya tashi suka karasa wajen mota suka shiga sai hotel din da suka sauka, ya yarda da kaddara tunda shi musulmi ne.


 ABUJA NIGERIA

Su axixa basu isa Nigeria ba sai karfe shida na yamma, saboda tsaye-tsayen da suka sha yi a kasashe iri-iri suna sauke matafiyan kasar suna daukar wasu. Kafin su karasa Nigeria daman an san da xuwansu don haka wasu galla-gallan motoci ne sun doshi guda ashirin suka xo taryensu. Motocin gidansu atika sun xo da ‘yan gidansu, haka mubarak, munnira, sadik, Ibrahim da ta gidansu axixa. ‘yan uwa da abokan arxiki su hallara a filin jirgin nan don murnar ganin axixa, hankali ya tashi da aka ce an rasata. Bayan an gaggaisa nan fa aka dungum gidan su mubarak saboda hadaddiyar liyafar da alhaji isah ya shirya musu. Musamman ma dai don axixa ya yi ta ta sannu da xuwa da barka da arxiki da aka ganta. An ci an sha an cashe yara da manyansu maxa da mata. Amma axixa karfin hali ta yi don babu walwala a xuciyarta kowa ya ganta ya san ba axxy ta da bace. Ta wani kode ba kwalliya ido ko kwalli babu hawaye ya wanke.


 Bayan an gama shagali kowa ya wuce gidansu. Alhaji ahmad baya gajiya da yiwa axixa nasihohi iri-iri dan ya ga hankalinta ya kwanta haka atika ma tana yawan xiyartar axixa tana bata baki duk da dai har yanxu basu san me ke damunta ba. daga mahaliccinta sai ita sai babanta suka sani, don haka su a tunaninsu batan da ta yi ne ta dawo haka, kullum cikin damuwa take. Da kyar da rubutun sha na dangana da addu’o’in da alhaji ahmad ya sa ake yi mata ya sa ta fara sakin jikinta tana rage damuwa. Alhaji ahmad ya roketa Allah, Annabi ta ringa kula mubarak kamar yadda suke da don shima yaron duk al’amuransa na walwalar yau da kullum duk sun canja har mahaifinsa ya fara cewa shi kwana biyu ya ga dan sa ya canja axixa ma ta canxa . Axixa ta yiwa mahaifinta alkawarin in Allah Ya so xata yi kokarin ta cire tunanin ashruf kuma xata dinga kula mubarak. Ya ji dadi da abinda ‘yarsa ta fadi yayi mata addu’a Allah Ya yi mata albarka Ya kuma bata da na gari wanda xai yi mata biyayya fiye da yadda take yi masa.


 Siyasar Nigeria ta yamutse xabe yana tunkarowa don yanxu saura wata tara xabe. Haka kuma auren mubarak da axixa bai fi sauran wata goma ba. don haka duk inda ka ga axixa ka ga mubarak. Wata sabuwar soyayya ceta sake budewa, hankalin mubarak ya kwanta haka na iyayensu, kai har ma kawayenta su atika da munnira. Axixar su ta dawo irin tada, su je ko ina tare kamar bikin auren kawayensu, bairthday parties na kawayensu su fita wuraren shakatawa iri-iri na Abuja kamar su 911, millennium park da dai sauransu. Bayan dawowarsu da wata biyu ne wata ranar asabar  mahaifin axixa yake liyafar murnar xagayowar ranar haihuwarsa ya cika shekara hamsin da biyar a  a duniya. Ya hada hadaddiyar liyafa a babban dakin taron nan a nicon Abuja , gaga-gaggan ‘yan siyasar Nigeria sun hallara abokan kasuwancinsu daga kasashe daban daban sun hallara, biki bidiri ya fara da karfe hudu na la’asar. Har da axixa da kawayenta mubarak da abokansa ‘yan uwa da abokan arxiki, kowa ya xo. Ana ta wasa da dariya, ciye-ciye da tande tande. Mahaifin mubarak ya kalli mahaifin axixa yace da sauran jama’ar ni kuwa ina son ku tayani yiwa shugaban fada yaki ya yi aure. Wane irin shugaban kasa xamu yi a Nigeria babu first Lady? 

Duk wajen aka sa dariya, harda su axixa. Da yawa suka yi ta mamakin ya aka yi mutum magidanci mai kamala da rikon addini bashi da aure. Alhaji ahmad shima yayi dariya sannan yace da alhaji isa ka fada musu bayan rasuwar uwar gidana aurena nawa me kuma yake rabani da matan? 


 Alhaji isah yace baka so a batawa wannan ‘yar diyar taka axixa, to axixar na aure xata yi ta bar ka. Alhaji sadam yace maigirma shugaban kasa ka bashi kunya nan da sati daya ka yi aurenka kar fa a xo ana bikin ‘ya’ya ana na iyaye. Nan ma kowa ya tunsture da dariya. Alhaji ahmad yayi murmushi yace af! Kune baku sani ba nan da wata daya xaku ga katin gayyata don na sami mata har an sa rana. Haka dai ana xolayar dan takarar shugaban kasa ana kyakyacewa har karfe bakwai bayan an ci an sha an gyaste sannan aka yi salla aka fara watsewa. Bayan axixa da kawayenta sun fito ne sai munira tace xata je maitama wajen wata auntynta . axixa da atika kuma suka nufi life camp unguwar su axixa. Axixa ce ke tuka galleliyar motar da babanta ya galla mata bayan dawowarsu, daga tafiya. Sun kusa shiga layinsu sai cikin axixa ya fara murdawa.


 Ta cije bata yi Magana ba, ta ji da gaske yake ciwo. Ta sulale gefen titi ta tsaya, atika tace lafiya kike cije baki kuma kika tsaya? 

Axixa tace cikina ne yake murdawa haka yake yawan yi min kwanan nan. Sai in dinga jin kamar ‘ya’yan hanjina xasu xubo. Atika tace subhan Allahi, fito in tuka mu karasa gida. Da kyar axixa ta fito ta dawo wajen atika, atika ta shiga ta tuka suka nufi kataferen gidan su axixa. Masu gadi ‘yan sanda suka bude babbar kofar shiga gidan da sauri gami da sarawa uwar dakinsu, suka wuce. Da taimakon Allah da taimakon atika axixa ta iya fitowa daga motar nan suka shiga cikin gida. Atika xata wuce da ita dakinta a sama tace ta barta a falon farko xata kwanta a kan kujera.


 Atika ta kwantar da ita kan doguwr kujera, tana ta yi mata sannu. Kowa ya ga axixa ya san ba karamar ukuba take ji a yau ba. ciwon ciki ai bala’I ne. atika ta nufi bandakin dake cikin falon don yin alwalar magaruba, tana shiga ta ji an banko kofar bandaki da karfi sai ga axixa a guje ta xo tana kwararo amai. Hanakalin atika ya tashi tana rike da ita amai sai xubowa yake har ‘ya’yan hanjinta motsawa suke, ta kyala amai, amai mai yawa, sannan atika ta bata ruwa ta kuskure bakinta ta wanke fuskarta. Atika na rike da ita xuwa kan kujera ta kwantar da ita. Ta koma bandaki, tayi alwala ta fito, ta fara sallah kenan ta ji axixa ta sake shiga bandaki a guje tana kwarara amai. Babu yadda xata yi salla take. Tana idarwa ba tare da ta tsaya yin addu’ar kirki ba ta tashi da gudu ta bi axixa bandaki. Ta iske ta a kwance a kasa tana kwararo amai daga kwance. Atika ta hau kwakwaxo tana hawaye tana na shiga uku axixa kar ki mace mun daga ni sai ke!


 Ta dagota da kyar ta wanke mata fuska da baki ta sakalo kafadarta suka fito, bayan ta kwantar da ita ta shiga cikin gida da sauri ta leka ko ina babu kowa. Ta shiga kicin  sai ta iske ‘yan aiki mata da kuma kuku su uku maxa. Ta ce idan daddy ya xo ku ce na tafi da axixa asibiti bata da lafiya. Cikin rudani suka ce me ya same ta? Suma ma’aikatan gidan sun ga canji a wajen axixa saboda yanxu tana kyautata musu babu abinda bata basu. Babu fada da kyara da kyama irinta da, wasa da dariya ce a tsakanin su. Kuma duk sati tun dawowarta take musu rabon kudi duk juma’a mai yawa kuwa wani lokaci har suturunta take bawa matan. Don haka suma tsanar da suka yi mata da sun daina, har basa so ta fita, amma da addu’a suke ta yi tayi tafiya su huta. Suka biyo atika yuu, har wajen axixa, suna ta yi mata sannu. Daya daga cikin masu aiki mai suna amina tace an yiwa daddy waya ba a same shi ba? 

atika tace af ni na rude ma na manta da wata aba waya.  Ta dauko handset dinta ta buga ta ci sa’a tana ringing kash amma ba a dauka ba, ta sake redialing tana ringing ba a dauka ba. ta  ce ba a dauka ba ina jin ya barta a mota ya shiga filin jirgi kin san sun tafi raka su mr henrry filin jirgi xasu juya London yanxu tace da guda biyu daga cikin matan  masu aiki ku tayani mu sata a mota mu tafi asibiti da ita.

Comment da sharhi su suke kara kwarin guiwa nayimuku posting inba

Comment to sai bayan kwana ashirin da hudu

[9/1, 6:17 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/3, 7:34 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT2

*11*

.

.

Ku tayani mu sata a mota mu tafi asibiti na nemi daddy a waya idan kuma ya xo gida ku gaya masa mun tafi international hospital. Amina da Rebecca ne suka tallafo axixa xuwa bakin mota, atika ta hau sama dakin axixa da gudu ta dauko dan karamin katin ganin likita. Ta fito ta iskesu a bakin mota nan ma wani sabon amai axixa ta kyelaya. Bayan an goge mata bakinta da fuskarta don hawaye ne keta xuba kiran Allah! Allah!! take sai daddynta kuma suka sakata a bayan mota ta kwanta. Atika tace amina ta xo su je dan ita babbace. Rebecce kuma ta je ta gyara duk inda ta yi amai. Sai international hospital. Basu wani bata lokaci ba suka wuce da ita wajen likitanta, mai suna dr Rislan. Idan axixa ta je ko mutane nawa ne ke jiran ganinsa xai bar su ya dubata tukunna, yana ganin axixa cikin wannan hali ya mike da sauri yace da matar daya ke dubawa ta yi hakuri ta jira shi a waje ya gama da axixa tukunna. Bayan sun dorata kan gadon duba marasa lafiya sai likita ya shiga yiwa atika tambayoyi wata ta amsa in ta sani wata kuma axixa ta amsa da kyar.


Ya ce da atika xai so ya auna fitsarinta yanxu don ya ga me ke damunta takmaimai, ya basu kwalba da bandaki a afishin atika na rike da ita suka shiga, ta yi fitsarin. Ta kawo masa, ya kira daya daga cikin ma’aikatan asibitin yace maxa ta kai laboratory na asibitin yanxu a auna fitsarin nan a kawo sakamako. Axixa kwance take cikinta na murda mata tace xata yi amai a kawo wata wata roba ta kasa, ta sake cewa ga amai nan a matso da robar ta kasa don duk abinda ta ci ta gama amayrwa babu komai a cikinta. Likita nata gwaje-gwajensa yana ‘yan tambayoyi ya matsa cikinta yace da xafi? 

Inda xafi tace eh, idan babu tace babu atika da amina mai aiki suna waje kan benci. Atika nata gwargwada  wayar daddyn axixa. Sai can ta ji an dauka bayan sun gaisa taji muryar bata daddy bace tace, da wa nake Magana? Ya ce ni ne habu direban alhaji isah. Atika tace ina alhaji ahmad din? Ya ce shi da alhaji isa tun daxu suka shiga cikin filin jirgi basu fito ba xasu ga tashin wasu baki. Atika tace to idan sun fito ka ce atika kawar axixa  ta kira cewar axixa bata da lafiya muna international hospital.


 Ya ce to Allah Ya sauwake. Tana cikin wayar ne taga nurse din da fitsarin da xa a auna taxo ta wuce. Sai ta tashi ta bita ciki. Bayan  ta bawa likita ta fita, sai likita ya bude sakamakon gwajin ya duba ya koma ya xauna a sanyaye ya sake ya duba rasitin ya kuma duba takardar sakamakon. Atika ta xo ta xauna a kujerar dake gaban teburin likitan tace. Dr rislan lafiya? 

Me nene yake damun ta? 

dr rislan ya dago ya kalli atika yace yaushe aka yi bikin axixa? 

Atika tace saura wata goma ba a yi ba ma. Ya ce an daura aure? 

Atika tace a’a ba a daura ba wani abu ne? 


 Dr rislan yace sakamako ya nuna axixa tana da juna biyu na wata uku. Yana rufe bakinsa axixa na rikito daga kan gado ta mike ta dora hannu aka ta kwalla kara. Atika da dr rislan suka riketa. Babu abinda axixa take gani sai jujjuyawar komai kafafunsa ya koma sama. Can ta sankare ta mike ido ya kame mata numfashi ya tafi. Wa’iyyaxu biLllahi, atika ta fasa ihu kira take likita dubata xata mutu. dr rislan ya danna kararawa, kan ka ce kwabo ofshin dr rislan ya cika da kwararrun likitoci, a cikin masu shigowa kuwa harda alhaji ahmad da alhaji isa da alhaji sadam, wato mahaifin atika sun shigo kenan suka ga likitoci a guje suma suka bisu, alhaji ahmad ya ga tashin hankalin da bai taba gani ba ‘yarsa axixa ce a mimmike a sankare ido a kafe akan gado an turata an yi dakin nemo numfashi da ita.


 Rislan dasu alhaji isa sai hakuri suke bashi suna bashi Magana cewar bata mutu ba cuta kuma ba mutuwa bace. Atika sharkab ta yi ta yi daidai tana rusar kuka. Amina na rirriketa, dr rislan yace su shiga ofishinsa su xauna xai je ya ga halin da axixa take ciki. Bayan xamansu da kamar awa daya da rabi, kowa yayi shiru yana karanto addu’ar da ta xo bakinsa, bude kofar dr rislan ce tasa kowa ya dago, alhaji ahmad yayi xumbur ya mike yana tambayar likita yaya? 

Dr rislan ya sa hankici ya goge gumin goshinsa yayi murmushi yace da alhaji ahmad ya xauna yace ka kawantar da hankalinka axixa ta bude ido har tace ina daddy. Su duka suka ce Alhamdulillah. Dr rislan ya xagaya kujerarsa ya xauna. Alhaji isa el yakub ya jawo kujerarsa gaban teburin likita yace wai takamaimai me ke damun ‘yar mu? 

Likita ya ciro takardun da ya yi rubuce rubucen bayanan da axixa ta yi masa da kuma takardar sakamakon gwajin da aka yi mata yace a bayanan da ta yi mana na abinda yake  damunta  ba mu tabbatar da takmaimai abinda ke damunta ba saida muka yi mata gwaji na fitsari. To sakamako ya nuna ‘yarku tana dauke da juna biyu na wata uku. Su duka suka hada baki CIKI!!! Likita yace ciki to saboda girgixar da ta yi da bacin rai shine ya sa ta fita hayyacinta ta fadi a sume.


 Kuma  bacin rai ya so ya yi mata yawa daman tana yawan tunani kuma ba a so yayi mata yawa da juna biyu da yawan tunani don haka kar a sake a yi mata wata maganar da xata bata mata rai, ko kuma a nuna mata ciki wani abu ne na tashin hankali, ku yi kokarin kwantar mata da hankali gami da yi mata fatan Allah Ya sauketa lafiya. Don yanxu saura kiris hawan jini ya kamata, kuma ban da Allah Ya kiyaye da cikin ya xube, amma yanxu ita lafiya abinda ke cikinta ma lafiya. Alhaji isah el yakub ya sa hannu ya dakatar da likita yace kai rislan ya isa dan Allah ka bar mu mu ji da abinda ke damunmu da wannan bayane bayane naka na banxa, wai ba dan Allah Ya kiyaye ba da cikin ya xube, ya xube mana dan uban cikin cewa muka yi muna so, yara sun ja mana abin kunya a wajen adawa, daman kiris ake jira.


 Alhaji ahmad kuwa tunda ya rike kai ya sunkuyar da kai kasa bai sake cewa komai ba sai xufa ke keto masa duk da fankar ofishin alhaji sadam kuwa babu wacce yake harara sai ‘yar sa atika cewa yake saura ke duk sai an gwadaku dan ubanku. Daman nima hankalina bai kwanta da barin ‘ya’ya mata ba balagaggu su tafi wasu kasashe da gardawan samari ace ba xa a yi masha’a ba, xamani dai an ce haka ake yayi rayuwar hutu. Yanxu ina hutun yake? 

Hutu ko tashin hankali, likita nata basu Magana yana basu hakuri, yace in kuna son ganinta tana can wani daki nurse a waje ta rakaku don mun bata gado xamu ci gaba da kula da lafiyarta sai ta huta sosai kar hayaniya ta sake saka mata wata damuwar a sanyaye  suka fita wata nurse ce ta rakasu dakin da axixa take kwance ana kara mata ruwa, suka yi mata sannu, ta amsa da kyar, alhaji ahmad dai kallon ‘yarsa yake samun lafiyarta shi ne burinsa, cikin ma ya dameshi amma ya san kome ya samu bawa kaddara ce daga Allah ya san ‘yarsa ya san halinta shedan yana tare da kowa amma mutum ya xamanto koda yaushe yana fada da xuciyarsa a duk lokacinda take kunsa masa sharri.


 Bayan sun yi kamar minti goma sha biyar da shiga sai suka ce xasu tafi. Alhaji ahmad yace xai aika a dauko yayarsa hajiya lantana dake kado estate gidan daya saya mata ita da ‘ya’yanta da jikokinta, atika ta yi sauri tace daddy xan xauna da ita abar hajiya lantana ni da amina mai aiki muka xo mun isa mu xauna da ita. Alhaji ahmad yace to madalla shi kenan. Haka suka shiga motocinsu sanyi kalau babu mai Magana har unguwar life camp gidan alhaji ahmad suka shiga kayataccen falon da yake xama da bakinsa. Tsawon minti ashirin babu wanda yace wani abu. Alhaji isa el yakub ya nisa yace wai alhaji ahmad me nene abin yi? Na ji ka yi shiru sai ni da alhaji sadam muke ta babatu. Alhaji ahmad yace alhaji isah mai xan ce da kaddarar Ubangiji? Kaddara mai kyau da marar kyau ta sami musulmi sai ya runguma. Daman ‘da ko ‘ya amana ce Allah (SWT) Yake bawa bayinsa kuma ranar gobe kiyama mutum yayi bayanin wacce irin tarbiyya ya bawa dan da aka bashi, musamman ‘ya mace sai an sa ido amma saboda al’adunmu sun yi baya, ba ma amfani da abinda Manxo (SAW) yace idan yarinya ta shekara goma sha biyu a aurar da ita, mun dauki al’adun turawa yara suna da ‘yanci su yi abinda suka ga dama ba a tsawatar musu, gashi nan yan ce ranar da nake dana sanin barin  axixa ta kawo xuwa yanxu ban aurar da ita ba, na dauka tana daukar gargadin da na ke yi mata. Inna liLlahi wa’inna ilaihi raji’un. Alhaji isa yace har yanxu ban ji mafita ba alhaji ahmad yaya xamu yi da cikin nan da dana ya yiwa ‘yarka? 


 Alhaji sadam yayi gyaran murya yace alhaji isa ai gaggawa daga shedan take ka bari a yi naxari sosai sannan a fara xancen mafita, babu laifin axixa babu laifin mubarak, laifin ya fi a garemu. Alhaji isa yace babu wani laifin,mu dan mun amince su fita su huta mun ce su siyo ciki? 

Ai babu ja, dan iskan namiji sai ‘yar iskar mace. Don ni na san na yiwa dana tarbiyya. Dukkansu suka bude baki don mamakin kalaman da suka fito daga bakin alhaji isa el yakub, kamar a mafarki. Ya tashi ya kade rigarsa ya sa kai xai fice har ya kai bakin kofar fita ya juyo yace wannan cikin a xubar idan bahaka ba xance babu ruwan ‘dana. Alhaji sadam y ace don ka san cikin ba a jikin danka yakeba ko? A xo cirewa ta mutu ba asararka bace ai.

 Ya ce oho ku kuka sani. Ya kada kai ya fice abinsa. Tashin hankali ya tabbata a xuciyar alhaji ahmad a daren yau ji yake dama ba a halicce shi ba, baya kunyar me mutane xasu ce masa kamar alhaji isa shi ‘yan adawa yake tunani. 


 Shi tsayuwa a gaban Ubangijinsa shi ya fi damunsa. Nan dai alhaji sadam yayi ta bashi baki akan ya yi hakuri ya cire tunani ya kuma toshe kunnansa akan abinda alhaji isah xai ce kasancewar sun sanshi butulu ne. daga karshe alhaji sadam yayi masa sallama yace saida safe, ya tafi. Alhaji ahmad ya kasance ya kwanan a xaune yana tunani, yana kuma addu’o’I Allah Ya rufa musu asiri Ya kiyaye gaba. A asibiti kuwa kwanan su atika suka yi basu runtsa ba, axixa na ta faman fixge ruwan da ake kara mata wai sai ta fita ta bar kasar an rasa  ta don abin kunya xai xamewa mahaifinta, likitoci na rikota atika na yi da kyar dai aka yi mata allurer barci ta samu ta yi barci sannan wajen asuba suma su atika suka samu suka kwanta hakarkarinsu saida su axixa suka kwana biyu a asibiti sannan mubarak ya xo dubata shi da abokansa ibarahim da sadik. 


 Bayan  sun yi mata sannu sun ajiye kayan dubiya sun xaxxauna akan kujerun dake dakin, sai atika tace mubarak kwana biyu ba mu ganka ba ko ka yi tafiya ne? ya yatsune fuska ya tabe baki y ace no! ina nan a gari xuwan ne dai kawai ban xo ba.  axixa ta ji gabanta ya fadi ras, tace a ranta yau mubarak ne yake mun irin wannan yatsunar kamar Kashi? 

Ta ce to ni dai sai yadda Allah Ya yi dani. Suka mike suka ce xasu tafi mubarak ya xaro bandir din ‘yan dari biyar biyar ya jefawa axixa kan gado yace gashi a siyawa baby kayan kara lafiya tunda ku masu ciki ana so ku ringa cin  kayan kara lafiya. Hawaye ne ke xuba daga idanuwan axixa kawai , ta  kasa Magana, atika ta fusata ta dauki kudin daya jehowa axixa ta biyoshi don a lokacin har sun fita daga dakin ta seta keyarsa ta buga masa bandir din kudin tace mubarak karya kake ka yiwa axixa irin wannan wulakancin kafin ka rike dubu hamsin axixa ta rike dubu dari, to ko a kotu xa ka yi bayani don axixa bata da wani saurayi daya wuce ka dan iska kawai. Ya kufula ya kawo mata mari abokansa suka rike shi, suka ja shi suka tafi. 


 Axixa na bakin kofar dakin tana kallonsu ta rushe da kuka. Nan atika ta tsaya tana lallashinta muryar mahaifin axixa ce yace lafiya kuka fito? 

Axixa ta tafi da sauri ta rungume babanta tana rusar kuka, alhaji ahmad yace ya isa mu shiga daki. Bayan sun shiga daki  ne yake tambayarta me yake faruwa. Atika ta xayyane masa duk yadda suka yi da mubarak. Alhaji ahmad take ya ji wani daci ya cika makoshinsa don takaici. Amma sai ya nuna musu su kwantar da hankalinsu wannan ba komai bane. Kwanan axixa takwas a asibiti aka sallame ta. Ranar da aka sallameta ne da daddare axixa atika da munnira suna wani falon da yake daga cikin gidan suna kallon wani American film mai suna SPECIES suna ta kokarin kwantar mata da hankali su bata wannan labari na abin dariya tana dan daurewa tana yi amma ba har xuci ba don xuciyarta cike take da takaici. Babanta kuma alhaji ahmad yana falo tare da wasu ‘yan uwansa da suka xo duba lafiyar axixa daga yobe, garinsu alhaji sadam da alhaji bala suma duk suna tare a falon ana ta hira ana kora lemo. Sai ga alhaji isa el yakub da dansa mubarak da tawagarsa babu sallama babu kwankwasa kofa sun fado musu falo budik! Kowa ya juyo yana kallonsu, alhaji sadam yace haba alhaji isah kai jahilin ina ne? haka babu sallama ka fadowa mutane gida.


 Alhaji isa yace sallamar me xan yi a gidan da ake aikata masha’a, ba abinda ya kawo ni bane, ni abinda ya kawo ni shi ne in fada anan ko kuwa xa a matsa a bamu waje mu kebe dan sirri ne amma alhaji sadam da alhaji bala ku xaku iya xama danku xama shaidu. Alhaji ahmad yace ko me ka xo ka fada ka fada ka fita ka bamu waje. Alhaji isa yace niba xai shafe niba kai xai shafa koma a gaban mutanen na fada amma adalcin da xan yi ma shi ne ina baka shawarar wadannan bakin su fita su jiraka a waje idan ka ki kuwa xan fada. Su da kansu suka mike suna hararar alhaji isa ji suke kamar su daga shi su dokeshi duk da ma basu san meye yake faruwa a tsakanin suba. bayan sun fice alhaji isa yace da tawagarsa su fita suma su jira  a waje yace da mubarak ya sami waje ya xauna mubarak ya xauna yace aje a kira axixa. Alahji sadam da kansa ya leka falon da su axixa suke ya kirata.


 Gabanta ya yi mummunan faduwa ta san yau ranar tonen silili ce. Atika da munnira kuwa suka yi fiki-fiki, suna fargaba da xulumin me ye kuma. Bayan ta shiga falon ta sami waje ta xauna a kasa gefen babanta shima alhaji isa ya xauna kusa da dansa, sannan yayi gyaran murya yace alhaji ahmad ka nutsu kai da sauran ku ji abinda ke tafe da ni masalaha na xo a yi ba bacin rai ba akan xancen cikin yarinyar nan axixa. Ya gyara xama gami da goge baki ya ci gaba da cewa a matsayinka na abokina duk da dai na girme maka amma kuma shugabana tunda kai ne shugaban ni ne mataimakinka. Gani ga ‘ya’yanmu ga alhaji sadam da alhaji bala ku yi naxari sosai ku bani amsa mai kyau saboda na san me yiwa abinda xan fada yanxu xai iya girgixa ku koma ya sa ku fita hayyacinku amma idan kuka nutsu kuka duba abu ne sassauka. Abinda na xo dashi shi ne na xo ne in baka xabi in ma ka sauko sadan-sadan ka bani kujerarka ta neman takarar xama shugaban kasar Nigeria ka dawo mukamina na mataimaki, ka kuma je da kanka ka fadawa shugaban jam’iyya da sauran al’umma baki daya, ta kafar watsa labarai rediyo, talabijin, jaridu da dai sauransu. Yana rufe baki alhaji bala ya mike ya yo kansa da fada yana cewa..


 Alhaji isa ka cika marar kunya marar mutunci da manta alherin baya kai idan ba don alhaji ahmad ba da ina ma xaka shigo cikin mu? 

Ya tarbeka da hannu biyu ya dora ka a hanyar arxiki ya nuna ka ga abokansa ji-jigan masu kudi da ‘yan siyasarsa. Ka shigo cikinmu harka xama mutum shi ne yau xaka nuna masa kai dan adam ne butulu ko. Alhaji sadam ya karba yace alhaji bala tsaya bar ni dashi alhaji isa kar fa ka manta satifiket din sakandire kawai kake dashi shima duk xiro muka yi murda-murda aka samo maka takardun bogi na karya, aka tsayar da kai a dan takarar neman mataimaki, idan aka ce yau kaine dan takarar shugaban kasa kana nufin yan Nigeria xasu xabe ka? Kar ka manta duk jama’ar dake tururuwar sonka ba don kai bane saboda alhaji ahmad ne, yau idan aka ce ka ware gefe da jama’ar da suke sonka alhaji ahmad ya ware da jama’arsa ko mutane dubu ba xasu xabe ka ba, kai ko a garinku shagamu ba xaka ci ba balle Nigeria kuma ‘yan Nigeria suna da hankali ba dabbobi bane irinka, suna da ilimi ba jahilai bane irinka da xasu xabeka.


 Alhaji isa ya tuntsure da dariya , ya sake tuntsurewa da dariya ya buga kafa yace na ji duk abinda ku ka ce amma ina mai shaida muku da da yanxu ba daya bane, yanxu na yi kudi har na fiku don haka xancen rashin ilimi ko jama’a sai dai idan babu kudin ne. ba naxo ne don in yi muhawara da ku ba yanxu, na xo ne in bawa alhaji ahamad xabi. Dana mubarak bai yiwa ‘yarka ciki ba, bai ma taba saninta ‘ya mace ba, saboda muguwar hudubar da kake kunsa mata karta yarda dashi, ashe kai ka san me yake faruwa a tsakaninku. Don haka alhaji ahmad sirri ne tsakaninmu kafin duniya ta ji dan takarar shugaban kasa ya ki yayi aure yana korar matansa akan ‘yarsa ashe nemanta yake har ya yi mata ciki wata uku ko ka sauka sadan-sadan ka bani kujerar ka ka dawo kan tawa ko kuma…………..


 Inna liLlahi wa’inna ilaihi raji’un alhaji ahmad yake karantowa, axixa ta fashe da kuka ta kifa kai kasa tana rusa kuka. Alhji sadam da alhaji bala suka kece da salati. Alhaji ahmad yace babu abinda xance maka alhaji isa sai tsakanina da kai Allah Ya isa, kuma in dai takara ce na ma hakura gaba daya da siyasar ka je ka tsaya a kujerar shugaban kasa, ka nemo mataimakinka, Allah ne xai yi mana hisabi da kai. Dadi marar misaltuwa ya rufe alhaji isa ya girgixa kai yana murmushin dadi yace ka huta da ka yanke hukunci cikin sauki ka rufawa kanka asiri. Alhaji bala  ya xabura yace alhaji ahmad me nake ji kana cewa? Ka bar masa kujerar ka? Ba xai yiwu ba alhaji ahmad. Ciki da gaskiya wuka bata hudawa, sharrin da kake nema ga bawan Allahn nan sai ya koma kanka alhaji isa.


 Alhaji sadam yace karya kake kujera ce ba xa a bar maka ba ka je ka ce kome xa ka ce. Axixa ta goge hawayen dake bulbulowa daga idanuwanta ta ce daddy kar ka hakura ka bar masa, in dai wannan mutumin ne sai yahau ya xama shugaban kasar ma sannan xai wulakantamu ya toxarta mu. Don haka duk sharrin da yake so yayi mana Allah Ya fiku alhaji isa. Alhaji isa yayi dariya ya dafa kafadar dansa yace ka ji wannan yarinyar abinda take cewa ko? Ba ku sanni ba amma yanxu xaku sanni. Alhaji ahmad me ‘ya axixa tana dauke da ‘da ko jika a cikinta xa a lakabawa ‘dana, to Allah Ya sa mun gane. Mubarak miko min mujallun nan guda biyu a fara basu su karanta kafin jama’a su fara karantawa. 


 Mubarak ya jawo wata akwati karama ya bude, kowa ya yi tsuru-tsuru xuciya cike da tsananin bakin ciki da fargabar ganin me xa a dauko, ya xaro mujalla mai tsananin kala tar ta dauku kamar ka yi kiran sunan wanda yake jiki ya amsa, ya jefawa alhaji ahmad daya ya jefa wa alhaji sadam daya, alhaji bala yayi sauri ya karkato hannun alhaji sadam suna kallo tare, axixa ma ta matsa kusa da babanta tana dubawa sai taga hotonta ne ta rungume babanta a lokacin da mubarak yayi mata wulakanci a asibiti babanta ya xo ya iske ta ita da atika a kofar daki, to wannan rungumar da ta je ta yi masa itace aka dau hoton shi ne a bangon. Suka yi sauri suka karanta abinda aka rubuta a saman sai suka ga kamar haka.


 Alhaji ahmad abdul fati, sannan dan takarar shugaban kasar nan na karkashin jam’iyyar J.U.T ya yiwa ‘yarsa guda daya tilo da yake ji da ita tamkar ransa ciki. Saboda tsananin son da yake yi mata ne ya wuce son ‘da da uba ya koma soyayyar miji da mata oho! Ko kuma tsananin kyanta ne ya rude shi yake kishi da duk saurayin da yake son ya aureta, ya hana kowa aurenta ashe shi yake so. Masu karatu ku biyo mu a sannu xa ku ji amsoshin tambayoyin na a cikin mujllar nan, xai xo kotu ya bamu amsar mu kuma………..


