************************
More Novels at https:/mynovels.com.ng
************************ 'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(01)
Kayataccen hotel ne na shak'atawa. Mafi akasarin mutanen dake zaune a farfajiyar wajen matasa ne da yawansu kuma 'ya'yan masu hannu da shuni ne. Mutane ne daga kabilu iri iri,ya had'a da larabawa da turawa uwa uba hausawa da fulanawa. Kowanne sha'anin gabansa kawai yakeyi ba ruwan wani da wani.
Lokacin k'arfe bakwai na daren alhamis. Daidai lokacin ne wata matashiyar budurwa sanye da siket wanda ko cinyoyinta bai gama rufewa ba da wata shegiyar riga wanda dashi da babu duk d'aya domin rabin jikinta daga saman wuyanta da kuma cikinta duk a bayyane suke. Kanta yasha gashin doki,ta tufkeshi da manya manyan ribbons har uku,maimakon tufkar ya kasance a tsakiya sai ya zamana a gefen b'arin kanta na dama. Fuskarta sai shek'i takeyi gata sarauniyar kyau. Lebban sun sha jan baki. (Nayi kyam rik'e da alk'alamina ina duban irin takalmi mai tsinin dunduniya dake sanye a kafarta tare da mamakin yanda bata ko tsoron ya karya mata k'afa. Ganin zata b'acemin ya sanyani watsar da tunanina nabi bayanta a guje yayin dana bar Hanne cillare a bayana tana cillara k'afafuwanta wanda hakan ya tunomin da Kayan moh...(Hasken Idaniya..na tagwayen marubuta...lol).
Cikin takunta mai sanya zuciyar dukkan wani d'a namijin da yayi kicib'us da ita motsawa take tafiya bata tsaya ko'ina ba sai gaban teburin wasu 'yan mata su uku wadanda duk cikinsu suma babu mai shigar arziki.
"Sexy angel"
Cewar wani bature dake zaune a kusa dasu, ya lumshe ido saboda wani irin k'amshi da ya busoshi. Bata ko kalleshi ba saidai ta murmusa saboda ta karanci da ita yake. Tsinken sigari ta janyo ta sanya a bakinta kafin tayi amfani da lighter ta kunna.
"Baby wallahi mutuminki yayi fushi,munkai (30mins) zaune tare dashi yana jira yaga b'ullowarki amma...."
Wacce aka kira da sunan Baby,ta dakatar da ita ta hanyar watsa mata kallo da shanyayyun idanuwanta,kafin ta fesar da hayak'in sigarin. Cikin zazzak'ar muryarta tamkar sarewa marar tashi sosai
"Ya kamata by now ace kin fahimceni sosai Manal, banason a dunga yimin karan tsaye a sha'anina ok? Da nasan ya bar nan da babu abunda zaisa nazo ."
Tana gama fad'in haka ta mike da niyyar tafiya,baturen nan ya katse mata hanzari
"Excuse me."
Bata ko kalleshi ba tayi gaba tana karkada jiki. Manal ta dubi yan matan nan kafin taja tsaki
"Zaman me mukeyi kuma? Saiku tashi mu wuce tunda 'yar mulkin tayi halin nata. Ta sanya muzo mu jirata,tayi mana rashin arzikin."
'Yar bak'ar cikinsu ta bugi tebur daidai lokacin da baturen nan ya katsesu da tambayar lambar wacce suka kira Baby. Harararsa sukayi kafin su bar wajen. Akan hanya bak'ar ciki wato Dalal ta ja tsaki
"Guy dinnan baisan wacece Baby ba da baiyi gigin tambayarmu lambarta ba."
Manal ta tab'e baki
"Kowane gayu idan ya tashi baby,baby. Sai kace muma ba mata bane. Ji fa yanda guys din wajen nan suka bita da kallo tamkar ita kad'ai ce mai abun kallo a jiki. Naga muma dai muna da dirin jikin nan da kyawun fuska ko? Me tafi sauran mata ne?"
Hibba wacce tun soma maganarsu batace dasu uffan ba ta saki dariya a daidai lokacin da Manal ke kokarin bud'e mota. Wannan yasa duk suka kalleta da alamar tambaya na me kuma ya bata dariya haka?
Hibba ta cigaba da magana
"Kuna b'ata lokacinku wajen had'a kanku da Baby Tasleem. Wallahi tayi mana zarra,ku nifa tunda nake a rayuwata ban tab'a cin karo da gogaggiyar 'YAR BARIKI ba wacce komai nata daidai da fushinta ke burgeni ba kamar Tasleem. Ta cancanci a kirata baby domin wallahi ku kanku kun sani daidai da mayuka da turarukan da take amfani dasu abun kallo ne. Ai samun guy irin KB wanda zai tsaya maka akan komai wanda ko mijinka sai haka abu ne da mai matukar wuya. Abu na gaba da zai k'ara tabbatar maku ita d'in ta dabance,ba kowane shara take mu'amala dashi ba. Wallahi komai muk'ami da kud'in mutum idan har bai yiwa Tasleem ba toh koda yafi kare naci karan kanku ne kunsan ba kulashi zatayi ba. Wannan sai mu."
Ta k'arashe tana 'yar dariya,inda ta k'ara k'ular da Manal da Dalal. A fusace Manal ke tuk'in har suka haura titi suka fita daga hotel d'in na Tahir. Kwarai su ukun sun kasance amininan baby saidai suna matukar kishin yanda ta fisu da komai,ta k'etaresu a harkar bariki. Haka Hibba tayi ta dariya tana k'ara b'ata ransu.
*******
Baby Tasleem bata tsaya a ko'ina ba sai kofar gidan KB. Hon d'aya tayi,maigadin yayi azamar wangale mata k'ofa sanin ko wacece ita ga maigidan. Da gudu ta shiga harabar gidan ta faka motarta ta fito. Cike da yanga ta nufi cikin gidan kai tsaye.... ..!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(02)
Tangameman falo ne,yasha kayan k'awace k'awace,b'ata lokaci ne tsayawa kwatanta kyawu da tsaruwar falon. Daga can wata 'yar kusurwa kuwa, matattakala ne wanda zai sadaka da sauran sashen na dake cikin gidan.
Baby bata b'ata lokaci ba ta haye saman kanta tsaye bata dire a ko'ina ba sai a falon da ta hakik'ance zata tarar da Kb. Fitilun wajen a kashe,ta lalubi makunninsu ta kunna,saidai wayam babu shi. Tana shirin fad'awa d'akinsa ne taji an rungumota ta baya. Ta d'an rufe ido kafin ta bud'esu tana murmushi yayinda ta k'ara damk'e hannuwansa tana murmushi. Tana jinsa ya d'ora hab'arsa akan kafad'arta bata iya hanashi ba.
"Kina sane da laifin da kikayimin ko?"
Ya fad'a daidai saitin kunnenta yanda ita kad'aice zata ji. Ta lumshe ido,cikin muryarta mai sanyi tace
"Laifinka ne, meyasa bakayi calling dina ba kafin kabar wajen? Na biya nasha mai ne shine dalilin jimawata. Kaima kasan banason yin nesa dakai."
Matashin saurayin da bai wuce shekaru talatin ba,bak'i saidai bak'insa mai kyau kasancewarshi d'an hutu,yana da kyawunsa daidai misali. Da ganinshi kaga cikakken namiji. Shine dai wanda aka kira da KB(Kabir). Ya saki Baby yayi gaba zuwa bakin firij dinsa,kofi ya dauka a saman firij din yana tsiyaya lemun da baya rabo da shan shi(barasa). Sanye yake da kayan bacci na(pyjamas),sai lokacin ya k'arewa Baby data zauna saman kujera kallo tun daga sama har k'asa kafin ya saki murmushi mai burgeta. Ta kauda kanta daga dubansa tana mai lumshe ido
"Kallon nan yayimin yawa,a rage."
Yayi 'yar dariya kafin ya dawo ya zauna gefanta
"Mamaki kike bani aduk lokacin da kikace bakyason nesa dani Baby,alhalin nasha gayyatarki zuwa Abuja inda acan nafi jimawa nan kuwa sai weekend,ke ma kin sani. Baki tab'a amincewa da hakan ba Baby,(I don't know your reason.)"
Ta tab'e baki kad'an kafin ta sakar mishi wani shu'umin kallo,baisan lokacin daya saki baki yana kallonta ba cikin shauk'i matuk'a.
"Kanason maimaita magana KB,munyi maganar nan yafi sau goma. Na sanar dakai dalilina,bazan iya binka ba domin banason shiga tsakaninka da iyalinka. Aduk sa'ilin da kake garin nan,nikam taka ce, muddin ka cire k'afa ka koma Abuja,ka zama ikon Yasmeen. So please mubar zancen banaso,daga yau kada a k'ara maimaicinta."
Kb ya cigaba da kurb'ar barasarsa yana dubanta cike da mamaki,ya za'ayi wacce kw ikrarin tana matuk'ar sonshi amma har ace bata kishi da matarsa. Wannan wane irin so Tasleem keyi mishi ne?"
Ta katse mishi tunani da salonta mai rikirkita tunaninsa,babu shiri ya mance a duniyar da yake.
******
Baby bata bar gidan KB ba sai washegari da yamma bayan ya cikata da kud'i. Nan ma da yayo mata rakiya kamar kada su rabu. Suna tsaye a wajen fakin,yana rike da ita a jikinsa inda yayi mata iznin zab'ar mota d'aya cikin tsadaddun motocinsa dake k'asan rumfar ajiye motoci. Saida ta kammala duban kowaccensu kafin ta zab'i
bak'ar (Mercedes Benz C300). Ya yafito direbansa da hannu,yayi mishi nuni da motar ba tare da yace uffan ba. Direban ya gyada kanshi cike da ladabi kafin ya fice. Can ya dawo d'auke da mukullin ya mik'awa ogansa,KB ya karb'a ya damk'awa Baby suka sakarwa juna murmushin kafin ta had'a mukullin da hannunsa ta sumbata.
"Thank you my soul,sai had'uwa na gaba."
Ta k'arashe tana mai kanne mishi ido d'aya. Baisan lokacin daya d'aga mata yatsunshi ba saboda duk lokacin da yake gaban Tasleem,mantawa yakeyk da komai sai ita. A gaban idonshi tayi ribas taja motar. Maigadi ya bud'e mata ta fita.
Akan hanyarta tasha kwanar shiga sultanroad taji anayi mata hon babu kakkautawa. Da fari ta dauka bada ita ake ba,saida ta rage sautin kid'an dake tashi ta k'ara duba side mirrow dinta,tabbas Honda civic dinnan ita take bi,a yanda ta lura da yacce fitilunta ke kawowa su dauke a lokaci guda tasan ita d'in akewa magana. Baki ta tab'e ba tare da tayi niyyar tsayuwar ba ta k'ara k'aimi wajen gudun da takeyi. Saidai me? Rikitaccen hon d'in da mai motar nan ke cigaba da danno mata ya fusatar da ita. Ala dole ta taka burki a ta tsaya,wannan ya sanyawa mai motar dake biye da ita taka burkinsa babu shiri gudun kada ya goga mata. Bata da niyyar koda fitowa daga cikin motar balle kuma mai shi ya samu damar cewa wani abu. Tana karkad'a yatsunta jikin sitiyari idanunta naga madubi tana duban motar ta bayanta. Bakin ciki ya turnuketa ganin an tsayar da ita sannan ba'a da niyyar fitowa balle kuma ayi magana. Takaici bai gama cika Tasleem ba saida taga motar nan tayi ribas tayi U turn ta koma baya. Wani wawan zuciya
daya taso mata batasan sadda ta juya ba itama ta bi motar. Gudu mai motar yakeyi,itama gudu take. Saidai abun bakin cikin suna zuwa danja ya b'ace mata domin kuwa yana ficewa kafin ta karaso aka dakatar dasu. Ta bugi sitiyari don bakin ciki,hakanan ta koma hanyar da ta nufa cike da bakin cikin yanda mai motar da batasan ko wanene ba ya raina mata wayo har haka.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(03)
A fusace ta wuce su ta fada kan kujera tana huci kafin ta janyo kwalin sigarin dake ajiye saman center table din,wanda da wuya ka rasa shi a wajen. Ta zari d'aya ta soma zuk'a.
Manal,Hibba da sauran abokan watsewarsu maza da mata duk suka bita da kallo cikin rashin sanin tak'amaiman dalilin fushinta.
"Baby ke da wa?"
Cikin murya irin na wacce ta sha kwaya,Hibba ta tambayeta. Ta kauda kai tana fesar da hayak'i,kafin ta sanya hannu ta cire tufkar da ta yiwa kitsonta na gashin doki,ya zubo har kafad'unta.
"Uban waye ne? Ina zan sake samun damar cin karo da mai motar nan?"
Hibba ta dubi Manal wacce tayi filo da cinyar abokin watsewarta,Manal ta tabe baki inda ta juyar da kanta gefe don kuwa zuwa yanzu kishin Baby fal cike a zuciyarta. Wani d'an karambanin aka samu ya kai hannu da niyyar tab'a fuskar Baby,batayi wata wata ba ta mik'e ta wankeshi da mari gami da nunashi da yatsa.
"Ba kowane tsami ne yake da damar tab'a jikina ba! Daga yau ina mai gargad'inka ka nisantar da kanka daga gareni if not..."
Tayi kwafa ba tare data k'arasa ba ta dauki mukullin mota da jakarta ta haye sama.
Dariya gayun suka sanya mishi,wani dake can gefe yana kokarin jona socket jikin TV ya d'ago mishi hannu
"Sorry Baaba,wannan fa babban goro kake gani sai magogin k'arfe. Ka kiyaye a zauna lafiya."
Wanda aka kira da baaba ya shafa kumatunsa yana murmushin takaicin marin da Baby tayimishi kafin yayi kissing hannunshi
"Me takeji dashi? Kud'i ko kyau?"
"Babu wanda bata ji dashi,kasan babu abunda zaka nuna mata don ubanka.Da kud'inka tsohonka kake tutiya,ita kuwa harkarta har da sa'annin ubanka da gayu irinmu da suka dame tsoffinmu a kud'i da komai Baby gogayya take dasu."
Baaba ya jinjina kanshi yana murmushin da shi kad'ai yasan manufarsa kafin yayi wuf yabar wajen. Suka k'ara sanya dariya,banda Manal wacce takeji tamkar ta tashi da kifawa Musty mari yanda yake ta kod'a Baby. A fusace ta mike zaune zatayi magana saidai ta fasa sakamakon kid'an da ya cika ko'ina na gidan. Nan wasu suka mik'e suka hau casu alhalin ga kiran sallah can na magrib yana tashi a masallatan unguwa.(Allah Ya shiryemu,amin.)
Baby tasleem kuwa tana shiga d'akinta wanka tayi na musamman ta fito ta k'ara mulke jikinta da mayuka da turarukanta tsadaddu kafin ta shirya cikin wata gown mai tsaga a gefe gefenta,tun daga gwuiwa har k'asa. Ta k'ara gyara gashinta,ta fesheshi da Hairsprays kala kala. Kafin tayi zaman shafa jan farce a yatsunta kalar skyblue(wato kalar gown dinta). Ta kwashi awa kusan uku gaba daya yayin wankan da komai nata na shiri. A lokacin da take jiran bushewar faratan nata ne,Dalal ta turo k'ofa ta shigo. Itama ta had'e cikin riga da wando matsastsu masu bin jiki. Sai taunar cingam takeyi na yan bariki ta rike k'ugu tana duban Tasleem wacce kallo d'aya tayi mata ta madubi bata k'ara dubanta ba.
"Zaki gidan Momi ne ko muyi gaba?"
Kamar bazatayi magana ba,har ta k'ular da Dalal.
"Kuje,zan biyoku. Hibba ta jirani mu wuce tare."
Harararta Dalal tayi kafin tayi gaba tana jan tsaki yanda Baby bazata jiyota ba. Ta iske Hibba cikin shiri zaune a saman mota
"Hakimar tace kiyi jiranta ku taho tare. Munyi gaba,kinsan Momi batason a b'ata lokaci."
Hibba tayi murmushi domin tasan yanda Momi ke ji da Baby ko don masu gidan ranar da take kai mata a kowane sati,domin nata kyautar ga Momi yafi na dukkansu yawa.
"Kada ku damu kuyi gaba."
Manal ta bud'e wutar hon,da azama Dalal ta shiga suka tafi. Basuyi mintuna da barin gidan ba,Baby ta fito cikin takunta na jin ita d'in ta isa tana tafe ko'inanta yana rawa,tana amsa waya tamkar bataso. Hibba dai kallon ikon Allah takeyi,har ta soma zargin kodai Baby 'yar wata basaraken ce? Haka tayi ta kallonta ita kuwa batasan ma tana yi ba,mota ta bud'e ta shiga ba tare da ta cewa Hibba uffan ba. Don kanta itama ta bud'e gidan gaba ta shiga. Minti uku da soma tafiyarsu,Hibba ta fahimci da shahararren mai kud'in nan Baby take waya, wato Alhaji Ridwan Naira. Gudu takeyi kasancewar dare ne,hakan yasa tafiyar mintuna talatin,sai gashi minti goma sha biyar ya kawosu gidan MOMI......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(04)
Falo ne babba,cike yake da matasan mata da manyansu. Kowacce tana ji da kanta da ganin tafi 'yar uwarta. Wacce aka kira fa Momi tana hakimce a saman kujera mai zaman mutum biyu ta kishingid'a tana cin tuffa. Kallonsu takeyi d'aya bayan d'aya fuskarta dauke da murmushi. Kowaccensu tasha shiga ta alfarma,saika rantse wani shagalin akeyi. Daidai lokacin Baby ta sanyo kai,a bayanta Hibba. Matasa da yawa dake mutanenta ne,suka hau jinjina da ihu
"Shegiya Baby,manya a baku naku daban."
Ta sakar musu murmushi mai bayyana hak'ora tare da mimmik'a musu hannu suna cafkewa. Manyan kuwa gaisheshu tayi kafin ta isa ga Momi wacce ta zuba mata ido tana murmushi. Hannu ta dunkule,alamun jinjina
"Na gaida uwata,ranki ya dade tuba nake."
Momi ta ja hannunta ta zauna da ita gefanta tana dariya ga hakoran Makkah farare a hakoranta biyu na gefe da gefe.
"Bakya laifi gareni baby."
Daga haka Momi ta juya don soma abunda ya tarasu. Magana ce aka cigabansu a harkokinsa. Ta kara gargad'insu akan su kiyaye kada su bari ciki ya shiga jikinsu koda wasa. A karshe ta dubesu sosai
"Maganata ta karshe ku sani, babu aure a tsarinmu. Nasha sanar maku koda ya kasance zakuyi auren,toh fa baifi na wata uku ba kin fito. Auren ba talaka ba,mai hannu da shuni,ki tabbatar kin tatso mana mai yawa kafin ki datse igiyar auren naki. Wannan shine jawabina. Batun balance kuma,ina jiranku babu wacce batasan acc.no. dina ba."
Haka suka jima suna tattaunawa kafin taro ya watse,Momi ta dubi Baby wacce tayi haramar tafiya. Lokacin karfe sha biyu da mintoci
"Baby baby,kodayaushe tauraruwarki kara haskawa takeyi. Ba daga kananun ba,daidai da manyan suna son mu'amala dake. Ina kuma ga an lek'a ga Hajiyoyinmu duk da dai kin nuna wannan baya kanki yanzu."
Baby tayi murmushi ta girgiza kanta
"Momina kenan,me zanyi da jinsi irin nawa? Wannan babbar kazanta ce, wannan dinma da nakeyi fatana nan gaba na daina."
Momi ta kyalkyale da dariya tana mai dafa kafad'ar Baby
"Babu ranar da wannan fatan naki zai tabbata kuwa,zan maki uzuri da alama bakisan alfanun jinsi ba sai nan gaba."
Baby tayi murmushi mai had'e da jan numfashi
"Ba halina bane,baya daga abunda nake sha'awar aikatawa. So,in sha Allah bazan tab'a bin wannan hanyar ba."
"Ja'irar kaya,ashe har yanzu kinsan da sunan Allah? Toh ba laifi muje zuwa."
Abun sai ya bawa baby dariya,ta d'an dara kafin ta mik'e tayi hanyar fita
"Momi kenan,na barki lafiya."
******
Mutum ne matsakaici,mai dogon fuska,yana da matsakaicin hanci saidai akwai magana(idanu). Girarsa a cike kuma bak'i wuluk,kamar dai yanda sajensa da gashin kansa yake. Fari sol,zubin Fulani.
Zaune yake a ofis yana aiki akan Laptop. Hankalinsa gaba d'aya ya tafi ga aikinsa,kallo d'aya zakayi mishi kasan yana hutawa. Daidai lokacin aka bud'e kofar gami da yin sallama. Ba tare daya kalli mai sallamar ba ya amsa ciki ciki kasancewar ransa a b'ace yake dashi. Ya k'araso da fara'a ya zauna
"An gaida mutumina,ba fad'a mai ya kawo gaba kuma? Ace har ka iso garin nan saidai don rashin mutunci ko waya bakayi domin sanar dani ba sai a bakin kanwarka na tsinci labarin."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(05)
Har ya gama maganarsa baice mishi komai ba. Ganin haka ya buga tebur wannan yasa shi watsa mishi wani irin kallo kafin ya karkato yayi juyi da kujerarsa yana fuskantarshi. Fuska a daure yace
"Kana da kunyar takowa ofishina bayan wulakancin kayimin?"
Cikin rashin fahimta,KB ya zuba mishi ido kafin ya tambayeshi
"Me kake nufi wai Haris? Nifa bansan takamaiman laifin dana aikata ba."
Ya dubeshi kadan kafin ya girgiza kai
"Jiya,(around 6:00pm),na had'u dakai anan wajejan sultan road. Saidai abun mamaki nayita hon baka tsaya ba saida kyar,karshe ma don rainin hankali kak'i fitowa daga motar. Saidai a yanda ka nuna yanzu ya tabbatar min ba kaine cikin motar ba saidai tabbas lambar motarka ce. Na soma tunanin direbanka ne,toh a gaskiya ka chanja direba,domin bakayi dace ba wallahi da zan ganshi zai sha mari ne...."
Kb ya katseshi
"Tsaya don Allah,gayamin menene ya faru?"
Haris ya labarta mishi,ya k'arashe da cewa
"Mercedes Benz dinka ce, kada kaso kaga gudun da direbanka ke...."
KB ya katseshi a kunyace
"Oh,Baby ce a ciki fa."
Haris ya yamutsa fuska
"Who the hell is Baby?"
Kb yayi murmushin basarwa
"Wata cousin d'in Mamina ce,ta ari motata ne tun kusan (last two days.)"
Haris ba don ya yarda ba,sai don kawai bai fiye bin kwakkwafin abunda bai shafeshi bane,ya gyada kanshi
"Ok."
Daga haka suka bar zancen suka fad'a hirarsu.
*****
Kabir Idris Babangida da Haris Aliyu Kazaure. Aminan juna ne,wadanda amintarsu ta samo asali tun daga iyayensu maza wadanda suma a baya can makwaftaka ta had'asu tun suna kauyensu na Kazaure kafin Allah Ya azurtasu a garin Kano. Kowannensu yayi gini na gani na fad'a ya dawo birnin Kano da zama.
Makaranta d'aya Haris da Kabir sukayi. Har ya zamana sun karanci course d'aya,wato business.
Kabir shi kad'ai ne d'a a wajen mahaifinsa Alhaji Idris. Shi kuwa Haris,su biyar ne. Saboda zumunta dake tsakanin iyayensu wadda bata wasa ba,ya sanya Alhaji Aliyu daukar Haris tun yana d'an shekara biyu ya damk'awa Alhaji Idris da matarsa Hajiya Jamila. Sunyi murna matuk'a domin Allah Ya sani,tun Haris na jariri suna matukar kaunarsa,kai bama su kad'ai ba. Mutane da yawa suna kaunar Haris saboda kyawu da farin jinin da Allah Ya bashi. Hajiya Aisha kuwa,mahaifiyar Haris mace ce mai alkunya wannan yasa ko kusa bata nuna damuwarta akan wannan kyautar ba tunda ga YASMEEN da sauran yaranta uku a gabanta.
Haka Kabir da Haris suka taso cikin kaunar juna da tsananin gatan da ake nuna musu. Rayuwarsu saita burgeka na yanda suka shak'u.
A fannin halayya kuwa,nan suka bambanta domin Kb mutum ne mai matukar son 'yan mata,karshe ma ya fad'a harkar nemansu. Abun bai k'ara gaba ba saida sukaje Malaysia karatu.
Duk abunda yakeyi yakanyi kaffa kaffa gudun kada Haris ya sani saidai kuma ba'aje ko'ina ba ya ganeshi. Yasha fama dashi kwarai dagaske domin har k'ararsa yakai wajen Alhaji Aliyu. Nan ya kirashi yayi mishi tas kafin daga bisani Kb ya daukar mishi alk'awarin ya dauka,nan ma ya daukarwa abokinsa alk'awarin dainawa. Hakan kuma bata canza zani ba,domin da abun ya bunk'asa sai ya zamana ma hatta da shaye shaye,KB yana gwada aikatawa.
Haka dai har suka kammala karatu suka dawo,saidai fa tun dawowarsu KB ya dora ido akan Yasmeen yaga yanda ta koma cikakkiyar budurwa. Nan ya shiga tura kanshi gareta. Ga Yasmeen kuwa,tuni itama ta mato akan kaunar Yaya KB. Wannan ya sanya ta bashi kai,soyayyarsu ta k'arfafa. A karshe iyayensu sukaji daga bakin Kb,ran Haris baiso 'yar uwarsa ta auri Kb ba. Ba wai don bai kaunarsa ba saidai tsoron halayensa a ganinsa tamkar bazai fasa ba.
A haka dai iyaye sukayi na'am,aka sanya ranar aure da zarar Yasmeen ta kammala secondary,idan yaso ta k'arasa a dakinta. Kafin auren ya iso,tuni Kb fa Haris kowanne ya kama aikinsa. Inda Alhaji Aliyu ya d'ora KB a matsayin manajan babban kamfaninsa dake a garin Abuja. Wannan mukamin da Alhaji Aliyu ya bawa Kb,ya bawa dukkan yan uwan Alhaji Idris mamaki,karshe suka k'ara ganin girma da kimar Alhaji Aliyu. Shima Abba yace baza'a barshi a baya ba,nan ya d'ora Haris a manajan kamfaninsa a Kano. A cewarsa baza'a yiwa danshi wannan son kan ba. Ba karamin karfi hakan ya sanya zumuncinsu ya k'ara yi ba. Shakuwa sosai da fahimtar juna. Ya zamana Kb baya dawowa garin Kano sai weekend. A haka har Allah Ya daukakasu.
Bayan aurensa da Yasmeen da shekara daya ya siya gidansa na kansa a garin Kano. A cewarsa nan iyalinsa zasu dinga sauka ba sai sunje gida ba. Shima Haris yana da hadadden gidansa mallakinsa a garin Kano.
Babbar damuwar iyayen,auren da Haris bashi da niyyar yinsa. Wannan ba karamin daga musu hankali ba musamman ma ga mahaifiyarsa wacce tafi damuwa ainun. Ganin ya nuna shi kam baiga matar aure ba saidai ko nan gaba wannan ya tsoratasu,suka tashi da addu a zatonsu aljana ce ta auri d'ansu.
*****
HADUWAR BABY DA KB NA FARKO........
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(06)
Haduwarsu ta farko a Nightclub ne. Kb yana zaune da abokinsa,Nas. Bai jima da isowa wajen ba,ya hau kallon gayun wajen domin ganin ta inda zai samu wacce tayi mishi. Shi kam a farko ya raina matan kano,ganinsa basu da wani wayewa na azo a gani. Wannan yasa yafi yin shegantakarsa a Abuja.
Maza da mata ne,kowannensu babu mai shigar kirki,ga kid'an dake tashi tamkar zai fasa wajen. Rawa sukeyi marar kyawun gani,a gefe kuwa wasunsu zaune suna iskance iskancensu basu ko damu da idanun mutune ba. Cikin nishadi ya tsiyaya barasa da niyyar kwankwad'a,yana niyyar kaiwa bakinsa ne ya hangota zaune cikin shigar kananun kaya kamar sauran matan wajen. Taci ado har ta gaji da had'uwa,shisha take sha hankalinta kwance. Tamkar bafulatana saboda hasken fatarta mai kama da madara,ga wani dan iskan rigar dake jikinta wanda bai rufe komai nata ba kasancewarsa shara shara.
Nas ya lura da hankalin abokinsa bai tare dashi,hakan yasa shi juyawa don ganin abunda yake kallo. Murmushi yayi kafin ya juyo ya taimaka wajen tura kofin hannunsa bakin KB,sai lokacin KB yasan ya lula tunani. Nas ya gyada mishi kai hadi da daga gira
"Baby tasleem sunanta,kaf bebs dake nan gurin babu wacce zata nuna mata komai na halitta. Ina gayamaka tana ji da kanta,gata da class. Ba kowane guy take mu'amala dashi ba. Kada ka kuskura ka tunkareta domin ba karamin aikinta bane ta disga ka a gaban kowa ba wajen nan."
Kb yayi murmushinsa,ya sanya hannu ya k'ara kwantar da sumar kanshi.
"Dats my girl,haka nakeson mace. Sha kuruminka kayi kallo."
Nas yana kokarin dakatar dashi saidai tuni shi kuma ya mik'e ya nufi inda baby ke zaune. Wannan yasa Nas tsayawa kallon ikon Allah tare da fargabar irin wulakancin da za'a yiwa abokinsa.
*****
Kb yana zuwa ya nemi kujerar dake fuskantar baby ya zauna. Baice da ita komai ba,sai kallonta da yakeyi itama ta kalleshi sau d'aya ta maida kanta ga abunda takeyi. Murmushi yayi kafin ya rik'o shishar hade da hannunta. Wannan ya sanyata dagowa a fusace tana dubanshi,saidai tunda baby take a rayuwarta bata taba cin karo da wanda dubansa ya sanyaya jikinta ba sai Kb. Tayi makwas bata iya hanashi abunda yake niyyar aiwatarwa ba. Rike da hannunta ya zuki shishar kafin ya d'ago ya dubeta. Ta kauda fuskarta,bazaka fahimci yanayinta ba sakamakon bata daure fuska ba kuma bata saki ba. Ta janye hannunta,ta mike tayi hanyar fita. A sannu take tafiya har ta kawo titi,saidai wayam ba motoci,gashinan manal bata gama shagalinta ba balle saurayinta ya maidasu gida. Hon taji ana yi mata,bata ko kalli motar ba,saida ya iso daf da ita ya faka ya fito. Ta saci kallonsa,shine dai. Ya bude mata mazaunin kusa da direba yana mai mata nuni a ladabce cikin murmushi
"Ba girmanki bane ranki ya dade,a ganki war haka a tsakiyar titi kin rasa abun hawa. Idan babu damuwa kizo ki shiga motata duk da nasan matsayinki ya wuce ki hau jagwal dita."
Ta dubi motar.babbar harka ce kwarai,range rover. Saima ya bata dariya,wannan ya sanyata murmusawa.
Lahaula! Tuni ta k'ara kashe Kb,ya sanya hannunsa akan murfin motar yana dubanta cike da murmushi,jinsa yake duk babu laka a jikinsa. Har ya fidda rai bazata shiga ba saidai ga mamakinsa yaga ta shiga ta zauna,cikin jin dadi ya rufe motar ya shiga ya zauna. Sai lokacin ya dubeta bayan ya matso daf da ita,murya kasa kasa yace
"Fatan zan samu rakiya gidana?"
Ta juyo ta dubeshi,numfashinsu na bugun juna,ta kauda kanta tana murmushi wannan ya bashi tabbacin amincewarta. Da gudu yaja motar, bakajin komai sai kid'a dake tashi ga sanyin Ac.
*****
Tun daga wannan ranar Kb da Baby suka dinke,dinkewa kuwa bata wasa ba. Su kansu su manal sunyi mamakin inda baby ta samo hadadden guy har haka. Karshe har gida ya sanya aka gyara musu,kudin kuwa da yake aikawa baby abun yaso ya baci. Ga sauran manyan da take harka dasu suma ba'a barsu a baya ba wajen cika mata account. Karshe Kb ya hanata mu'amala da kowa,acewarsa shi kadai ya isa dauke mata nauyin komai. Baby murmushi kawai tayi ta bishi a hakan,saidai kuma abunda bai sani ba,duk sadda yasa kafa ya koma Abuja babu irin tsiyar da bata shukawa da manemanta. Mota kyauta ya bata,wasu lokutan idan taga dama koda baya gari,zataje gidansa ta huta ta fita da motar da takeso. Babu wanda yake cewa uffan cikin ma'aikatan sanin matsayinta a wajen ogansu. Saidai suyita gulmammakinsu tare da rok'awa maigidansu shiriyar Allah.
