Ad Code

Bayani kan Zamantakewar aure A Kasar Hausa



A zamantakewar aure, miji da mata suna da hakkoki da kowannensu ya kamata ya kiyaye.

Abu na farko da ya kamata ma’aurata su sani shi ne: Allah ne Ya halicce su daga rai guda, wato annabi Adamu, sannan Ya halicci matarsa Hauwa’u daga gare shi domin samun natsuwa, to hakkin Allah a nan shi ne su bauta maSa Shi kadai ba tare da gwamutsa wani abu ba wajen bautar.

Wannan ya hada da dukan sauran abubuwan da imani da Allah ya kunsa.

Bayan wannan ya kamata ma’aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne shari’a ta dora wa kowannensu.

Zaman aure wani abu ne da ake fatan daga lokacin da aka fara tunaninsa ya zamo wani abu na mutu-ka-raba, domin hakan ne zai tabbatar da cewa an san abin da ake nufi da aure da kuma irin halin da za a shiga. Sanin hakkokin da ke kanka a matsayin miji, sanin matsayinki na mata a gidan aure yana da mahimmancin gaske, domin hakan ne zai ba da damar tabbatar da wanzuwar wannan aure.


Yana da kyau ma’aurata su sani, aure ba tsari ne na zama zuwa wani dan lokaci kayyadadde ba, wato da an chinye kayan gara an gama zakin amarci a kama masifa a rabu ba, a’a tsari ne da Allah Ya shirya mana shi, sannan Ya tsara mana yadda zamantakewar za ta kasance. Ya dora ma kowannensu; miji da mata wadansu dokoki. Idan muka ji tsoron Allah a cikin zaman auratayyarmu, za mu kasance cikin wadancan biyun da na ambata a baya.


Ya kasance zaman aure ne wanda a kowane hali kuka sami kanku za ku iya jurewa cikin yanayin jin dadi ko akasin hakan; cikin halin lafiya ko rashinta, domin a halin da muke ciki a yau za ka tarar daga karamin abu ya faru tsakanin miji da mata, wani abin ma bai kamata ko wanda ke bakin kofar dakinku ya sani ba, amma haka za ka ga ana ta yamadidi da maganar har sai ta kai ga rabuwar wannan aure.


Idan har za ku iya jure wa wahalhalun da kuka yi ta sha lokacin da kuke samartaka, me zai hana ku karfafi aurenku ya zama na har abada? A ’yan watanni a farkon aure har zuwa shekara daya ko biyu Allah kan jarabci ma’aurata, amma duk wadannan abubuwa ba za su zama wani dalili ne na samun sabani a tsakaninku ba idan har kun san dalilin da ya sa kuke zaune a matsayin ma’aurata.

Yana da kyau ma’aurata su san halayyar junansu ta hanyar da babu yaudara, karya, ko cuwa-cuwa.


Ya kasance ma’aurata sun fahimci hanyar da za su iya sulhunta kansu ba tare da wani mutum na uku ya shigo tsakaninsu ba, hakan na samuwa ne ta irin yadda kowannensu ya fahimci matsayinsa a zamansu na ma’aurata. Miji ya sani cewa ragamar tafiyar da gida a hannunsa take, a same shi mai kyautata wa matarsa, wannan ya hada da mazauni, tufafi, ciyarwa da uwa uba koya mata addini.


Haka ita mace ta sani hakkokinta ne kula da mijinta ta wajen kare masa kanta da dukiyarsa da yi masa biyayya gwargwadon abin da bai saba wa shari’a ba. Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tallafa wa juna a cikin halin zamantakewar gida, wato miji ya tallafa wa matarsa a wajen girki, shara, wanke-wanke da sauransu, ita kuma ta taimaka masa ta wajen wanki, guga da sauransu domin yin hakan na kara karfafa dankon zaman aure. Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tausasa wa junansu.


A matsayinka na maigida ka da ka kasance kullum mai ganin laifin matarka, kada kuma ka zamo mai yawan mita ga abin da aka yi maka na laifi. Hausawa na cewa ka gani, ka ki gani, ka ji ka kuma ki ji, wannan na nufin ba kowane abu za ka gani ka yi magana ba, sai abin da ka ga ya wuce gona da iri, a tsawata a kan abin da ya dace kuma idan aka yi maka laifi ka yi magana idan aka ba ka hakuri, to ka hakura, kada ka zama mai riko.

A matsayinki na mata, ki kasance mai hakuri a kan duk abin da mijinki zai yi miki ko da kuwa a kan laifin da kike da gaskiya ne, domin maza a mafiya yawan lokuta ba sa son karban laifi, to ki yi hakuri a irin wannan lokacin idan abin ya yi tsanani ma ki ba da hakuri, idan hakan ne zai zama mafita ko masalaha, don matar na tuba ba ta rasa miji. Idan rai ya baci a rika kai zuciya nesa, a rika duba abin da yake ginshiki wanzuwar auren.

Da fatan Allah Ya yi mana jagora; Ya ba mu ikon kiyaye zamantakewar auratayyarmu, amin.

Close Menu