 Alhaji sadam ya yi cilli da mujallar da ke hannunsa gami da mikewa tsaye da sauri ya shrbe gumin da yake ketowa a goshinsa yana cewa subhan Allahi wannan jahilci yayi yawa alhaji isa ka kuwa san abinda kake ka cika jahili bakauye, me nene na borin kunyar? Dan danka ya yiwa budurwa ciki abin mamaki ne? barewa ta yi gudu danta yayi rarrafe? Tasha nawa ka yiwa ‘ya’yan jama’a ciki kuma kowa ya sani. Alhaji ahmad ya dago da kyar ya dubi alhaji isa saboda nauyin da idanunsa suka yi masa don karanta abinda ko a mafarki bai taba xato ba, yace alhaji isa hakika xan fi ka son ka shigar da karar na saboda sharrin da ka yi min ba xan yafe maka ba, ba kuma xan bar maganar nan ba ko ka fasa shigar da kara to nixan shigar da kara.


 Alhaji bala yace duk ku tsaya xancen bana kotu bane alhaji isa ka yi kuskure don axixa da mubarak suna son junansu, su kuma akan kansu sun san mafarin cikin nan kuma suna son abinda xasu Haifa, kowa ya san axixa bata da saurayi sai mubarak. Alhaji isa ya mike tsaye yana murmushin dadi yace kun gani? Ina da irin wannan mujallu fiye da kwafi dubu dari biyar ana kuma kan bugawa ta hausa da turanci, yarbanci da ibo kai harda fulatanci da barbanci duk nasa a buga da kowanne yare don kowace kabila ta gane, kyauta xan raba ga ‘yan Nigeria. Bayan labari ya iske kowa xan shigar da kara babbar kotun dake nan Abuja, sai ka xo ka yi mana bayani yadda aka yi ka yiwa ‘yar ka ciki aka so a likawa ‘dana, a matsayinka na mai shirin hayewa kujerar shugaban kasa a shugabancin al’umma. A Kur’ani da Bible da duk wani littafan addinai daban-daban babu inda aka halasta uba ya yiwa ‘yarsa ciki. Don haka na baka KWANA ASHIRIN DA HUDU ka kirani ka gaya min hukuncin da ka yankewa kanka kafin in fitar da mujallun nan, ina ka yafe  ka bani kujerarka aje a kona mujallun babu wanda xai ji idan kuwa ka ki hakika xaka sha mamaki dan ko sakan ashirin da hudu ba xan kara maka ba da xarar kwanan ashirin da hudu ya cika ke nemi mujallun nan a fadin kasar nan, ka kuma saurari kira a kotu.


 Gaban axixa yayi mummunan faduwa da jin xancen kotu ta san tabbas tunda ba mubarak bane yayi mata ciki to wa nene? Don sai wanda yayi mata ciki ya xo ya amsa, idan kuwa babu hakika mutane xasu ce da gaske dadynta ne yayi mata. Inna liLlahi wa’inna ilaihi raji’un take karantowa a xuciyarta tace a ranta muddin daddy ya ji ashruf ne ya yi mun ciki xai kasance mai tsananin bacin rai kuma xai tashi mutum a tafi Croatia a nemo ashruf, amma ba xa a sami ashruf ba don Ubangidansa abokin aikinsa mr Johnson mun yi waya shekaranjiya na tambaye shi ashruf yace ai rabuwarmu da ashruf shima rabuwarsu kenan, ashruf yace ya bar aiki dasu ya koma Jamaica  ya ginawa iyayensa gida ya ci gaba da juya jarinsa. Na roki mr Johnson ko xai aika Jamaica a nemo min ashrfu yace gaskiya garin daya san ashruf da, ya tashi ba a garin ya sayi gida ba, kuma ashruf bashi da waya ko bayan tafiyarsa wayar da yayi masa daga  gidan waya ya yo don haka takamaiman ba a san inda ashruf yake ba.


 Hankalin axixa ya sake tashi ta sake tsundumawa wani halin ha’ula’i. hawaye ya yi ta xubowa daga idanuwanta ta bi alhaji isa da dansa mubarak da kallo suka doshi kofar fita fuskarsu cike da annuri, har sun kai bakin kofa mubarak ya juyo ya kalli axixa yace nan da KWANA ASHIRIN DA HUDU ya tintsure da dariya suka fice.

.

.

 A nan muka kawo krshen KWANA ASHIRIN DA HUDU KASHI NA BIYU.

.

.

TAMBAYA, tsakanin ASHRUF da AXIXA wa ye ya soma padawa so da kaunar wanin sa? 

Sannan kuma wa ya pi so da kaunar wanin sa?


TAMBAYA ta BIYU: idan Kaine Alh Ahmad ya xakayi?

Idan kece Aziza ya xakiyi?


Muna son jin amsoshin kowa a gidan nan kapin mu daura littapi na 3.

.

Comment da sharhi su suke kara karfin guiwa

Ina godiya da comment dinku

[9/3, 7:34 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/5, 3:22 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU

LITTAFI NA UKU. 

*12*

.

.

 Bayan fitarsu alhaji isa sama da minti goma babu wanda yayi Magana a falon, sai muryar axixa ke sharbar kuka. Alhaji  bala ya nisa yace axixa kiyi hakuri ki daina kuka, kuka ba magani bane ki yi addu’a Allah Ya saukeki lafiya. Ki kuma dauki wannan abinda ya sameki jarrabawa ce ta Ubangiji, ya kuma xama darasi ne a rayuwarki. Alhaji sadam yace kwarai kuwa kar ki saka damuwa da bacin rai ganin mubarak ya bujire shi da mahaifinsa sun ce fur cikin ma ba nasu bane da yake hauka suke, kansu da kansu xasu kai kotu. Nanfa gaban axixa ya sake yankewa ya fadi tace a ranta lallai akwai ranar tonar asiri, na shiga uku na lalace na jawa ubana abun kunya. Tabbas su mubarak sun fi mu gaskiya, ni mubarak bai taba sani na ‘ya mace ba. ta yaya kuwa xance shi yayi min ciki? Karo na farko da taji wata muguwar tsanar fyaden da ashruf yayi mata. A da bai dameta ba, ta yafe masa cuta daya dai yayi mata shi ne ya cire mata mutuncinta na budurcinta. Amma yau da ranar tonar asiri ta xo wa xata tunkara ta fada masa gaskiyar al’amari nan? Ko jikinsu dukka kunne ne ba xa su taba yadda da cewa fyade ashruf din yayi mata ba. wani babban tashin hankali waye uban dan da xata Haifa? Ya shiga uku da gori da cin mutunci har karshen rayuwarsa ‘ya’yansa da jikokinsa. Nan fa ta nemi hawaye ta rasa sai ta sulale ta kwanta, nan da nan mahaifinta da abokansa suka mike a rude suka dagota, ina axixa ta fita hayyacinta sai asibiti. Su atika a guje suka fito da suka ji salatin da ake ta rafkawa.


 Dr rislan ya kasance a ko da yaushe yana kusa da axixa yana bata hakuri cewar ta kwantar da hankalinta. Saboda xuciyarta ta fara tabuwa tsananin tunani da damuwar da ta shiga. Yana ga yaki tana ga kuru ita a koda yaushe ta ganshi sai ta rushe da kuka tana rokarsa Allah Annabi yayi mata allurer da xata bar duniya ko nawa ne xata biya shi. Abin yakan daurewa dr rislan kai yana ganin yin ciki ba tare da an daura aure ba ai ba wani abin tashin hankali bane, yama xama ruwan dare a ko ina. Birane da kauyuka, gara ita tasan wanda yayi mata ma, wasu da yawa karuwai ne basu san takamaiman wanda yayi musu cikin ba, haka suke xuwa a cire musu ko kuma su haife. Amma saiga axixa da dunbin iliminta da gogewarta tana kokarin ta halaka kanta saboda saurayin da xata aura yayi mata ciki kafin bikinsu.


 Yau kwanan axixa hudu a asibiti hajiya lantana ce yayar mahaifinta ke xaune a wajenta. Axixa ta daddafa ta tashi xaune a kan gadonta ta dan jingina da filo, hajiya lantana wacce ke kokarin fitowa daga bandaki dake cikin dakin dauke da buta a hannunta. Ta iske axixa tana kokarin gyara xama ga robar Karin ruwa da karfen da aka sakale yana kokarin ya fadi. Ta ajiye butar  dake hannunta da sauri ta nufo gadon da axixa ke kwance tana fadin axixa bakya kira na inxo in dago ki? Kika tashi da kanki ga wannan katan karfe yana kokarin ya fado miki. Ta tallafo ta gami da gyara mata filon da ta jingina a jiki ta kuma gyara mata hannun da ake yi mata Karin ruwa taxo gefen gadon ta xauna daga wajen kafafuwanta. Ta ci gaba da kallon axixa tana kwalla, can da aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da kowa yace komai ba sai hawayen da suke xubowa daga idanunwansu. Hajiya lantana ta goge  idonta da gefen mayafinta tace Allah sarki, Allah mai yadda Ya so da bawan Sa . Dube ki axixa kalli yadda kika xama babu mahalukin daya sanki da xai gane ki, banda mu da kika xama haka a gaban ido ya kumbure miki kamar yar japan. Kin cukurkude kin yamutse kamar ba ke ba oh Allah ka yaye mana masifa. Axixa ta rushe da kuka mai wuyar fita na tsananin takaici. 


 Hajiya  lantana ta matso kusa da ita tasa gefen gyalenta tana goge mata hawayen tace kukan da kike yi ne yasa miki kumburin fuskar amma kinki ki daina. Addu’a xamu yi, ki kuma toshe kunnuwanki da duk abinda mutane xasu ce, ba a kanki farau ba kuma ba akanki xa’a kare ba. banda ma iskanci da rashin munci irin na alhaji isah me abin juyo Magana ta koma tashin hankali? Bayan sun kawo kudin aure da komai da komai na aure sadaki ne kawai ba a bayar ba, haka taxo ta kasance ai sai ayi shiru a gangada ayi bikin kije gidanki ki haihi baki alaikum, wa yasan a waje akayi cikin? Nanfa axixa ta sake rikicewa an tabo mata maganar da take firgitata. Tasa hannu a kirjinta ta dafe saboda tsananin bugun da xuciyarta ke yi mata, hajiya lantana hankalinta ya tashi saboda rikicewa ta mike da sauri ta rike axixa tace lafiya? Xuciyar ceke wannan bugun kamar ganga? Sai hawaye ke fita daga idanuwanta tana karkarwa, inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un hajiya lantana ke karantowa ta nufi kofar fita da sauri xata je ta kira likita. A bakin kofa suka hadu da dr rislan yana ganin hajiya lantana yaji gabansa ya fadi yasan jikin ne ya tashi cikin sauri yace hajiya lafiya? Ta ce alhamdulillahi shigo likita axixa ba lafiya.


 Da sauri likta ya karaso wajen axixa ya sameta a wannan hali nan ya cire filon da take jingine ya kwantar da ita akan gado, cikin ikon Allah da dubarunsu na likitoci minti goma sha biyar yayi yawa xuciyar axixa ta dawo dai dai da yadda ta kowa take bugawa. Har bacci ya fara daukarta lum, sannan dr risalan ya matsa daga kanta ya koma kan daya daga cikin kujeru biyu da suke dakin ya xauna, yayi shiru yana tunani. Hajiya lantana kuwa tana xurga xurga tsakanin wannan kusurwa xuwa wannan kusurwa ta dakin tana koke koke da ‘yan surutai Allah Kai Ka bamu axixa Kai xaKa kwace, ita kenan Ka ba wa dan uwana ahmadu Allah Ka raya masa ita Allah Ka dubeta Ka fito da gaskiya akan mugayen mutanen nan da suke kokarin su sheganta mata abinda ke cikinta.


 Mubarak ashe haka kake? Mun dauka kai na gari ne? ashe badon Allah kake son yarinyar nan ba? ka lallaba ta kayi mata ciki, sannan ka guje ta? Kamar a mafarki axixa take jiyo surutan hajiya lantana firgigit ta mike xaune tana mikewa ta tashi da axababben ciwon kai da mummunan bugun xuciya dr rislan aguje ya taso ya riketa ya mayar da ita ya kwantar akan gado. Hajiya lantana wacce tuni tadau kuka kai kace axixar ta cika, cikin sheshshekar kuka axixa take cewa dr rislan ka taimake ni dr ka yi min allurer nan yanxu na bar duniya dan xamana a duniya bakin ciki ne. baka ji abinda mubarak suke cewa ba? likita nata kokarin lallashinta yana cewa xanyi miki allurer kwanta tukuna. A daidai lokacin ruwan da ake kara mata yakare, dr risalan ya dauko wani sabo akan ‘yar karamar lokar dake gefen gadon ya xare na da ya saka mata wannan, ya dauko  wata allurer ya matsa a cikin ruwan allurer da xata sata tayi bacci mai nauyi.kafin yagama ‘yan soke soken sa har bacci ya fara daukar ta surutan dake yi tana Allah Ka dauki raina yau yana yin kasa kasa har tayi shiru luf bacci ya dauketa.


 Dr rislan ya kalli lantana yace hajiya kiyi shiru ciwon ya lafa bakya ganin ta yi bacci kuyi dai addu’a Allah Ya sawake mata, a naxarin da nayi da kuma abinda idona ya gane min ciwon nan na axixa baya bukatar dan xaman jinya saboda akwai kalma guda daya da in an fadeta take tayar mata da ciwon, koda yake xanyiwa Alhaji ahmad mahaifinta waya ko kuma idan ya xo xamu yi maganar, ina ganin xamu canja mata sashe inda kwatakwata ma babu mai xuwa wajenta balle ya fadi Kalmar da xata ringa bata mata rai sai mu ma’aikata kawai xamu ringa kula da ita. Nan fa hajiya lantana ta hau dr rislan da fada tana cewa yaushe aka fara wannan sabon tsari abar marar lafiya shi kadai babu ‘yan’uwa? Tun tashina idan an kwantar da mutum da wani daga cikin en uwasa a wajensa, sai dai idan da gaske ne da aka ce likitocin yanxu su suke karasa maras lafiya su cire masa kayan cikin. Dr rislan ya yi murmushi ya nufi kan kujerar da yake xaune daya kwashi ‘yan kayayyakinsa na aune aune ya nufi kofar fita. Hajiya lantana bata yi shiru ba, ta ci gaba da cewa yaro ina maka kallon mai gaskiya da imani karfa ka sake ka bawa ahmadu wannan shawara ta dauke dan xaman jinya don ni ko da ya yarda babu inda xani ina tare da axixa.


 Dr rislan ya sake kecewa da dariya yace hajjaju kenan, mu ma likitoci burin mu muga marar lafiya ya sami sauki. Kuma koda Allah Ya sa cutar ta mutuwa ce ya rasu a hannunmu wallahi hajiya wani lokacin munfi ‘yan uwansa jin tashin hankali, balle axixa ki tambayeta ni ne likitansu duk kasar nan shekara da shekaru. Ya sa kai ya fice yana murmushi. Hajiya lantana a tsaye take ta sankare tana sake maimaita maganar dr rislan a ranta babu dan xaman jinya, babu dan xaman jinya kamar yaya? Kashe ‘yar xasu yi. Bari ahmadun ya xo na ji abinda xai ce. Amma babu yada xa a yi marar lafiya a barshi shi kadai ace kuma xasu barshi da rai basu karasa shi ba sun cire wani waje nasa ba. haka kuwa akayi baban axixa na xuwa ofishin dr rislan ya wuce  kafin ya shiga dakin da axixa ke kwance. Dr rislan yace alhaji na lura akwai wata muguwar muguwar Magana da axixa take tunawa ko kuma idan wani ya furta take jin tashin hankali har budun xuciyarta yake canjawa ya bambanta dana kowa. Haka ne? alhaji ahmad yayi ajiyar xuciya yace hakika likita nima na lura da hakan.


 Dr rislan yace to ni dai abinda nake gani shi ne mai xai hana mu dauke axixa daga nan sashen mu kaita bangaren da ba a yarda ‘yan dubiya su shiga ba kuma babu dan xaman jinya. Domin ‘yan dubiya da ‘yan xaman jinya suna kara creating problems a wannan rashin lafiyar tata. Muna da ma’aikata masu kula da ita. Kai ko motsi tayi cikin dare akwai ma’aikaciya da take xaune akan ta xata yi kararrawa likita ya xo. Haka xa a kula da tsaftar jikinta da ta makwancinta. Cinta da shan ta da kuma uwa uba lafiyarta, ko yaya ka gani ranka ya dade? 

Alhaji ahmad yace lallai haka xaifi dacewa da axixa ya xamo bata ganin kowa balle taji mugun labari , don haka dr na baka wuka da nama, ga axixa duk wani taimako irin naku na likitoci ayi mata rislan I trust you. Bana fargaba a aikinka no matter wat it will cost xan biya ni dai fatana axixaa ta sami lafiya hankalinta ya kwanta, ta daina damuwa. Kuma baka ganin idan axixa taga bata ganin kowa a cikin ‘yan uwanta da kawayenta ba xa ta shiga wani damuwa ba tayi xaton kowa ya gujeta ne akan wannan larurar da ta same ta? 


 Dr rislan yace hakika xata damu idan aka ce kwata kwata babu wanda xaixo wajenta a cikin ‘yan uwanta, wasu kadan xasu iya xuwa kamar kai xaka iya xuwa a koda yaushe ka ke son ganinta, sannan da wasu daka kula tana sansu a ranta masu hankalin da xasu kwantar mata da hankali ba wadanda xasu kara hargitsa taba, yanxu xanso ka bani sunan irin mutanen da kake ganin axixa xata so ta gansu don hankalinta ya kwanta. Xan rubuta sunansu na bawa security dake gadin bangaren don idan wasu daban sun xo ta hana su shiga. Baya ga wadanda xaka bamu sunansu babu wanda xa a bari ya ga axixa. Alhaji ahmad yace fara rubuta sunana da abokaina alhaji sadam da alhaji bala, dr risaln ya yi ‘yar dariya ya dukar da kai yace ranka ya dade banda ku aiku ba sai an rubuta sunan ku ba koda yaushe kuka xo xaku iya wucewa. Alhaji ahmad  yace to rubuta sunan kawayenta biyu atika sadam da munnira bala, sai kuma wata karamar yarinya jikar hajiya lantana ce yaya ta axixa na sonta sosai sunanta Nilfa itama  xa a ringa kawo mata ita duk bayan kwana biyu.


 Daga karshe kuma ka rubuta nafi’u sangali wani dan nijar ne a gidanmu yana bawa fulawa ruwa shima mutuminta ne yana bata dariya sosai, ina ga a duk sanda na bushi iska xansa a kawoshi ya dubata su danyi wasa da dariyarsu. Dr rislan ya rubuta sunayen da alhaji ahmad yake xano masa. Bayan y agama rubutawa yace hakika axixa xata sami saukin tashin hankalin da yake damunta, kuma baka ganin akwai wasu fina finai da kake ganin tafi so ta ringa gani wanda yake sata nishadi da dariya, don xai yuwu idan aka kunna mata satilight xata iya ganin wani film da xai yi kama da halin da take ciki hankalinta ya tashi koma tayi xaton ita ake kwaikwayo kuma mai larura irin wannan abu kadan xa a yi sai ta tsargu ta dauka da ita ake . don haka xamu  so ta ringa kallon fina finan ban dariya wanda bai kunshi wani abu ba da xai yi kama da halin da take ciki. Alhaji ahmad ya yi murmushi yace dr banda abinka ina marar lafiya ina kallon kaset? Dr rislan yace alhaji xaka yi mamaki a kwana biyu kaga axixa daram a xaune tana hira da kowa radai, domin har yanxu babu takamaiman wajen da yake yi mata ciwo a jikinta tsabar damuwa ce da tunani ga tashin hankali shi ke damun axixa, da xarar duk wadannan sun kau a ranta to axixa lafiyarta kalau sai dai xanso ko ta warke mu cigaba da riketa a nan asibitin har sai ta huta sosai.


 Alhaji ahmad yace babu damuwa xansa atika ta debo mata irin kasissinan data fi so a cikin kaset dinta, amma ina ganin duk a cikin films tafi son na Ibro (Allah Ya jikansa da rahama, amen.) don ko a hoto ta ganshi sai ta sha dariya, balle a film yana bata dariya matuka kuma tana son film dinsa don bata ganin film din hausa sai idan da ibro, ina ganin  ma idan ta warware xan aiko da mota aje kano a dauko mata ibro ta ganshi ayi suprising dinta dashi. Dr rislan yace kwarai kuwa xata ji dadi, amma fa alhaji nasan xaka sha fama da hajiyar da take xaman jinyar axixa don naji tana cewa babu inda xata je ta bar axixa ita kadai wai likitoci suna kashe mara lafiya idan ba dan xaman jinya. Alhaji ahmad ya kyalkyale da dariya yace bari naje na sameta idan na yi mata bayani xata gane sai dai kuka ne yau xata sha rafsawa. Alhaji ahmad ya mike tsaye yana cewa  thank you so much doctor rislan ya mike da sauri don girmamawa yace nima nagode alhaji, Allah Ya bata lafiya yayi sauri ya budewa alhaji ahmad kofa ya fita nan da nan yaransa (bodyguard) da suke tsattsaye a bakin kofar ofishin suna jiransa yana fitowa suka xagaye shi daya  agabansa. Dukkansu suna sanye da bakar riga suit da bakin wando, bakin takalmi da bakin gilashi. Suka nifi dakin da axixa take kwance.


 Alhaji ahmad ne kadai ya shiga dukka a bakin kofa suka tsaya daya ne dai ya rakashi har ciki da yaga ya xauna a gefen gado kusa da ‘yar sa sun fara Magana da ‘yar sa sai ya fito ya jawo musu kofa ya rufe, cika aiki. Bayan ya gaida hajiya lantana ya tambayeta yaya mai jiki ta kwana da jiki hajiya lantana tace jiki dai gashi nan ya lafa ya tashi abin dai sai addu’a. ta rushe da kuka tace wadannan mutane sun cuce mu yanxu ahmadu mubarak din nan da mahaifinsa kasan haka suke ka yadda da xaka dauki ‘yar taka kwaya daya jal ka basu mararsa mutunci? Axixa wacce kamar a mafarki take jiyo sunan mubarak don shaker bacci take haikan. Amma jin sunan abin da ta tsana ya farkar da ita sai hawaye ke kwaranyo mata. Ta kalli mahaifinta tace daddy me su mubarak suka sake yi maka kuma? Alhaji ahmad ya juyo sosai ya fuskance ta yace axixa babu abinda su mubarak suka yi min sunce ma a gaisheki.


 Ta rushe da kuka tace daddy ya xa a yi suce a gaishe ni, bayan har sun kai kara kotu, na gansu fa a kotun. Alhaji ahmad ya fuskanci a mafarki ta gansu saboda tsabar ta sa abin a ranta. Da kyar ya bata baki da dabaru sannan ta daina xubar da hawayen dake xubowa daga idanuwanta, ya lura da cewa hajiya lantana tana daya daga cikin masu furta maganar da take kara tayarwa axixa hankali jikinta ya kara hargitsewa. Ba tare da alhaji ahmad yace da hajiya lantana komai ba akan shawarar da suka yanke da dr rislan yace ta dauko kayanta su xo su tafi. Ta tsaya xata tambaya me nene dalilin da xai ceta tafi tabar axixa ita kadai yace xasu yi maganar a gida. Da kansa ya kinkimi Jakarta ya mikawa daya daga cikin yaransa ya rike yace da ita hjiya yafa gyalenki ki xo mu tafi da sauri wasu manyan likitoci ne turawa daga kasar waje xasu shigo su dubata basu so suga kowa a wajenta muje gida xan kara miki bayani yace da axixa suna dawowa yanxun nan, suka dunguma suka fuce suka nufi wajen da suka ajiye motocin da suka xo dasu, suka shiga suka tafi.


 Axixa a kwance take tana kallonsu har suka fita suka jawo mata kofa suka rufe, ta mayar da idonta ga kallon silin din dakin tana mai tsananin tunani akan abinda ya addabi rayuwarta, tasa hannu ta shafa cikinta taji tauri tauri kuma har ya fara dagowa yana girma  ba kamar daba ita da cikinta yake a shamule kamar xai hade da doron bayanta, amma yanxu ya fara dan dagowa. Taji takaici marar misaltuwa a ranta, tunanin yaya rayuwarta xata kasance nan gaba ashruf, ashruf ta fada a ranta yayin da hawaye yayi mata kawanya tun daga idonta har bayan kunnenta. Tace yaushe xan ganka ashruf? Ina xan ganka? Dama na ganka ashruf, ta rushe da kuka mai tsanani yayin da xuciyarta ta sake rikicewa da wannan mugun bugun daya bambanta  dana sauran mutane. A daidai lokacin dr rislan da wasu ma’aikatan jinya su biyu (nurses) suka sako kai cikin dakin. Axixa suka iske ita kadai cikin wannan halin yayin da suka karaso aguje don taimaka ma xuciyarta ta sauko daga bugun da take .


 Da kyar da kyar xuciyar axixa ta lafa, cikin sauri aka dorata a gadon turawa aka turata sashen da ba a yarda kowa ya shiga dubiya ba daga marasa lafiya sai likitoci nurses da wasu ‘yan tsirarai a cikin yan uwa. Nan ne kuma bangaren wadanda jikinsu yayi tsanani wasu ma basa cikin hayyacinsu (intensice care unia ) don haka basa son a damesu, tsit xaka ji bangaren kamar babu bil adama sai karar takalman likitoci da sauran ma’aikatan jinya suna takai kawo akan mararsa lafiya. Awa ashirin da hudu likitoci suke a tsaye kan mara sa lafiya….

.

Comment da sharhi su suke kara karfin guiwar me posting comment kamar dubu Ashirin da hudu

[9/5, 3:22 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/5, 3:23 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3

*13*

.

.

  Wannan ya canji wannan wancan ta canji wancan, saboda suna bukatar kulawa sosai, don haka  kudin da suke biya yafi na sauran bangarorin. Musamman bangaren da aka kai axixa, bangare na masu kudi akan masu kudi, daban yake kawatacce a cikin likitocinma kwararrun likitoci ne suke kula da ‘yan wadannan dakuna. Baya gad r rislan wanda yake daga cikin manya manyan likitocin da ake ji dasu a wannan asibiti, wanda shi kadai ne bakar fata, duk sauran da suke duba axixa turawa ne suna kula da ita fiye da kima.


 A ranar da daddare alhaji ahmad da alhaji bala suka ga sabon dakin da aka kawo axixa, suna xaune akan kujeru biyu da ked akin yayin da axixa ta ke kwance akan gado tayi lamo ana yi mata Karin ruwa a hannunta na hagu. Idanunta sunyi luhu-luhu don kumburin kuka da bacci. Ta rame kurket sai wani dashewa da ta yi, ta yi jajur sai kace marar jin a jiki. wayarta ce take kara karkashin fulonta, gabanta ya yanke ya fadi ras domin karar ringing din data sakawa mubarak ce  tunda daban ta sa nasan. Tasa hannunta na dama a sanyaye tana laluben wayar, ma’aikaciyar data ke kula da ita ta taso da sauri ta jawo mata wayar a karkashin fulo ta mika mata ta karba ta dannan a sanyaye gami da yin shiru ba tare da t ace komi ba. tana sauraron abinda take ji a cikin wayar.


 Hallo, hallo yak eta fadi, ta yamutsa fuska t ace ina jinka yaya! Ya ce yauwa axixa ce ko, to daman ba wani abu bane illa naji ance kin sake sumewa an kaiki asibiti shi ne xan baki shawara da ki dinga suma a banxa ba gara ki roki daddy bay a hakura ya janye takarar nan ya barwa daddy na, baki ganin yin haka kema samun saukin ki ne! yaya kika gani ina ganin tunda kece kadai a wajen mahaifinki mai tsananin son abinda kike so ki shawarceshi. Mana ya bar bana mu kuma mu kame bakinmu muyi shiru ba sai kowa yagi ba .daga karshe ina tare da sumayya emma sabuwar masoyiyata yar  gidan gwamnan legos wacce da xarar an gama hada hadar xabe mun xama prexident xa a yi bikinmu. Su dukka wajen taji sun sheke da dariya muryar mata da maxa ga disco na tashi a wajen da suke da alama dai a wani club din ‘yan iska suke. 


 Tashin hankali ya sake rufawa xuciyarta yayin da hawaye ya dinga xubowa daga idanuwanta, kirjinta yah au dukan fat-fat bakinta yana karkarwa tana son tayi Magana ta kasa. Cafdijam yau mbarak ne yake yabawa axixa irin wadannan bakaken maganganun haka! Hausawa sunce duniya rawar ‘yan mata na gaba ya koma baya, axixa da don tsabar iya yaba Magana da ciwa mutum mutunci sai nace itae misss  world, amma yau ga mubarak din da ko musu baya iya yi mata yau yana gaya mata ba dadi. Tana kokarin mayar masa da martini ta nemi Magana ta rasa a bakinta  sai karkarwa dab akin nata yakeyi. Hakika axixa babu lafiya bata data cewa sai yadda akayi da ita, makami daya ne ya rage mata wanda xata iya amfani das hi wajen kare kanta shi ne hawaye. Idan aka kuntata mata sai ta rushed a kuka, shi ne kadai sinadarin da yake sanyaya mata da xuciyarta. Mahaifinta da abokin mahaifinta alhaji bala suka kula da halin da axixa take ciki ga wayar kuma ta rike gam a kunnen ta kamar dole akace  sai ta saurari abinda mubarak yake fadi. Alhaji ahmad y ace axixa lafiya! Waye kuke waya dashi kike kuka hankalinki kuma a tashe! Alhaji bala ya mike  yaje ya fusgi wayar a hannunta ya saka a kunnensa ba tare day a karanta ko sunan waye a jiki ba, yayi kasake yana sauraron abinda ake fada a cikin wayar, kalma daya yaji ya fuskanci ko wanene yake  Magana, mubarak isah ne yake cewa axixa gashi yau saura  kwana ashirin cif-cif a cikin kwanankin da muka debar muku kafin mu fitar da mujallun na. 


 Kinga ashe kuwa da sauran lokacin da xaki shawarci mahaifinki, ya sake kyalkyalewa da dariya y ace shawara na ke baki fa bawai rokarki nake yi ba… alhaji  bala ya katse maganar da yake yi a fusace y ace kai! Kai!! Mubarak dakata kada ka sake ka sake kirawo axixa a waya baka da hujjar ka xabar mata abinda xata yi kana jina ko! Mubarak y ace shin da wa nake Magana na ji dai ba muryar alhaji ahmad bace, alhaji bala y ace koma dai dawa kake Magana ba dole ne ka sani ba, ka rabu da axixa ta huta bata jin dadi, duk wasu kwanankin da kuka dauka duk na banxa ne babu wanda xaku iya tsoratarwa duk abunda xaku yi kuje kuyi, in Allah Ya yarda kanku xai koma. Mubarak ya nisa y ace ok yanxu na fuskanci da wanda nake Magana, abban munnira ina ganin kune fasagurbin kwai da kuke dumama wannan Magana kuke tursasawa, kuke xuga alhaji ahmad kada ya sauka ya barwa daddyna.

 

 Hakika shi ya fiku sanin gaskiyar al’amari kuna cutarsa ne xaku kaishi ku baro shi kuma.  alhaji bala ya daka tsawa y ace kai mubarak ka iya bakinka nib a da kai xanyi ba sai dai nayi da ubanka marar kunya, banxa shashasha, dabba… alhaji ahmad ya taso ya fusge wayar daga kunnen alhaji bala ya yi sauri ya kasha wayar ma kwata kwata ba tare day a bari mubarak ya mayar da amsa ba, alhaji bala ya dawo kan kujerar da yake xaune ya xauna yana huci ga gumi don tsabar fushin day a dira a xuciyar sa, ji yake inama mubarak a kusa das hi yake day a masa habo don   naushi xai skar masa a wannanbudadden hancin nasa irin na ubansa sai ya fashe . alhaji ahmad y ace haba bala ina kai ina tsayawa  da wannan yaron kana fadi in fada das hi, ai ba sa’anka bane, to ko ubansa ma yanxu ka tsaya kuna fadi in fada kasancewar kasanshi bashi da hankali mahaukata ne fa, alhaji ahmad ya karaso gadon da axixa ke kwance tana hawaye har yanxu, ya dafa kanta y ace axixa ki daina kuka, kukan me kike akan mahaukacin yaron nan!


  Ban gaya miki ba idan kinji irin wadannan abubuwan ki yi ta addu’a Allah Xai yaye miki, kiyi shiru. Ya warwaro tissue yana goge mata hawaye. Alhaji bala yace ai wannan anyi ba’ayi ba ne, an canja mata daki don kada mutane su dameta ashe kuma a waya  xasu ringa damunta. Alhaji ahmad y ace ai nima tunanina da nake yi ken an ina ganin da wayar xan tafi gida don ba xasu kyaleta ta huta ba. ya kalli nurse din da take kula da ita y ace baiwar Allah mu xamu tafi idan ruwan nan da aka saka ya kare ki cire mata  ki kaita bandaki tayo alwala taxo tayi sallah gad an karamin kur’aninta nan akn loka ki bata ta karanta ko ta daina jin yawan faduwar gaba da bacin ran nan. Axixa ki  dage da addu’a Allah Xai fitar dake daga duk wani makircin makiya,  kinji ko! Axixa ta gyada kai da kayr alamar taji, tausayinta ya lullube shi yaji kwalla ta cika masa idanunwa, yaji tsana kan tsana fiye da tad a yake yiwa mubarak da babansa alhaji isah. Haka suka yi sallama da axixa suka tafi suka barta a nan a kwance cikin halin damuwa musamman ma wayarta da babanta ya tafi mata da iat. Tana shirin idan ta sake samun saukin jikinta ta sami karfin yin Magana tana so tayi wa mr Johnson waya ta sake ji ko ya jiyo inda ashruf yake ya nemo mata shi kafin nan kan kwana ashirin da hudu da aka dibar musu ta cika, to gashi yanxu daddynta ya tafi da wayar tata. Hawaye ya sake kece mata hard a sheshekar kuka, Halima ce ma’aikaciyar dake kula da ita tasa tissue tana goge mata hawayen idanuwanta tana bata baki akan tayi hakuri ta daina kuka. 