******
Ta gama komai na tarar mijinta,ta gyara gidanta da jikinta. Jiran dawowarsa kawai takeyi.
Tana cikin sanyawa diyarsu,Nasreen,ribbon a jelar kitsonta,taji shigowar motar mai gidan. Nasreen ta kwace kanta daga wajen maminta tayi waje a guje.
"Daddy oyoyo,daddy oyoyo."
Haka tayita fad'i har takai ga jikin motarsa. Ya fito ya daga diyarsa cak yana sumbatar kumatu da goshinta cike da farin ciki ganinta.
"Bebin daddy oyoyo,I miss you soo much."
Tana ta dariya haka suka shiga ciki. Ya ajiye nasreen,daidai lokacin Yasmeen ta karaso tana duban mijinta cike da so da kauna saidai fa a sanyaye take sanin da tayi waccan zuwan nashi bai wani saki jikinsa da ita ba. Abu kadan da baikai ya kawo ba zai soma gayamata magana.
"Sannu da zuwa."
Ga mamakinta taga ya amsa tare da rungumeta. Ta saki ajiyar zuciya gami da hamdala a ranta.....!
Rufy: 'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(07)
Ya dagota yana mai riko kafad'unta
"Ya dai na ganki haka a sanyaye? Ko bakiyi murna da zuwana ba na juya?"
Ya saki kafadunta ya soma tafiya da baya, da hanzari ta riko hannunshi tana dariyar farin ciki
"Wace ni na guji prince dina? Barka da zuwa."
Ta ja hannunshi suna murmushi har zuwa d'aki,Nasreen tana biye dasu.
Yasmeen mace mai biyayya,ta taimaka mishi ya gyara jikinsa ya sanya kayan shan iska. Sannan suka fito ta zuba mishi abinci yaci.
Ranar kam sun farantawa juna saidai ko kusa zuwa yanzu bayajin dadin mu amala da kowacce mace sai Baby. Yau dinma tausayin matar tashi ne ganin yakan jima bai kusanceta bane.
*******
JUMA'A,5:00pm
Baby ce tafe cikin motarta,tuki takeyi cikin kwarewa. Kallo daya zakayi mata kasan tana cikin nishad'i. Dawowarta kenan daga gidan gonar Alhaji Ridwan Naira,wanda kusan sati yayi yana magiya da rokonta akan don Allah tazo gareshi. Sai a yau baby taga damar amsa kokensa bayan ta jera satuttuka tana lashe kud'ad'ensa.
Kai tsaye gidan Kb ta nufa duk da cewar tasan bazai shigo Kano wannan satin ba gudun kaucewa zargin iyayensa da matarsa. Yau kam a gidansa take sha'awar kwana don tasan koda ta koma bazata samu su Dalal a gidan ba. Manal tana Kaduna,yayinda Hibba da Dalal ke tare da mutanansu a gidajen shak'atawarsu.
Tayita hon saidai maigadin yayi nisan kiwo,wani maigadin ne daga makwafta yazo ya bud'e mata ta shiga. Ta fiddo 'yar bigmama dinta da wayoyinta ta rufe motar ta shiga ciki. Bata da matsalar mukullaye kasancewar tana da safayar kowanne mukulli na gidan a wajenta duk saboda mukamin data samu a wajen Kb. Wanka kawai ta fad'a sakamakon gajiyar data kwaso.
Daidai lokacin ya shigo layin,duk a zatonsa aminin nashi ya shigo gari kamar yanda ya sanar mishi a waya cewar watakila ya shigo. Hon yayi har sau uku,maigadin har lokacin bai kusa. Wanda ya bude kyauren da farko shine dai ya k'ara zuwa,Haris ya sauke gilashi ya yafitoshi da hannu. Yazo cike da ladabi ya kwashi gaisuwa,haris ya amsa gami da tambayar
"Mai gidan yana nan?"
Maigadin ya dubi gidan kafin ya dubeshi
"Eh toh,inaga dai yana nan don Hajiya bata jima da dawowa ba ni na bude mata kofa."
Haris ya dauka kanwarsa Yasmeen ce, yaji dadi domin yayi kewarta sun kwana biyu basu hadu ba saidai gaisuwa ta waya. Ya jinjina kanshi
"Taimaka ka bud'emin mana."
Da azama ya bud'e mishi ya shiga ciki yayi fakin. Bayan ya fito ya tsurawa motar da baisan da zamanta ba a gidan ido,cike da mamakin mamallakin motar ya dubi gidan kafin kuma ya tunkari cikinsa.
Fitowarta kenan daga wanka,tana shirin goge jikinta taji sallama a falon gidan. Farin cikin ya k'aru,ashe daman zai zo gari shine bai sanar da ita ba duk da wayar da sukayi? Cikin sauri sauri ta nufi hanya ta fita.......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(08)
Tana fitowa falon,wayam! Hakan ya tabbatar mata daga falon k'asa ne. Sai ta soma shakku akan anya kuwa Kb ne? Don bai tab'a tsayawa k'asa ba sai ya k'araso falon sama.
Haris jin da yayi sallamar ba'a amsa ba,kawai ya tunkari falon sama yana fadin
"Little,ina kika shiga ne?"
Baby ta tsaya cak daga bakin matattakalar,kafin takai ga yunkurin kaucewa har ya nufo benen. Ido hud'u sukayi,duk da batasan ko waye ba saida ta d'an tsorata. A gefen Haris kuwa,kallonta yayi tun daga k'asa har sama,bai k'ara marmarin kallonta ba. A fusace ya juya kanshi yana mai kokarin korar shaidan daga zuciyarsa. Cikin kakkausar murya yace
"Who are you?"
Cike da mamakin yanda gayen ya juya baya daga barin kallonta,baby ta kalli jikinta. Tawul ne ko cinyoyinta bai gama rufewa ba. Ita kam bata taba ganin namijin daya ganta haka ba harma ya iya juya mata baya ba sai a yau.
"I said who are you?!!! Mekikeyi a gidan nan?!!"
Ta razana matuka,tunda take wallahi ba'a taba yi mata tsawa har irin haka ba a rayuwarta. Ta tsaya kyam tana dubansa bata ko iya bud'e bakinta ba. Jin tayi shiru ne yasa shi juyowa a fusace ya karasa hawa matattakalar baiyi wata wata ba ya d'aga hannu da niyyar marinta,sai lokacin ta iya karfin halin rike hannunshi. Kallon juna sukeyi ido cikin ido,wani kwarjini yakeyi mata wanda ya hanata yin magana cikin tsiwa. Ta saki hannunshi ta kauda idanuwanta fuskarta a daure
"Ganganci ne tab'a lafiyata,gaba ka kiyaye."
Ta ja baya ta janye kafafuwanta daga matattakalar zuwa sama. Ya zamana matattakala uku ce tsakaninsu,ta tsuke baki kafin ta kad'a idanuwa ta k'ara dubanshi,har lokacin kallonta yakeyi saidai cike yake da mamakin karfin halinta,ganin yanda ta iya rike hannunsa da nufin dakatar dashi.
"Game da tambayar da kayi,ka tambayi kb. Inaga shine yafi cancanta ya baka wannan amsar ko?"
Ta k'arashe tana mai murmusawa,daga haka ta juya ta tafi. Haris na tsaye har saida ta b'acewa ganinsa,ransa idan yayi dubu toh ya b'aci. Ashe har yanzu Kabir bai bar neman mata ba? Ya rasa irin wannan akuyanci na Kb,menene amfanin auren nasa toh? Tsananin tausayin Yasmeen ya turnukeshi. Saidai ya rantse bazai tafi ya bar tsinanniyar karuwar nan a gidanta na sunnah ba,dole ta fice yanzu kuwa!
Gama tunaninsa keda wuya ya nufi hanyar data bi a fusace,saidai kuma tunanin da yayi na watakila a wannan lokacin tana shiryawa ne,ya sanyashi tsayawa a falon gami da samun waje ya zauna. Layin wayar Kb ya shiga nema......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(10)
"Assalamu alaikum warahmatullahu wabarakatuhu."
Cikikkayiyar sallamar da a yau ta fito daga bakin Kb kenan,wanda ya k'ara nuna tsantsar rashin gaskiyarsa. Tunda dai a sanin da Haris ya yiwa aminin nashi,baya taba cika sallama haka tun suna k'ananu sai idan yana cikin firgici.
Dariya taso kubcewa Amadu maigadi,yayi saurin tosheta. Harara kb ya watsa mishi da sauri ya sauke jakar ya fice.
Haris ya amsa ciki ciki,har kb ya iso ya zauna kallonshi kawai yakeyi cike da tsabar bakin ciki. Tun kafin Kb yakai ga cewa komai ya tareshi
"Ka bani mamaki Kb,abune da koda ace za'a tareni acemin baka bar aikatawa ba zance karya akeyi. Karuwa fa!! A gidan da kake raya sunnar ma'aiki?!!! Da sunan kana da aure? Ka gayamin wane jin dadi ne a bibiyar kazaman matan nan da har yau ka kasa russuna?! Ya kake tsammanin su Daddy zasu dauki wannan zancen?"
Haris ya dakata,kallo d'aya zakayi mishi ka gane yana cikin tsananin bacin rai,wannan farin fatar tashi ta fuska ta chanja launi zuwa ja,hakanan kwayar idanunsa. Ya numfasa
"A ture maganar iyayenmu,me zaka cewa Mahaliccinka akan wannan d'anyen aikin da kakeyi na aikata zina? Baka tsoron mutuwa ta riskeka a wannan yanayin Kabir? Inace Ubangiji Ya halatta mana auren mata hud'u idan har zamuyu adalci? Why not ka nemi wata ka aura tunda mace daya bazata iya kashe maka kishirwarka ba. Amma wannan(yayi nuni da matattakala) ba alheri bace gareka face halakarka.!!"
Kb wanda tsananin kunyar Haris ta mamayeshi,yana ganin tamkar Yasmeen ce a gabanshi. Ya runtse ido kafin ya bude cikin sassanyar murya na rashin gaskiya
"Hakane,nasan ban kyauta ba. In sha Allah daga yau bazaka k'ara kamani da laifi makamancin wannan ba. Na amsa laifina,babu shakka bakayi karya ba duk abunda ka fad'a na aikatashi. Kayi hakuri,don Allah ka rufamin asiri a matsayinka na dan uwana kuma amini...."
"Its ok,baka da matsala dani Kabir,fatana ka gyara tsakaninka da Ubangijinka. Abu na gaba,yarinyar nan tazo ta fice yanzu yanzun please."
Kai da kaga yanayin fuskar Haris kasan yana tsananin kyamarta. Kyakkyawar matashiyar budurwa saidai fa kyawun dan maciji ne.
Shi kuwa Kb,mikewa yayi ya nufi saman gami da jin dadin cewa Baby batayi fushi tabar gidansa ba.
Tana zaune taga mutum tsaye a kanta,ganin kb ya sanyata mikewa tana murmushin jin dadin ganinshi,bai ankara ba har takai ga rungumeshi. Kamshin jikinta da taushin fatarta,ya mantar da kb dukkan wasu nasihu na Haris. Sai yaji sam bazai iya rabuwa da Baby ba,tun haduwarsa da Baby,baya iya hada shimfida da kowace Yar Bariki sai ita. Yasmeen ma,gudun kada takai korafi ga iyayensu ya sanya yake mu'amala da ita. Ta dago ta sumbaci lebbansa har lokacin da murmushi dauke a fatar bakinta. Baisan lokacin da shima ya sakar mata murmushin ba. Ta fidda earpiece daga kunnenta,ta zuba mishi shanyayyun idanuwanta kafin daddad'an sautin muryarta ya ratsa cikin kunnuwansa
"Welcome back my dear."
Ya riko hannuwanta cikin nashi salon kallon,ji yakeyi nan duniya bashi da farin ciki sama da Baby. A shirye yake ya aureta idan har hakan zaisa ya dauwama tare da ita bata haramtacciyar hanyar da za'a gani a rabasu ba.
"Thank you my baby,hankalina a tashe yake."
Ta janye jikinta tana murmushi kafin ta nufi hanyar sauka k'asa
"Daukomin handbag dina, kada ka damu na fahimci matsalar."
Yayi mamakin yanda akayi ta fahimceshi sosai har haka. Cikin jin dadi ya shige dakin,ya dauki harda mukullin motarta.
Haris dake zaune yana jiran fitowarsu,suka dubi juna,ta sakarmishi murmushinta mai burgewa saidai ko kad'an bata burge Haris ba. Ta zagaya ta bayan kujerar da yake,daidai saitin kunnenshi ta furta
"Sai had'uwa ta biyu."
Daga haka tayi gaba cikin takunta na jin ta isa. Mamaki ya sanya Haris binta da kallo. Amma ta tabbata Baby tsohuwar 'YAR BARIKI ce, ya kauda kansa yana takaicin yanda mace kyakkyawa har haka ta b'ata wayonta. Son duniya ya sanya tana siyarda jikinta ga wanda ya isa da wanda baima isan ba. Tunaninsa ya tsaya sa'ilin da abokin nashi ya taho da sauri rike da jaka da mukullin mota. Ya zuba mishi ido yana duban ikon Allah,Kb ya tsuke fuska
"Mantuwa tayi,banason komai nata ya rage a gidana domin daga yau na barta kenan."
Shi dai Haris baice komai ba,fuska a daure. Kb ya fita a fusace wanda zaka rantse zancensa har zuci ne.
Yayi ta hangen inda Baby ta shiga, hon yaji. Ya juya ga daya daga cikin motocinsa,hantar cikinsa ta kad'a. Wannan ma fa wata matsalar ce, ta yaya zata shiga motarsa? Ya dubi hanyar gidansa,Haris bai fito ba,da gudu gudu ya isa bakin motar. Fuskarta a daure kai ka rantse bata tab'a dariya ba.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(09)
Ringing uku ana hud'u,Kb ya d'aga.
"Yadai mutumin? Kana ina ne kazo ka daukeni a airport. Allah Yayi zuwana bisa neman da Abbana(Alhaji Aliyu) ke yimin akan harkokinmu."
Haris ya runtse ido cikin jin haushin Kb,dakyar ya iya dannewa yace
"Banajin zan iya zuwa,ina gidan naka yanzu haka tare da matarka wacce bamu da masaniyar sadda kuka kullawa junanku aure. Kana iya shigowa taxi kazo ka samemu."
Daga haka ya kashe wayar,a bangaren Kb kuwa,hankalinsa idan yakai dubu toh fa ya gama tashi. Kada dai baby ce? Ya salam! Yanzu menene abunyi?"
Ya lalubi lambar Baby ya danna kira.
Ta kammala shiryawa cikin riga da wando gajera marasa nauyi,ta kunna karan sigari ta soma zuk'a hankali kwance kafin ta sanya earpiece a kunnenta tana shirin danno wak'a ne kiran Kb ya shigo wayarta. Murmushi ta saki kafin ta d'aga alokacin data nufi falo.
Kafin takai ga cewa wani abu,Kb ya soma magana
"Babyna kina ina?"
Daidai lokacin ta fito falon,lokaci d'aya suka dubi juna dashi,ta dauke kanta ta nufi kicin.
"Ina gidanka,wani abu?"
Ya zaro ido,hantar cikinsa ta kad'a
"Baki ga wani bak'o ba da yazo?"
Daidai lokacin ta fito dauke da glasscup tayi hanyar firij,
"Gashinan zaune,da alama baisan wacece ni gareka ba ko?"
Kb ya dafa goshi,ya rasa ta inda zai b'ullo. Ashe a gaban Haris take magana dashi?
"Look,he's my bestfriend. Please kada ki sanar mishi komai dangane da relationship dinmu dake kin fahimta? Gani a airport,na iso Kano. Yanzu zan zo gidan."
Ta tab'e baki,daidai lokacin ya kashe wayar. Ita kuwa freshmilk ta tsiyaya ta koma ta zauna a kujerar dake kallon Haris. Kurb'a takeyi tana duban fuskarsa yanda duk yabi yayi kicin kicin tamkar ya tashi ya rufeta da duka. Saida tayi kurba uku kafin ta ajiye ta cire earpiece dake kunnenta.
"Nice meeting you."
Ta fad'i a tausashe. Bakin ciki ya sanyashi watsa mata kallon da taga ya k'ara fiddo kyawunsa zallah. Murmushi ta sakar mishi kafin ta d'ora tafin k'afa d'aya akan kujerar da take zaune
"Fuskarka ya nuna baka son ganina."
Ta tabe baki inda ta k'ara zuk'ar sigari ta fesar da hayak'in.
"Abun mamaki,bamu tab'a had'uwa ba sai yau. Ban fiye kaunar naga mutum yana kuntata rayuwarsa ba musamman akan abunda ba matsalarsa...."
Tashin da yayi ya hanata k'arasa zancenta. Dubanta yayi cike da tsana,ya soma tafiya saidai ya tsaya cak ya juyo
"Da gaskiyarki,ban sanki ba,asalima yau na tab'a ganinki a inda bai cancanci ace kina nan ba. A matsayinki kuma na kilaki. So,as you said,bake zaki bani amsar kowacce tambayata ba. Ke kuma kiyi hankali da kazantacciyar rayuwar da kike ciki,na lura baki da damuwa ko kuma d'igon bakin cikin wannan rayuwa taki. Saidai fa..."
Ya dubeta,sai lokacin ya sakar mata murmushi wanda daga gani kasan na yak'e ne
"Akwai ranar k'in dillanci."
Daga haka ya sauka zuwa falon k'asa domin jiran aminin nashi.
Ta maido dubanta ga falon,ta lumshe ido tana murmushi
"He's very handsome,saidai ba wayewa."
Ta furta cikin zazzak'ar muryarta,bata ko damu da kalamansa ba ta maida earpiece dinta ta kunna wak'a abinta tana kurb'ar lemo,a gefe kuma zuk'ar taba.
*******
Taxi yana tsayawa,kb ya biyashi ya fito. Da azama Maigadinsa ya iso a guje yana kokarin karb'ar akwatin hannunsa. Kyakkyawan mari yayi mishi a kunci,kafin ya soma magana a fusace
"Don ubanka wace doka na sanya maka?!!! Bance maka idan bana gari ba,banda baby kada kabar kowa ya shigomin gida ba?!!"
Matashin maigadi wanda yaci suna Amadu,yana rike da fuskarsa ya russuna cike da girmamawa
"Kayi hakuri yallabai,wallahi ina fama da ciwon ciki shine na lek'a kemis bansan da zuwan Madam ba."
"Mts!"
Kb yaja tsaki yayi gaba,da azama Amadu ya ciccib'i akwatinsa jiki yana rawa yabi bayanshi bayan ya watsawa Ado maigadin makwaftansu kallon baka kyautamin ba.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(11)
"Babyna wannan motar kuma?"
Ta dubeshi
"Nufinka na sauka na baka abarka?"
Yayi azamar dakatar da ita
"No,bance ba. Saidai kinga Haris zai iya d'ago..."
Ta soma kiciniyar bud'e mota, yayi saurin dakatar da ita.
"Haba babyna,please ni bance ki sauka ba. Ga handbag dinki,daga baya zanzo gidan please. Kada kiyi fushi dani."
Sai lokacin ta sakar mishi murmushi na gefen kumatu
"Ko kaifa."
Daga haka ya matsa tayi ribas,tuni Amadu ya bud'e mata k'ofa ta fice.
Kb ya dawo da hankalinsa akan motar Baby,dabara ta fad'o mishi,ya sami k'usa ya sace taya d'aya kafin ya mike. Ido hudu sukayi da Haris wanda fitowarsa kenan,ya dubi motar kafin ya nufi tasa a fusace ya hau kokarin budewa. Kb ya isa da sauri ya riko hannunsa
"Don Allah kada kayimin gurguwar fahimta mana,tayar motarta d'aya ne ya sace shine dalilin daukar tawa da tayi. Amma idan an gyara zan aika mata sai a karb'omin tawa. Kada.."
"Ya isa Kabir,gyara kuma ya rage tsakaninka da Mahaliccinka. Shi yafi cancanta ka tsorata ba kowa ba. Kayi tunani da ka haihu,baka gudun ace yau diyarka ce cikin wannan..."
"Haris please! Banason wannan irin zantukan! Ya wuce,na fadamaka kaddara ce yasa nake kula wannan d'inma amma nayi maka alk'awarin daga yau ta k'are. Don Allah ka rufamin asiri."
Ya tabe baki gami da daga kafad'a
"Ka tsaya mana muyi sallah,nasan ko magrib bakayi ba. Gashi kafin ka kai gida nasan anyi isha'i."
Sanin da yayi haka dinne,ya sanyashi dakatawa. Sukayi sallah,sannan ya wuce.
******
Tun komawarsa gidansa,tunani da matsanancin tausayin kanwarsa Yasmeen sun hanashi sakat. Har lokacin surar yarinyar ya kasa b'aceqa daga idanuwansa,ba don komai ba saboda tsanarta da yakeji tare da mamakin karfin hali irin na karuwan mata masu maida gidan wani nasu. Kodayake dai babban laifin yana ga Kb wanda har ya iya bata wannan fuskar. Zina fa!! Wai ma menene abun dadi da tunkaho a cikinta?!! Me Kb yakeji idan ya tafka irin wannan sab'on? A gefe d'aya ga Yasmeen,a yanda yasan kanwarsa,yarinya ce mai hakuri da halayen mijinta. Tabbas bata boyemishi dukkan sirrukanta tun tana budurwa ma. Dukkan abunda hankali zai dauka na neman shawara,daidai da wanda ya dace ya sani takan sanarmishi ta waya. Ko kuma idan yaje su kwashi fin awa suna hira. Duk da ba gida d'aya suka taso da Yasmeen ba,sun shaku sosai dashi.
Idanunsa suka kad'a sukayi jazur,hakikanin gaskiya,ko kusa kanwarsa batayi sa'ar miji ba. Manemin mata wanda har yake zargin yana shaye shaye. Duk da har zuwa yanzu bai taba kamashi dumu dumu cikin mayen ba saidai ganin yanda neman matan nasa yayi yawa yasa ya soma gaskata komai akace kb yayi zai aminta da haka.
K'arar wayarsa ce ta katse mishi tunani,dakyar ya lalubota ya duba mai kiran. Yasmeen dince. Murmushi ya saki wanda yafi kuka ciwo,kafin ya daga. Tun kan yace wani abu,ta soma magana cikin farin ciki
"Yayana kasan wani abun mamaki kuwa? Au,Assalamu alaikum,yayana barka da dare."
Nan da nan ransa ya danyi sanyi jin cewar kanwarsa tana cikin farin ciki. Cikin tattausar muryarsa ya amsa sallamar ya d'ora da fad'in
"Fadamin da sauri little,bazan iya jira na wani lokaci ba."
Tayi dariya mai nuni da tana cikin farin ciki
"Wallahi yayana wannan zuwan naga chanji sosai a wajen Prince..."
"Me yayi maki?!! Gayamin ko menene?!!!"
Ta danyi shiru kad'an jin ya fusato,a sanyaye tace
"Cool down yayana,bafa wani abu yayimin na bacin rai ba. Kawai dai umm...mun dawo tamkar new couples."
Ta karashe tana dariya kasa kasa,ya lumshe ido yana mai sauke ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah little, burina na ganki cikin kwanciyar hankali. Ina diyata?"
"Allah Sarki yayana,nima farin cikinka shine nawa. Ai bansan ya zanyi ba idan aurenka yazo don murna."
Murmushi yayi wanda bai shirya mishi ba,ita kam Yasmeen bata gajiya da tunasar dashi batun aure sai kace wani karamin yaro. Ya shafi sumar fuskarsa
"Zanyi,lokaci ne baiyi ba little. Ki tayani addu'a. Baki amsamin tambayata ba."
"Oh,nasreen tayi bacci. Ai yanzu muka gama waya da babanta yace min ma Monday zai juyo da safe."
"Kabir kenan."
Ya fad'a a zuci,don ya fahimci ba karamin razana yayi ba yau.
A fili kuwa ya amsa da ok.
"Bari na kyaleka kaji da gajiyar ofis. Bye."
Sukayi sallama ya ajiye wayar. Tausayin kanwarsa ya k'aru a zuciyarsa,tabbas har yanzu batasan waye Kb ba,kuma baya fatan tasan wannan boyayyen al'amarin,daidai da iyayensu baiso zancen yaje wurinsu. Shi kam,sai inda karfinsa ya k'are akan ganin rayuwar amininsa kuma dan uwansa ya daidaita.....!
*****
Misalin (1:00am) na dare......
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(12)
Kwance suke a dakinta kan makeken gadonta,tayi
matashi da cinyarsa.
"Babyna."
Ba tare data amsa ba ta dago idanuwanta
lumsassu ta dubeshi,ya sanya hannu yana wasa
da girarta kafin yace
"Inason muyi wata magana ne."
Batace komai ba,sai kallo da take binsa
dashi,wannan ya bawa Kb damar cigaba da
zancensa.
"Kinga dai a yanzu babu damar haduwa a gidan
ko? Sannan yanzu idanun Haris a kaina yake na
tabbatar bai gamsu cewar na rabu dake da gaske
ba."
Ya danyi shiru kamar mai nazari,kafin ya riko
hannunta yana cigaba da duban kwayar idanunta
masu k'ara dulmiyar dashi kogin kaunarta.
"Abu ne da bazan taba iya aikatawa ba,saidai
zuwa yanzu ina tsoron kada Haris yakai k'arata
wajen iyayenmu....."
"Menene dangantakarku da guy dinnan ne? Na
lura ka bashi matsayi da yawa a rayuwarka KB."
Baby ta katseshi ta hanyar jefo mishi wannan
tambayar. Murmushi yayi ya shafi gashin dokin
dake kanta wanda sai yace shi dai tunda yasan
baby bai taba ganin iyakar jelar gashinta
ba,baisani ba tana da yawan gashin ko babu.
"Haris Aliyu kenan,iyayenmu aminan juna
ne,wannan yasa mukayi sabo dashi sosai fiye da
tunanin mai tunani. Ya kasance dan uwana
wanda bama boyewa juna sirri. Nan da kike
ganinsa ustaz ne,ya fiye takura kansa baison ya
more rayuwarsa."
Kb ya dan tabe baki kafin ya cigaba
"Abunda zai baki mamaki ma,har yau bai taba
sanin diya mace ba sannan har zuwa yanzu yak'i
aure a cewarsa gareni,baiga wacce tayi mishi
bane."
Baby ta lumshe ido kafin ta muskuta ta juyawa
Kb baya
"Karancin wayewa ke damunsa,saidai kasan wani
abu? Da ace nice kai babu wanda ya isa hanani
yin abunda nake ra'ayinsa. Kaban mamaki KB,
akan wannan guy din saika rabu dani."
"No baby,ni wanene da zan bar mace irinki?
Wannan karya ne. Shiyasa na samo mana
mafita,kawai ki nutsu ki saurareni please."
Har lokacin idanuwanta a rufe suke,haka kawai
take tsintar kanta da tunano kyakkyawar halittar
fuskar HARIS,
"Ina sauraronka."
"Zaki aureni Tasleem?"
Cikin matukar razana ta bude idanuwanta,kafin ta
mike zaune tana duban kwayar idanuwan
Kabir,kwarai babu alamun wasa a abunda yace.
Gabanta ya shiga faduwa haka kawai,yayi azamar
matsowa ya riko hab'anta
"Wallahi Tasleem zan iya aurenki,babu kyankyami
ko wani abu. Sonki nakeyi,bazaki gane yanda na
shaku da soyayyarki..."
Ta cire hannunshi ta juya mishi baya gami da
sauke kafarta akan gadon,har lokacin bugun
zuciyarta bai daidaita ba
"Na gayamaka tun a farkon mu'amalarmu kafin
muyi nisa haka. Kamar yanda ka taba zuwarmin
da batu irin wannan a yanzun ma amsar d'aya
ce,bazan iya aurenka ba."
Kb hankalinshi ya tashi,kaunarta na kara karfi a
zuciyarsa. Zuwa yanzu ya amincewa kansa lallai
ba sha'awa kawai yake yiwa Baby tasleem
ba,harda soyayya. Hannunta cikin nasa,yayinda
kalar kwayar idanunsa suka sauya launi saboda
tsabar tashin hankali na jin maganar dake dake
fitowa a bakin baby.
"Me kikeso a rayuwa wanda har yanzu baki samu
ba? Wallahi ki fad'amin ko menene shi zan
mallaka maki Tasleem dan har zaki yarda na
killaceki a gidana ya zamana ni kadai nake da
hakki akanki. Ya zamana kinbar mu'amala da
kowa. Wallahi tasleem zan iya mallaka maki
dukkanin dukiyata matukar hakan zaisa ki amince
dani matsayin mijinki. Please ki....."
Ta mike a fusace
"Ya isheni Kb!!!!"
Ta dakatar dashi kafin ta watsa mishi duban da
tunda suke tare bata taba yi mishi ba. Duba ne na
raini da wulakanci,
"Bazaka taba samun biyan bukatar nan ba. Na
tsani aure! Bazan taba yinshi ba!! Babu komai a
rayuwar aure sai tozarci da wulakanci! Wannan
ikrarin da kakeyi na kana sona,zai tafi da zarar na
kasance matarka."
Kb ya nufeta da niyyar rikowa tayi azamar
dakatar dashi ta hanyar daga mishi hannu. Daga
haka ta fice da gudu tabar dakin. Bata shige
ko'ina ba sai d'akin Dalal ta sanya mukulli jikin
kofar ta rufe. Kuka takeyi sosai wanda ya tada
hankalin kb dake tsaye daga waje yana jiyo
sautin kukan nata.
"Please baby i'm sorry,indai maganar aure ne
bazan k'ara yi maki ba."
Ita kuwa baby,ita kadai tasan me me kalmar aure
yake tunano mata.
Daren babu wanda yayi kwanan farin ciki a
cikinsu.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(13)
Kukan da Baby tasha a wannan daren ne ya sanya ta tashi da matsanancin ciwon kai. Bata fito daga d'akin nan ba saida tayo sallar asubahi ta kara kwanciya bacci,a takaice dai saida rana ta fito. Ta bud'e kofa ta fito,falon babu kowa kamar yanda tayi zato,Kb ya tafi. Ko a kanta bata damu ba,ita kam idan har zancen aure ne bazai tab'a samun goyon bayanta ba. Tabbas saidai alak'arsu ta yanke anan.
Kai tsaye dakinta ta nufa,tsayawa tayi cak,ganin Kb kwance yana bacci bayan ya rungume hotonta dake ajiye gefen gadon. A hankali ta karasa ta durkusa saitin fuskarsa tana duba,murmushi dauke akan fuskarta. Lallai ba karamin so Kb yake yi mata ba,duk da cewar nata zuciyar ba wani sonshi takeyi ba sosai. Tafi daukarshi a matsayin mai biya bukatarta. A hankali ta mike ba tare da tayi yunkurin tashinsa ba. Wanka kawai ta fad'a. Bayan ta fito ta iske har lokacin kb bai farka ba,mamaki ya kamata. Kodai baiyi bacci bane daren jiya. A sannu isa gefen gadon ta zauna kafin ta jijjiga gashinta,ruwa ya fallatsar mishi a fuska. Sannu sannu ya bude ido,kafin yakai ga cewa wani abu ta mike da sauri ta koma gaban madubi
"Ya kamata ka tafi gida kafin ustaz din naka ya nemeka."
Ta karashe tana murmushi,kb ya taso ya janyota ta mike tsaye suna fuskantar juna. A karshe ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna. Yanda ya karanceta ko kusa bata da fushi sosai,tana da saurin hucewa,(hum).
"Na bata ranki Babyna,amma daga yau nabar zancen nan tunda har bakiso,kinji?"
Tayi murmushi kafin ta sauya salon zancen nasu. KB bai bar gidan ba sai wajen goman safe,ya k'ara tabbatarwa kansa bazai iya rabuwa da Baby ba. Ta musamman ce. Cike da nishadi ya koma gidansa.
*****
Dattijai ne guda biyu masu kimanin shekaru Sittin da d'oriya,suna zaune a kayataccen falon gidan. Kowannensu ya sha babbar riga suna hira cikin nishad'i. Lokaci guda kuma fuskar Alhaji Idris ta sauya zuwa yanayin damuwa. Wannan yasa Alhaji Aliyu tsagaita dariya ya dubeshi
"Lafiya kuwa?"
