HAK'K'I NE
( *NEMESIS*)
_Ummu Asma'u(sa'adatu)
*Bismillahirahamanirrahim*
Godiya ta tabbata ga Allah (SAW), Alhamdulilahi, ina godiya ga dukanin masoyana, na gode maku sosai.
Nah sadaukar da wanan littafin mai suna *HAK'K'INE* Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
Wanen labarin Kirk'iraren labari ne, banyi don wani ko wata ba.
*page* 1⚜2
A garin *MISAU* a jihar Bauchi, a unguwar central layin makama, cikin wani kyakyawan gida mai kyan tsari, wasu kyawawan fararen 'yan mata ne suka yi sallama suka shigo cikin falon.
Wata kyakkyawar mace fara sosai irin farin nan na ainihin fulanin asali ce ta amsa sallamar 'yan matan, cikin jin dad'in ganin su tace har an taso makarantar.
Wadda tafi girman tace mun taso Aunty sannu da gida, matar da suka kira Aunty tace sannunku, me ya samu Auta ta? Ummi da tun shigowar su falon ita ke magana, tace ita da yan ajin su ne, maganar ko yaushe, wai babanta mai kudi ne amma muna makarantar gwamnati, Ummi na magana idon ta na cika da hawaye.
Aunty tayi murmushi ta jawo k'aramar mai suna Mubina, cikin sigar lallashi tace haba mamana, nasha fad'a maku Ku kwantar da hankalin Ku, da makarantar kudi da na gwamnati duk karatun daya ne, duk wanda kika ga ya zama wani abun a Nigeria manyan mutanen in kin bincika yayi makarantar gwamnati.
Mahaifinku kansa baiyi makarantar kudi ba. Mubina ta dago tana kallon fuskar Aunty, tace meyasa mu Abba baya zuwa damu Abuja ya samu makaranta su Hafsa?
Anty tayi murmushi tace zakuje idan lokaci yayi, na fada maku komai lokaci ke garesa, kuje kuci abinci kuyi shirin islamiya.
Cikin dayan dakin dake falon suka Shiga, shigar su dakin hawayen da Aunty ke kok'arin kar su zubo suka fara zubowa.
**** *****
A garin *ABUJA* a cikin unguwar asokoro cikin wani kyakkyawan gida, wata babbar jeep ce aka budema get din gidan ta samu wajen parking, wasu kyawawan yara su hudu suka fito cikin motar, uniform din dake jikin su shi zai sa ka gane makaranta suka fito, uniform din ma abun kallo ne.
Cikin gidan suka wuce, a wani had'ad'd'en falo, wata guntuwar mace bak'a mai k'iba, zaune kan had'ad'd'un kujerun
dake cikin falo, zama suka yi suna Mamee mun gaji, cike da kulawa, Mameen tace dole Ku gaji tun safe sai biyar.
Cikin yan aikin gidan daya ta shigo ta fara had'a jikkunan littafai da abinci da yaran suka zube a tsakiyar falon
Mameen tace suje su debe uniform su ci abinci, zama duk suka yi a falon suka ce zasu debe anjima kar series din su ya wuce, Mamee murmushi tayi tace nan kuka fi ai.
**** ****
A garin *JUMA'ARE* cikin jihar Bauchi a unguwar tudun wada, cikin wani madaidaicin gida, wasu yara ne rakub'e gefen wani daki.
Wata mace ta fito sai masifa take zubawa, ta rantse duk basu nemo mata cenjin nik'a da ta aike su ba, sai sunga bala'e yau.
Cikin rawar jiki yarinyar da tafi girman tace wallahi Inna bamu kashe maki kudi ba, mun dawo dasu magaji ya ajiye kamin ki fito bai gan su ba.
Matar da suka kira Inna cikin fushi ta dauke yarinyar mari sai da taga wani haske.
Kuka yaron ya fashe dashi ganin Marin da akayiwa yayarsa kan kudin da shi ya batar da su.
Wani yaro ne ya fito hannunsa rike da plate yana cin abinci, yace K'arya sukeyi Inna su suka kashe maki kudi.
Inna tace kyale su d'an albarka nasan sune, sata ai gado suka yi, d'ebabbun albarka, zuri'ar wahala tsinannun yara marasa.....
Gyaran muryar da aka yi shi ya hanata karasa maganar da take yi, wani dattijo ne ya shigo gidan ga dukkan alamu shine maigidan cikin muryar damuwa yace lafiya Hajjo kike zagin yara haka?
Cikin masifa tace kudina suka sace kuma wallahi yau duk basu fito min da kudina ba sai sunga masifa, shiru yayi yana sauraren ta, sai da ta kare yace nawa ne kudin? Tace Hamsin ce, hamsin din ya ciro a aljihunsa ya bata.
Wani kallon banza tayiwa yaran ta wuce dakin ta tana kunyi arziki yan iska tsinanun yara.
*ASALIN LABARIN*
Muje zuwa
Ummu Asma'u(Sa'adatu)_
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*)
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Gaffara.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 5⚜6
Lokacin da Abba Lawal yazo suka sameshi da maganar auren Amina, sam baiyi masu musu ba kasancewarsa mai biyayya, anan yace duk yanda sukayi dai-dai ne ya amince. Albarka suka sa mashi haka ya tashi ya tafi yana tunanin yanda zai fad'ama Bilkisu wannan maganar, sai dai ya yanke shawarar gara ya fad'a mata da kanshi.
Koda yaje bayan ya gama komai ya fara tunanin yanda zai fad'a mata, tunawa da yanayin kishinta yasa ya kasa fad'a mata, saurin tashi yayi yace zaije gidansu ya dawo. Bilkisu tace wai lafiyarka naga kamar kana cikin damuwa? Abba yace bakomai bara na dawo dai.
Abokiyar zaman mahaifiyarsa ya samu ya fad'a mata akan ta kira Bilkisu ta fad'a mata saboda tana jin maganarsu. Murmushi tayi tace dan wannan ai bakomai, kowa yasan Bilkisu mace ce mai kirki gata da son dangi nasan bazata ki amincewa ba, dan haka idan kaje ka turo mani ita. GodIya yayi mata ya tafi.
Koda Bilkisu taji maganar auren Abba sai da taji tashin hankali marar misaltuwa, amma tunawa da tayi kowa yana mata kallon mutuniyar kirki yasa tayi saurin dai-daita kanta lokaci guda ta saki murmushi tace haba Inna saboda wannan maganarce dama kika kasa fad'a mani, ai koshi Abban su Khalifa ya fad'a mani bazan damu ba, da aje waje a d'auko maka wata daban ai gara 'yar gida, wallahi babu komai, nida Amina ai tamkar ciki d'aya muke, munsaba sosai kuma nasan halinta kinga zamu zauna lafiya. Murmushi Innar tayi nan tayi ta sa mata albarka.
Lokacin da zuri'ar gidan sukaji Abba zai auri Amina sosai sukayi mamaki, haka kuma sunji dad'in yanda Bilkisu tayi, kowa ya jinjina kok'arinta ganin bata tada hankalinta ba, haka zalika bata canza ma Amina fuska ba, shi kansa Abba da yake ta jin kunyarta sai ta nuna masa ba komai, tana dai son yayi mata wani al'kawali, Abba Lawal jiki na rawa yace yayi me take so? Bilkisu tace alk'awalin duk inda akayi posting dinka gun aiki da ni zakaje da yarana, Amina sai dai ta zauna misau.
Abba Lawal shiru yayi yana tunani, ya riga yayiwa Balkisu alk'awali amman yasan yin haka zai zama cutarwa ga Amina da yaranta nan gaba, ba tunanin komai yace ya amince, *shine asalin zaman Amina da yaranta a misau* .
*** ***
Bayan bikin su haka suka zauna lafiya babu wanda yake jin kansu, gaba d'aya dangin mijin Bilkisu suna matuk'ar sonta, sosai suke girmmata sam basa son laifinta domin ta gama sayesu da halayenta masu kyau na fili.
*** **
Bayan wata d'aya da biki sai Amina ta fara fuskantar canji daga Bilkisu, gashi Abba baya zama yana Bauchi wajen aiki, sosai Bilkisu ta canza mata, sam yanzu bata jin dad'in zaman, gashi babu halin ta fad'ama wani domin kota fad'a babu wanda zai yarda.
Domin agaban kowa tana nuna tafi kowa son Amina, abayan idonsu kuma ta cenza mata, sosai take nuna mata *KISHIN MUMMUK'E* wanda yafi komai ciwo, domin gara ka samu wadda zata rik'a dukanka agaban kowa da wadda zata rik'a maka irin wannan kishin domin kashe mutum yake atsaye.
*** ***
Kafin wani lokaci Amina tayi muguwar rama har duhu-duhu ta farayi saboda damuwa, tarasa wanda zata tunkara da damuwarta, idan tace ta fad'ama mijinsu bazai tab'a yarda ba, domin koda yaushe cikin sama Bilkisu albarka yake akan yanda take nuna ma Aminar so, a dangi ma babu wanda zai yarda da ita. Mahaifiyarta ce kawai ta fara tunanin kamar Aminar tana cikin damuwa, amma saboda kawaici irin na fulani yasa ta kasa yi mata magana.
*** ***
Cikin haka Amina ta samu ciki, Balkisu kamar tayi hauka kan bak'in ciki, a gaban mutane kulawa sosai take ba Amina, in su biyu ne gida ko kallon arziki bazata yi mata ba, lokacin da Amina ta fara zuwa awo aka gano tagwaye ne ke cikin cikin ta, tare da Balkisu suka je, tun da suka dawo Balkisu ta kasa zama, tana tunanin mafita, zatayi duk yanda zatayi taga bayan cikin Amina.Kulawa sosai take ba Amina, har Amina na tunanin ko ta cenza ne.
Magani ta samu tasawa Amina a abinci, Amina taci abincin sosai cen zuwa yamma ta fara ciwon mara, sai jini ya fara zuba, koda suka je asibiti kwantar da Amina akayi duk dubaran likitocin sai da cikin ya zube, kwanan Amina biyu aka sallame ta, ta wahala sosai, Abba Lawal yazo ya tausayawa Amina duk ta rame.
Tun daga lokacin da cikin ya zube hankalin Amina ya kasa kwanciya da Balkisu, ranar da cikin ya zube tana gama cin abincin ba a jima ta fara mugun ciwon mara, sosai take taka tsan- tsan da Balkisu, lokuta da dama tafi zama dakin ta, Amina mace maison addini tun suna k'anana suka sauke alqur'ani, tana da ilimin addini sosai, ba kamar Balkisu ba sai dai na sallah.
*** ****
Bayan wasu watani Amina ta samu ciki, sai da ya fara fitowa Balkisu ta gane, tayi duk yanda zatayi ciki daram, har lokacin haihuwa yayi, Amina ta haifi yarta ta farko, jajir da ita sak Abba Lawal duk kyan Amina yarinyar tafi ta, Balkisu ranar da aka haihu taji ciwon ba a gidan Amina ta haihu ba da sai ta shak'e yar ta mutu, Amina na fara jin ciwon ta wuce gida, a gidan su ta haihu, Balkisu sai da aka haihun taji, tazo tana iyayi ba'a kirata ba.
Ranar suna yarinyar taci sunan Mahaifiyar Abba Lawal *KHADIJA* ana kiranta da *Ummi*. Hidima sosai Abba yayi ba laifi lokacin albashin sa nada dama, Balkisu Abun yayi mata bak'in ciki, sai dai itama ta dage akayi hidimar suna da ita, kowa sai da ya yaba mata, hakan da tayi sosai ta sake shiga zukatan mutane.
Lokacin da Ummi ta taso taji su khalifa na kiran Balkisu *Mamee* ita ma tana kiran ta haka, Amina *Anty* ita tama tana kiran uwar Anty.
Bayan haihuwar Ummi Mamee Balkisu ta haifi yara mata ukku *Maryam da Farida da Hafsa, Anty Amina ma ta haifi yarinyar ta, ta biyu Fatima *Mubina*
*** ****
Bayan wani lokaci akayi posting Abba Lawal kaduna, Balkisu tayi murna sosai, lokaci yayi da zata nuna wa Amina matsayin ta a gidan, shiri sosai Balki keyi na zuwa kaduna, Abba ya rasa yanda zai tunkari Amina da maganar, lokacin mahaifinsa da na Aminan duk sun rasu yaran su maza suka gaji saurautar.
Dole ya daure ya fad'awa Amina, Amina baiwar Allah tayi masu fatan alhairi, yan uwan Abba basu damu ba ganin dama da Balkisun ya kamata a fara zuwa tunda itace uwar gida, a nasu tunanin wani karon zai je da Aminan, ko baije da ita ba ai Aminar zata zauna acikin danginta.
*** ***
Ranar da zasu wuce Balkisu sai d'aga kai takeyi ita matar so, Abba Lawal kuma cen k'asan ransa yana jin zaiyi missing Amina don ta daban ce cikin mata. Sun shirya sun wuce sun bar Amina da yan yaranta biyu, Amina har ga Allah ta ji dad'in haka don zaluncin da Balkisu ke ma yaran ma ya isheta, gashi duk dangin su yabon Balkisun akeyi.
**** ****
*MALAN BELLO JUMU'ARE*, haifafen garin juma'are ne, malamin makaranta ne, yayi karatu har matakin *NCE* wancen lokacin yana koyarwa har ya kai headmaster, ya auri matarsa ta farko *Inna Jummai* mace mai mutunci da son jamma'a, yaran su biyu *Nasiru da Zainab* Malan Bello yazo wa Inna jummai da maganar zaiyi aure, bata tada hankalin ta ba tayi masa fatan alhairi
A nan cikin garin jumu'are ya nemi auren wata bazawara *Delu* , duk auren da Delu tayi masifa da tujara kesa a sake ta, Delu masifaffiyar mace ga jarabar kishi.
Zuwanta gidan Malan Bello ta kwantawa Inna Jummai sosai, har Malan din nata yabon ta, Delu kallon su takeyi tana nata shirin, sosai take tunanin yanda zatayi da Inna Jummai don duk cikin mazan da take aure ba kamar Malan Bello yana da rufin asiri yana kula da iyalin sa, *saiwar Lalle Delu tasa aka nemo mata* lokacin Inna Jummai ciwon ulcer dake damun ta ya tashi sosai.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)_
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
( *NEMESIS* )
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
*Bismillahirahamanirrahim*
*page* 3⚜4
*ASALIN LABARIN*
*Abba Lawal misau*, haifafen garin misau ne, dan sarautar Fulanin misau, Mahaifin su ne *Chiroman misau*, duk zuri'ar su farare sosai irin farin fulanin asali, mahaifin sa matan sa ukku, mahaifiyar Abba Lawal ita ce uwargida. Abba Lawal ne yaron ta na Biyar, su ashirin da biyar ne wajen mahaifin su.
Bayan rasuwar mahaifin su Abba Lawal, babban yayan su ya gaji sarautar mahaifin su chiroman misau, gidan su babban gidane, gidan sarauta.
Abba Lawal yayi karatun primary da secondary a garin misau, bayan ya kammalla karatun secondary, ya samu admission a university Bauchi a cen yayi dgreen sa na farko.
Bayan ya samu aiki a local govt a nan cikin garin misau, ya auri matar sa ta farko, *Balkisu*. Asalin su Balkisu barebari ne, Mahaifan Balkisu sun rasu tun Balkisun na k'arama, a hanunun kakarta ta tashi, duk abun tsofafin mata Balkisu ta iya,tun Balkisu na yarinya wani abun in tayi zakayi mamaki a shekarun ta, wayon Balkisu yayi yawa ga mugun kishi, tun tana k'arama take cewa kakar ta bata son kishiya, ita da mijin ta da diyan ta zasu zauna, bazata auri mai mata ba, kakar tayi ta biye mata, ita da kishiya sai lafira.
Balkisu tayi karatun primary, da secondary a garin misau, Balkisu bak'a ce guntuwa mai dan jiki, da yawan mutane lokacin da aka kawo amarya sunyi mamaki yanda Abba Lawal dake kamar bature ya auri bak'ar mace.Bilkisu ko kadan bata samu matsalar zama cikin family su Abba Lawal, sosai take yiwa Mahaifansa da yayun sa biyayya, Balkisu zatayi komai na kyautatawa a dangin Abba, don su sota, kullun kakar ta fada mata takeyi gidan sarauta sai da makirci.
Balkisu mace mai mugun son kanta, kyautatawar da takeyiwa dangin Abba Lawal don su so tane badon Allah takeyi ba, ga mugun kishi, zata iya yin komai akan Abba Lawal, lokacin da sukayi aure abubuwan sai a hankali, so dayawa wata lalura sai an taimakawa Abba Lawal kasancewar albashin ma'aikatan local govt sai a hankali.
Bayan shekaru biyu da auren su Balkisu ta haifi yaron ta na farko, jajir dashi ko kadan bai biyo kalar mahaifiyar sa ba, hidima sosai dangin Abba Lawal sukayi wa Balkisu, bayan sati daya yaro yaci sunan mahaifin Abba Lawal, Muhammad ana kiran sa Khalifa.
Khalifa nada shekara biyu Balkisu ta haifi yarinyar ta, ta biyu zainab, bayan haihuwar zainab Abba Lawal ya samu aiki da Nigerian prison service aka yi posting din sa a Bauchi, duk karshen sati yake dawowa misau.