 Xuciyar Halima cike da mamakin ko me ya sa axixa take kuka! Dunbin dukiyar babanta, da iliminta, ga kyau ga gata ita kuwa me xai dameta a duniya! Halima take tambayar xuciyarta. Hakika kowa da abinda yake damunsa wani rashin kudi ya dameshi wani ko kudin ya dameshi inji wani mawaki.


 Bayan dawowar axixa wannan sabon sashe cikin taimakon Allah saboda yawan addu’o’in da axixa ta dage tana yi ita da mahaifinta, cikin kula ta musamman da likitoci suke bata Allah Ya sauwakewa axixa yawan damuwa ta daina jin bugun xuciyar nan da yake damunta. Don takan tashi xaune kan gadonta tana kallon talabijin, an sayo mata kasissinan ibro iri-iri sababbi da tsofaffi na da, tana kallo wani lokaci tayi murmushi wani lokaci kuma ta tsuntsure da dariya idan yayi wata kwabar. Yau axixa kwananta tara a asibiti kwananta biyar kuma da dawowa wannan sabon sashi. Amma sai yau da kyar da sudin goshi sannan alhaji sadam ya bar  atika da munnira xasu xo wajen axixa. Da yaki fur wai ba xa su xo su dameta ba. gani yake xasu iya fada mata wasu maganganun akan abubuwan da alhaji isah da dansa suke yi a gari, sun fara yadawa amma indirectly cewar alhaji ahmad xai sauka daga kan kujerar takarar shugaban kasa ya bawa alhaji isah. Har alhaji isah duk ya fara sawa ana lillika fostocinsa duk da dai bai fito fili ya fadi cewar shi dan takarar shigaban kasa bane yanxu amma yana cewa yana batawa alhaji ahmad da abokansa rai alhaji sadam da  alhaji bala, don bayan su biyun nan babu wanda yasan abinda yake faruwa tsakanin alhaji isah da alhaji ahmad said a kuma a can bangaren alhaji isah ya fara yadawa wasu kadan daga cikin abokansa cewar alhaji ahmad xai sauka ya bar masa kujerarsa saboda wani abin kunya day a dunguma.


 Don haka kafin alhaji sadam ya bar su atika su taho asibiti wajen axixa  said a ya kirasu falonsa ya ja musu kunne sosai y ace to yau asabar xan barku kuje ku yini a asibiti wajen axixa, ban yarda ku saki baki ratata kuna hira ba balle ku yi subutar baki ku fadi wata Magana da xata sake dagawa axixa hankali. Don yanxu jikinta da sauki hankalinta ya fara kwanciya ana hira da ita radai da wasa da dariya, musamman ke atika kinfi munnira shegen surutu ko sunan mubarak karku furta mata balle wasu abubuwanda yake yi, kinga rannan ina nan falo nake jiyo muryarki kina bawa mamanki labara wai kinga mubarak a mr bigs shi da wata sumayya Emmanuel ‘yar gidan gwamnan lagos ya rike hannunta suna siyan ice cream ina ruwanki! To ki iya bakinki karki sake ki fadwa axixa. Atika t ace to in Allah Ya yarda ba xa mu fada mata maganar da xata tayar mata da hankali ba. alhaji sadam y ace yauwa idan kuma ita ta tambaye ku wani abu game da mubarak ko kuma mijallar nan da xasu fitar don alhaji ahmad ya gaya min har mafarki take taga su mubarak a kotu, to sai ku ce mata ai yanxu xancen mujalla ko xancen kotu yak au an daidaita da alhaji isah ya amince yanxu mubarak ne yayi cikin harma an kone mujallaun xance ya wuce.. da dai sauran maganganun da xasu kwantar mata da hankali in Allah Ya yarda ma har kwana ashrin da hudun ta cika su fitar da mujallaun suyi haukarsu su gama ba xata sani ba tana asibitin a kulle. Daga karshe su atika suka yi gidya suka mike suka doshi wajen mota suka shiga suka nufi asibiti dake daman sun gama shirin su tsaf xasu tafi ya kirasu yayi musu wannan gargadi.


 Atika sadam c eta ke tukawa wata tsadaddiyar motar da mahaifinta ya bata a matsayin kyauta ta kammla jami’a da suka yi. Munnira na gefenta suna tafe suna hira suna tuntsira dariya. Atika ta kalli munnira t ace wai baba ni yake cewa na fiki shegen surutu lallai baba nai sanki ba, ina na kai rabinki ma a surutu, sai dai y ace kinf I ni wayon ladabin karya idan kinga manya ki rika sum sum da kai da kyar kike magna,  ni da axixa ne ‘yan gaste gates munnira ta kyalkyale da dariya t ace kamar kin sani amma fa kwannan nan abbana ya gano hali nay a ce munnira munafuka ce mai ladabin karya. A haka dai suka ci gaba da hira ta makaranta hard a ta gida har suka isa shop suka yi siyayyar kati ta get well soon da kayan kwalama masu yawa, nan cikin ma’aikatan shop din suka taimaka musu da kwashe kayan. Akujerun baya suka xuba kayan sannan suka yi musy Allah Ya kiyaye hanya. 


 Gaskiya en matan nan biyu sun bawa mutanen dake wajen matukar sha’awa, samari da alhaxai da masu kudin inyamurai da suke shige da fice a wajen wato chief, babu wanda ransa bai biya da son ‘yan matan nan a xuciyarsa ba, musamman ma irin shigar da suka yi, kayansu iri daya, mayafansu ne da takalman su kawai suka banbanta, suna tafe suna hira har suka shiga mota, jama’a na kallonsu, wasu  suna satar kallonsu wasu a kiri kiri suke bawa idanunsu hakkinsu.


 Mahnud sa’ad mijinyawa dan gidan gwamnan baushi state ne yana daya daga cikin masu kallon kuru kuru, babu abi8nda xuciyarsa take sai dukan uku-uku tke domin shi har yaga matar da yake so, ya dade yana mafarkin irinta ta xama matarsa gasu nan ‘yan maa gwanin kyau wannan na cewa munnira ce tafi wancan na cewa atika tafi kyau, amma babu wanda yayi karya kuma idan mahawara xa a fafata akn wacce tafi kyau atika ko munnira bana jinx a a iya kayar da kowa a duk bangarorin biyu, atika tad an fi mannira tsaho duk da dai su duka dogaye ne marasa kiba, kyawawa.


 Yanxu a cikin ‘yan matan nan biyu idan aka ce ka xaba wa xaka xaba! Imran ya tambayi abokinsa Mahmud sa’ad da basher. Basher y ace farar, imran y ace a’a a ganina bakar ta fi kyau, dube su sosai kafin su shiga mota. Mahmud sa’ad wanda har yanxu yake xaune a bangaren direba dake shi ne wanda yake tuka motar bai ce komai ba yana kallon atika wacce tun da yayi toxali da ita ya bawa xuciyarsa shawarar ga abokiyar rayuwarsa. Shigowarsu kenan suka tsaya a kusa da motar su atika ko kiftawa basu yi ba daga cikin motar suka hango ‘yan matan nan suna fito shi ne suka yi lamo  a mota suka ki fitowa suna kallonsu ta cikin gilas din motar su dake baki ne wulik (tinted) na waje baya ganin na ciki. Dai dai sanda atika take bude kofar motarta xasu shiga imran da basher suka yi xuruf suka fito daga motarsu da sauri wai bari su wuce ta gabansu sun san suma sun hadu dole ‘yan matan xasu yaba, Mahmud sa’ad yana kallonsu suka fita suna tafe suna gyara riga (shirt) suka wuce ta gaban ‘yan matan nan, suka ga ko gexau su da bola duk daya ne k inda suke ma ‘yan matan basu kalla ba, suka shiga motarsu. Atika ta kunna mota inda taja wani dogon ribas har wajen get din tasa giyar gaba ta tayar da kan motar sannan ta hau titi dodar ta bude wuta tana keta gudu a titi. Imran da basher ya suka jiyo suna kallonsu har suka kure, sannan basher ya bugi imran da bayan hannunsa y ace dalla malam ga irin tan an n ace muyi musu Magana kace wai mu wuce ta gabansu xasu dasu aiga irinta nan sun kufce mana, kai ba kyau ba, nib a fasali ba, ya xa a yi su wani dasa! Ai na so mu tsara su suga  muma akwai dollars a bokina sais u sauraremu.


 Imaran y ace mun yiwa kanmu wallahi amma ai na rike nambar motar tasu (ATI ONE) aka rubuta a irin wuraren nan na ‘yan hutu ina sa ran wataran xamu sake haduwa. Kafin imran ya rufe bakinsa Mahmud sa’ad ne ya ja wani dogon ribas ya fita a guje. Wait wait! Suke fadi amma ina ya taka tad a karfi ta fisgeshi aguje yake don kada su atika sub ace masa, imran ya kalli basher y ace shegen nan fan a san ‘yan matan nan xai bi, gara ma nayiwa usman direba waya ya kawo min motata nan idan bah aka ba sai dai mu kwana a nan don na san Mahmud ya manta da mu tunda yabi ‘yan matan nan bama xai sake tunawa da yabar wasu a 911(nine eleven) ba sai ya ganmu xai hau salati y ace ya manta. Atika gudu take sharawa tsakaninta da Allah kasancewar ta sami titi makeke marar cunkoson motoci ko gargada. Haka xalika shima Mahmud biye yake da ita a guje, atika tana lura da hadaddiyar bakar jif din dake binta gaf da gaf ta madubi. Ta ce da munnira kai munnira nifa wannan bakar jif din dake bina banfa yadda da ita ba, kinsan garin nan ba lafiya karfa shegun nan ne suke binmu da wani mugun abu. Munnira ta juya da sauri tana liken motar dake bin su t ace wai suwa kike xargi!


 Su mubarak ai munfi karfin su da ikon Allah sharrinsu ya koma kansu, tsaya su wuce in ymu mu bisu  baya. Atika tasa siginal alamar xata tsaya kana tayi slow ta fara gangarawa gefen titi, ta samu waje ta tsaya cak. Abin mamaki sai wannan bakar motar da take binsu itama tayi gaba dasu kadan ta gangara gefen hanya ta tsaya, wannan abu ya karatsorota ‘yan matan nan biyu suka kuma sake gaskatwa su wannan motar take bi, suna xaune a mota suna kallon motar a gabansu xuciyarsu cike da fargaba, kwakwalwarsu cike da xulumin yaya xasu yi, sai suka ga an bude kofar gaba ta bangaren direba, wani  santalelen saurayi ne mai gwarxa-gwarxan ido ‘dan kyakkyawa ya fito daga motar, (NI KUMA NACE KOMAI KYANSA BAI KAI BOSS INA BA)  ya fito ya tunkaro su atika. Cikin fargaba da rudani munnira t ace da atika, atika yi sauri ki danna mana lock din motar atika ta danna kofofin motar dukka hudun suka datse, ya karaso daidai wundon atika yana mata Magana ta gilas dake duk gilashin motar a dage suke daman saboda na’urar sanyin da suka kunna a motar wato A.C ya sake matsowa ya sunkuyo yana Magana, amma babu kalma daya da ta shiga kunnuwansu basa jin abinda yake fada, yasa hannunsa ya kwankwasa gilas din da wani xoben da yake jikin babban dan yatsansa yana ci gaba da Magana, munnira da atika sai xare ido suke yi a tsoroce suke musamman ganin hannunsa daya a aljihunsa yake, suna fargabar ko wata ‘yan bindiga ce . atika ina ga mu ruga a guje mu bar mutumin nan bashi da gaskiya haka kawai daga ganinmu a mota ka ringa binmu mun tsaya shima ya tsaya to me xai ce mana! Ko kin san shi ne a wani wajen atika t ace kin jiki, ina xan san wannan halittar ke baki sanshi, bakya ganinsa kamar ma bad an…

.

.

Comment dinkufa yaragu ko littafin babu dadi mucanza wani ina neman shawararku

[9/5, 3:23 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/5, 3:24 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3

*14*


.

Ba kya ganinsa kamar ma ba dan Nigeria ba, kamar wani black American, ko wani dan south Africa koma wani dan Somalia ne oho, kuma da yadda akayi bashi kadai bane a wannan bakar motar don tun a 911 na ganta a kusa da mu har wasu samari guda biyu suka fito daga ciki. Munnira tace ah to wannan mu suke  bi dan Allah tada motar mu gudu rabu dashi, sai wani murmushi yake yi na mugunta, duk ire-irensu mubarak ne ‘yan iskan lagos ne kinsan yanxu mubarak sune da lagos saboda sumayya Emmanuel, muje muje atika karki sake kallonsa ma. Atika  ta kunna mota da sauri yayain da ta fussga a guje tabar shi a nan a tsaye. A guje take tukin har saida ta daina hango shi sannan tayi ajiyar xuciya. Ta ce munnira kina ganin xamu ci gaba da yawo a cikin Abuja  haka mu kadai, nifa su mubarak sun fara bani tsoro kinsan me ya faru? Munnira tace a’a sai kin fada. Atika ta sauke numfashin daya tunkaro hancinta ta juya tadan kalli munnira sannan ta mayar da idanuwanta ga kallon gabanta tace kinsan ada sadik gulma yake yi irin baya bin bayan axixa baya kuma bin mubarak, to yanxu da gulmar ta kare masa shi ne ya fito sarari yana cemin wai gaskiya axixa bata kyauta ba, me nene da me nene wasu surutan banxa dai harda cewa in har ina so dangantakar mu da soyayyarmu ta ci gaba dole ne naja baya da axixa don ba xai yiwu yana hulda da mubarak ba yaxo yana yi da axixa domin idan ina tare da axixa xasu ringa haduwa, munnira ta danyi kara don mamaki yayin da wani ashar ya kubuce mata tace A’uxubillahi har ina danna asher yanxu  haka sadik yace miki? Mamaki xai kashe munnira atika ta kyalkyale da dariya, nace masa kai yanxu sadik banda abinka soyayyar ma da muke yi kara ce kawai, ba wai har xuciyata ba, babu inda xata je. Wato kai a xatonka nayi nisan da bana jin kira akanka har wasu dokoki xaka sakamin kenan? 


  Na ce to kuwa da ka cire matsayin da ka kai kanka a wajena don kuwa Karen gidansu axixa ma baxan rabu dashi ba balle axixar kanta. Xanfi jin ciwon rabuwa da beran gidan su axixa da rabuwa da kai. Munnira ta kyalkyale da dariya tana tafawa saboda bala’in burgeta din da ta yi wajen bashi amsar da ta dace da maganar daya fada. Atika ta ci gaba da cewa sai nan da nan ya canja haushi ya kamashi yayi wani farat ya mike daga kan kujera daman a farfajiyar nicon hlton muka hadu wajen ‘yan runfofin nan na hutawa yace haka kika ce ko? To naji daga yau na janye soyayyar nima da nake yi miki kije da axixa ni xanje da mubarak mu xuba. Ko kallonsa banyi bana yi watsi dashi na kau da kai ina wakar Jennifer lopex ta “if you have my love”. Munnira ta mika mata hannu suka kashe tace atika kin burgeni, kina kan burgeni kuma ai nima munyi haka da Ibrahim jiya jiyan nan ina jin mubarak ne ya turosu wato so yake ya xugesu su rabu da mu dan shi sun rabu da axixa.


 Kin san tsoransa suke juya su yake kamar waina, kamar yadda ubansa yake juya iyayensu suma, ai gara keda sadik da soyayyar har yana miki xancen aure ke kika ki. Ni kuwa fada nake fada da uwarsa ina xancen ta bari ya aure ni, atika ta juyo tana mata kallon mamaki gami da bude bakin mamaki. Munnira tace wallahi fada ni da uwarsa sosai harda yaba Magana, na tsaya nayi mata tatas dan nasan na rabu da Ibrahim nagama, tun kafin haka ta faru tsakanin axixa da mubarak. Atika tace ban labari a dai dai lokacin ne suka karaso get din shiga babban asibitin wato international hospital yayin da masu gadi suka bude musu get suka shige ciki. Munnira tace a ranar birthday party daddyn axixa muka hadu da ita, kinsan ta je ita da kawayenta en duniyar nan su hajiya rabi , na xo wucewa ina nemanku sai naji ance gata nan , itace munnira, na juyo da sauri don naga magulmata. Sai naga suruka tace naje da ‘yar kunyar nan na duka na gaishe su, ke kinga dakyar suka amsa har maman Ibrahim dinfa sai daya daga cikinsu tace surukan xamani ko durkusawa sosai ba a yi, sai maman Ibrahim din tace  ina xan yadda daman na kai dana wajen masu soyayyan ido kesashshe ai sai a xamar min dashi bawa, wata motsatstsiya a ciki da wani bakin lebenta sai tace ko kai a raba ki da shi kwatakwata an ga naira.


 Raina yabaci, da har xan wuce na yi shiru sai nace kai bari  na gyara musu daurin dan kwalin kansu naga duk a karkace suka yi shi na juyo nace, Allah Sarki masu da, idan ma yace xan aureshi to karya yake yi, don ibarahim bashi da abinda xan iya aurensa sai dai ma cane shi ne xai kwasa ya kaiwa uwarsa, dan ‘yan kano to jidda masu bakin lebe ragowar taba. Kowa gaba yake so ya ci, ba baya ba. napi ibarhim kudi sai dai na nemi wanda ya fini sai duk suka rike baki wasu na salati, daurin dankwalin da suka turoshi gaba sai naga ana turashi baya. Na wuce ina karkada mukullin mota ina juyawa, bayan da aka gama party ina fitowa na hango kungiyarsu wasu tafka tafkan mata da kyar suke juyi a gabana, kawai na bangaje wasu na wuce, shi ne babarsa take wani fadace fadacenta wai marar kunya ko girmanmu bata gani, ko kallonta banyi bana wuce amma ibarhim yaki rabuwa da ni sai a kan axixa da mubarak muka rabu jiyan nan atika tace Allah mutuniyar, yanxu haka kuka yi baki gaya min ba, lallai? 


 A daidai lokacin ne suka karaso wajen da ake tsayawa suka tsaya, sannan suka fito suka debo ledojinsu, hannunsu bibbiyu cike  da kaya suka doshi dakin da axixa take kwance. Security dake wajan ta ruga da sauri ta karbi ledojin hannunsu tana yi musu sannu da xuwa. Xuciyarta cike da farin ciki ta san yau ko ba komai xata samu ‘yr dubu biyar a wajen ‘yan matan nan, don daman ta san masu xuwa duba axixa masu kyauta ne don kullum alhaji ahmad da abokan sa sai sun bata kudi masu yawa idan suka xo, tana gaba suna biye da ita har cikin dakin. Axixa suka gani xaune a kan gado sanye da doguwar riga da hijab carbi a hannunta. Munnira ce a gaba ta karasa da sauri wajan axixa ta rungumeta su duka suna hawaye, atika ma da sauri ta karaso ta rungume axixa. Suka ga axixa ta rame tayi wani fari fau, sai dara daran idanuwanta ne suka sake fiffitowa, dogon hancinta ya sake fitowa ya yi dodar, suna kallonta xuciyarsu cike da tausayinta babu wanda ya iya Magana a cikinsu sai axixa take hawaye. Shigowar wani mutum ce tasa dukkansu ukun suka juya idanuwansu xuwa bakin kofar dakin,

 Mahmud sa’ad ne, wannan saurayin da yake binsu tundaga 911. Yayi wuri wuri ya kasa cewa komai sai kallon kallo suke yi shi da ‘yan matan ukun.


 Munnira ita kam harta karkata rabin jikinta xuwa ga bandaki wai idan taga alamar ya nufosu da mugun abu ta fada bandaki ta rufe. Mahamud sa’ad ya ji kamar a mafarki daya daga cikin ‘yan matan uku ta kira sunansa, yayi furgigit ya kalleta gami da karasowa wajen gadon cike da mamaki, ta yi murmushi tace Mahmud baka gane niba ko? Ya yi mata kallon kurilla ya yi ajiyar xuciya yace ah axixa kece? Long time yaya kike? Atika da munira suka sauke numfashin daya kasa durgowa waje don tashin hankali. Axixa ta nuna masa kujera tace ya xauna. Bayan ya xauna ne suka sake gaisawa da axixa tace a’a na dauka wani ne ya gaya maka ina nan ka xo. Mahmud ya yi doguwar ajiyar xuciya yace eh to tare da sisters dinki muke. Ya nuna su atika wadanda har yanxu suke tsatstsaye suna kallonsu, suna tambayar kansu da kansu to wannan ina axixa ta sanshi ya sansu ne a wajen axixa shi yasa  yaketa binsu? 

Axixa ta kalli atika ta kalli munnira taga kamar fuskarsu ta nuna sufa ba tare suke ba, basu sanshi ba. tace atika ya dai kuke kallon kallo da Mahmud ashe tare kuke baku gaya min ba, munnira tayi murmushi tace tare muke das hi amma ai bamu sanshi ba mu dai tun daga  911 yake binmu we don’t know why? 

Mahmud yayi ‘yar siririyar dariya ya kalli axixa yace axxy kamar yadda kika san ni da har yanxu haka nake, I don’t hide my feelings and I said what is in my mind . naga kawarki ko sister ki wannan ya nuna atika, naji ina son ta xama kawata atleast mu ringa gaisawa, atika ta galla masa uwar harara, munnira da axixa suka kyalkyale da dariya. Kallo daya xaka yiwa Mahmud xaka gane yana cikin wani hali na fargaba idan atika ta ki bashi hadin kai.


 Yayi narai narai da ido kamar xai yi kuka, Magana yake tsakanin sa da Allah bada wasa ba, axixa tace kar ka damu Mahmud atika sunanta and she is my best friend every thing will be alright, just cool down and relax. Mahmud ya yi ajiyar xuciya yayin da wani jini mai sanyi ya fara xagawa a cikin xuciyarsa. Axixa ta juya ta kalli atika ta bata rai tace ke atika ga yayana Mahmud ki xama kawarsa yanxun nan. Dukansu suka tutsire da dariya har Mahmud din. Ya ce axixa har yanxu kina nan da manyancenki din nan dana sanki dashi a da ko? 

Atika tace, kece ma baba ko kuma ince mama, to mama axixa na ji. 

Mahmud ya xare gilashin dake fuskarsa ya kura ido akan atika tana Magana sai kallonta yake yi nan dai munnira ta kula da kallon Mahmud yayi yawa da yake yiwa atika, ta kamo hannun atika ta tura ta waje tace Mahmud bita kuje ku gaisa muma musa so mu gana da ‘yar kawata. Mahmud ya samu abinda yake so ya yi xumbur ya mike ya bi atika wacce take kokarin dawowa dakin, Mahmud ya tarbe gabanta, munnira tayi sauri ta rufo kofar dakin, atika da Mahmud suna tafe suna ‘yar hira har wajen motocinsu , munnira ta dawo ta xauna kan gado tana dariya tace, Allah mutumin ya cika naci tun a hanya yake binmu yana yi mana Magana bamu kula shi ba, ashe saida ya biyo mu ya xo ya kura mata ido harda cire gilashin idonsa, ina kika sanshi ne wai ke? 


 Axixa tayi murmushi tace Mahmud sa’ad mujinyawa wani senior na ne a high school muna shekarar farko su kuma suna ajin karshe, suka fita suka barmu, munyi mutunci da Mahmud sosai sune masu tar mun fada idan na tsokano kinsan tun ina yarinya baki na baya shiru, ban sake haduwa dashi ba sai a spain wata shekara da aka yi min aiki a wuya, shi kuma ya raka dad dinsa ganin likita sai a talabijin nake dan ganinsa sometimes a wasu occations kinsan dan gidan gwamnan bauci ne, gaskiya Mahmud yana da kirki ga nutsuwa akwai ilimi kuma. Munnira tace af axixa ga kayanki a leda irin wannan shaddar ta jikinmu tare muka dinka, tashi ki cire wannan doguwar rigar ta jikinki ki saka. Axixa tayi murmushin karfin hali tace haba munnira ina ni ina wata kwalliya? Ku dai kuyi ‘yan mata wallahi tunda kuka shigo nake kallonku kunyi min kyau kamar wasu’yan biyu. Dole Mahmud ya rikice da ganin atika, munnira tace to ke in kin saka sai kin fi yin kyau fiye da mu. Axixa tace munnira kima daina bata bakinki babu wani farin cikin danake ji a rayuwata balle nayi wani ado, nayi ma wa? 

Munnira ta cire gyalen da ta yane jikinta tace da axixa shin xaki tashi ki sa ko sai na saka miki da Karfi? 

Kinga fa baki da lafiya banso na matseki ki tashi  kisa axixa me ye bambancin ki a da da kuma yanxu ki daina sawa ranki da banbanci, shi yasa kike damuwa mu duk daya muke ganinki kece dai kike ganin wani iri, dan Allah kawata tashi ki saka kinga ba za mu ji dadi ba, musamman atika da kanta taje ta sayo mana a wani kanti ta kai dinki tace lallai a dinka kafin yau asabar saboda mu taho miki dasu ki saka. Kalar da kike so ce fa axixa karki sanyayar mana da gwiwa.


 Sallamr dr rislan ceta katse axixa daga amsar da take shirin bawa munnira suka amsa masa cikin fara’a. ya shigo bayan sun gaisa ya kalli axixa yace yaya jikin naki? Axixa tace Alhamdulillah na ji sauki. Ya ce to Allah Ya kara sauki, ya dauko abun aune aunensu yace to bari na auna BP dinki. Munnira daga kan gado ta koma kan kujera. Dr rislan ya daure mata dantsan hannunta yasa a kunnensa yana matsa wani dan kullutun da yake hura iska a jikin abinda ya daure hannun axixa, bayan yayi dan gwaje gwajensa ya ciccire mata sai yayi murmushi yace yauwa axixa ko kefa? Sauki ya fara samuwa ya dauko magungunan daya kamata tasha ya bata sannan ya juya ya kalli kujerar daya kamata ma’aikaciyar jinya daya mai kula da ita tana xaune yace, a’a wa cece yau ya kamata ta xama tana nan? 

Axixa tace mis na’omi ce, ta xo nace ta je can ofishinsu ta hutawarta, tunda niba abinda xata yi min. komai ina iya yi da kaina, kuma ga kawayena nan sunxo xasu tayani hira yau har dare kaga na’omi gara ta huta.


 Dr rislan ya juya ya kalli munnira yace ok, kawayenki sunxo ashe amma kamar banga atika ba kwata kwata, ko bata gari ne? axixa tace ah tare suka xo da atika tadan fita ne yanxu xata dawo. Dr rislan yace itama wannan kamar na so na santa dan dai kunfi xuwa da atika ne. axixa tace xaka santa mana sunanta munnira bala cikin fara’a yace oh munnira Bala ce ok dad dinki ya bani sunanta a cikin sunayen wadanda xasu xo su dubaki. Munnira ta danyi murmushi ta kawar da kai gefe alamar ta kagu ya yi fice ya basu waje, gashi sai kallonta yake yi yadda ta tsani kallo maimakon ya fita sai ya je kusa da kujerar ta ya xauna akan dayann kujerar, kamar yadda ya saba bayan ya dudduba axixa sai ya dan xauna su taba ‘yar hira sannan ya fita, haka ko da xai shigo sau goma sai ya taba ‘yar hira da axixa don ya ji ko akwai wani abinda yake damunta a rai yake sata damuwa a rai, ta sigar wayo da dabaru irin nasu na kwararrun likitoci yayi bugun cikin axixa har ya gaji amma baiji tak ba akan abinda yake daga mata hankali har take tunanin gara mutuwarta da irin rayuwar da ta ke ciki.


 Bayan dr rislan ya xauna a kusa da munnira suna ‘yar hira da axixa amma yau yanayin hirarsu ya bambanta da kullum sai axixa tayi ta Magana ita kadai dr rislan bai ji ba yana satar kallon munnira.   Axixa ta lura da hakan sai taji bakinta tayi shiru ta xuba musu ido kawai tana kallo. Munnira ta lura kallon da dr rislan yake  yi mata ya yi yawa sai ta yi dan siririn tsaki ta harareshi ta mike ta nufo wajen axixa ta xauna akan gado  kusa da ita tace, axixa muyi hirarmu kinji yaya gari? 

Axixa tayi murmushi tace gari ku xa a tambaya ke da dr rislan  ni da nake a makale kamar wata kaxa a akurki. Dr rislan yace gaskiya munnira ke xa a tambaya gari ke ce a gari don nima ina nan asibiti tare da axixa idan kinga na fita to gida naje ina xuwa kuma bacci xanyi saboda na gaji gani gwauro. Munnira ta yi shiru ta sakar musu hirar don dr rislan ya saka baki, ita tafi son  ya tashi ya fita ya barta da kawarta, har wani gyara xama yake yi. Can ya sake lakuto munnira da hira yace hajiya munnira ko kina tsoron allura ne naga tun daxu kinki sakin jiki muyi hira? Kuma ma baki cika rako axixa asibitin nan ba.


 Munnira dai har yanxu taki ta tanka masa ba wai ko in yaga tayi shiru xai tashi ya fita. Axixa t agama karanta dr rislan wannan yan shinshine shinshinen da yake yi tabbas kokarin kawo hira yake wajen munnira yana son su saba daga karshe kuma soyayya ce batun. Ita ko taki fur, ko me nene dalilin da taji bai kwanta mata ba? 


dr rislan saurayi ne san kowacce budurwa kin wacce ta rasa ya hadu inji samari, yaro ne dogo santalalle siriri mai kyan gaske. Kallo daya xaka yi masa kasan ya hada jini da farar fata, mahaifinsa ne bahaushe, mahaifiyarsa kuwa ‘yar dubai ce, don haka ya dauko kamar mahaifiyarsa, gashin kansa ne mai tauri irin namu na hausa, amma farin hancin duk irin na larabawa ne.


 Dr rislan ya mike tsaye kyakkywar fuskarsa cike da murmushi yace axixa bari na fita na barki da kawarki ko ta sake naga bata son na xauna na taya ku hira, yanayi yana kallon munnira wacce cikin rada tace da yafi m. dr rislan da axixa suka hada ido suka tuntsire da dariya domin dukkansu sun lura da motsin bakinta sun gane abinda tace dr rislan yace kawarki cewa tayi dama yafi na fita din, to babu inda xani idan kuwa kinga na fita sai dai in ke ce kika rakani har office. Munnira tace doctor don Allah kaje ni har ciwon kai  nake ji wallahi, axixa tace aiko kin hadu da maganin ciwon kai tunda gaki ga dr rislan don haka ki tashi ki raka shi office dinsa ya rubuta miki magani ki sha ki wrake doctor rislan yace yauwa axixa haka xa a yi, kafin munnira tace wani abu axixa ta tashi taja hannunta ta tura waje tace haka kika yiwa atika daxu kema kije. Munnira tace Allah axixa tausayinki nake don baki da karfi to bari na dauki gyale na. axixa ta jawo gyalenta ce gashi nan ta wurga mata. Doctor  rislan yace yauwa axixa yau ni kin gama mun komai. Ya bi munnira suka fice axixa ta tura kofa ta rufe, sai ta tsinci kanta cikin matsananciyar damuwa, ta kara tausayawa kanta da kanta.


 Sha’awar munnira da atika ta kamata, ta gansu das gwanin sha’awa yanmata masu jini a jika wadanda xabga xabgan samari suka mace a sonsu. Hakika na tashi daga aiki axixa ta fada a bayyane yayin da hawaye ya fara bulbulowa daga idanuwanta akan kujera ta xauna ta sa hannu biyu ta dafe goshinta hawaye yana xuba ratata akan cinyarta.wani gumi ya keto mata yayin da ta fusge hijabin da ta kunsumawa kanta akan doguwar rigar da ta bunjuma. Haushi da takaicin rayuwa ta isheta, hakika ashruf bai cika alkawari ba tunda gashi har yau bai neme ni ba, koda yake tunda yaga ban amince na karbi xobensa ba, a matsayin sadaki nasan ya fitar da rai akai na. wata kila ma ya dauka har anyi bikinmu da mubarak, shima me yiwa ya samu wata. Axixa take tunani a ranta, hawaye ya ci gaba da shatatowa daga idanuwanta. Shigowar na’omi ce tasa axixa ta tsagaita da kukan da take yi tadago idonta da kyar ta kalli na’omi wacce ta sankare a tsaye da ture din abinci a hannunta . tace madam axixa kukan ne ya dawo haba kyakkyawa dake kina damuwa ko akwai wani ciwo ne da yake damunki na kira likita? 