Alhaji Idris ya sauke ajiyar zuciya
"Wallahi lamarin Harisu ya soma tsoratani Alhaji. Ace yaro yak'i zancen aure,har rana mai kama da yau ya kasa kawo mana zancen da zai sanyamu farin ciki? Babu ranar da bana rokon Allah,daidai da liman saida na sanarwa domin a taimaka mana da addu'a. Kaga fa har rukiyya anyi mishi a zatonmu aljanu ne saidai ko gezau babu. Anya tafiya zata yiwu haka?"
Alhaji Aliyu yayi murmushi
"Ka gafarceni Alhaji idris,zuwa yanzu na daina ganin laifin yaron nan nafi ganin laifinku na iyayensa."
Daddy ya dubi Abba da alamun rashin fahimtar maganarsa. Abba ya jinjina mishi kai
"Kwarai ma kuwa Alhaji Idris,wannan laifin bana d'anku bane,naku ne. Kada ka manta fa,yaron nan ba shine ya haifeku ba! Akan wane dalili ne zaku zuba mishi ido sai yanda yakeso za'ayi? Ga yan uwansa nan mata a Kazaure,wadanda sukayi karatun na addini dana zamanin don me bazaku samar mishi wata a can ba? Haba jama'a,yaron nan fa ba fin karfinmu yayi ba. Yau ga dan uwansa nan har ya soma tara zuri'a shi ya zauna jiran autar mata? A'a fa,gaskiya laifi yana wajenka Alhaji."
Daddy yayi murmushi
"Gadanga kenan,zamanin nan da kake gani ba'a yiwa yara auren dole,ba irin zamanin mu bane wanda ko fuskar matanmu bamu gani ba sai bayan an mik'o mana su gidajenmu. Wannan zamanin za'a kuntata rayuwar yaro ne kawai."
"Nima bance kuyi mishi dolen ba idi(ya fada cikin zolaya kasancewar sunan da yake kiranshi kenan a baya da kuma wasu lokutan na yanzu),ku turashi kuce yaje ya zab'a idan yaso sai ya sanar maku wacce ta kwanya mishi ko kuwa?"
Daddy yayi dariya
"Gaskiyane,sai ayi hakan toh. Fatanmu Allah Yasa mu dace."
Abba ya amsa da amin. Daga haka hira ta mik'a.......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar
(14)
Misalin karfe sha biyu da rabi na dare,baby tafe akan hanyarta na zuwa birthdayparty na Hibba da saurayinta ya had'a mata. Taci kwalliya har ta gaji da had'uwa. Kid'a ke tashi kawai a motar,saidai cak motar ta soma kokarin tsayawa. Karshe ta tsaya cak akan titin daya kasance shiru tamkar babu mutane sai tsilli tsillin motoci suke wucewa. Ta buga sitiyari da k'arfi ganin mai ne ya k'are mata. Shaf ta mance cewar Dalal ta ari motar taje kasuwa da ita dazu,gashi babu alamun masu siyarda mai a kusa. Wayarta ta dauko,ta kira lambar Hibba,yana ta ringing bata dauka ba. Hakanan Manal da Dalal. Ta tabbatar dukkansu hankulansu yana wajen party. Taja karamin tsaki kafin ta soma duban hanya taga ko zata samu mai taimakonta.
Tafe yake a hanyarsa ta komawa gida daga meeting da yayi (attending) na aikinsu. A gajiye yake saboda ya mance rabon da yakai war haka baiyi bacci ba. Hannu ya gani an sanya mishi ana tsayar dashi. Ya duba dakyau,mace ce,kuma da alama motarta ce ta sami matsala. Ba tare daya lura da ko wacece ba,ya samu waje ya faka domin shi ya dauka ma kabila ce duba da yanayin suturar dake jikinta na gown marar hannu ga kuma gashi a waje.
"Sannu,please ko..."
Sauran maganar ya makale a fatar bakinta ganin Haris. Shi kanshi baisan ita bace saida ya fito daga cikin motarsa suka nufo juna.
Zallar kyawun fuskarsa ta k'ara fitowa a lokacin daya tamketa,ya juya da niyyar komawa motarsa ya tafi. Tayi azamar tarar gabanshi,cikin marairaicewa tace
"Domin Allah ka tausayamin mana bestfriend,wallahi ka tafi ka barni anan za'a saceni ne. Man motata ya k'are ne."
Sai lokacin ya lura ashe harda hudin hanci gareta,ta maka barima fara akan hancin. Ganin yanda ta marairaice ne ya sanyashi kauda kansa,baice komai ba ya gifta ya shige motarsa. Har ta fidda ran cewa zai taimaketa taji yana mata hon. Cikin sauri ta dauki wayoyinta da fos dinta. Ta rufe gilasan motar ta kulleta ruf sannan ta nufi motar tasa. Sai lokacin hankalinta yakai ga lambar motar,nan da nan ta tunano inda ta santa. Ashe shine ya taba binta a guje sadda ta tuk'o motar Kb. Murmushi ta danyi kafin ta zagaya ta bud'e gaban motar ta shiga. Nan da nan kamshinsu ya mamaye motar, har suka rasa fahimtar na wanda yafi tashi.
"Nagode bestfriend."
"Haris sunana."
Ya fada cikin fusata. Ta dubeshi ganin yanda yayi kicin kicin,ta kad'a idanuwanta
"Ok,Haris."
"Ina zan kaiki?"
"Tahir."
Baisan sadda ya dubeta ba,itama har lokacin idanuwanta na kansa. Saidai baice komai ba ya fisgi motar a fusace,gudu yakeyi kamar zai tashi sama,baby kuwa ko a jikinta. To yau ya soma sanin gudu a mota ne? Kallonsa kawai takeyi cike da mamakin irin kyawu na Haris. Bayan haka ma,tafi mamakin yanda duk haduwarta ko kallo bata isheshi ba. Toh ita kuwa iyakar zamanta a rayuwa bata taba ganin namijin daya ganta bai kara kallo ba saboda zubin da halittar da Allah Yayi gareta.
Taka burki da yayi,ya maidota hayyacinta. Wannan ya sanyata kauda kanta daga barin kallonsa. Ta duba,kwarai sun iso kofar hotel din.
"Rayuwar da kika zab'awa kanki ina mai tabbatar maki akwai ranar k'in dillanci. Sam,wannan bai dace da musulma ba. Kin maida kanki kasuwar da kowa yake da damar shiga. Kin zubda k'imarki ta d'iya mace akan son duniya wanda bazai kwatoki daga azabar Allah da kwanciyar kabari ba. Kiyi tunani,matan aure nawa kika dauki hakkinsu wajen nasarar dauke hankulan mazajensu a kansu? Allah bazai kyaleki ba,da rai da lafiyarki muddin baki tuba ba sai kinga sakayya. Idan zina abun yi ce kije kiyi tayi,ke da karya baku da bambanci."
Yayi shiru yana mai duban titi,murya a kausashe ya kara magana
"Get out."
Kamar wacce aka daskarar,gaba daya ta gaza motsi. Bata ce mishi uffan ba. Jin tayi shiru ya sanyashi juyowa da niyyar fad'a,abun mamaki hawaye ya gani suna zuba daga kwayar idanun Baby. Tayi azamar sharesu,murmushi ta k'ak'alo ta jefeshi dashi
"Nagode da taimakon da kayi gareni,Allah Ya kaika gida lafiya."
Daga haka tayi saurin ficewa tayi ciki,saidai kana dubanta zaka fahimci a sanyaye take ko daga yanayin tafiyarta. Ko kadan bata bashi tausayi ba,saidai har ya tafi yana mamakin yanda akayi kalamansa suka sanyata hawaye. Karshe dai ya watsar a cewarsa,munafunci ne. Wanda yayi nisa bazai tab'a jin kira ba....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(15)
"Kiyi tunani,matan aure nawa kika dauki hakkinsu wajen nasarar dauke hankulan mazajensu a kansu? Allah bazai kyaleki ba,da rai da lafiyarki muddin baki tuba ba sai kinga sakayya."
Har zuwa yanzu da take kwance a gadon d'akin na hotel d'in,ita kad'ai. Wadannan kalaman ke yawo a kwakwalwarta. Damuwar da ta yawaita a zuciyarta ya hanata zuwa bangaren da ake fatin hibba,hakan yasa ta kama d'aki da zummar ta kwana da safe tayi gida. Batayi iya runtsawa ba kalaman Haris sun shigeta matuka. Ta tuno yanayin fuskarsa wanda ke nuni da tsantsar takaicinsa na halin da rayuwarta ke ciki. Bata taba cin karo da wanda ya nuna kyama a harkar rayuwarta ba kamar shi.
"Nan da kike ganinsa ustaz ne,ya fiye takura kansa baison ya more rayuwarsa."
Kalaman Kb akan Haris suka fad'o mata. Tabbas ta yarda da hakan,Haris kamilin mutum ne wanda bai sha'awar rayuwar da suke ganin itace ta arziki a garesu.
*****
Da zarar ya runtse ido,ita yake gani. Bai manta sa'adda ta dubeshi fuska dauke da ruwan hawaye wanda yasan na munafunci ne. Amma meyasa ta kasa b'acewa tunaninsa,bai manta sadda ta fice a motar ba jiki a sanyaye. Toh hakan yana nufin taji nasiharsa ne ko kuwa? Amma ai inda ace ta dauki zancensa,babu abunda zaisa ta shiga hotel d'in. Ya dafa goshinsa yana mai runtse ido,bayason ya dunga tunanin wacce bazata amfaneshi da komai ba. Hakan yasa ya mike tsam yayo alwala ya soma nafila duk domin kaucewa tunanin wacce ko sunanta bai sani ba.
******
"Gobe zan koma Abuja,inaso muyi wata magana ne."
Ya tsayar da rubuce rubucensa sannan ya dago fararen idanunsa ya saukesu akan Kb,fuska ba walwala.
"Na'am,ina sauraronka."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(16)
Kb ya numfasa yana mai sassauta muryarsa,ba tare daya yarda ya dubi kwayar idanun Haris ba ya soma magana
"Look Haris, nasan na aikata ba daidai ba. Nasan zuwa yanzu ka dauki zafi dani baka kaunar sanyani a idanuwanka ma,amma don Allah kayimin uzuri wallahi kaji na rantse maka babu macen da nake mu'amala da ita a waje idan ba Baby Tasleem ba."
"Baby Tasleem."
Haris ya nanata sunan a ransa,sai yau ma yasan sunanta. Kb ya cigaba da magana
"Nasan ban kyautawa Yasmeen ba kamar yanda ban kyautawa kaina ba. Gaskiyar magana rabuwa da Tasleem abune mai matukar wuya agareni,shiyasa na yanke shawarar zan aureta a matsayin matata ta sunna."
Wani mugun kallo da Haris ya watsa mishi ya sanyashi kauda kansa cikin jin nauyi,ya numfasa kafin ya cigaba
"Yes Haris, kabar yimin irin wannan duban,raya sunnah nakeson yi ba wai zina ba. Duk da dai zuwa yanzu Baby tak'i bani had'in kai,ta nunamin babu abunda ta tsana kamar aure,wannan shine hakikanin damuwata. A matsayinka na amini kuma d'an uwana don Allah ka taimakamin da shawara."
Ba tare da ya jira cewar Haris ba ya mike tsam ya nufi hanyar fita cikin jin nauyin amininsa. Saida yakai k'ofa sannan ya dakata ba tare da ya juyo ba
"Ba hakan dana fada yana nufin na rabu da soyayyar matata ba,a'a. Inason Yasmeen matuka saidai inason raya sunna. Idan har ka amince da bukatana,ka taimakeni kayi jihadi wajen shawomin kan Tasleem domin cetomu daga wannan rayuwa please Haris. Goodbye."
Ya fice cikin sauri ba tare da ya juyo ba ballantana ya lura da irin firgicin dake akan fuskar amininsa.
Rike kai yayi yana mai runtse ido,gabansa na duka da sauri da sauri. Aure?!! Tsakanin Kb da baby tasleem?!!
Ya nanata a zuciyarsa,kafin ya kwantar da kansa akan kujerar ya runtse ido. Toh menene matsalarsa? Me zaisa zancen nan ya dameshi? Amma kuma dole zai dameshi ai,ko babu komai,kanwarsa ce fa Kb ke shirin yiwa kishiya da karuwa! Dole yaji tsanar auren,dole ne ya taya 'yar uwarsa kishi. Kishi mai tsanani.
Ya bud'e ido,kafin ya hasko halittar Baby da wayewarta sannan ya dawo ga kanwarsa wacce baby bazata nunawa kyau ba saidai ta fita a halittar jiki da kuma barikanci. Ita d'in ta kasance saliha,domin ko a gida bata fiye magana mai tsawo ba,sam, bata da hayaniya tamkar Haris d'in take. Wannan yasa duk cikin kannensa yafi tausayinta yafi sonta tasu tafi zuwa d'aya. Anya kanwarsa zata iya kishi da gogaggiyar mace irin Tasleem?
"Idan har ka amince da bukatana,ka taimakeni kayi jihadi wajen shawomin kan Tasleem domin cetomu daga wannan rayuwa please Haris."
Ya tuno zancen Kb,wannan ya nuna kenan yayi kokarin shawo kan Tasleem domin ta amince da bukatarsa na suyi aure amma sam,tak'i aminta.
Haris ya girgiza kai cikin takaici da bacin rai
"Tabbas Kabir bashi da kunya."
Ya fad'a a fili. K'arar wayarsa ta katseshi,ya duba yaga sunan Daddy. Da sauri ya d'auka. Bayan sallama da gaisuwa ne Daddy ya sanar dashi ya shigo yazo ofishinsa yana nemansa. Ya amsa kafin ya tashi a hanzarce ya nufi ofishin director kuma uba a gareshi,Alhaji Idris.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(17)
Ya shiga da sallama. Daddy zaune akan kujerarsa sanye yake da riga 'yar ciki da wando ya rataye babbar rigar jikin (hanger). Idanunsa boye cikin farin gilashi. Ya bar danna laptop dinsa ya dago yana mai amsa sallamar d'ansa. Cike da girmamawa ya russuna ya gaida Daddy. Daddy ya amsa fuska a sake kafin yace
"Gaisuwarka bata k'arewa Harisu,ayi ta gida ayi ta ofis ko?"
Haris yayi murmushi mai bayyana hak'ora,baice komai ba ya zauna saman kujera bayan yayi kokarin d'an rage tsawo duk da hakan. Daddy yayi gyaran murya ya soma magana
"Haris,kwanaki sun shude sun zama watanni,ga watannin sun koma shekaru. Dan uwanka gashinan zaune da iyalinsa,a dukkan tsawon watannin nan mun barka ne akan ka nemi zab'inka gudun shiga rayuwarka. Saidai har kawo yanzu,shiru Harisu."
Daddy ya k'arashe cikin rarrauniyar murya mai russunar da zuciyar wanda ake yiwa. Haris baice komai ba yayi shiru yana sauraron Daddy
"Ga iyayenka nan girma yana k'ara hawan kanmu,wannan ya sanya naga tunda abun ya zama haka na baka zab'in zuwa can Kazaure,ka duba cikin 'yan uwanka dake can ko Allah zaisa ka sami wata cikinsu da zakaji nutsuwar zuciya akanta. Nidai fatana Allah Ya baka mace ta gari."
Haris yayi murmushi kad'an jin wannan batu da Daddy,a gefe kuma ya gama gaskata cewa ba k'aramin so Daddy da Hajiya sukeyi mishi ba,tamkar daga cikinsu ya fito. Ya tabbata gudun abunda zai b'ata ransa ne yasa Daddy b'ullowa ta wannan hanyar.
"Tashi ka koma ga aikinka Harisu,zan jiraka daga nan zuwa gobe duk abunda ka yanke toh,idan ma akwai wacce ka gani kake so toh Alhamdulillah. Wannan ma shi muka fi muradi. Allah Yayi jagora. Tashi ka tafi, ka turomin sakatare."
Cike da jin nauyi Haris ya mike yana mai amsawa da toh,ya fice jiki a sanyaye. Ya isar ga sak'on Daddy ga sakatare kafin ya koma ofis.
Kasa nutsuwa yayi,zancen Daddy yake ta juyawa. Toh wai ko zai koma ya sanar dashi cewar ya bashi zab'ine? Su zab'a mishi kawai mace tagari? Idan ba hakan ba ya zaiyi toh? Shi kam bai taba budurwa ba,a takaice ma basa gabansa. Allah Ya yishi mutum ba mai son magana sosai ba,baisan ta inda zai soma zuwa ga mace da zummar soyayya ba. Toh yace mata me? Ai shi kam matan ma bakin jini yake a gurinsu,bai mantawa dai da wata abokiyar karatunsa a Malaysia,Rahima. Babu irin bibiyar da batayi ba akan ya amince da soyayyarta amma sam bata samu fuska ba.
Bai mance ranar da Kb ya tursasashi akan sai ya saurareta ba. Suka shirya suka fita wajen shak'atawa inda tuni Kb ya yiwa Rahima maganar ta isa wajen zasu zo. Koda sukaje,nan suka hangeta zaune a kujera bakin swimmingpool na wajen. Kb ya daki kafadarsa yana dariyar mugunta
"Oya jeka,sannan don Allah kada ka bani kunya. Nasan wannan ne farkon tsayuwarka gaban mace a matsayin saurayinta,be a man!"
Harararsa yayi kafin yayi gaba cikin takunsa na nutsuwa,tana ganinshi ta mike tsaye domin girmamawa gareshi tana dariyar farin ciki.
"Sannu da zuwa Haris na."
Yayi dan murmushi kafin ya amsa ya zauna,hakan ya sanyata zama itama. Shiru ya ratso,ya zamana hirar ita keyi yayinda shi ya zama macen. Daga um,sai um um,ga murmushi da yakeyi baya ko dariya. Tun yana burge Rahima,har ya daina cikin yanayin damuwa tace
"Haris na yadai? Ko ka gaji da ganina ne? Na dameka?"
Ya duba agogo kafin ya kalleta yana murmushi
"No,ba haka bane saidai akwai wani uzuri dake gabana yanzu. Kiyi hakuri dai sai mun hadu a makaranta."
Daga haka ya mike da niyyar tafiya,tayi azamar dakatar dashi ta hanyar cewa
"Ya makomar soyayyarmu? Ka amince dani ne ko kuwa..."
"Yanzu kam karatu ne a gabana ba soyayya ba. Kiyi hakuri "
Yayi gaba,yayin da ya barta cike da bakin ciki da dana sanin zuwanta. Yana haduwa da kb wanda yake dubansu. Ya shiga dariyar mugunta har yana kwarewa. Daman yasan amininsa ba iya zancen yayi ba,saidai ta duri haushi. Abun ma bai bashi dariya ba saida Haris ya labarta mishi yanda sukayi shima yana dariyar. Kb ya bugi sitiyari
"Amma kai kam anyi d'an iska,wato baka soyayya sai karatu. Kalaman yayi yanayi dana mace."
Tun daga wannan ranar Rahima bata k'ara neman shiga harkarsa ba. Hakan ma sai yayi mishi dadi domin sam ba sonta yakeyi ba.
****
Haris yana kaiwa nan a tunaninsa yayi murmushi kafin ya watsar da komai ya cigaba da aikinsa.
****
Dalal,Manal da kuma Hibba,sai Baby. Zaune a falon.
Baby sanye da wando three quarter sai 'yar shimi,kwance take akan two sitter ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana (game) da iPad dinta,tana yi tana taunar cingam. Hankalinta kwance,jifa jifa take sanya baki a hirarsu na duniya. Manal ta dubesu tana murmushi
"Albishirinku."
Suka amsa da goro banda Baby dake sha'aninta saidai kuma hankalinta yana ga sauraron abunda zai fito daga bakin Manal.
"Zanje zaman wata uku gidan Alhaji Ubale Kwangila."
Cikin rashin fahimta Dalal da Hibba suka yamutse fuska
"Bamu fahimceki ba."
Kafin ta basu amsa,Baby tayi dariya ba tare data dubesu ba
"Kudai kam baku saurin fahimtar mutum,kasuwanci na wata uku zataje yi gidan Alhaji Ubale. Don wannan baikai kimar da za'a kirashi da aure ba."
Dalal da Hibba suka buga shewa,Manal tana dariya tace
"Dad'ina dake saurin fahimta Baby,toh kun fahimta inace?"
Hibba tace
"Kwarai kuwa,amma fa yana da mata ko?"
Ta rausaya idanu
"Taci kaza kazanta(ashar),ke aure ne fa tun ana fama da shan miyar kuka a kauye. Babu abunda zata hanani,wai kin manta nafi kunama radadi?"
Ta buga hannuwanta
"Wata uku kacal,nayi na gama dashi na fito. Batun da nakeyi maku wahalallen ya kammala yimin gyaran gidansa na Abuja. Can zan lula mubar shegiyar a Kaduna. Magana ma ta isa kunnen Momi,aure nan da wata d'aya sai a soma shiri."
Sukayi dariya gaba daya har Baby,domin yanayin da Manal tayi furucin duka ya basu dariya.
"Kidai shiga da shirinki,kada a samu matsala ya gark'ameki. Me akeyi da aure?" Cewar Hibba.
Dalal tayi dariya
"Shegiya,kada ki manta shine ya haifeki,ko kin mance gyatumarki Sarai mai kosai na tuna maki?"
Dam! Kirjin Baby ya buga,jin furucin daya fito daga bakin Dalal......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(18)
Shewarsu ta katse mata tunani,hibba tace
"Allah Sarki uwata,hauka nakeyi zan mance da ita? Karki ganni anan, duk wata saina tura mata kud'i ta account kawata Balaraba. Ba don wannan mugun uban nawa ba ai da wataran saidai ta ganni naje ziyara. Kunsan dai duk iskancina bana manta MAHAIFIYA."
Baby tayi shiru,jikinta a sanyaye. Ita kam yaushe rabonta da tata uwar? Shekaru biyu kenan,gwara ma mahaifinta,tana da masaniya akansa,ta tsaneshi shima ya tsaneta,wannan dalilin ne yasa babu wanda ya taba yunkurin neman wani a cikinsu. Amma mahaifiyarta fa?
Dalal tace "Ai gwara a dungayi ana tuna asali,nikam saidai nace Allah Ya jik'an nawa iyayen. Ita kuwa Gwaggona da ita muke ci da sha. Ina yawan zuwa gidanta a Kano,kuma kun sani."
Ga mamaki sai sukaga Manal na hawaye tace
"Gwara ku, kuna da iyayen. Nikam idan baku manta ba tsintata akayi a bola,sai ya zamana wanda ya daukeni ya rikeni har girmana,shine mutumin farko daya soma aikata masha'a dani."
Tayi shiru tana sharar kwallah,kowannensu jiki yayi sanyi na tuno abubuwan daya shud'e a rayuwarsu. Baby daga kwance itama hankalinta taji ya tashi,babu wacce ta tsaya a ranta kamar mahaifiyarta. Taji gaba daya tanason taje duba lafiyarta. Manal ta share hawaye ta mike
"Yan iska zaku tunomin bakin labarin rayuwata,ku tashi muje shan ice cream. Yau jakata a cike take."
Sukayi murmushi don babu wacce keda kuzarin dariya,Manal ta dubi Baby.
"Zakije ne?"
Baby ta girgiza kai
"Banajin fita ne."
Sun lura jikinta yayi sanyi, tausayinta ya mamayesu musamman ma Manal wacce anan duniya ita kadai tasan wacece Baby Tasneem. Ita kadai tasan tarihin rayuwarta. Don kafin ta hadu da kowacce cikinsu,Baby tasleem ta soma haduwa da ita harma ta sauketa a gidanta. Haka suka fice suka barta a gidan. A ranar Baby taci kuka sosai,ba don komai ba sai don rashin sanin halin da mahaifiyarta ke ciki. Karshe ta mike ta shiga daki ta kwanta ba don tanajin bacci ba. Sai don kawai tunanin rayuwarta.
*****
KWANA HUDU BAYAN HAKA
Tafiya takeyi da baya da baya tana kallonta,yayinda ita kuwa ke kwance duk fuskarta ya baci da kuraje,hannu take miko mata alamun tsayar da ita tana ihun kuka
"Ya d'iyata,kada ki gujeni! Karki barni cikin wannan halin! Ki dawo gareni!"
Maimakon ta dawo,sai ta juya a guje zata tafi, karar da taji uwar tayi ya sanyata itama kwala ihu kafin tayi wuf ta fada wata rijiya a wajen."
A tsananin firgici Baby ta tashi sakamakon wannan mafarki mai rud'arwa,gumi ya wanke fuskarta duk da Ac dake a kunne. Sai haki takeyi tamkar wacce tayi gudu. Ta sanya hannu ta dafe kirjinta dake dukan uku uku. Can kuma tayi wuf ta sauko daga gadon. Wani d'an karamin akwati ta dauko ta bud'e. Hoto ne a cikin (envelope),nan da nan ta zaro tana duba. Dattijuwa ce tare da yarinya mai shekaru uku,sai dan saurayi mai kimanin shekaru goma sha daya a hoton. Dukkansu suna dariya.
Ta rungume hoton a kirjinta yayinda hawayenta suka karu. Tausayin kanta ya dabaibayeta,taji nan duniya bata sha'awar komai daya wuce na zuwa kauye ganin Mahaifiyarta. Tun hirar da sukayi tare dasu Manal,hankalinta yake a tashe. Ta amince bazata taba samun nutsuwa ba har sai ta dangana ga duba lafiyar mahaifiyarta.
******
Karfe goma na safiyar Asabar,ya shirya tsaf cikin kananun kaya ya feshe jikinsa da turaruka. Bai dauki komai ba sai karamin trolley dinsa inda ya shirya kayan sawarsa. Saida ya soma zuwa gidansu yayi sallama da Daddy,kafin yaje gidan Abba. Nan ma yayi musu sallama,mahaifiyarsa ta bashi sako a kaiwa uwarta,wato kakarsa. Daga haka ya kama hanya.
******
Zaune suke suna karyawa,basu ankara ba suka ganta ta fito tana jan akwati. Ba jan akwatin ne yafi basu mamaki ba,tunda sun saba tafiye tafiyensu. Shigar dake jikinta ne ya burgesu kuma ya basu mamaki. Doguwar rigar atamfa ce, anyi mata dogon hannu three quarter,maimakon ta dora dankwalin saita yafa karamin mayafin (pashmina) a kanta. Saida tazo kusa dasu sannan ta dubesu fuskarta babu wata kwalliya ta daukar ido sai hoda da jan baki mai kalar ruwan hoda(pink).
"Zanyi 'yar tafiya ne,amma in sha Allah bazata wuce kwana uku ba. Amanar gidana yana hannunki sister."
Ta dubi Manal. Murmushi manal tayi kafin tace
"Karki samu damuwa baby,shigarki tayi mana kyau,tamkar bake ba."
Tayi murmushi batace komai ba ta nufi waje. Babu wata wata,ta fada motarta ta shiga. Duk da dai bata taba karambanin tuk'i mai nisa ba,yau kam tanason yi. Dole taje ga mahaifiyarta ta duba lafiyarta. Tsananin kewarta yana neman hanata sukuni,ga fargabar abunda zata tarar sskamakon mafarkin da tayi a daren jiya......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(19)
Tafe take kawai saidai dukkan hankali da tunaninta yana ga zantukan karshe da tayi da mahaifiyarta kafin su rabu.
"Na sanki,yarinya kike mai basira da kula dakai. Kada ki sake ki bari shaidan yayi maki hud'uba Tasleem. Kibi matar ubanki sau da k'afa,kiyi biyayya ga mahaifinki kada ki sanya damuwar komai a ranki. Allah Yana tare dake."
Hawayenta suka k'aru,yayin data k'ara karfin gudunta.
"Fitarmin daga gida,yar iskar yarinya! Kin bata wayonki! Bazaki zo ki b'atamin tarbiyyar yarana ba! Shegiya! Kedai kam ina kwakwanto akanki! Anya nine ubanki?!"
A zuciye ta kuma k'ara karfin speed dinta,hawaye bai bar kwaranyo mata ba.
"Kin bani mamaki kanwata,kin bata wayonki. Har da kanki ki dunga kai kanki dakin namiji?!! Tirr da wannan d'abi'a taki. Toh wallahi ki barmin gidana,kuma kika kuskura kikaje ga mahaifiyarmu kika kashe aurenta,wallahi saikin raina kanki! Kije duniya ce! Daidai take da kowa!"
A fusace take tafiya,bata ankara ba,motar ta kufce mata, ta rasa yanda zatayi ta tsayar da ita. Taka burki takeyi saidai batasan dalilin cijewar burkin ba,haka tayita wala wala har ta k'umu da bishiya. Bata k'ara sanin duniyar da take ba.
******
Farkawa tayi ta ganta kwance a gadon da yafi kama dana asibiti,ta tsurawa rub'abb'en kwanon silin din ido tana duba,hannunta tayi kokarin d'agawa da niyyar tab'a goshinta wanda ke sarawa tamkar zai fad'o saidai wani irin azaba da hannunta yayi ya sanyata cije lebbanta tana 'yar k'ara kad'an.
Wannan ya jawo hankalinsa,yana zaune saman gadon dake fuskantarta yana danne wayarsa a kokarinsa na kiran gida domin kada a jishi shiru ayi tsammanin ko babu lafiya. Ya dubeta,nan da nan zuciyarsa tayi sanyi ya mike ya karaso wajen kanta
"Sannu,ya jikin?"
Ta waiwayo dakyar sakamakon ciwon kan da takeji ya addabeta,ido kawai ta zuba mishi ba tare da tace komai ba. A zuciyarta mamaki kawai takeyi,meyasa Allah Yake yawan kawo mata shi aduk lokacin da take da buk'atar taimako? Abun tambayar ma shine,ya akayi yazo nan?
Kafin ta kammala tunaninta tuni ya juya ya fita. Minti daya sai gashi da likita,likitan ya karaso yayi mata gwaje gwaje kafin ya dubeta yana murmushi
"Sannu fa madam,yanzu meke damunki bayan hannunki? Kina jin wani ciwo daban ne?"
Baby ta k'ak'alo murmushi kafin ta d'aga hannu ta dafe kanta.
"Oh sorry,bari na sanya nos ta k'ara baki magungunanki. A sannu zai daina. Saidai kafin nan..."
Ya juya yana dubansa
"A samo mata abunda zata ci don bana zaton taci wani abu a yau."
Ya dubi Baby wacce tayi tsai da ido tana kallonsa,fuskarta babu yabo ba fallasa kamar dai wani tunanin na daban takeyi. Ya dauke kansa ya maida ga likita yana mai gyada mishi kai.
Likitan yana fita yabi bayanshi ba tare da yace mata uffan ba. Ta bishi da kallo sannan ta kauda kanta tana tuna abunda ya janyo mata hatsarin. Hawaye suka gangaro saman kuncinta,ko kusa batayi yunkurin sharesu ba,saima ta barsu suka cigaba da shatata.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(20)
Haka har ya dawo ya sameta cikin wannan yanayin. Shigowar baisa ta sharesu ba,a zahiri ma sam batasan da wanzuwarsa ba. Lura da cewar ko kusa batasan da shigowarsa bane da kuma sallamarsa,yasa shi yin magana
"Tasleem."
Batasan lokacin data dubeshi ba,haka kawai sanyi ya ratsa zuciyarta domin tunda take bata tab'a jin wanda ya iya kiran sunanta ba kamarsa. Ya kauda kansa yana mai bude ledojin,fuskarsa a daure
"Tashi ki d'an ci wannan."
Ta mike dakyar ta zauna bayan ta sauke kafafuwanta dake ciwo kadan kadan a k'asa. Batace dashi komai ba ta mike tana dafe gado,band'aki ta zagaya. Can kuma sai gata ta fito.
"Ko zaka taimakamin da brush da maclean please?"
Ya mike ya fita, sai gashi ya dawo dauke dasu sabbi. Saida ta tabbatar da tsaftar bakinta sannan ta fito. Maimakon ta iskeshi saita iske nos. Da taimakonta ta ci abincin kadan ta sha yoghurt din da yawa kafin daga bisani tasha magungunan. Bayan nan tayi mata godiya,nos din tana shirin fita ta tsaidata
"Don Allah karfe nawa ne? Inason gabatar da sallar dake kaina."
Ta bata amsa
"Ai Hajiya yanzu haka ma isha'i ta kusa."
Cikin mamaki Baby ta mike tayo alwala ta fito, rarraba idanuwa ta tsaya yi ganin babu wani darduma ko abunda zata rufe jikinta dashi. Turo k'ofar da akayi ta sanyata waigawa. Sukayi ido hud'u dashi,ta sakar mishi murmushi ya kauda kai.