**** ****
*ANTY AMINA*, itace diya ta goma a gidan *'DAN IYAN MISAU*, Mahaifin ta 'Dan Iyan misau da mahaifin Abba Lawal Wa da K'ani ne, gidan 'Dan Iyan Misau da Chiroman misau makwabtan juna ne, akwai zumunci sosai tsakanin su.
Gidan 'Dan Iyan Misau babban gida ne, matan sa na aure hudu, mahaifiyar Amina itace mace ta ukku, Amina itace diyarta ta biyu.
Amina tayi karatu har matakin diplomer, don mahaifin su yana son karatun diya mace, bayan kammalla karatun aka yi mata aure da mijin ta na farko, sati biyu da auren yayi hadarin mota ya rasu, bayan ta kare takaba ta koma gidan su da zama, sosai Amina ke shiri da Balkisu matar Abba Lawal, duk lokacin da Abba ke Bauchi Amina ce yar firan Balkisu, sosai Amina ta fahimci halin Balkisu wani lokaci har mamakin halayenta takeyi, fuska biyu kega Balkisu bazaka fahimceta ba sai ka zauna da ita.
Duk Abba Lawal yazo week end Amina ta Shiga gidan Balkisu zata matse fuska, da Amina ta gane sai ta dauke k'afar ta gidan, in ya wuce Balkisu da kanta zataje tayi ta yiwa Amina da'din baki, koda taje bata jin da'di, da yake duk gidajen suna ganin mutunci Balkisu sai Umman su Amina tace ba'a haka nan taje mana.
Yaran Balkisu zainab da Khalifa ke cewa Amina *ANTY* nan sunan Anty ya samu Asali, Amina kyakkyawa ce fara sosai, duk zuri'ar gidan chiroman da 'Dan Iya ba bak'i sai dai wani yafi wani fari. Bayan wani lokaci Amina ta sake aure, basuyi shekara daya tare da mijin ya rasu, sosai Amina ta Shiga tashin hankali.
Zuri'ar su kowa ya tausaya mata, bayan ta kare takaba, Mahaifin Abba Lawal ya samu 'Dan uwansa 'Dan iya da maganar a had'a Amina aure cikin yan uwanta, sosai 'Dan Iya yaji dad'i, yace duk wanda aka had'a, Chiroma yace da Abba Lawal za'a had'asu shike da mata d'aya kuma ba Fulani bace, don duk 'yan uwan sa fulani suke aure. Sun bar maganar in Abba yazo weekend za'a daura aure.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)_
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 7⚜8
Saiwan lalle Delu ta zuba kadan cikin fura, ta sa sugar don ya rage d'acin saiwan lallen dakin Inna Jummai taje tace ta tashi ga fura, yini ranar bata ci komai ba, Inna Jummai tace bata iya cin komai, Delu ta matsa ta tashi tasha fura, tasha fura ta kwanta, cikin k'ankanin lokacin cikin ta ya fara wani irin zafi, don saiwan lalle kamar guba ce, sai da Inna Jummai ta fita hayacin Delu ta kira Malan Bello yana wajen aikin sa.
Ya tsorata da yanayin da yaga Inna Jummai cikin sauri aka wuce da ita asibiti, suna isa cikin asibitin ta rasu, likitan da ya dibata ya fada ma Malan Bello sai hank'uri ta cika, Malan Bello sai da aka rik'e sa, kuka yakeyi kamar mace, haka aka dawo da gawan Inna Jummai don yi mata sutura, murna a zuciyar Delu ba'a magana, a idon mutane kuka takeyi sosai kamar gaske.
*** ***
Tun bayan rasuwar Inna Jummai su Zainab da Nasiru suka shiga ukubar Delu, duk mahaifin su na gida zata kula da su sosai in yafita tayi ta gana masu azaba, koda Inna Jummai ta rasu Zainab nada shekaru tara, Nasiru nada shekaru bakwai, ba irin wahalar da basu gani ba, abinci sai taga dama take basu in Malan Bello bayanan, lokacin da ya fara ganewa, Delu ta shiga yin asiri, da abun ya fara cin Malan Bello duk abun da zatayiwa yaran bazai ce komai ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, har Zainab ta kai shekaru goma sha biyar, Nasiru nada sha biyu, Delu nada yaro daya Abu tayi neman haihuwa dayan ma da kyar ta samu, Abu nada shekaru bakwai lokacin, ko yaushe Delu zata kira yaran sai da mugun suna tsinannu debabbun albarka, b'arayi anyi gadon sata . Duk girman Zainab ko wane lokaci aikin takeyi bata ganin mace, ranar da take masu masifa nik'a ta aiki Nasiru cike da bokitin Fenti, a hanya ya hadu da Zainab ta dauka mashi cenjin da
aka basu, da suka dawo gida Abu ya dauke.
Ko yaushe Abu ke dauke mata kudi ta lak'awa Nasiru, Abu tun bai kai haka ba yake sace mata kudi tana lak'awa marayun Allah, so dayawa Abu zaiyi laifi tace Nasiru ne.
*WANNAN SHINE LABARIN DELU*
**** ****
Sai da Abba Lawal yayi wata biyu baije misau ba, so biyu yana shirya tafiya misau Mamee Balkisu na watse ta, farko tace bata da lafiya zuciyarta ke ciwo kamar zata fito, ya fasa, na biyun ana gobe zai tafi, tsakiyar dare ta tashi tana kuwa ga wani mutun yana kiran sunan ta, dole ya fasa tafiyar har wajen mai magani ya kai ta yace aljannu ne ke bibiyar ta.
Har aka yi wattani biyu, makaran ta mai kyau aka sa yaran Mamee a kaduna, Abba Lawal yana samu, zuwan sa kaduna ya samu karin girma zuwa rank din Acp, duniya tayiwa Mamee yanda takeso gida daga ita sai yaran ta, idanun ta sun kara budewa.
Anty Amina tun tana zuba ido Abba Lawal zaizo har akayi wata biyu, sosai ta damu, kayan abincin sunyi k'asa sosai, lokacin daukar yara makaranta ne, tana son akai Ummi da Mubina makaranta, ko yaushe sukayi waya zai ce mata zaizo aiki yayi masa yawa a office.
Wata jumma'a bayan masallaci Abba Lawal ya sauka misau, Anty Amina tayi kwaliyar jumma'a, ta gyara gidan tsaf da yaranta kamar tasan Abba Lawal zai zo, sosai yaji da'din ganin su, yayi kewar yaran sosai, har Ummi, soyyayarta dabance a zuciyar sa.
Kwanan sa biyu ranar lahadi ya shirya zai wuce, Anty Amina tayi masa maganar sa su Ummi makaranta, ya bar komai hannun k'anin sa na karatun yaran. A misau model school aka sa su, private ce mai kyau.
Haka rayuwa Anty Amina da yaranta taci gaba, suna misau Mamee Balkisu na tare da Abba Lawal a kaduna tun dangin sa na magana yaje da Anty Amina har kowa ya k'yalesu ganin ita Anty Aminar bata nuna damuwar ta ba.
Har aka cenza ma Abba Lawal gurin aiki zuwa Enugu cen ma haka Mamee Balkisu da yaranta suka wuce, bai jima Enugu aka mai dashi lagos tare da k'arin girma ya samu Ac, assistant controller na lagos state Balkisu duniya tayi mata da'di yanda take so haka takeyi.
Controller na lagos din dan kano state, sosai suke mutunci da Abba Lawal, *Alhaji Muhamud kazaure* a unguwar da yake da zama Abba Lawal ya samu gida, hul'da sosai tsakanin matar Alhaji muhamud *Hajiya Rabi* da Mamee yaranta biyu mata *Fadila da Laila* Hajiya Rabi rik'akkar yar bariki ce idanun ta a bude suke, sosai tayi imani da asiri don batada dogon ilmin addini.
Ba itace matar Alhaji muhamud ta farko ba, matarsa ta farko ta rasuwa *Hajiya Badiya* yaron su daya, *Auwal* tun Auwal nada shekaru goma ta rasu, Alhaji muhamud bai k'ara aure sai da Auwal ya kare secondry school, K'anwar Alhaji muhamud *Baba Ladidi* ita ke zama da Auwal har ya kare secondry school.
A kaduna Alhaji muhamud ya hadu da Hajiya Rabi, da asiri da shige -shige ya aure ta, sosai take nunawa Auwal kulawa kamar ita ce mahaifiyar sa, bata son zaman Baba Ladidi tare dasu don zata hanata cimma burin ta, tayi duk yanda zatayi Baba Ladidi ta bar gidan bata ci nasara ba, har Auwal ya samu admission a UK ya wuce zai karanta medicine, Auwal yaron ne mai hankali da natsuwa ya samu kyakkyawar tarbiya ga Baba Ladida.
Lokacin da Awal zai wuce Uk kamar Hajiya Rabi tayi hauka, bayan tafiya Awal ta haifi Fadila sam bata ji 'dadin haka ba, taso namiji, bayan shekaru biyu ta haifi Lailai tayi ta yawon asibiti bayan haihuwar Laila ko zata samu wani cikin, bata samu ba, dole ta hank'ura da alkawalin sai taga bayan Awal, yazan daga ita sai yaran ta, bayan Awal ya k'are ya zama cikaken likita ya dawo gida, murna wajen Baba Ladidi ba'a magana.
*** ***
Hajiya Rabi bak'in ciki yayi mata yawa, taso jirgi ya fadi dashi ya mutu ta huta, asiri ta shiga nema taga bayan Awal bata ci nasara ba, karshe ta samu wani bakanike ya kwance break din motar Awal din, da yammah ya fita yana tafiya yayi birkin mota yaki yi, mumunan hadari yayi, ya samu internal injury a kai tunanin sa gaba daya ya koma na yara, duk komai game da rayuwar sa ya mance, Alhaji Muhamud ya kaishi asibitoci kala-kala abun ba nasara, ana ta rok'on Allah.
Hajiya Rabi ba haka taso ba, taso ya mutu, Baba Ladidi ko yaushe ta kalli Awal kuka takeyi sosai, komai nasa ya koma na yara, ya mance kowa rayuwarsa.
*** ***
A haka Mamee Balkisu ta hadu da Hajiya Rabi, ta dalili Hajiya Rabi Mamee ta fara yin asiri, wani lokacin sam Abba Lawal mancewa da Anty Amina da yaranta yake yi, duk abin da Mamee tace shi zai yi, wani zuwa da sukayi misau har Mamee din, ta bashi shawaran ya maida yaran makarantar gwamnati baida bambamci da na kudin, ba wani tunani ya debe yaran ya maida su, Anty Amina Abu yayi mata ciwo sosai, da tayi masa magana yace yaranta ko nasa, da ta matsa yace duk ta sake yi masa maganar karatun su bakin auren ta.
Duk yaran suka dawo gida ita keyi masu lesson a gida, tana masu magana da turanci don su iya, don shine matsalar makarantun gwamnati, cikin ikon Allah yaran na ganewa sosai, haka rayuwar Anty Amina da yaran taci gaba.
** **
Bayan wani lokaci Alhaji muhamud ya samu CG, controller general Abba Lawal ya samu DC, depty controller general, suka koma Abuja, har lokacin nemawa Awal magani akeyi ba nasara, abin ma sai k'aruwa yakeyi, Hajiya Rabi nata zuba asirin ta, aminci sosai tsakaninta da Mamee.
Alhaji Muhamud baida damuwar da ta wuce ta Awal, wani lokacin gaba yake sa Awal yana kuka da hawaye, ko yaushe Awal kayan wasan yara ne yake wasa dasu, lokacin da yake lafiya lau dan gaye abinsa ga tsafta, kyakkyawa ajin karshe.
**** ****
*CIGABAN LABARI*
_Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
( *NEMESIS*)
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 9⚜10
*CIGABAN LABARI*
Sosai Anty Amina ta damu don Ummi tafi Mubina hank'uri, sam Mubina bata da hank'uri, akwai wani zuwa da Abba Lawal yayi ta same sa, tace Abba me yasa mu baka zuwa damu Abuja?, me yasa kafi son Mamee kan Anty, sai ka tafi kabar mu, ka dade baka dawo ba. Abba Lawal fada yayiwa Anty Amina tana sawa yaranta magana a baki, Anty Amina har rantsuwa tayiwa Abba Lawal acewan bata fadawa Mubina hakan ba, yak'i yarda, karshe yace tayi ta koyawa yaranta mugun hali mata ne, zasuje gidan wani.
Anty Amina ranar har kuka tayi, tayi ta wa Mubina fada, duk da lokacin shekarun Mubina goma sha biyu tana jss2 a makaranta, ranar da suka dawo makarantar Mubina na kuka yini ranar ko abinci k'in ci tayi, Abun ya damu Anty Amina, ko Ummi ta lura tana da damuwa tana wayancewa dai ne, bayan yaran sun wuce islamiyya zaune tayi tana nazari me zata yi?
Wa zata fadawa damuwar ta?
Farkon zuwan su Mamee Balkisu inda Abba Lawal ke aiki dangin sa na magana, daga baya kowa bai cewa komai, ko yayan su Abba din Chiroma, ada cen yakan yiwa Abba fadan ya bar Amina, daga baya shima bai cewa komai, in ma tayi magana zasu ce me ya rage ta da shi. Bayan ya samu DC babban gida ya gina masu a nan layin makama, komai yasa cikin gidan, ya ajiye masu mota daya mai masu hidima, da masu aiki.
Anty Amina ganin tunani bazai fishe ta ba, ta tashi ta dauro arwala ta fara karatun alqur'ani ta dade tana rok'on Allah ya kawo mata mafita akan karatun yaranta, sosai tasan suna cutuwa makarantar gwamnati ba'a karatun kwarai, akwai wani zuwa da Mamee tayi da yaranta, ko Hausa basu cikayi ba turanci suke yi sosai, saboda zama bariki da suka yi, sosai hakan ya bata sha'awa, ina ma ace itama yaranta zasu samu irin wannan ilimin.
Bayan da ta gama karatun sosai taji sanyi a zuciyar ta, har yaran suka dawo, Mubina ta sake sai fira sukeyi da Ummi, Anty Amina sosai taji da'di da kwanciyar hankali ganin yaran sun sake, zata nemi mafita ko don gaba, kada rashin samun karatun kwarai ya shafi rayuwar su.
Bayan sallar isha'e suna falon Anty Amina suna lesson Abba Lawal ya kira Anty, ido ta tsurawa wayar yau tsawon kwana biyu bai kirata ba, ta kira sau daya bai daga ba, ya turo mata yana meeting in ya k'are zai kirata, har aka kwana bai kira ba, har wayar ta katse bata d'aga ba, ya sake kira, a na biyun ta dauka, cikin girmamawa ta gaishe shi.
Bayan sun gaisa ya tambayi yaran tace gasu nan suna lesson, Abba Lawal yace gamu airport tare da Mamee zamuje china wajen wani aikin, sai bayan sati biyu zamu dawo, za'a kawo maki kudi, duk abubuwan da babu ki rubata za'a kawo maki, ranar saturday ki shirya da yara da Lami driver zai kaiku kano ku duba Hajiya Ladidi k'aunar CG tayi rashin Lafiya, naso Mamee taje ga tafiya nan zamu yi, zamu wuce sai mun dawo ba komai ko? Anty Amina tace ba komai Allah ya kaiku lafiya. Abba Lawal ya kashe wayar.
Ummi sai kallon Anty Amina take yi, ta fahimci ranta ya baci ko me Abban nasu yafada mata? Anty Amina ta tashi tace suyi home work din da aka basu zata shiga toilet ta fito.
Kallo suka bita da shi, Ummi sanin halin Mubina ta dauke mata hankali, tace ta kawo home work din ta koya mata, Amina dakin ta shiga zama tayi tana zubar da hawaye, wannan wane irin zalunci ne mutanen ke mata? zaman ta da Abba Lawal sau daya taje hajji lokacin yana controller a lagos ya biya masu ita da mahaifiyarsa, sun tafi hajji da ummara shi da Mamee yafi sau biyar.
Zaman sa depty controller nan bata iya kirga fitar da sukayi waje, duk zasu fita sai yana airport ya ke kiran ta, kuka Amina ta fashe da shi, ta gaji da zaluncin mutanen zata nemi mafita.
Wanke fuskarta tayi kar su Ummi su gane, falon ta koma sosai Ummi ta gane akwai damuwa a idon Anty Amina, Anty Amina na shigowa falon ta kirkiro murmushi tace gobe zamuje kano diba mara lafiya a gidan Alhaji Muhamud CG Abbanku.
Sosai suka yi murna zasu fita wajen misau, Mubina tace Anty yaushe Abba zai zo? Anty Amina tace yayi tafiya in ya dawo, shiru sukayi, Ummi a ranta tace nasan akwai dalilin bacin ran Anty, Abinda akewa Anty yayi yawa an tauye su an danne HAK'K'IN Anty.
**** *****
Rayuwa irin ta turawa yaran Mamee keyi, anfi ba karatun boko muhimmanci kan karatun Allah, basa zuwa islamiya, Malamin dake koya masu karatu a gida, in yazo zai yi awa daya yana jiran su fito, in yazo Abba Lawal na gida zasu fito kamar gaske.
Duk yaran har Khalifa da ke shirin ha'da dgreen sa a turai bai sauke alqur'ani ba, sallah ma manya suka dan iya k'ananen yaran ana dai yi, in yaran Mamee zasuyi birthday kamar za'a yi bikin haihuwa ko aure, duk rayuwar turawa ita akeyi.