 Axixa ta girgixa kai alamar a’a tasa hijab dinta tana goge idonta na’omi ta ajiye farantin abinci a gaban axixa ta dauki fulet da cokali tana kokarin bude flask din abincin ta xuba mata. Axixa ta daga mata hannu alamar ta dakata da xuba abincin nan. Na’omi tayi kasake tana kallon axixa, axixa ta nisa tace don’t worry na’omi bana jin cin abincin ne kwashe kawai ki mayar musu kicin ko kuma kuje kuci. Ta mike ta shiga bandaki ba tare da ta jira amsa daga bakin na’omi ba. cikin tausayawa da jimami na’omi ta sintimi farantin abinci, wani bangaren na xuciyarta cike da farin ciki yau xata yi lunch da abinci mai maiko. Duk a irin wadatattun kudi da alhaji ahmad yake biya a ciki ne ake dafawa axixa hadaddun abinci wanda ko a gidansu ne abinda xa a bata kenan. Tana shiga bandaki ta mayar da kofa  ta rufe ta doshi wajen wani katon madubi da yake sakale a jikin bangon bandakin, wanda girmansa ya isa xaka iya ganin surar jikinka gaba daya daga sama har kasa taga dai itace dai axixa kamanninta basu canja ba,  ba kamar yadda xuciyarta take aiyana mata ba cewar duk kin yakune kin tsufa, kinyi muni, taga kamar ma yanxu tafi da kyau ramar da tayi ta kara fito mata da dogon hancinta da gwarxa gwarxan idanuwanta, chocolate colour dinta ta kara yin haske. Ta tube rigarta don taga girman cikinta, sai taga kai idan ba ita bata san tana da ciki kuma take aiyanawa a ranta babu wanda xai kalli cikinta ta yace tana da ciki har wata uku.


 Sai dai kuma taga kirjinta ya cicciko ba kamar daba. tayi ajiyar xuciya gami da sake goggoge guntayen hawayen da idanuwanta ta kalli idonta a kode suke fari fat babu kwalli, tace a ranta nasa kaina a kunci, rabona da kwallia har na manta, mai yayi xafi? 

Kamar wata mai takaba abinda ya sameni ya riga ya same ni to wannan damuwa da nake yi baxa ta yi min maganin halin da nake ciki ba. duka wanda yasa Allah a gaba ba xai gaba dai dai ba, ina cikin xamana Allah Ya turo ashruf har ya yi min haka, kuma ina cikin xamana Allah Xai kawo min hanyar da xan fita daga cikin xulumi. Xuciyarta ce take mata nasiha don itama ta gaji da tsananin kunar bakin ciki har bugunnta yake canjawa. Axixa ta kalli xoben da ashrfu ya saka mata a hannu a ranar da aka gansu a dajin nan. Ta kuma tuna kalaman daya gaya mata a lokacin, sai ta tsinci kanta cikin wani farin cikin damuwar da ta gallabe da ta fara kama gabanta. Ta xauna a gefen bahon wankan dake bandakin a hankali. Tana tunano rayuwar soyayyar da suke yi da ashruf a wannan dajin da suka xauna, tace a ranta, “ashruf me yasa ka bari aka ganmu? 

Gashi nan na xo gidan namu amma na tagaiyara, yanxu da har yanxu muna can sai nayi rainon cikinka na haife babu wanda yaji, mu tafi wata kasa muyi auren mu gashi na dawo gida nasa mahaifina a cikin musifa, hakika ashruf ina sonka, ina sonka har yanxu, ko da har abada ba xa mu hadu ba to xan dinga ganin danka, Allah nagode da ka sa abunda ya faru ya xamo sanadiyar ciki, cikin ashruf”. Tasa hannu ta shafa cikin tayi murmushi. 


 Yau ce rana ta farko da axixa taji wannan muguwar damuwar ta saketa, ta tsani abin cikinta a da, sai gashi yau soyayyar da take yiwa ashruf ya shafi ‘yarsa ko ‘dansa na cikin cikinta. Ta ci gaba da cewa a ranta naji dadi na kuma godewa Allah, da wannan cikin bana mubarak bane, mutumin da bana so irin tsiya marasa mutunci. Sai dai yanxu abu daya ne matsala shi ne baxan iya tarar daddy na ba, na gaya masa ba mubarak bane yayi min cikin ashruf ne. yadda daddyna ya nuna ya tsani ashruf balle ace yayi min ciki kuma ba a ma san inda yake ba , ai na shiga uku. Sannan ba a ga ashruf ba kuma ba mubarak bane to mutane xasu ce da gaske su alhaji isah suke kenan musamman ma yadda alhaji sadam da alhaji bala suka xake suna tayar da jijiyoyin wuya su a dole sai mubarak ya amsa har suna xancen kai kotu. Ta yaya xan fito nace musu mubarak ya fi su gaskiya? axixa ta yi ajiyar xuciya tace a ranta ina cikin mummunan hali, bani da ta cewa, Nigeria gaba daya ma tana cikin wani hali na rudu, babu wanda xan tara na gaya masa halin da nake ciki ko da kuwa kawayena baxan iya gaya musu ba mubarak bane ashruf ne,  me xasu dauke ni? 

Yar iska? 

Tayi shiru ta dauki lokaci mai tsawo tana tunani, to amma kalma dayace da xarar ta tuna ta take jin sanyi a ranta, itace babu abinda ya gagari Allah mai kowa mai komai. (NIMA NA CE HAKKUN BABU ABINDA YA GAGARI ALLAH, INA ROKONSA YA CIKA MANA BURINMU NA ALKHAIRI CIKIN DUKKAN KHAIRI, YA KUMA RUPA ASIRINMU, amen) ta danka gaba ki daya lamuranta gare Shi Shi ne kadai xai iya fitar da ita daga tarkon makiya ba wani ashruf ba. daga karshe ta mike ta fada baho don sake sabon wanka, ta ciro karamin tawul dinta dake rataye a bandakin tadaura ta bude kofar bandakin ta leko cikin dakin taga babu kowa su atika basu dawo ba har yanxu.


 Murmushi ne ya kubuce mata tace munafukai da kowace taki xuwa sai da aka turata shi ne suka je suka yi bulunbukui. Ashe suna so ni mutumin da bana so ko minti biyar ai ba xan iya yi dashi ba balle awa. Take fada axuciyarta, ta fito daga bandakin ta doshi kan lokar dake gefen gadonta don shafa ‘yan mayukanta da aka jera mata. Bayan tagama shafa mai sai ta jawo jakar atika ta bude tabbas tasan xata sami abinda take nema, hoda da janbaki da turare , wannan dole xaka same su a koda yaushe a jakar atika. Yawan kwalliya ce da ita don haka take yawo da abinta a jaka. Axixa ta shafa hodar atika, tayi kwaliya nan ta koma kamar axixanta na na da, harta fida kyau, ta dauko irin dunkinda suka kawo mata irin nasu ta saka, ta koma bandaki don sake kallon madubi, itama kanta ganinta tayi kamar ba ita ba, tayi kyau sosai. Ta sake kallon fuskarta a mudubi tayi murmushi tace a ranta inama nima yanxu ashruf ya shigo ya xo ya ganni kamar yadda Mahmud yaga atika, dr rislan yaga munnira. 


 Bana sha’awar ko wane da namiji baya ga ashruf. Muryarsu atika ceta katse mata tunanin da take yi a gaban mudubi. Ta fito daga bandakin da sauri suna ganinta cikin murna da mamaki suka yo kanta, kai! Gaskiya axixa kinyi kyau harma tafi yi miki kyau fiye da mu. Daman axixa akwai iya dauri, ta yi daurin ta mai kyau, ita ko a ranta take cewa dama nima naga ashruf dina nima yanxun nan. Duka suka xaxxauna a kan gado, munnira ta debo ledojin da suka yi mata sayayya suka jifge mata a gaban ta, tana bubbudewa fuskarta cike da fara’a, komai ta daga sai ta yaba dashi tayi murna tace kai waye ya xabo wannan ashe kun iya xabe? 

Kamar kunsan ina so naci cingam kuka siyo min. suma dadi ya lullube su don daman suna xulumin ba komai bane yake burge axixa amma sai gashi yau duk abinda suka kawo mata yayi mata, ta dago greating cards ta bude na farko taga sunan munnira ne mai kunshe da kalmomin fatan samun sauki “get well soon” ta yi murmushi ta ajiye ta jawo dayan na atika ne shima dai na fatan samun sauki ne. ta kalle su ta yamutse fuska tace duk abubwanda kuka kawomin sunyi mun amma banda wadannan cards din duk kuka sayo na get well soo babu wacce ta tuna da  ‘dan cikina tace bari na siyo na babies, ko wani mai cartoons a cikin ku, ko ba ku san ina son baby na ba? suka yi wuri wuri da ido, ko wace cike da mamaki suna kuma fargabar furta wata kalma da xata tasowa axixa ciwonta don sunji gargadin da akayi musu.

.

.

 To jama’a, a cikin tambayoyin mu na da, wanda muka yi tambaya a kan, cikin axixa da ashruf wa ya fi so da kaunar wanin sa? 

Da yawa daga cikin ku suke cewa ashruf ya fi axixa , ni dai nace laa,a nawa ganin, axixa ta pi kaunar ashruf yadda nima na pi so da kaunar …………… 

Comment da sharhi su suke kara kargin guiwa nagode

[9/5, 3:24 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/5, 3:25 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3

*15*

.

.

 Munnira tace a ranta ashe dana siyi mata na welcome to the world new born baby xata ji dadi atika ta hanani  babu wacce ta tanka wa axixa akan maganar da ta yi musu. Wannan abu ya bawa axixa matukar mamaki tana  ta Magana  ita kadai basu bata amsa ba sai xare ido suke. Tayi murmushi kawai, don ta gane abinda suke gudu kada su fadi abinda xai tayar mata da ciwon ta . Sai  kawai ta bar hirar itama ta share.  Ta dauko hirar Mahmud da dr rislan nan fa ka ji muryoyinsu rangadai, axixa tace daxu a raina nace munafukai nan  kowacce tana cewa bana so ana turata nace kinji su mucus an sami abokai. Atika tace ke dai bari axxy Mahmud din nan ya iya hira shi ne kika ga na jima waishi dan Allah na dinga bashi ko kwana daya ne  a sati yana kawo min xiyara, yana so ya zama abokina, tunda yasan yaxo late yasan wani ya rigashi don babu yadda  xa’a yi kyakkyawa kamata na rasa wanda ya mace min.


  Axixa ta yi dariya  tace Mahmud kam ya yi gaskiya  sadik ya riga shi atika tace wane Sadiq? Ai munyi baram baram. Kifkifta idon da munnira ta ke yiwa atika shi ne ya tunatar da ita gargadin da mahaifinta yayi musu. Atika tace a ranta ai kuwa Baba yayi gaskiya daya ce min me shegen surutu gashi har na manta na fara xuba axixa bata lura da kifta idon da munnira tayiwa atika ba sai taji kawai atika ta yi shiru, da ta dauko hira, axixa ta gyara xama tace meye ke kuwa xai sa kuyi baram baram da sadik. Shi da baya son bacin ranki? Atika ta kasa bawa axixa wannan amsa, munnira ceta yi caraf tace karyar atika  ce, babu abinda ya hadasu da sadik yanxu muka rabu dasu, har mubarak dinma.


 Axixa tayi wani kagaggen murmushi da kyar tace yau saura kwana goma sha biyar su mubarak su fitar da mujallarsu ko? Ragas kake ji a xuciyar atika da munnira, munnira ta nisa tace axxy wato ke duk sasantawar da akayi tsakanin daddyn mubarak da daddyn ki baki sani ba? . atika ta gyra xama tace ai alhaji isah da kansa yaje ya sami daddynki ya bashi hakuri suka ce sunsan sunyi kuskure abubuwan da suka fada, mujallu kuwa duk an kone su xance ya wuce. Munnira ta kara da cewa ai shi ne yanxu mubarak ya xo yake ce mana yaya xaiyi ya xo wajenki yana jin kunyarki, mu tayashi baki hakuri yasan ya yi kuskure, ya kuma yarda ciki nasa ne. axixa ta kyalkyale da dariya ta sake kallon fuskokinsu ta sake tuntsirewa da dariya harda kwalla takeyi dan dariya, farin ciki ya kama su munnira wato su gasu masu iya tsara maganar kwantar da hankali. A tunaninsu axixa ta tsaru da tsarin da suka yi mata, gashi har hankalinta ya kwanta axixa ta lafa da dariya tace ina jinku wato yanxu xance ya wuce mubarak da mahaifinsa sun ce dai cikin nasu ne dai ko? Atika ta yi murmushin dadi tace kwarai kuwa axixa tace to yaushe ne bikinmu don nafi so na haifar masa dansa a gidan sa? Munnira tace to ai duk sai kin samu sauki ne naji an fara tsara yadda xa a yi bikinku wai sai kin warware. 


 Axixa ta sake tunstirewa da dariya ta ce makaryata. Yaushe kuka kware da karya ban sani ba? suka tsaya cirko cirko can atika tace au baki yarda ba? yaushe muka taba yi miki karya? 

Axixa tace yau dai kun fara daga jin wannan kalamai naku kakaf abinda xaku xo min dashi ne, kawai don hankalina ya kwanta, to na gane ku karya ne har abada alhaji isah da mubarak ba xa su taba amincewa da cikin ba, mubarak kuma yanxu ya sami sabuwar budurwarsa sumayya tajuddeen Emanuel ‘yar gidan gwamnan lagos  radau kake jin bugun faduwar gaba a tare dasu atika, suka yi tsit basu da ta cewa. Ta ci gaba da cewa tunda alhaji isah ya furta sai ya fitar da mujallun nan  harda sa rana kuwa, gashi yau saura kwana goma sha, babu wani xancen sulhu, axixa ta daddaka musu dundu a kai tace kawayena ku saki jikinku muyi hira kunji ni ku sake, babu wata Magana da xata gigita ni, don haka muyi labarin gskiya da gaskiya. ta sake yin dariya, ta sake tambayarsu, suka biye mata suna yiwa kansu da kansu dariya, atika tace shegiya axixa wato kin gane mu shi ne don kanki kika ci gaba da bugun cikinmu ko? Wallahi karya bata da dadi musamman idan aka kamaka. Munnira tace ai shi yasa ake cewa ramin karya kurarre ne. mu kam yau an kama mu, yanxu dan Allah wane munafiki ne har ya xo ya baki labarin mubarak da sumayya? Axixa tace mubarak ne ya fada min a waya, atika tace wannan mubarak din ya cika marar mutunci nifa shi yasa kika ga muna jin tsoron Mahmud sa’ad da yaketa binmu daxu na dauka ire iren su mubarak ne.


 Axixa ta yi tsaki ta kau da kai t ace meye kuwa mubarak xai iya yi muku ko ni da muka yi haka dashi ya isa ya hana ni yawo a garin Abuja, ai da shi da ubansa duk basu isa ba, su din me? 😏 Don haka kuje duk inda kuke so babu abinda ya isa yayi muku. To ku meye ma ya hadaku dashi? 😏 Ba ni yake fada don haka bai shafe ku ba. ga abokansa samarin ku dole xaku haduwa, kuyi gaisawar mutunci, ni wallahi bana so ku dauki gaba da mubarak a kaina. Atika ta tabe baki tace in gaya miki gaskiya mun bata dasu sadik, mubarak ya xugasu sunxo munyi baram baram. Atika ta kwashe labarin yadda suka yi da sadik kakaf ta gayawa aixa kamar dai yadda ta bawa munnira labari a mota.


 Axix tayi murmushi tace amma atika akwai ki da wulakanci wato beran gidanmu ya fi sadik matsayi a wajenki kenan lallai dole sadik yaji haushi duk irin son day a nuna miki. Munnira ta yi dariya tace to ai atika da sauki tayiwa sadik, ni kuwa jiya jiyanan juma’a muka yi rashin mutunci dashi ibarahim ya fada min inda xaki xaki san mutum daya ne ya turo su, kuma shi kadai ya  xo min babu dan rakiya. Ana saukowa daga masallacin juma’a sai gashi a gidanmu na fito ina wasa da willi dog Karen gidanmu. Kinsan masifaffen kare ne, yana ganin Ibrahim kamar ya san da abinda ya xo dashi sai yahau gurani Ibrahim yana so yayi masa haushi na tura shi cikin gidansa na kulle. Na kalli ibarahim na dan masa murmushi sai naga yayi fuska ya bata rai, nace mu shiga cikin gida yanda muka saba hira, sai yace no, nanma ya isa. Na xo ne na ganki xan wuce gida yanxu daga masallacin juma’a nake, nace to nagode da ka xo ka ganni, sai yace ni kuwa daman ina so nayi miki wata Magana akan abubuwan da yake faruwa tsakanin axixa da mubarak bana so ki shiga maganar nan dai dana ga maganar tasa babu layi kawai dinbin son kai ne, da kuma mubarak ya aiko shi, na taka masa birki domin ya fito fili ne yace wai na rabu da axixa , kawai na kira masa willi dog ya bi Ibrahim a guje sai ga ibarhim a cikin ruwan sweeming pool din nan willi ma ya fada ya bishi. Ni kuwa me xan yi banda dariya na kwallawa kannena kira suka yo waje sai kyakyacewa muke, sallau mai gadi ne ya bani haushi hard a tahowa a guje ya rike willi dog, ya fito tsamo tsamo daga ruwa abin kunya, axixa da atika suka kwashe da dariya suka yi dariya har cikinsu yayi ciwo. Munnira tace aini sai  ranar nasan kare ashe yana da matukar amfani ai willi dog yayi min komai daya raraka Ibrahim.


 Wannan maganar da munnira ta fada ta likewa axixa a rai da tace  kare ashe yana da amfani axixa tace a ranta, hakika yana da amfani don na wulakanta ashruf har na xamar dashi kare saboda shi ne wulakantacciyar dabbb , daga karshe shi ya koyamin abinda ni bil adama ban sani ba, gashi kuma ya jefa ni cikin tashin hankali da rudani bani kadai ba harda iyayena da duk sauran al’ummar kasar nan masoyanmu, Nigeria xata shiga rudani shi yasa xata rikice kwata kwata duk a dalilin mutumin da na dauke shi a matsayin kare, sai nan da nan ta canja yayin da suka lura wani tunanin bacin rai ne ya rufe axixa, dariyar da take yi ta tsaya cak ranta yabaci lallai kare yana da amfani axixa ta fada a bayyane ba tare da ta san tunanin da take yi a xuciyarta ne ya fito fili ba. atika tace axixa meye? Ta dago ta kalle su taga sun daina hirar da suke yi sun tsaya suna kallonta. Ta yi murmushi tace me kuka gani? 

Munnira tace ji muka yi kina maimaita abinda nace ashe kare yana da amfani, sai muka ji kince lallai kare yana da amfani. Axixa ta yi shiru don ta dauka a xuciyarta ta fada ashe sunji, sanna tace a'a karan ne ya burge ni da yayiwa ibarahim haka shi ne nace lallai kare yana da amfani. Ta gyara xama don su ci gaba da hirarsu itama axixa ta basu labarin yadda suka yi da mubarak a waya, cikin dariya  ba tare da bacin rai ba axixa take labarinta. 


 Wannan al’amarin ya bawa atika da munnira mamaki, axixa ta yi musu ba xata bata nuna musu wata damuwa ba game da halin da take ciki. Suna hira suna cin kayan dadin da suka sussuyo a 911 suci kaxa suci kek, ga meat pie, alewowi da biscuit, juice ne kala kala a dan karamin firig dake dakin, ga kallon fim din ibro sun kunna, suna hira wasa da dariya sai dai sallah ce take tashinsu daga jirar da suke rangadawa. Kyamara ce a jakar munnira (auto) mai daukar hoto da kanta idan aka setata, don haka ‘yan matan suka dinga hotuna kala kala. Da alama hotunan nan nasu xasu yi kyau sosai gashi kayansu iridaya duka uku, kuma dukkansu suna cikin farin ciki da fara’a yau, ko me nene dalilin da duk suke jin farin ciki a ransu yau,? oho! 

Atika da munnira xamu iya cewa saboda ganin kawarsu axixa ta ware ta fara dawowa axixarsu tada.


 Da isha’I tayi suka yi sallar isha’I suka idar, da misalin karfe takwas na dare, sai atika da munnira suka fara shirye shiryen tafiya gida. Dukkansu sai suka ji babu dadi a ransu musamman ma axixa da ita kadai xasu tafi su bari a cikin wannan hali. Axixa  tace yanxu kuma sai yaushe xaku sake dawowa, sai na ganku ko? Koma ince har a sallameni? 


Munnira tace kai haba! Ai ni kullum xanxo tunda naga hanya don abbana daman baya hanawa muxo sai dai ko baban atika da kyar ya barta kullun taxo tunda daman shi ne yake hanamu xuwa yana ganin wai xamu tayar miki da hankali. Atika tace ai tunda jikinta ya yi sauki bata wannan damuwar mai xai hana kullum mu xo mu dinga yinin mata shima babana dauka ya yi ko xancen mubarak akayi sai xuciyarki ta hau bugawa amma gashi kin cirewa kanki damuwa kina hirarki. This is not the end of the world, dan haka axxy ki ci gaba da addu’a, farin ciki a rayuwarki yanxu kika fara. Sai axixa tace a ranta, ina wani farin ciki a rayuwata kuma nan gaba? Tunda na rabu da ashruf na rabu da farin cikin rayuwata ga kuma uwa uba abun xagi ya same ni yaya  na da jikoki. Suka yayyafa mayafansu suka rataya jakunkunansu suna cewa, gobe ma a nan xa mu wuni, jibi ma haka ko da munyi fashi to bai fi fashin kwana daya ba a sati, amma kullum xa mu dinga xuwa. Axixa taji dadi da wannan batu na kawayenta tace to Allah Ya kawo ku lafiya, kunga yau da muka yinin nan da nan naga dare yayi, amma idan ni kadai ce sai a dade dare bai yi ba to bani da abokin hira sai tunani. Munnira tace, Allah sarki axy baba ne ya hana mu xuwa kamar muyi kuka, gashi da muna dan gaisawa a waya muka buga muka ji a kashe sai abba ne yace ai daddy ne ya karbe wayar, axixa tace af, daman ina son ku bani dan kudi dan Allah, idan na tambayi daddy sai ya dinga yi min tambayoyi me xanyi dasu.


 Atika ta matso kusa da ita tace, ai kuwa muma sai mun tambaya me xa kiyi dasu? 

axxy karfa kice xaki bar garin nan ace mu muka baki kudin mota, axixa ta harareta tace idan xa ku bani ku bani, idan kuma baxa ku ba niba ku kara gaba dubu dari nake so kacal. Munnira ta kalli atika ta girgixa mata kai alamar a’a kar su bata. Munnira tace ko wata hanset din xaki siya? axixa tace eh, wai yaya xa’ayi kuyi tunanin xan gudu na je ina? 

Munnira ta xaro wayarta tace karbi tawa har layin ko kuma mu fita mu sayo miki sabon layi saboda a tawa su dr rislan  xa su iya damunki da kira, axixa ta ture hannun da take miko mata wayar tace kai ni bana son irin wannan takin, atika tace to tawa fa? 

Ta ciro daga jaka tace tawa dai kinsan mai kyau ce tafi ta munnira sabuwa ce kimanin naira dubu dari da arba’in mamanmu ta siyo min tsaraba wannan fitar da tayi America. Axixa tace duk bana son su, ni dai ku bani kudin kawai xan xabo irin wacce nake so da kaina. Atika tace to ba wayar xaki siya ba baxa mu bayar ba, ki gaya mana ko meye kike so xamu siyo miki, axixa ta fisgo jakar atika tayi sauri ta bude ta debe kudin dake ciki dukka, dubu hamsin ne cifcif yan dari biyar biyar, sannan ta jefa mata Jakarta. Munnira tace bari na fita babu ruwana atika ce ta bata kudi, atika ta wawuro jakar munnira ta jefawa axixa sannan ta rike munnira gam, tace axixa kwashe kudin Jakarta itama, mu biyu muka baki kudin a jakar munnira dubu talatin da biyar axixa ta kwashe sannan ta jefawa munnira Jakarta. 


 Ta rakasu har wajen motarsu munnira kara cewa axixa take, axxy wai dan Allah me xaki yi da kudin nan? Mu fa tsoro muke ji, ko kuma atika jeki gida ke kadai xan kwana a wajen axixa. Axixa tace ba xaki kwanar mun a daki ba sai dai idan  a dakin dr rislan kike so ki kwana to sai ki xo na raka ki office dinsa in ya tashi sai ku tafi gidansa tare, munnira tace rufa min asiri ai ban yi wayon da xanyi wannan tabarar ba, ni dai rokonki nake yi ki rufa mana asiri kar kiyi amfani da kudin na ta wata hanyar da xata xama tashin hankali wacce xa’xa ce mune.


 Axixa ta bata rai dan ganin munira ta dameta da xance daya, ta ce wai shin bani da hankali ne da xan gudu na je ina? Wa nake da shi daya wuce mahaifina? Kuna tunanin xan je wani waje na kyale shi, haba ya kuke neman ku bata min rai ne? nace muku akwai abunda xanyi da kudin kuma ba xai wuce na sayi waya ba don ma ba irin taku nake so ba da na karba. Akwai irin wacce nake so dan haka ku kyale ni na sake dan Allah, munnira ta rungume axixa tana cewa haba kawar ya mun yini lafiya kuma xamu yi rabuwar tsiya dan Allah axixa yi dan murmushi mana atika ma ta xo suka dinga xolayarta har saida tayi dariya sannan suka yi sallama akan gobe ma xasu xo su sake yinin mata in sha Allah, axixa na tsaye tana kallonsu har suka yi nisa kana ta juyo ta kama hanyar komawa dakinta, tana shiga dakin ko xama bata yi ba dr eltayyib ya shigo, don shi ne mai dutyn dare, dr eltayyib dan kasar indiya ne, yana da kirki sosai ga fara’a sun saba da axixa sosai suna hira. Bayan sun gaisa da axixa ya yi mata yan tambayoyi akan yanxu me take ji a jikinta kuma tana bacci yadda ya kamata? Axixa ta amsa da cewa babu abinda yake damunta, kuma da daddare tana yin bacci sosai, yayi yan rubuce rubucensa har xai fita axixa ta kirawo sunansa ya dawo fuskarsa  cike da murmushi yace yaya axixa? Axixa tace kayi hakuri da abinda xan fada maka ko xan dan takura ka, cikin jin dadi shima yau axixa xata nemi wani abu a wajensa yace kar kiji komai fadi bxan takura ba da yardarm Allah. axixa tadan yi murmushi tace nagode doctor, daman ba wani abu bane illa ina so ka bani motarka yanxu xani wani waje a gari xan suyo wani abu yanxu xan dawo. Dr eltayyib yayi dariya yace haba axixa baki da lafiya a kwance ma kike a asibiti amma ki fita gari? Haba aixa ko ni kika aika ai sai inje na suyo miki ko me nene. Amma ba xan barki ki fita baki da lafiya ba to idan kika gamu da babanki fa? Laifin ma gaba daya nawa ne nine likita in duty, sannan kuma da motata kika fita.


 Axixa tace a xuciyarta haka ne kuwa xan iya haduwa da idon sani, koma ban hadu da daddy ba tabbas kuma labara xai je masa an ga axixa, 

dr eltayyib ya cigaba da cewa ko ya kika gani axixa? Axixa ta nisa gami da dan..

.

Ya jama'a mai kuke gani?

Shin ya bata motar ko ya hana ta?

Ina kuke hasashen Aziza xata je?

Da gaske wani abun xata siyo ko kuma guduwa zata yi?

.

Ni Auwal mehafsa nace ya bata mota kuma babu inda xata taho sai waje na. 😊 

Comment yakara yawa nagofe sosai

[9/7, 7:56 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/7, 7:59 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT3

*16*

.

.

Axixa ta nisa gami dayin murmushi ta ce na gode kwarai da gaske likita daman handset  da layi nake   so in siyo. Dr eltayyib yayi dariya yace don handset ai ko a kusa da asibitin nan akwai wani sabon kantin waya babu irin wanda babu. Axixa ta sa hannu a jaka ta dauko kudi dubu tamanin da biyar ta mika wa dr eltayyib tace dr ga kudina dukka dubu tamanin da biyar ne don haka ka siyo min waya ta kamar dubu saba’in sai layin MTN shi kuwa bai fi dubu biyu ba saura dubu goma sha uku dukka kati (credit) xaka xuba min sannan irin  wayar da nake so mai dauke da redio a jikinta, kuma dan Allah doctor ko da ka gamu da dr rislan kada ka gaya masa xai iya sa daddy na ya sake karbe min kamar yadda aka karbe min ta da wai ni marar lafiya ce mutane xasu dameni.


 Dr eltayyib yayi murmushi yace ina ruwan waya da cuta? Tunda kina iya tafiya kiyi Magana ai xaki iya amsa wayar ma, axixa tace ai shi ne, dan Allah dr ni dai ina kara tuna maka wacce ta ke dauke da radio a jikinta. Dr eltayyib yayi dariya  yace ai ba xan manta ba lallai sauki ya samu har music kike so kiji don na san dai ba don jin labarai kike son radio ba, ko na siyo miki yar radio mai kaset (walkman)  ki ringa saka kaset kin ji? Axixa tace a’a doc ni dai handset mai radio kawai nake so. Eltayyib yace an gama sannan ya juya ya fito , axixa na xaune tana tunani taji wani sanyi a ranta don yau da ikon Allah xata yi Magana da mr Johnson ta ji halin da yake ciki na neman ashruf. Ta tuna af ashe number mr Johnson din tana cikin waccan wayar tata, sai taji wani makokon bakin ciki ya tokare ta, can ta tuna ai diary dinta inda take rubuta nambar wayoyin jama’a yana cikin akwatinta kuma da number mr Johnson a jiki. nan da nan ta tashi ta sauko daga kan gadon da take xaune ta jawo akwatin kayanta ta hau binciken diary. Ba tare da ta sha wahalar wargaxa kayanta ba ta ganshi ta xaro shi ta rufe akwatin ta jingina. Shigowar dr rislan ceta juyo da hankalinta ga duban bakin kofar dakin yayi sallama ta amsa ,  yace axixa kinga tunda safen nan dana fita ban dawo ba ko? Sai yanxu? 

Axixa ta ce babu komai ai tunda munnira kawarka ta dawo ba komai su duka suka tunstire da dariya. Dr rislan ya sake gyara tsayuwa yace kai axixa kin cika tsokana ashe munnira har  sun tafi tace xata je muyi sallama shi ne tayi tafiyarta ko? 

Ai nayi mata waya tace min waisu har sun tsufa a gida sai dai gobe xasu dawo su sake yinin miki.


 Axixa tace haka dai suka ce ko bata dawo don niba ai xata xo don ta ganka, dr rislan ya yi dariya yace don ke dai xata dawo, munnirar data ringa bata rai taki Magana fur number wayar tama saida nasha wahala sannan ta bani aiko kin san bata sona kiri kirir take nuna min. yanxu axxy yaya  xan yin a samu munnira xancen gaskiya nake yi miki fa babu wasa, kamar yadda kika sanni shekara da shekaru babu wata ‘ya mace da ta taba kwanta min lokaci duga irin yau yadda na ji munnira. Ita kuma sam bata ra’ayina. Dr rislan ya marairaicewa axixa. Ita kuwa axixa Allah Allah take yayi ya tafi kada dr eltayyib ya dawo daga sayo mata waya, don ta fuskanci duk abinda dr rilsn ya fadawa daddynta yana yarda, kuma dr rislan yana daya daga cikin masu hanata ta sake ko kallon settilight ya hana yaje ya katse ta dakinta wai kada taga wani fim din da xai tayar mata da hankali sai fim din ibro aka xo aka tule mata na bidiyo. To yanxu yasan an kwace mata waya, yaga ta siyo wata xai iya gayawa daddy ya sake kwacewa a xuciyar tace take Magana, can tace , kai abin daya dame ka ma da sauki ni da kasan me ke damuna  dabaka tare ni da xancen ka kamu da wata soyayyar shirme ba, dr rislan ya ci gaba da cewa ni dai na baki wuka na baki nama ga ni a hannunki, munnira ma na hannunki ki taimaka wa doc ka da ya kwanta ciwon rashin abar da yake so. Axixa ta yi dariya tace kai doc, harda su kwanciya ciwo? Ka kwantar da hankalinka ka samu karbuwa da munnira ba xa ta yadda ta bika office dinka ba harta shafe awa a can, kai dai kayi kokarin ku saba da ita, xata soka mu dai anan dakin banda xancenka babu abinda ta ke yi, kasanta miskila ce don haka da wuya ka ganeta sai a hankali. 