"Sannu HARIS,don Allah inason yin sallah ne."
Wani irin kallo yayi mata,ta kauda kanta. Ya jinjina kai baice uffan ba ya fita. Sai gashi dauke da akwatin kayanta da kuma dardumar dake cikin motarsa. Ajiyewa yayi kawai ya koma gefe ya tsaya domin son ganin ikon Allah. Ga mamakinsa sai yaga ta fiddo Hijab zunb'ulele ta sanya. Baki ya saki har lokacin bai bar jifanta da kallon mamaki ba. Ta lura da hakan,murmushin dai ta k'ara yi mishi a karo na ba adadi. Batace komai ba ta soma kokarin shimfid'a dardumar da hannunta na hagu wanda baya ciwo,saidai ta kasa. Ba zato taga hannuwansa sun kama mata. Ta dubeshi,bai ko kalleta ba. Yana gama shimfid'a mata ya kauce.
"Nagode."
Ta furta a sanyaye. Salloli uku dake kanta ta rama,kafin ta zauna ta kwararo addu'o'i tana hawaye. A karshe ta shafa. Tana shirin mikewa,aka soma kiraye kirayen sallar Isha'i,wannan yasa Haris ficewa zuwa masallaci.
Itama ta gabatar da sallar isha,ta had'a da shafa'i da wutri. Nan ma addu'ar tayi ta shafa duk da irin radadin da hannunta keyi bata k'i d'agashi ba yayin addu'a.
Anan kan darduman ta zauna,kafafuwanta a mik'e tana mai jingina kanta da bango. Bata fi mintuna ba,Haris ya dawo da sallamarsa. Bakinta ya motsa alamun amsawa. Ya zauna a gefen gadon kafin ya soma magana
"Nayi iyakar taimakon da nake ga ya dace nayi gareki a matsayinki na 'yar uwa a musulunci dana sameki rai a hannun Allah na kawoki asibiti. Alhamdulillah,tunda har sauki ya soma samuwa zan tafi. Ga wayoyinki nan..."
Ya sanya hannu a aljihu ya fiddo mata su gami da ajiyewa a gefenta.
"Kina iya kiran d'aya cikin abokan harkarki,anan babban asibitin kauyen danbatta kike. Batun motarki kuma,gaskiya ta samu matsala,amma tana nan a police station na nan gefen asibitin(inji ni.. Lol)idan yaso idan kun tashi saiku janyeta ku koma. Na barki lafiya."
Ya sanya hannu ya fiddo bandirin kud'i na 'yan d'ari biyar biyar ya ajiye mata. Caraf ta riko hannunsa,da sauri ya dubeta. Hawayen da yaga tana fitarwa ne ya sanyaya mishi jiki. Ta narkar da fuskarta tana mai marairaice murya
"Kada ka gujeni a wannan yanayin da nake ciki don Allah Haris. Babu wanda zai taimakeni kamar kai,babu mai bani kulawar daka bani. Da ace kasan inda na nufa yanzu,da bazaka barni ba har sai kayi kokarin sadani da muradina."
Ya dauke hannunsa ya koma ya zauna yana dubanta baice uffan ba.
"Duk tsawon rayuwata a Bariki,ban tab'a cin karo da mutumin da yayi kokarin yimin fad'a akan wani abu na daga bakar rayuwar dana zab'arwa kaina ba,sai kai Haris. Ban taba fahimtar kuskuren da nakeyi ga rayuwata ba sai a wannan lokacin dana kusan mutuwa ba tare dana kai ga neman gafarar Ubangijina ba game da b'arnar dana jima ina aikatawa ba."
Ta tsagaita gami da sanya hannunta marar ciwo ta share hawayenta kafin ta dubi Haris wanda ya zuba mata ido kawai yana sauraronta,auna maganganunta kawai yakeyi a zuciyarsa. Wai gaskiyarta take fad'a mishi ko kuwa dai barikancin ne ya dawo kanshi?
"Da wuya ka aminta da zancena,saidai don Allah ina neman alfarma agareka,ka taimakeni kada ka barni anan. Ka amince na taso mu tafi?"
Ta karashe tana karya wuyanta gefe idanunta a kansa. Ya tabe baki kafin ya girgiza kansa
"Ni ba d'an BARIKI bane,saidai na karanci halayyarku. Ki sani, Allah ba abin wasa bane. Yanzu idan kikace zakiyi karya da sunanSa,zai iya hukuntaki. Ba don ni zaki tsorace shi ba Tasneem. Ban hanaki aikata masha'arki ba. Saidai wannan hatsari daya sameki ya kamata ya zamto izna gareki,da ace mutuwa ta riskeki a daidai wannan lokacin,wane guzuri kika tanada da har kike ganin zai tseratar dake daga azabar Allah?"
Ya k'ara girgiza kansa,bakin ciki karara da kuma tsana ya bayyana saman fuskarsa.
"Kuna ganin cinyewa ce ga diya mace ta fad'a yawon barikanci! Kuna kallon lamarin a matsayin wayewa,alhalin babu abunda zaku tsinta ciki nan gaba sai bakin ciki idan kuwa har mutuwa ta riskeku ba tare da kun tuba ba,hakika zakuyi nadama irin wacce baku tab'a yinta ba a duniya. Babbar DARAJAR DIYA MACE,shine ta kasance a d'akin mijinta. Babu mutunci a zamowarta tamkar wata kasuwa da kowane kara da kiyashi zai shiga."
Ya dakata sakamakon sheshshekar kukan Baby Tasneem daya cika d'akin. Gaba daya a rayuwarsa ya tsani kuka,musamman ma na d'iya mace. Yanzu yanzu ne zaiji zuciyarsa ta karaya,wannan ya sanyashi mikewa da sauri ya nufi hanyar fita.
"(No Haris, please don't leave me alone,please!)."
Baiko juyo ba ya fice daga d'akin. Kuka sosai Baby takeyi,babu abunda take tunanowa sai rayuwarta. Ji takeyi tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta a gaban mahaifiyarta kwance a jikinta. Dakyar ta share hawayenta.
Kasancewar cikin magungunan da nos ta bata harda na bacci,ya sanya ta soma hamma. Tun tana korewa har dai ya dauketa anan kan dardumar ba tare data shirya masa ba........!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(21)
Sanyin asuba ne ya farkar da baby. Duk shaidanci irin na Baby,bata wasa da sallah. Ta mike tana mutsistsika ido. Sai lokacin ta tuno abunda ya afku. Tausayinta kanta ya mamayeta,ta mike ta zagaya bandaki.
Ta jima tana addu'o'inta kafin ta mike ta dauki wayoyinta ta hau kan gado. A sannu ta shiga sarrafata tamkar bataso. Missedcalls din Kb har shida a Mtn dinta dinta,hakanan a Airtel dinma missedcalls har goma. Text message kashi kashi harda na whatsapp,duk tambayar tana ina. Ta samu missed calls daga Momi ma da kuma kawayen nata. Wato su Manal. Sai sauran wadanda ta daukesu matsayin tarkace. Murmushi tayi kafin ta kashe wayar gaba dayanta. Ta kurawa silin ido bata da niyyar bacci. Tunanin Haris ya fado mata, yanzu dagaske shikenan ya tafi ya barta? Hawaye suka kwaranyo mata, haka tayi ta tunane tunane kafin bacci na ba zato ya saceta.
**** BAKWAI DA MINTUNA(7:00AM)
Turo kofar da akayi gami da sallama ne ya farkar da ita daga baccin da takeyinsa ba don dad'i ba sai don kawai yana fisgarta. Idanuwa ciki ciki take dubansa,daman ya lumsassun idanuwanta suke a farke ballantana kuma akwai bacci cikinsu. Ta k'ara lumshesu tana murmushi duk a zatonta mafarki takeyi ba gaske bane. Saida ta k'ara jin sautin ajiye leda a kusa da 'yar dirowar gefanta,tayi firgigit ta bud'e ido ta zuba mishi.
Fuskarsa a daure tamau babu alamun dariya,kallo daya yayi mata ya dauke kansa,baice da ita komai ba ya fice. Bayansa tabi da kallo tana murmushi kafin ta cije lebbanta.
Tabbas Haris yana da tausayi,mutumin kirki ne sannan Ustaz ne na hakika kuwa kamar yanda Kb ya shaida mata. Bata tab'a tsammatar yana nan asibitin ba bai tafi ba sai a yanzu daya shigo. Ta mike ta janyo ledar,murmushi tayi ganin jug dauke da ruwan shayi da batasan daga inda yazo ba,saidai yayi mata kama da sabo. Sai kayan shayin. Mikewa tayi a sannu,zuwa lokacin banda hannunta da take fama dashi babu kuma sauran wani ciwon dake addabarta. Wanka ta soma yi kafin tayi daura kirji ta fito. Kayanta ta dauka a akwati ta koma bandakin ta kimtsa cikin riga da siket 'yan kanti,bakak'e anyi musu kwalliya da fari da bulu. Ta yafa mayafin (pashmina) a kanta,saboda dukkan kayanta bata da wadataccen mayafi kwata kwata. Tana shirin ninke wanda ta cire ne nos ta shigo. Suka sakarwa juna murmushi,kafin nos ta ajiye kayan aikinta akan gadon.
"Sannu madam,bari na taimaka maki. Ai yanzu kada kice zaki dunga wahalar da hannun nan naki,ki bishi a sannu har ya warke."
Ba musu baby ta zauna tana dubanta yayinda take linke mata kayan. Cikin siririyar muryarta ta jefo mata tambaya
"Don Allah na tambayeki mana."
Nos ta juyo tana dubanta
"Inajinki madam."
"Wannan yayan nawa daya kawoni yana nan har yanzu?"
Ta danyi dariya
"Yana nan madam,ai bazai iya tafiya ya barki a wannan halin ba. A masallaci ya kwana yanzu haka ya sanya a wanke mishi motarsa da alama dai yau zaku wuce don likita yace zai iya baku sallama a yau."
Baby ta gyada kanta,ita kanta ta k'agu tabar wajen nan,don ma dai babu laifi,suna kula da tsaftar asibitin nasu. Tana kallo nos dinnan ta k'ara yi mata dressing na hannunta tare da yin allura,sannan ta fice bayan ta gargadeta akan tasha magungunanta.
Ta hada shayin kad'an tana tunanin ko Haris ya karya? Ta daure ta ci ta sha.
Daidai lokacin da take b'allar magungunanta zata sha,ya shigo da sallama likita yana biye dashi. Duk iyakar kokarinta na ganin sun had'a ido bai yarda ba,gashi sai faman d'ad'd'aure fuska yakeyi. Hakan duk ya sanyayar da jikinta.
"Sannu ko? Ya jikin?"
Ta maida dubanta ga likitan,wanda ba shine wanda ya dubata da farko ba. Dakyar ta iya amsa mishi
"Alhamdulillah."
Ya aunata kafin ya duba takardunta sannan ya dubeta
"Akwai inda keyi maki ciwo?"
Girgiza mishi kai kawai tayi domin a zahiri hankalinta yana ga Haris dake danne danne a waya. Batasan dalilin daya janyo bata gajiya da dubansa ba. Haka kawai ya zame mata tamkar farin wata,wani irin kyau da kwarjini ya k'ara yi mata. Zancen likita ya katse tunaninta a inda ya dubi Haris
"Alhamdulillah,zamu iya bata sallama yanzu. Jikinta yayi sauki sosai. Saidai ta kula da shan magunguna hakanan kada ta takurawa hannunta da aiyuka."
"Ok."
Daga haka suka fice tare da Doctor din.
Kafin tayi wani yunkuri,wayarta ta soma k'ara. Ta duba,Kb ne. Dauka tayi tana mai karawa a kunnenta batace uffan ba.
"Hello,hello babyna. Kina jina? Don Allah kiyimin magana kafin na fita a hayyacina."
"Na'am,ina sauraronka Ka..."
Ta gaza k'arasawa sakamakon shigowar Haris. Ya dubeta ta dubeshi kafin ya dauke kai ganin yanda tayi yanayi da marar gaskiya. Akwatinta kawai taga ya bude zif dinsa,ya dauki kudaden daya bata ya sanya mata ciki. Sannan ya dauke dardumarsa yayi gaba tare da akwatin. Ranta yayi sanyi.
"Hello,me kike cewa ne?"
Sai sannan ta tuno da ashe fa waya takeyi
"Look kabir,yanzu ba lokacin magana bane. Zan nemeka."
Ta kashe wayar gaba dayanta. Tana shirin mikewa ya dawo,ledojin magungunanta ya dauka sannan ya ajiye mata silifas dake a hannunsa sabbi fil. Har yakai k'ofa yayi magana tamkar bayaso
"Kina iya tasowa."
Ya ficewarsa,ta mike ta sanya silifas din tana murmushi. Komai na Haris burgeta yake, a tun ranar data soma ganinsa.
*****
A harabar asibitin ta hangoshi yana kokarin mikawa wani kud'i da alama dai shine wanda yayi mishi wankin mota. Kallonta da yayi ne ya sanyata soma tafiyar nan nata mai kama da yanga ta nufeshi bayan ta dauke idanunanta a kansa. Zagayawa yayi ya shiga motar, itama ta zagaya ta shiga gidan gaba. Ribas yayi ya fita daga asibiti
"Barka da asuba Haris."
"Barka. Ya jikin?"
Ya fad'i tamkar dole akayi masa,
"Alhamdulillah,na samu sauki sosai."
Baice uffan ba,kai tsaye police station dinnan ya nufa. Anan baby taga motarta a ajiye.
"Ina zuwa."
Ya fice, magana taga sunyi da wani sanye da kayan 'yan sanda kafin ya fiddo kud'i ya bashi. Sai kuma taga sun zaro waya,Haris na magana mutumin yana kwafa hakan ya fahimtar da ita cewar lamba ya bashi. Tayi tsai tana dubansa,ta tsani yawan kallo,batayi hakanan batason ayi mata. Amma menene da Haris wanda ke daukar hankalinta ga kallonsa.
"Kefa banza ce, keda ake ganin kin fita daban ko cikin kawayenki da sauran hadaddun 'yan barikin da kuke tare. Menene na yawaita kallon wanda a kyau babu abunda zai gwada maki?"
Zuciyarta ta kwab'eta,wannan yasa ta gyara zamanta ta maida dubanta ga gabanta. Saidai kamar jan idanunta akeyi,sai gashi suna komawa ta gefe gefe suna duban Ustaz Haris. Ganin ya taho yasa ta daure ta sunkuyar da kanta har ya bud'e motar ya zauna. Sai anan ya dubeta....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(22)
"Zan mik'a ki tasha. Idan yaso saiki hau mota ya k'arasa dake. Nima naje ga abunda ya kawoni."
Bai saurari cewarta ba yaja motarsa ya soma tafiya.
"Nagode da taimakonka gareni,fatana Allah Yasa zumuncinmu ya..."
Kallon daya watso mata ne hanata k'arasawa. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta murmusa
"Wai har yanzu ba'a bar fushi dani ba? Ya dace kayimin uzuri,tunda kaji nace maka nayi na damar ayyukan da nake aikatawa wanda daman tilastani akayi,toh iyakar gaskiyata na fad'a maka. Ban iya rantse rantse ba,nafiso mutum ya yarda dani. Banga wanda zan yiwa karya ba Haris, ba halina bane."
Ta kauda kanta gefe tana wani d'an tunani,shi kuwa nanata maganarta yakeyi. Tilasta ta akayi tayi karuwancin kamar ya? Haka yayita juya maganar,zuwa yanzu zai so yaji tarihinta saidai bayason yiwa mutum shishshigi a sha'anin rayuwarsa.
"Baka tambayeni inda zanje ba?"
Ta jefo mishi tambayar tana dubansa da wannan shu'uman idanuwan nata. Ya dan kalleta babu laifi ya dan saki fuska kad'an.
"Mahaifiyata zanje gani."
Baisan sadda yayi mata duban mamaki ba,tana murmushi yayinda hawaye suka kwaranyo mata ta gyada mishi kai
"Eh Haris,mahaifiyata zanje gani. A yau bana bukatar komai sai ita. Rabona da ita shekaru uku kenan."
Ya shanye mamakinsa yana maida dubansa ga titi
"A wane gari kenan?"
"KAZAURE."
Ya gangara ya sauka gefen titi,bayan mamaki daya bayyana a saman fuskarsa har da d'an murmushi. Haka kawai yaji dadin kasancewarsu 'yan gari guda. Ita kam kamar a mafarki haka take ganin murmushin da yakeyi gareta. Wannan yasa ta dan lumshe ido ta budesu domin tabbatarwar,saidai har zuwa lokacin basu gushe ba.
"Menene ya baka mamaki na kasancewata 'yar Kazaure?"
Yabar kallonta,fuska a sake yace
"Kasancewata d'an Kazaure shiyasa nayi mamaki."
Itama baby ta d'an bude ido cike da mamaki kafin ta langab'ar da kai tana marairaice murya
"Daman garinmu d'aya amma kake kyamatana?"
Yayi tsai yana dubanta,ita kam wayewar har tana neman yi mata yawa. Yanayinta ne a haka ko kuwa dai tsabar kwarewa a bariki ne?
Ya kauda wannan tunanin ta hanyar fad'in
"Ban tsanar dan uwana musulmi saidai na tsani wani hali nasa. Me kikayimin da har zan tsaneki Tasleem? Hakikanin gaskiya gurb'atacciyar rayuwa irin wacce kikeyi ne na tsana,bana kaunar dukkan mabiyanta. Babu wani burgewa a cikinta face tsantsar nadama a karshe wanda wasunku ma alokacin komai ya k'are maku babu damar tuba. Ki godewa Allah da akwai sauran numfashinki,yaci ace kinyiwa kanki fad'a da karatun ta nutsu. Kisa misali idan da ace ya zamto mutuwa ce ta riskeki yayinda kikayi hatsarin nan,wani guzuri zaki tafiyarwa Ubangijinki dashi da kikejin ya isheki kufcewa azabobinSa?"
Ta share hawayen da tun soma maganarsa suke ambaliya,idanunta yana ga kallon titi tace
"Nasani dukkan abunda ka fad'a babu k'arya aciki. Hakika rayuwar dana zab'arwa kaina ba rayuwa ce ta abun tutiya da tak'ama ba. Rayuwa ce tamkar ta dabbobi,inda mutum yake da damar yin kowane kalar sab'o ba tare da tunanin makomarmu ba. Na tafka kuskure a rayuwata Haris,saidai kamar yanda na fad'amaka,tursasani akayi."
Tun soma maganarta idanunsa ke kanta,maganarta ta karshe ta chanja yanayin duban da yake mata zuwa na rashin fahimta.
"Har ila yau,bangane manufarki ba Tasleem. Daman akan tursasa mutum ya sab'awa umarnin UbangijinSa shi kuma ya amince yabi?"
Tayi murmushi mai ciwo,ta jinjina kanta
"Bacin rai da bakin cikin kazafi da akayiwa mutum bada hakkinsa ba,ya sanyani fad'awa wannan yanayin. Abun bakin cikine ace makusantanka sune basu yarda dakai ba,har suke gaskata sharrin makiyanka. Meyasa wannan bazai dameni ba? A halitta irin tawa,na kasance mai saurin fushi da zuciya. Duk da cewar inada saurin sauka kamar yanda wasu suka fad'a,saidai na rasa yanda akayi na kasa barin abunda ya faru ya wuce a rayuwata. Babu wanda na tsana tamkar mahaifina,duk duniya babu wanda yafi bani mamaki kamar d'an uwana da muka fito ciki d'aya dashi."
Ta tsagaita ta dubi Haris wanda shima idanunsa ke kanta cikin rashin sanin inda ta dosa da maganganunta.
"Kada kayi mamaki idan kaji cewar mahaifina sananne ne a fad'in jahar Kano ba b'oyayye ba."
Ai sai ya kasa dauke ido a kanta,yayinda ta cigaba da yi mishi murmushin nan wanda ke k'ona zuciyarta. Haris ya numfasa
"Idan kinga babu damuwa,ko zaki iya bayyanamin labarinki Tasleem?"
Ta d'anyi shiru tamkar bazatace komai ba,can kuma ta karkato jikinta sosai tana mai lankwasar da kafafuwanta a saman kujera. Idanuwanta suna duban na Haris, yayin da fuskarta ta chanja kala zuwa ja. Murmushi ta k'ak'alo ta jefamishi
"Zakaji tarihina,zakaji wacece ni Haris. Na yarda dakai dari bisa dari."
Ta jingina kanta jikin kujera ta tsurawa sitiyari ido kafin ta bud'i bakinta ta soma magana...
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(23)
"Mahaifina Doctor Abba Waziri,d'a a wajen marigayi Wazirin Kano,Alhaji Ma'aruf Waziri.(ahuwan kanawa..lol)."
Haris ya fiddo ido kadan yana dubanta cikin razana,Doctor Abba Waziri? Shi kuwa ya za'ayi ya kasa saninsa? Babban likita kuma kwararre a fannin k'ashi. Dukkan fad'in garin kano harma da yawa daga sauran garuruwa ansan da zamansa. Ko marigayi mahaifinsa,Alhaji Ma'aruf Wazirin kano,baiyi sunan da d'an nasa yayi ba. Wajen taimakon mutane da kiyaye lafiyarsu.
Baby ta cigaba da zancenta bata ko damu da razanar data sauka a saman fuskarsa ba.
"Mahaifiyata kuwa,Hajiya Maryam Abdulmalik,haifaffiyar Kazaure ce. D'iya a wajen babban limamin masallacin juma'a na Kazaure,Malam Abdulmalik Hussein."
Ai sai Haris ya k'ara sarewa,Malam Abdulmalik Hussein,babban aminin kakansa ne na wajen uba. A iyakar saninsa,gidansa ya zamto na mahaddata Al-k'ur'ani. Suna da nutsuwa yaransa hakanan kowannensu suna zaune ne a gabansa. Duk shine ya aurar da yaransa. Kenan Gwaggo Maryama itace mahaifiyar Tasleem? Unbelievable!
Sai lokacin ne ma idanuwansa suka soma hasko masa kamannin Gwaggo maryama a fuskar Tasleem.
Hawaye akan fuskarta
"Wad'annan bayin Allah biyun,sune sukayi silar samuwata a duniya da ikon Allah.
Mahaifana sunyi rayuwa cike da jin dadi a matsayinsu na ma'aurata kafin Allah Ya albarkacesu da samun d'a namiji,Abdullah. Yaya abdullah yana da shekara d'aya a duniya,kakanmu Alhaji Ma'aruf ya rasu aka nad'a Yayan mahaifina,Alhaji Nasir akan karagar mulki.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(25)
Mamma tana nan zaune har na kusan mintuna sai gasu sun fito suna dariya. Abba yayi shirinsa na tafiya asibiti yayinda briefcase dinsa ke a hannun Raliya tana takowa da murmushi dauke saman fuskarta. Mamma duk da haushinta da takeji ta kasa cewa uffan akan wannan al'amari,saidai ta daure fuska. Wai ma duk a banza,Abba baisan tana yi ba. Har ya nufo teburin sai Raliya tayi saurin magana,wai me yake nufi ne? Bazaici wainar da tayi mishi ba? Ga mamakin Mamma sai ya juya ya dubeta ya bata hakuri cewar zaije yaci wainar Raliya kada tayi fushi. Mamma kai kawai ta gyada mishi,ta kasa cewa uffan har suka fice.
A ranar kuma,da daddare tana zaune a falonta,Abba yayi kiran wayarta yana nemanta. Ba musu ta tafi da tsohon ciki,ta nufi sashensa. Turus tayi ganin matasan da basu wuce ashirin da wani abu ba,zaune saman kujera tare dasu Abba da Raliya sai hira akeyi da dariya. Abba ya ankara da shigowarta,ya dubeta kafin yayi mata iznin shigowa. Ta karasa ta zauna a gefensa. Abba ya dubi samarin
"Banji kun gaisheta ba?"
Sai lokacin dukkansu suka hau kwasar gaisuwa,Mamma ta amsa. Bayan ya kira sunanta,ya shaida mata yaran Raliya ne,da Hamza,Nura da kuma Usman. Anan gidan zasu cigaba da rayuwarsu kasancewarsu marayun da ubansu ya rasu. Zai dauki nauyin karatunsu da komai ma na rayuwarsu. Maganar ta daki Mamma,sai lokacin ta k'ara gaskata magana gwaggo sarai. Ta boye mamakinta tayi mishi fatan alheri akan niyyarsa sannan tayi mishi alk'awarin itama zata daukesu tamkar Abdullah d'anta. Bazata bambantasu ba kamar yanda ya nema. Abba yaji dadi,yace su bata girmanta a matsayinta na matarsa. Suma kamar gaske sukayi na'am. Daga haka ta tashi ta koma.
Zamanta da Raliya kuwa zama ne ba yabo ba fallasa,Raliya aikinta bai wuce jaye jayen fad'a ba duk da ba sashe d'aya suke ba. Tsakaninta da Abba ma ya chanja,ya zamana mukullan motar gidan a hannunta suke,acewarsa itace babba don ta girmeta. Mamma batace komai ba ta bisu hakanan.
Babbar matsalar data soma tayarwa Mamma hankali,bai wuce kwananta da yake kaiwa ga Raliya ba. Ya chanja mata kullum cikin daure dauren fuska. Abdullah bashi da damar sakewa da Abba kamar a baya,ya zamana bai fiye janshi da wasa ba.
Cikin wannan yanayin na rashin samun kulawar miji,abunda bai kai ya kawo ba zai hau ta da fad'a marar dalili koda a gaban 'yan aiki ne. Nakuda ya kamata,gatanan ita d'aya a d'aki. Da abun yaci tura ta lalubo wayarta ta kira Abba. Cikin magagin bacci ya amsa,jin cewar tana nakuda ne ya wartsakar dashi domin har lokacin akwai burbushin sonta a ransa. Haka ya taso Raliya na biye dashi."
Baby ta dakata tayi dariyar takaici gami da kwafa
"Ta hana akai uwata asibiti,shegiyar taso ta kasheni Allah Yayi zan fito duniya na zame mata annoba."
Haris dai kallon Baby yakeyi,murmushi kawai yayi jin abunda ta fad'a kafin ta cigaba.....
Sorinku...bana gida ne...sai zuwa dare in sha Allah.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(24)
"Mamma,wato mahaifiyata. Sunan da muke kiranta dashi kenan,tana dauke da cikina ne babu zato Abba ya soma shirye shiryen aure. Sam,Mamma bata tayar da hankalinta ba kasancewarta mace tagari,wacce take da ilimin addini kuma take aiki dashi. Ta bashi goyon baya sosai har kuma a yanda ta labartamin yazo yana jin kunyarta ba kuma ya fasa batun auren nasa ba.
Hankalin Mamma bai tashi ba har saida labari ya risketa ta hanyar kanwar Abba,Gwaggo Sarai akan wacce Abba zai aura ba yarinya bace. Asalima a girme ta girmeshi nesa ba kusa ba sannan tana da manyan 'ya'ya maza har su uku sai kuma mace d'aya dake gidan mijinta. A yanda Gwaggo Sarai ta ji harda yaran Abba yayi na'am zai rike mata su tunda dai marayune mahaifinsu ya rasu gashinan su d'in basu kasance masu kudi ba. Wannan babban taimako ne zaiyi. Tun alokacin ma ya zamana shine komai na karatunsu,domin kuwa sun kusan yin watanni uku suna tare da Abba kafin ya sanarwa Mamma halin da suke ciki. Wannan shine ya d'agawa Mamma hankali saidai ta nunawa Gwaggo Sarai hakan ba damuwa bace tunda a irin girma na gidan Abba da kuma tazara dake tsakanin sasunan guda uku sai mutum yayi abunda zaiyi babu wanda yaga wani tsakaninsu. Sai bayan tafiyar Gwaggo Sarai ne hankalin Mamma ya tashi,ta nemi yin shawara da aminiyarta wacce bani da masaniyar ko har yanzu suna tare,wato Hajiya Aisha,itama 'yar Kazaure ce kamar yanda Mamma ta gayamin. Ta sanar da ita halin da take ciki,Hajiya Aisha ta bata shawara akan ta dage da addu'a domin dai idan ta d'aga hankalinta babu ribar da zata tsinta a ciki. Haka dai Mamma ta nutsu ta zubawa sarautar Allah ido. Lokacin kuwa Abdullah babu inda baya yawonsa ya soma wayo.
Akayi shagalin biki tamkar na wata budurwa da saurayi harda dinnerparty. Koda Mamma ta nunawa Abba rashin alfanu ayin wani party sai ya hau fad'a acewarsa tunda ita Hajiya Raliya haka tafiso toh bazai hanata ba,idan Mamma taga zata amsa gayyatarta toh,idan kuwa bazata je ba nanma matsalarta.
Tun lokacin Mamma ta soma shan jinin jikinta,ace tun kafin ta Raliya ta shigo har ta soma ganin chanji daga Abba?"
Baby ta dakata da tabe baki tana girgiza kai cikin tsana
"Hum,Haris yawancinku maza baku da kunya. Baku kunyar nuna rashin adalci k'arara a bayyane."
Ta numfasa kafin ta d'ora
"Saida Mamma ta toshe kunnuwanta ta kauda kanta. Ga tsohon ciki da take fama dashi ga kuma wannan damuwa na auren da Abba zaiyi data sanya a ranta. Ta gwammace ace Abba ya samu matashiya daidai ita ya aura akan dai ya auro mata babbar mace wacce ta doshi arba'in. Don alokacin Mamma bata wuce talatin ba,gwara ma Abba ya girmeta don zai kai talatin da takwas. Haka Mamma ta rame,ta zamana Abba hankalinsa kacokam ya koma ga Raliya tamkar wanda ya auri budurwa,kai a yanda Mamma ta misaltamin cewa tayi koda budurwar ya aura sai haka.
Bayan Raliya ta tare ne,Abba ya sami Mamma a daki a niyyarsa ta wucewa dakin Raliya. Anan ya tambayeta game da kwana nawa ta bashi,takaici ya sanya tace mishi sati biyu. Ta dauka zai nuna wata alama ta damuwa saidai walwala data k'aru a fuskarsa,yayi mata godiya ya ajiye mata leda ya fice.
A wannan sati biyun kuwa,Mamma sai ta wuni cur bata sanya Abba a idanunta ba duk da tasan yanayin aikin likitanci,wani sa'in da daddare yake fita amma abun yayi mata ciwo. Ko irin ma a kawo maka amarya ku gaisa baiyi ba.
Saida yayi kwana uku kafin ya lekota,anan ne tayi mishi tambayar ko bazai kawo mata matarsa su gaisa bane. Sai cewa yayi,a girme fa Raliya ta girme mata don haka ita ya dace ta taka taje su gaisa. Domin shi kanshi yana bata girma a matsayinta na wacce ta fishi shekaru. Mamma shiru kawai tayi don mamaki,don alokacin idan Abba yana wani furucin saika rantse baida ilimin addini. Ta rasa dalilin juyamata baya da yayi. Abun sai ya kasance tun tana ganinsa da wasa har dai ta daina,don koda girki ya dawo hannun Mamma sai ya chanja mata. Komai tayi na burgewa sai ya gwatsale yace baiyi mishi ba. Batun Raliya kuwa,Mamma bata ganta ba sai a safiyar da take da girki. Tana cikin shiryawa Abba kayan karin kumallo akan tebur,Raliya ta shigo. Mamma ta kalleta a d'an firgice saboda rashin jin sallamar da batayi ba. Kyakkyawan harara ta watsawa Mamma tana yiwa cingam wani d'an iskan tauna.
Raliya gajeriyar mace ce,mai k'iba. Fuskarta sai godiyar Allah,domin kuwa bata daga layin kyawawa da kuma tsaka tsaki. Kallo d'aya zakayi mata kasan an gwabza a duniya. Ta k'araso ta watsawa Mamma duba na raini a karo na biyu,gaban Mamma ya bada sautin dam! Haka kawai taji matar tana bata tsoro,tayi saurin sunkuyar da kanta ba tare da tasan dalilin dayasa take tsoron Raliya ba daga haduwa da ita a farko.
"Mijina na biyo."
Ga mamaki sai ga Mamma ta d'aga yatsa tana nuna mata hanyar d'akin Abba,muryarta na rawa tace
"Yana ciki,ki shiga."