Ba wata cikakkar tarbiya, Zainab tana level2 a wata private university, in zataje lectures jeans take sawa in Abba baya gida, Abban bai cika zama gida ba yanayin aikin sa, Maryam ma tana ss3 secondry a best school a Abuja, Farida ss1, Hafsa jss1, tsarin Mamee tsarin turawa ne, tun haduwar su da Hajiya Rabi rayuwar Mamee ta cenza.
Idanun yaran a bude suke sosai tashin lagos da Abuja, komai na yan bariki akeyi a gidan Abba Lawal yayi fada basa ji, ko in yana nan ba'a yi sai yayi tafiya ko ya fita, ko yaushe cikin matsalar yake da Mamee kan yaran, bai iya yin komai, sai abinda Mameen tace.
Wani lokacin in abun ya sake shi yana daukar mataki, akwai lokacin da yace Mamee ta bar masa gidansa, duk ta bata tarbiyan yaran, tana kuka ta samu Hajiya Rabi suka je wani gari mai suna *kuje* a kauyen Abuja, Abba da kansa ya kira Mameen. Mamee ta cusawa yaranta k'in tallaka ko kadan in bakada kudi yaran Mamee basa hul'da da kai.
*** **
Bayan Abba ya kare waya da Anty, Mamee na gefe duk abun da yake fadi tanaji, sosai ranta yayi mata da'di bata da burin da ya wuce a wulak'anta Anty Amina da yaranta, duk wanda ya auri mijinta bazai zauna lafiya ba, Abba Lawal mijin tane ita daya, duk macen da ta aure shi zata zama yar kallo. A daren jirgin su ya tashi zuwa china.
**** ****
A kano Alhaji Muhamud ya dawo da Auwal, Baba Ladidi ta matsa dole ya maida su gidan sa na kano, mahaifin Alhaji Muhamud dan kazaure ne, a kano yayi rayuwarsa, duk 'yan uwan Alhaji Muhamud din a kano suke, Baba Ladidi bata yarda da Hajiya Rabi shine ta matsa zasu koma kano, in lokacin zuwa asibiti yayi zasu dawo Abujan a tafi.
Lokacin da zasu wuce Hajiya Rabi da'di sosai taji, dama zaman Baba Ladidi gidan ya ishe ta, gidan zai koma ita da yaranta, ta rasa wace irin matace Baba Ladidi tayi asiri yak'i tasiri(Hajiya Rabi kin makara Baba Ladidi Allah ta rik'e).
Sosai Baba Ladidi ta samu kwanciyar hankali bayan sun koma kanon, don ganin take yi a Abuja Hajiya Rabi zata iya cutar da Auwal sam bata yarda da matar ba, gara zaman Auwal kano, zata cigaba da neman masa taimako har Allah yasa a dace, abinda ke bata tsoro abun sai gaba yakeyi.
Bayan sun koma kanon, Baba Ladidi tayi rashin lafiya, kwanan ta biyu asibiti, Abba Lawal da Mamee zasuje dibata tafiya ta kama Abban, shine yace Anty Amina ta shirya suje kano su debo Baba Ladidin, hul'dar Abba da Alhaji Muhamud sun zama tamkar yan uwa, sosai Abba ke girmama sa, komai Alhaji Muhamud zaiyi zai shawarci Abban.
**** *****
Duk da Malan Bello ya biya hamsin din da su zainab da magaji k'aninta suka b'atar , sai da ta hana masu abincin dare, Magaji sai kukan yunwa yake yi, Zainab ma tana jin yunwa, kukan da magaji keyi ne damuwar ta, sai karfe tara Malan Bello ya dawo, a dakin da suke kwana ya same su, Magaji na kuka rik'e da ciki, abincin sa ya dauko ya basu lokacin Delu tayi bacci.
Abincin suke ci kamar dabobi sosai yunwa suke ji, Malan Bello fita yayi ya siyo hura ya k'ara masu, yasha sauran, sai da suka yi bacci yaje ya kwanta.
Tun da asuba Zainab ke tashi tayi shara wanke-wanke, tayiwa Inna Delu diban ruwa, koda zata kare suyi wanka suje makaranta lokaci ya tafi, wani zubin ko wanka bata samu gashi girma ya taso mata, shekarunta shabiyar Magaji nada goma. Zainab ba aikin wahala da Inna Delu bata sata, tun bata saba har ta saba, samun hutun ta in taje makaranta.
Ko makarantar sai da Malan Bello ya ha'da da shugaban makarantar yazo har gida yacewa Inna Delu duk bata barin yaranta na zuwa makaranta zai yi k'ararta gurin maigari, dole ta barsu zuwa makaranta.
Duk sukaje makaranta Abu baya zama makaranta, yawon sa yake zuwa in anyi sa'a ya zauna ba ya maida hankali, haka rayuwar marayun Allah ta kasance cikin ukuba da takurawa, Inna Delu bata tunanin HAK'K'IN marayun ko kadan, ga HAK'K'IN kisan mahaifiyar su.
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
07064551049
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 11_12
Matsi sosai Zainab da Magaji ke fuskanta wajen Inna Delu, Abincin da take basu Sam baya Isar su, in suka samu k'oshi da kyau, Malan Bello ne zai basu cikin nasa, ko shi in Inna Delu bata gida, don mugun shakkar ta Malan Bello yake yi, sauk'in daya bata cika zama gida ba, tana yawon dillanci, Abu ma duk ya dawo gida yunwa yake ji, in zata fita sai ta tarawa zainab aiki.
Wani aikin k'yeta dai ce, Zainab tasha yi mata wanki tace bai wanku ba, duk unguwar ba Wanda ya isa ya fadawa Delu gaskiya kowa tsoron tijara ta yake yi, akwai makwabciyar su *Maman Sadiya* sunyi mutunci sosai da Inna Jummai ita kadai ce ke taimaka masu in Inna Delun ta fita,Lokacin da Zainab ta fara period tsoro taji sosai.
Tana tsoron ta fadawa Inna Delu, tace maza take bi, don ko yaushe ce ma takeyi sai tayi cikin shegi sai ta barwa zuri'ar su abun kunya, Zainab na kuka ta samu Maman Sadiya ta fada mata, Maman Sadiya tace ta daina kuku girma ne yazo mata, tayi mata bayanin duk yanda zatayi, ta k'ara koya mata wankan tsalki.
Ta siyo mata pad da pants ta nuna mata yanda zatayi, tace kar ta fadawa kowa har Baba Delu, Maman Sadiya sosai ta tausayawa Zainab irin wanan girman in yazo wa diya mace, ya dace ace akwai kulawa sosai, Sam ba ruwan Baba Delu buk'atar ta
daya bautar da Zainab ke mata, abun da yasa tace Zainab din ta boye tayi imani duk Delu tasan Zainab ta fara al'ada sai tayiwa rayuwar ta illah.
Har Zainab ta k'are al'ada Baba Delu bata sani ba, wani lokacin in ta fita dillancin sai yammah, bata damu da sunyi sallah ba ko basuyi ba,
ko ita kanta sai ta Ha'da sallah biyu tayi, Malan Bello ya yi ta shiga islamiya tak'i shine ke koya mata, wani ta gane wani bata ganewa, cen wajen yawon dillancin suka hadu da *GAJE*.
Gaje sani'ar ta daukar yara tana kai su aikatau gida-gida, gari-gari in ta samu iyayen da suka aminta da kai yaran su wani garin, sosai Gaje ta kwadaitawa Inna Delu samuwar da zatayi in ta bada yarinyar ta aikatau, Inna Delu ta shiga tunanin, tana tunanin yanda zatayi da Malan Bello, tana tunanin in ta bada Zainab aikatau wa zaiyi mata aikin gidan, sai dai zuciyar tafi karkata kan ta yardar Zainab taje ko ba ko mai Zata samu kudi, Zainab zata ita kunso abun kunya ta dawo, daman Gajen zata iya kai mata zainab din gidan Karuwai tayi masu aikatau.
**** ****
Sai bayan kwana daya Abba Lawal ya kira Anty, bayan sun gaisa ya fada mata sunyi sammakon tafiya kano gobe, ta rok'i alfarma su kwana daya kano gidan yayarsa, matar *WALI KANO* Anty Amina nata addu'ar ya barsu kwana kanon, yace Allah ya tsare sosai Anty Amina taji da'din hakan.
Cike da farinciki ta kira yaya Maryam tana fada mata zasu zo kano, ya Maryam yayar Abba Lawal ce uwa daya uba daya, suna shiri sosai da Anty tun kan Anty Amina ta auri Abba Lawal, yaya Maryam walin Kano take aure ita ce matar sa ta biyu, tana da yara bakwai da shi, tanada mutunci.
Ranar assabar da sasafe Anty Amina da yaranta suka hau hanyar kano, bayan ta shiga tayiwa Umman ta da Umman su Abba sallama, sai kusan azahar suka isa kano, gidan yaya Maryam suka wuce, sosai taji da'din ganin su, sosai zaluncin da akewa Anty Amina yake damun yaya Maryam, ko tayi niyar magana bata iyawa ko tayi maganar batada amfani don ba ji Abban zaiyi ba, yanzun ma tasan akwai dalilin Barin Anty Amina tazo wani abun da ya shafe sa, komai na Abukanin hul'dar sa Mamee ce
Sosai ta tarbe su, duk mata da yaran gidan su zo suna masu sannu da zuwa, bayan sunci abinci, Anty Amina ta fadawa yaya Maryam dalilin zuwan su, yaya Maryam tace Mameen bata nan ne, Anty Amina tace tare sukayi tafiya, sosai yaya Maryam ta damu, tana
jima k'anin nata ranar da HAK'KIN Anty Amina zai kamasu zaluncin yayi yawa.
Anty Amina tace yaya in bawan ya dame in ba, duk inda zasuje sai sun dawo, damuwana karatun su Mubina, ta kwashe abun da ya faru ranar da Mubina ta dawo tana kuka a makaranta ta fada ma ya Maryam, ya Maryam tayi shiru tana nazari abun na Abba Lawal akwai tsoro, me ke damun sa? hankuri taba Anty Amina tace zata yi wani abun kan karatun yaran, suje su dawo sai suyi magana.
Shiryawa sukayi zuwa gidan Alhaji Muhamud, cikin kyakyawar shiga, ko yaushe Anty Amina da yaranta zasu fita, abaya suke sawa, bak'a ko wani kala, duk kyan kayan da suka saka zasu dora abaya kai, sunyi kyau sosai cikin bak'ar a baya mai ratsin ja.
Dan Lami driver yasan gidan Alhaji Muhamud dake unguwar zoo road, su Ummi sai kale-kale sukeyi duk rayuwar su, a misau ne, wani k'aton gida suka tsaya, masu kakin prison ne ke gadin gidan, gate din gidan aka bude masu, suka shiga cikin masu gadin gidan, daya ya yi masu jagora zuwa gefen da Baba Ladidi take.
Sun samu bak'i a falon har lokaci mutane na zuwa gaida Baba Ladidi, bayan an gaisa Anty Amina tace daga Misau suke gidan Abba Lawal, Baba Ladida cikin farinciki suka k'ara gaisawa tana jin Alhaji Muhamud na fadin Abba Lawal nada wata matar misau, sosai Baba Ladidi ke mamakin Kyakyawar mace haka.
Yaran ta ma masu kyau, masha Allah, abinci da abin sha aka kawo masu, sai jan Anty fira Baba Ladidi ke yi lokaci daya taji Anty Amina tayi mata Sam ba irin rayuwar su Mamee da Hajiya Rabi ke gare ta ba, sun jima suna fira Anty Amina tace zasu wuce, gobe sammako zasuyi su ko ma misau.
Tace su jira Alhaji Muhamud na hanya, tun dazun yace sun kusa kano, suna zaune Auwal ya fito, hannusa rik'e da jirgin wasan yara da mota, ido Mubina ta tsura masa mamaki takeyi babba na wasa da kayan yara, Ummi hankalin ta na kan wayar Anty tana game, bata ga shigowarsa falon ba.
Gefen Baba Ladidi ya zauna yana wasa da jirgin, Ummi ta dago suka ha'da idanu da Auwal kallon ta yayi, ya dauke Kansa yaci gaba da wasar sa, Ummi gabanta ne ya fadi, kallon sa takeyi tunanin ko bayada hankali babba da shi yana wasar yara.
Baba Ladidi tace Auwal baka ga ba'ki, ba ka gaida su ba, umman kace ta misau, Auwal tashi yayi yaje ya zauna kusa ga Anty sai kallon ta ya keyi yana murmushi, Anty Amina murmushi tayi tace Auwal kallonta yayi.
Anty Amina tanajin labarin Auwal a wajen Abba Lawal, Baba Ladidi tace Amina ke ta dabance duk bak'o da yazo gidan nan, Auwal gudu yakeyi, ke har yana zama kusa gare ki.
Sallamar Alhaji Muhamud ta katse fira, sosai yaji dad'in ganin su, yasan Anty in yaje misau yaran be duk zuwan da yakeyi basa haduwa, sai jan Mubina yakeyi da fira, ya tambaye ta ajin ta Nawa tace jss2 ya tamabaye makaranta su, tace govt day misau, shiru yayi yana nazarin makarantar gwabnati ko ba makarantar kudi a garin ne, zai bincika yaji.
Sai dare suka bar gidan, alhairi sosai Alhaji Muhamud yayiwa yaran, Auwal rike rigar Anty Amina yayi da zasu wuce ya nuna hannun alamar zai bisu duk mamaki abun ya basu da lalami Baba Ladidi ta jasa zuwa cikin gida, Anty Amina sosai ta tausayawa Auwal ta amshi num Baba Ladidi zasu rak'a gaisawa.
Tun a mota Mubina ta fara tambayar Anty Amina waye wanan babba yana wasa da kayan yara, ko bayada hankali ne? Amina tsawa ta daka mata, tace ta cika surutu da hankalin sa bayada lafiya ne, Ummi kallon Any Amina tayi tace Anty me ya same sa? Anty Amina tace hadari yayi, duk shiru sukayi suna tausayawa Auwal din.
**** ****
Hajiya Rabi bayan Alhaji Muhamud ya wuce kano, daki ta shiga tana murna, magunguna Auwal da aka kawo ta cenza, lokacin da Dr ya kawo Alhaji Muhamud bai bude ya ajiye ya fita wajen bak'in da yayi
Cenza magunguna tayi da wasu, wani likitan ta nema ta bashi kudi sosai, ya bata magungunan duk Auwal nashan su tunaninsa bazai dawo daidai ba, Alhaji Muhamud ya dauki magungun cike da addu'ar su zama waraka ga Auwal.
Ummu Asma'u(Sa'adatu)
07064551049
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifina, Allah ya maku Rahama.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 13_14
Bayan wucewar su Anty Amina, Alhaji Muhamud ya ba Baba Ladidi magunguna, yace likitan yace da yardar Allah in aka tsare magungunan komai zaiyi dai-dai, tunanin Auwal din zai dawo, Baba Ladidi amsar maganin tayi tana fadin ameen Allah yasa haka, ruwa ta dauko ta zaunar da Auwal ta bashi magani, rik'e maganin yayi yana kallo, Baba Ladidi tace yasha, amsa yayi yasha maganin.
Bai jima da shan maganin ba yayi bacci, Baba Ladidi sai addu'a takeyi Allah ya kawo wa Auwal sauk'in wannan lalura, haka Auwal yaci gaba da shan maganin abun ko yaushe ba sauki, yanda suke tunanin maganin zaiyi ba cigaba, Baba Ladidi sosai hankalin ta ya tashi, wasu abubuwan da baiyi a da yanzun abun nason ya zama kamar tab'in hankalin.
Akwai lokacin da Auwal ya dauko wani karfe plasma tv dake jikin bangon ya fasa da karfen tv ta fashe, ranar Baba Ladidi kuka tayi sosai dole sai da aka rufesa cikin daki, sai yayi ta rik'e kansa kamar kansa na ciwo, cikin tashin hankalin Baba Ladidi ta kira Alhaji Muhamud cikin dare ya iso kano.
Tun da safe suka wuce Abuja, duk drugs din da yake sha akayi stopping, abin yayi sauki, satinsa daya asibiti aka sallame sa, Baba Ladidi ta rok'i Alhaji Muhamud a bar maganin haka, suyi ta rok'on Allah, ta lura lokacin da Auwal ya fara shan maganin da aka kawo masa abun yayi muni, abun takaicin sunzo da drugs din Abuja, an nemi maganin an rasa, har Alhaji Muhamud nacewa ko kano suka bar maganin.
Hajiya Rabi na gefe tana kallon su, tun zuwan su ta dauke drugs din, don tasan in anje asibiti zaa tambayi maganin, likitan ta kira tayi masa bayanin yace, ta nemi wani hanyar k'ara basa magungunan za a iya ganeta, don maganin ya ba Auwal reaction dayawa yanda tayi masa bayanin .
Hajiya Rabi zaune tayi tana tunanin meye abun yi, dole ta dauki mataki bazata yarda Auwal ya warke ya dawowa tunanin sa ba, ko yau Alhaji Muhamud ya mutu gadon Auwal gadon yaranta mata biyu, dole Auwal ya bar duniya, me zatayi? asirin tayi bai ci ba, taso ya mutu da yayi ha'darin mota bai mutu ba, wanan karon zata dauki babban mataki akan Auwal, (mata masu duniya duk akan kishi da gado sam ba tsoron Allah a zuciyar Hajiya Rabi ko ya zatayi da HaK'K'IN Auwal? .