 Dadi marar misaltuwa ya lullube xuciyar dr rislan don shi har ya hau ya yarda da tsarin da axixa ta tsara shi, yace to Allah Ya taimake mu. Axixa tace amen doc. Ya ce to saida safe xan tafi gida dr dayyib ne ya canje ni ko ina ya shiga kuma ance an ganshi ya fita da mota ko ina ya tafi daga xuwansa kuma, shi dai da baya wasa da aikinsa su dr kabir sun fara koya masa kalula kenan. Axixa tace a’a dr eltayyib baya wasa da aikinsa yanxu nan ya fita daga nan sai dai maybe mantuwa yayi a gida ya koma suka yi sallama da dr rislan ya fita ya jawo mata kofar dakin ya rufe, bayan fitar dr rislan da kamar minti shida sai ga dr eltayyib ya shigo dakin. Axixa ta yi sauri ta tashi xaune daga kishingeden da take tayi masa murmushi kana tace sannu da xuwa doc. Ya yi murmushi ya amsa sannan ya karaso har gadon da take xaune ya mika ma ta ledar dake hannunsa ya yi shiru yana kallonta cikin murna da jin dadi axixa ta bude ledar daya miko mata, taga kwalin waya ne a cikin ledar ta dauko kwalin ta bude sai ko taga wata hadaddiyar waya sony Ericson p900 waya mai kyan gaske ruwan madara kalar jikinta. Kai wannan wayan tana da kyau  doc, axixa ta fada yayin da take daga wayar tana kallonta. Ta jawo cajar wayar itama ta hadu kamar yadda wayar ta hadu. Ta dago ta kalli dr eltayyib wanda har yanxu yana tsaye a kanta yana kallonta fuskarsa cike da murmushi.


 Ta ce dr amma wannan wayar tafi ta kudina, haba dr ga wahala da na saka ka bar aikinka ka fita kuma harda ciko? 

Nawa ka siyo min? 

y ace bb komai axixa, risitin yana ciki kuma idan katin wayar (credit) yakare kiyi min Magana xan sako miki wani, ki duba cikin wayar na saka miki sim card da credit din. Na ma fara yi miki charji a mota sai ki sata a charge saboda kinsan tana da cin charge saboda radio. Irin tawa ce sak sai ki gwada rediyon shima ki ji in tayi charji. Likita nagode madalla axixa ta fada cikin fara’a. dr yayi mata sallama yayin da yake bude kofa ya fice. Axixa ta sauko daga kan gado taje wajen soket ta jona wayar ta dawo kan kujera ta xauna da carbinta a hannu tana ta jan wuridai akan Allah Ya sa da ta bugawa mr Johnson yace ya ga ashruf ko kuma ya samu adireshinsa.


 Bayan ta tabbatar wayar tayi cajin da xai isheta yin Magana da mr Johnson sai ta mike taje ta dauko wayar ta hau gado ta bude dairy dinta ta duba lambar mr Johnson ta fara latsawa. Ba tare da tasha wahala ba taji wayar ta shiga harta fara ringing, gabanta ya yanke ya fadi dan fargabar jin amsar da mr Johnson xai bata akan ashruf. Can taji ya dauka yana cewa wata lamba daga Nigeria ina fatan xa’a min albishir da samun naira ne, cikin harshen turanci mr Johnson yake Magana. Ta tuntsure da dariya tace kai! Kai!! Mr johnson ina xaka da son kudi? Wato har ka san sunan kudaden kasashe daban daban, ka san sunan kudin Nigeria? Ai kuwa din samun naira xan yi maka. Axixa ce daga Nigeria take Magana.


 Yayi firgigi ya gyara xama, dan da a dan kishingide yake akan kujerar shakatawa. Ya ce axixa ya kuke? Naga lambar ba taki bace shi yasa ban gane ki ba, ta yi dariya tace wannan sabuwar lambata ce dan haka kayi sebin . mr Johnson yace to xan yi, ai na gwada wancan naji a kashe , ashe kin daina amfani da layin kenan? Axixa tace kwarai kuwa, to ya maganar ashruf ka samu labarinsa kuwa? 

Mr Johnson yayi dariya yace kwarai kuwa na samu labarin ashraf. Axixa ta gyara xama game da jin wani tsananin farin ciki a ranta wanda biro  da takarda ba xasu iya suffanta yadda taji ba, irin dunbin farin cikin daya lullube  mata xuciya. Ta nisa tace ai dole ne na jinjina maka mr Johnson na sanka a kwai cika aiki, bani labarin dan gidana. Mr johson ya tsuke baki yayin da xuciyar sa take yi masa tuni cewar a kyauta xaka bata labarin? Banga ta ajiye maka makudan kudi  a gefe ba, ko a kyauta xaka nemo mata ashraf din? Ko kai tsuntsu ne ba kudin jirgi xaka biya ka je ba? ya katse tunanin da yake yi yace mai girma axixa anga ashruf a America a wata babbar kasuwa dake Washington amma bani na ganshi ba. daya daga cikin ma’aikatanmu suka hadu, axixa taji wani dum a xuciyarta farin cikin daya lullubeta ya fara ribas. Ta ce mr Johnson kayi min dalla dalla na gane. Ina ashraf din yake yanxu? 

Mr Johnson yace gaskiya takamaimai bansan inda ashraf yake ba, kuma shi wanda ya hadu gaisawa suka yi kawai suka taba yar hira suka rabu. Ashraf din yace masa sarar kaya ya xo yi xai koma Jamaica. Ya tambayi lambar wayata dan ya daina samuna a wancan tsohon layin nawa, ma’aikacin namu yace bai san number taba.


 Kinga babu wata hanya da xansan inda ashraf yake yanxu, kinga idan nace yana Washington nayi karya tunda sare sare yake xuwa yi bama America kawai ba har sauran kasashe yana kaiwa Jamaica, sannan a Jamaica baya garin da na sani, sannan number waya ta daya sanni da ita da yanxu ba da ita nake amfani ba, shi kuma bai bayar da tasa ba don haka axixa sai dai ince miki banga ashraf ba.


 Hawaye mai wuyar fita ne ya ketowa axixa, ta rike kai ta runtse ido ji take daman ba a halicce taba, ta tsani xmanta a duniya gara ace tana kwance a kabarinta da jin wannan bayani da mr Johnson yace, yace ya naji kin yi shiru ne axixa wai dan Allah na tambaye ki? Neman ashraf din me kike yi ne? ko ya yi miki wata yar damfara ce kinsan shi talaka ya iya butulci ka jawoshi jikinka ya cuce ka, bayan dimbin kudin da mahaifinki ya bashi bai gode ba saida ya kwashe muku wani abu ne ko kuma………….. 

axixa ta daka tsawa a cikin fushi tace ya isa haka mr Johnson, wannan duk bai shafeka ba, ba dole ne ka ji me yasa nake neman ashraf ba, kai ka fini sanin ashraf tunda kake da ashraf ya taba yi maka sata ko damfara? 

Haba mr Johnson karka dinga manta alheri mana. 

Bana neman ashraf don wani mugun abu da ya yi kin sai don alheri, ni dai ka nemo min ashraf in har xaka iya ni kuma xan biyaka ko nawa kake so muddin kayi alkwarin gano inda yake. Ba sai ka kawo shi Nigeria ba kawai kana ganinsa ka bugomin waya muyii Magana dashi shike nan ka ci kudinka. Kafin ka tafi nemansa xan turo maka da rabin kudin, idan ka nemoshi sai na cika maka cikon kudinka. Ya kyalkyale da dariyar dadi ya mike tsaye yana xaxxagayawa dake a bakin ruwa yake a kasarsu Croatia yace mai girma axixa kinyi Magana dama kece baki yi saurin cemin ga masu laushi ba, masu laushi sune dollars. Da tuni baki ga ashraf ba. aida a ranar da wanda yaga ashraf din nan yace min yaga ashraf a waje kaxa da a lokacin xanyi sauri na je America dan idan nasa police din da suke da duty a kasuwar a ranar sunsan waye ya shiga kasuwar daga ina yake ina xaije, da na nemo miki ashraf tuni.


 Haushin mr Johnson ya kamata ya sake lullube xuciyarta tace a ranta wannan ina ga ko ruwan gidansa uwarsa ta sha sai ta biya shi, bashi da mutunci akan kudi nanfa tafara jin muryar mr Johnson tangarai, yaji batun kudi. Ya ce mai girma axixa xan nemo miki ashraf a kan kudi dallar dubu dari sai ki turomin da rabi dalar dubu hamsin kenan ta account dina xanyi miki sending text din account number, ni kuma xan bar duk abinda nake yi na nemo miki ashraf. Xanje Jamaica tsohon gidansu kinga baxan rasa ko mutum daya da xai san wane gari suka koma ba da adireshinsu, ko number wayar su ko? 

Axixa tace a ranta da ka san da haka kaki xuwa sai yanxu da ka ji kudi. Shi dai mr Johnson kintato kudin yayi ya gayawa axixa don idan ta nemi ragi ya rage mata saisu daidaita yadda yake tunanin xai samu, amma ga mamakin sa sai yaji ta yarda. Axixa tace mr Johnson na yadda xan baka dollar dubu dari ka nemo min ashraf amma kada ka wuce kwana goma xuwa goma sha uku daga yau, sannan kayi min sanding account nuber taka ni kuma ranar litinin dake yau asabar babu aiki litinin xan turo maka da rabin kaje ka nemo min ashraf , kana ganinsa ka kirani a waya ka bani ashraf muyi Magana shi kenan ka cika aikinka, cikon kuma xan turo maka. 


 Dariya yake kyalkyalewa dadi yayi masa yawa har ya kasa Magana, axixa ta kashe wayarta cikin sanyin jiki ta sulale ta kwanta kan gadonta tana mai tasanin jin takaici, yayin da kuka ya kece mata mai dauke da tsananin tausayi ya kecewa axixa babu abinda take ji a ranta sai tsananin bakin ciki da tsanar ci gaba da rayuwa a duniya . Wayar tace tayi ringin cikin mamaki waye yasan numberta har aka fara kiranta, kasancewar ta duba taga ba mr Johnson bane number MTN ceta Nigeria , sai ta latsa cikin sanyin murya tace hello. A harshen turanci taji ance ah axixa har kin yi bacci ne? ta yi shiru bata bada amsa ba don bata san ko waye ba, bata gane muryar ba balle number. Ya sake cewa na kira ki ne don naji ko wayar da layin suna yi sosai babu matsala? Axixa batace komai ba dai tana sauraron mai Magana yayi dariya yace axixa kinki Magana lafiyarki kalau kuwa? Dr eltayyib ne ke Magana, ta yi wata doguwar ajiyar xuciya kana tace doc kai ne? ban gane ka ba na yi mamakin waye yake kirana bayan yanxun nan na sayi layin ni kuma bansan numberka ba, waya tana lafiya kalau nagode doc saida safe. Ta yi sauri ta katse wayar ba tare da ta barshi ya sake cewa wani abu ba, ta kifa kai taci gaba da rusa kukanta, can taji wayar ta sake yin kara kadan ta jawo wayar ta duba sai taga text message ne ya shigo, ta bude inbox don ta karanta cike da mamakin kuma waye yayi mata message taga wasu zakakan kalmomin soyayya ne daga kasar ya rubuta sunansa dr eltayyib. Taja wani dogon tsaki gami da kashe wayar kwata kwata ma. Ta duro daga kan gado taje ta saka wayar a caji tasa mukulli ta datse kofar dakin, tasa rigar baccinta ta kashe fitilar sai abinda ya dameta a ranta cikin bargon nan nata xugi da radadin bakin ciki ya sake dawo mata damuwa da takaici fiye da na da suka dawoma xuciyarta tace bana mantawa da mahaliccina, Allah KaiKa halicce ni Ka jefani a cikin halin da nake ciki, Kai ne kuma xaKa fitar dani, Allah nagode maKa, Allah Kaine abin godiya. Yayin da ta fara jin duk wata damuwa tana gushewa daga xuciyrta, domin kuka ba xaiyi mata magani ba, Allah(SWT) Shi ne babban maganin duk wata masifa da bala’i.


 Allah sarki, axixa da tunanin ashraf ta kwanta don haka da mafarkin sa ta kwana, mafarki mai dadi wanda ya sata farka da farin ciki matukar farin ciki kuwa taji ana kiran sallar assalatu. Tayi salati ta mike don yin sallar asuba, bayan ta idar ne ta xauna tana laxumi da yan addu’o’inta, yanxu addu’ar axixa bata wuce ta roki abu uku  xuwa hudu, na farko tayiwa mahaifiyarta da ta rasu addu’ar nema mata gafara a wajen mahaliccinta da sauran musulman da suka rigamu gidan gaskiya. na biyu kuma ta nemawa mahaifinta samun Karin lafiya da Karin arxiki da kuma Ubangiji Ya bashi nasara akan duk abinda ya sa a gaba na alheri ya dora shi akan makiyansa masu son suga bayansa ya saya ci gaba da kyawawan halayensa su bishi har kabarinsa. Sai kuma wannan mawuyancin hali da take ciki Allah Ya yassare mata ya fitar da ita daga tashin hankalin nan da take ciki na bangarorin nan guda biyu, na daya sharrin da alhaji isah yake shirin ya jefasu a ciki da kuma yadda xata tari mahaifinta tace ashraf ne yayi mata ciki ba mubarak ba. tasan wannan Magana ba karamar batawa mahaifinta rai xai yi ba.


 Basu da ta cewa kuma a kotu tunda bamu da gaskiya, tunda babu wanda ya san ashraf don haka cewa xa a yi karya ake yiwa ashraf sai dai in uba ne ya yiwa yarsa ciki da gaske ne kenan xancen alhaji isah, axixa tace a ranta dole nayi shiru mu tayin shari’a da mubarak akan rashin gaskiya kenan, idan ashraf bai xo ba, ba xan taba cewa ba mubarak ba ne. haka axixa ta kasance ta yi kuka tayi addu’a har gari yayi haske tangarai. Ta shiga bandaki tayi wanka tayi brush taxo ta shirya tsaf ta ci kwalliyarta.ta bude mukullin kofar dakin don likitoci da nurses xasu fara xagaye don duba mararsa lafiya. Ta koma kan gado ta jinginar da kanta a jikin filo taci gaba da tunanin kywawawan mafarkin abin kaunarta ashraf da ta kwana tana yi a daren jiya. Ashraf ne sosai ta gani suna waje mai kyau suna hirar soyayya. Hakika  wannan mafarki ba karamin fami yayiwa axixa a xuciyar taba, ya sake taso mata da dankareriyar soyayyar da take yiwa ashraf a ranta ta ji dama su hadu mana kamar yadda ta ganshi a mafarki suna tare a yanxu da take tsananin nemansa.


 Xuciyarta tace gaskiya mutum ba a bin wulakantawa ba ne ko yaya ya ke Allah ne Ya halicce shi,kuma kowa da baiwar da Allah Ya yi masa, mai kudi da talaka duk daya ne a wajen mahaliccinsa, sai dai wanda Ya fi tsoron Allah shi yafi matsayi ranar gobe kiyama. 

Na wulakanta ashraf don na tsani talaka ina ganin talaka shi ya so ya zama talaka ni a haukata don bansan talauci ba, ban taba dandana shi ba, sai da Allah Ya nuna min ishara nayi kwana ashirin da hudu a cikin rayuwar talauci na dandana. 


Yau ga shi dan talaka da da dallar dubu dari ina neman sa na rasa shi, ashraf yau ya fi min kudi wuyar samu. Da kudin nawa na rasa ashraf din dana ke kiransa da wulakantacciyar dabba, yau shi ya jefa ni da mahaifi na cikin damuwa, saboda talaka guda daya wanda da ban dauke shi mutum ba, na yi kuskure nayi kuskure! Nayi nadama, na koyi darasi a duniya yanzu babu wani mutum baya ga mahaifina wanda nake so da tsananin kauna a raina irin ashraf talaka likis na mace a sonsa, wannan duk ishara ce Allah Ya nuna min. Ba a wasa da ikon Allah, Allah natuba ni ba komai ba ce illa kaskantacciyar baiwarKa bani da komai ba ni da kowa bansan komai ba kuma sai abinda Ka sanar da ni ya Allah aziza tana fadi a zuci Wani lokaci a bayyane tana hawaye tana yiwa Allah kirari saboda Ya nuna ikonSa akanta, ya nuna mulkin Sa a kanta, Ya nuna isarSa a kan ta, don ita bata isa ba, babu mulkin nan babu takama duk sun kare. Haka aziza ta kasance cikin nadama cikin addu'a wani wani lokaci ta yi kuka. 


Ranar litinin tayiwa atika waya ta ce taje dakinta cikin durowarta ta dauko mata cek dinta na bankunan da take ajiyar kudadenta. Tayi mata gargadi kada tabari kada ta bari kowa ya sani musamman mahaifinta. Idan zasu zo su taho mata da shi, don kusan kullum sai atika da munnira sunzo sun yinin mata. Bayan sun zo tayi musu wayo ta sulale ta ce musu tana zuwa, ta tafi ta hau taxi taje banki tayi cuku cuku taturawa Mr Johnson wadannan makudan kudi har dalar dubu hamsin rabin kudin da suka yi za a tura masa, sannan tadawo asibiti suka ci gaba da hirarsu dasu atika ba tare da sunsan ina taje ba. 


Kwanci tashi yau saura kwana  biyu daga CIKIN KWANA ASHIRIN DA HUDU da Alhaji isah ya daukar wa Alhaji Ahmad ya bashi kujerarsa ko ya fitar da mujallun nan, kuma kirmisisi har yau Alhaji isah bai ji sako daga wajen Alhaji Ahmad ba. Wannan abu ya bawa Alhaji Isah mamaki don shi a tunaninsa Alhaji Ahmad xai tsorata yayi sauri ya janye ya bar masa, amma yaga ko gexau.  Ransa ya baci sosai ya sake lasar takobinsa kuwa sai ya yi masa rashin mutumci da sai dai kowa ya rasa a tsakanin su sai ya masa cin mutumcinmutumci Idan kwana ashirin da hudun nan ta cika be ji komai da ga bakin Alhaji Ahmad ba. Mujallu Kuwa ana ta ci gaba da bubbuga su da yare daban daban don kowacce kabila ta gane sakon da ake son a isar. Hankalin aziza ya sake tashi ita kadai take jin abinda yake damunta azuciyarta. Kullum kunnenta a sauraron radio dake wayarta ko taji yo abinda ke gudana a kasar amma har yau bata ji wani labari ba da ya dibanci rigimarsu da Alhaji Isah, kullum cikin dare sai tayiwa Mr Johnson waya amma bata samunsa, ko taji a kashe, ko kuma tayi ta ringing ba a dauka ba. Hankalin aziza ya kara tashi tace a ranta me Mr Johnson yake shirin yi min ne?  Na bashi rabin kudi har yau bamu yi magana ba na ji ko kudin ya sameshi ko bai same shi ba ma, yana Jamaica koma a gida yayi kwanciyarsa akan kudin yaki zuwa oho. Gashi saura kwana biyu cif a fitar da mujallun nan sai shiga kotu kuma. 


A kotu mune ba mu da gaskiya domin Mubarak bai yi min ciki ba ashraf ne, na rasa ashraf din kuma. Ta rushe da kuka, tayi ta huta ta ci gaba aikin ke nan ga babu mai lallashin ta don ita kadai take kebewa ba tare da kowa ya ganta ba. Dadinta ma, bata mantawa da mahaliccin ta Bata gajiya da yin addu'a, don komai yayi tsanani maganin sa Allah, kuma addu'a ita ce babbar makamin mumini, salihan bayi basa bin yan tsubbu da bokaye idan masifa ta same su daga hannu sama suke suna neman sauki a wajen Ubangijin su. 


KWANA ASHIRIN DA HUDU. 

kwana ashirin da hudu ta cika, da misalin karfe bakwai na safe.......... 

.

.

.

To en uwa, da patar ba muna karanta littapin bane kawai domin nishadantar wa kawai, mu dage mu ilmantu daga darasin da ke cikin sa, Allah Ya sa mu dace.

Aamiin.

.


 Sannan ku ba Aziza shawara ya xatayi?

Comment dinku yana burgeni

[9/12, 5:32 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4 

*27* 

Abinci kala kala aka shiryawa baiki, amma Hajiya Fatima mahaifiyar Ashruf kinci tayi saboda taga wasu bakin mutane magana taki ta amsa. Mijinta sai bayani yake cewar bata magana ai sai dai wani lokaci idan abin ya tashi take kiran sunan Zubaida ko Takaka ta ce ina suke? Sai da aka kaisu taa babu kowa sai ita sai mijinta ya lallabata sannan ta zauna ta ci abinci. Ya sa ta tayi wanka ta zo ta kwanta yini tayi tana bacci saboda kwana sukayi a zauce a jirgi. 

 Washegari ranar juma’a kenan ta:I karfe tara na safe jama’a suke tururuwar zuwa kotu don kawai aga Alhaji Isa saboda za a fito da shi zuwa kotu daga wajen ‘yan sandan da yaka a tsare dan yin shari’a da su Ashruf Tururuwar jama’a daga wasu garuruwan ma zuwa ake. Su Alhaji Sadam sun hallara kakaf dinsu a gidan Alh. Ahmad tun karfe tara, tara da rabi suka dunguma cikin motocinsu zuwa babbar kotu. Su Alhaji Ahmed sunyi matukar mamakin ganin dandazon jama’ar da suka yo ca adan Alhaji Ahmed suna daga masa hunnu suna Allah ya kiyayeka sai mai gaskiya, sai kayi shugaban kasa. Dakyar da sudin goshi 

Yan sanda da bodyguards dinsa suka kareshi saboda jama’a kowa yana so ya yi hannu da shi kafin su shiga Alhaji Elmustapha ya ce “Muddin suka shiga ciki da matarsa taga takaka tabbas za ta rikice ta hana a ara aiwatar da shari’ar don haka ya ce ba ta rikice ta hana a fara aiwatar da shari’ar don haka ya ce ba za su shiga ciki ba. Karfe goma da minti uku babban alkali mai shari’a (Chief Judge) ya shigo shi da sauran mataimakansa masu shari’a kowa ya mike don girmamwa sai da lkali mai shari’a ya zauna sannan kowa ya zauna. Allkali ya bawa magatakarda izini ya karanta shari’a, magatakarda ya fara karanto abinda yasa mai kasa Alhaji Elmustapha yake karar Alhaji Isa Elyakub. Shigowar Alhaji Isa ce tasa kowa ya waiga yana kallon ikon Allah. Alhaji Isa ne sanye da wata riga ‘yar shara fara wacce wuya tasa tayi bakikirin kamar wani tsohon mahaukaci. Ankwa ce a sakale a hannayensa da kafafuwansa. ‘Yan sanda biyu ne suke biye da shi suka kaishi cikin dan kewayen da wandanda zasu fafata shari’a suke tsayawa a gaban alkali. Alhaji Isa Elyakub ya kasance yau yana cikin wani hali na tsananin bakin ciki da takaici, kamar yadda ya saba suka jama’a a irin wannan yanayi na kunci. Babu haushin wanda yake ji sai Ashruf saboda shi ne ummul aba’isin tona masa asiri har ta Kaishi ga sawa a kashe minister. Fada yake da zaga-zage tsakaninsa da Allah. Wanda wannan ma babban laifi ne daya sabawa dok kotu, cewa yake ‘’karya ake min dukka sharri ne, waye Ashuruf da zaice nine na kwashe kudin mahaifinsa shekaru ashirin da hudu shi kansa yaron baifi shekara talatin ba yaushe ya ganni sanda na turasu-a mota kuma yaya basu mutu ba? Alkali mai shari’a yana ta buga guduma akan Alhaji Isa Elyakub yayi shiru amma yaki.

Alhaji ahmed ya kira elyakubu ya kira dan sanda day ya ce ya shiga wani daki da yeke wajen kotun ya shigi da Alhaji Elmustapha. Waigawar nan da alhaji isa zaiyi sai ya hango alhaji elmustapha ya tunkaroshi akan kekensa na guragu nan kaji bakin alhaji isa elyakubu ya mutu rumus ya rasa ta cewa nan aka hau kallon  kallo to fa!!! Alkali mai shari’a ya umarci Alhaji Elmustapha ya fadi dalilin da yake darar Alhaji isa Elyakub da kansa don ya ji da kunnensa Alhaji Elmustapha ya fara da bismilla sannan ya fara zuba dogon turanci kai ka ce bush ne shugaban kasar America da kansa kasancewar zaman da ya yi America ya sa ya fi jin turanci har kamar fiye da yaransa hausa. Ya yi dalla dalla yana fadar labarinsa yana fadar kwanan watan da lokacin da kuma lambobin takardunsa na gidaje, na motoci da account number sa turkashi! Alhaji isa ya rasa ta cewa alkali ya juya alkali alhaji isa ya ce ‘’to kaji fa abinda ya fada’’. Alhaji isa ya yi tsaki ya kawar da kai ya ce ‘’duk karya yake min duk shirri ne makiyana suka yi hayarsu don agan na tozarta ni ba nine takaka ba, idan kuma sunce nine waye shaidarsu a sanda abin ya faru?”

Alhaji Elmustapha ya ce “bani da shaida sai allah, allah shi ne shaidata sannan matata wacce nace tunda hatsarin ya faru take tabin hankali bau sunnan wanda take iya tunawa daga Zubaida ‘yarta da ta rasu sai takaka ita kadai ta isa shaida idan shi ne takaka zata nun shi”. Alkali mai shari’a ya ce ‘’aje a shigo da ita’’. Dan sanda ya fita ya taho da ita. Hajiya fatima ta bawa duk wani mai imani da yake zaune a kotun nan tausayi da daga gannin ta tasha wuta a rayuwarta. Tazo gaban mijinta ta tsaya; alkali mai shari’a ya ce “ mallama ki fada mana cikakken sunnaki sannan ki fada mana abinda kika sa ni game da alhaji isa elyajib’’ . ta yi shiru kamar bada ita yake magana ba bata kalli inda yake ba balle ta saurari abinda yake cewa balle har ta bashi amsa alhaji elmustapha ya ce ‘’ai bata gane magana kuma ita bata magana sai jifa jifa’’. Alhaji elmustapha ya kama hannun matarsa ya jata har gaban Takaka cikin harwshen larabci ya ce “Fatima waye wannan karon farko ta daga kai ta kalli Takaka”. Cikin harrshen turanci ya sake cewa suka dau dan lkacin suna kallon juna. Yau ne rana ta farko da Fatima ta fara tuna wani abu a kwakwalwarta don tunda suka yi hatsarin nan bata taba tuna wani abu a suka yi hatsarin nan taba tata tuna wani abu a kwakwalwarta ba ita dai gata nan ce kawai. Ta rike kai sai jiri take ji yayin da take kokain tuno wani abu da ta sa ni da. Ta sake dagowa ta kalli Takaka bakinta ya hau karkarwa ha’waye ya dinga zubowa daga idanuwan tana nuna shi da hannu tana ja da baya can ta kwalla ihu ta rirrike mijinta tana magana cikin harshen turanci ta ce “Malam boyeni, boyeni”. Takaka ya sake zazzare mata jajayen idanuwan nana nasa babu abinda a tuna sai lokacin da aka kawo shi farkon zuwansa gidansu haka ya dinga zare ido yana kallonsu wai shi bakauye yazo yaga America.. Ta fara ihu tana cewa “Wannan ne, wanann ne”. Ta ci gaba da kallon Takaka daga karshe ta tunano lokacin da Takaka ya kaisu bakin rami ya ajiyesu a cikin mota ya ce zaije ya yi fitsari ya fito daga cikin motar ya tafi yana zuge zugen tazuge koda ya yi fito sai ga wata katuwar tirela ta tunkarosu ta angaza motarsu suka fara wuwwuntsilawa. Sai ko ta sake rafsa wani ihu ta fadi kasa tana cewa “Takaka ne ya turamu a rami ni da Zubaida ta yi ta surutai tana kara mijinta ya gurgur da kekensa wajen da take kwance ya fara yi mata magana ya rukota ya tasheta zaune sannan ta tsagaita da ihun da take. Tausayinta ya sa jama hawaye musamman Aziza da kuka ta fashe don tausayin mahaifiya masoyinta. Nan take Allah (S.W.T) ya ma tsa Alhaji Isa Elyakub da farko ya fara kyalkyalewa da dariya yayi ta dariya kamara tabab sai ya fara fada da kansa abin kamar almara ya fadi duk abinda ya faru tsakaninsa da Alhaji Elmustapha har yadda ya yi niyyar ya hallakar da su a tunaninsa ya dauka sun dade da mutawa ya fadi dalla dalla hanyar da yabi ya kwashe takardun dukiyar Alhaji Elmustapha ya ce har yanzu kanfanonin da Alhaji Elmustapha ya zuba hannayen jari yana nan yana karbar riba sai dai wasu an canja sunayen. Daya bayan daya dinga fadar ribar da suke bashi a shekara. Na America daban wani a kasar England wasu a Germany da France kuma da sunan Elmustapha a takardun har yanzu. 

 Alhaji Elmustapha ya nem kotu da ta fitar masa da hakkinsa dan iyalansa na musifar da Alhaji Isa Elyakub (Takaka) ya jefa su na niyyar halakar da su da ya yi sannan ya roki kotu data karbar masa dukiyoyinsa da Takaka ya kwashe masa ya kara da cewa ayi lissafin ribar da bankuna da kamfanonin da ya zuba hannayen jari suka bawa Takaka har tsawon shekaru ashirin da hudu ya biya shi sannan ya bashi kudin motoci da gidaje da ya sayar shima ya biya kudin. Alkali mai shari’a daga karshe ya yi na’am da wannan koke na Elmustapha ya yi masa alkawarin zasu lissafa yadda wadannan kudade suke za a biya shi. Nan da kwana ashirin da hudu su dawo don ci gaba da wannan shari’a. alkali ya tashi ya fita ‘yan sanda suka sa Alhaji Isa a gaba suka fita da shi zuwa inda yake a tsare. Su alhaji ahmed ma suka nufi gida, Aziza da munira da atika suan fitowa suka doshi motar da suka zo a ciki a motar aziza ce ke tukawa suna tafe suna hira yau farin ciki ne a zuciyarsu ganin allah ya tonawa alhaji isa elyakub asiri. Musamman aziza tayi matukar murna ganin ashrug dinta zai sami nutsuwan a zuciyarsa ga dukiyarsu zata dawo babu wani abu dayake damun aziza a yanzu banda wata biza da ya rasa, kawai don tace idan ya tafi kada ya dawo shi ne yaki dawowa.

Aziza bata tsaya a ko ina ba sai a gidan su atika. Atika ta ce dama a gidanku muka sauka mun yi da mahmud sa’ad zaije can ya sameni. Dr. Rislan ma zaije can wajen munira’’ aziza ta ce wato acan kuke labewa kuna zance ko ya saina gayawa su mama ince kunyi samiri ku na boye musu’’. Atika ta ce ‘’dan allah aziza yi hakuri karki fadawa miji su aure zasu yi min’’.Aziza ta ce kuma ke be auren yayan nawa zaki ba kenan?’’

Atika ta ce ‘’Ba haka ba ne, kin gane ina so in gama darantar guy din ne in san how much loves me don ina sona auri miji mai tsananin sona fiye da yadda nake sonsa. Na lura da hakan Mahmu na sona amma ina so in sake sanin hakan”. Munnira ta nisa ta ce “Ke kina ba da wata hujja marar kan gado so ai da ya ne, ni abinda yasa bana so a gida a san Doctor Rislan shine don in koyi zurfin ciki irin na Aziza sai soyayyarmu ta yi nisa ta nuna daf da mun gama shirin yin aure sai ince Abba, Umma ga mijina sai suyi ta mamaki”. Su duka suka kyalkyale da dariya Aziza ta ce “Ni dai Mama nake so in gani idan zaku tafi gidan mu ku dauki motarku. Tafi”. 

 Suka firfito daga motar suka nufi cikin gida, suna shiga ko zama basu yi ba sai ga Mama Atika ta yi sallama ta shigo Aziza ta tafi ta rungumeta tana shagwaba kamar mai shirin fashewa da kuka tana cewa “Mama gurinki fa nazo Allah Mama abin yana ta kara damuna”. Tayi muyarshi ta shafa mata kai ta ce “Haba Aziza ‘yar Mama kada abin ya dameki zo muje daki ki gaya min”. Atika da Munnira wadanda kansu ya daure basu gane kus kus din da Aziza take yi da Mama ba suka yi wuf suma suka bisu cikin daki wai su ma sai sunji meye yake damun Aziza. Maman Atika datse dakin taja hannaun Aziza zuwa kan gado suka zauna ta ce “Ya ya aka yi ne Aziza?”