Malalacin murmushi Raliya ta sakar mata sannan ta karasa ciki. Sai fa a lokacin ne Mamma taji tamkar ta jawota ta shak'eta alhalin a farko bata iya tab'uka komai ba....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(26)
"Ta sanya Abba ya fice daga dakin tace mishi babu komai ai ta iya karb'ar haihuwa. Abba ya fita. A haka Raliya ta zauna tana duban Mamma tana faman salati. Bata yi wani yunkurin komai ba,cikin ikon Ubangiji kuma ta haifeni,jin nayi kuka Abba yana shirin fadowa dakin tayi azamar mikewa ta isa ga Mamma. Anan ta tambayeta inda ta ajiye kayan haihuwar,Mamma tayi mata nuni da hannu,nan ta sami reza ta yanke cibiyar domin dai ta iya d'in tsabagen mugunta ce ya hanata taimakawa Mamma koda da sannu ne. Daga haka ta wanke hannunta ta fito ta dubi Abba tace yayi kiran yar aikin mamma. Yaje ya kira kulu,itama tayi mamakin nakudar da Mamma tayi a daren kuma sam bataji ba. Nan ta shiga ta tsaftacemu ta gyara wajen.
Haka washegari mutane sukayita tururuwar zuwa ganina. Ranar suna aka sanyamin Tasleem.
Rayuwa tana tafiya har nayi shekaru biyu a duniya da dadi da rashinsa babu kalar wanda Mammana da yayana Abdullah basu gani. Daidai da 'ya'yan Raliya basu kyaleta ba,sun raina Mamma,rashin kunya babu irin wacce basuyi mata. Wani sa'in idan suka fita yawon darensu basu shigowa gidan sai washegari. Mamma tana lura da komai nasu, har dai rannan ta kasa daurewa a matsayinta na matar gida mai kokari wajen kiyaye dokokin Allah,ta yiwa Abba maganar akan ya dunga sanya ido kan 'ya'yan daya kira amana gareshi. Ta fada mishi yanda suke tafiyar da rayuwarsu wannan ya sanya Abba zuwa sashen Raliya ya tarar dasu yayi musu tambaya game da hakan. Nan suka k'aryata,sukace su kam idan sunyi dare toh basu wuce majalisarsu. Raliya tayita bambamin fad'a har da tashi taje sashen Mamma wai don ba yaranta bane shiyasa takeyi musu sharri da yawon banza. Haka dai tayi ta fada mamma mai hakuri batace komai ba. A karshe ta fice, shima Abba ya bawa Raliya hakuri,ita kuwa ta tubure wai idan har ya kasance mai daukar magana ba tare da bincike ba toh lallai bazasu daidaita dashi ba zata dauki mataki kan hakan. Abba ya lallab'ata kafin ya juya ga Mamma ya hau yi mata fad'a akan tana neman shiga tsakaninsa da matarsa.
Tun daga wannan ranar ne kuma,yaran Raliya suka daina ganin girman Mamma,acewarsu ta sanya musu ido. Sai ta wuce su wuce amma ko gaisheta basuyi.
Shekara biyu ne tsakani da Yaya Abdullah,shekara kuwa na zagayowa,aka sanyashi a makaranta yana da shekaru uku a duniya. Duk da alokacin yayana baida wani girma saidai Allah Ya bashi baiwa ta hankali ga wayo. Yakan zauna ya fashe da kuka idan yaga Mamma ta zauna tana yi,hakan ne ya janyo tabar yin kuka a gabansa saidai ta kulle kanta a d'aki idan abun yayi mata yawa tasha kukanta ta share hawayenta. Ita kadai tasan wuyar da Abba ya gasa mata kafin na girma nayi hankalin sanin abunda ke wakana.
Duk fa wani arziki da mace zata rayu cikinsa idan har mijinta bai bata kulawar daya sabar mata dashi ko kuma ma ace baya bata gaba d'aya,toh fa bata da wani jin dadi a rayuwa idan har tasan ciwon kanta. Menene amfanin rayuwa namiji yana wulakantaka alhalin karkashinsa kake?
Ko Hajiya Aisha bata da masaniyar halin da Mamma ke ciki don macece mai zurfin ciki,ni kaina sai bayan dana ziyarceta bayan mutuwar aurenta nakejin wannan d'an labarin daban sani ba a bakinta duk da a rufe ta bani ba komai take bud'emin ba.
Raliya bata rufa shekaru biyu ba a gidan,Allah Ya azurtata da haihuwa 'yan biyu,mace da namiji. Kar kaso kaga dukiyar da aka kashe,Abba kuwa sai kace ba'a tab'a yi mishi haihuwa ba. Haka ran suna sai gidan Waziri akaje akayi taro. Nan ma anyi shagali,Mamma ko a kanta saidai fa tayi mamaki kwarai na yanda wasu cikin yan uwan Abba suka bar shiga sha'aninta saima suyi zuwa biyu gidan Abba amma saidai ya samu labarin ko daga yar aikinta kulu na ta ga fitarsu ko sunce a gaisheta. Aka sanyawa yara suna,Hamid da Hamida.
Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka,'yan biyu suna da shekara daya ta kara haihuwar mace aka sanya mata Hindatu. Mamma kuwa tun daga kaina sai cikin ikon Allah haihuwarta ya tsaya abun yana damunta saidai hakanan ta barwa Allah.
Yan biyu suna da shekaru shida a duniya,hakanan suna aji daya a primary,yayinda Hindatu ke a Nursery 2. Yaya Abdullah kuwa lokacin yana (primary 6) ne,akayi auren Hamza,ni kuwa lokacin shekaruna takwas a duniya ina aji na uku a firamare. Ranar da Yaya hamza ya tare a gidan aurensa,har 'yar walima nayi da k'awayena a ajinmu bayan mun fito break saboda tsabar murna. Na wahala sosai a zaman Yaya hamza a gidan nan duk da cewar banda wani wayo amma alkawari ne duk sadda muka hadu sai ya murdemin kunnena. Gashi sam bashi da fara'a,akwai sadda ya aikeni nak'i zuwa domin mamma ta hanani shiga b'angarensu shi kuwa yace naje na dauko masa canvas dinsa,ba tsoro nace mishi ban zuwa Mamma ta hanani shiga dakinsu. Ranar saida na gwammace kid'a da karatu. Haka ya kamani ya zaro belt ya jibga tamkar ya samu wata babbar mace. Saboda azaba ko tashi ban iya yi daga wajen ba saida Maigadi ya daukeni cak ya kaiwa Mamma. A can ma mamma saida ta bubbuge bakin nawa sakamakon Allah Ya isan da nayita jero mishi. Tun daga ranar ko yaya na yiwa Hamza laifi,kai koda ace banyi bama toh fa sai ya kamani ya mora da duka. A lokacin kuma,Nura da Usman basu k'asar,Abba ya biyamusu sun fita London karatu. Tun ina Nursery,amma har nayi wayo na shiga Primary basu dawo ba. Allah kadai yasan abunda suke shukawa. Koda ace twins sunyimin laifi,nakan kamasu na jibga a hanyar zuwa makarantarmu domin makaranta daya ake kaimu. Haka zan horasu a mota,koda Malam Nasir yayimin magana saidai na zumbura baki nace ya rabu dani tunda baisan abunda sukeyimin ba. Haka kuwa idan muka dawo zasu sanar da uwarsu,har nan gaban Mamma take zuwa koda ina kuryar daki,shiga takeyi ta jawoni ta jibga wataran kuwa Yaya hamza take sanyawa ya kamani ya jibga.
Yaya abdullah ya tsani wannan rashin ji nawa,domin haka Allah Ya yini,bani yarda a taka uwata. A gabansa a mota zan jibgi yan biyu bai isa ya hanani ba don koda ya hana banaji. Sannan baison taba lafiyata tun ma muna yaran,haka zaiyita lallab'ani saboda yasan na fisu gaskiya ni ce sama dasu basu bani girma. Allah Ya yini mace mai son girma tun ma kafin na zama wata cikakkiyar budurwa.
Tun ina da kankanin shekarun nan na soma tsanar Abba ganin yanda yake budewa Mamma wuta ba tare da tayi mishi wani kwakkwaran laifi ba.
Yasha cewa wai yaranta basu da tarbiyya ta k'ara gyara tarbiyyarmu tunda har a matsayina na babba bana tausayin kannena nakan kamasu na duka. Mamma taji ciwon furucin Abba saidai kawai ta bashi hakuri akan bazai kara faruwa ba.......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(27)
Auren da Hamza yayi shine ya kawomin kwanciyar hankali kad'an a gidan. Domin duk sadda yazo idan har zamu had'u ban tsira ba.
A wannan lokacin ne Abba da Raliya suka tashi tafiya Saudiya domin aikin umrah aka shirya tafiya harda yaranta. A lokacin ne nayita kuka ina korafin Abba bai taba zuwa dani ba. Nan ta Mamma ta hau yimin fad'a na rufe bakina,domin ko yayana abdullah bai taba ketarawa zuwa Saudia ba ballantana kuma akai ga ni. Haka nayita fushi,a karshe naje batare da sanin Mamma ba na iske Abba a falonsa shi kadai. Rok'onsa na shiga yi akan a tafi dani saidai hakuri daya bani kan cewar nima zanje wataran. Duk da kankancin shekaruna nayi bakin ciki kan haka. Ga twins masu aikin yi mini gwalo. Babu yanda na iya haka suka fice akan idanunmu.
Saida sukayi sati biyu sannan sukayo waya zasu dawo. Mamma bata damu ba ta shirya abinci ta jera akan dinningtable na sashen Abba bayan an gyara komai na sashensa. Na kalli jerun kulolin da aka ajiye naja tsaki cike da bakin cikin wannan rashin damuwa da Mamma batayi akan irin cin kashin da kuma bambanci da ake nuna mata. Dabara ta fadomin,a guje na koma sashenmu,jakar Yaya abdullah na bude na fiddo office pins guda hud'u kafin na koma a guje sashen Abba. Mamma na kwalamin kira tana tambayar inda na nufa saidai ban ko saurareta ba. Haka nace na samu kujerun da Raliya da yaranta suka mayar kamar na gado, na caccaka kafin na kwashe da dariya. Ina hanyata ta fita dakin mukaci karo da Abdullah. Harara ya watsamin kafin ya tambayeni abunda nayi da officepins dinsa,a zatona bai ganni ba saidai fa yana daga falo alokacin,ganin na fito daga dakinsa yasa shi shiga kuma ya taras na zubda wasu a k'asa. Na nuna mishi banyi komai ba yace karya nakeyi,wannan yasa na fashe da kukan karya sanin da nayi baison ganin hawayena.
Nan fa ya hau rarrashina ya ja hannuna muka koma dakinsa ya bani alawa. A zuciyata banda Allah Allah da nakeyi na dawowarsu bana komai. Ai fa wajen magrib sai gasu sun shigo. Nan yan uwan Raliya da sukazo tararsu suka kacame da ihu da murna cikinsu kuwa harda hamza da matarsa Zakkiyya. Sai wajen bayan isha'i kowa ya watse. Yan biyu da kuma Hindu sun kara murjewa abinsu,da ace sun fini kyau dana sha haushi alokacin don har kalloni sukeyi suna gwalo. Na tabbatar sai sun dunga mamakin yanda nake murmushi ga wani ladabi dana soma yiwa Raliya. Ni ce harda zuwa sashenta na durkusa ina yi mata sannu da zuwa. Ita kanta tayi mamaki,saidai ta amsa tana dariyar mugunta. Nima ficewata nayi da dariyar ta mugunta.
Misalin tara na dare akayi zaman cin abinci,saida na tabbatar da kujerun da ban sanya alluran nan ba,ba nan mamma da abdullah suka zauna ba,haka nan Abba baya chanja wajen zama,waje daya ne kadai nashi. Nima naja na zauna don nafi kowa zumudin azo aci. Abba ya dubeni
"Tasleem tashi maza kije ki kirawo Maman.."
Bai karasa ba sai gasunan sun iso,Raliya sai shan kamshi takeyi ala dole an zama Hajiya. Abunda yafimin dadi lokacin bai wuce na itace ta soma zama ba,sai ta sanya k'ara ta mike tsaye tana sosa mazaunanta. Abba da Mamma suna cikin tambayarta ko lafiya,suma yan biyu suka zauna har da Hindu. Ai kuwa Hindu ta canyara ihun kuka,yan biyu ma haka. Raliya ta fusata ta hau duba kujerun,ai kuwa nan ta fiddo alluran,ta ajiyesu kan teburin. Dukkaninmu muka kalla,ciki harda ni,bansan ya akayi ba sai ji nayi na saki dariya. Abba ya buga tebur a fusace
"Waye da wannan aikin? Ke kuma yar iskar yarinya shine kike dariya?!"
Mamma a sanyaye tace
"Wallahi bansani ba doctor,Tasleem kodai kece?"
Ta jefomin tambaya,Yaya abdullah kawai hararata yakeyi,
"Bani bace nima.."
"Kinci kaza kazanki! Munafuncin da uwarki ta koyamaki kenan na ki raina matata ko? Toh yau zaki gane shayi ruwa ne! Amma kuwa Maryam kin bani mamaki,sai kace wata jahila har kike tiwa yaranki tarbiyya b'atacciya! Me kikeso ki koyarwa yarana ne?!"
Bansan lokacin dana mike ba
"Abba ba laifin Mamma bane! Ka daina yi mata fad'a."
Mari naji,nan kuma Raliya ta rufeni da duka,Abba cewa yakeyi
"Kinga irin tarbiyyar ko? Wallahi kedai Maryam kin cuceni."
Mamma mikewa tayi a fusace tabar falon na tabbata haushina taji,Yaya abdullah ma fita yayi. Raliya ta dauki allurar nan tayi ta tsikaramin ina ihun kuka. Saida ta gaji da jibgata sannan ta sakeni,Abba baice komai ba. Haka na fice ina kuka. Saidai kuwa ina shiga falon Mamma na tarar da ita zaune tana kuka wannan ne silar shanye nawa kukan. Na karasa na durkusa a gefe,
"Ya zanyi dake Tasleem? A shekarunki da ko tara baki cika ba kinsan kiyi wannan muguntar me zaki zama a yayinda girma ya tasa ki? Ashe haka zaki cigaba da janyomin magana da cin mutunci?"
Gaba daya hankalina ya tashi,mukayita bawa Mamma hakuri,anan ta gargadeni da kada na kuma. Saida mukayi yini cur Yaya Abdullah bayamin magana don tsabar bakin ciki,hakanan a karshe ya sauko.
Na sanya a raina sai nasa an jibgi twins a makaranta. Na fidda homeworks dinsu a jaka na cusa a nawa jakar dayake antinsu muguwa ce. Ai kuwa a ranar saida ta zanesu don har muka baro makaranta suna kuka da Allah Ya isa. Banda kyakyata dariya dana dunga yi a motar bance uffan ba. Saida mukazo gida na fiddo na basu abinsu. Ai kuwa kai tsaye wajen Mamma sukaje suka gayamata. Mamma bata taba dukana ba sai a ranar,Kulu ce ta kwaceni daga hannunta.
Bayan dana cika shekaru goma sha biyu a duniya.............
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(29)
Ina nan zaune tare da Gwaggo Hajara naji sallamar Yaya abdullah. Harara ya soma makomin kafin kuma ya kama kunnena ya murd'a. Tunda nake da yayana bai taba yimin abunda naji zafi ba sai yau. Ihu nakeyi,wanda hakan ya shigo da gwaggo Hajara dake dakinta. Ta dakamishi tsawa kafin ya hankad'ani nayi baya ina kuka.
"Menene haka Abdullah? Metayi maka?"
Yana huci yace
"Duk wata matsala da mamma ke shiga,Tasleem tana da kamasho a ciki. Yanzu kin janyo Malam yayi fushi yace ta zauna har sai ya nemi Abbanmu yaji abunda ke faruwa anyi zaman sulhu. Ga mamma na kuka,nikam ban taba ganin yarinya irinki ba. Duk da irin kwab'ar.."
"Kai dakata,menene ya faru da Adda Maryam din?"
Gwaggo Hajara tayi tambayar da batasani ba. Abdullah baice komai ba ya fice. Sai ni na labarta mata komai ina kuka. Na kara da cewa indai Mamma bazata koma ba toh nima babu inda zanje anan wajenta zan cigaba da rayuwata
Gwaggo Hajara dai batace mini komai ba sai jinjina halin zurfin ciki irin na Mamma takeyi. Ba don ma dai so GAMON JINI bane,manyan mutane nawa ne a kauyen nan da suka nemi auren Maryama basu samu ba,Allah Yayi sai tayi zaman birnin Kano.
Muna ganin abun da wasa sai gashi kuwa hutunmu yana k'arewa na sati daya da zamuyi a Kazaure. Direbanmu yazo,nan Malam yace babu inda Mamma zataje sai Abba ya tako yazo anyi magana. Ko a jikina,don da a sona ne nima bazan koma va saida Mamma ta budemin wuta daman cike take da haushin na tona sirrinta da take rike dashi. "
Baby ta numfasa ta dubi kwayar idanun Haris
"Ban taba ganin mace mai matukar son mijinta ba kamar Mamma. Duk da wannan wahalar da take sha wajen Abba bai sanya ta tsaneshi ba. Kullum cikin fatan su dawo daidai takeyi."
"Haka muka koma muka barta,Abba kuwa har mukayi kwana uku baisan ba tare da Mamma muka dawo ba. Kwananmu uku da dawowa kuma yabar garin zuwa Minna don yin wani aiki daya shafi likitanci. Wannan abu ya konamana rai. Kullum sai munyi waya da Mamma. Har na soma damuwa,nayi danasanin zamanta a gida. Kulu ita zatayi ta rarrashina da ban baki. Ita ta zame mana madadin Mamma. Ita ke mana girki da komai na gyare gyare. Dattijuwa ce sosai da zatakai shekaru arba'in. Yaya abdullah yafini kewar Mamma,saboda tsananin shakuwar da yayi da ita. Don kuwa Mamma alokacin data haifi Abdullah ta dauki son duniya ta doramishi musamman ma da taga ta shafe shekaru uku bata haihu ba saita dauka shi kadai ne rabonta. Sau da yawa sai su kashe su binne ina can ina harkata bansan sunayi ba. Wataran ma saidai ina gefe ina assignment na jiyo dariyarsu.
Ranar wata asabar ina zaune cikin garden dinmu ina game da wayata da Mamma ta siyamin. Allah Ya yini mace mai son game a rayuwa hakanan ban fiyeson kaya masu nauyi ba gaskiya. Lokacinma sanye nake da riga da wando marasa nauyi 'yan kanti. Shekaruna sha uku alokacin,kaga kenan ban zama wata cikakkiyar budurwa ta azo a gani ba. Hankalina gaba daya ya raja'a akan wayata,banyi zato ba naji hannu yana shafani. A firgice na wurgar da wayar ina mikewa zaune daga kwanciyar da nayi akan lilon. Tsananin tsoro da mamaki da kuma rawar jikin da nakeyi yasa na kasa cewa komai. Ba kowa bane illa Usman. Kallo daya ya tabbatarmin a bugensa yake. Yana dariya irin ta maye yace
"Hey you girl,mene kike ja da baya? Ke kanwa kike gareni menene ciki?"
Ya fada yana k'ara nufoni,na suri wayata na arce a guje. Ina zuwa falo nayi arba da yaya abdullah wanda ke shirin fita hannunsa rike da ruwan swan. Na rukunkumeshi ina rawar jiki.
Ya dagoni a tsorace yana fiddo ido
"Ke! Menene haka?"
Na hadiyi miyau ban iya cewa komai ba. Ya dakamin tsawa
"Bakyajina?! Me akayi maki?"
Na tsorata da yanayinsa duk da kankantar shekarun yaya abdullah,wato sha shida. Babba ne a kaina. Ga mamakina sai na kasa fada mishi na girgiza kai
"Kadangare ya biyoni."
Tsaki yaja kafin ya tureni yana fadin
"Banza kawai."
Ya ficewarsa. Ranar haka na yini sukuku,bansan usman cikakken dan iska bane sai ranar. Duk wani kuzari bani dashi,abunda nakeji a bakin kawayena suke cewa iskancine sai ma'aurata keyi yau gashi a kaina. Haka dai na dunga kiyayewa ban kara bari munyi arba da usman ba balle Nura.
Kwanan Abba uku muka ganshi ya dawo. Washegari da safe ya fice bamusan inda ya nufa ba.
Cikin ikon Allah washegarin ranar da muka ganshi yayi fitar safe,sai ga Mamma ta dawo da Gwaggo Hajara da tayo mata rakiya. Ihun murna muka hau yi da tsalle. Mamma ita kanta farin cikin ganinmu takeyi.
Babu laifi Abba ya chanja don har girki Mamma tana karb'a. Wannan ya dagawa Raliya hankali sosai,ashe sanyin da tayi mana a baya ganin Abba yabar shiga harkarmu ne. Abba yanzu da taga har girki ya bawa Mamma sai hankalinta ya tashi. Nan kuma ta dawo da masifarta. Sai ta kintaci Mamma ta shirya fita da mota, zata hana mukulli tace motocin gidan babu mai,hakanan Mamma ke hakura ta koma don sau daya ta taba zuciya ta hau mashin saboda alokacin ba'asan da adaidaita ba, Abba ya ganta. Ranar saura kiris ya saketa Allah Ya tak'aita.
*******
Bayan shekara biyar,inada shekaru sha bakwai a duniya. Na zama cikakkiyar budurwa kuma alhamdulillah sai Allah Ya bani wani irin farin jini. Maza da mata a makarantarmu suna kaunata. A gida kuwa,har doka Mamma ta sanyamin akan babu ruwana da shiga sashen matan Nura da Usman,don kuwa anan suka tare kowannensu da matarsa su dinma matan irin gogaggun nan ne kamarsu. Hakanan ta sanyamin dokar fita da hijabi ko kuma sanya abayoyi tunda ta kula mayyar kananun kaya ce ni, duka duka manyan kayana irinsu atamfa da leshi yawanci sai anko ko kuma na dinka don sha'awa na ajiye. Yaya abdullah baya garin gaba daya, a can k'asar waje yake karatunsa,shekararsa uku acan ya zamana baifi mishi sauran shekara daya da rabi ba ya takarkare karatunsa fannin bussiness. Twins suma sun girma,fad'a tsakanina da Hamida na cacar baki wataran ma har da duka babu abunda aka fasa. Dama dama Hindu ce bana tunanin zata dauki d'abi'un uwarta duk ta fisu hakuri sannan ta kasance marar hayaniya. A makaranta ina ganin sharholiyar da Hamida keyi dukkan abunda ya hada na raye raye da kula kulan maza ba wanda bata cusa kanta ciki. Hamid ne dai ya wuce boarding school wannan ne bazance ga halinshi ba."
Baby ta gyara zama tana yamutsa fuska saboda gajiyar da hannunta ya soma yi
"Sorry."
Haris ya furta cike da kulawa,abunda bai taba yi bane. Hakan ya sanyata murmusawa shima ya mayarda martani yana mai basarwa ta hanyar shafa sumarsa.
Ta cije lebbanta na kasa mai nuni da abunda zata fada akwai ciwo(lol)
"A wannan lokacin ne,Allah Ya kawo karshen zaman Mamma da Abba,Yaya abdullah yana can wata duniya baisan abunda ke wakana ba...."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(28)
Alokacin ina jss1,yayana ss1. Twins kuwa suna primary 4,Hindu kuma 3. Na soma hankali da fahimtar abubuwa,a fannin islamiyya ma tuni Yaya abdullah yayi haddar Al-kur'ani,sai hadisai da sauran litattafai da akeyi mishi. Nikam sauka nakeyi don ko haddar ban soma ba alokacin. Twins ne abinsu sai a hankali,don uwar tasu cikin yawon biki da suna da gaisuwar mutuwa take. Koyaushe bata fiye zama gida ba duk fitarta da yaranta take tafiya(note! Ban taba rayuwar kowa ba!). Wannan ya janyo wala wala a karatunsu na addini,malaman har korafi sukeyi don har Abba sun samu sunyi magana dashi ya nuna za'a kiyaye saidai fa bata canza zani ba.
Wataranar juma'a da yamma na dawo daga gidan Waziri inda nakai ziyara ga aminiyata Juwairiyya,misalin karfe biyar da mintuna ne,direba ya faka. Na fito ina duban wasu matasa biyu tare da Hamza anan kusa da motar Hamza suna hira da kyakyata dariya. D'aya gajere ne,bak'i saidai kalar fatar ta haskaku tamkar dai na yan gidan hutu. Bashi da wani kyau na azo a gani yayinda d'ayan kuwa ya kasance dogo yana da d'an haske. Sannan yayi kama matuka da Raliya. Bazasu wuce talatin da wani abu ba,kansu wani dan iskan aski ne na yan duniya. Gashi duk sun matse cikin kananun kaya masu wanduna iyaka gwuiwa. Na dauke kaina kamar ban gansu ba zan shige gida. Tsawar da Hamza ya dakamin ce ta rud'a tunanina,na dubeshi. Jajayen idanunsa ya shiga zaremin,yace naje. Ba musu ta isa jiki yana rawa.
"Don ubanki baki iya gaisar da mutane ba? Ko bakiga Nura da Usman bane? Kina daukarsu bare ne? Toh don ubanki sun fiki matsayi a gidan nan."
Jin abunda yace na zumburo baki,a ganina rainin hankali ne ace wani can ya fika alhalin gidan ubanka ne. Naji an kaimin hauri da k'afa a bakin. Nura ne,gajeran ciki. Ya zaromin ido
"Barta Yaya hamza,ashe har wannan lokacin wannan yar iskar yarinyar bata nutsu ba. Tun tana 'yar ficikarta take tsula tsiya a gidan nan. Toh don ubanki tunda muka dawo garin nan keda gyatumar taki zaku magantu. Tashi kibar nan!"
Ya dakamin tsawa,ai da gudu gudu nayi ciki cikin ihun kuka. A falo na zube inata bori,Kulu da Mamma suka fito suna tambayar ko lafiya? Yaya abdullah kuwa bai nan yana tare da abokansa na unguwa suna ball. Na shaida musu abunda ya faru,Mamma taja tsaki
"Allah Ya kyauta."
Daga haka tayi gaba bata ko damu da wankemin jinin dake d'iga daga bakina ba. Kulu ta kamani mukayi bandakina ta wankemin bakin tsaf sannan ta sanyani na chanja kayan kasancewar sun b'aci da jini.
Result din Nura da Usman ba wani kyau sukayi ba,tun dawowarsu ma banda yawo da suka sanya a gaba basu da wani aiki. Ga yan mata da suke yiwa b'arin naira. Bayan bautar kasarsu Raliya ta sanya Abba ya nema musu aikin yi saidai babu wanda akayi dacen samarwa. A karshe tace ya basu jari. Nan ya basu kudade da yawa don suyi sana'a koda kasuwanci ne. Saidai ba wanda ya yunk'ura,karshe ma mota suka saya kowanne da tasa. Rayuwarsu ta baya sai abunda ya k'aru,neman mata kamar me don hatta da shaye shaye sukan d'an tab'a. Mamma tasha gargad'ina akan kar na kuskura koda wasa na dunga shiga sashensu. Baruwana dasu, naji gargadinta sosai duk da inajin haushinsu. A duniya babu wadanda na tsana bayan Abba sai su. Tsakanin Mamma da Abba kuwa,har ta manta rabon da Abba ya zauna sukayi hirarsu cikin nishadi har ma ya nemi shawararta akan wani aiki nasa, ko kuma ya sanar da ita abunda yake niyyar yi ko kuma yayi. Zuwa lokacin ma Mamma bata damuwa,idan da sabo yaci ace ta saba domin kuwa abun gaba yakeyi. Na takaice maka saida ya zamana Abba ko girkin Mamma bayaci,sam Mamma bata da kwana a gidan. Kiyayyarsa gareta tamkar an k'ara ne. Domin hana kawo abinci sashensa yayi,yace tayi zamanta a nata sashen idan yana da bukata ai yasan inda take amma anan ita ya lura bata da aiki sai korafi akan abunda baikai ya kawo ba. Tun ina zuwa sashen Abba da kaina duk da kwab'ar Mamma har nazo na daina domin ko kallo ban isheshi ba. Zafi ya hadewa Mamma,gashi ita ba suruka ba balle takai k'ara don tun Abba yan karami mahaifiyarsa ta rasu. Shi kadai ne a wajen mahaifiyarsa,a hannun mahaifiyar Alhaji Nasir,uwargida a wajen marigayi Waziri Ma'aruf wato mahaifinsu Abba,ya tashi. Itace komai nasa kafin itama ciwon sugar yayi ajalinta. Mahaifiyar Gwaggo sarai ita kadaice tsohuwar data rage a matan Waziri,sai yaransa su goma sha biyar cif. 'Ya'ya goman duk na uwargidan ne,sai Abba cikon na sha daya sannan ya yan amaryar waziri,uwar Gwaggo sarai,itace mai yara hudu.
Kwarai dukkansu matan sun watsar da Mamma,hatta da Gwaggo Sarai mai kawo mata tsegumin auren da Abba zaiyi a farko. Matar Waziri mai ci a yanzu,Alhaji Nasir,Hajiya Hajara. Itace suke mutunci sosai da Mamma don shekarunta bai wuce na Mamma ba. Itace kuma k'arama ta uku a matansa. Ita ta kasance mahaifiyar Juwairiyya.
Wannan kenan!!!
Mamma ta rame ta rasa meke mata dadi,Abdullah shine mai rarrashinta. Akwai sadda naji yana bata shawarar kodai zataje Kazaure ta sanarwa Malam? Don lokacin bai zama limamin juma'a ba,marigayi Malam Abubakar ne Limamin. Mamma tak'i. Yaya abdullah shine abokin shawararta wasu lokutan yanda ta suka shak'u ko ni da nake mace ba muyi wannan shak'uwar ba.
Rayuwa na tafiya da dadi babu dadi. Saida muka samu hutun watanni uku na makarantar boko,ina shirin shiga jss2 Yaya abdullah kuwa zai shiga Ss2,mukaje Kazaure ziyaran kakannina. Yan uwan mamma babu wanda bai firgita da ganin yanda ta koma ba. Sukayita tambaya tana cewa babu komai. Har Malam ma haka ta fada mishi. A karshe ta sanyamu a d'aki ni da abdullah ta k'ara kwab'armu akan kada mu sake mu gayamusu halin da take ciki. Ai kuwa bayan ta fita ziyarar yar uwarta. Naje na samu Malam,ina kuka na zayyane mishi komai na yanda Mamma ke rayuwa a gidan nan don har yan aikin Raliya sun fita muhimmanci a wajen Abba. Ga rashin kunya da yaran Raliya sukeyi mata,babu mai ganin girmanta musamman ma manyan. Malam ya fusata ainun,yace nabar kukan bari ta dawo. Ai kuwa Mamma tana dawowa nabar gidan da zummar lekawa gidan kanwar Mamma,Gwaggo Nusaiba......
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(30)
"Maganar da nakeyi maka har ila yau,bansan takamaiman silar rabuwar iyayena. Abunda zan iya tunawa shine. Adaidai wannan lokacin da sakin ke daf da faruwa,Mamma ta shiga wani irin yanayi na yawan tunani da kuka. Nasha kamata a daki tana kuka,tambayar duniya nayi mata tak'i sanar dani. Ga Abba ma bai shiga sha'aninta,na fahimci ran girkinta saidai tayi mishi abinci takai ta juyo bata zuwa inda yake. Ta rame gaba daya, zuwa lokacin nayi hankali nasan menene ya kamata hakan yasa ban sanarwa Yaya abdullah ba duk kuwa da cewa muna yawan chatting dashi yayita bani labarin wata budurwarsa da yake fatan aurarta,Hidaya. Itama 'yar Kano ce karatu ya kaita London. Na gaji da ganin halin da Mamma ke ciki wannan yasa na tambayi kulu ko tana da masaniya saidai ta tabbatar min babu abunda Mamma ta gayamata,itama ta tambayeta amma ta nuna mata bakomai.
Wataranar alhamis na dawo daga makaranta ina mai murnar kammala paper dina na jarabawar karshe da mukeyi. Karab mukayi ido hudu da Yaya Usman tsaye a bakin motarsa sanye da kananun kaya tana shirin fita. Naja tsaki ganin yanda yake sakar mini murmushi,a fili nayi magana
"An girma ba'asan an girma ba."
"Tasleem."
Sunana daya kira yasa na tsaya don kuwa bai taba ambaton sunana ba saidai yace "ke."
"Zo nan."
Na nufi inda yake cikin tsabar takaici domin a rayuwa na tsani 'ya'yan Raliya gaba dayansu musamman ma wadannan agololin da suke mana karfin hali a gidan uba. Na isa na tsaya kerere gami da hard'e hannuwana a kirji fuska ba walwala don a yanzu sam bana tsoron ta kwab'e mana dasu. Inajin zan iya karawa da duk shegen da zai hanani taka rawata da tsalle a gidan mahaifina.