Har su Anty Amina suka isa gidan ya Maryam ba Wanda ya k'ara magana, Ummi tunanin kala-kala takeyi Auwal ya bata tausayi sosai, abun sosai ya tsaya mata a rai, Mubina tana son magana tana tsoron fadan Anty Amina dole tayi shiru, Anty Amina ma tunanin Auwal din takeyi, tayi alk'awalin duk tayi sallah zatayi masa addu'a Allah ya kawo masa sauki.
Ranar Lahadi sammako su Anty Amina suka yi komawa misau, alhairi sosai ya Maryam tayi masu, ta fadawa Anty Amina ta k'ara hankuri tasa Allah gaba da yardar Allah komai zai dai-dai zai wuce wata rana kamar ba'a yi ba, sai da suka biya sahad store tayiwa su Mubina sayayya sosai, da mutanen gidan su da gidan su Abba Lawal.
**** ****
Sai bayan sati biyu su Mamee suka dawo, Mamee kaya sosai ta siyo a China, gadaje kujeru na sayarwa, kudi sosai Abba Lawal ya bata, da zasu wuce yaran Mamee da masu aiki ta barsu yanda suka ga dama haka suke yi har uwayen suka dawo, Abba bai so hakan ba, yaso ta dauko yan uwanta ko cen misau tak'i tace ba yara ne kowa zai iya kula da kansa.
Tun tafiyar su duk dare sai su Maryam sun fita night party tare da friends din su yaran masu kudi, masu gadin ba ruwansu, suna tsoron Mamee ba wanda ya isa yace ga laifin yaranta, duk mai aikin da yayi kaudin magana bakin aikinsa kenen.
Yanda su ke so haka suka yi har su Mameen suka dawo, tun da suka dawo Abba Lawal bai je misau ba, har aka yi wata daya, duk abun buk'ata zai tura masu, sosai Anty Amina ta damu su Ummi sunyi magana Abban su bai zo har sun gaji.Umman su Abba Lawal in tayi magana sai yace aiki yayi masa yawa.
Ranar jumma'a Abba ya shirya zuwa misau, wata kusan biyu rabon sa da misau, yaje office din Alhaji Muhamud yana fadi masa zai je misau, Alhaji Muhamud yace ya gaida Mubina da Ummi, har Abba Lawal zai tashi Alhaji Muhamud ya tuno yana son tambayarsa karatun yaran.
Alhaji Muhamud ya tambayi Abba Lawal me yasa bazai dawo dasu Mubina makaranta nan Abuja ba? zai fi karatun misau, saboda ya tambayi Mubina tace a government day misau suke zuwa, Abba yace baya son barin Anty Amina ita daya cikin gidan ne, in aka dauke yaran bazata ji da'di ba.
Alhaji Muhamud yace gaskiya ne, a nan misau a nema masu makaranta mai kyau, zai fi makarantar gwanati, Abba yace zaa cenza masu makarantar yayi masa sallama ya wuce, sosai yaji haushin surutun Mubina, sai magrib ya isa misau da escort din sa, Anty Amina kwatsam ta gansa, bata nuna masa komai ta tarbe shi sosai.
Abba Lawal yana ta kame-kame aiki yayi masa yawa, bayan sallar isha'e ya shiga wajen Umman sa wanan karon tayi masa fada sosai, yayi adalci tsakanin iyalin sa, abun da yake yiwa Amina ba dai-dai bane, hank'uri ya bata zai gyara, gidan su Anty Amina ya shiga wajen Umman ta, sai kame-kame yakeyi aiki yayi masa yawa shine ya kwana biyu bai zo ba, bata ce komai, tasan abun da yake yiwa Aminan bai kyautawa.
Sai goma ya samu shiga cikin gidan duk lokacin da yazo, mutane sosai ke zuwa gidan neman taimako, Abba Lawal yana da alhairi sosai, a falon Anty Amina ya sameta da su Ummi suna homework tasha gayunta tayi kyau, dogowar rigar material tasa ta daura dankwalin rigar kamar hula, kamshi ko ina cikin falon, cikin yaran Abba ya zauna yana diba littafan su.
Mubina ya kalla yace ranar monday bazan wuce ba sai na cenzawa autan Anty makaranta wane makarantar kike so?, Mubina tsale tayi cike da farin ciki tace Abba misau model school Inda muka fara farko makarantar nada
kyau, Abba yace ranar monday zamuje, Ummi tace Abba zaka kai mu school da kan ka?.
Yace zan kai Ku, Ummi murmushi tayi taji da'di sosai, Anty Amina bata ce komai ba, sai tunanin takeyi wannan karon har Monday zai kai, ba abinda yayi mata da'di irin cenzawa yaran makaranta da yanda ya nuna kulawar sa, bayan yaran sun kare homework din suka wuce dakin su.
Abba da Anty na kwance sai hankuri yake bata, bata ce komai ba, irin hakan tasha faruwa in ya tafi dadewar da zaiyi sai yafi na bayan, Abba rungume Anty Amina yayi sosai yake jin natsuwa in yana tare da ita, Mamee tayi Neman layin Abba bata same sa ba, taji ciwon abun sosai, ita za a yiwa rainin wayo zatayi maganin su.
**** ****
Lokacin da Baba Delu tayiwa Malan Bello maganar kai Zainab aikatau, rufeta da masifa yayi sosai Baba Ladidi taji mamakin yau ita Malan kewa masifa haka dole ta tashi tsaye, yace duk ta tura masa yarinya wani aiki sai yayi k'ararta Allah bai hana masa abun lalura iyalin sa ba, cikin fushi ya fita gidan ransa ya baci sosai dai- dai yana da rufin asirin sa me ya rasa da za'a kai masa yarinya aikatau.
Duk maganar da suka yi Zainab naji hankalin ta ya tashi sosai, tasan halin Baba Delu tunda ta fara, bazata k'yale su ba, saukin ma wannan karon taga Abban su ya taso mata, Magaji dake kwance gefen ta, ta kalla shi take tausayawa tun rasuwar Umman su, yaron ke cikin wahalar rayuwa.
Dangin Mahaifiyar su sunso su dauki Magaji Malan Bello yak'i yarda sunyi biyar sa yak'i, Zainab kuka sosai takeyi, Inna Delu na daki ta tunanin yanda zatayi bata da tashin hankalin da yafi ta bude ido taga su Zainab cikin gidan, kashe mahaifiyar su da tayi an kashe maciji ba'a sare kan sa ba, bata da kwanciyar hankali in ba ta salwantar da rayuwar yaran ba.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Asma'u)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Gaffara.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 15_16
Ranar monday Abba Lawal ya kai yaran makaranta, model school misau, sosai yaran ke cikin farin ciki, Abban su ya kai su makaranta karo na farko tun shigar su makaranta, Ummi ss2 aka dauke ta, Mubina js2, sai da komai ya kammalla ya bar makaranta, Anty Amina sosai ta nuna masa farin cikin ta, abun yayi masa da'di ganin ita da yaranta cikin farin cikin, sai karfe goma ya bar misau zuwa Abuja cike da kewar yaran da Amina.
A hanya ya kira Mamee bata 'daga ba, ya kira ya kai sau biyar bata 'daga ba, duk ya damu ko kadan baya son damuwar Mameen yana gudun bacin ranta sosai, yasan don ya kai monday ne, ranar da zai tafi misau din ce mata yayi Sunday zai dawo Abuja, fadan da mahaifiyar sa tayi masa, yana son kai yaran makaranta da kansa shine yasa ya kai monday.
Koda ya shiga Abuja office ya wuce yana da meeting ya turawa Mamee text ya shigo gari yana da meeting, sai bayan magrib ya koma gida, tun a office ya shirya abun da zai fa'dawa Mamee. A bedroom din ta ya sameta sai cika take tana batsewa anyi mata laifi yayi kwana ukku a misau, gefen gadon da take zaune ya zauna yace baya da lafiya tun zuwansa misau din.
Yau ma kamin ya taso sai da aka yi masa allura, Mamee cike da kulawa take tafa jikin sa, tace zata kawo masa abinci yaci ya sha magani, (hattara mata kan bak'in kishi har sai mijinka ya ha'da maka da karya, duk tsawon lokacin da yayi abuja, kwana ukku da yayi misau shine laifin sa)
Abba Lawal kwantawa yayi kan gado, Mamee cikin rawar jiki ta fita ta dauko masa abincin yace bazai iya zuwa table ba baya jin dadin jikin sa, Mamee damuwar ta in ba Anty Amina ce ta dauke masa hankali ba, alk'awali tayiwa rayuwar ta, Abba Lawal mijin tane ita daya, ba macen da zata aure sa ta gane komai .
Ranar Abba Lawal Kulawa sosai ya samu wajen Mamee. k'arfe tara Abba na falon sa yana kallon network news aka budewa Maryam get ta shiga gidan ta dawo birthday party wata friend din ta, tun dawowar Abba Mamee ta kira wayar ta bata zuwa, tana son tace mata ta dawo gida, Abba jin bude get din ya fito harabar gidan, tun dawowar sa, ya lura Maryam bata gida.
Tana ganin Abba jikin ta ya hau rawa, wani matsatstsan wando tasa da body hug duk shape din jikin ta ana ganin, ba yanda zatayi dole ta fito, Abba na ganin shigar da Maryam ta fita dashi ransa ya baci sosai, 'yarsa ke wannan shigar kamar diyar ar'na? Tsawa ya dakawa Maryam cikin fushi yace gidan ubanwa ta fito haka, shiru tayi tsawa ya k'ara daka mata duk ta rude jikin ta sai rawa yake yi, cikin ina ina tace birthday wata abokiya ta naje.
Ran Abba Lawal ya kara baci, janyo hannun Maryam yayi, dakin sa ya wuce da ita, ya cire belt din uniform dinsa ya fara dukan ta. Mamee kuwar Maryam taji cikin tashin hankali ta shiga dakin tayi ta amshi belt din yak'i saki, sai da ya gaji ya yarda belt din, Maryam duk jikin ta yayi rada radan duka sai kuka takeyi sosai, Mamee jan ta tayi zuwa dakin ta.
Mamee dakin Abba ta dawo tana masifa so yake yi ya kashe mata yarinya, don taje birthday, Abba 'dagowa yayi cike da takaici yace Balkisu kina fadin don taje birthday, kin ga shigar da tayi, 'ya mace taje birthday da irin wannan shiga har dare, wace irin sakaryar uwa ce ke, Mamee cikin mamaki ta 'dago tana kallon Abba Lawal, cikin fushi yace ta fice masa daga daki, duk yaron da ya kara fita gidan da irin wannan shigar sai ya dauki mummunan mataki a kanta.
Mamee cikin tsoro da tashin hankali ta fita dakin, Abba kwantawa yayi yana jin ciwon tarbiyar yaran Balkisu ko kadan basa da tarbiya, Mamee dakin ta taje tace Maryam taje tayi wanka ta gasa jikin ta, num Hajiya Rabi ta kira ta fada mata abun da ya faru, Hajiya Rabi cikin takaici ta fada mata nata matsalan sunyi su hadu gobe zasuje wajen wani Malami a sake sabon aiki.
Mamee ta kira kakar ta Habi ta fada mata Habi tace ta kwantar da hankalinta zata je mata gidan wani Malamin, Habi duk shige shige ta iya ko ina taji zata nemowa Balkisu magani, mahaifin Mamee Balkisu daya ne yaron ta, Balkisun dai ce diyarsa, komai Mamee ta ajiyewa Habi har yar aiki, duk wani mugun halin Habi Balkisu nada shi.
Abba Lawal kwance yake yana tunanin tarbiyar yaran tsoron sa kar su lalace masa, khalifa ma da ya tura waje karatu, hutun da ya dawo kwanaki yaga cenji a halayen sa yayiwa Mamee magana ta saka masa ido tace bakomai, yace ya nemo masa transfer Mamee tace a barsa cen ya kusa k'arewa ai.
**** ****
Hajiya Rabi da Mamee sammako sukayi zuwa wani kauyen Abuja aiki sosai aka yi masu, kudi sosai suka bada, za a yanka shanu biyu bak'ak'e za a yanka bunsuru bak'i bak'in kolo, duk sun bada kudi a saya komai za a yi, Mamee aikin ta kan Abba ne, Hajiya Rabi kan Auwal ne da Alhaji Muhamud.
Sun dawo cikin jin da'di Mamee da kanta ta shiga kicin ta shiryawa Abba abinci, akwai maganin da aka ha'da mata da zuciyar kare, Abba na office ta aika masa abincin tayi masa text ya yafe mata zata gyara tayi kure, sosai yaji da'din hakan, abincin sosai yaci ya kira ta yace girki yayi, tace na dare zaifi haka.
Mamee murna sosai tayi, ba tunanin za a mutu, ba tunanin HAK'K'IN wayyanda ake zalunta.
**** *****
Inna Delu ta shiga ta fita sai da Malan Bello ya amince ta tura Zainab aikatau, ranar da Gaje tazo daukar Zainab kuka sosai Zainab da magaji sukayi, Zainab taje wajen Maman Sadiya ta rok'e ta ta kular mata da magaji, da kyar Inna Baba Delu ta jaye magaji jikin Zainab, Malan Bello fita yayi ya bar gida, haka aka raba Zainab da k'anin ta magaji.
Inna Delu tace wa Gaje ta kai Zainab gurin masu sayar da abinci yafi kawo kudi, a ranta abinda takeso Zainab din ta zama yar iska don duk masu sayarda abinci a hanya zaka samu yan iska ne, haka suka wuce Zainab na kuka damuwar ta k'anin ta, bata san halin da zai shiga ba.
Abu duk abun da akeyi gidan bai sani ba yana cen wajen yawon sa makaranta ma ya bar zuwa, in ya fita da uniform gida zai debi ya ajiye wani gurin, duk abun da yayi dai-dai ko kadan Baba Delu bata ganin laifin sa, Magaji kuka yayi sosai dakin da suke kwana yaje ya kwata yana kuka, Baba Delu sai zagin sa takeyi tana cewa ya mutu karewar kuka dan iskan yaro b'arawo duk satar da akeyi gidan shi ke yi mata, ba imani ko kadan a zuciyar Baba Delu, bata tsoron HAK'K'IN marayun Allah.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
_Ummu Asma'u Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
*Wanan page din naki ne Aminiyata, Nabila Rabi'u Zango, nagode nagode, Allah ya baki abinda kike nema duniya da lafira.*
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 17_18
Lokacin da su Gaje suka sauka tashar Bauchi ana ta kiran sallar azahar, haka ta tasa Zainab wadda take matse da ledar kayanta taci kuka harta gaji sai ajiyar zuciya takeyi, duk wanda ya kalleta ba sai an fad'a maka tana cikin damuwa ba, idanuwanta kawai zaka kalla ka gane tasha kuka.
Haka tabi bayan Gaje zuwa cikin tasha. Wata babbar rumfa suka nufa, suna k'arasawa Zainab taga ashe wajen siyar da abinci ne, cike wajen yake da mazan cikin tasha wasu kuma matafiya ne sunke cin abinci, ga mata nan wasu da shigar banza sai kai kawo suke a wajen teburan da mazan suke zaune suna aje masu abinci.
Wata ma idan ta aje haka zakaga suna ta wasa da mazan. Suna saka k'afar su cikin rumfar Zainab tayi ido biyu da wata budurwa ta aje ma wani bak'in mutum abinci tana juyawa ya bugar mata mazaunan ta yana fad'in mutuniyar jiya ina kika shige nazo ban ganki ba? Murmushi tayi tace naje cikin kasuwa ne.
Gaban Zainab ne ya fad'i tunawa da tayi Inna Delu tace ma Gaje a gidan sai da abinci take so tayi aiki, kada dai ace anan ne zatayi aiki? Dan ita atunaninta ko abinci Gaje zata saya masu. Bata gama tunani ba taji Gaje tana fad'in ke ina *UWAR AUDU* take? Da sauri Zainab ta maido hankalinta wajen Gaje dan taji mai zata ce. Wadda aka tambaya tace kishiga tana ciki. Wucewa tayi ciki yayin da Zainab tayi saurin bin bayanta ganin yanda mazan wajen suke k'walo mata na mujiya.
Gaje na shiga Uwar Audu tayi shewa tana fad'in Gaje Uwar mugu ashe ana ganinki? Dariya Gaje tayi tace wallahi kuwa muna nan, ai ganin mu baya wahala sai dai idan buk'atar ganin bata taso ba, kinsan duniya ba'a zama sai da neman na kai.
Uwar Audu tace wannan haka yake, shiyasa gamu nan muna ta fama kullum cikin neman yaki *halak* yaki *haram* muke. Dariya Gaje tayi tace wato kome yazo kina so? Uwar Audu tace sosai ma. Zama Gaje tayi tana fad'in yau ma gani nazo maki da wata hanyar samuwar, kallon Zainab tayi tace zauna mana. Zama Zainab tayi tana cira idanu. Uwar Audu tace ina Batula akawo plate biyu na bak'ina hada lemu da ruwa.
Gyara zama Uwar Audu tayi tana fad'in ina jinki Gaje bani nasha. Gaje tace wannan yarinyar ce na kawo maki ita aikatau dan nasan kina son kyawawa acikin harkar ki. Uwar Audu tace kema kinsan albashin mai Kyau daban yake awajena domin nafi samun customers, amma ba haka ba, ina kika samo wannan mai zafin? Kallon Zainab tayi tace tashi kije daga ciki d'auki abincin kije kici. Zainab tace sallah nake son nayi.