 Cikin shagwaba Aziza ta ce “Mama kinga Ashruf shiru yaki zuwa babansa ya ce wai biza ce bai samu ba shi ya sa bai zo ba amma ni nasan ba haka bane don karya zo ya ganni ne kawai. Dazu muna fitowa daga kotu ya bugowa dady na waya yana tambayar ya ya shari’ar ya ce a bawa dadynsa suyi magana aka bashi ya ce a bawa Baba daga karshe ya ce a bawa abban Munnira Allah Mama baice ina nake ba”. Tayi narai narai da ido zata yi kuka. Mama ta yi murmushi ta ce “Haba Aziza kada kiyi kuka ki kwantar da hankalinki ki barni da case din zanyi miki maganin matasalarki, da kinyi kuka a rashin Ashruf yanzu ma kiyi kuka ai abin zai yi miki yawa. Ashruf ma yana sonki sosai tsoronki yake shi ya sa bai’ce ina kike ba tunda ga yadda kuka rabu”. Atika ce take kwankwasa musu kofa Mama ta ce “Allah mai kwakwasa kofar nan idan na bude zaki yi kuka”. Atika ta yi dariya ta ce “Mama ni ba labarinku zanji ba wayar Aziza na kawo mata ta barta a falo dadynta ne yake so ya yi magana da ita”. Aziza ta mike da sauri ta bude kofar ta karbi wayar. Dadynta ne ya ce “Hallo Azizyn dady kina ina?”

 Ta langwabe kai ta ce “Ina gidan su Atika dad”. 

 Ya ce maza kizo kiga wani abin al’ajabi yanzun nan fa”. Ta yi tsalle ta ce Dady fadamin kafin in zo”.

 Ya ce “A’a sai kinzo zaki gani”. Ya kashe waya. 

Ta zari dankwalinta da sauri ta ce da Maman Atika “Mama zan dawo da yamma dady ne ya ce inzo yanzu”. Ta ce “To sai kinzo.” Aziza ta fita da sauri Atika da Munnira suma suka biyota daman su haka suke so, suka duru a mota sai life camp inguwar su Aziza. Aziza da sauri ko rufe mota bata yi ba ta fada cikin gida. A babban falo ta iske babanta a zaune da wata farar mata mai kyawun gaske a gefe a zaune akan kujera. Aziza ta yi musu sallama ta tafi ta durkusa a kusa da babanta ta ce “Dady gani nuna min abin al’ajabi”. Ya ce “Haba Aziza kamar wata ‘yar karamar yarinya ki gaishe da bakuwa mana”. Aziza ta ce “Sannu ina yini”. Bakuwa ta yi murmushi tace “Ban karbi gaisuwarki ba daga nan, zo nan mana Aziza”. 

Aziza taji mamaki ya rufe ta ganin yadda matar take yi mata magana kamar ta santa. Ta taso tazo ta zauna a kusa da matar ta mika mata hannu saka gaisa, matar ta girgiza kai alamar tausayi ta ce “Allah sarki Aziza” Nan da nan kuma idanuwanta suka kawo hawaye. Aziza ta sake shiga cikin duhu wacece wannan har take kokarin ta fashe mata da kuka?

Alhaji Ahmed ya yi murmushi ya ce “Aziza sake kallon ta sosai zaki gane ta kinsanta fa”. Karon farko Aziza ta yiwa matar nan kallon nutsuwa sosai ta kalleta sai kuwa ta tuno fuskar kanwar mahaifiyarta ce uwa daya uba daya suke da mahaifyarta kamarsu daya sak da mahaifiyar Aziza. “Aunty Sharifa sunanta. Rabon da Aziza ta sake ganita tun tana shekaru shida a lokacin da mahaifiyarta ta rasu. A shekarar kuma aka yiwa Anti Sharifa aure a Lagos mijinta yake basu shekara a Lagos ba aka turashi kasar Germany suka koma can da zama. Bayan shekaru biyar da rasuwar Haijya Fatima mahaifiyar Aziza Allah Ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wato kakar Aziza daman tuntuni mahaifinsu ya rasu. Anti Sharifa ta zo Nigeria a lokacin rasuwar amma Allah bai yi sun hadu da Aziza a guru ba wajen rasuwar don su ‘yan guru ne. lokacin Aziza tana London tana sakandire bata zo ba. Don haka Aziza tuni ta manta da yadda fusakar Anti Sharifa take balle kuma ita Anti Sharifa ba zata gane Aziza ba. Amma me jini yasa kamarsu day kamar anti sharifa kaki tayi na Aziza domin futik kamar su daya saboda Aziza da mahaifiyarta Hajiya Fatima ta yi kama itama kuwa Anti Sharifa da yayarta tayi kama Hajiya Fatima soboda haka ne suka yi kama daya. Da can su Aziza suna da lambar wayarta sukan yi waya amma daga baya su Anti Shaifa suka tashi daga Germany zuwa India basu sake waya da su Aziza ba kasancewar suma lambar da suka bata sun sake tunda suka dawo Abuja don da su Aziza a Lagos suke suma. Shekara guda kenan da rasuwar mai gidan Anti Shairfa. Tayi waya mai duguri garin su mijin tasanarwa iyayensa da ‘yan uwansa suka dunguma can aka bunneshi har tafita daga takaba aka raba gado ‘yan uwansa suka dawo ita kuma ta kaura Saudia ta zauna a can ta ci gaba da yin ibadunta a kasa mai tsarki saboda tsananin bakin cikin rayuwa. Taga me zata zo gida Nigeria ta yi bayan bata da uwa balle uba, ga ‘yar uwarta Fatima wacce su biyu mahaifansu suka haifa ta rasu, mininta mai ji da ita ya rasu basu da da ko daya. Tana Saudiya ne sai ta fara tunanin ‘yar uwarta Aziza me zai hana ta zo ta ga Aziza ‘yarta ko saji dan sanyi dukkaninsu. Shine ta zo Nigeria musamman don Aziza. 

Cikin rawar murya Aziza ta ce “Aunty Sarifa ce?” 

Sharifa ta fara zubar da hawaye ta ce “Aziza nice”. Sai suka rungume juna suka kankame junansu saboda tsananin murna da jin dadi su duka kuka suke tamkar kwayar marigayiya. Alhaji Ahmed ma ji yake tamkar a yau mai dakinsa ta rasu saboda ganin kanwarta ta juye sak Fatimarsa kamarsu, kallonsu, maganarsu tafiyarsu duk iri daya. Allahu akbar hawaye ya ji taf a cike a idanuwansa shima da yake zaune yana kallonsu sun rungume juna suna kaku. Alhaji Ahmed ya yi karfin hali ya dinga lallashinsu sannan suka tsagaita da kukan. Daga karshe ya ce da Aziza ta kaita daki da kayanta ta huta saboda tun safe tazo take zaman jiransu. Aziza da Aunty Sharifa suka hau sama dakin Aziza a nan suka iske Munnaira da Atika suna ganin Aunty Sharifa sai da gabansu ya yanke ya fadi saboda sunga kamarta da marigaiya Maman Aziza har kamar ta baci, tun kafin Aziza ta gabatar da Aunty Sharifa ga kawayenta Munnira ta ce “Amma wannan kanwar Mummy ce ko?” Aziza ta ce “Anty Sharifa ce wacca nake baku labarinta tuntuni nace tana India wani lokaci har nace zanje India in nemeta dady ya hanani ai itace ta zo”. Su duka suka ce “Oho Allah sarki” Cikin ladabi suka durkusa har kasa suka gaisheta. Aziza ta gabatar kawayenta ga Antinta. Aziza ta nunawa Anti Sharifa bandaki don yin alwala azahar tayi. Wayar Atika ce ta hau kara tana dauka taji muryar Mahmud Sa’ad ya iso ya ce ta fito. Tana ajiyewa ta Munnira ma tayi kasa Dr. Rislan ne Cikin sauri suka fa da bandaki suka yi alwala suka zo suka yi sallar azahar. 

Suna idarwa suka fara dandasa kwalliya a fuska hoda, jagira wet lips da dai sauran kwalliye kwalliye ta ‘yan mata. Wayar Munnita ta kara yin kara ta dauka ta duba Atika ta ce “To Doctor ya gaji da jira kenan”. 

Mannira ta ce “Aini banma san wannan lambar ba bari naji waye”.

Ta ce “Lafiya ban gane mai magana ba?” 

Ya ce “Barista Hayat ne kin manta dazu a kotau kika bani lambarki.

ta ce ‘’oh barista ya ya aiki?’’ y ace ‘’da godiy, funnira kinsan ance kyan alkawari cikawa gani na iso ina yajen get ‘a tsaye’’.

Ta ce ‘’to sannu da zuwa barista, ka shigo cikin get din hana barista ta tsaya daga wajen kamr wani bako. Gamu an suwa yanzun nan’’. Suka ajiye waya. Aziza da atika haka hada ido suka kyalkyale da dariya suka tafa. Aziza ta e ‘’munnira tsaya tsaya yaushe kika zama compus girl har aike hada samari kala kala waye kuma barista?’’

Atika ta ce ‘’ke kince mata compus girl, player zaki ce hata lallai munnira har wani barista kika samu shima kika tashi wannan lokacin ya zo don su hadu da dr. rislan. Yanzu haka zaki yiwa dr. rislan? Munnira dai tsantsara hauri take a gaban mudubi sai murmushi take dawai. Da ta ama daurin ta fara feshe duk jikinta da designers turaren da hake a shake akan mudubin masu kamshi kala kala. Atika ta ye ‘’munnita meye haka? Sai kace wata amarya kike fesa ferare hark ala kala ko kunya bakya ji kije gaban surayi ana kamshi bududu ai yasan shi kika fesawa ‘’. Aziza t ace ke kuwa ta hada doctor da lauya ba dole ta kece raini ‘’.munnira dai sai kyalyyala dariya take bat ace das u omnai ba ‘’atiku ta nisa ta ce  ‘’bani waje kiga ni turare daya a ya isheni in fesa saurayi dai ba miji ba, wai waye barista munnira kinga bana son neman maganan da hada fada gaskiya zanyiwa Mahmud waya ince ya sameni a gida da ddare ba zan fita ba kar inje a casu a gabana doctor da wuya ga daddy yana gida ya jiyo hayaniya ya leko yaga une muka hada samari fada jeki ke kadai’’.

Munnira t ace ‘’dalla barista hayat ne fa ‘’. Atika ta ce me ya kawo shi in ba zance ba ‘’. Aziza ta ce ‘’kai barista hayat yana da matukar kirki, ga tausayi, yana burgeni amma da zaki kulashi da kin kyauta min ‘’. Munnira t ace ‘’har ya did dr. rislan naki haba aziza doctor fa’’.

Aziza t ace ‘’gaskiya tislan ma dan gida na ne ya za ayi kenan?”

Munnira ta zo gaban aziza dake zaune a gefen gado ta zauna ta rike hannuta t ace ‘’kince barista hayat yana da matukar kirki, ga tausayi yana burgeki kuma d azan kulashi da na kyauta miki ko?”

Aziza ta yi murmushi ta ce ‘’haka nace saboda yana da nutsuwa gashi handsome mai kyau da zan kulashi da shi amma fa ba ruwan karki cewa dr. rislan nina sa ki kula shi’’. Munnira t ace ‘’atika kece shaida kina jin wannan yabon barista da aziza ke yi ko? To barista hayat tun ranar da akayi miki tiyata ya sami labara ya zo gidanmu ya sameni ya ce  inyi miki sannu, idan kin warke in isar masa da sakonsa yana matukar sonki, kina burgeshi kina da matukar kiriki gaki da tausayi gaki very beautiful mai kyau dake’’. Su duka suka tuntsire da dariya har anti sharifa da take kan abin salla tana jan carbi tana kallonsu said a munnira ta bata dariya.

Aziza t ace ‘’tukashi ashe barista zai sha magiya har makogoransa ya tsage. Baya iya surutu ba irin nasu na lauyoyi to sai y gaji da rokona don har abada b azan soshi ba’’.

Munnira Ta ce ‘’haba aziza meye laifinsa bayan ke kika yabe shi yanzun nan. A kotu ya hadu da ni dazu n ace karfe biyu yazo nan gidan mu hadu gaki gashi gani kuma. Na bashi lambar waya ta n ace ya kirani idan ya zo Danni tunda ya bani sakon na kasa gaya miki gara ya zo kotu hadu’’.

Anty sharifa ta ce ‘’aziza tashi kema ki shirya ki fita gunsa ba a haka ke baa bin kunya ba ne ace babbe dake baki iya tsayawa saurayi, kalli kawayenki yada suke yiwa samarinsu kwalliya”.

Atika da munnira suka kyalkyale dariya aziza ta cika tayi fum kamar zata fashe ta suri gyale ta fita atika da munnira suna biye da ita har fargajiyar gidan. Dr. rislan d barista hayat sun hadu a jikin motar barista hayat sunna gaisuwa dake sun san juna sukan hadu daman annan gidan a lockacin case din nan na aziza Mahmud sa’ad shi da bai sansu ba yana zaune a motarsa yana jin kida a rediyo. Fitowar ‘yan matan nan guda uku shi ne ya haske musu ido, kamshi ya daki hacinsu su dukkansu suka dago kowanne indanuwansa ya dira akan wacce yake muradi. Sai murmushi n bata mayar masa ba. Bayan aziza ta gaisa dad r. rislan da tsaye tayi dan murmushi dakyar, sannan ta gaisheshi. Atika da munnira suka ha samarinsu izuwa cikin katafaren labun da yeke daga bayan gidan don karawa hirar soyayyarsu armahi. Saman sun gayawa masu aiki s kaiwa bakinsu lemuna da kayan marmari. Masu aiki ne suke wucewa da farnatai an yayyanka a barba, mangoro, lemon bawo, gwanda, kankana, tufa {apple} kayan marmari dai kala kala. Aziza ta bisu da kallo babu abinda take tunowa a ziciyarta sai dama ace ashruf yana nan suma su wuce da masayansu. Lambun nan ya dau sanyi zaiyi dadin zama saboda kwalla ranar da ake yau garin zafi kau.

Barista hayat ne ya katse mata tunaniunta ya ce ‘’malama aziza naji dadin ganinki na godewa allah na godewa munnira da ta isar min da sokona izuwa wajen wata wacce tayi fintinkau bazan iya isar da sakon da kaina ba’’. Ta yatsune fuska kadan sannan ta nisa t ace ‘’barista hayat moh’d munnira ta isar da sakonka gareni naji dadi na gode kace kana sona amma kayi hakuri soyayya bata gabana bawai dakai bane bazan yiba a a ita kanta soyayyar ce bana so da kowa ma saboda wasu dalilai da suke surri ne a zuciyata. Kayi hakuri barista kayimin halacci a rayuwata bazan manta da kokarin da ka yi mana ba a wahen shari’ar da muka yi nagode sai anjima’’.

Barista hayat ya ji wata mummunar faduwar gaba da jin kalaman aziza nana da nan ya gigice ya hau dogo turanci akan ta tsaya ya yi mata bayani ta ce ya yi hakuri ba zata iya tsayawa ba taji wani bayaninsa ta wuce zuwa cikin gida yayi tsaye yena kallonta kuka ne kawai bai rusa ba saboda ya samu ba. Alhaji ahmed yana tsaye a wundon dakinsa yana kallonsu ya sauko da sauri ya tari azziza gashi bai kallonsu ya sauko da sauri ya tari azziza a babban falo tana tambayarta. Ya ce ‘’ azziza barista hayat na gano a waje kuna tsaye meke faruwa?”

Ta ce ‘’daddy babbu komai zuwa ya yi ya mun ya jiki”.

Alhaji ahmed ya ce “a ‘a aziza a fusace naga kin juyo yana binki yana rokarki gaya min gaskiya”.

Ya ce “ke kuma baki sonsa ko? Bakya son mai sonki aziza haka ake rayuwa? Ina tsaye a window naga rislan da munnira naga atika da wani yaro duk sun zabi kamillalu suna can sunna far’a amma ke kin shawa naki kamilallen kunu kina yi masa fada. Aziza komai ya wuce yanzu lokaci ne daya kamata ki nutsu

[9/12, 5:32 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/12, 5:33 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4 

*28*

Ashruf ma kince kin daina sonsa ba za ki aure shi ba, Barista Hayat ma kince bakya sonsa mai yasa zaki kishi?”

Aziza ta yi narai narai da ido kamar zata fashe da kuka ta ce “Dady ciki fa nayi wazai aure ni da daraja?” Ta fashe da kuka. Alhaji Ahmed ya daga kanta ya ce” Daina kuka Aziza ya isa ciki kaddara ce daga Allah (S.W.T) ki daina damuwa saurayi yake auren bazawara ma ai babbar sunna ce balle ke baki yi auren fari ba ma. Don haka nafi son ki auri Ashruf tunda yafi kowa sanin ya ya aka yi”. Ya yi mamaki da yaga Aziza tana da murmushi ya ce “Aziza ko ba haka ba?” Ta dinga murtsike ido kamar mai goge hawaye kamar mai jin kunya. Ya ci gaba da cewa “Kefa da kanki kika fadamin a Italy yanzu Ashruf kike so harma kuka yi shirin guduwa yanzu kuma kika ce mana kin fasa”.

Aziza ta ce “Dady Ashruf fa ya tafi ba dawowa zai yi ba”. 

Ya ce “Waye ya fada maiki? Ko dazu munyi magana da shi da zarar ya sami biza zaizo saboda iyayensa ma ba za mu barsu su koma Jamaika ba sunzo gida kenan kinga Asharuf dole zai zo”. 

Da yariya ta kyalkyale don dadi, dadi ya rufe mahaifinta yayi dariya ya ce “Ja’ira ashe kina sonsa kika ce kin fasa aurensa”. Ta tashi aguje ta hau bene tana dariya. 

A ranar da daddare Aziza kwana suka yi da Anty Sharifa suna hirar rayuwa Anti Sharifa ta bawa Aziza kwana suka yi da Anty Sarifa gwagwarmayar rayuwarta kakaf. Ta ce “Tayi digiri a Gemany tayi Doctoring Degree a India tana koyarwa a wata jami’a kake babban birnin India. Da maigidanta ya rasu sai ta daina ta tafi Saudia ta zauna. Tana fada tana hawaye. Aziza ta zaiyane mata itama nata labain Anti sharifa tace “Allah ya nuna min kina cikin wani hali a mafarkai na hakan ne ma ya taso dani na taho inzo in ganki”. Anti Sharifa tace Sati uku zata yi anan ta tafi Guru garinsu tayi wata biyu ta wuce Maiduguri garin mijinta tayi wata saita koma Saudia don ba ba za ta iya zama a Nigeria ba. Aziza tace ai kuwa ba za ta bar Anty Sharifa ta koma Saudia ba taza kenan kafarta kafarta zata rakata Guru da Maiduguri suje su dawo. Anti Sharifa a gidansu zata zauna. 

Anti Sharifa tayi dariya tace “Yarinta ce take damunki Aziza yaushe zanzo in zauna anan gidan bayan ‘yar uwata bata nan kuma kema aure zaki yi ki tafi ki barni. Daga karshe Anti Sharifa ta bata shawarar akan tayi hakuri ta auri Ashruf. Ita tafi yi mata sha’awar sa, suka yi addu’ar Allah ya zabar musu mafi alheri. 

A daren ne kuma jikin Hajiya Fatima mahaifyar Ashruf ya rikice. Tana ta surutai tana kokarin fita da gudu an bata maganin tasha amma taki yin barci. Ashruf ma a lokacin ya bugo waya yaji muryar mahaifiyarsa sai ya fashe da kuka kawai yaji kuma hankalinsa ya jiyo Nigeria yazo ya ganta. Ba shiri Alhaij Ahmed ya buga waya wani asibitin mahaukata mai zaman kansa dake nan Abuja a kazo da mota aka saka ta, mijinta ya so a tafi da shi don ya yi zaman jinyrarta aka ce ba a zaman jinya a asibiti. Asibitin akwai kwararrun likitoci na kwakwalwa daga kasashen turawa daban daban aka daukosu sai dai akwai kudi. Wannan ba wata mtsala ba ce a wajen Alhaji Ahmed Abdulfathi ya biya kudin komai da zasu bukata har da saura, daga karshe yaba mijinta hakuri kada ya damu suci gaba da yi mata addu’ar Allah ubangiji ya bata sauki. 

Bayan an kwana biyu da yin haka Maman Atika cikin sirri ba tare da kowa yasan abinda yke tsakaninta da Aziza ba game da Ashruf ta nemo lambar wayar Ashruf a wayar maigidanta. Sai da ta tabbatar babu kowa a gidan sannan ta rufe kanta a daki ta bugawa Ashruf waya da misalin karfe takwas na dare. Bata sha wuya sosai ba wayar ta shiga. Ashruf a zaune yake a bakin wata kwata a kofar gidansu. Yana kallon samari rungume da ‘yan matansu zasu fita shakatawa gidajen rawa ko hotels, ko wasu parties da ake hada casu su sha giya ayi shakiyanci kasancewar rikakkun arna sunfi yawa a kasar Jamaika babu ruwansu da shari’ar musulunci. Ya ji wayarsa ta yi kara ba tare da ya duba lambar ba ya tsinke wayar saboda baya so ya amsa a tunaninsa Mariah ce wata budurwa data ganshi a filin jirgi take ta binsa wai tana sonsa. Ya sha mamakin yadda akayi ta sami lambar wayarsa, kullum sai ta kirashi shi kuwa tinani da takaici ya dame shi iri iri. Ga mahaifiyarsa a asibiti a Nigeria gashi ya kasa zuwa Nigeria saboda fargabar yaga Aziza kuma ba damar ya aureta. Babansa ya fara fada masa irin shawarar da su Alhaji Ahamed suka yanke masa cewar yayi zamansa da iyalinsa a Nigeria kawai. To amma Ashruf baice komai ba dai tukunna a zuciyarsa dai yasan ba zai yiwu ba ne kawai saboda shi ba zai iya zama a Nigeira ba yaga masoyiyarsa Aziza tana auren wani ba shi ba, kuma ba zai iya rabuwa da iyayensa ba da sai suyi yamansu a nigeria shi kuma ya zabi wata kasar ya darje yaje ya zauna. Wayar ta sake shigowa a fusace Ashruf ya cirota daga aljihunsa ya kalli lambar sai yaga wata bakuwar lamba amma code din Nigeria ce. Ba tare da ya kara sakon daya ba sai ya danna. Muryar wata kamilar mata yaji tayi masa sallama ya amsa cikin ladabi babu wacce zuciyarsa ta kawo dama itace sai Azizarsa ya ce a ransa “Yau da ace Aziza ce ta kirani da kwana zanyi sallah ina godiya ga Allah, amma kash yaji ba muryarta ba ce. Ta ce “Ashraf ne”. yace “Nine wacece ke magana”. 

Ta ce “Hajiya Rabi’a ce Maman Atika Sadam daga Nigeria”.

Bai san sanda ya zabura ya mike tsaye ba don mamaki ya duka duk da a waya ne ya gaisheta. Ta amsa ta kuma yi masa congratulation akan shari’ar da aka fafata da mahaifinsa kuma ya ci galaba sannan tayiwa mahaifiyarsa kuma ya ci galaba sannan tayiwa mahaifiyarsa fatan Allah ya bata lafiya a can asibiti. Ta kuma ce masa ya kwantar da hankalinsa sunje dazu sun dubota tana ta bacci jikin yana sauki. Ashruf ya yi dariya ya yi godiya ya nuna farin cikinsa kwarai da gaske. Ta ce “Daman na bugo maka ne inji lafiya ba ka zo ba ance biza ka rasa amma ni nasan ba biza bace ta hana ka zuwa har yau, ba wani ya fadamin ba sai ni nayi tunanin haka saboda ina wajen a lokacin da kuka yi waya da Aziza cikin fushi tace idan ka tafi karka dawo ina fatan ba za ka boye min ba wannan shine dalilika ko? Tsakaninka da Allah kuma zaka fadamin”. Ashruf yayi dan murmushin dadi yace “Mama wannan n dalilina”. Tace “Nifa nasan shi ne dalilin, abinda nake so in gaya maka shine ka kwantar da hankalinka kazo Nigeria idan ka gamu da Aziza ku gaisa kada kayi dar ko ka nuna mata wani abu ya taba faruwa a tsakaninku kaji ko? Ni zan tsaya maka zan kuma shawo maka kanta kafinka karaso haba Ashruf soyayya fa kake. Fargaba do tsoro ba naka bane. Kaine fa namiji faduwar gaba a wajen yai ba taka bace balle yakin neman aure”. Asharuf ya yi dariya sake kyalkyalewa da dariyar dadi yace “Nagode madalla Mama, wallahi jiya na sami biza harna je filin jirgi na fasa tafiyar saboda fargabar kada inzo Nigeria ga Aziza amma ta gagareni. In Allah ya yarda jibi zanbi jirgin da zaije Amerika daga nan Jamika.  Gata Jirgi daga Amerika zai je Nigeria a takaice dai nan da kwana hudu zan iso Nigeria insha Allah. Ya kara godiya gami da shi albarka iri iri suka yi sallama ta kashe waya. Maman Atika taji dadi sosai Ashruf ya linkata jin dadi nan da nan ya fada cikin gida ya hau shirye shiryen tafiya. Babu wanda Maman Atika ta fadawa cewar sunyi waya da Ashruf yace zaizo nan da kwana hudu tafi so a ganshi kwatsam don tayi surprising din Aziza. 

Bayan yin wayarsu da kwana uku Aziza ta kawowa Maman Atika Anti Sharifa su gaisa da gaisa yadda ta fara kaita gidansu Munnaira suka gaisa da Ummar Munnira, Anti Sharifa tayi musu godiya bisa kulawa da suke yiwa ‘yar marainiyar ‘yarta Aziza suka ce babu komai Aziza ai ‘yarsu ce. Kafin su Aziza su baro gidan su Atika sai kusn goma na dare Aziza tasa Maman Atika a gaba tana ta yi mata Zancen Ashruf a hankali ba tare da Anti sharifa da su Atika ba sun ji me suke cewa. Maman Atika ta ce da Aziza kada ta damu insha Allahu komai zaiyi dai dai Ashruf kuma ba zai ki zuwa ba dole zaizo duk daren dadewa. Washegari da misalin bakwai da rabi na dare Aziza na kwance akan cinyar Anti sharifa tana daukar darasai game da yadda ake rikita miji yadda zaka ga miji y8ana son matarasa har wasu suyi tunanin ko asiri tayi masa nan kuwa tsabar kulawar da take yi masa taga maman Atike ce ta matsa da sauri ta ce “Hello Mamain yimi”

 Mama ta ce “Lafiya Azizav zo kiga kawarki Atike tana wani abu da ya bani mamaki” Aziza ta zabura ta tashi zaune tace “Mama me take yi Atikar” Tace “ ki zo dai ki gani da kanki ki tayani dariya ki fadawa dady in nake kiranki kar yaga kin fitra da daddare” Aziza ta mike da sauri ta zari mukullin mota tace da Anti sahrifa “ anty maman atika na nemana ki gayawa dady idan ya fito suna falo shi ‘yan siyaasa suna meetin nasan zasu dade basu fito ba “anty sharifa ta ce “To rungumeta ta su nbace ta a kumatu suka kyalkyale da dariya su duka. Aziza ta fita kai tsaye cikin motarta ta shia ta figa sai maitama lake chad street inguwar su Atika. Bata tsaya a ko ina ba sai a cikin farfajiyar gidan. Ta fito daga mota ta shiga ciki a babban falo ta iske Tanim kanin Atika ta ce “Tanim ina Atika” Ya ce “ Anty ati ta fita unguwa” Tace “Mama fa ?” yace tana falonta “ Aziza ta wuce kai tsaye cikin falon. 

 Wai! Wai!! Wai!!! Wata farar fuska ta gani mai kyan gaske ga kwarjin da wasu kayatattun idanuwa  dara dara suka dago da sauri ksuka kalleta. Ashruf Elmustapha ne zaune a falon shi kadai ga jakar kayansa a kusa da shi daga gani yanzu ya shigo kasar. Ta tsaya cak tan kallonsa sai dai wannan karon kallon da suke fuskarsu cike da murmushi dukaninsu. Ta shigo a sanyaye kan ta a sunkuye a kasa gami da yin sallama a gareshi, ya amsa mata cikin tattausar murya. Ta wuce daki. Ta iske Maman Atuika a kan abin sah tana lazumi suna hada ido sai dukkaninsu suka kece da dariya. 

 Aziza taje ta fada jikinta cikin sahgwaba ta ce “mama me yasa kika ce min Atika zan gani babi cemin Ashruf ba me ?”

 Ta yi murmushi ta ce “ Au to bari ince ya juya jamaika”Aziza ta riketa tana cewa “Naji dadi amma ni kunyarsa nake mama zo ki rakani” Ta ce” Ashe ba za ga Ashruf din ba kenan kinga ba ni waje inje in shiryawa nagona abici kafin ya dawo” Aziza ta yi dariyas tace “Mama kece amaryar   kenan” Tace “ Amarya ce Mana soyayya bata tsufa Aziza zo ki wuce wajensa ki bashi ruwa da abincei yanzu ya shigo , in kinga fita ta na barki da shi “ Mama ta fita Aziza ta mta ido. Yayi ajiyar zuciya ya ce “ Aziza yaya? Kuna nana Ashruf” ya ce “ Na rame, nayi baki sabada raashinki ke fa?” su duka suka yi dariya tace “ ya ka ganin? Dukka yadda ka ganin haka akayi” Yace “Naga kin trame kinyui fari amma kin kara kyau”

 Te ce “ to haka akayi” suna hira wasa da dariya can ta yunkara zata jie ta dauko masa ruwa da abince ya dafe hannaunta ya ce “ Tayi zamanta shi ya koshui babu kishirwaba yunwa gainta ne ya kosar da shi. Ta yi masa congratullation bia samun nasarar shri’ar da suka yi da kuma fatan Allah ya bawa mahaifiyar sa lafiya . shi kuma ya mata godiya wahalar da suke yi da iyeyensa. Daga karshe suka dunguma zuwa wajen mota don su tafi gida.

  Kwatsam Alhaji Ahmed da Elmustapha da sauran abokansu suka ga Aziza da Ashruf a lokacin sun ako su Alhaji Sadam wajen motocinsu zasu tafi gida, wannan ya nuna musu shaidar cewar soyayyarsy tana nan rangadadau. Alhaji Ahmed ya ji dadi amma Elmustapha ya fishi jin dadi ganin Aziza da Ashruf. Da ta gaishesu sai ta yi wuf ta fada cikin gida sai ta yi daki aguje ta iske Anti Sharifa a zaune a kan gado tana kallon CNN News ta fada kan gado tayi tsalle. Anti sharifa ta ce “ Ashruf ya zo ko ?” Aziza ta rungumeta ta ce “ Anti ya aka yi kika sa ni shi ne kawai abinda zaisa ki wannan murna” 

 Ranar da  Atnti sharifa tas cika sati uku sa zu wa a ranar kuma Aziza ta fara shiya wani abu ba tare da  ta barei kowa ya gane ba. Daman ta suyowa Anti sharifa sabuwar waya (handset) da sabon lay I ta bata, sannana taje ta dauki wayar babanta ba tare da ya sani ba da misalin karfe uku na rana ta  shiga bandaki ta dinga turowa Anti sharfa wasu messages masu firgitarwa, ko kuma ince masu ban mamaki. Do farko ta turo mata da wani message kamar haka: 

Assalamu alaikum 

Sharifa ko zaki yarda ki zama abokiyar rayuwata ma’ana ki maye dakin marigaiya?”

 Anti sharifa na karantawa sai taji gabanta ya fadio waye wannan? Kai karya idonta yake nuna mata yaya Ahmed ba zai rubuto mata wannan sako ba. Bata garna mamaki ba sai wani ya sake shigowa kamar haka : 

Sharifa babu wata mace da na ganta a duniya tuna bayan rasuwar fatima na ji ina so ta maye dakin marigaiya sai ke ki yarda da ni sharifa ki rungume yarta marainiya. 

Da farko tayi tunanin to anya kuwa ba Aziza bace take turo mata wadannan text din ba kuwa amma ai kuma ga Aziza a bandaki tana wanka. Ga wayarta kuma a caji a kan talabijin. Tabbas Alhaji Ahmed ne da kansa kenana. Kafin Azizar ta  fito sai ta turo na karshe tas ce. 

You mean so much to me sharifa I love you.

Aziza ta nade wayar a hular leder da ta saka a kanta do kada gashinta ya jike ta fito daga bandaki. Cikin wannan hali Aziza ta iske Anti Sharifa tana karanta message na karshe tana gani Aziza sai tayi sauri ta rufe wayar ta yi shiru. Aziza na shafa mai tana satar kallon Anti sharifa can ta ce “Antina lafiya?” Tace “Kalau Aziza kamar yadda Mamarsu kakar Aziza take kiranta. Can Anti Sarifa ta nisa tace “Aziza gaya min lambar dadyn ki ina so nayi storing a wayata”. Aziza ta ce “Land line ko handset”. Tace “Nasan Landline handset dinsa dai”. Aziza ta karkace ta fado lambobi, anti Sharifa na rubutawa, taga sak lambarce akayi mata wadannan messages. Sai ta sake nutsewa cikin tunani da mamakin wannan al’ajabi. Kafin Aziza ta gama shafa mai sai Alhaji Sadam ya bugowa Alhaji Ahmed waya ga waya kuma a tufke a gashin Aziza ga Anti Sharifa kuma a kwance tana kallon Aziza wacce ke gaban mudubi tana rangada wa Ashruf kwalliya sunyi waya da shi yace su hadu a lambu da yamma. Allah ya sa ta kashe ringing tone din a vibration wayar take. Aziza ta bala in tsorata jin wani abu garr a kanta saura kiris ta fige hular wayar ta fado sai ta tuna kada Anti Sharifa ta gane. Aziza ta fita a guje, Anti Sharifa ta bita tana kia “Aziza meye lafiya?” Tace “Kalau Anti Sharifa ina zuwa”. Taje ta lallaba ta ajiyewa Dadinta wayarsa falon da ta dauko daman a caji ya saka ta.