"Gani."
Na dauka zanji babu dadi sai ga mamakina cikin maganarsa mai sauri yace
"Inye,au yanzu an daina ganin girmana ko? Ba laifinki bane,kin isa ne don a yanzu kin zama biggurl."
Furucinsa yasa na dubeshi,ya dagamin gira hakora a washe, na tsuke baki gabana yana faduwa nadai daure nace
"Ina sauri ne,nagaji."
"Kada ki damu,nima saurin nakeyi zan fita. Tambayar da zanyi maki daman meyasa bakya shiga sashena? Kodai baki daukeni yayanki ba? Kin daukeni bare?"
Na kauda kaina don a zahiri ban fiyeson kallo ba. Banayi banso kuma a tsawaita yimin,saidai yanda na kula Usman mayen kallo ne. Muddin waje da mata baya saurarawa,yan matan dake gidan Waziri nasha jinsu suna korafin yawan kallonsa da son kulasu da yakeyi acewarsu haushin zuwansa sukeji saidai kuma abokin yayansu ne,Bukhari ba yanda zasuyi.
"Daman ai ba wani zumuncin mukeyi a tsakaninmu ba ballantana har na dunga ziyartar gidajenku. Babu laifi idan mun hadu sai adunga gaisawa."
Yayi mamakin maganata,har yayi dariya. Nikam wani lokacin ma mamaki yake bani,mutum mai zuciya da ashariya shine yake bina har haka?
"Gaskiyane Tasleem,komai ya wuce. Ke dince akwai rashin kunya sadda kina da kuruciya,amma yanzu tunda kin nutsu ai shikenan."
Na d'an tabe baki kafin naja kafata nayi gaba
"Ban sallameki bafa."
Ko kallonsa ban k'arayi ba domin na tsani rainin hankali. Ya tsayar dani da surutan banza. Da sallama na shiga saidai babu kowa a falon,na karasa dakin Mamma,kafin nakai na tsaya cak saboda maganar Mamma da naji cikin kuka.
"Kulu don Allah ki rikemin sirrina,nayi iyakar kokarin ganin na gyara zamantakewata da Abban Abdullah,saidai tamkar tunzurashi nakeyi. Bansan takamaiman abunda nayi mishi ba ya tsaneni. Kada ki sanarwa Tasleem komai dangane da abunda na fadamaki. Ayau zan koma garinmu,na bar maki amanar yarana Kulu. Bada son raina ba na rabu dasu. Haka Allah Ya kaddaro zamana da Abbansu bazaije ko'ina ba. Bari na tafi domin banason Tasleem ta iskeni....."
Shigar da nayi ba a hayyaci bane yasa sukayi turus gaba daya. Mamma ce rike da akwatin kaya sai jakar hannu,sanye cikin hijabi fuskarta tayi jazur ga hawayen da take fitarwa daya yana bin wani. A durkushe kuma Kulu ce ke kuka sosai.
Tsananin tashin hankali yasa naji kafafuwana sun kasa rikeni,kawai sai na zube a k'asa kafin nasa tafukan hannuwana na rufe idanuna ina kuka sosai. Mamma ta karaso ta ja hannuna na fisge naja baya ina kuka
"Ki rabu dani nace! Ba kin riga kin shirya guduwa ki barmu a wannan bak'in gidan ba? Kin shirya barinmu wajen azzalumin uban.."
Ta toshemin bakina da sauri
"Kina da hankali kuwa? Kada ki k'ara zaginsa,kada ki kara zagarmin...."
Na fisge hannunta
"Wa?! Waye naki? Mamma ki farka ya rigaya ya sakeki! Baya kaunarmu tunda bayason mahaifiyarmu. Shekaru nawa yana nunamana kiyayya? Babu wata shakuwa tsakaninmu dashi a matsayinsa na ubanmu,tunda nake da wayona ban taba ganin Abba ya tako zuwa sashenki domin duba lafiyarki daga kowace irin cuta data sameki ba! Mamma wallahi bazaki tafi ki barni ba! Nima bana sonsa bana kaunarsa! I hate me so..."
Marin data sakarmin ya dakatar dani, saidai ban fasa fad'i ba na mike naja baya ina kuka da karfin murya nace
"Saidai ki kasheni Mamma! Amma na tsani Abba! Na tsani Raliya! Har abada bazan taba son makiyin uwata ba kowanene!"
Na fice a guje,kayana na soma hadawa a akwati,kulu ta shigo ta sameni. Duk yanda taso ta hanani amma nak'i hanuwa. Na fito saidai Mamma tuni ta fice. Banyi wata wata ba nima na mara mata baya. Kulu na bina tana kwalamin kira saidai ko waigowa banyi ba.
*****
Ga wanda baisani ba,sai yace tare muka isa Kazaure da Mamma domin shigarta da mintuna nima na shigo. Malam na soma cin karo dashi yayi niyyar tafiya masallaci gabatar da sallar la'asar.
"A'a,matata daman tare kuke?"
Kawai saina sanya kuka,wannan ya fiddo mutan gidan. Ba karamin mamaki nagani akan fuskar Mamma ba,saidai batace komai ba ta juya ta koma ciki. Malam ya rikeni
"Lafiya kuwa? Meke faruwa ne?"
Cikin kuka na sanar dashi sakin da Abba ya yiwa Mamma. Matan suka hau salallami,Malam banda innalillahi wa inna ilaihir raaji'un babu abunda yake maimaitawa. Kafin ya numfasa yace
"Shiga kiyi sallah Tasleem,bari har na dawo daga masallaci."
Daga haka naja akwatina,ban yarda na shiga dakinsu Mamma ba,sai nayi zamana dakin Gwaggo Fatsima,matar kanin Malam, Yunus. A zatona Mamma zata shigo ta rufeni da duka,wanda na riga na kudurta a raina ko kasheni zatayi bazan koma ba saidai ko alamunta banji ba.
Malam sai bayan isha'i ya nemi Mamma. Sun jima suna magana kafin yayi kirana. Nan ya lallabani akan nayi hakuri na koma ga mahaifina na tubure mishi karshe na sanya kuka ina fadin sun tsaneni suma. Jin haka Malam yace Mamma ta barni na zauna. Mamma zatayi magana ya hanata yace na tashi na tafi. Bansan me suka tattauna ba,nidai burina ya cika tunda Mamma bata kara matsamin ba akan batun kome na daga ranar.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(31)
Kwana uku da zuwana Kazaure,Mamma ta sakarmini sosai. Inajin dadin kauyen nan domin duk sadda naje kowa haba haba yakeyi dani. Sau da yawa Malam ya kanyi murmushi idan yaga nayi wani abun musamman yanayin maganata da yasha fadamin yana bashi mamaki,yakan ce ni nayi gadon waziri kakana bawai Abbana ba. Bashi kadai bama,hatta kawayena da wasu cikin yan uwana sunsha gayamin na fiye jin kaina da kasaita,wanda ya jima tare dani ne zai gane nature na ne haka bawai girman kai ko wulakanci bane kamar yanda wasu ke dauka suke kuma jin haushina.
Saida na cika sati daya cif a kazaure sannan saiga direbanmu. Nayi mamakin zuwansa,yayi sallama da Malam ya gayamishi cewar Abba ne yace yazo ya tafi dani. Malam ransa bai baci ba domin zuwa yanzu ya dawo daga rakiyar Abba. Ya lura abun nashi sai addu'a. Ya shigo yace na shirya na tafi. Ai kuwa na fasa ihun kuka,yayita ban baki shi da inna,kafin Mamma ta hadamin jakata ta jawoni daki tana rarrashi.
"Na sanki,yarinya kike mai basira da kula dakai. Kada ki sake ki bari shaidan yayi maki hud'uba Tasleem. Kibi matar ubanki sau da k'afa,kiyi biyayya ga mahaifinki kada ki sanya damuwar komai a ranki. Allah Yana tare dake."
Wadannan shine kalaman karshe da Mamma ta gayamin,wanda bani taba mancewa. Haka na share hawayena mukayi sallama da kowa nabi direbanmu muka tafi raina cike da bakin cikin komawa gidan mutumin dana fi tsana a rayuwata.
Babban tashin hankali dana tarar bai wuce ganin babu komai na Mamma a sashenta ba. Toh wai yaushe akayi kwasar kayanta ina Kazauren amma bansamu labari ba. Hankalina ya tashi,babu komai sai ragowar kayana dana Yaya abdullah a kwabobinmu. Na hau kwalawa kulu kira saidai tsit,na fito na tambayi Direba ina kulu. Kafin ya bani amsa sai ga Abba.
"Ta koma kauyensu ai."
Cewar direba,nikuwa kallon Abba nakeyi cike da tsanarsa. Ya kalleni fuskarsa a daure,kafin yace
"Ki sameni a falona."
Daga haka ya wuce,kamar bazanje ba sai kuma na nufi falon saboda tunano nasihar da Mamma tayimin. Yana zaune,daga shi sai matarsa dake b'antalar tuffa a nishadance tana ci. Na durkusa gefe bance uffan ba.
"Ke." (Sai ince da wayona shine sunan da Abba ke kirana kamar bai yankamin rago da Tasleem ba.)
Banko dubeshi ba saboda gudun kada kallon da zan mishi ya zamana na samun zunubi don kallone na tsana.
"Ki tattaro kayanki ki dawo sashen maminki da zama. Bazai yiwu abarki ke d'aya ba kuma kina mace a wancan bangaren. Don haka kizo ku hadu da yanuwanki don bana shakka akan kyakkyawar tarbiyya irinta Hajiya Raliya. Na tabbatar bazanyi kaico ba."
Raliya tasa dariya,wallahi Haris bansan sadda na jefeta da mugun kallo ba,banyi aune ba ta jefomin ragowar tuffan da take ci tana zaromin idonta masu razana matsoraci.
"Yar iskar yarinya ni sa'ar kice da kikeyimin wannan kallon?"
Abba ya dubeta da mamaki,sai naga ta bagarar tana murmushi
"Bakaga hararar da tayimin bane? Lallai sai nayi da gaske wajen gyarawa Tasleem tarbiyya domin na kula tayi nisan da batajin kira a gurbataccen tarbiyyar da uwarta ta bata."
Zuciya ta kaini bango,me suke nufi? Kenan suna tantamar tarbiyyar da Mamma tayimin? Muryar Abba ta katseni
"Tashi kije kiyi abunda nace. Hajiya Raliya bana shakkarki,na gaskata cewar zaki rike amanar dana damk'a maki. Zaki kula da.."
"Wai Doctor ya kake wasu maganganu ne? Yarinyar nan fa ba 'yar gwal bace. Haihuwata nawa,yara nawa kuma na raina? Yanzu ya kake zargin bazan iya kula da 'yar tsakon 'diyarka ba?"
Abba yayi murmushi,kafin naji me zaice nayi wuf na mike na fita saboda nagaji da ganinsu. Ji nakeyi da ace kisa halal ne ni zan zama ajalinsu."
Haris ya katseta cike da mamaki
"Wace irin tsana kika yiwa mahaifinki haka ke kuwa?"
Baby tayi murmushin takaici
"Bazai misaltu ba Haris."
"Bazai misaltu ba?!"
Ya nanata a ransa,baby ta share zancen ta cigaba
"Na dawo sashen Raliya,dakinsu Hamidah. Saidai na gwammace inama ban dawo Kano ba. Aikin sashenta tsaf ni nakeyi,ta sallami 'yar aikinta daya,dayar kuwa tace iyakarta kicin da baranda. Amma komai ni nakeyi. Bana k'in yi mata aiki,saidai idan ina aikin kallo daya zakayimin ka gane rashin sabo. Nan da nan nake gajiya. Abun kona ran bai wuce tarewar dasu Nura da Usman da kuma matansu,Bilkisu da Meena sukeyi ba. Kodayaushe suna nan suna kallo da hira tare dasu Hamida da Raliya tamkar zasu fasa falon. Ni ce zanyita zirga zirgar kaiwa da komowa wajen kawo musu abinci da abin sha. Bilkisu ce mai yaro daya,Junaid. Ya zamana ni na zama yar raino matukar tana sashen. Cire mishi pampers,goyashi,bashi ceralac da sauran ayyuka masu cimin rai. Ga wannan shegen kallon dana tsana a wajen Usman,duk sadda muka hada ido sai ya hau yimin murmushi yana kashemin ido,harararsa nakeyi alokacin saidai wai an tsikari kakkausa ko a jikinsa. Hindatu kadai ke tausayamin.
Bana kwanciya bacci saina kammala ayyukana. Abu daya naki yarda da gyarawa,dakin kwananmu,rantsuwa na yiwa Raliya a gabanta akan cewar bazan gyara ba tunda nikam shimfidata,Kafet ne. Sune masu kwanan gadon,bandaki kuma duk sadda zanyi amfani dashi zan gyara idan ta kama. Zata mareni naja baya nace wallahi ta mareni saina gayawa Abba. Nasan ba tsorata tayi ba,saidai bansan dalilinta nayin kwafa ta fice ta kyaleni ba. Hamida tayi wuf ta taso zatamin fitsara,ta juyo ta daka mata tsawa. Wai ita saita mareni din taga abunda zanyi,ganin uwarta ta hanata nayi murmushi nace "Kinci sa'a domin wallahi sai kin gane kurenki muddin kika tab'a jikina."
Jin haka ta harzuka ta daga hannu zata mareni,Raliya ta daka mata tsawa,ni kuwa na rike hannun na murdeshi ta fasa k'ara. Raliya ta iso ta hankadani ta janye Hamida sukayi gaba. Na rasa dalilinta nak'in daukar mataki akan hakan,saidai gaba mai tsanani ta shiga tsakanina da Hamida babu maganar dake had'ani da ita.
Ranar da zamuyi Graduation kuwa,ban nemi komai daga Abba ba hakanan ban gayyaci kowa daga bangarena ba. Yaya abdullah kadai na shaidawa ta waya, duk da har lokacin baisan Mamma bata gidan ba. Ya tayani murna yace inama yana nan dashi za'ayi. Yayimin alkawarin tahomin da kyauta ta musamman idan zaizo. Murmushi kawai nayi. Sauran kudadena na hada na biya komai da makaranta ta bukata. Ranar kuwa da sassafe na shirya,Hamida sunsan da maganar saidai basu cewa kowa uffan ba,hindatu ma ta shirya cikin uniform kamar yanda dokar makarantar tace dalibanta suyi a ranar. Ta dubeni"Zaki rigamu tafiya ko Tasleem?" Murmushi nayi mata na amsa da eh. Daga haka na dauki yar karamar handbag dana zuba kayan amfanina na fito sanye da rigar T-shirt na school da jeans na gida. Mukayi arba da Raliya,ta daure fuska "Ke kuma ina zaki? Kodayake wannan ba matsalata bace bazan hanaki yawon banzanki,aikina fa? Wa zaiyimin? Kada ki sake kibar gidan nan batare da kinyisu ba." Daga haka tayi dakinta,tsaki naja bana tsoron dukanta balle na Hamza,yau ranata ce babu wanda ya isa ya hanani zuwa makaranta. Ina waige waigen neman direba naji hon,ina dubawa naga Usman zaune a motarsa yana dagomin hannu yana murmushi. "Dan iska." Na fada a fili na kauda kaina.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(32)
Kai tsaye wajen Baba Maigadi na nufa. Na tambayeshi ko direba yazo saidai ya sanar dani cewar matarsa ke nakuda yaje kaita asibiti ba lallai ne ya dawo nan kusa ba. Bakin ciki ya turnukeni,da ace na iya mota da duk hakan bata faru ba,gashi kuma koda yazo dole ne sai na amso mishi mukulli wajen Raliya domin shaf ina manta cewar mukullayen motar gidan a hannunta yake. Daidai nan Usman ya iso acikin motarsa,baba Maigadi ya tafi don budemishi gate.
"Zaki makara fa my sister,zo ki hau na saukeki."
Kamar nace bazan hau ba,saidai tunawa da nayi Abba kansa baya gari ballantana nasa ran dakewa zuciyata na amso kudin mota yasa banyi musu ba na shiga don kuwa bani da ko ficika. Ai daman kudin ubanmu ne suke takama dashi,babu laifi don alokacin Abba dayake am shanyeshi a rubutu ya k'ara bude musu shaguna kowanne da nashi a kantin kwari suna d'an maida hankali. Na shiga gidan gaba na zauna fuska a daure. Bai damu Usman ba ko kadan,sai bayan mun soma tafiya naji yace"Ba gaisuwa ko?"
Ni wallahi mamaki ma yake bani har lokacin ganin yanda yake yimim sanyi sanyi a yanzu. Banda niyyar gaisheshi,na dauke kaina ma. Yayi dariya"Ke kam don kinsan kin hadu shiyasa kike yiwa mutane yanga Tasleem. Hakane dalilin dayasa kike wulakanta masu zuwa gidan nan da sunan sunzo zance wajenki ko?"
Na watsa mishi harara,ko a jikinsa na kauda kaina bance uffan ba.
"Tasleem kina da kyau sosai kamar mominki ko ince kinma fita. Gashi Allah Yayi maki baiwar diri ko ta ina ke macece. Dole ki dunga yiwa maza yanga."
Na dauki surutan Usman a matsayin wofi,banko kara dubansa. Har muka iso yana zazzaga shirmensa don shirme na dauki zantukansa. Na soma hango take takensa,akwai abunda yake nufi a kaina saidai ko kusa ban nuna alamar na fahimci komai ba. Muna isowa na yunkura zan bude kofar ya dakatar dani ta hanyar cewa na tsaya. Na dakata,kudi ya mikomin har dubu uku ba musu na karb'e ai kudin na ubana ne. Ko godiya banyi ba na fice.
Anan muka shirya,sannan muka nufi inda ake taron,Afficent. Waje ya cika makil da iyayen yara da sauran yan makaranta. Tausayin kaina ya kamani sanin cewa bani da wanda zaizo mini cikin yan uwana gashi ko abun rabo banyiba. Haka na kutsa na zauna,saidai a ranar nayi hotuna da kawayena,Munnira da Jamila, da yan ajinmu maza da mata. Saida akayi kirana domin amsar certificate na mike a nutse naje. Nayi mamakin ganin wanda ban taba zato ba yazo da niyyar daukata a hoto. Yaya Musty(dominka,yaya mustyna..love u forever..miss you:ur bloodsis..rufaida) ne,d'an gidan Gwaggo Hafsatu yayar Mamma dake Kazaure. Na saki fuska sosai,ina karba na nufeshi bakina a washe
"Yaya mustyna kai dawa kuke tafe? Ya akayi kukasan da wannan ranar?"
Ya harareni
"Bayan da kika k'i kiranmu a waya ki sanar damu sai Abdullah dake a wata k'asar ne zai gayamana?"
Nayi dariya a shagwabance nace
"Afuwan yayana,yanzu kai da waye kuke tafe?"
Yana dariya yaja hannuna yana fadin
"Muje ki ganewa idonki."
Haka mukayita kutsawa taron jama'a bai tsaidani gaban kowa ba sai Mamma da gwaggo Hajara. Ihun murna na saki ban damu da wadanda suka kalloni ba. Na rukunkume Mamma kafin na saketa na rungumi Gwaggo Hajara. Bansan ya akayi ba kawai sai na fashe da kuka sosai,har wani malamin Chemistry dinmu sarkin shishshigi ya matso wai bai taba ganin kukan Headgirl ba(kasancewar mukamin dana rike kenan a makaranta)sai a yau. Su mamma sukayi dariya,nikam na harareshi dariya kawai yayi ya kara gaba bayan yace"Madam,your daughter is one of my best students,very talented." Mamma murmushi tayi kawai. Kirana da aka karayi ne naje nayi speech a matsayina na headgirl na mike na tashi bayan na damkawa Mamma certificate dina. Tiryan tiryan nayi na gama na yiwa manyan bak'i fatan komawa gida lafiya sannan na bada shawara ga juniors dinmu nan aka hau tafi raf raf akarshe na koma gasu Mamma mukayi ta daukar hotuna. Munnira da Jamila suma suka iso suka gaida Mamma.
Ina zaune kawai sai naga yaya musty ya shigo da kwalaye,nayi mamakin ganin jakunkunan rabo dauke da memo fa handfan a ciki. Na kalleshi idona taf da kwalla,yace
"Zaki soma kuma dai? Muddin kikayi kuka zan fasa baki."
Gwaggo Hajara tayi dariya
"Wannan hukunci yayi."
Nayi azamar share fuskata
"Kaga nabar kuka yayana."
Mukayi dariya,ashe tun sadda na sanarwa Yaya abdullah ya gayamusu. Shine Mamma ta bayar ayimin memo,anan shima Malam ya k'ara mata kud'i. Don farin ciki na rasa inda zansa raina.
"Hamida,hindatu."
Hamida ta kalleta ta tabe baki tayi gaba,hindatu ce ta tako ta gaishesu. Mamma ta dafa kanta tana murmushi bayan sun amsa. "Ina maminku? Ku gaisheta."
Kusan lokaci daya muka dubi Mamma nida gwaggo Hajara,gwaggo Hajara harararta tayi. Nikam mamakin rashin zuciya irin na Mamma nakeyi,bata fushi. Da hindatu kadai na dauki hotuna,a karshe yaya musty ya amshi camera dita da zummar zaisa a wankemin hotunan harda na tasa wayar. Naji dadi sosai.
Har kusan azahar muna tare kafin a watse suma su soma shirin komawa Kazaure. Anan ne idona ya raina fata,gwaggo Hajara ta dafani
"Haba 'yata,menene abun kukan? Kiyi hakuri,tunda kunyi hutu saiki tambayi Abbanki idan ya amince sai kizo mana koda sati kiyi kinji? Kukanki sai ya karyar da zuciyoyinmu."
Suka lallabani suka tafi.
A ranar kuwa nasha zagi wajen Raliya dana koma,saidai batayi gigin taba lafiyata ba. Aikin da acewarta na gudarwa,dole na yishi. A banza kam tunda na samu ranar nan ta tafimin cikin matsanancin farin ciki. Ban kwanta ba sai wajen goman dare. Anan ma banyi baccin ba don hira nayi tayi da hindatu akan makarantarmu kafin bacci ya suremu........!
Tun daga wannan ranar kuma sai na soma
sakewa Usman kadan kadan,nakan gaisheshi
hakanan nakan je dukkan wani aiken da zaiyimin
zuwa gidansa ko kicin din Raliya da sauransu.
Ban dai sakarmishi sosai ba,amma babu wannan
rainin sosai. Har kuwa zuwa lokacin bai rabu da
fita yawon dare ba. Nasha ganin Meena tazo
wajen Raliya tana bala'i akan ita ta soma gajiya
da bin mata irin na Usman,mutum tamkar wanda
aka yiwa asiri. Raliya saidai ta bata hakuri don
babu laifi iyayen meena akwai naira hakanan
takan lasawa Raliya sosai domin ita din macece
wacce bata godiya ga Allah. Duk da irin arzikin da
ta hau kai tayi zaune na Abba,ga kuma business
da takeyi,hakan bai hanata hangen na wasu ba.
Bayan watanni uku,lokacin Mamma ta kusa
shekara a gidansu,kawai na tsinci wayar Yaya
musty yana yimin albishir cewar an daurawa
Mammana aure da wani almajirin Malam. Har
tsalle nayi don murna. Yara da yawa sukanyi
bakin ciki idan uwarsu zatayi wani auren alhalin
ubansu na raye, kai koda ace baya raye akwai
yaran dake taya ubansu kishi amma nikam
baruwana ko a jikina. Daga dariya kuma sai na
fashe da kuka. Ina cewa shine ko a gayamin nazo
da wuri? Dariya yayi yace kada na damu anan
Kazaure Mamma zata zauna duk sanda naga
dama na tambayi Abba ya barni toh nazo na
ganta. Naji dadi kwarai ya kara tambayata game
da Yaya abdullah nace mishi sauran mishi
watanni uku kawai ya dawo. Daga haka mukayi
sallama tare da alkawarin idan yaje gidan zai
kirani mu gaisa da Mamma.
Ai kuwa ko awa biyu ba'ayi ba yayi kirana,na hau
bud'a karshe na saki dariya. Nayi mamaki dana ji
muryar Mamma a sanyaye har na tambayeta ko
bata farinciki da auren nan? Bata bani amsa ba
ta share da tambayar lafiyata. Nace
alhamdulillah,tace zan cigaba da karatune? Na
tabe baki "Bansani ba Mamma." "Kamar ya baki
sani ba Tasleem? Keda mahaifinki? Kije kiyi mishi
magana tun lokaci bai kure maki ba."
Na amsa da toh saidai kuma abunda Mamma
batasani ba shine,idan har sai naje ga Abba na
gwammace nayita zama haka a gidan. Haka
mukayi sallama da ita.
Bayan kwana biyu,Meena matar Yaya Usman ta
haife tsohon cikinta ta samu d'iya mace. Murna a
wajen yan gidan ba'a magana. Nikam ko ajikina
daman ba wani mutuncinsu nake gani ba.
*******
Bayan kwana uku da haihuwar meena,misalin
biyar na yamma,ina zaune a bakin firij na Raliya
ina gogewa,ita kuwa da yaranta suna falon suna
kallon wasan Hausa saidai ko inda suke bana
kalla ballantana film din da suke kallo ya dauki
hankalina don tun fil'azal fina finan hausa ba
burgeni sukeyi ba barni da da kallon Indian series
da Korea anan kam ko makiyina ke kallo zan saci
kallo. Sallamar Usman ta katsesu,Hamid bai
amsa ba saima ya mike ya fice saboda a yanzu
haushinsa yakeji akaina. Bayan su hamida sun
gaisheshi ya dubi Raliya.
"Wa kike ganin ya dace ta zauna wajen Meena
ne?"
Yayi maganar tamkar da sa'arsa,Raliya bata ko
damu ba ta kyabe baki
"A'a toh,ko Dijangala ai sai ta zauna. Idan kuwa
batason aikinta ga waccan tsiyar saiku kwasa."
Sai lokacin na dubeta kafin na watsawa Usman
mugun kallo wanda na jima banyi mishi irinsa ba.
Murmushi yayi ya dubi Raliya
"A'a dijangala shiririta ne da ita,tunda dai ga
gwaggon meena zata dunga yi musu wanka sai
Tasleem ta dunga gyare gyarem gidan."
Raliya bata musa ba domin duk yanda zan
kuntata a rayuwa shi tafi kauna. Tace
"Hakan ma yayi,ke! Idan kin kammala ki tattaro
kayanki ki koma gidan Usman har sai matarsa ta
gama wanka sannan zaki dawo."
Bance uffan ba don bakin ciki,a matukar fusata ta
kammala aikin na mike na shiga daki. Haka na
tattaro kayan na fito. Hamida mukayi arba da ita
ta tuntsire da dariya gami da yimin gwalo"Haka
zaki k'are." Kamar nace mata wani abu saidai na
fasa nayi gaba,Raliya har lokacin tana falon
banko kalleta ba nayi gaba abina a fusace.
Saida nazo daidai garden na zube anan na fashe
da kuka,wai haka rayuwata zata k'are? Wane irin
uba gareni da bai daukeni komai ba? Ya manta
da ya haifeni ne har ya banzatar dani a gidansa
ya maidani wofi? Ace yan aiki ma sun fini daraja
da kima a gidannan? Na daga kaina nakai duba
da d'an lilon da muka saba wasa da Yayana.
Haka zaiyita cillani yana goyani muna zagaye
garden dinnan muna dariya. Ba zato naji an
dafani ta baya,nayi azamar juyowa ganin Usman
bansan lokacin da naja tsaki ba nayi kokarin
mikewa yayi saurin dawowa ta gabana.
"Haba Tasleem,ashe tsanar da kika yimin har
takai ace kije ki taimakawa matata ki zauna kina
kuka? Duk cikinmu waye mai tausayinki bayan
ni? Haba Tasleem,banji dadi ba wallahi."
Ganin yanayin fuskarsa sai naga kamar ban
kyauta ba,nace
"Ni ba gidanka ko matarka na tsana ba ai,irin
wannan rainin hankalin da akeyimin a gidan
ubana ne na kasa gane dalilinsa. Bansan kuma
me na tsarewa mutane ba."
Na karashe cikin tsiwa,yayi dariya ya kawo hannu
zai dora kan lebbana nayi azamar ja da baya,cikin
tsoron yanayin kallon da yakemin
"Tasleem komai naki abun sha'awa ne wallahi. Ni
bana k'inki,inason ganin kanwata a kusa dani
shine ma dalilin da yasa na nemi alfarmar
zuwanki. Kiyi hakuri inajin dadin yanda kika kware
a gyara muhalli. Meena KAZAMAR GIDA ce,
banason ganin gidan nan da kazanta. Don Allah
kanwata wallahi tana yin arba'in I promise you
zaki komo gida."
Bance komai ba na mike na dauki jakata nayi
gaba yana magana ko juyowa banyi,menene
saukin da nan da can din?
****
Baby ta numfasa,hawayenta ya karu wani yana
bin wani. Haris ya miko mata (handkerchief)
dinsa,tasa hannu ta karb'a saidai bata da niyyar
share hawayen. Ta dubi Haris wanda shima ya
gaji da waigenta ya karkato gaba daya yana
duban fuskarta don jin dadin hirar.
"Haris a wannan zuwan nawa ne gidan Usman
komai na rayuwata ya soma tabarbarewa. Yanda
akayi kuwa shine......."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(33)
Kwana uku da yin candy dinmu,Abba ya dawo
daga tafiya hakanan Hamid shima ya dawo
daga makaranta anyi musu hutu. Zuciya irin
tawa ta hanani tunkarar Abba da zancen zuwa
Kazaure. Sai ince rabona da sanya Abba a ido
tun sadda yayi kirana yayimin batun komawa
sashen Raliya da zama.
Wataranar asabar ina gugar falon Raliya,ina yi
ina wake wakena wanda yana daya daga cikin
abunda ke konawa Raliya rai ganin bana nuna
damuwa a dukkan ayyukan da take sanyani.
Saidai batasan cewar kawai dannewa nakeyi
amma ji nakeyi kamar na shak'ota don bakin
ciki. Hamid ne ya shigo da takalmi ya bi ta inda
na taka zuwa bakin firij,na kalli yanda wajen ya
b'aci da k'asa bance komai ba na k'ara
gogewa,yazo ya kara wuce hannunsa rike da
lemon b'awo yana sha yana yarda kwallayen
nan ma bance uffan ba don na lura tsokanar
fad'a yakeyi. Saida nazo daf da kammalawa ya
kara tahowa zai shige. Ai kuwa na sanya mop
din na hankad'e kafafuwansa tuni ya zube a
wajen,banyi sanya ba na kara dauka na kwala
mishi a goshi. Ihun daya fasa yayi daidai da
shigowar Hamza da Usman da Nura. Tsayawa
nayi ina huci da fada"Wallahi gobe ma ka k'ara
gigin b'atamin aikina sai nayi maka abunda
yafi wannan haka kawai..."
Hannu Hamza ya daga da niyyar kwad'eni ga
mamakina Usman ya rikeshi,bani kadai ba
dukkansu suma sunyi mamaki hatta da Raliya
dasu Hamida da suka fito.
"Kana da hankali kuwa? Sakarmin hannu!"
Usman shima yace"Meyasa kake da son kaine
Hamza?(Kasancewar raini ya shiga tsakaninsu
bama kadan ba) Baka ganin laifin na dan
banzan yaron nan ne da har zakayi gigin marin
Tasleem? Wannan ma ai son kaine."
Ya saki hannunsa,ya dubeni
"Ke wuce ki tafi."
Na dauki mop da robar zan fita,Nura ya
dakamin tsawar data firgitani,ya iso ya janyo
rigata wannan yasa na fadi na zubda ruwan,ba
karamin buguwa k'uguna yayi ba. Kukana ya
tsaya sa'ilin da Usman ya daga hannu ya mari
Nura. Dakin yayi dif,ya cakumi wuyansa
"Wallahi ka kara gangancin taba lafiyarta saika
raina kanka! Metayi maka?!"
Nura ya fisge hannun Usman daga wuyansa
"Nika mara akan wannan yar iskar?"
"An mareka!!"
Nura yayi kwafa ya fice a fusace.
"Hamza bimin bayansa kada ka bari ya dawo
nan." Cewar Raliya sanin halin dabancin Nura
don ba karamin aikinsa bane ya dawo da wuka
ko wani makamin. Hamza ba musu ya fice.