Uwar Audu tace E lallai Gaje kice 'yar larabawa kika kawo mana? Shiga daga cikin akwai band'aki na sai kiyi amfani dashi kici darajar Gaje, k'ofa zaki kalla nan ne gabas. Gaje tace su Uwar Audu ai na d'auka kin manta gabas d'in.
Dariya Uwar Audu tayi tace rufa mani asiri, ko bamu yita akan lokaci ba ai dole mu kalli gabas. Dariya suka sa ita dai Zainab ta d'auki abincinta tayi ciki gabanta yana fad'uwa ganin inda ake so ta zauna tayi aiki.
Uwar Audu tace ina jinki Gaje. Ruwa Gaje tasha sannan tace d'iyar mijin aminyata ce, kinsan halin 'ya'yan miji da jan sharri, kwata-kwata K'awata bata jin dad'in mijinta saboda wannan yarinyar, kullum Delu sai dai ta girka ta bata taci, to shine fa tace na taimaka mata shine nashiga na fita har ta kama mijin a hannu, bayan ya shigo hannu shine tace tana so ta fanshe wahalarta, shine nace ta ban Zainab na kawota wajenki tarik'a aikatau kud'in aikinta sai arik'a aika ma Delu.
Dariya Uwar Audu tayi tace ashe dai har yanzu akwai ire-iren mu a duniya? To me za'ayi da 'ya'yan miji, basu da wata rana agareka sai tarin wahala, shiyasa nace ko zan sake aure bazan auri wanda yake da yara uwarsu bata gidan ba, domin nayi alk'awarin bazan tab'a rik'e yaran da ba nawa ba, to gashi ma tunda Baban Audu ya rasu ban sake wani auren ba.
Gaje tace yanzu dai zata samu aikatau d'in? Uwar Audu tace agaskiya zuwanta yayi mani dad'i, domin zan kaita inda zanci riba biyu, idan nace anan zan ajeta riba d'aya zanci kuma dole aljihuna ya koka, amma idan na kaita inda nake tunani to riba biyu zanci.
Gaje tace ban gane ba? Uwar Audu tace akwai wata Hajiya Mairo da Audu yake tuk'a yaranta yana kaisu makaranta, muna matuk'ar kiriki da ita, mace ce mai mutunci, ta d'auki Audu kamar d'anta, mijinta ma yana da kirki sosai, sai dai ba mazauni bane yana aiki acan wajen tuk'in jirgi agarin Lagos, duk bayan wata guda yake zuwa.
Kinsan Audu baya wani gane karatu, da k'yar ma ta kammala secondary kawai ya rik'a bin motar gidan ruwa suna kai ruwa da haka har ya iya mota, gudun kada alalata manishi yasa naje wajen Hajiya Mairo na nema masa aiki.
Cikin sa'a tace mani ya iya tuk'a mota nace mata E, anan tace mani dama tana neman wanda zai rik'a kai yaranta makaranta dan direban su ya koma garinsu, kinji yanda akayi Audu ya samu aiki a wajenta, kuma cikin ikon Allah lafiya lau kullum cikin yabonshi take, wallahi har mamaki nakeyi yanda Audu ya nutsu.
Kinsan wani lokacin har tambayar kaina nake ashe ana samun irin haka, ace Uwa mai irin halina amma 'Danta a nutse. Gaje tace lallai kinyi sa'a Uwar Audu, Allah ya baki 'Da d'aya gashi kuma ya shirya maki shi. Uwar Audu tace shiyasa wani lokacin nake ragewa, a duk lokacin da na kalli Audu sai naji wani abu ya tsaya mani azuciya, to kinsan shed'an baya barin azauna lafiya sai ya canza mani tunani, babban farin cikina d'aya ne duk abuna bana bin maza, kinsan yafi komai illa.
Gaje tace wannan haka yake. Uwar Audu tace barni dai zan sa yaran mutane suyi kome zasuyi domin su samo mani kud'i. Dariya Gaje tayi tace ana nan dai. To yanzu ita wannan matar kina ganin babu matsala? Uwar Audu tace babu matsalar komai, sosai Hajiya zata amsheta duka yaranta hud'u, babban d'anta namiji ne sunanshi *Hasheem* yana k'asar waje ma acan saudiya yake karatu dan shi ustaz ne nake fad'a maki yafi bama karatun addini muhimmanci, bayan daya gama karatun lafiya ya koma saudiya domin ya karanci na addini, sai yaranta ukku duk mata ne, d'aya ta kusa gama secondary biyun kuma suna primary, da yake haihuwar 'yan boko sukeyi.
Gaje tace nifa ba haka Delu take son Zainab ta kasance ba, tafiso ta wahala sosai. Shiru Uwar Audu tayi tana jinjina rashin imani na K'awar Gaje, duk da za'a aika mata da kud'in aikinta amma tana son ta wahala. Saurin kallon Gaje tayi tace waya fad'a maki acan d'in hutawa zatayi? Ina tabbatar maki sai ta gwammace abarta anan da akaita can, kinsan kuwa yanda girman gidan yake? Komai da kika sani itace zatayi, idan ta tashi tun k'arfe hud'u na asuba ita data huta sai dai sallah, abinci ma atsaye zata cishi saboda aiki, Hajiya 'yar hutu ce komai sai anyi mata.
Murmushi Gaje tayi tace yanzu naji batu, dan haka kawai ki kaita, idan yaso sai arik'a aika ma Delu kud'in aikinta kema kina samun naki. Jinjina kai Uwar Audu tayi tace bakida matsala, yanzu ki barta anan idan na gama abinda nake zamu tafi da ita.
Gaje tace ai na d'auka dani zamuje naga gidan? Uwar Audu tace keda zaki koma yau kawai kibar mani komai. Gaje tace wai da kwana zanyi. Uwar Audu tace a'a, kinsan bama haka dake, da can baki kwana sai yau dan kinji ance za'aje gidan masu kud'i? Hannu tasa ta ciro dubu biyar ta mik'a mata tana fad'in kin gama aikinki, albashin farko kamar yanda aka saba kina da kashi d'aya, ita Delu d'aya ni ma zan d'auki d'aya, daga lokacin kuma tsakaninki da Delu ne.
Washe baki Gaje tayi tace wannan ma yayi dai-dai, ba damuwa duk yanda kikayi yayi, bara na tashi ba zama zanyi ba kada nayi dare. Zainab ta kwala ma kira, da sauri ta fito dan har bacci ya fara d'aukarta.
Gaje tace toni zan tafi, sai ki tsaya kiyi aiki da kyau domin ki samu kud'i masu yawa idan kinaso akular maki da K'aninki Magaji, idan kuma kikayi halin naku na sata aka koroki ba ruwana, idan kuma a kulle ki babu mai k'wato ki.
Duk'ar da kai Zainab tayi tana hawaye Gaje tace Uwar Audu sai munyi waya. Tashi Uwar Audu tayi tana fad'in Zainabu jeki zauna ba yanzu zamu tafi ba sai zuwa anjima bara na rakata na dawo. Fita sukayi Zainab ta koma d'aki tana hawaye.
**** *****
Aikin da Mamee tayiwa Abba Lawal wannan karon yaci sosai, duk yanda tace ba gardama, duniya tayiwa Mamee da'di, Maryam tun ranar da Abba ya duke ta, ta cenza takon fitar ta, in zata fita gida dogon hijab har k'asa take sawa, in taje makaranta ko gurin party sai ta debi, duk halin da Maryam ta ke ciki Mamee ta sani, ranar da Maryam tafara saka hijab din Mamee dariya tayi tace kinyi maganin Abban ku da sa idon sa.
Rayuwar Hajiya Rabi ita Mamee ke bi, Hajiya Rabi yar kaduna ce, bakatafiya ce rabin dangin ta duk kiristan ne, haukar Mamee wayewa ce ta shigo bariki ta hadu da yan bariki tawaye. Maryam da Farida idanu sun bude sosai, in ka gan su makaranta bazaka ce zuri'ar chiroman misau ba ne, in zasu dawo gida su saka hijab, Mamee
matsawa Abba tayi sai da ya siyawa su Maryam manyan motoci na zuwa makaranta, siyen mortar ya k'ara rikita yaran.
Ko yaushe lectures din su 8-6 ne in sun fita tun safe sai dare suke dawowa gida, wani lokacin ko lectures din basa zama suyi yawo dai sukeyi cikin makaranta, cikin matsatsun kaya ansha attachment, Maryam nada wani sauriya *Zero* zero mahaifinsa ne governor CBN, sosai suke son juna da maryam duk makarantar kowa yasan zero yasan Maryam ko yaushe suna tare, zero rik'aken she'dani ne, London yake karatu da uwayen sa suka ga lalacewar tayi yawa suka dawo dashi gida aka nema mashi university Abuja.
Duk wani iya shege Zero ya koyawa Maryam, zero baya shaye shayen komai matsalarsa mata, wani lokacin har maza nema yakeyi, ko yaushe nunawa Maryam yakeyi aure zasuyi, bai fito ya nuna mata halinsa ba a hankali yake bibiyar ta, zasuyi rungume- rungume, tun Maryam bata saba har ta saba, wasani kala-kala zero ke yi mata.
Cikin sati Abba Lawal sau daya zai kira Anty Amina wani lokacin har mancewa yakeyi dasu, in ya kira tace suna da lalura sai ya tura kudi, Anty Amina ta shiga damuwa sosai, duk litinin da alhamis tana azumi addu'a sosai takeyi don lamarin Abba tsoro yake bata, saukin yaranta karatun su lafiya lau suna ganewa sosai, Ummi sauka na biyu zatayi, Mubina saura kadan tayi saukar farko.
**** ****
Baba Ladidi sosai ta shiga damuwa, Alhaji muhamud ya kwana biyu bai je kano ba, in ta kira zai ce aiki yayi yawa wani lokacin har su k'are wayar baya tambayar Auwal, yawan sadakar da Alhaji Muhamud keyi, shine duk abunda akayi masa bai cika tasiri
ba, (sadaka na karya duk wani mugun asiri Allah yasa mu dace).
Baba Ladidi sosai ta Shiga addu'a tasan akwai matsala ba abinda yafi Auwal muhimmanci wajen mahaifin sa, tana tsoron lamarin Hajiya Rabi komai zata iya kan abun duniya, bayan kwana biyu Alhaji muhamud yazo kano tare da wani likita da ya gayyato daga Ghana zai diba Auwal, tsowon kwana biyar yana diba Auwal.
Bayan ya kare binciken sa yacewa Alhaji Muhamud mataki na farko da za'a dauka, ayiwa Auwal aure, Alhaji Muhamud da Baba Ladidi kallon sa sukeyi suna tunanin wa zai yiwa Auwal aure yanzun, likitan yayi masu bayanin yana buk'atar kulawar da tafi wannan, ba wanda zai basa irin wannan kulawar sai Matar sa, duk abun da za a yi masa zai biyo bayan auren, shiru sukayi suna tunanin Mafita.
*** ***
Sai dare Uwar Audu tace Zainab ta dauko kayanta su wuce, haka nan taji Zainab na bata tausay, haka suka fita suka nufi gidan Hajiya Mairo.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Gaffara.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 19_20
Zaune suke a falon Hajiya Mairo suna jiran ta fito. Zainab sai raba ido take tana kallon kayan alatu, tun d'azu take tunanin mai zasuyi a wannan gidan mai kyau? Da farko ma ta d'auka sai data zatayi, sai da taga mai gadi ya bud'e masu gate sun gaisa da Uwar Audu yana tambayar ta kasuwa sannan hankalinta ya d'an kwanta.
Uwar Audu sai kallonta take ganin yanda take a takure, domin batayi mata bayani ba dan bata so tace bazata zauna ba, ganin kada Hajiya tazo batayi mata bayani ba yasa ta kira sunanta. Da sauri Zainab ta kalleta. Uwar Audu tace ki kwantar da hankalin ki, na fuskanci irin zaman ta kike a wajen matar mahaifinki, ban tab'a jin tausayin wata mace ba sai akanki, kuma naji har cikin raina ina so na taimaka maki.
Sun so kiyi aiki a wajena domin ki lalace, ni kuma sanin Hajiya tana son mai aiki yasa nace zan kawo ki nan amma na nuna masu anan ma wahala zakisha, sai dai gaskiya bata da mugunta, matuk'ar kika rik'e gaskiya zakiji dad'in zama da ita, d'ana anan yake aiki direba ne, zata baki wajen kwana komai zatayi maki idan kika rik'e gaskiya, ina fatan bazaki bani kunya ba? Hawayen farin ciki ne suka zubo ma Zainab jin abinda Uwar Audu ta fad'a.
Jinjina kai tayi tace nagode Umma, ban tab'a tunanin rayuwata zata canza haka da sauri ba, Allah ya biya maki buk'atunki na alkhairi, gashi zan kwanta a irin wannan gidan amma K'anina yana can bansan a wane hali yake ba.
Uwar Audu tayi murmushi tace amin, kuma ki kwantar da hankalinki babu abinda zai samu magaji, kicigaba da addu'a wata rana zakiyi farin ciki, ki rik'e amanar aikinki Allah zai taimakeki. Zainab tace insha Allahu bazan baki kunya ba.
Motsin fitowar Hajiya Mairo sukaji hakan yasa sukayi shiru, da sauri Zainab ta goge fuskarta. Da sallama Hajiya Mairo tashigo fuskarta d'auke da murmushi. Bayan sun amsa Uwar Audu tace Hajiya kinga sai yau kike ganina.
Hajiya tace ai tunda naji shiru nasan ba'a samu bane. Risnawa Zainab tayi tana gaishe da Hajiya. Idanuwa Hajiya ta zuba mata aranta tana fad'in masha Allah, wannan yarinya tubarkalla. Amsawa tayi tana fad'in sannu ko.
Uwar Audu tace wallahi sai yau Allah yasa aka samu, bana so na kawo maki ko wane tarkace shiyasa na tsaya sai da na duba, wannan d'in daga garin Jum'are take, d'iyar Mijin wata k'awar Gaje ce ta turota wajena tarik'a mani aiki, to da yake Gajen na sani shine na yaba da hankalinta sai nace kin fini buk'atar ta shine na kawo ta.
Murmushi Hajiya tayi tace gaskiya kin kyauta, nima tunda na ganta na yaba da ita, ya sunanta ne? Sunanta Zainab. Murmushi Hajiya tayi tace kice babban suna gareta, domin sunan mahaifiyata ne, kinga kuwa wannan sunan bazai fad'u a gidan nan ba.
Uwar Audu tace lallai kam. Hajiya tace zan rik'a kiranta da Ummina. Uwar Audu tace wannan suna yayi dai-dai, sai yaran kuma. Hajiya tace babu wanda zai kira wannan sunan a gabana, domin ban tab'a kiran mai sunan da haka ba, dole surik'a kiranta da Ummi. Uwar Audu tace hakan ma yayi.
Kallon Zainab Hajiya tayi tace Ummina sannu da zuwa, ina fatan zaki saki jikinki kuma zaki rik'e mu amana, duk abinda ya shige maki duhu kada kiyi shiru ki tambaya, kinsan ance matambayi baya b'ata, bana son munafurci da gulma, kitsaya tsakani da Allah kiyi abinda ya kawo ki, kada ki bari wasu su canza maki zuciya, babu ruwanki da abinda ba'a saki ba, duk abinda bai shafeki ba to kibarshi, bance ki bama yarana fuska su rainaki ba, gaba d'ayansu Laila ce kawai zata girme ki itama da kad'an, dan haka ki rik'e girmanki kuma suma zanja masu kunne duk da nasan halinsu suna girmama duk wanda na kawo.
Duk'ar da kai Zainab tayi tace insha Allahu Hajiya bazaki sameni da aikata wani abu marar kyau ba, duk abinda na aikata ba dai-dai ba ina rok'on da ki gyara mani. Murmushi Hajiya tayi tace insha Allahu zaki sameni mai cika alk'awari. Bayan wannan akwai wani abu da kike da buk'atar nayi maki? Zainab tace abu d'aya nake neman alfarmarshi.
Hajiya tace kada kiji komai fad'eshi naji. Zainab tace dama... Dama.. Sai kuma tayi shiru. Hajiya tace ki fad'a mana ai ni nace ki fad'a. Zainab tace dama ina son karatun islamiya ne shine nace ko zan samu anan? Tausayi Zainab ta bama Hajiya. Murmushi tayi tace kada kiji komai, tunda har na kawoki k'ark'ashina dole komai naki ya dawo hannuna, yanzu ke amana ce awajena, dan haka aiki bazai hanaki neman ilimi ba ki kwantar da hankalin ki. Murmushi Zainab tayi wanda ya bayyana wushiryarta tana fad'in nagode.
Uwar Audu tace tun zuwansu na gane tana da ibada, suna zuwa sallah ta fara tambayar inda zatayi. Hajiya tace ga goshinta nan ma ya gwada ai, insha Allahu babu abinda zai tab'a karatunki kinji. Kai Zainab ta d'aga tana murmushi.
Hajiya tace Uwar Audu ya maganar albashinta fa? Uwar Audu tace matar mahaifinta tace arik'a aika mata da kud'in domin akwai K'aninta acan kuma zata rik'a tara mata. Murmushi Hajiya tayi tace kaji mata mai gaskiya, insha Allahu da wata yayi za'a baki sai ki aika mata, idan yaso sai arik'a bama Ummina wani abu ko zata sayi kayan amfani kinsan mace sai da gyara.