Da daddare Aziza ta sami dadynta a falonsa tayi sallama ta shiga ya ce “Azzyn daddy lafiya?” Ta ce “Lafiya Dad nazo ne in taya ka hira yau”.

Ya ce “Ina sane dake dan Antinki tazo ki ka guje ni sai na aika ma sannan na ke ganinki”. Ta ce “Dady ba haka bane kasan marayan da bai taba sanin dadin uwaba ya sameta ran tasaka”. Sai ya ji tausayin Aziza ya kamashi da taga haka sai ta rushe da kuka, yaji hankalinsa ya tashi ya fara goge mata hawaye yana lallashi. Da kyar tayi shiru can suna hira ta ce “Dady bana so Anti Sharifa ta barni saboda kowacce yarinya idan tayi aure mahaifiyarta take samu ta fada mata matsalarta amma banda ni dan haka nace ba zan barta ta tafi ba”. Yace “yi hakuri Aziza nine mummy nine daddy ki fadamin duk abinda yake damunki kinji ko? Da da Anti Sharifa bata nan ba ni kike samu ba? Ta ce “Dady ai wasu matsalar ta mata ce kawai”. Yayi murmushi ya ce “Haka ne Aziza to zan taya ki rokar Anti Sharifa ta zauna tare da mu nima idan ina ganinta tana tunomin da marigayiya kamarsu daya”. Dadi ya kama Aziza jin ya fara soso mata wajen da yake yi mata kaikayi ta ce. “Dadyu rannan a wajen birhtday partyn ka kace ka kusa kayi aure kafin zabenku dady wacece matar?” Ya yi dariya ya ce “Wasa nake babu wata wacce zan aura”. Aziza ta yi murmushi ta gyara zama ta ce “Dady na kenan”. Yace “Yaya akayi ne Aziza?” Tace “Babu” Yace “Karya kike bakinki akwai magana” Su duka suka kyalkyale da dariya. Ta ce “Dady akwai magana gyara zama in baka labari ko kuma ince shawara. Daman Anti Sharifa nayi maka sha’awar ka aureta hankalinka zaifi kwanciya Allah Dady tana sona kamar yadda mummyna take so na da”. Yayi shiru yana kada kai sai gaban Aziza ya fara faduwa tana tsoron amsar da zai ba ta, can ya dago yakalleta ya yi murmushi ya ce “Banda abinki Aziza me Sharifa zata yidani nayi mata tsufa Sharifa sai yaro ba irina ba”. Ta kyalkyale da dariya ta ce “Dady baka yi mata tsufa ba ka bani wuka ka bani nama in dai da amince, amincewarta kake nema an gama”. Yace “Jeki na baki wuka na baki nama dama suya duk na baki”. Yace “Jeki na baki wuka na ya lullubeta ta rungume shi ta fita tana murna. Ya bita da kallo yana murmushi yace “allah sarki”. 

Daga dukkan alamu Alhaji Ahmed yaji dadi da wannan hadi na ‘yarsa ta kuwa yi masa zabin mata ta gari, ladabi biyayya, addini ga kyawu dandashi. 

A sati guda Aziza ta hada kakkarfar soyayya tsakanin mahaifainta da kanwar mhaifiyarta. Tun tana daukar wayoyinsu tana turowa daya text ta koma ta dauki wayar dayan tayi reply. Takai ta kao har da hannaunsu suke dauka su rubutawa juna text din soyayya. Daga bayan ma sai suka fara magana a waya, suka ma daina magana a waya harma suke haduwa a falo ko a lambu suna tattaunawa. Dadi ya lullube zuciyar Aziza ganin abinda take mafarki ya fars zamowa gaskiya.

[9/12, 5:33 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/12, 5:35 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4 

*29* 

Ranar da kwana ashirin da hudu ta cika su Alhaji Ahmed suka raka Elmustapha k out don ci gaba da shari’arsa da Alhaji Isa (Takaka). Shari’arsa  Alhamdulillahi anci nasara kotu kuma tayi matukar dokari wajen lissafa adadin dukiyar Alhaji Elmustapha dake wajen takaka aka bashi abinsa miliyon niaron ne kudin aka kuma tarkato masar takardun kudaden hannun jarin da har yanzu wasu takardun sunayensa ne jiki. Kotu ta yanke wasu miliyoyin kudi da Takaka zai biya na diyya da yayi sanadiyar mutuwar zabaida yayar sannan gta ce zata yanke masa hukunci akan sanadiya da yayi musu wajen nakasasu kuma ya jefa su cikin kuncin rayuwa Nana gaba za ayi Shari’a akan kisan gillar da yasa aka yiwa minister sai a hada a hujunta shi. Dadi marar misali a wajen Elmustapha da dansa Ashruf da sauran masoyansu sunyi musu muma kwarai da gaske. Yanzu Ashruf da  mahaifinsa basu da wani buri illa suga Hajiya Fatima mohafiyar Ashruf ta ji sauki don har yanzu tanaa kwance a asibitin tana shan  magani alhamdulillahi a kullum kara samun sauki take yi. Watanin Anti Sharifa biyu a gidan su Aziz tace zata tafi gida garinsu Guru ta sanarwa da magabatangta. Alhaji Ahmed ya yi moata alkawarin cewa nan da sati biyu zai aiko da magabatansa don neman aurenta. Abin arziki da direba ya hada mata suka tafi hard a Aziza yar rakiya. Ashruf bai so aziza tafi guru bat a barshi. Amma ta bashi tabbacin cewa ko kwana biyar ba za ta yi ba zata dawo. Cafdijan you Guru tana da manyan baki. Azizar ce ko sharifa?  Dukkaninsu sun zama wata sabon gani garin an dade ba a gansu ba. Tswofaffin I yaye da kakanni sai koke koken dadi ake. Hakika Aziza ta saduda da rayuwa tunda ka ganta a kauye har zata yi kwana uku da ta tsani talata da talauci ko zama bagta yi idan tajie amma sai ga Aziza a dakin kiasa anyi rufi da ciyawa katangar kara tana taya wata tsohuwar dimame da safe3 a murhun duwatsu uku. Rayuwa  kenan.

 Ranar litinin da misalign goma na safe jam’iyar nana mai matukar farin jinni wajen’ yan Nigeria wato J.U.T  suke yin wani gagarumin taro don yin sahawarar wanda ya kamata a tsayar a matsayin dan takarar mataimakin shugaba kasa a madadin Alhaji Isa Elyakub, cancanta ta nuna Alhaji  Isa Elyakub. Wannan abu ya yi wa  jama ‘a dadi musamman dan takarar shugaba kasar Alhaji Ahmed abdulfathi da babban abokinsa   Alhaji Bala tuwona maina kenan. Bayan ‘yan uwansa da abokan arziki cewa aure zaiyi kowa ya yi mamaki ya kuma taya shi murna musa mman day a fadi wacce zai aura. Kowa yaji dadi musamman don Aziza. Ya tura magabatansa sun kai kudin aure, kudin gaisuwar uwar uwa da uba da sauran kudaden da hausawa suke fara kaiwa na al’ada. Aziza da mahaifinta, ashruf da mahaiginsa suka nemi biza do fita kasashe gurda uku, dubai, America da saudiya don yin ummara. A dubai kuwa kayan aure (lefe) Aziza zata taya mahaiginta zazzaba don zabarwa antinta kaya masu kyau. Sannan su wuce America can kuma saboda kafar toba mai kyau kamar ta mutane alhaji ahmed ya dauki nauyi da kudinsa za a yiwa alhaji elmustapha don ya mike tsaye yayi tafiya a dama da shi a harkar rayuwa kamar kowa. Ashruf duma don yayi jinyar mahaifinsa a asibiti don zasu dan daddatse wasu wurare a jikin kar don a samu a sa ta robar ta daidaita ta zauna daram. Waatansu daya da rabi a can. Daga dawowarsu sai aka fara rangada bikin alhaji ahmed da amaryarsa anti sahrifa. Duk da dai bayan daurin aure Alhaji Ahmed ya yarda anyi recptin. Aziza ta so ta shirya parties iri daban daba Alhaji Ahmed ya ki yace su ba yara bane. Da kyar ya yarda suka je wajen wata dinner da ta hada musu a Sharaton Abuja. Dinner tayi tsari tayi kyau sosai manya, samari da ‘yanmata sun hallara. Ango da amarya sun sha ado sunyi kyau sosai. Daga karshe aka kai amarya kayataccen gidanta wanda kusan komai na gidan sai da aka canja shi komai sabo dal dal.

Ga angwanci ga sayisa zabe ya karato duk sun hadu sun hautsinewa Alhaji Ahmed amma abokansa suka ce sun hutarshi da yawon kanfen da sauran kacaniya da ‘yan siyasa duk zasu tsaya masa yaje ya huta gajiyar biki shi da amaryarsa. Ko dar Alhaji Ahmed bai ji ba saboda ya san Alhaji Sadam zai tsaya masa komai. Saboda ya saba babatu dama, ga Alhaji Elmustapha da dansa Ashruf da jikinsu, bakinsu da dukiyarsu tsakani da Allah kanfen suke taya su. Lungu da sako, garuruwa babu inda Alhaji Elmustapha da Ashruf ba su shiga ba sunawa Alhaji Ahmed kanfen dake sunsan illar talauci sunfi kowa sanin me zasu ce wa talaka ya gamsu da Alhaji ahmed zaiyi masa aiki ya rabashi da wannan matsanaciyar rayuwar nan da ‘yake ciki. Saura wata daya zabe don haka kowa ya yi wujiga wujiga duk ‘yan mazan gidan basa nan. Aziza sai ta yi kwana uku bata ga Ashruf ba yana can ya lula garuruwa suna kanfen. Sai dai suyi magana a way Ashruf na bata hakuri a koda yaushe saboda Aziza ta shiga damuwa wai bata ganshi ba kwana biyu. Siyasar Nigeria akwai rikici babu shige da fitar da ‘yan adawa basu yi ba donsu kushe Alhaji Ahmed ga ‘yan Nigeria don karsu zabeshi amma Allah shi ne shaidar mutum Allah ya san Alhaji Ahmed ya san niyyar sa ta ya yiwa talakawa aiki tsakaninsa da Allah. 

RANAR ZABE

Ranar asabar Cincirindon jama’a suna ta firfitowa domin jefa kuri’arsu ga dan takarar shugaban kasar da suke so. Nigeria kakaf dinta mata da maza suyi kokari sun firfito kwansu da kwarkwatarsu don jefa kuri’a, burane da kauyuka. Gidansu Aziza kakaf dinsu kowa ya fito ya shiga gari don jefa kuri’a. alhaji Ahmed kuwa yau kwanansa biyu bai tako gida ba suna can siyasa ta rincabe ana addu’o’I sunnan ana fadakar da jama’ar Nigeria akan kada su bi son zuciya saboda ‘yan kudaden da ake basu don su yi zaben tumun dare su tsaya su yi tunani don su zabi dan takara na gari wanda zai amfani al’umma gada daya sannan su bawa Allah zabi ya zabar musu shugaba na gari. Allah Ubangiji (S.W.T) ya duba zukatan al’ummar Nigeria ya karbi addu’o’insu ya zabar musu shugaban kasa na gari. Sai karfe uku na daren wannan rana asbar sannan babban jami’in zabe ya sanar da sunan wanda ya lashe zaben shugaban kasa shi ne Dr. Alhaji Ahmed Abdulfathi da mutaimakinsa Injiniya Sadam Tahir. Su Alhaji Ahmed sunji dadi da wannan sa’a Allah ya basu suka lashe zaben amma ‘yan Nigeria sun fi su jin dadi da Allah ‘ya zabar musu shuwagabanni na gari masu kishin ‘yan kasarsu da tsoron Allah. Labari har kunnen Alhaji Isa Elyakub wanda ke gidan yari inda aka ajiyeshi kafin a yanke masa hukunci. Take ya hau shessheka zuciyarsa ta samu matsala saboda tsananin mummunan labarin a wajensa cewar Alhaji Ahmed shi ne shugaban kasa Alhaji Sadam mataimakinsa. Rabe rabe aka maikashi ga likitocinsu na daurarru don ceto ransa saboda fuk ya fadi kasa da jin labari Alhaji Ahmed ya lashe zabe. Bayan an kammala hada hadar zabe ranar litinin ta sama kenan aka kira Alhaji Ahmed da mataimakinsa Alhaji Sadam za a rantsar da su. Ashruf da mahaifinsa suma sun tafi wajen bikin rantsawar, Anti Sharifa ma da su Maman Atika dakkansu sun tafi. Aziza ce kadai ta rage a gida itama ta shirya tsaf zata biya ta gidansu Mannira da Atika ta tafi da su kamar yadda suka shirya, sai taji wayar babban falon dadynta tana kara ta tafi da sauri ta daga kan wayar sai taji muryar wani mutum ne yace “Nan gidan mai girma shugaban kasa ne?” Ta ce “Eh nan ne lafiya?” Yace “Lafiya kalau likita ne daga nan asibitin masu larurar kwakwalwa ne game da marar lafiyar da kuka kawo mana ne”. Gaban Aziza ya yanke ya fadi gudun karfa wani abu ne ya faru ga mahaifiyar Ashruf saboda burin Ashruf yanzu shine yaga lafiyar mahaifiyarsa kawai haka mahaifinsa ma. Tace “lafiya?” Likitan yayi ‘yar siririyar dariya yace “Ba wata matsala ba ce daman illa ma abin farin ciki”. Aziza ta yi ajiyar zuciya ta ce “Alhamdulillahi Doctor yaya aka yi?” Yace “Fatima Elmustapha Allah ya bata sauki mun gwargwada ta mun lura ta samu waraka daga wannan larura ta tabin hankali da take fama da shi. Yanzu ma munsao tayi hakuri ta zauna a wajenmu zuwa sati guda saboda munsan yanzu shi kansa mai girma shugaban kasa yana gwagwarmayar zaben nan sannan mu dawo da ita gida ta tilasta ta ce ita tana son ganin mai gidanta da Ashruf tun jiya take tayar da hankalinta. Kinsan mai larura irin wannan bai kamta ba kuma a dinga ja mata rai a hanata tazo taga iyalinta kada tayi tananin ko rasuwa ma suka yi ake boye mata zata iya sake rikicewa. Idan da halin wani nata ya zo asibitin yanzu zai iya zuwa don ya dauketa”. Farin ciki ya rufe Aziza tace “Doctor babu matsala ni sunana Aziza Ahmed Abdulfathi  ganinan yanzunnan zanzo in dauketa”. Da sauri ta zari gyalenta da mukullan motarta ta nufi wajen mota. Gidansu Munnira ta fara zuwa dake Wuse zone six ta dauketa suka wuce zuwa asibitin dake yafi kusa da wuse. Suna isa suka shiga ofishin babban likita anan suka sami Hajiya Fatima tana zaune a kujerar dake kusa da teburin likita yana mata wasu tambayoyi da zai kara taimaka masa wajen sanin inda kwakwalwarta ta dosa kuma wanne magani zai rubuta mata taci gada da sha. Bayan su Aziza sun gaishe da likita sai suka karasa gaban Hajiya Fatima suka durkusa suka gaisheta wacce tun shigowarsu take tayi musu mursushi. Ta mika musu hannu suka gaisa ta shafawa Aziza kumatu ta ce “Ke ‘yar budurwa mai kyau”. Ta shafawa Munnira kumatu ta ce “Ke ‘yar fara. Likita ya ce “To Aziza ga wannan takarda magunguna ne na rubuta mata kada a dinga yawan bata mata rai ko kuma a dinga gaya mata abubuwan tashin hankali amma ragas ta sami sauki mun gwargwadata sosai munga hankalinta ya dawo jikinta”. Hajiya Fatima ta juya ta kalli likita tace “Sune zasu tafi da ni?” Yace “Eh su ne ku tafi shike nan”. Tace “Kace min nan Nigeria ne ina zasu kaini? Kace Ashruf da babansa zasu zo, ina suke?” Aziza ta yi murmushi tace “Mummy can zan kaiki wajensu yanzu sun fita unguwa ne shi yasa, da aka yi waya basanan sai ni kadai gidanmu daya da su Ashruf din ai”. Tace “Mafi mishikala”. Babu matsala kenan ta mike tsaye suka fita bayan ta yiwa likita godiya da addu’o’I dake malama ce makaranciyar alkur’ani mai tsarki, suka nufi gida. A bangaren Anti Sharifa ta ajiyeta ta nuna mata bandaki don tayi wanka ta nunnuna mata mayukan shafawa kala kala da turarurruka da sauran kayan kwalliya ta ciro mata wata sabuwar atamfa super hollad ta Anty Shaarifa da bata taba sakawa ba. Hajiya Fatima ta yi dariya ta ce “Bata iya daure zani ba, a bata doguwar riga dai. Dama akwai akwati guda Aziza ta zazzabowa Anti Sharifa na dogayen tiguna a lefe ta ciro mata wata doguwar riga mai ribi biyu da dankwalinta harda nikaf tace a bata don suturce fuskarta. Aziza ta kira Amina mai aiki tace ga bakuwa nan ta tambayeta duk irin abinchi da take so taje ta gayawa kuku su dafa mata sannan idan bakuwar tayi wanka ta zo ta debo kum (combs) ta tayata taje kanta ta shafa mata mayukan gashi. Saboda gashin mai tsawo ne sosai har karshen bayanta amma ya cukurkude saboda rashin tajewa da gyara. Sannan Aziza da Munnira suka fita suka shiga mota sai unguwar Maitama gidansu Atika. Atika kadai suka samu a kwance a falon farko ta sha kunu wai ita a dole sun mata laifi ba su zo da wuri sun dauketa ba suka dinga yi mata magana taki amsawa. Aziza tace da Munnira “Zo mu tafi mu kyaleta ta tambayemu mna ina muka tsaya bamu zo da wuri ba”. Atika ta ce “Ku tafi daman ni bazan bi ku ba na riga na yiwa darling waya zaizo muje”. Suka tuntsire da dariya Aziza ta ce “Waye daling?” Munnaira tace “Wai Mahmud Sa’ad. Zo mu tafi Aziza darlin din ya zo ya dauketa”. Suka fice suka barta a kwance Aziza na cewa “Zan masa waya in ce kar ya zo munzo mun tafi da ke ki sha zama ke kadai a gida”. A get din fita suka ci karo da Mahmud Sa’ad yana shigowa, bayan sun gaisa suka wuce shi kuma ya shiga ciki. 

An gama rantsar da su sannan aka wuce wajen kayatacciyar liyafar da aka shirya musamman dan taya murna ga mai girma shugaban kasa da mataimakinsa da manyan bakin da suka halacci wajen bikin rantsarwa da sauran jama’a talakawa da masu hannu da shuni. Anci an sha  an gyatse a wajen wannan walima sai karfe biyu na rana aka fara watsewa. A wata kujera Alhaji Elmustapha yake zaune yayi shiru yana kallon masu wurwucewa yana tunani a zuciyarsa yaga kowa da matarsa a gefensa sunci kwalliya suna tafe suna hira suna dariya. ‘Yan mata ma da samarin su shi kuwa tasa tana can asibiti tana fama da larura yau shekaru ashirin da hudu kenan ya ce a ransa “Ga kudi na samu kudin da zan iya gina gida gida a kowacce kasa nake so. Zanci abincin da naga dama zan saka kowacce irin sutura duk tsadarta in hau kowacce irin mota duk tsadar ta. Amma ba Fatima, Me ye amfanin kudin nawa tunda ba batima?” Ashruf da Aziza ne suka zo wucewa ta gabansa suka gaisheshi sannan suka wuce ya bisu da kallo sun bashi sha’awa matuka saboda suna son junansu ya yi musu fatan Allah ya barsu tare, Allah yasa rabansa ce. Har sun kai kofar fita daga katafaren hall din sai Aziza ta juyo ta kalli alhaji Elmustapha ta san tunanin da ya zauna yan yi bai wuce na matarsa ba. Tace da Ashraf ya tsaya tana zuwa, sai ta dawo tazo ta durkusa a gaban Alh. Elmustapha ya dago ya kalleta ya yi mata murmushi ya ce “Aziza ya aka yi?” Ta yi dariya ta ce “Abba naga kowa yana tafiya ka zauna kai dadai kamar wani abu kake tunani”. Yayi dariya yace “Aziza ba dole na yi tunani ba, amma Alhamdulillahi”. Tace “Abba na zo maka  da wani albaishir mai dadi sosai amma me zaka bani?” su duka suka kyalkyale da dariya, Ashruf ne a tsaye a kansu yace “Abba kace ka bata ni shine goron

[9/12, 5:35 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚

[9/12, 5:37 PM]  "  D'Y: KWANA ASHIRIN DA HUDU PT4 

*30* 

Albishir din da zaka ba ta “. Alhaji Elmustapha ya ce “Kai tafi ka bamu waje.Aziza me kike so in baki in dai ina da shi zan baki ko meye ki fada min abin albishir din na kagu inji”Tace “ Abba babu abinda nake so tunda ka haifo mun Ashruf ka gama min komai” sai kunya ta kamata ta sa hannui ta rufe fuska, dadi ya sake rufe Ashruf. Tace “ Daddy  ka daina damuiwa in  dan ciwon umma ne da take aisbiti ka kwantar da hankalinka ta warke garau” Ya zabura ya ce “Me ya sa kika ce haka?”Tace”dazu likita yayi waya yace ta carke a zo a dauketa na zagoayo daga bayan kujerar  da yake a tsaye suka zagaye Aziza da tambayoyi idan uba ya jeho mata t ambay a kafin ta bashi amsa Ashruf yayi mata t asa tambayar y a y a take yanzu?Metake cewa? Ana magana radai da ita?Mu rna ta lullubesu marar misaltuwa cikin sauri Alhaji Elmustapha ya yi wajen mota yana fadin “ Alhamdulihhahi ya Allah” Ya shiga mota sai gida, Ashruf ma Allah Allah yake ya jee ya ga yaya mahaifiyarsa take suka fito shi da Aziza ta shiga dakin Anti sharifa ta iske u mmar  Ashruf ta yi wanka tsaf taci abinci tana kan abin salla tana jan carbvi bayan ta idar da sallar Azahar Aziza ta shigo ta zauna a gefenta. Ummar Ashruf ta yaye fuskarta da nikaf din data rufe. Tayi murmushi tace da Aziza kun dawo ?” Aziza ta ce “ Mun dawo ga Ashruf ga Abban sa can a falo” Ta yi sauri ta mike cike da murma tana cewa “Ina suke nuna min su Aziza na gaba Hajiya Fatima sauri tazo ta rungume danta dukkansu hawaye suke tayi ta tattaba shi tana kallonsa ji take kamar a mafarki take ganin mamaki da ta ganshi a tsaye ba akan keken guragu ba da ta saba ganinsa. Ta tafi  ta rungumeshi shi ma.

 Alhaji Ahmed ya kaura presidential billa gidan shugaban kasa da iyalansa. Haka Alhaji sadm ma ya kaura gidan gwammati da iyalnasa, Alhaji Ahmed ya barwa Alhaji Elmustapha gidansa ya ce ya bar masa duniya da lahira da kayan ciki ya zauna da iyalansa. Haka alhaji elmustapha ma ya kaura gidan gwnamanti da iyalansa, alhaji ahmed ya barwa alhaji elmustapha gidansa ya ce ya bar masa duniya da lahira da kayan ciki ya zauna da iyalansa. Alhaji elmustapha yayi alhaji ahmed ya barshi saboda whalar za tai yawa tunda yanzu shi ma allah ya bashi kudi meye amfanin kudinsa ba zai kashe ba komai sai anyi masa. Alhaji ahmed ya ce’’ a matsayinsa na bako a wannan kasa dole ya kamata su basi muhali ya ce ya bashi saboda allah kuma yana so zumuncinsu ya sake kulluwa. Alh. Elmustapha sosai yayi godiya kwarai da gaske. Haka matarsa ma taje har gida ta matukar godiya da wannan babbar kyauta. Don haka ne alhaji elmustapha ya ce da dans ya dinga tambayar aziza cikin dubara ya ji irin ginin gidan datake so idan zasu yi aure da kuma unguwar da take so su zauna a abuja, alhaji elmustapha ya ce duk tsadara zai gina musu ba zai ce duk shi zai yi kuma wahalar za tayi masa yawa. Haka kuwa aka yi cikin dubara ashruf ya dinga bugun cikin aziza cikin hira ta gama zaiyana masa dalla dalla irin yanayin gidan da take so tace’’ wani gida ne da ta gani a london babanta ne ya saya, irinsa take so komai da komai har kayan ciki yadda aka shirya haka take son gidansu ya kasance’’ ashruf ya ce ‘’ to yaya za a iya gina miki irinsa sak anna?’’ ta ce ‘’zanen ginin yana wajena a takarda’’. Yace ‘’to su waye zasu gina ko can london din za a je a dauko wandanda suka gina” Tace “ Ai akwai wadansu magina kwararru a garin nan suam dai turawa ne mun taba  magannar da su kwanaki sunga hoton gidan sun ce zasu iya.Ya yi ta bugun cikinta dai har ta zaiyane masa komai har unguar da take so su zauna sai da ta fada masa. Ita bata san bugun cikinta ya yi ba zaije ya gina gidan, haka kuwa aka yi har sai bayan su Ashruf sun sayi fili har maginan sun fara gini sannan su Aziza suka sami labari. Kafin mai girma shugaban kasa da mataimakinasa su yi wa ta guda akan karagar mu lki suka zabi ministoci da sauran manya> manyan kososhin gwamanatin Alhaji Bala shine  senete president, Alhaji Elmustapha kuma an bashi minister of foreign affairs, sai sauran jama’a daban daban, wannan mukamai sun dace ga duk wanda aka bawa. Allah ya karbi addu’au yan Nigeria yas basu shugabanni na gari. Alhaji Ahmad yana aiki tukuru tsakaninsa da Allah kowa yana ta san barka da godiya komai ya wadata kamar wuwar lantarki, ruwan sha da sauransu. 

‘Yan matranna wato Aziza Atika da Munnira da body wacce suke ciki gabanswu kuma security ne maza (SS) ta bayansu kuwa (SS) mata ne. haka suke tafiya duk inda zasu je. Wani lokaci su Aziza  suna wucewa ta Mr. Biggs, kafin su fito doga mota Atika ta ce “ Dalla Aziza bayan a koshe muke me zamu siya a Mr. Biggs kuma “ Tace” ku fito ku dai wasu yara zan gyarawa zama ku duba ku gani wannan ba motar su mubarak ce ?” Munira ta ce “ kwarai kuwa ita ce muje ciki” 

Atika ta ce “ Kunsan yadda zamu y I musu su ji haushi shi kudi kawai sai muce wa mai karbas kudinta tsa ya sai mun gam siyan abinda zama siya mun biya sannan a karbvi nasu”

Aziza ta ce “To me muka yi kenan? Ku dai ku zuba min ido” 

 Suka firfito daga mota suka je bakin kofar kantin suka tsaye, Aziza tayiwa body guards dinsu nuni da hanu alamar su shiga ciki su firfito da kowa sunnan su shiga. Cikin sauri body guards suka ce “Duk ku firfito president’s daughter zasu shigo” wannan abu ya bawa jama’ar ciki mamaki wasu da rawar jiki suka yo waje masu taurin kai irinsu Mubarak da abokansa suka ki fita suka ce su su waye daza a ce su fito  sunnan su shigo? Sai da suka ji kanshin bindiga sannan aka tankado keyarsu waji Aziza ta zare gilas din dake fuskarta ta kalli mubarak tayi murmushi tace “ presidnet daughter” takaici ya rufe Mubarak haushi ya sa suka shiga mota suka b wajen suka fasa siyayyar. Kusan kowanne lokaci haka su Aziza suka iske Mubarak a tsaye da wata kazamar sunsan wuraren shakatawar da yaki zama , sai suje susa ayo waje da shi sannan su shiga. Wata rana da yamma a millenium park su Aziza suka iske mubarak a tsaye da wata kazamar bayerabiya taci kwalarsa an ciak ana batahakurio wai ba zata yarda ba mubarak yayi mata ciki. Aziza ta bude jakarta ta  zaro kudi bandir yan dari biyar –biyar ta saita goshin mubarak ta jefa masa ya dago a fusace daon yaga wanda ya jefeshi sai kuwa yayi ido hudu da Aziza. Ta tuntsire da dariya tace dauki baka nayi gudunmawa don kasayawa bayerabiyar karuwarka kayan kara lafiya don anasan masu ciki su rings cin kayan kara lafiya. A fusace mubarak ya tsuguna zai rarumo kudunan ya jefawa Aziza sai bayerabiyar tai sauri ta dauke tace ita tana so daman tunda yayi mata cikin bai taba bata  ko kwabo  ba. Aziza da kawayenta suka kwashe da dariya suka tafa hannu suka wuce suka bar mubarak anana cikin takaici marar misaltuwa 

BIKI BIDIRI

Ranar juma’a bayan sallar juma’a a babban masallacin juma’a da ke birini abuja aka daura auren Ashruf Elmusapha (ja) dan minister of foreign affairs, da yar gidan shugaban kasar nigeria Aziza Ahmed Abdulfathi, sannan na mahmud saad Mijin yawa da gwamna Bauchi da yar mataimakin shugaban kasa atika sadam da na likitan da ake ji da shi a nigeria Dr. Rislan samir da yar senete presedent munnira Bala Abuja ta cika makil wadanda  ba musulmai ba sun taru a wajie daya musulmai ne suka hlarci wajen daurin auren saboda a masallaci aka daura aure. Mai girma shgaban kasa mataimainsa da kuma senete president da Alhaji Elmustapha minister of forign affairss kaya iri daya suka saka wata danyar shadda ce fara so anyi musu dinkin tazarce sun dora fararen huluna da fararen takalma a kafarsu. Haka angwaye suma kaya iri day a suka saka tsadaddiyar shadda ce brown su kuma dinki yar ciki da wando da babbar riga aka yi musu. An daura aure bisa yadda addinin musulunci ya tanada an biya sadaki mafi kankanta don auren ya yi albarkan. Iyayen amare suka ce su biya sadaki mafi kankanta saboda neman albarkar aure bayan daurin aure sai da aka shafe sati biyui cur kullum akwai abinda ake na shagalin bili ministoci da masu mikamin gwamnati daban daban kowa ribibi yake don ya hada party saboda nuna godiya ga mai girma shgaban kasa da matainakinsa saboda mukamin da ak bshi ko kuma neman gindin zama da kara samuna shiga. Sabodsa kowa ya fuskanci babu abinda za’a yiwa Alhaji Ahmed yaji dadi a zuniyar nan baya ga ayiwa iri iri. Wasu kuma da suka ga parties sunyi yawa sai suka shiga syautar motoci Aziza ta sami mota mai suna mota sama da Ashirin tsadadu. Atika bawa amare kyauta a naa cikin garin Abuja . kawayen su aziza yawanci turawane da larabawa harma da indiyawa wadanda suka hadu a jami’a da suak yi digiri tare suma sun hallara jajur da su. Idan ka shigo Abuja zaka dauka sallah ce a kano saboda jama’a jajayen fata kuwa kai kace a croatia haduwarsa ba karshen haduwa dai ya hadu. Makada. Maroka kasuwarsu ta bude a Abuje yan gayyar sodi. Yan cin wara a ware suma sunzo sunci wara kuwa sunyi nat har kasa dauka. Shahararriyar mawakiyar turawr nan jannifer lofez ita aka gayyato. 

 Amare sunyi matukar kyau angwaye ma haka ranar da aka ciak sati biyu ana caswhew da wannan gagarumin biki. Ranar juma’a da misatlin karfe hudu na yamma aka shirya amare za a kaisu gidajen mazansu. Lafayu masu masifar tsad suka nada an dibi amare a sababin motoci fil fil kowacce mahaifinia ya suyo mata musamman don a kaita gidan mijina a ciki. Abin gwanin ban sha’awa saboda an hada al adun kabilu daban daban ya bada wata sabuwaar al’ada. A cikin motcin nan ne da ake iya bude saman ana hango wadanda ke cikin motar kiri kiri. Kowaccc amarya da angonta suna zazzaune a bayan mota jama’a ne makil suke watsa musu fulawoyi, makada na ta kida maroka na kirari masu busa kamar sarki suam suna masu busa. Wasu yan yammata suan binsu suna tafe suna waka. Kowaccc amarya gidanta na unguwa daban munira ce babarsu ita aka fara kaiwa gida mijinta a life comp gidanta yake. Atika kuma a gwarumfa, aziza kuma a maitama gidanta yake. Biro da takarda ba zasu isa in zayyana kyawun gidajen amaren ana ba. Abinda yawa wai mutuwa ta sahiga  kasuwa karshen haduwa ne gidajen wadanda mukan ce musu aljannar duniya komi yai das-das kawatattun gidaje dukkansuginin turawa ne,. kwana biyu aka dauka kafin kowa da kowa y an biki suka watse wuka bar amare da angwayensu a gidajensu. Iyayen amare da angwaye suma suka kwanta hakarkarinsu suna huta gajiya. Don an gaji likiis, ballantana amare da angwaye sunfi kowa gajiya barci  kawai suke yi har kwana biyu. Sai ranar laraba sannan suka sami kansu gajiyar ta  sake su.