Raliya ta dawo gaban Usman
"Meke yawo a kwakwalwarka?! Akan wannan
yar iskar ka daki kaninka abunda baka tabayi
ba shekara da shekaru sai yanzu da girmanku
da komai?! Me ta baka kaci?!"
Bai saurareta ba ya dawo gabana ya dagani
"Sannu Tasleem,tafi zansa a goge."
"Uban wa zakasa aikin? Wallahi kaji na rantse
maka idan baka fita harkar shegiyar nan ba
ranka zai mummunan baci. Dawo ki gogemin
waje!"
Ta dakamin tsawa,ina hawaye na sunkuya
dakyar zan dauki robar saboda zafin buguwar
da nayi saidai Usman ya rigani ya dauka ya
mikomin.
"Kiyi a hankali."
Raliya ta sanyashi ficewa na lura baiso hakan
ba,haka nayi aikin nan ina mamakin abunda ya
faru.
Tun daga wannan ranar kuma sai na soma
sakewa Usman kadan kadan,nakan gaisheshi
hakanan nakan je dukkan wani aiken da
zaiyimin zuwa gidansa ko kicin din Raliya da
sauransu. Ban dai sakarmishi sosai ba,amma
babu wannan rainin sosai. Har kuwa zuwa
lokacin bai rabu da fita yawon dare ba. Nasha
ganin Meena tazo wajen Raliya tana bala'i
akan ita ta soma gajiya da bin mata irin na
Usman,mutum tamkar wanda aka yiwa asiri.
Raliya saidai ta bata hakuri don babu laifi
iyayen meena akwai naira hakanan takan
lasawa Raliya sosai domin ita din macece
wacce bata godiya ga Allah. Duk da irin arzikin
da ta hau kai tayi zaune na Abba,ga kuma
business da takeyi,hakan bai hanata hangen
na wasu ba.
Bayan watanni uku,lokacin Mamma ta kusa
shekara a gidansu,kawai na tsinci wayar Yaya
musty yana yimin albishir cewar an daurawa
Mammana aure da wani almajirin Malam. Har
tsalle nayi don murna. Yara da yawa sukanyi
bakin ciki idan uwarsu zatayi wani auren
alhalin ubansu na raye, kai koda ace baya raye
akwai yaran dake taya ubansu kishi amma
nikam baruwana ko a jikina. Daga dariya kuma
sai na fashe da kuka. Ina cewa shine ko a
gayamin nazo da wuri? Dariya yayi yace kada
na damu anan Kazaure Mamma zata zauna
duk sanda naga dama na tambayi Abba ya
barni toh nazo na ganta. Naji dadi kwarai ya
kara tambayata game da Yaya abdullah nace
mishi sauran mishi watanni uku kawai ya dawo.
Daga haka mukayi sallama tare da alkawarin
idan yaje gidan zai kirani mu gaisa da Mamma.
Ai kuwa ko awa biyu ba'ayi ba yayi kirana,na
hau bud'a karshe na saki dariya. Nayi mamaki
dana ji muryar Mamma a sanyaye har na
tambayeta ko bata farinciki da auren nan? Bata
bani amsa ba ta share da tambayar lafiyata.
Nace alhamdulillah,tace zan cigaba da
karatune? Na tabe baki "Bansani ba Mamma."
"Kamar ya baki sani ba Tasleem? Keda
mahaifinki? Kije kiyi mishi magana tun lokaci
bai kure maki ba."
Na amsa da toh saidai kuma abunda Mamma
batasani ba shine,idan har sai naje ga Abba na
gwammace nayita zama haka a gidan. Haka
mukayi sallama da ita.
Bayan kwana biyu,Meena matar Yaya Usman
ta haife tsohon cikinta ta samu d'iya mace.
Murna a wajen yan gidan ba'a magana. Nikam
ko ajikina daman ba wani mutuncinsu nake
gani ba.
*******
Bayan kwana uku da haihuwar meena,misalin
biyar na yamma,ina zaune a bakin firij na
Raliya ina gogewa,ita kuwa da yaranta suna
falon suna kallon wasan Hausa saidai ko inda
suke bana kalla ballantana film din da suke
kallo ya dauki hankalina don tun fil'azal fina
finan hausa ba burgeni sukeyi ba barni da da
kallon Indian series da Korea anan kam ko
makiyina ke kallo zan saci kallo. Sallamar
Usman ta katsesu,Hamid bai amsa ba saima
ya mike ya fice saboda a yanzu haushinsa
yakeji akaina. Bayan su hamida sun gaisheshi
ya dubi Raliya.
"Wa kike ganin ya dace ta zauna wajen Meena
ne?"
Yayi maganar tamkar da sa'arsa,Raliya bata ko
damu ba ta kyabe baki
"A'a toh,ko Dijangala ai sai ta zauna. Idan
kuwa batason aikinta ga waccan tsiyar saiku
kwasa."
Sai lokacin na dubeta kafin na watsawa Usman
mugun kallo wanda na jima banyi mishi irinsa
ba. Murmushi yayi ya dubi Raliya
"A'a dijangala shiririta ne da ita,tunda dai ga
gwaggon meena zata dunga yi musu wanka
sai Tasleem ta dunga gyare gyarem gidan."
Raliya bata musa ba domin duk yanda zan
kuntata a rayuwa shi tafi kauna. Tace
"Hakan ma yayi,ke! Idan kin kammala ki tattaro
kayanki ki koma gidan Usman har sai matarsa
ta gama wanka sannan zaki dawo."
Bance uffan ba don bakin ciki,a matukar fusata
ta kammala aikin na mike na shiga daki. Haka
na tattaro kayan na fito. Hamida mukayi arba
da ita ta tuntsire da dariya gami da yimin
gwalo"Haka zaki k'are." Kamar nace mata wani
abu saidai na fasa nayi gaba,Raliya har lokacin
tana falon banko kalleta ba nayi gaba abina a
fusace.
Saida nazo daidai garden na zube anan na
fashe da kuka,wai haka rayuwata zata k'are?
Wane irin uba gareni da bai daukeni komai ba?
Ya manta da ya haifeni ne har ya banzatar dani
a gidansa ya maidani wofi? Ace yan aiki ma
sun fini daraja da kima a gidannan? Na daga
kaina nakai duba da d'an lilon da muka saba
wasa da Yayana. Haka zaiyita cillani yana
goyani muna zagaye garden dinnan muna
dariya. Ba zato naji an dafani ta baya,nayi
azamar juyowa ganin Usman bansan lokacin
da naja tsaki ba nayi kokarin mikewa yayi
saurin dawowa ta gabana.
"Haba Tasleem,ashe tsanar da kika yimin har
takai ace kije ki taimakawa matata ki zauna
kina kuka? Duk cikinmu waye mai tausayinki
bayan ni? Haba Tasleem,banji dadi ba wallahi."
Ganin yanayin fuskarsa sai naga kamar ban
kyauta ba,nace
"Ni ba gidanka ko matarka na tsana ba ai,irin
wannan rainin hankalin da akeyimin a gidan
ubana ne na kasa gane dalilinsa. Bansan kuma
me na tsarewa mutane ba."
Na karashe cikin tsiwa,yayi dariya ya kawo
hannu zai dora kan lebbana nayi azamar ja da
baya,cikin tsoron yanayin kallon da yakemin
"Tasleem komai naki abun sha'awa ne wallahi.
Ni bana k'inki,inason ganin kanwata a kusa
dani shine ma dalilin da yasa na nemi alfarmar
zuwanki. Kiyi hakuri inajin dadin yanda kika
kware a gyara muhalli. Meena KAZAMAR GIDA
ce, banason ganin gidan nan da kazanta. Don
Allah kanwata wallahi tana yin arba'in I
promise you zaki komo gida."
Bance komai ba na mike na dauki jakata nayi
gaba yana magana ko juyowa banyi,menene
saukin da nan da can din?
****
Baby ta numfasa,hawayenta ya karu wani yana
bin wani. Haris ya miko mata (handkerchief)
dinsa,tasa hannu ta karb'a saidai bata da
niyyar share hawayen. Ta dubi Haris wanda
shima ya gaji da waigenta ya karkato gaba
daya yana duban fuskarta don jin dadin hirar.
"Haris a wannan zuwan nawa ne gidan Usman
komai na rayuwata ya soma tabarbarewa.
Yanda akayi kuwa shine......."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(34)
"Usman ya dunga jana a jiki da wasa da dariya musamman idan ba idon matarsa a wajen. Tun ina daure masa har dai na hakikance dagaske tausayina yakeji kuma kauna ta don Allah yakemin. Hakan ya zamana na amince cewar bashi da wata manufa akaina. Yaya Abdullah kuwa munfi sati lokacin bamuyi magana dashi ba don bana samun kudin da zan sayi data,hakanan shima bansan meya hanashi kirana ba.
Wahala iri iri babu banayi a hannu meena,ni ce kula da jaririyarta da taci sunan uwar meena wato Sadiya suke kiranta da Ummi. A farko Usman so yayi ya sanya sunan mahaifiyarsa saidai ta murje idanunta tace sam bazata amince ba,UWA TAFI UWA don haka saidai a sanya sunan nata uwar. Haka dai Usman ya goyi bayanta,dayake itama Raliyar irin dukiyar da ake kawowa Meena daga gidansu a matsayinta na wacce ta haifi jikar fari ya hargitsa mata kai tace bakomai abi tsarin da Meena da takeso.
Wanki kuwa babu ranar da hannuna baya taba ruwa,hakanan daidai da undies din Meena ni nake aikin wanke mata su. Sau daya na taba gigin yi mata musu akan wankin ta jibgeni ba tare da kowa yayi yunkurin cetona ba. Hakanan nayi jinyata na warke domin alokacin Usman baya garin yaje daurin auren abokinsa a Zaria kamar yanda ya shaidamin.
Bakar ranar da bazan mance ba itace ranar da babu kowa a sashen usman sai ni. Gwaggo ta raka meena asibiti don allurar da zata kai Ummi,ina zaune a falo zaune kan kujera ina hutawa sanin da nayi matar gidan batanan balle kuma ta gani tunda dai ta rigaya ta sanyamin dokar hawa kujerunta nikam gajiya da aikin dana kammala yasa na shimfide saman kujerar ina kallon tashar Zeeworld da suke hasko series dinnan na Destiny wanda an riga anyimin nisa sakamakon jimawa da nayi ban kalla ba. Yawo naji wani abu kamar hannu yana yimin a kunnena nayi azamar mikewa zaune don ba karamin firgita nayi ba. Ganin Usman yasa nayi murmushi kadan ban kawo komai a raina ba na gaisheshi hade da tambayar
"Yaushe ka shigo?"
Wani kallo yake watsomin,hakan yasa cike da mamaki na dubi shigar dake jikina naga babu inda na kuskuro da shigar banza. Na kara dubansa "Lafiya dai baban ummi?"
Ya basar yana mai mikewa tsaye da dariya
"Lafiyar kenan Kanwata,kallonki nakeyi ina tausayawa rayuwarki. Ace ke kam baki da wani hutu sai masu gidan basunan kike da yancin sakewa tamkar ba gidan mahaifinki ba?"
Nayi murmushi ina mai jin dadin yanda Usman ke nuna damuwarsa akaina,alokacin na ayyana cewar ko na manta kowa bazan mance kaunar da Usman ya nunamin ba alokacin da dukkan gidan suka juyamin baya.
"Ayya,bakomai Baban ummi wataran sai labari fa."
Yayi dariya yace "Hakane kanwata,kiyi kallo abinki domin kuwa ina maki albishir cewar matar gidan bazata shigo yanzu ba don zata biya ta gidansu." Naji wani sanyin dadi shi kuwa yayo hanyar dakinsa na maida kaina ga kallo. Jimawa kadan ya fito ya shiga kicin bayan ya chanja suturar jikinsa zuwa doguwar jallabiya. Ban damu da sanin abunda zai aikata a kicin ba,a cewata ma,ai gwara kada ya matsamin ya barni na dan huta kafin hakimar tasa ta dawo. Hankalina ya nutsa sosai ga kallo saidai naji alamar ajiye kwalin a kusa dani. Hakan yasa na juyo na dubeshi,murmushi ya sakarmin yana kurbar lemon kwalin na Chi exotic dake hamnunsa,yayimin nuni da ido ga lemon da yake ajiye akan tebur kusa dani.
"Bismillah kina kallona,nasan rowa irin ta Meena bazaisa ta baki damar daukar abun sha ba. Bari na dan kwanta kafin nan da la'asar." Ya mike ya shige daki,nayi murmushi don nasan gaskiya ya fada. Meena rowan tsiya ne da ita,koda bak'i tayi sai sun nemi ruwa sannan ake basu balle akaima ga lemo. Na dubi kwalin lemun ina tunanin yaushe ma rabona dana samu yancin shan lemun kwali duk da a baya katon katon babu irin wanda Abba baya ajiyewa Mamma. Na dauka na bude na sha sosai,inayi ina kallo. Tsayawa nayi cak yayinda kaina yayimin nauyi,na ajiye kwalin lemun na dafe kaina ina mai runtse ido. A hankali na soma fita hayyacina,tun ina jiyo muryoyin dake fitowa a tv har dai na daina ji da ganin komai."
*****
Baby ta dakata tana mai sheshshekar kuka sosai,Haris cike da tausayawa ya daure yace
"Kiyi hakuri Tasleem."
Kamar bazatayi shiru ba,har ta soma rikita mishi tunani don hakikanin gaskiya ya tsani kukan mace. Dakyar ta nutsu ta goge fuskarta da (handkerchief) din daya bata. Kafin ta zubamishi jajayen idanunta wadanda sukayi kusan kwana uku suna zubar da ruwan hawaye.[2/3, 21:29] Rufy: 'YAR BARIKI ©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(35) "Haris a wannan ranar Usman ya ketamin haddina.
Yayi amfani dani ba a hayyacina ba." Ta numfasa kafin
ta cigaba "Baccin nan bai sakeni ba sai wajen magriba.
Nayi mamakin irin radadin da naji a gabana. Na yunkura
da zummar mikewa daga shimfidar da nake kwana na
katifa a karamin dakin yar aikin meena wacce zuwana
yasa ta koma sashen raliya da aiki,saidai ko kalilan ban
iya motsawa ba. Kawai sai na fashe da matsanancin
kuka,a hankali kuma tunanina ya dawo da lemun dana
sha hakanan cikin magagin bacci na hango fuskar
Usman lokacin daya kwasheni zuwa dakina. Nayi
azamar duba pant dina,jinin dana gani ba karamin
dagamin hankali yayi ba. Ihu nasa hadi da fashewa da
kuka. Yayi daidai da shigowar Meena da Gwaggonta,wuf
suka fado dakin. Meena na fadin "Wane irin iskancin
banza ne zaki...." Sauran maganarta ta makale ganin
halin da nake ciki,gwaggo ta matso tana buga salati
"Mun shiga uku,Aminatu kinga abunda nake gani? Yau
tsinanniyar nan ta janyo mana abun magana." Meena ta
dubi Gwaggo tace"Wa?! Wallahi badai dani ba! Kanta ta
janyowa,karuwae banza da wofi. Bazaki janyomin zagin
mutane ba." Daga haka ta hau buguna kamar Allah Ya
aikota. Ihu nakeyi ina kuka kakkarfa saboda radadin
daya hademin biyu. Ta sakeni tayi wuf ta fita ina nan
zaune ina jan jikina zan shiga bandaki ta dawo rike da
bokiti,kafin na ankara ta gwalemin kafafuna ta
watsamin. Ai bansan sadda na saki razananniyar k'ara
ba saboda azabar ruwan zafin nan,daga haka na sume.
Ban farka ba sai a gadon asibiti. Nayi mamakin ganin
har da Abba cikin wadanda ke tsaye a kaina,sai Raliya
da kuma Gwaggon Meena. Na dubesu daya daya kafin
na maida dubana ga Abba cikin matsanancin tsanarsa.
Dukkansu babu masoyina ciki,makiyana ne. Bansan me
suka kawoni ayimin ba bayan sun rigaya sun gama da
rayuwata,inama ace sun barni na karasa rayuwata
anan. Na kauda kaina ina mai jin saukin radadin azabar
da nakeji a gabana bansani ba ashe wai har dinki
akayimin. "Munafuka,ke juya keyarki mana kin jawo
mana zagin mutanen gari. Haba Tasleem,me muka
rageki dashi da har sai kinje ga bibiyar yan iskan gari?
Har nawa suka baki kika basu kanki? Tir!" Cewar Raliya
tana matsar kwallar munafunci. Bance uffan ba,jira
nake naji abunda zai fito daga bakin Abba saidai baice
komai ba fuskarsa cike da bacin rai ya nufi hanyar
ficewa. "A'a Doctor ina zakaje kuma?" Cikin takaici ya
fice baiko k'ara kallonmu ba. Yana fita itama Gwaggon
Meena tace zata koma gida don ba aikin kula dani ya
kawota gidan ba. Bayan fitarta Raliya ta tuntsire da
dariya harda hawaye,idona na runtse inaji kamar na
mike na janyota na d'irka. Naji maganarta daf dani
"Usman ya biyani! Da ace tun farko nasan kudurin nan
yayi a kanki da tuni na bashi goyon baya hakanan da
banji bacin ran kulaki da ya dungayi ba. Ki godewa
Allah ma da abun ya tsaya a iya nan. Na tsaneki! Na
tsani uwarki da dukkan tsatsonta! Nafison ganina da ya
yana kadai a gidan ubanki.! Sai kiyi jinyar kanki!" Ta
kara tuntsirewa da dariya ta juya zata fita, wallahi
bansan lokacin dana fisgota ba na janyo almakashin
dake ajiye cikin tasa a gefen kaina. Saitin wuyanta na
sanya kafin na soma magana a fusace "Kina zaton kinci
galabar abunda kikayimin ko? Toh wallahi ki ajiye a
ranki saina dauki fansa akan Usman! Sai ya gane shayi
ma ruwa ne RALIYA! Don ina shanye dukkan wahalhalun
da kuke sanyani ba wai hakan yana nufin tsoronku
nakeji ba! Kawai dai biyayya nakeyi ga MAHAIFIYATA!
Wallahi ko ba dade ko ba jima sai na dauki FANSA.!" Na
wuncikalar da ita,na ajiye almakashin,a fusace tayo
kaina wanda hakan yayi daidai da shigowar nos. Ba don
taso ba ta bini da mugun kallo,na tabbata tayi mamakin
karfin hali irin nawa,da shekarunta da komai nayi mata
haka? Hum, bari dai akai mutum bango Haris, wani
abun da bai taba zaton zai aikata ba sai ya aikatashi.
Kwanana uku a asibitin Abba,wata nos me mutunci ke
kula da lafiyata bansani ba ko bisa umarnin Abban ne
kodai a'a. Ni nake lallabawa nayi wankana nasa sutura.
A rana ta hud'u ne ina zaune ina shan lemun b'awo naji
sallamar wanda banyi tsammanin ganinsa nan kusa ba.
YAYA ABDULLAH. Gaba daya ya chanja yayi
haske,saidai fa ya rame akan yanda naga hotonsa
kwanakin baya. Sanye yake da shirt da wandon jeans
bak'i ya dora brown jacket a samanta. Farin cikin
ganinsa ya koma ciki sakamakon yanayin dana gani a
fuskarsa. Kallon da yakeyimin ba karamin kad'amin 'yan
hanji sukayi ba. Salati na shigayi a zuci kafin na
russunar da kaina sai hawaye.......
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(36)
Karasowa yayi ya durkusa a gabana,hannuna ya
riko na hagu kafin ya fashe da kuka. Hankalina ya
tashi ainun ganin kukan Yaya abdullah tamkar na
wani karamin yaro. Saidai ban iya cewa uffan ba
nima sai karfin kukana daya k'aru. Na ajiye
lemun b'awon dake hannuna. Ya dawo ya dubeni
cikin rawar murya yace
"Why Tasleem? Why?! Meyasa kika bari rayuwarki
ta lalace har haka? Wane irin halin rashi kike ciki
da har zaki bawa wani kanki? Meyasa Tasleem?
Akan wane dalili kika boyemin rashin Mamma a
gidan nan?"
Ya karashe cikin sheshahekar kuka. Na tsayar da
idanuna bana ko iya kiftasu a kansa, bakina a
bude na kasa cewa komai. Tsananin mamakin
yanda akayi yayana jinina ya yarda da wannan
kazafin da akayimin nakeyi. Ashe Yaya abdullah
shima zai amince da wannan zancen nasu?
Ya mike tsaye ya zauna gefen gadon,na cigaba da
bin fuskarsa da kallo yayinda ya dauke kansa
yana mai kara tamkemin fuska. Murmushin bakin
ciki nayi,tabbas an rabani da yayana kuma dan
uwana. Babu sauran wata magana,banga amfanin
sanar dashi komai dangane da lamarina ba. Babu
wani amfani a yin hakan. Zuciya irin tawa tasa
nak'i bayyanawa Yayana gaskiyar abunda na
sani. Maganarsa ta katseni
"Nayi bakin cikin jin rabuwar Abba da Mamma.
Kodayake naga alamar akwai wata a kasa tun
rayuwar da nayi a abroad. Wallahi Abba baida
masaniyar a yanda na kammala karatuna na
dawo. Duk a zatona Mamma tana tare da
Abbana,wannan yasa nayi kiranta na shaida mata
dukkan halin da nake ciki,bani da komai sannan
na tabbatar idan a wannan gab'ar nace zan ajiye
karatuna na dawo toh fa nan ma wata matsalarce
don bani da kudin jirgi. Mamma hankalinta ya
tashi tace kada na sake nayi kokarin tahowa na
bata nan da kwana uku. Haka na cigaba da zama
a gidan yayan abokina,Rilwan da muke makaranta
tare. Har saida ya zamana inajin nauyinsu,gani
nakeyi kamar ina matsa musu. Rilwan ya fahimci
halin da nake ciki domin ya lura har lokacin bani
da niyyar biyan kudin makaranta. Bansan ya
akayi ba sai ji nayi yace na shirya na rakashi
wani waje. Ban kawo komai ba nayi shirina tsaf
muka tafi. Nayi mamakin ganin Rilwan ya
biyamin kudaden nan,bawai ina mamakin ko a ina
ya samu kudaden nan bane,ko kadan saboda
nasan waye mahaifin Rilwan. Babban ma'aikaci
ne a 9ja garin Abuja. Mamakin da nakeyi har
wane matsayi Rilwan ya bani da sai biyamin
kudin shekara biyun daya ragemin. Na rasa
kalmar daya kamata na godemishi. Har hawayen
farin ciki nayi,ya nunamin babu komai domin shi
don Allah yake sona. A haka bayan kwana uku sai
gashi Mamma ta turomin kudi har dubu dari uku.
Nayi mamaki sosai,a karshe nayi kiranta na
shaida mata yanda akayi,kusan ta fini murna tace
na tattala wadannan zasuyimin amfani kada na
damu Abba ayyuka sukayimishi yawa shiyasa naji
shiru. Na bita a haka. Kinji yanda na kammala
karatuna,da taimakon Rilwan da Mamma sai
matar da nake niyyar aura, Hasinat kamar yanda
kika san tsakanina da ita. Ita kam dukkan wani
abu daya danganci sutura da kayan kamshi ita ke
siyamin batare dana sanyata ba. Tun bana shiga
harkarta har nazo ina shiga,iyayenta sun sani
hakanan mamanta na yawan waya da Mamma.
Itama hasinat tasan mamma sosai."
Yaya abdullah ya numfasa ya share hawayensa
yana dubana cikin mugun takaici
"Na kammala na dawo saina riski labari marar
dadin ji daga bakin Maman twins(Raliya),wai
Tasleem kin siyar da mutuncinki saboda abun
duniya?!! Wane irin kunci kika shiga?!! Abba ya
cucemu daya dauke mana mahaifiyarmu daga
gidansa!"
Zuwa lokacin hawayena sun gaji da zuba sun
dauke,murmushi kawai nakeyi wanda yafi kuka
ciwo
"Kaddarata ce mai yiwuwa! Haka nawa..."
"Ba kaddara bace!!"
Ya katseni a tsawance har na firgita ina dubansa
yanda ya mike cikin fusata.
"Son zuciyarki kika bi tasleem! Kin manta
tarbiyyar da Mamma ta jima tana iyakar kokarinta
wajen baki? Meyasa zaki lalata rayuwarki har
haka? Nayi bakin ciki marar iyaka jin wannan
batu! Nayi danasanin tafiyata na barki,wallahi da
nasan Abba zai rabu da Mamma da ban amince
na ketara ko nan da can ba!"
Ya dakata yana mai hade kansa da bango kafin
yayi wuf ya fice, ina kiransa saidai ko waigowa
baiyiba.
Kaina na cusa cikin filo ina kuka mai karfi. Gaba
daya zaman asibitin ya isheni hakan yasa na
sauko na dauki hijabin da bansan ko na waye
ba,dashi dai nakeyin salla,ban iske takalmi ba
hakanan na fice.
Ban tsaya ko'ina ba sai kofar gidanmu,na nemi
rance wajen baba Maigadi don bawa mai
adaidaita,baba maigadi yace babu komai naje zai
sallameshi. Yayimin sannu banko tsaya amsawa
ba nayi ciki. Tsayawa nayi cak ina duban ko'ina
na gidan,ina ya dace na nufa? Wajen wa zanje?
Waye zai saurareni? Na kara taku daya biyu,na
daga da niyyar yin na uku mukayi ido hudu
dashi,cikin sanyin jiki na maida kafar baya na
dukar da kaina. Ya k'araso a fusace
"Me kika dawo kiyimin?!!!"
Na dago kaina murya na rawa na soma magana
"Abb..." Marin daya saukemin a fuskata ya
dakatar dani daga karasawa
"Fitarmin daga gida,yar iskar yarinya! Kin bata
wayonki! Bazaki zo ki b'atamin tarbiyyar yarana
ba! Shegiya! Kedai kam ina kwakwanto akanki!
Anya nine ubanki?!!!"
"Wannan shine furuci na biyu cikin ukun da bazan
taba daina tuna su ba,hakanan tunaninsu ya
sanyani yin mummunan hatsarin da har ka kaini
asibiti Haris." Cewar Baby tana duban
Haris,sannan ta cigaba.
Kalaman Abba yayi daidai da fitowar yayana
Abdullah a guje daga sashen Mamma.
Gwuiwoyinsa a k'asa ya shiga rokon Abba akan
yayimin afuwa ya barni na rayu koda a sashen
'yan aiki ne. Abba ya hankad'ashi
"Gidana ne! Ina ajiye wanda naso a ciki amma
banda yan iska! Kaima kuma idan bakayi wasa ba
yanzun nan zaka bita ku tafi."
Maganar da Abba keyi da karfi ce ta janyo
hankulan yan aiki. Zuciya ta kwasheni cikin kuka
da daga murya nace
"Naji gidanka ne! Zan fita na barshi,zan barshi
har abada!! Kai uba ne ga wasu amma ba ni ba!
Na amince idan har ka manta hakkina dake
kanka ka manta akwai hisabi a tsakaninmu! Toh
hakika zan bar gidanka yanzu ba anjima ba. Ko a
kiyama bana fatan Allah Ya kara hadani da
azzalumin uba..."
Mari Yaya abdullah ya daukeni dashi,
"Kina hayyacinki kuwa? Kin manta waye
agareki?!!"
Cikin kuka da daga murya nace
"Ban manta ba yaya abdullah! Amma shi ya
mance diya nake awajensa. Abba ina kake sadda
nake rayuwar garari acikin gidan ka?! Ina kake
sadda abincin yan aiki ma yafi nawa mutunci da
dadi a harshe? Ina kake sadda na kammala
karatu?!! Ka taba zaunar dani kaji damuwata?! Ka
taba yimin nasiha koda sau daya akan rike
addinina?! Ka taba damuwa da ni?! Wallahi na
tabbatar ko sunana bazaka iya tunawa ba saboda
baka sona! Ka tsaneni! Har gashi ayau kana
kokwanto ko kaine ubana!!! Shikenan gaka ga
gidan naka! Allah zai mana sakayya!!"
Daga haka nayi waje a guje,Yaya abdullah yana
kirana amma ko juyowa banyiba. Nayi nisa sosai
da gidanmu kafin na samu kasan bishiya na zube
ina kuka da numfarfashi. Kaicona!!!!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(37)
Taku naji da sauri sauri kafin aci burki a gabana. Na dago kaina,Yaya abdullah ne. Kaina na cusa cikin cinyoyina,dagomin kai yayi kafin ya rungumeni shi kansa hawayen yake. Ganin mutane sun soma taruwa ne yasa ya mikar dani tsaye yaja hannuna. Na turje na tsaya cak, ya dubeni na girgiza kaina
"Kayi hakuri yaya,bazan koma gidan nan ba."
Ya dan dubi mutanen da suka taru kafin ya sassauta muryarsa
"Nima ba nan zan kaiki ba,biyoni kawai."
Adaidaita sahu ya tarar mana muka shiga. Har lokacin jikina kakkarwa yakeyi ga hawaye wani yana bin wani.
"Duk da laifin da kika aikata Tasleem,I can't change the fact that you are my blood sister. Bazan iya bari rayuwarki ta tagayyara ba Tasleem. Abba mahaifinmu ne,a yanda Mamma ta koyamin tace duk runtsi da tsanani kada na gujeshi wataran sai labari. Zan kaiki inda nasan zaki zauna cikin aminci har zuwa lokacin da Abba zai sakko ya yafemaki. Amma bayan da na samu labarin Mamma tayi aure bazan amince da zuwanki Kazaure ba har ki dagamata hankali."
Tunda ya soma maganganun hankalina yana ga waje, sai alokacin na waigo na dubeshi. Kallonshi nakeyi kamar wata tab'abb'iya ina mamakin yanda Yaya abdullah ya hakikance cewar na aikata zina da gangan. Murmushi nayi alokacin da ruwan hawaye ya malalo kan hancina. Na yarda sharrin mace yafi na shaidan. Usman!! Shine wanda ya fadomin a raina,kwarai ya tafka babban kuskure a rayuwa tunda yayi gangancin yimin wannan ta'asar,nasha alwashin daukar FANSA.
Unguwar tarauni,anan muka yada zango,yaya abdullah yayita yiwa mai adaidaitan nuni,har a karshe muka tsaya a wani gida karami na sumunti saidai babu ko fenti. Muka fito ina ta kallon gidan kallon rashin sani.
"Muje." Ya katsemin tunani bayan yace mai adaidaitan yayi tsumayinshi. Yace na soma shiga. Na shiga da sallama,matar dake zaune ta juya baya tana alwala ta waigo tana amsawa. Ganin Kulu yasa naje a guje itama ta mike da azama na rungumeta na fashe da kuka sosai. Tun tana farin cikin ganina har dai jikinta yayi sanyi,sallamar Yaya abdullah ta katseta daga tambayar da take shirin jefomin. Ta sakeni tana "Lale marhabin da d'ana. Saukar yaushe?" Yayi murmushi yana kokarin mayarda kwallarsa,ta dubeni ta dubeshi a sanyaye tace"Lafiya kuwa d'ana? Menene ya faru?"
Kafin muce wani abu tayi daki tana fadin"Ina zuwa."
Ta fito dauke da tabarma ta shimfida. Bayan mun zauna yaya abdullah ya dubeta
"Nayi bakin cikin dawowa naga bakya gidan Kulu,kamar yanda mutuwar auren Mamma ya tayarmin da hankali. Saidai tunda a yanzu tayi aure mun dauki hakan matsayin KADDARA."
Kulu wacce tun soma maganarsa taji babu dadi saidai furucinsa na karshe ya dan sanya ta saki fuska"Kai Hajiya tayi aure? Toh ai Alhamdulillah. Kada ka damu dana karatun da kakeyi ne yasa ba'a bari labarin ya riskeka ba amma komai na Allah ai mai kyau ne."
Ya gyada kai"Hakane." Ya danyi shiru kafin yace"Kulu nazo neman karamar alfarma a..." "Fadi ko menene D'ana,babu abunda banajin zaka nema da nayi maka na kasa yinsa."
Ya numfasa yana murmushi"So nakeyi ki rikemin amanar Tasleem zuwa nan da wani lokaci......"
Kulu taji abun banbarakwai,koda ta nemi dalili. Ya sanar mata Abba ya baya gari shine matsi da wahalarwa suka sanyani nayi kokarin guduwa shine ya yanke gwara ya kawoni gabanta na zauna. Jin abunda yace yasa na kalleshi kwalla ta cikamin ido,yayimin alamar cewar kada nace komai sai kawai na sunkuyar da kaina har mamakin yanda Yaya abdullah ke son kare laifin Abba nakeyi. Wane irin zuciya ce dashi har haka? Kulu ta hakikance sanin halin Raliya zata aikata abunda yafi haka acewarta,irin hakan ke sa yaro ya shiga duniya.