Uwar Audu tace haka ne, dama bazai yuwu a aika mata duka ba ita ba'a bata komai ba, angode sosai Hajiya. Zainab kuwa shiru tayi tana mamakin k'aryar da Inna Delu tayi. Hajiya tace tashi Ummina muje ciki na nuna maki d'akin ki.
Uwar Audu tace nima wucewa zanyi dare yayi. Hajiya ta d'auko kud'i ta bata tana fad'in ga naki. Amsa Uwar Audu tayi tana fad'in nagode sosai. Ummi sai kwana biyu idan nashigo ko. Shiru Zainab tayi dan bata san da ita ake ba
Tab'ota Hajiya tayi tana fad'in bata saba da sunan ba, da kinji ance Ummi ke ake nufi saboda sunan mamata gareki. Murmushi Zainab tayi ta d'aga kai, kallon Uwar Audu tayi tace Umma nagode. Uwar Audu tace bakomai. Sallama tayi masu ta fita.
Bayan Hajiya Zainab tabi suka shiga ciki, ta kusa da d'akin su Laila suka bi, lek'awa Hajiya tayi tace masu su fito, kai tsaye wani d'aki na kusa da nasu tashiga. Zainab sai kallon d'akin takeyi, gado da durowa ne aciki sai madubi, agefe kuma a kwai band'aki, sosai d'akin yayi mata kyau.
Bata gama kallonshi ba taji Hajiya tana fad'in Ummina wannan shine d'akin ki, ga band'aki nan aciki, kayanki ki sasu cikin wannan durowar, zuwa gobe zan kawo maki sauran kayan amfani.
Duk'awa tayi tana mata godiya. Su Laila ne suka shigo da sallama. Amsawa Hajiya tayi tana fad'in ina Auta fa? Laila tace gata nan baya. Hajiya tace ga sabuwar ma aiki nan an kawo, sunansu d'aya da Auta, zaku rik'a kiranta da Ummi, kamar yanda kuka sani ba sai na mai-maita maku ba, bana son fitina nasan baku da ita, kada ku wulak'anta ta saboda tana karkashinku, Allah shine ya yota ahaka, kuma badan baya sonta ba, dan haka bana son jin wani abu.
Murmushi Laila tayi tace amma Momy naji dad'i da aka kawo Ummi, kinga nima na samu k'awa. Murmushi Hajiya tayi tace haka ne, kusan kanku d'aya ai. Zarah tace nima ai k'awata ce.
Hajiya tace kowa ma k'awarshi ce, idan kuna gida zaku rik'a taya ta aiki ko? Auta tace emana nima zan rik'a taya ta aiki. Murmushi Hajiya tayi tace Laila kije ki kawo mata abinci sai tayi wanka ta kwanta ta huta nasan ta gaji. Laila tace to Momy. Fita Hajiya tayi cike da farin ciki dan tana matuk'ar son halayen yaranta, sam basu da hali irin na yaran masu kud'i. Zainab kuwa zama tayi a gefen gado tana ta murmushin firar dasu Auta da Zarah suke ma.
**** ****
Alhaji Muhamud sosai ya shiga damuwa, ya bar kano zuwa Abuja, Baba ladidi ta kwantar masa da hankali suyi addu'ar sosai Allah ya zab'awa Auwal mafi alkhairi. Ranar monday yana office Abba Lawal ya same sa, a fuskar Alhaji Muhamud ya fahimci akwai matsala, bayan sun gaisa yake tambayar sa lafiya?.
Alhaji Muhamud cikin damuwa yayiwa Abba Lawal bayanin yanda sukayi da likitan, Abba Lawal ma ya shiga damuwa, a irin halin da Auwal yake ciki ayi masa aure, duk shiru sukayi kowa da tunanin da yake yi, Alhaji Muhamud hannun Abba Lawal ya rik'e, yace Lawal babu zumunci na jini tsakanina da kai, amincin da ke tsakanin mu, babu shi tsakanin na da yan uwana, duk inda zan nemawa Auwal aure ba don Allah za'a so sa ba, za'a soshi ne don daular duniya, ina neman alfamar ka taimaka min ka diba maraicin Auwal da halin da yake ciki ka bashi auren daya daga cikin yaranka.
Abba Lawal 'dagowa yayi ya kalli Alhaji Muhamud, jikin sa yayi sanyi sosai, duk abunda akeyi Alhaji Muhamud yayi masa, duk wani Abu da ya samu zai sa Abba Lawal gaba, ba zai tab'a samu yaci shi d'aya ba, tun kamin su kawo hakan ba abunda bai masa ba, duk da yasan akwai matsala, wa zai aura masa cikin yaran?.
Abba Lawal hannun Alhaji Muhamud ya rik'e yace ka kwantar da hankalin ka da yardar Allah za'a yi, na basa auren Maryam,cikin murna Alhaji muhmud yace na gode Lawal yanda ka taimakamin Allah ya taimake ka hakan.
Bayan Abba ya fita, Alhaji muhamud Baba Ladidi ya kira yana fa'da mata yanda sukayi da Abba Lawal, Baba Ladidi sosai hankalinta ya tashi, Mamee Balkisu da Hajiya Rabi duk halayen su daya, ko yaran Mamee sun yarda su auri Auwal ba don Allah ne zasuyi ba, tsoron ta a ha'da kai da su a kashe Auwal din.
Har sukayi sallama Baba Ladidi batada natsuwa ta shiga damuwa sosai, me zatayi? ko me zata fadawa Alhaji Muhamud bazai yarda ba,Malamin da take kai Auwal wajen sa ta kira, tayi masa bayanin maganar auren da ake son yiwa Auwal, ta rok'esa yayi mata istihara Allah ya zab'ama Auwal din alkhairi.
Abba Lawal bayan ya koma gida ya rasa yanda zai fa'dawa Mamee
maganar, zaune yake falon Mamee ta shigo, gefensa ta zauna, tace yau kamar Kana da damuwa lafiya? Abba Lawal yace wani hukunci na yanke ban nemi shawararki ba, Mamee tace meya faru? Abba yace na bawa Auwal yaron Alhaji Muhamud auren Maryam .
Mamee cikin tashin hankali ta tashi tsaye tace Lawal diyar tawa zaka ba mahaukaci, wallahi bazai yuwu ba, ka cenza shawara tun wuri, da raina Maryam bazata auri mahaukaci ba, cikin fushi Mamee ta fita falon.
Hajiya Rabi ta kira cikin damuwa ta fada mata abunda ke faruwa, Hajiya Rabi tace shine ake rufemin, tacewa Mamee ta kwantar da hankalin ta zasu nemi mafita, zatayi tunanin mafita sai ta nemeta.
Hajiya Rabi murmushi tayi tace dama tazo min zanyi amfani da Bilkisu da yarinyar ta don cimma burina.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u (Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 21_22
Hajiya Rabi ta kira Mamee ta fadi mata wajen da zasu hadu, Mamee cikin sauri ta shirya zuwa inda zasu hadun. A wani park ne dake kusa ga gidan Abba Lawal, Mameen ta fara isa, bata jima ba Hajiya Rabi ta iso. Hajiya Rabi tace Balkisu ki kwantar da hankalin ki, naga baki da natsuwa, wannan ba abun tashin hankali ne ba.
Yanzun zaki lalab'a Maryam ta yarda da auren Auwal din, bayan auren da kamar watanni uku zamu kauda Auwal din, sai ta auri wanda takeso, zata samu dukiya sosai gadon Auwal din, wasu kaddarorin Alhaji Muhamud duk da sunan Auwal din ne, zata yi rayuwa gidan Auwal ta yanci, shi ba hankali ne garesa da zai iya takura mata, kinga mu jefi tsuntsu biyu da dutsi daya, zaku samu dukiya mai yawa, nawa burin zai cika na ganin bayan Auwal.
Ko Alhaji Muhamud ya mutu ni da yarana dai ne zamu gaje sa. Mamee shiru tayi tana nazari, ga k'oshi ga kwannan yunwa, zasu samu kudi sosai in Maryam ta yarda da auren Auwal din, matsalar tasan Maryam bazata yarda ta auri Auwal din ba, sosai take son zero, ko yaushe maganar zero takewa Mamee cewa yace zai aure ta, Mamee cikin damuwa tacewa Hajiya Rabi Maryam ce matsalar nasan da k'yar in zata yarda da auren Auwal din, Hajiya Rabi tayi murmushi tace haba Balkisu Maryam har nawa ce da zata gagare ki.
Mamee shiru tayi tana tunanin irin kudin da zasu samu, tana tunanin Maryam, Hajiya Rabi tace ta natsu tasan me take ciki, ta tsara mata yanda zata fitowa Maryam, sunyi sallama, Hajiya Rabi tace gobe zata zo gidan ta k'ara yiwa Maryam din magana.
Bayan Mamee ta koma gida, Abba ta kira tace ta yarda da auren damuwar ta Maryam ko zata amince, Abba yace ta kwantar da hankalinta yasan Maryam bazata basa kunya ba.
Sai magrib Maryam ta dawo gida, bayan sallar magrib Mamee ta kirata dakin ta.
Cikin hikima ta fa'dawa Maryam Abba ya bada auren ta ga Auwal din Alhaji Muhamud, tayi mata bayanin yanda sukayi da Hajiya Rabi, Maryam cikin mamaki take kallon Mamee, tasan me take fa'da, ta rasa wanda zasu ha'da ta da shi sai mahaukaci Mamee tasan tana da wanda take so.
Maryam tashi tayi tace, Mamee bazan auri mahaukaci ba, ina da wanda nake so, ki fadawa Abba tun wuri Ku sani bazan auresa ba, fita tayi dakin, Mamee shiru tayi tasan Maryam bazata yarda ta auri Auwal a halin da yake ciki ba. Wayar Hajiya Rabi ta kira ta fa'da mata yanda sukayi. Hajiya Rabi tace gobe zata zo gidan zatayi magana da Maryam din.
Abba Lawal da yayiwa Maryam magana cewa tayi bazata auri mahaukaci ba, yayi ta lallami tace bazata yi ba, Abba yaji haushi sosai yace ta fice masa a falo, aure sai ya daura da Auwal, Maryam na kuka ta fita falon, dakin su tawuce ta kira zero ta fa'da masa auren da Abba keson yi mata, Zero hankalin sa ya tashi sosai kuka ya sawa Maryam za'a rabasu, Maryam tace ya kwantar da hankalin sa gara ta mutu da a raba su
Mamee da Hajiya Rabi sunyi Maryam tace bazata auri mahaukaci ba, Abba ma yayi tace baza tayi ba, Abba yaji haushi sosai yace Alhaji Muhamud ya aika mutane ayi tambayar aure. Wajen Dan iyan misau akaje tambaya, anyi tambaya an sa sadaki, ranar jumma'a za'a daura aure.
Anty Amina sosai tayi mamaki jin Maryam zata auri Auwal, tasan Mamee akwai dalilin amincewa auren Auwal din, Mamee bazata yi hakan a banza ba. Yan uwan Abba basu San halin da Auwal din yake cikin ba, sun San irin amincin dake tsakanin Alhaji Muhamud da Abba Lawal.
Shirin biki sosai Alhaji Muhamud da Hajiya Rabi keyi, Hajiya Rabi ta ha'da lafe na gani a fada, cikin gidanjen Alhaji Muhamud dake Abuja zasu zauna, Baba Ladidi sai addu'a takeyi, ta shiga damuwa sosai, hankalin ta bai kwanta da auren diyar Mamee da Auwal ba, ba yanda zatayi.
Mamee hankalinta tashe yake, ta kasa gane kan Maryam, tun safe in ta fita makaranta sai magrib, in ta dawo ta shige dakin su ta rufe, Mamee tayiwa Abba Lawal magana yace ta k'yaleta in an daura auren zata zauna ne, Mamee hankalinta bai kwanta ba.
**** *****
Zainab tace Laila ta nuna mata aikin da ake da safe ta fara yi kamin su tashi, Laila tayi dariya tace zaku shirya da Mumy kenen Ummin Mumy, Zainab tayi murmushi, Laila ta wuce dakin su, Zainab ta Shiga dakin da aka bata, wanka tayi ta kwanta tana tunanin halin da Magaji yake ciki, hawaye ne suka zubo mata, addu'a tayi Allah ya tsare Magaji.
Zainab tun da ta k'are sallah subahin ta fara share -share da goge -goge, tas ta share gidan ta goge, ta gyara ko ina, ta zauna tana jiran su tashi, lokacin da Mumy ta fito sosai tayi mamaki ko ina an gyara, kicin suka wuce tana nuna ma Zainab yanda ake amfani da kayan kicin din, cikin k'ankanin lokaci Zainab ta fara fahimta.
Bayan sun ha'da abin kari Zainab ta gyara kicin, Mumy sai albarka take sawa Zainab, sosai taji da'din aikin Zainab din komai cikin natsuwa take yin sa, su Laila da zasu wuce makaranta Zainab kallon su take cike da sha'awa, tana son karatu sosai.
Bayan sun wuce ta gyara dakin su har dakin Mamee, ta wanke toilet din Mumy, bayan ta kare Mumy tace taje tayi wanka ta huta tasha aiki, Zainab murmushi tayi ina aikin yake kan aikin da take yiwa Inna Delu, Mumy tace anjima in sun dawo in zasu je islamiya tare zakuje ayi maki register Zainab godiya tayi sosai, Mumy tace Ummina ki tsare min amana, komi zan yi maki.
Da yammah da su Laila zasuje Islamiya, Mumy tace Zainab ta shirya suje tare Zainab murna sosai tayi, Audu ke kai su ya dauko su, Islamiyar babu nisa daga gidan su, Zainab duk motsin da tayi Magaji take tunawa ko wane hali yake ciki.
**** ****
Magaji na daki kwance Baba Delu ta kwalla masa kira jiki na rawa ya fito , tace yazo yayi aiki, duk aikin da Zainab ke yi, shi zai rik'a yin sa, tsintsiya tace ya dauka ya fara shara, Magaji jikina rawa ya dauki tsintsiyar don mugun tsoron Baba Delu yakeyi.
Yana shara Baba Delu na zuba mashi masifa, sai da ya share gidan, bayan ya k'are shara ya fara wanke -wanke, yana wanke wanken yana kuka sosai ya gaji bai tafa aiki mai yawa haka ba, duk aikin mai wahala Zainab ke yi, bayan ya kare Baba Delu tace yaje ya dora tukunyar tuwo ido ya bude yana kallon Baba Delu.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
*Bismillahirahamanirrahim*
*page* 23_24
Magaji da k'yar ya ha'da wuta, idanun sa sunyi jawur kan hayak'i, Baba Delu na gefe tana masifa, shinkafa ya dafa, ta ha'da miya tace ya diba, ta shige daki tana mita, haka yayi ta diba miyar, ganin ta fara kama tukunya ya sauke, ya fa'dawa Baba Delu ya kare, abincin ta kwashe a kula, tana zubawa Abu ya shigo gidan, plate ya
dauko ya zuba ya zauna yana ci, Baba Delu duk abincin ta zube a kula, karkaren tukunya ta barwa Magaji tace ya dauka yaci.
In ya k'are ya wanke mata tukanen, Magaji yunwa yake ji sosai, haka ya dauki abincin ya koma wajen da suke wanke wanke yana ci, Abu na gefe yana masa dariya, Magaji abincin bai kai masa ko ina ba, ya wanke kayan, bayan ya k'are Baba Delu ta ajiye masa kayanta dana Abu ya wanke.
Daukar kayan yayi ya fara wankewa yana wanki yana kuka, duk jikin sa ciwo yake masa, yana wankin Malan Bello ya shigo, kallon Magaji yayi ya wuce cikin daki, sosai yake tsoron yi masa Magana Baba Delu na gida, Abu na kare cin abincin ya ture plate din ya tashi ya fita, wani lokacin abincin dai ke kawo sa gidan, Baba Delu ma shiryawa tayi ta fita yawon dillancin ta.
Tana fita Malan Bello yazo yace Magaji ya kawo wankin, duk kayan ya wanke ya shanya Magaji na zaune har ya fara bacci, yini ranar baije makaranta boko ba, sai da akayi la'asar Malan Bello ya tashe sa yace yayi wanka ya wuce islamiya, shiryawa yayi yawuce, Delu nacen na yawon dillancin ta, ta hana Magaji zuwa makarantar boko, nata yaron Abu yana cen yana yawo a titi da sunan makaranta, ba tunanin HAK'K'IN marayen Allah.
**** ****
Mamee har rama tayi kan damuwa, ko kadan bata son damuwar yaranta har Maryam duk cikin yaran ta fison Maryam, duk wani bak'in halin Mamee Maryam ta fita, Mamee jin takeyi a bar auren tunda Maryam din bata so, ta auri Wanda take so, in ta tuno irin kudin da zasu samu sai taji gara a yin, bata son batawa Hajiya Rabi, don tasan burin Hajiya Rabi taga bayan Auwal, Hajiya Rabin duk abun da ake yi tayi mata.
Mamee ta kira Hajiya Rabi tace akwai matsala ta rasa ganewa kan Maryam din, Hajiya Rabi tace suje wajen Malan ya taimaka masu, a hanya suka hadu suka wuce gidan Malamin da suke zuwa, magani ya basu yace su tabbar Maryam taci duk abun da suka ce tayi zatayi(Mamee tayi nisa wajen neman duniya har kinawa diyar cikin asiri Allah ya tsare mana imanin mu).