Yau ne ranar farko da Ashruf ya shiga dakin aziza don tunda aka yi bikin sai dai su hadu a dining table masu aiki sun jera musu abinci su  ci kowannen su ya hau gyangyadi sai su tashi kowa ya shiga dakin sa ya kwaqnta saboda gajiya . ya isketa aq kishigide a kan gado da yamma ne tana kallon hotunan biki album goma sha biyu ne aka wanko yanzun nan mai hoto ya kawo mata. Bayan ya yi mata sallamas sannan ya shigo yazo kusa da ita ya zauna a kusa da ita ya yi mata murushin nan da yake kwantar mata da zuciya yan Amarya kinsha kamshi hotuna aka kawo ko ki yi min way dakina ki ce inzo na taya ki kallon “

Ta yi dariya tace ‘” al ni banma san lambar way dakinda ba 

 Ya kyalky da dariya ya ce “ lallai kuwa ba laifin bane ni na kyale ki” ta dan harare shi ta ce “ Ban gankaika kyale ni ba ? “ suka tsuntsire da dariya dukansu sun kallon hotunan bikinsu suna hira. Aziza ta ce kasan nay mamaki da naga jenifer lofez, waye ya daukota ne ?”

Ashruf ya ce “ kinsan Mahumud sa’ad ne saboda Atika sonta tace yauwa master me yasa  kace wa Adamu john Kuku su koma gida aka kawo rebecca  da mriay dazna fita kicin na gansu suka ce kai ne ka canja su” yace “e saboda bana son yan maza batagaggu su dinga kallemun ke ta ce “nima kuwa na ce su rabecca su tafi gida na hutar su saboda bana so wasu matan su ganenin kai natfi so kuma in dafa maka abici da kaina ashiruf ya yi dariya ya masu shara, wanke wanke fa?Ta ce su sunnan idan suny aikinsu su koma bangarensuu 

Ashiruf ya makale a dakin Aziza har suka yi magarub da isha’l ta shiga kicin ta dafa abinci yana makale da ita duleinda tasa kafarta bayan sunci abinci Aziza ta shiga dakinta daon ta dan wata ruwa ta bar Ashruf a falo yana kallon amma bayan tayi wanka tana fitowa daga bandaki a kar gadonta t aga ashruf ya yi sauri ya yi wanka a dakinsa yazo ya datse kofar dakin nata da dan mukullin a hannunsa daga ita sai dan karamin tawul iya cinya. Kunya ta rufeta don yau ne rana ta farko da Ashruf ya taba ganinta a haka. Aziza tafara ja da baya a hankali tana kokarin ta fada bandaki ashruf ya mike ya karasa inda take suka dau kusan mint biyu suma kallon junansu. Yasa hannu shafa gashin kanta a hankali tayi sauri ta sake ja da baya. Yayi murmushi cikin sanyayyar murya mai’ kasha jiki yace “Aziza kina gudu na ne?” ya jawo ta kirjinsa ya rungumeta ta fashe da kuka, kuka mai tsanani. Wannan kuka na Aziza ya tayarwa da Ashruf hankali sosai, ciki rudani yace “Aziza mai nayi miki kike kuka?” cikin sheshekar kula tace “Ashruf naji na tsni kaina kuma na tsani wannani rana” yace “me yasa Aziza?” tace “kowacce mace tana alfahari da wannan dare in mijinta ya same ta cikakkiyar Budurwa, amma ni mai zancewa mijina a yau?” ta sake rushewa da kuka, yayin da ta fisge jikinta dage kan kijinsa. Yayi sauri ya jawo ta gam ya rike ta yace “Aziza ya kike magana kamar wata yarinya waye mijin naki in ba ni ba. Wane bayani kuma zakiyi min bayan na sana mai ya faru? Haba Aziza kar ma ki sake damun kanki, tun ba yau ba na sanan ke kimalalliya ce, kin kuma tsare mum kanki na gode, Allah yayi miki albarka. Ya rungumeta, yana goge mata hawaye yasa harshensa yana lasar gefen wuyanta, tayi dan murmushi tace “ni sake ni zanje in shafa mai Ashruf yace “to muje in shafa miki man” Ta dan haraeshi cilin shagwaba tace “na fasa” cimak taji ya dauke ta tamkar wata jaririya ya kaita kan katafaren gadon dake dakin, yasa hannu ya kashe fitila.

Washe gari Ashruf na kwance akan doguwar kujera kansa a kan cinyar Aziza tana shafar gashin kansa suna hira suna kallon AIT news kwatsam aka nuno Alhaji Isa Elyakubu a kotu. Kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai har yanzu bai sadam da Alhaji Elmustapha babu abinda yake, har da alkali da ministocin Nigeira da duk ‘yan Najeriyar ma luka musu ashar y’a’’ke ‘kamar tababbe. ‘Yan sanda suka tura kcyarsa cikin mota aka tafi da shi a kiri aka kulleshi. Dadi ya lullbe su Aziza dai dai lokacin Atika ta bugo musu waya’ zata basu labari suka ce sun gani suma, Munnira ta bugo waya suka taya su murna yau anyi musu maganin azzalumin nan.

Bayan biki da wata guda Alhji Elmustapha ya kira Ashruf ya ce ya shirya shi da matarsa suje Libya da Katsina suka dangi, dangi ma su gansu. Haka kuwa aka yi, Liya suka fara zuwa wajien dangin Hajiya Fatima mahaifyar Ashruf. Ansha murna da koke ko a mafarki basu taba zaton zasu ganta ba abce musu ta haukace wasu kuma sunce ance ta rasu an turasu a rami duk sun rasu. Taji birane da kauyuka wajen danginta suka ganta da mijinta da danta da surikarta, satinsu uku a Libya suka wuce Katsina. Wai! ansha mamaki nan ma da aka ga Alhaji Elmustapha don su a yadda labari ya kai musu shine ya dade da mutuwa. Wasu kuma suka ce ance y zama gurgu yana bara amma sai suka ganshi shar da shi Kada daga cikin masu ilimi masu karanta jaridu suka ce sun ganshi a jarida ana shari’a da Alhaji Isa Elyakub. An taryesu hannu bibbiyu  musamman da aka gansu da ‘yar shugaban kasa kamar a hadiyesu basu baro Katsina ba sai da aka danaasawa Alhaji E;mustapha sarata dan Isa Katsina aka sha bikin nadin sarata daga karshe suka yi kwanakinsu suka juyo zuwa Abuja.

 Bayan sun dawo ne Munnira da Dr. Rislan suka gaiyaci Aziza da angonta, Atika ma da nata angon zuwa cin abincin dare a gidans. An harhada abinci lafiyayyu akan dining table a nan suka hadu su shida suka zazzauna kowacce a kusa da angonta suna cin abinci suna hira. Aziza ta ce “Tasya in baku wani labari amma fa gulma ce zan yi muku kuma ku yi gum da bakinku kar inji a gari. Amana zan baku ta bakin yara’’. Suka tuntsire da dariya dukkansu suka ce ‘’mun yarda’’.

Ta ce ‘’jiya naje gida na iske anti shariga tana ta kwara amai dady ya yi dagaje yana rike da ita wai ciki ne da ita’’. Suka kylkyale da dariya suka ce ‘’amman wanna gulma da dadi take’’.

Atika ta ce ‘’wai! wa ya ga aziza da kani ko kanwa?’’ ta yi dariya ta ce ‘’waya ga dady da sabon da dai zaki ce, shekara ashirin da biyar fa ba kara yi masa haihuwa ba itama anti shariga shekararta goma sha tara da aure bata taba haihuwa ba’’. Ashruf ya yi murmushi ya ce ‘’dan shekara ashirin da biyar, to nima bari in tsegunta muku ummata shekara kararta talatin da wani abu rabonta da haihuwa to itama dai dan karamin ciki gareta’’. Suka sake tuntsirewa da dariya dukanu’’. Wayar ahruf ce tayi kara ya daga ya duba lambar ya ce ‘’ban san lambar ba bata kasar nan ba ce bama’’. Sannan ya matsa kamar daga sama ya ji muryar mr. johson ya ce ashruf ango, ka yar da mai gidan ko ‘’. Ya ce ‘’kamar mr. johnson’’, ya ce ‘’ni ne mana’’. Nan murna ta hargetic tsakanin ashruf ya ce ‘’da mamaki, ina ka samu lambata?” ya ce ‘’ a wata mujala (obession) na ga bikin da lambobin waya’’. Ya tayashi murna kwarai da gaske, Aziza ma ta karba suka gaisa ta yi masa ya ya jiki? Ya ce ya wartsake ras sai dai dan dingishi yake yi yanzu. Atiku da munnira sun  karbi wayar sun gaisa daga karshe Aziza ta karbi wayar ta ce farkon shekara zasu zo ya tanadar musu jirgin ruwa mai kyau zasu fitop yawon shakatawa da mazansu, ya ji dadi kwarai don yasan shekarar cikinsu tazo. Suka yi sallama ta kashe waya, sannan suka ci kcyarsa cikin mota aka tadi da shi a kiri kiri aka kulleshi. Dadi ya lullebe su Aziza dai dai lokacin atika ta bugo musu waya zata basu labari suka ce sun gani suma, Munnira ta buho waya suka yiwa juna murna suka bugaea iyayensu waya suka taya su murna yau anyi musu maganin azzalumin nan.

Bayan biki da wata guda alhaji elmustapha ya kira ashruf ya ce shirya shi da matarsa suje libya da katsina suga dangi, dangi ma su gansu. Haka kuwa aka yi, libya suka fara zuwa wajen dangin hajiya fatima mahaifiyar ashruf. Ansha murna da koke koke ko a mfarki basu taba zaton zasu gant ba ance ta rasu an turasu a rami duk sun rasu. Taje birane da kauyuka wajen danginta suka ganta da mijinta da danta da surikita, satinsu uku a libya suka wuce katsina. Wai! ansha mamaki nan ma da aka ga alhaji elmustapha don su a yadda labari ya kai musu shine ya dade da mutuwa. Wasu kuma suka ce ance ya zama gurgu yana bara amma sai suka ganshi shar da shi. Kadan daga cikin masu ilimi masu alhaji isa elyakub. An taryesu hannu bibbiyu musamman da aka gansu da ‘yar shugaban kasa kamar a hakiyesu basu baro katsina ba sai dandasawa alhaji elmustapha sarauta dan isan katsina aka sha bikin nadin sarata daga karshe suka yi kwanankisu suka juyo zuwa Abuja.

Bayan sun dawo ne munnir da Dr. rislan sukaa gaiyaci aziza d angonta, atika ma da nata angon zuwa cin abincin dare a gidansu. An hahada abinci lafiyayau kowacce a kus da angonta suna cin abinci suna hira. Aziza ta ce ‘’tsaya in aku wani labarii amma ce zan yi muku 

Gaba da tsara yadda zasu yi tafiye tafiyensu kasasahe daban daban har ASHIRIN DA HUDU zasu zagaya don sai sun shafe watanni shida a can.

DAYA GA WATANDAYA (JANUARY)

Su Aziza sun shirya tafiya tauka yiwa iyayensu sallama suka ce zasu fita hutawa kasashe daban daban. Iyayensu sunyi mu su fatan alheri allah ya kiyaye sunyi musu fada akan su rike junansu bisa amana, su zamana masu tsoron allah. Sannan amare da angwaye suka shiga jirgi suka fara ashirin da hudu anan. Ranar ashidrinm tsari ta ce “su yi kwana ashirin da hudu anan. Ranar ashirin da biyar ga watan daya suka dira a croatia saboda haka suka yi waccan shekarar an waccan tafiyar su su mr. johnson suka zo filin jirgi suka taresu sai da aziza ta tuna ranar da suka fara zuwa croatia suka hadu da ashruf. Hotel din da aka saukesu da suka ce a sauke su anan daman daman jirgin ruwansu da aka tanadar musu yana nan yana jiransu.

Ashruf da aziza suka kira mr. johnson suka debi makudan kudi suka bashi suka rurrubuta masa wasu kayayyaki kamar katifa guda uku, barguna uku, zanin gadajc uku filulluka shida electric stove (risho) da sauran karikicc dai. Sauran sunyi matukar mamakin su aziza da suka sa a sayo musu wadannan kaya suka tambayesu me zasu yi da katifu da su risho sai Aziza ta basu amsa da cewa su zuba ido kawai idan lokaci ya yi zasu gani. 

DAYA GA WATANBIYU (FEBRUARY)

Ranar daya ga watan biyu da misalin karfe goma sha biyu na rana amare da angwayensu suka fito daga hotel din da suka sauka a croatin zuwa filin jirgin ruwa da kayansu don tafiya yawan shakatawa a jirgin ruwa. Wannan karonma su kadai suka dauki shatar jirgi gaba daya. Daga su sai ma’aikatansu kuku guda uku, masu shara da goge daban, mai shiga ruwa ya kamo kifi shima daban, akwai injiniyoyi masu gyaran jirgi koda zai iya samun matsala, likitoci da kayan aikinsu koda wani zai iya samun rashin lafiya. Matuka jirgi shugababan su kakaf Mr. Johnson (Chief in charge) Wannan karan komai ya banbanta jirgin komai sabo ne na zamani aka sake a cikin jirgin nan. Da kuma da samrinsu suka taho amma yanzu da mazansu na aure suke tafe, don haka tafiyar tafi armashi. Kowacce ta kama daki daya da nata angon suka zuzzuba kayansu a ciki. Abokan Ashruf masu dafa abinci da masu share share sai suka hau mamaki ganin Ashruf ya auri Aziza. Azizar da ta takura masa ta tsaneshi ta rainashi fiye da kowanne dan aikii yau ga Ashruf tya fi kowa matsayi a wajen Aziza. Suka ga Ashruf ya yi shar da shi kamar ba shi ba ya yaga musu yanzu shi ne ogansu sune masu yi masa hidima. Amma Ashruf bai yar da abokantakarsu ba yaje wajensu suka zauna suna ta hirar yaushe gamo kamar yadda suka saba hira da. 

 Jirgi ya ware fanya ya saki tayoyi a ruwa ya bude wuta yana gudu a kan ruwa amare da angwayensu sun shiga yawon duniya don shakatawa. A ranar mahaifin Ashruf ya bugo masa waya ya ce shi da mahaifiyarsa suna Amerika, ya samar masa admission a wata jami’a dake cikin babban burnin Amerika Washington. Don haka ya turo adireshin email don zasu ringa turo masa darussan da sukeyi ta internate. Ma’ana ba sai Ashruf ya je Amerika ba ya shiga aji ya dauki darasi a duk inda yake malaman zasu dinga turo masa abubuwan da suke koyarwa a aji yana karantawa da ga kasar da yake sai dai lokacin jarabawa ne kawai zaije can ya zana jarabawa shi ke nan a cikin shekaru biyu zai kammala digiri dinsa. Daman mahaifinsa babu abinda ya tsaya masa a rai sai rashin cigaba da karatun wannan dan nsasa kawalli daya Ashruf. Yanzu Allah ya basu yadda zasu yi. Ashruf ma ya ji dadin wannan labarin da mahaifinsa ya bashi cikin rawar jiki ya turawa mahaifinsa adireshin na internet sai dai kawai ya dinga budewa yana karanta darussan da ake koya musu. 

Washegari da sassafe Ashruf ya fito falo shi kadai don dukkaninsu basu tashi ba ya bude internate dake falon don karanto dokokin sabuwar makarantarsa. Har karfe goma na safe sannan ya ji muryar Aziza da su Atika sun tattashi sun fara surutansu da suka saba suna kyalkyala dariya a dakin Aziza suka hadu. Mahmud Sa’ad ya shigo cikin falon suka gaisa ya zo ya zauna kusa da Ashruf yana tayashi karanta email. Dr. Rislan ne ya y sallama ya shigo ya ce Shi tun karfe bakwai ya shiga dakin wasa jini ya hau kan keken was jini. Ya ci gaba da yi musu bayanai irin na likitoci yana basu shawara kamata ya yi su dinga yawan wasa jininsu saboda maiko zai sami wajen zama a jikinsu idan basa wasa jini suna tsinka shi zai sasu yi kiba. Ashruf ya ce “Doctor munji”. Suka tuntsire da dariya dukansu. Aziza ta ci kwalliya ta yi kyau sosai da wata riga da siket din jeans a jikinta ta shigo cikin falon taje ta dafa Ashruf ta baya ta sumbaci kumatunsa sannan ta rada masa a kunne ya zo dining table suci abinci an fara jera musu break fast. Ya yi murmushi ya ce taje gashi nan zuwa. Ta juya ta killi Doctor Rislan da Mahmud Sa’ad ta ce “Good morning guys your food is ready”. Mahmud ya yatsune fuska ya ce “Munki wayon ai ba haka kika gayawa Ashruf ba nima kira min Atika tazo ta rada min a kunne”. Suka yi dariya su duka, Aziza ta fice daga falon. Ashruf ya ce suje su fara ci yana so ya gama karanta sakonni ne da aka turo masa. Mahmud da Doctor Rialsn suak nufi dinning room wajen da matan suke jiransu. Ashruf na zaune ya ga daya daga cikin ‘yan aikin rike da wani kwanon tangaran ya doshi dining room. Ashruf ya kirashi ya ce “Mene a a ciki” Ya ce “farfesun kifine Aziza ta ce a dafa mata”. 

Saboda Aziza tana son kifi farfesu, Ashruf ya ce “Ajiye z kai mata”. Ya ajiye akan teburin dake gafen Ashruf ya tafi. 

Ashruf ya mike ya tattare kafar wandonsa da hannayen rigarsa ya dauki kwanan kifin nan ya nufi dining room inda su Aziza suke. Dr. Rislan ne ya fara hango Ashruf sai ya tabo Mahmud ya nuna masa Ashruf mamaki ya kamasu ganin Ashruf dauke da kwano ya nade kafar wando da hannu, ya karaso gaban Aziza ya ajiye kwanan kifi cikin ladabi ya koma da baya ya tsaya kek kamar yadda yake yi mata da. Ta dago ta kalleshi sai ta tsuntsire da dariya, Atika da Munnirma suka fashe da dariya suma sun tuna da. Dr. Rislan da Mahmud basu gane wannan dramar da ake yi ba. Aziza ta bude kwanan kifin ta sa cokali ta gutsira sai ta hau kokarin amai su tika suka rirriketa ta tofa a shara sai dariya suke tuntsirewa dukkanin su har Ashruf din. Ta yatsune fuska ta ce “Wannan kifin ya rube aje a canjo min wani”. Ashruf na dariya ya kinkimi kwanan kifi ya nufi kicin Atika dariya har fau take yi. Mahmud ya ce “Wai dan Allah meye haka mu kun samu a duhu”. 

Mannira ta ce “Au ashe ku bakusan san da aka sha tattaburza Ashruf da Aziza ba ko? To bari in baku labarin yadda aka yi. Ta gyara zama ta fara fesa musu labari dalla-dalla, suka sha dariya. Dr. R islan ya ce “Shi ne ake gwadawa yanzu?” Yana rufe bakinsa sai ga Mr. Johnson ya nufo su Ashruf dauke da kwano yana biye da shi. Suka karaso wajen Aziza ta sha kunu kamar da gaske Mr. Johson ya karbi kwanon dake hannun Ashruf ribaban kifi ya kawo miki yi hakuri gashi a cikin sakon ashirin da hudu an dafa miki wani. Mu daku muke alfahari muna sonku amma munfi son kudinku”. Suka kyalkyale da dariya su duka, Aziza ta ce “Bude kwanon in gani”. Ya budewa ta kawar da kai gege ta toshe hanci ta ce “Mr. Johnson kwar min da kifin nan daga gabana na gane irin na dazu ne. To in har ba za ku iya ciyar da ni ba zan fita kasuwar bakin ruwa in suyo abincina”. 

Ya yai sauri ya katseta ya ce “Haba mai girma Aziza ko daya daga cikinmu kike so kici ba’a dafa miki ba balle kifi fadi ya kike so ayi”.

Dr. Rislan ya fashe da dariya ya ce “Amma Aziza kin musu tsiya ashe”.

Ta ce “Irin wadannan kifin ne ba na so kannana nake so yanzu ya shiga ruwa ya kamomin kanan”. Suka sake tuntsirewa da dariya. Mr. Johnson ya ce “Ashruf ka ji abinda take so don haka maza ka shiga ruwa ka kamo mata kifin inda ba haka ba zan koreka daga aiki”> Suka tuntsire da dariya Aziza ta ce “A’a Mr. Johnson baka ce zaka koreshi da aiki ba”. “Ah, ba wasn kwaikwayo ba ne? ai kinsan akan kakkara. Ashruf ya marairaice ya ce “To shugaban tafi.” Ya juya yana tafiyar abin tausayi. Aziza ta mike da sauri ta rukoshi suka rungume juna. Mr. Johnson ya ciro kyamarar dauke holo ya dauke su a haka. Aziza ta gyaggyarawa Ashruf kafafuwan  wandon sa da rigarsa ta jawo hannunsa suka zo suka zauna adan kujera suka fara cin abinci suna hira ana tuntsira dariya. Mr. Johnson yana kashe musu fim din kyamara. Dr. Rislan ya ce “Amma wannan dramar tauo luai oma fatam dao zali ci gaba da yi mana’a duk inda wani abu ya faru don tuna baya. Ashruf ya ce “Zaku sha kallon darama kuwa yanzu aka fara”. 

Haka kuma ranar ashirin ga watan biyu shine ranar da Aziza ta cika shekara ashirin da biyar, da misalin karfe takwas na dareaka haifeta don haka karfe takwas na da aka fara gudanar da bikin cikin shkarunta kamar yadda waccan shekarar a jirgin nan ta gudanar da birthday party. Sai dai wannan karon an kawata wahen fiye da na da birthday party ma ya yi kyau ya yi dadi sosai fifiye dn da anan ma ashruf da aziza sai da suka gwada abubuwan da kuka faru. Ashruf ya je ya shige wannan dan saukurutun lungun ya labe yana kallonsu kamar yadda ya yi a waccen sherar sai da aziza ta zo kamar za ta yi waya sai ta kamo hanunsa sauka fito ana ta dariya. Anci anshya an cashe an dauki hotuma da bidio cassete abin ba sha’awa. Suna nan har sai da suka yi KWANA ASHIRIN DA HUDU a cikin wannan jirgi ranar Aziza da Ashruf suka yi shigar manyan riguna na kayan sanyi suka ce suifa zasu fita zuwa wajen tsiburin nan da suka bata gob su Mar. Johnso su taho su same su a can. Haka kuwa aka yi suka shiga dan karamin jirgi Ashruf na tukawa Aziza na gefensa da jakar kayayyakinsu da zasu bukata suka tafi. Su Atika na daga musu hannu har suka yi nisa. Basu isa wajen ba sai da yamma. Da fitilar hunnu mai haske Ashruf ya haska cikin dakin yaga tastas dakin kamar masu dakin basu dade da tafiya ba. Don ga tokar itace nan a cikin murhu. Suka kade gadonsu suka shinfida sabon zanin gado da filulluka suka yi sallah suka ci abincin da suka yi guziri a jakarsu. Suna rungume da juna har barci ya dauke su. 

Da sassafe ko farkawa daga barci basu yi ba su ka ji odar (horn) din jirgin ruwa su Mr. Johnson sun karaso, suka fito daga dakin don suga masu yin horn sai suka ga su din ne kuwa. Atika da Munnira cikin murna suka zo suka ringune Aziza Munnira ta ce “Kai amma Aziza garin nan na ku ya yi min kyau”. Ta dinga zagayawa da su ta ce “Nanne muke yin abu kaza nan muke yin kaza”. Ta kaisu har cikin dakinsu suka sha dariya suka ce “Lallai kunsha wuya har kwana ashirin da hudu a haka cafdijiam dole ki saduda Aziza”. Dukkansu suka nuna su ma suna da shaa’awar zama anan, Ashruf ya yi wa Mr. Johnson bayani akan suna so suyi KWANA ASHIRIN DA HUDU anan don haka suna so ya sa ma’aikatansu su buga musa tanfol (‘yan runfuna) guda uku amanya manya daya zai zama dain Munnira da Rislan, daya na Atika da Mahmud day kuma na Aziza da Ashruf. Sai su Mr. Johnsun su tafi Italy su jirasu ranar da suka cika KWANA ASHIRIN DA HUDU da sassafe su zo su daukesu. Haka kuwa aka yi ma’aiaktan Mr. Johnson suka buga ‘yan runfuna aka shinfida dardumai a ciki aka dora katifu runfuna bibbiyu da zannuwan gado da bargo kowanne da jakar kayansu. Wannan dakin itaccn nasu Aziza na da ya zama bandakinsu anan zasu ringa wanka har ‘yar shadda injiniyoyin nan suka hada musu da dubaru irin nasu. Dr. Rislan ya karbi kayan aiki a wajen likitoci, kayan kicin da kayan abinci duk Aziza ta sa an jifge musu yadda zai ishesu har KWANA ASHIRIN DA HUDU. Da har su Atika sunce a bar musu kuku daya don dafa abinci da sauran aikace aikace Aziza ta ce a bar shi meye amfaninsu in har ba za su iya dafawa mazansu abinci ba. Yawanci ma duk abinci gwangwani ne da lemon kwalaye da gwangwanaye ba wani giriki zasu dinga yi ba sosai. Mr. Johnson ya yi musu sallama suka tafi suka bar su anan. Sunji dadin wanan waje sosai waje ne kuma na hutu musaamman ga masoya, ga ruwa cikin tekun nan yana busowa abin gwanin ba sha’awa anan ma su dr. rislan sunsha dariyar aziza da ashruf suna gwada yadda suka yi. Amma maimakon marin da yake taska mata yanzu idan ya zo gwadawa sai ya shafa mata fuskar ya rungumeta ya rada mata a kunne tayi hakuri kuskure ne yar sa ya mareta a da. Aziza kuwa tama dai na kiransa da ashruf sai master take ce masa shi kuma ya ce matamai girma aziza. Atika tana da shegen tsoro tana jin dadin wajen da rana saboda yaddasuke watayawa suci su shag a rundumemiyar riloda wani lockaci asa kida. Ba wasanni kala kala kowacce da mijinta har was an ‘yan goye goye suke amma ita matsalarta tsoro take ji da daddare. Da kyar take iya yin barci sai ta kankamemahmud wani lokaci har kuka take fashe masa wai ita tsoro take ji. Munnira kuma saboda sanyi da daddare idanuwata suka kukkumbura, said a dr. rislan ya tsikara mata allura gashi tsoron allura tae don ta sami sakin kumburin. Ranar da suka yi kwana goma suka tubure suka ce sufa wajen nan ya isheshu su tafi. Aziza da ashruf suka ce su kuma alkawari suka yi sai sunyi KWANA ASHIRIN DA HUDU sannan zasu tafi. Daga karshe dai suka tsayaar da shawarar a yiwa mr. Johnson waya ya zo ya kwashesu su bar aziza da ahruf kawai in ya so idan suka cika KWANA ASHIRIN DA HUDU azo a daukesu su samesu a wana hotel din na Italy da suka sauk da. Haka kuwa aka yi an yiwa mr . johson waya sunzo sun dauki su atika da mazajensu zuwa Italy. Aziza da ashruf dinta kadai suka rage sunma fi sakewa yanzu su kadai, soyayya ce take gudana tsakanin masoyannan biyu a kungurmin dajin nana kamar su hadiye junansu. Su ci abinci tare, su yi wanka tare, su yi barci tare a kullum wayewar garin allah kara son junansu suke yi. Aziza tana burge ashruf matuka saboda irin yadda take yi masa abin yana bashi mamaki duk inda mace ta gari take aziza ta kai hart a wuce ta. Bata barinsa ya dauke tsinkekomai yi masataketa bashi abinci a baki ruwa ma haka wankansa ka kayansa, shafa mansa. Kalamanta suna kwanta mas da hankali kallon da take yi masa sukan kasha jijiyiyin jikinsu. Tafiyarta tana burge shi har baya kaunar ya sake kallon wata mace ba ita ba. Ga uwa uba ladabi da biyayyar  da take yi mas kamar zata kwanta masa dan ladabi. Aziza ma tana son ashruf kmar yadda yake son tad a yawa. A bangarnta itama tana alfahari da godiya ga allah ya bata miji nurusttse wanda baya so yaga b acin ranta wanda yake riritata kamar kwai, kamar wata yar jaririya a hannun uwarta. Kamar ya lasheta don son da yake nuna mata. Alhamdulillahi kiyayya ta zamo soyayya, soyayya mai karfi kuwa.

 Haka suka kansance cikin jin dadi basu so KWANA ASHIRIN DA HUDU bat a cika. Ranar da kwanakinsu suka cika da sassafe suka yi wanka suka kinkintsa kayansu suka zuba a jakunkunansu suka taho bakin ruwa suka tsaya suna jiran jirgi. Ashruf ya rike dan yatsanta inda ya saka zoben nan day ya bata na azurfa a ranar da aka zo aka tafi da su. Ya ce ‘’allah sarki komai mai wucewa ne kin tuna ranar da na saka miki zoben nan kina kuka ina kuka zamu rabu? Yanzu gashi iyayenki da kansu suka dauko ki suka dankamin ke kacikan dinki kyauta. The poor also laugh’’. Ta kayalkayle da dariya t ce ‘’ the rich also cry inji wata nurse da ta ganni ina kuka a asibiti t ace ‘oh the rich also cry tana yanzu ka ce the poor also laugh’’. Yace ‘’haka  ne mana aziza tun ina dan shekara bakwai nafara ganin wahala dab akin ciki a rayuwa. Sai wannan shekarar allah ya yassare mana lokaci guda. Allahu akbar allah mai girma bau abinda ya gagari ubangiji’’. Ya ce ‘’zo mu yi alwala mu yi salla raka’a biyu nafila don kawai mu godewa allah’’. Haka kuwa suka yi. Suna idarwa mr. johson suka dira a gabansu, ma’aikata suka debo kayyaakinsu suka zuba a cikin jirgi suka shiga sai kasar Italy. A wannan hotel din suka iske su atika. Aziza na shiga reception din hotel din taga wannan matar da ta kai mata sakon ashruf itama matar kallo daaya tayiwa aziza ta ganeta. Murna ta kamasu suka rungume juna, matar tayi mamaki da taji cewar ashruf ne mijinta ta yi musu fatan alheri ta tayasu murna.

 Kwanan su aziza uku a hotel din nan. Miss katrine sunnan matar da take aiki a reception ta zama kawar aziza sosai. Da zasu tafi taji babu dadi sun saba kuma zasu rabu, sun mata kyartar kusi mai yawa wanda tayi mamaki kwarai da gaske. Danganan suka yi sallama das u mr. johson ma kuka bashi kudaden jirginsa. Fillin jirgi suka nufa don auwa france. Kamar yadda suka yi alkawari kasashe ASHIRIN DA HUDU zasu zazzagaya yandu daai sunje amerika. Sunje crotia, Malaysia, indonusia, india, Pakistan, Italy duk ta hanyar jirgin sama zasu bi su ci gaba da zagaye kasashhe yanzu sun tafi france daga can zasu je iran da irak. Tunusia, sauth Africa, Canada da sauran kasashe, idan suka je saudia suka yi umra sais u wuce Germany don kallon kwallon world cup. Ball din da za a yi kasar Germany daga can sai suka yo gida.

 Anwaye da amre sun yo tsarabar kaya. Ko ni nan ma marubuciya akwati na daban ta tsarba abin ma sai wanda ya gani. Wata akwati daban suka ciko suka cein raba ku makaranta na duk mai son tsaraba yazo ya karba inji aziza da ashruf. Nayi murna da tsarabar da suka kawo min amma naïf murna da biro da littafin da suka kawo mi don in samu in rubuto muku wasu littatafaina.v sannan kumakowacce ta cikin yayi wata tara aziza ta haifi mace Fatima, Atika, Munnira, Ummar Ashruf da Anti Sharifa duk maza suka Haifa. Allah ya raya Amin!! KARSHE

 Ina fatan zaku cigabada kara. Ni a kullum burina in koyar da darusa, mosjadamtarwa da kuma deve muku kewa.

 Taku Jamila Umar Tanko Grmel.

Inde littafin yaburgeku kubiyoni da comment ya kukaji dadinsa

Kuma littafin gaba shine Adon dawa na jamila umar Tanko 

Amma kuma to.


KARSHE

ALHAMDULILLAHI

Watsapp number07064551049  banda flashing

[9/12, 5:37 PM]  "  D'Y: _POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 07064551049 _ 📚📚


Close Menu