Bayan sun dawo Hajiya Binta tacewa Mamee ta tabbatar Maryam taci abinci, Mamee tace angama, koda ta koma gida Maryam bata nan, tun da maganar auren ya tashi bata dawowa sai dare.Mamee ta kira, in ta k'are lectures tazo gida, lokacin tana cikin motar Zero rungume saman kirjin sa, Maryam matse murya tayi tace lectures takeyi in ta k'are zata dawo kashe wayar tayi kar ta k'ara kira.
Zero k'ara rungume Maryam yayi yace zai shirya yanda zasuyi dole a bar maganar auren, Maryam tace ya shirya yanda zaa yin, k'ara matseta yayi yace muje gidana pls, Maryam bakin ta, ta ha'da da nasa tace cikin ra'da tace ya bari har su k'are da maganar auren mahaukacin nan, Zero yayi nisa bai iya cewa komai, sai nishi suke yi, ranar Maryam lectures ko daya batayi ba, haka suka gama lalatar su a mota, Zero bayan ta wuce yake tunanin zai samu Abun da ya bata, in tasha zata nemishi da kanta, ba zai yarda tayi aure ba, yana son yarinyar sosai.
Bayan Maryam ta koma gida Mamee ta kawo mata abincin tace kar ta damu duk abun da takeso shi zaa yi, Maryam ta rungume Mamee tace nasan bazaki yarda a yi min haka ba, ki budewa Abba wuta Mamee yana tsoronki komai kikace zaiyi, ko ki kai shi wajen Malamin Ku(wannan bala'in har ina, diya tasan mahaifinta na tsoron mahaifiyar ta tasan mahaifiyar na zuwa gun Malan yin asiri, Allah ya tsare mana imanin mu)
Mamee tace kar ki damu ci abinci, Maryam toilet ta Shiga tace zanci yunwa nakeji, mai aikin gidan ta shigo tace Mamee tayi bak'i, bayan Maryam ta fito wanka abincin ta dauko zata ci, curry da aka sawa aminci taji bata son kamshin sa, daukar abincin tayi taje taba masu gadin, ta dawo da plate din kicin, bayan bak'in sun wuce Maryam tace wa Mamee ta cinye duka, don bata son Mamee tayi mata fadan bata son cin abinci, Mamee ta kira Hajiya Rabi murna sosai suka yi.
**** ****
Anty Amina tun lamarin na damun ta har ta dangana, Abba baya kira ko ta kira sai yaga dama yake dauka, zaune take tana gadin gidan mai gidan bayada case da ita sai yayi wata biyu bai zo ba, in Umman sa tayi masa fada sai ya kira Anty Amina yayi ta mata fa'da, akwai lokacin da Umman sa tayi masa magana kiran Anty Amina yayi yace in ta gaji taje gidan su ta huta.
Abun yayi mata ciyo, ta kira yaya Maryam a kano ya Maryam tace tayi hank'uri ko don su Ummi in ta barwa Mamee yaranta rayuwar su zata lalace, hakan ta hank'ura da tafiya gida. Ranar Anty Amina na zaune Abba yazo zaa yin fentin gidan don auren Maryam, fuskar sa ba annurin rahama, Anty Amina tayi mai laifi ta ha'da sa da mahaifiyar, duk tsawon lokacin da ya dauka baizo ba, bai yi laifi ba.
Su Ummi ma da suka dawo makaranta, sama sama ya amsa gaisuwar su, Mubina tace Abba lafiya ko munyi ma laifi ne? tsawa ya daka mata, tana kuka ta wuce falon Amina. Aminan duk abun da ya faru taji, jawo Mubina tayi tace kuje ku shirya zuwa islamiya Abban ku baya da lafiya bai son damuwa, shiryawa sukayi zuwa islamiya, da zasu wuce Abban na waje da masu aiki komai basu ce masa ba, suka wuce, harara ya bisu da shi, sosai yake jin haushin su da Amina, duk cikin aikin Mamee ko ina zata kai HAK'K'IN Su.
**** ****
Anyi wa Zainab register islamiya aji biyu aka sakata, ba wani nisa tayi ba, ba ko yaushe take samun zuwa islamiya ba, a gidan su, sai k'arfe shidda suka dawo, Zainab hijab ta cire ta wuce kicin ta taya Larai mai dafa abincin gidan, Larai nan cikin unguwar take zuwa takeyi in ta k'are abinci ta wuce gida, dattijuwa ce ta iya girki sosai, Zainab tuwon da Larai ke tuk'awa ta amsa tana tuk'awa suna fira ta Larai.
Mumy ta fita kayanta sun iso daga Dubai, kasuwanci sosai Mumy keyi tun rasuwar mahaifin su Lailah, cen farko tana aiki daga baya tayi ritaya, mace mai Zuciyar maza, bayan Mumy ta dawo kicin ta samu Zainab tana kwasar tuwo, Mumy murmushi tayi tace Ummina sarkin aiki baki gajiya, Zainab murmushi tayi ta amshi jikar Mumy ta wuce sama.
Larai tace sannu da zuwa Hajiya, Ummin ki akwai aiki, tun da tadawo islamiya ta amsar min aiki, Mumy murmushi tayi tace wannan karon na dace yarinyar nada natsuwa sosai, ina da burin taimaka mata, an
ce marainiya ce.
Bayan sallar isha'e duk tare suka cin abinci, Zainab tana ci tana tunanin magaji, Mumy ganin Zainab nacin abincin kadan-kadan tace Ummina lafiya, Zainab ta share hawayen da suka zubo tace Mumy k'anina magaji bansan halin da yake ciki ba, Mumy tace Ummina dena kuka, Magaji lafiya lau yake komai bazai same sa ba. Mumy tace Ummina bani labarin rayuwar ku da k'anin ki mana.
Zainab ta kwashe duk labarin su tun rasuwar Mahaifiyar su da irin azabar da Baba Delu keyi masu, Mumy sai da tayi hawaye kan tausai, tace Ummina ki kwantar da hankalin ki, zan taimaka maki har k'anin ki magaji, zata nemi num Maman sadiya gobe, Zainab ta fada mata unguwar su da sunan mijin Maman sadiya, duk Zainab ta fada mata, Mumy tace tana da yan uwa a Bauchi gobe zata san abun yi, Zainab na kuka tana godiya, Mumy sai mamaki takeyi wanan rashi imanin har ina bata tsoron HAK'K'IN yaran nan, Allah na yafewa mutun komai banda HAK'K'IN Wani kyakyawan hadisi mazon Allah(SAW) ne.
Ummu Asma'u
(Sa'adatu)
07064551049
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Gaffara.
*Bismillahirahamanirahim*
*page* 25_26
Hajiya mairo kwana tayi tana tunanin hanyar da zata bi don taimakon Magaji k'anin Zainab, sosai labarin yaran ya tsaya mata a rai, yanzun da uwar Audu ta bar ta wajen siyar da abincin, da rayuwar ta zata iya lalacewa, yara mata masu talla a titi da yawan su wajen tallah rayuwar su ke lalace, tallah ha'dari ce sosai a rayuwar diya mace. *Muktar* ya fado mata a rai, Muktar dan uwan maigidan tane margayi, *police* ne kwanan aka yi posting din sa jumu'are hamdala Hajiya Mairo tayi.
Bayan gari yawaye duk yaran sunyi makaranta, Zainab ta fara gyara gida, Hajiya Mairo ta kira Muktar, bayan sun gaisa ta kwashe duk labarin su Zainab ta fa'da masa sosai ya tausayawa masu, yace wane irin taimako take son ya yi mata, bayani Maman sadiya tayi masa da unguwar da da suke, tana son ya samo mata num Maman sadiya, zata turo kudi ya bawa Maman sadiya duk abun da yaron ke buk'ata ayi masa, taimako na biyu, tana son yayi amfani da kakin sa ya tsorata Inna Delu kan karatun Magaji, don bata bari suna zuwa makaranta sai taga dama.
Muktar yace Hajiya Mairo ta kwantar da hankalin zai taimakawa yaran har ga Allah yin hakan nada lada,taimakon marayun Allah, sunyi sallama yace ta bashi awa biyu za
nemeta, Hajiya Mairo cikin farin ciki ta sauko k'asa, Zainab ta gyara ko ina gidan tasa turaren wuta sai k'amshi ke tashi, Hajiya Mairo cikin jin da'di tace Ummina sarkin aiki, Zainab har k'asa tai gaidata ta wuce sama don gyara dakin Hajiya Mairo, kudi ta gani kan gado bunch din dubu daya daukar kudin tayi, bayan ta k'ara gyaran gadon ta mayar da kudin dai-dai Inda ta gan su.
Bayan ta k'are da daki toilet ta wanke, tasa turare ta rufe dakin ta fito, Hajiya Mairo leader babba ta ba Zainab, Zainab tace Mumy sama za'a kai, tayi murmushi tace kayanki ne Ummina, Zainab cikin murna ta bude leader dogan rigunoni ne guda biyar da atamfa biyu da lace dinkaku, dogayen rigunoni sababine atamfofi da lace kayan su Laila ne ta dibo mata suma duk sababi ne.
Takalma biyu da kayan kwaliyya, Zainab hawaye suka zubo mata, tana godiya, Hajiya Mairo tace batason kukan nan, ta dauke ta tamkar Mahaifiyar ta,duk abun da takeso kar ta ji nauyin tambayar ta, abun da takeso ta rik'e mata amana, Zainab tace Mumy nayi maki alk'awalin zama da Ku tsakanin da Allah, Mumy kinyi min abun da bawanda yayi min rayuwata na gode Mumy, Hajiya Mairo tayi murmushi, kiran Muktar ne ya shigo wayar ta.
Hajiya cikin sauri ta dauki wayar, Muktar yayi mata bayanin gashi tare da Baban Sadiya da Maman Sadiya, Hajiya Mairo tace ya bata Maman Sadiya, bayan sun gaisa Hajiya Mairo tayi mata bayanin tun farkon zuwan Zainab Bauchi har kawo ta gidan ta, Maman Sadiya hawaye ne ke zubo mata, ko yaushe cikin maganar Zainab suke da Maigidan ta, sosai tayiwa Hajiya Mairo godiya.
Tace zasu zo suga gidan ita ma yar Bauchi ce, Hajiya Mairo tace zata turowa Muktar kudi ya kawo masu, su kula da Magaji, Maman Sadiya tace zasu yi iya k'okarin su, Hajiya Mairo tace Muktar din zai je wajen Baba Delu da Malamin su Magaji zaa ja mata kunne kan karatun Magaji, Maman Sadiya tayi murna sosai, tace hakan ma yayi, Zainab tun fara wayar Hajiya take kallon ta jin tana fadar Maman Sadiya Magaji.
Mumy ta mik'ama Zainab waya tana fadin Maman Sadiya ce kuyi magana, Zainab naji muryar Maman Sadiya sai kuka, Maman Sadiyar ma kuka takeyi, Maman Sadiya tace Magaji yaje makaranta dazun ya shigo ki kwantar da hankali zamu kula da shi, Hajiyar ki tace zata turo kudin lalurorin sa, bayan sun kare magana, Muktar yayiwa Hajiya bayanin wani dan unguwar ya ha'dasa da Baban sadiya, Hajiya godiya sosai tayiwa Muktar tace ya turo acct num ta, zata sa kudi ya basu Maman sadiya zata sa masa nasa, Muktar yace ya gode abun da yayi Allah ya bashi lada.
Godiya sosai tayi masa yace zai wuce makaranta su Magaji tare da Baban Sadiya, Zainab dakin ta wuce tayi wanka cikin murna da farinciki anjima zatayi magana da Magajin ta.
**** ****
Bayan an k'are gyaran gidan Abba Lawal ya wuce Abuja, tun zuwan sa Misau makwanci bai ha'dasa da Anty Amina ba, Abincin ma sai tayi masa da'di zai ci, har yaran sun fahimta, Ummi ta damu sosai, bayan ya wuce suna kici tana taya Anty Amina girki, Ummi tace Anty kiyi hank'uri da Abban mu, Anty Amina kallon Ummi tayi tana murmushi dole tace wani abun akayi Ummi tace naga wanan zuwan Abba fada dai yake yi, Anty tace ba komai Ummi watarana sai labari komai zai wuce.
Ummi shiru tayi tana tausayin mahaifiyar su, tasan ba k'aramin hank'uri takeyi ba, sosai ake zuluntar ta, Anty Amina hawayen dake son zubo mata ta mayar, daki ta wuce ta shiga toilet kuka sosai tayi, ta wanke fuska ta fito, kwalli ta shafa, Ummi ta shigo tace ana sallama, Dan Lami ne driver ya dawo dakai Abba airport a Bauchi, envelop ya bata , kudi ne da note suyi dinkin biki da su, amsar sak'on Anty tayi, bayan ta shiga daki ta kira yaya Maryam zata aiko a sayi lace a dinka masu na biki, a wajen yaya Maryam suke dinki kano.
Anty Amina bata son yaran su shiga damuwa tace su shirya su wuce wajen su Umman ta, cikin gidan suka wuce, Anty Amina ko yaushe tana ma Auwal addu'a Allah ya kare shi shairin su Mamee don tasan ba a banza Mamee zata yarda Maryam ta auri Auwal ba, dole akwai babban dalilin yin hakan, ko menen?.
Ta rok'i Allah ya kare Auwal din, ko sun ha'da kai da Hajiya Rabi ne? Maryam bata da natsuwa ba tarbiya Auwal wahala zaiyi, sauk'in abun Baba Ladidi na nan.
**** ****
Mamee hankalin ya kasu biyu, tana shirin biki tana tunanin Maryam , ko kadan hankalin ta bai kwantar da shirun Maryam ba, duk abun da akeyi kallon su takeyi, ana hakan Khalifa ya dawo, sosai ya cenza da ka kalle sa,kasan bayada natsuwa shaye- shaye yake yi sosai, Makarantar ma korosa akayi bai fa'dawa kowa ba, ranar da ya dawo wasu abokanin sa sukazo suka dauke sa, sai dare ya dawo gida buge, Mamee sosai ta tsorata da kyar suka shi daki suka rufe batason Abba yaga halin da yake ciki lokacin Abba baya gida.
Mamee zama tayi tana tunanin Anty Amina tayiwa Khalifa asiri, an samata hannu ne kan yaranta zata rama, bazata k'yale ba(Mamee kin mance Hakkin Wanda aka zalunta)
Maryam sun shirya yanda zasu yi da Zero, kwana biyu saura auren, Zero sai tsara yakeyi yanda Maryam zata shigo hannun sa, Maryam duk abun da Mamee tace tayi shi takeyi duk tunanin su Mamee Maganin yaci.
Hajiya Rabi kudi take amsa sosai wajen Alhaji Muhamud rabi duk gidan Malamai ake kai, har Marayam da Mamee takai ayi masa aiki, in anyi auren duk abun da takeso suyi kar suyi mata gardama, su Lailah yaran Hajiya Rabi shek'e ayar sukeyi yanda sukeso ba k'wafa ba hantara, in sun fita lokacin da sukeso zasu dawo lokacin Auwal na lafiya shi ke taka masu birki, Laila har Dan shaye shaye take taf'awa, duk uwar bata gane ba, ko yaushe alfaharin ta yaranta masu yanci ne rayuwar turawa akeyi ba takura, sosai HAK'K'I ke
bibiyar su, sun k'asa ganewa.
Ummu Asma'u (Sa'adatu)
07064551049.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifiyata, Allah yayi maku Rahama.
*sisters na gode sosai da addu'arku, wayyanda suka kirani da wayyanda suka aiko a rubuce Allah ya saka maku da alhairi ameen*
*Bismillahirahamanirrahim*
*Page* 27_28
Ranar Laraba su Mamee suka wuce misau, ranar jumma'a za'a daura aure, bayan daurin aure za'a yi dinner a Abuja, cewan Mamee da Hajiya Rabi misau k'auye ce bazasu yi komai a cen ba, daura aure dai zaa yi, su wuce Abuja, za'ayi har mothers day a Abuja.
Mamee sosai hankalinta ya kwanta ganin har sun wuce misau Maryam bata yi wani abun ba, duk tunanin su aikin da akayi wa Maryam ne yayi tasiri, sai yammah sosai suka isa misau, har Abba duk ranar suka sauka misau.
Anty Amina batasan zasu zo ba, sai bayan la'asar dan Lami driver yake fadi mata oga na hanya, sosai abun ya bata mamaki duk da tasan kwana biyu suka rage a daurin auren, cefane ta bada a k'aro aka dora masu abinci, baa kai ga k'are girkin ba Mamee ta iso, Mamee ta fara isowa da baya Abba ya iso, bayan an k'are girkin ta aikawa Mamee abincin.
Abincin Mamee tasa a dawo mata da shi, a fa'da mata a k'oshe suke Anty Amina sosai taji ciwon abun, ta shirya abincin Abba Lawal a falon sa, gefenta ta koma tayi wanka ta shirya cikin kyakyawar shigar riga da siket na shadda dark blue, cikin dinkunan da ya Maryam ke mata, tayi kyau sosai sai kace ba ita ke haihuwar su Ummi ba.
Ummi da Mubina na falon Anty Amina suna bitar alqur'ani Anty Amina ta fito Ummi murmushi tayi, tace Anty kinyi kyau, Anty dariya tayi ta wuce falon Abba,Ummi a ranta sai addu'a takeyi Allah yasa a k'are bikin nan lafiya batare da an wulak'anta masu Antyn su ba, duk zuwan da su Mamee suyi, ba ruwan su Maryam da su Ummi, cen farko duk sukazo misau yaran na tare, da baya Mamee ta hanasu hul'da da yanuwan su, ko sunzo kowa na gefen Mahaifyar sa.
Koda Anty Amina taje falon Abba ya shigo, suna zaune da Mamee, cikin ladabi ta gaida shi,ta gaida Mamee da tambayar ya hanya, Abba Lawal kallon Anty Amina yakeyi cike da sha'awar ta sosai kwaliyyar ta birgesa, Mamee ganin hankalin sa na kan Anty Amina ta fara jansa da fira tana dauke masa hankali, biye mata yayi.
Mamee ido ta tsurawa Abba tace tun a Abuja munyi maganar kwana biyu zanyi girkin ko ba komai akwai shirye_ shirye bikin da zamuyi, Abba cikin bin umurni yace to, ya juyo ya cewa Anty Amina, Balkisu zatayi girki, in tayi kwana biyu ki karfa, Anty Amina kallon Abba tayi tace to ba matsalar Allah ya tashe mu lafiya.
Ta fito falon, wani irin juya take gani, wani abun taji ya tsaya mata a wuya, Abba rabon sa da misau anyi wata daya, yana Abuja tare da Mamee yau din ma da yazo bata da girki, wanan wane irin tauye HAK'K'I ne, bama shi yayi mata ciyo ba, irin yanda a gaban Mameen ya wulak'anta ta, girkin da tayi masa ne yake ci, koda taje gefenta su Ummi sun shiga dakin su, tana kok'arin shiga dakin ta, Ummi ta fito daukar ruwan sha da suke ajiye wa dakin su, ganin Anty ta dawo, Ummi ta dauki ruwa cike da tunanin ko lafiya.
Duk da bata ga fuskar Antyn ba, tasan irin wulak'ancin da Mahaifyar su ke gani tun bata kai girman hakan ba, ruwan ta dauka ta wuce daki, Anty Amina bayan ta shiga dakin zama tayi k'asan center Capet din dake tsakiyar falon, tana zubar da hawaye, ranta ya baci sosai, arwala tayi ta fara sallah ta da'de tana karanta alqur'ani.
Bayan taji natsuwa, gefenta ta rufe bakin ta dauke da addu'oin tsari, kwantawa tayi ko kadan bata jin bacci, har asuba tayi bata runtsa ba, ba kalar tunanin da batayi ba, karshe ta mik'a lamarin ta gurin Allah.
Mamee bayan Anty Amina ta fita, murmushi tayi tace a ranta, kwana biyu nan da zanyi a garin nan sai na k'unsa maki bak'in ciki da har mutuwar ki ta dauke bazaki mance ba, kinyi kure na auren mijina, mijina ne in daya, mijin da na aura tun bayada komai na kare wahala da shi da kayan ki a kai, ki zo ki ji da'di kinyi k'arya Amina( ko yaushe tunanin Mamee Balkisu Abba Lawal ita daya ta wahala dashi don ta aure sa baya da hali, yanzun don ya samu kudi wata tazo taci wahalar da batayi ba, Mamee kenan don kina uwargida ko yaushe ita ke ikirarin ta, ita ce ta wahala da Abba Lawal to Mahaifiyarsa fa?, nata wahalar fa?
Babban kuren da mata keyi rayuwar su kenan ince na wahala da shi ince matarsa ta farko, duk wadda tazo bayan ki matsayin ku daya, ko mutuwa yayi maigidan ku, kashi daya bisa takwas din dukiyarsa da Allah yace a raba maku shi zaa baku, mata muji tsoron Allah, Allah kansa ya haramta zaluncin a kansa, Allah zai iya yafewa bawa duk girman laifin sa banda HAK'K'In wani, Allah yasa mu dace.)
Mamee kwana tayi cike da farinciki, Abba Lawal kwana yayi juyi a gado da kyar bacci ya dauke sa, duk motsin da yayi kyakyawar fuskar Anty Amina yake gani sosai yake buk'ace, tsoro da shakkar Mamee ne, suka sa shi bin umurnin ta, Mamee duk abun nan period take yi don bak'in zaluncin tasan girkin Anty Amina ne ta tauye ta, don tana tunanin ta saka mata bak'in ciki.
Anty Amina tun bayan sallar subahin suke kicin da Ummi, duk da daurewa take yi bata son Ummi ta fahimci wani abun, don tun jiya da yammah suka hada sinasir da cewan da safe zasu yiwa Abba sanin yanda yake son sinasir din,dole ta fito kicin din tafara tuya sinasir din, Ummin a kicin ta sameta suka cigaba da aikin, duk aikin da Anty Amina zatayi tare sukeyi da Ummi, Ummi sosai ta fahimci damuwa a fuskar Mahaifiyar ta, bayan sun k'are duk wanka sukayi suka sha k'waliyya abun su.
Ummi tace wa Anty Amina zasu shiga Babban gida, gidan dan iya da chiroma ainihin kakani su haka duk family ke kiran gidajen don makwabta ne gidan dan iya da chiroma hade suke,duk lokacin da su Mamee suka zo Ummi Babban gida take wuni ta jaye Mubina suje gun kakanin su, Anty Amina bata hana su ba,don bata son su fahimci wani abun, sinasir din ta zubawa Ummanta da Umman Abba suka wuce dashi bayan sun wuce karatul alqur'ani tasa a CD ta kwanta a falon tana bi.
Har goman safe gefen Mumy yaran bacci sukayi, don a cewan Mamee yaranta yan hutu ne, sai dai masu aiki suyi aikin gidan, yan aiki ne keta kai da komowa, Abba sai shadaya ya fito, soyayen dankali ya samu a table da ruwan zafi, tsuki yayi yasha tea kadan ya fita ko yaushe abincin gidan Mamee tea da soyayen dankali ko doya, wanda yan aiki keyi,cen da komai Mameen yi take yi, haduwar su da Hajiya Rabi tace isasar mace bata shiga kicin komai sai dai ayi mata, shine komai ta dai na, ita matar DC prison service.
Abba gidan Umman sa ya samu su Ummi suna cin sinasir tare da kakar ya shigo, cike da mamaki yace Ummi yaushe kuka zo nan tace basu jima ba, shiru sukayi har Mubina uwar surutu sosai abun da yayi masu wancen zuwan ya tsaya masu, duk yaji wani irin yasan akwai abun ke damun su, hannun ya wanke yasa hannu plate din Mubina yana cin sinasir din daman yunwa yake ji, duk yanda yaso yaran su sake suka k'i karshe Ummi tashi tayi ta shige cen bedroom din kakar ta kwanta.
Abba Lawal duk yaji ba da'di, bayan ya kare yayi magana da Umman sa ya fita, su Maryam sai da rana ta fito aka yi sallah, Zero ya kira ta toilet ta shige suna waya komai suke k'ullawa?.
**** ****
Muktar da Baban Sadiya sun samu headmaster su Magaji sunyi masa bayani ya goya masu baya, yace duk da Magajin ba kowane lokaci yake zuwa makaranta duk jarabbawar da akayi shike zuwa na daya ko na biyu.
Daga Makaranta wajen Baba Delu suka wuce, ganin Muktar da uniform din police da headmaster cikin Baba Delu ya mur'da, ta tabbatar masu Magaji bazai k'ara rashin zuwa makaranta ba, Muktar yace har islamiya tace duka
Bayan sun k'are, Muktar ya kira Hajiya Mairo, dariya sosai tayi da yake bata labarin yanda suka yi da Baba Delu, bayan Magaji ya dawo makaranta Maman Sadiya ta aiko kiran sa, lokacin Baba Delu ta fita, gidan ya wuce da addu'ar ya samu abincin, aiki sosai Baba Delu ta bar masa ba abinci, Maman Sadiya abinci ta basa yaci, bayan ya k'are ta kira Hajiya Mairo, Zainab Hajiya ta ba wayar, Zainab na kuka tana magana da Magaji duk wahalar da ake basa ya fada mata, kuka suke yi sosai, Hajiya Mairo sai fada takewa Zainab tana kara tadawa k'anin hankali.
Hajiya Mairo tacewa Maman Sadiya a nemi wanda zai taya Magaji aikin kamin lokacin islamiya, Maman Sadiya tace ga almajirinta nan zaije suyi tare, tasan Baba Delu sai dare zata dawo, Hajiya Mairo godiya tayi sosai, Zainab murna sosai take yi tana sawa Mumy albarka, hankali kwance suka wuce Islamiya dasu Zara, Audu sai kallon Zainab yake yi a zuciyarsa yana jin son ta, zai mata magana, duk da bai ga fuska ba, Zainab tayi kyau sosai cikin uniform din Islamiya.
**** ****
Baba Ladidi abun duniya ya dame ta saura kwana daya daurin aure, Auwal bawan Allah bai san komi ake ciki ba, ranar alhamis duk su Hajiya Rabi suka wuto kano, ranar jumma'a zasuyi sammakon zuwa misau, sai bayan jumma'a zaa daura aure, Baba Ladidi duk jikin ta yayi sanyi
A fuskar Hajiya Rabi, ta fahimci hasashen ta gaskiya ne, tasan tabbas wannan murna na Hajiya Rabi ba banza ba, duk dangi Alhaji Muhamud ba wanda yaran Hajiya Rabi ke kallo da daraja, Baba Ladidi na falon gefenta, Fadila ta shigo, Auwal na gefe yana wasa da jirgin wasan yara, Fadila dariya tayi tace bros mun fiso ka zauna haka, ba matsi ba takura, Baba Ladidi ranta ya baci, kamin tace wani abun Fadila ta fita,hawaye masu zafi suka zubo mata, hannu ta d'aga sama tana rok'on Allah ya kawo wa Auwal sauk'i, Allah ya bi masa HAK'K'IN sa.
Ummu Asma'u(Sa'adatu)
07064551049.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: HAK'K'I NE
*NEMESIS*
_Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Gaffarta.
*Bismillahirahamanirrahim*
*Page* 29_30
Sai da yammah su Ummi suka koma gida, gefen Mamee sai hidima ake yi, Anty Amina taje ta tayasu aikin Mamee tace ba wani aiki, daurin auren ya kawo su da an kare zasu wuce, zama k'auye sai yan k'auye, Anty Amina gefenta ta koma, bacci sosai tayi don jiya bata samu yin bacci ba, shigowar su ya Maryam da wasu dangin Abban Lawal dake wajen misau suka tashe ta.
Ya Maryam tace lafiyar ki ana biki kina bacci, Anty Amina ta fa'da masu yanda sukayi da Mamee, ya Maryam tace ko mu da muka shiga naga ta hade fuska, zamu koma cikin Babban gida, tun da cen zaa daura auren tayi nata hidimar, mu muyi namu a cen, 'diyar dan uwan mu ce, baza mu fasa hidimar biki ba, kema Amina gobe ki shirya ki shigo cikin Babban gida wajen yan uwan ki, ko baki auren Lawal, irin goben dole zaki gida, Anty Amina tace to, sallama sukayi mata suka wuce, da mamaki Mamee don yanzun wasu halayenta ke fitowa.
K'awayen Mamee sunzo daga Abuja sai zugata suke yi, kanta sama-sama bata kallon kowa da gashi, nata ganin ta k'are da Abba Lawal, Ummi gefen Anty suka wuce duk hayaniyar da ake yi gefen Mamee basuyi tunanin shiga ba, falon Anty suka zauna suna kallo, suna zaune Abba ya aiko dan Lami in akwai abinci a ba bak'i Anty shiru tayi, dan Lami na tsaye yana jira, ganin su Ummi sun zuba mata ido ta tashi zuwa kicin.
Abincin duka ta juyo a warmers ta bashi, tuwon shinkafa ne da miyar ganye, yasha busashen kifi da manshanu, warmer din masu kyau, ya dauki abincin ya fita, ta kofar baya ya fita don Abba Lawal yace kar ya bari Mamee ta gani, har su dan Lami sun san Abba shakkar Mamee yake yi, Anty tacewa Ummi taje ta dafa abinci in zasu ci, abincin kenan ta bada aka fita dashi, Mubina tace tea zasu sha da cake, Anty Amina tana yawan yin snacks in case bak'i, ko wani uzirin.
Anty Amina tunani take yi me Abba ke nufi da ita, amfanin ta, ta girka masa abinci, baya tsoron ranar da zai tsayu gaban ubangijin yayi bayanin yanda ya tafiyar da gidan sa, yau tun da garin Allah ya waye bata saka shi a idanun ta ba, yanzun ya aiko a bada Abinci yasan da ita kenan, bayan su Ummi sun shiga dakin su, sun kwanta, Anty Amina ta kashe TV ta wuce dakin ta, tayi shirin bacci call din Abba ya shigo, yace yana wajen gefen ta, ta bude kofar,kamar kar ta bude, taje ta bude, shigowar sa cikin falon ya rungumo Anty Amina, cikin mamaki take kallon sa, turesa tayi tace lafiya?
Bai ce komai ya jata zuwa cikin bedroom dinta, kan gadon ya kwanta ya jawo ta da karfi ta fada jikin sa, Anty Amina sai kallon ikon Allah takeyi, Lafiyar sa lau ko? cikin kunen ta ya rada mata, girkin kine kin sani nasani, Anty Amina cikin takaici ta tashi Abba ya kara kwantar da ita, karfi yasa mata, tun tana k'okarin k'watar kanta ta gaji ta k'yale sa, yanda yake yi mamaki abun ya bata sai kace wanda bayada wata matar, duk abun da ake yi.
Mamee bata sani ba, tana cen da bak'in ta, labari take basu ta hana Anty Amina girki, Abba Lawal tun bayan magarib tace masa tanada bak'i, sai kusan subahin Abba ya fita gefen Anty, zuciyarsa wani nisha'di yake ji Amina daban ce,cikin mata.
Ranar jumma'a Anty Amina ta shirya da su Ummi suka shiga babban gida, Mamee na gefenta tana hidimar bak'in ta, abincin duk hotel suka bada aikin, komai baa dora gidan ba,kudi sosai Abba ya bata, su ya Maryam ma ya basu kudi ayi abinci Babban gidan, koda Abba ya fito Anty Amina ta wuce, tun jiyan tace masa zasuje cikin Babban gida, kiranta yayi yace ta shirya abinci zai aiko adauka kudi ya aika mata, kayan abincin kadan aka k'ara ya Maryam tace suyi amfani da wayyanda aka siyo ba wanda ya koma wajen Mamee, duk nan Babban gida suke ta hidimar su, yan uwan ma duk wanda yaje wajen Mamee zai fito rai bace sam bata nasu na manyan mata abokaninta take yi, yaranta basa iya gaida yan uwan mahaifin su.
Hajiya Rabi tazo da nata mutanen hankalin Mamee ya dauke sosai, Maryam na dakin su, dasu Lailah yaran Hajiya Rabi call din Zero ya shigo, murmushi tayi ta fita waje tana waya, cen bayan gidan taje ta dauko jikar da ta boye cikin flowers, bak'ar abaya tasa har nikaf, baza tafa cewa Maryam ce, ta bayan gidan ta fita, keke napep ta hau ta wuce inda sukayi su hadu da Zero.
***** *****
Bayan Audu ya dauko su Zainab islamiya ita ce karshen fita motar Audu sai washe baki yake yi yana kallon Zainab, Zainab tun farkon Zuwanta ta tsanin irin kallon da Audu ke mata, ganin yana ta washe baki ta k'ara hade fuska, ta wuce cikin gidan Audu tsaye yayi, yana cewa yar aiki sai jin kai, zan bita a hankali har ta amince min,na samu mata.
A falo suka samu Hajiya Mairo tana diba wasu takardu, Zainab ta nunama tana fadin Ummina admission ya samu sai maganar fara zuwa makaranta, Zainab zubewa tayi gaban Mumy tana murna godiya sosai tayi wa Mumy, Mumy tace ba komai nan ne bayan gida, makaranta take,in zaa ajiye su Zara sai a ajiye ki, godiya takeyi wa Mumy, private ce mai saukin kudi nan bayan layin su Mumy take, ba laifi makarantar nada kyau.
Zainab kici ta wuce tana taya Larai aiki, duk da Mumy tace ta rik'a tsayawa ta huta Zainab duk Larai na aiki in ta k'are nata zata taya ta, sosai Larai ke son Zainab din, jin su Zara nata kuwa da murna, Zainab tacewa Larai ko sunyi bak'i ne, Larai tace ko suna waya da *HASHEM* ne, naji Hajiya na fadin kwanan zai zo hutu, Zainab ta maimaita Hashim waye haka?
Larai tace babban yaron Hajiyane saudiya yake zama, mutunin arziki, duk kirkin Hajiya ya shafe ta, yana da mutunci sosai,bayan sun kare aikin Zainab falo ta wuce, Zara cikin murna tace Ummin Mumy ya Hashim zai zo jibi Mumy tace ya yiwa Ummin ta tsaraba, Zainab murmushi tayi tace Allah ya dawo da shi lafiya, Mumy tace ameen kusha aiki, duk yazo su Zara basa da hutu,Zainab murmushi tayi.
Ummu Asma'u( Sa'adatu)
07064551049.