Yayi mana sallama bayan ya tabbatar min zai sanya mai adaidaita sahun nan ya kawomin kayana banko kalleshi ba ya lura fushi nakeyi dashi. Bai kulani ba yayi gaba,wajejan yamma sai ga mai adaidaitan ya kawo jakar kayana,ciki kuwa koda na bude na samu dubu goma a samansa. Damkasu nayi gaba daya ga Kulu.
Muna hira take shaidamin cewar da matar d'anta suke zaune da yaransu amma yanzu sunje ganin gida acan Ringim. Na nuna mata babu matsala zan iya zama. Na lura a zamanmu tana son takura kanta akan lallai sai tayimin cima mai dadi. Saida na nuna mata banaso zan iya irin rayuwarta sannan ta hakura.
Satinmu biyu tare,Salamatu da yaranta uku da mijinta suka dawo. Sunyi mamakin ganin bakuwar fuska,saida Kulu ta fahimtar da d'anta Salmanu ko ni wacece tukunna. Nan da nan kuma naga fuskar Salamatu ta chanja har ta kasa boyewa tace wai Baba ta fiye yi musu kwashe kwashe alhalin daman da yaya suke rayuwar? Kulu dai jiki yayi sanyi don ba ranar ta soma ganin rashin arziki wajen Salamatu ba hakanan d'anta kansa yana shayin matar tasa. Nidai bance musu uffan ba.
Rayuwata tana cigaba da tafiya a wajen kulu da dadi babu dadi,Yaya abdullah baya wuce sati baizo ba kafin kuma ya dauke kafa yaje Kazaure. Nan ma daya dawo ya tahomin da tsarabe tsarabe duk daga yan uwa. Banyi wani murna ba tunda dai da nayi mishi korafin tafiya dani ya nunamin kamar bayason kaini a yanzu,na lura kyamata kawai yakeyi.
Watana uku a gidan,lokacin cikin hukuncin Allah takardun Yaya abdullah sun kammalu har ma da taimakon abokinsa Rilwan ta samu aiki a wani kamfanin mahaifin Rilwan na Abuja,suka bashi karamin gida da motar kamfaninsu. Koda ya dawo ya sanarmin nayi mishi murna saidai lokacin bani da cikakkiyar lafiya. Kullum cikin zazzabi nake ga kasalar jiki. Ya kwasheni ni kadai a mashin dinsa mukaje asibiti. Koda mukaje likita ta nemi fitsarina,a tsorace na mike naje nayi na mika lab. Muna nan zaune jiki a sanyaye har aka kammala aka bamu result muka kai ga likita. Ta dago tana murmushi
"Congrats, you are pregnant."
Ihu na fasa na zube a wajen ban kara sanin meke wakana ba saidai na farka na ganni kwance a gado. Likita na tattaba goshina,tunawa da nayi da abunda naji a karshe yasa na kara sakin ihu ina fadin "Wallahi saikin zubarmin! Banaso!! Wallahi ..."
Yaya abdullah ya toshemin baki yana kuka
"Kin ja mana Tasleem! Baki kyauta mana ba."
Likita dai sannu take bina dashi.
Bayan mun fito Yaya abdullah yace bazai iya barina kuma a hannun kulu ba,dole dani zai koma Abuja ba yanda zai iya. Nidai babu bakin magana illa bakin cikin dake nukurkusata ya zamana daidai da shi kansa haushinsa nakeji. Naji duniyar na tsani kowa da komai. Mahaifiyata kadai ta fadomin a raina,kawai sai na fashe da kukan tausayawa rayuwata. Ya zataji idan tasan abunda ya sameni?
Haka dai muka koma mukayi sallama da kulu bayan Yaya ya cikata da kudi yayi mata godiya. Ita kanta salamatu saida ya bata,ba kunya ta karba da rawar jiki.
A karshe muka koma ya ajiye mashin din daya aro na makocinmu kuma abokinsa sannan ya tsayar mana da adaidaita sai tasha domin tuni daman kayansa suna tashar a hannun wani amintaccensa.
*****
Baby ta tsagaita hadi da jan majina,fuskarta tayi jazur tamkar kosai kamar yanda fuska da fararen kwayar idanun Haris suka sauya launi zuwa ja.
Zuwa lokacin shi kanshi hawayen yake fitarwa. Ta cigaba
"Haris wannan shine silar zamana a Abuja na shekara daya da watanni a gidan Yayana da matarsa Hasinat."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(38)
Watanmu shida cif a garin Abuja,babu yanda na iya cikina ya girma ya fito so sai. Akan bakin cikin ganinsa ya sanya Yaya abdullah kauracewa yini a gidan,kasancewar estate ne wajen akwai mutane da dama saidai ba wanda ke shiga harkar wani sosai. Kullum rufe nake da hijabi zunb'ulele saboda nauyin da nakeji musamman ma na yayana. Shima baya yini a gidan. Wataranar laraba ne na tashi da matsanancin ciwon mara da baya. Lokacin kuwa karfe uku na rana ga Yaya abdullah bai dawo gidan ba. Sai murkususu nakeyi a tsakar falon ina salati a zuci don bakin nawa ma mutuwa yayi murus. Na rasa yanda zanyi,cikin ikon Allah sai ga Yaya abdullah bayan nakai tsawon awa daya ina abu daya. Jaka da ledar dake a hannunsa ya yasar ya nufoni a guje.
"Lafiya tasleem? Haihuwar ce?"
Na gyada kai ina runtse ido don babu baki, ya fita a guje ya bude motarsa sannan yazo ya daukeni ya sanyani ciki. Har ya bude motar zai shiga ya dubeni a rikice "Kin hada kayan dana kawo na baby kuwa?"
Ban iya magana ba,ya fita da sauri saidai yayi mamakin ganin yanda ya kawomin haka suke a ledar ban fidda komai ba. Ya kinkimo ledar karshe da ya rasa abunyi ya kinkimo harda akwatin kayana kasancewar nak'i jerasu a kwaba don komai ba burgeni yakeyi ba a lokacin. Haka muka isa asibiti,nidai ina motar nan tunda wani azababben ciwo ya murdomin na saki k'ara na sume bansan me ya wakana ba. Bayan farkawata kuwa na ganni kwance a gado wai ashe aiki akayimin aka fiddo jaririn. Saidai kuma baizo da rai ba. Bansan sadda nayi hamdala ba sa'ilin da nos ta shaidamin hakan,ta taimaka ta gyarani tsaf sannan aka chanja min daki. Mintuna kalilan ina nan kwance ina hawayen farin ciki,Yaya abdullah ya shigo da wani wanda kallo daya nayi mishi na fahimci cewa Rilwan ne. Na kauda kaina daga dubansu. Yaya abdullah ya riko hannuna yana murmushi "Sannu kanwata,ya jikin?"
Murmushi kawai nayi mishi,kafin shima Rilwan ya matso yana min sannu. Na amsa a nutse, sallamar wata matashiyar budurwa ce ta katsemu. Ta shigo dauke da kwando,a bayanta kuma wani saurayi ne ya tsuke cikin kananun kaya askin kanshi kadai sun wadatar su nunawa mutum irin matasan nan ne masu wankan kwalabo. Suka karaso ciki,nayi yunkurin mikewa da azama naga budurwar ta ajiye kwandon ta iso wajena.
"Sorry." Ta fada cikin muryarta na gogaggun yan boko. Ta jinginamin filo na kwantar da bayana akai. A hankali na gaishesu suka amsa min.
"Amaryarmu,da alama garin na Abuja yayi maki dadi shiyasa daga sati gashi kin kusa yin wata."
Cewar rilwan ya fada yana duban matashiyar nan wacce tuni na daina tunanin inda nasan fuskarta saboda na fahimci itace dai Hasinar Yaya abdullah. Saidai wanda suke tare dinne mai shegen kallo,ban sani ba. Dariyar Hasina ta katsemin tunani
"Wai kai ina ruwanka ne? Baka ganin Abdul dina yana jinyar kanwarmu,haka kake so na tafi na barshi duk su wahala? Ayya na manta ma,ban maki gaisuwa ba sister,ya hakurin rashin bebinmu? Allah Yaji kansa."
Nayi mamakin yanda Yaya abdullah bai boye musu cewar haihuwa nayi ba,sai duk na tsargu na dauka ya gama sanar dasu dukkan abunda ya shafi rayuwata.
"HAYAT kaji kanwar taka ko? Ya kamata ka dunga taka mata burgi irin wannan love haka?" Rilwan ne ya fada ganin ban amsa zancen Hasina ba. Yaya abdullah dai murmushi kawai yakeyi,ta dubesu
"Don Allah ku fita kuna matsawa kanwata da hayaniya gashi ko abinci bata ci."
Haka suna dariya suka fice, ni kuwa Allah Allah nakeyi su fita saboda bayan tsarguwa da nayi harma da kauracewa mayen kallon da Hayat ke watsomin wanda yana daga cikin abunda na tsana.
Hasinat ta hadamin tea ta zubamin chickensoup da suka taho dashi haka ta taimaka ta dunga bani da zafi zafi babu laifi naci sosai.
A karshe dai bayan su Yaya sun shigo akayita hira da dariya,nikam kallonsu kawai nakeyi,anan na fahimci cewar an kusa sanya ranar auren Yaya da hasina. Babu laifi na lura tana da mutunci,kamar bazatayi hayaniya ba. Allah Allah nakeyi su fita na tambayi Yaya abdullah abunda ya sanarwa Hasina a kaina. Saidai fa koda suka tafi na tambayeshi,nayi bakin cikin jin cewar ya sanar da ita wai nayi aurena mijina ya rasu ya barni da ciki yanzu ma na haihu d'an babu rai. Koda nayi tunani daga baya na fahimci rufamin asiri yayi.
Bayan wata daya da yin hakan,Yaya abdullah yayimin batun komawa makaranta,naji dadi kwarai saidai na nuna mishi ya bari ya kammala hada lefansa tunda a kansa yake. Yayi naam da batuna. Kullum muna waya da Mamma da mutan Kazaure kowannensu na lura a zatonsu ina kano ne basu san cewar ina tare da yayana ba. Gaba daya suna da labarin lefan da Yaya abdullah ke hadawa. Bayan ya kammala ya zaunar dani yace zaije dashi ya kaiwa Raliya ko ba komai tana ganin kimarsa yanzu da yayi kudi amma hakan ba damuwarsa bace shi dai su mika lefansa gidansu Hasinat. Baki kawai na tab'e bance uffan ba. Idan ma ba don Allah take jan yayana a jiki ba ita ya shafa yanzu kam na fidda kaina da lamuran gidansu Yaya Abdullah don ya tashi daga gidanmu.
Ranar da aka kai lefa da kayan saka rana ya shaidamin nan da wata uku za'ayi bikinsa. Na tayashi murna. Saidai sabon al'amarin da yake niyyar bullowa cikin rayuwata ya dagamin hankali,banason wata soyayya,asalima ba burgeni takeyi ba alokacin. Amma hakanan Yaya Rilwan ya shiga cusa kansa gareni,tun ina ja baya har dai Yaya abdullah yace kada na damu ya amince da rilwan amininsa ne kada na wulakantashi a hankali sai a rabu. Wannan yasa na sakarwa Yaya rilwan harma nake sauraronsa. Alokacin kuma yayana ya hau gyaran gida bayan ya soma kokarin nemamin admission.
Bayan sati uku aka samar min,na soma zuwa nan jami'ar Abuja inda na soma karatuna a fannin shari'ah.
BAYAN WATANNI HUDU
Anyi auren Yaya Abdullah da anti hasina. Har alokacin sun cinye wata daya suna shan amarcinsu. Tsakanina da Yaya rilwan soyayya ce tsantsa,yana mutuwar kaunata hakanan nima ina sonshi so bana wasa ba. Ana cikin haka kuma na soma jarabawa ta 1st semester ?򚈨a daidai lokacin Yaya abdullah ya dauki hutu zaije Kazaure tare da anti hasina. Har kuka nayi wai dole sai na bisu,ya bani hakuri yace idan na kammala jarabawa sai naje yanzu kam bazasu iya zuwa dani ba. Hakanan na hakura ina ji ina gani sukayi tafiyarsu............"
Baby ta dubi Haris
"Alokacin kuma KADDARA ta biyu ta afku gareni Haris......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(39)
"Koda dai bazance kaddara ba Haris, nafi jin kunyar nan gab'ar akan na baya domin kuwa a wannan sai ince a hayyacina nake kawai RUD'IN SHAIDAN ne ya jani."
Baby ta muskuta tana runtse ido sakamakon gajiyar da hannunta mai rauni yayi. Ta jingina kanta jikin kujera tana mai duban wata mai suyar kosai a gefen titi
"Rilwan masoyina ne,wanda ganin irin kusancinsa da Yaya abdullah yasa na saki jiki na hakikance bazai yaudareni ba. Soyayya ta zamani babu irin wacce baya gwadamin. Kayi hakuri da abunda nake fadi Haris, saidai bansan sha'awa ba sai akan Rilwan. Bansan wata soyayyar ba ma sam sai akan Rilwan. Wannan shine babban kuskure dana soma tafkawa a rayuwa. A inda har watarana misalin goma na dare muna hira da Rilwan anan falon gidan kamar yanda muka saba. Shaidan ya rudemu muka aikata b'arna a karo na farko dashi. Sai bayan da komai ya gama afkuwa sannan muka ankara, kuka na fashe dashi ina dukansa ina ihun kiran ya cuceni. A karshe na gudu zuwa daki na kulle,bugu yakemin yana kirana yana mai bani hakuri saidai ina na riga na fita hayyacina. Kukan da bazai dawomin da kima da darajata ba a karo na biyu nayi asara. Dakyar a daren na rarrashi kaina. Nayita istigfari,gaba daya na rame ko makaranta naje bana fahimtar komai na daga tambayoyin da akeyi mana a jarabawa saidai na rubuta abunda na tuna. Ana tashi kuwa a mota har nakai gida ina driving ina kuka. Mantawa nayi ban gayamaka ba,a rayuwar da muka shimfida da Rilwan har tuki ya koyamin motar kanta da nake hawa shine ya siyamin. Yan uwan rilwan suna kaunata,mutane ne marasa daukar kai wani abu. Ko sadda ya siyamin motar banso karb'a ba har ma yayana saida ya yi mishi magana ya nunawa yayanmu wallahi da gaske aurena yakeson yi,kada yayanmu ya damu."
Baby ta dubi Haris "Na amince da hakan kuma,saidai zan kira abunda ya faru tsakanina dashi RUDIN SHAIDAN,wannan na daya daga cikin illar kadaicewa tsakanin namiji da macen da ba muharramai ba.
Sati biyu da faruwar al'amarin,Yayana suka dawo. Nasha tambaya a wajensu na dalilin ramata saidai na rufesu da cewa rashin lafiya nayi. Suka aminta da hakan. Yayana yana dariya yayimin albishir da samun cikin anti hasina,ihun murna na sanya kafin na rungumeta muna dariya. Ya dakamin tsawa wai nayi a sannu kada na karyamishi mata. Na saketa muna dariya har lokacin. Nasha tsaraba daga Mamma,ciki kuwa harda hotunan graduation dina Yaya musty ya bada aka wanko ya aikomin da Camera dita. Nan na hadasu na adana da wadanda mukayi dasu Mamma ranar birthday dina na sanyasu a akwatina amatsayin tarihi.
Rilwan koyaushe cikin rarrashina yake amma sam na daukemishi wuta,kudin da yake turomin ta account har ba'a magana. Ganin abun zaiyi yawa naje na samu yayana da anti suna zaune a falo na fashe da kuka. Hankalinsu ya tashi suka hau tambayata ko lafiya,nan na sanar dashi bayanin kudaden da Rilwan ke aikomin ta account na kara da cewa yayi mishi magana banaso ya daina sannan ya fita hanyata. Sukayi sukayi suji dalilina amma ina saima na kara fashewa da sabon kuka domin lokacin ma shekaruna ashirin da daya(21). Ganin haka yayana yace shikenan zai mishi magana. Bansan yanda sukayi ba saidai kam hankalina ya kwanta sakamakon daina shiga harkata da Rilwan yayi. Ko gidan yazo baya matsawa sai an kirani,amma da zarar ya hangeni ya shiga satar kallona kenan saidai na ja tsaki na harareshi.
Hum,yawan samarin da suke biyoni har gida hakanan a makaranta su matsamin yasa yayana kirana yaji ta bakina ko aure nake ra'ayin yi. Nayi azamar cewa a'a yace toh dai na kula domin baison tara samari da nakeyi. Allah Sarki baisan ma basu gabana ba,don har lokacin akwai burbushin son Rilwan a zuciyata duk da tsanar da nakeji nasa a wani gefe na sashen zuciyata.
Hum! Bayan watanni uku,mummunan labari ya fito wanda yayi silar rabuwata da yayana da duk wani na jikina.........
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(40)
"Ba don Allah Ya kiyaye ba da auren hasina da yayana sai ya mutu. Mummunan labarin kuwa,fitowar ciki a jikina a karo na biyu."
Baby ta karashe tana mai jin takaici da tsanar kanta,Haris kansa ya girgiza hakanan yaga bak'in baby anan da har ta kara mikawa wani gangar jikinta duk da dai ta kirayi hakan RUDIN SHAIDAN. Maganarta ta katseshi
"Kasalar jiki,yawan bacci da kuma amai da nakeyi ya janyo anti hasina soma tsorata da abunda ta hango a jikina matsayinta na kwararriyar likitar mata kasancewar fannin data karanta kenan. Har take shirin soma aiki a asibitin da Abbanta ke ginawa a garin Abuja. Ta sameni kwance a gadona amai har ya galabaitar dani. Fuskarta a daure cike da tashin hankali ta kirayi sunana. Na dago idanuna na dubeta. "Yaushe rabonki da ganin al'adarki?" Gabana ya bada dam,lallai sai lokacin na ankara da abunda ke shirin faruwa dani.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Haris bana fatan na kara ganin wannan ranar,ranar da dan uwan da muka fito ciki daya yayimin dukar kawo wuka kafin ya umarceni da na fice na bar mishi gida." Baby ta fada hawayenta babu ko digon hawaye,muryarta har ta dashe tsabar kukan data sha.
"Rabona da period kuwa,tun a watan da Rilwan ya sadu dani. Hum! Ina gayawa anti hasina nakai wata uku rabona da period, sai ta buga salati tana kwalawa yayana kira "My dil! My dil!!" Da gudu Yayana ya shigo,kana ganinsa kasan a firgice yake. "Lafiya?" Ya watso mata tambaya,ni kuwa kuka na sanya don nasan abunda anti hasinat ta gano. Jikina banda kakkarwa ba abunda yake, kafin na ankara tuni ta sanarwa Yaya Abdullah ciki ne dani. Wallahi nan da nan tsikar jikinsa ta tashi,kukan kura yayi ya jawoni ya zare belt din jikinsa yayi ta buguna. Ihu nakeyi ina kuka saidai bai fasa ba. Na tabbata ni ce da laifi. Duk wani zargin da sukayimin a baya cewar karuwanci nakeyi ya fito a bayyane yanzu kam bani da wata mafita. Anan ne yaya abdullah yayi sub'ul da baka da cewa "Shi ne kika kara daukar ciki Tasleem! Kika kara bawa wani kanki?!!! Kin cucemu!"
Anan anti hasina tasan cewar cikina na farko ma shege ne. Har tayita hayaniya da fadin ita kam saidai ya maidani gidanmu idan kuwa ba haka ba ita ta fita ta bar mishi gidan. Yaya abdullah ya rasa ya zai ce mata,tuni ta fice ta koma dakinta ya bita ya a bugu amma tak'i bud'ewa. Nikam dakyar na iya mikewa tsaye duk fatata tayi rud'u rud'u tayi jazur. Ina zaune bakin gadona ina kuka da bakin cikin tsanar kaina Yaya abdullah ya k'ara fad'owa d'akin a fusace,jikinsa har rawa yakeyi ya tsaya a kaina.
"Kin bani mamaki kanwata,kin bata wayonki. Har da kanki ki dunga kai kanki dakin namiji?!! Tirr da wannan d'abi'a taki. Toh wallahi ki barmin gidana,kuma kika kuskura kikaje ga mahaifiyarmu kika kashe aurenta,wallahi saikin raina kanki! Kije duniya ce! Daidai take da kowa!"
****
Baby ta tsagaita anan gami da dafe kanta tayi jim,a karshe kuma kukan ya taho mata ta fashe da kukan sosai,cikin kukan tace
"Tell me Haris, ya akeso nayi da rayuwata ne? Ina akeson naje? Mahaifina wanda yayi silar zuwana duniya,wanda shi kadai ne waliyin aurena,shine abun alfaharina,ya koreni daga gidansa yace na fice mishi. A gefe ga yayana wanda muka fito ciki d'aya dashi,komai nawa na damuwa a ganina da hangena ya shafeshi,saidai ashe ba haka bane. Sai gashi da kansa yake yimin korar kare daga gidansa,bayan yayimin kashedin kada naje da mahaifiyarmu! Ina akeso na shiga? Ina akeso naje naji sanyi a duniyar nan? Shakikaina sun gujeni,sun koreni daga wajensu,ya akeso nayi? Waye kuma zai so zama tare dani?"
Haris baisan sadda ya janyo hannunta ba ya sanya cikin nashi,alokacin hawayensa sun kasa tsayawa sai zuba sukeyi. Yana son cewa wani abu sai kuma ya fasa gami da sakin hannunta ya janyo handkerchief data ajiye ya mika mata
"Kiyi hakuri." Ya fada murya a dusashe.
Ta dago kwayar idanunta tana dubansa,yayi amfani da wannan damar ganin bata da niyyar karb'ar handkerchief din ya kai hannu zai share mata fuska,ta rike hannun tana girgiza masa kai kafin ta mayar mishi da hannun kasa. Dariyar bakin ciki ta saki tana mai kauda kanta
"Kada ka wahalar da kanka ga fidda hawayen da bazasu taba daina zuba ba a rayuwata Haris. Banajin zan daina zubar hawaye. Banajin ina da sauran dama na jin dadi a rayuwata. Don haka kabar sharemin abokan rayuwata,na tabbata su kadai sukafi kusanci dani, banason suma a rabani dasu."
Baby ta fadi cikin sheshek'a,ya sunkuyo yana duban fuskarta
"Nayi maki alkawarin idan har ina raye BAZAN BARKI BA tasleem. Daga yau inaso ki bani damar kasancewa mai share maki su, idan ina raye Tasleem bazan k'ara barinki kiyi rayu...."
Meke damunsa ne?! Ya tambayi kansa, me yake shirin cewa? Ya dauke kansa ganin yanda baby ta saki baki tana kallonsa. Ya Salam,ya fada yana mai juya kansa. Murmushi kawai tayi
"Kanason jin karashen labarina? Ban matsa maka.."
"Baki matsamin ba,cigaba don Allah."
Ta watsa mishi kallo mai tarin ma'anoni wanda yaji shi har tsakar kansa kafin ta gyara zama ta d'ora a inda ta tsaya............
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(41)
"Haka na tattara kayana na hada da muhimman takardun makarantana da kuma hotunanmu da duk dai abunda nasan zai amfaneni ciki kuwa harda Atmcard dina. Mai taxi na samu bayan munyi cinikin inda zai kaini na shiga. Abu na farko da na soma yi shine,rubuta wasika na damk'awa maigadin gidansu Rilwan,nace ya bawa mahaifinsa a karshe nayi mishi sallama na hau taxi,muna cikin tafiya ina kuka,naji maganar mai taxi yana fadin"Kinga Hajiya idan babu damuwa ga wata can da alama itama tashar ta nufa ko zamu dauketa?"
Bance kala ba duk da nasan shatarsa nayi ina da ikon cewa aa saidai tashin hankalin dake gabana yafi gaban na bata lokacina anan. Ya tsaya ko kallon matar banyi ba,illai kuwa itama tashar dikkon ta nufa. Tana zama wani kamshi ya dokarmin hancina,duk da haka dai ban kalleta ba saidai na share hawayena sai numfarfashi nakeyi.
"Sannu ko? Nagode fa."
Tace dani, na dan kalleta,tabbas da ganin shigarta kasan tana hutawa kuma tafi kama da irin masu kud'in nan. Sanye take da wata atamfa yar ubansu tasha kwalliya ko yatsunta ka kalla kaga jerun zobbuna biyu na gwal sun wadatar dakai ka gane ba karamar Hajiya bace. Ita dinma ni take kallo fuskarta dauke da murmushi,wannan yasa na maida mata martani da murmushin da baikai zuci ba kafin na maida dubana ga gefen titi. Ina jinta tana waya kamar dai mota akayi niyyar aikomata don naji tana surfa ashariya tana fadin ita tafi karfin wulakanci,yasan yana. Tsoron matar tasa ya kwana da ita a hotel? Anan na fahimci lallai ba macen arziki bace. Har muka isa waya takeyi tun suna hayaniya har dai akarshe ta hau tuntsira dariya tana fadin babu komai ma zatabi motar kasuwa.
Da isarmu na sauka,zan biya mai taxi ta dakatar dani tace ai nayi mata alfarma don haka kada na damu itama yimin zatayi,ina kallo ta biya. Nayi godiya,ina shirin kinkimar akwatina ta zagayo ta dubeni
"Ina zaki ne?" Ganin da nayi mata na wacce ta fini shekaru yasa na amsa ba don naso ba don ta soma bani haushi ta soma takuramin.
"Kano." Tayi dariya"Nima nan na nufa,tsaya a sama mana mota."
Nidai bance uffan ba,abunda na soma tunani bai wuce ma ina zan nufa ba a Kanon? Waye zai amsheni da cikin shege??
Banyi mamaki sosai ba ganin Hajiyar nan ta dauki shatar karamar mota mai zuwa Kano guda daya. Tace nazo muje,wallahi Haris banji ko d'arr wai na rashin yarda da ita ba. Na sadakar idan ma yar yankar kai ce toh ta kaini a yankani na huta da bakar rayuwar da nake ciki. Koma dai menene alokacin ji nayi muje kawai.
Motar mu ta d'aga daga ni sai Hajiyar nan da direba,lokacin wajejan uku na rana. Daidai lokacin da muka soma tafiya wayata ta dauki kara,shaf na mance ban kasheta ba. Na duba,sunan wanda na gani yasa a fusace na kashe wayar na fiddo sim din na cusa dukansu a jakata. Me kuma rilwan zai min? Ina waigowa karaf muka hada ido da Hajiyar nan.
"Namiji ko?"
Mamaki ya kamani,tayi murmushi tana kashe ido na yan duniya "Ai bakin cikin mace bai wuce akan d'a namiji baiwar Allah. Tun ganina dake a farko na fahimci kina cikin matsanancin damuwa,idanunki kadai zasu tabbatarwa mutum kinci kuka kin koshi. Idan bazaki damu ba,zaki amince dani ko zaki sanar dani matsalarki? Ni kuma zanyi maki taimako daidai gwagwadon iyawata."
Na dubeta sai naji na aminta da ita. Hakanan na zayyane mata komai dangane dani da rayuwata. Ta jajinta min,na kara da cewa
"Babu abunda na tsana a yanzu kamar cikin nan Hajiya! Ki taimakamin don Allah ki kaini inda kikasan za'a ciremin shi."
Tayi murmushi ta rungumo kafadata
"Kinzo wajen share hawayenki BABY."
*****
Baby ta dubi Haris "Wannan itace Hajiya Hannatu Bariki wato MOMY. Itace ta sanyamin suna Baby wanda har ila yau ya bini, don wasu da yawa basu sanni da Tasleem. A gidanta na soma sauka inda kuma washegari ta kaini aka zubarmin da cikin jikina. Itace ta gogar dani a harkar bariki. Ita ta kasance tana nunamin hanyar da acewarta shi kadai ne jin dadin rayuwa babu wanda zai takura maka babu mai matsa maka. Tun ina tsoro har dai na bada kai bori ya hau,abun nufi dai ta shiga hadani da manyan alhazai wadanda cikin sa'a kowannensu rububina yakeyi. Komai Momi ita ta koyamin,Momi itace shugabarmu,yan mata da yawa da zauwarawa sanadinta suka rike kansu suka zama tantiran 'YAN BARIKI. Sai ya zamana nabar yayin dukkan manyan kayana,koda dai ba sosai daman nake sakasu ba nafi mu'amala da kananun. Saidai fa a lokacin ya k'aru sosai,Momi haka ta bada oda aka kawomin su kala kala daga Dubai. Haka nan babu kudina da ake tabawa,haka kawai jininmu ya hadu sosai da Momi tana ji dani kwarai da gaske. Duk da wasu kayan maye da Momi ke sha da sauran yan kungiya,bana shan komai sai taba,shima sai idan ina cikin matsanancin damuwa ko nishadi ban fiya sha sosai ba gaskiya."
Baby ta murmusa adaidai nan,da alama kuma abunda zata fadi,fari ne fat a wajenta.
"Daidai wannan lokacin ne,na shirya daukar fansa a wajen Usman. Ga Rilwan kuwa,Abbansa na zayyanewa komai a wasikar nan kuma inada tabbacin Abbansa mutum ne nagari da yasan ya kamata,kamar dai yadda nasan Rilwan da fadar gaskiya komai dacinta. Nasan bazai musa cewar shine yayimin wannan aika aikar ba. A yanda kuwa akayi na dauki fansar da taimakon Momi shine......."
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(42)
Prince,dattijo ne mai kimanin shekaru arba'in,sunansa na gaskiya Alhaji Shitu Ibrahim. Shine na kusa kusa ga Momi,hakanan wani suka ne a gwamnati. Yana da yaransa ko kuma ince maka 'yan dabansa da yake sanyasu kashe dukkan wani rai dake kawomishi matsala a rayuwa. Daidai lokacin da muka sameshi da bukatarmu yayi dariya yace"Wannan abu ne mai sauki ai,yarana da suke kashe rai wannan karamin aiki ne a wajensu. Saidai kuma nima inaso a bani abunda na jima ina marari amma an tsaya yimin yanga." Ya karashe dadm dariyar 'yan duniya yana kallona. Murmushi nayi don a duniya ji nake alokacin ko me Prince ke so zan bashi saboda ya gama yimin komai da na bukata. Ba shiri na harhada kayana muka wuce dashi. Acan ya had'ani da babban yaronsa nayi mishi bayanin abunda nakeso ayi. Farko dai nayi mishi kwatancen inda babban shagon Usman yake domin alokacin yaci gaba har ma ya fito daga kwari ya bude babban shagon kaya wadanda yake sarowa daga Dubai. Nayi umarnin a k'onashi kafin nayi musu iznin nakastamin rayuwarshi ta hanyar yanke mishi dukkanin kafufuwansa."
Baby ta dakata a yayin data tuntsire da dariya cike da jin wani irin nishad'i,Haris kuwa mamaki kwarai yakeyi ashe daman zata iya aikata mugunta har haka? Tunaninsa ya tsaya cak sa'ilin da dariyar dake kan fuskarta ta dauke ta koma zubar hawaye. Kanta ta girgiza cike da takaici
"Saidai Haris, nasan ban dauki fansa ba. Domin babu yanda za'ayi na dawo da budurcina kuma mutuncina. Ya rigaya ya cuceni ya cuci rayuwata tun farko."
Baby ta fada kafin ta kara duban Haris
"Yanda kuwa na lissafa musu babu ko tangard'a hakan suka aikatamin. Ita kuwa Raliya itama saida suka tabbatar da fitowarta ita d'aya tana driving wataran suka tareta suka daure baki da idanunta. Ba wani abu sukayi mata mai yawa ba illah dai jibgarta dana sanya sukayi,yayinda a karshe dayansu ya kusanceta. Kafin su yi mota biyu da daddare daya yana jan nata,sauran kuma duk suna motar baya, wajejan sha biyun dare kenan. Daidai kofar gidan ya dire ta kafin ya koma motarsu suyi gaba ban kara bi takansu ba. Koda suka sanarmin sun cikamin aikina sai naji kuma na fashe da kuka kafin na saki dariya. Momy taso shima Abba a dan tab'ashi saidai naji bazan iya ba."
Baby ta dubi haris cikin hawaye tace
"Ban dauki fansa ba Haris,ban dauka ba. Saidai bana nadama ko kadan akan abunda nasa aka aikata musu a rayuwa. Haris tafiyata taci gaba kafin na samu na sayi gida wanda anan nake da zama yanzu. A hanya ne kuma na tab'a buge Manal da kullin kayanta,bayan na kaita asibiti naji likitan yana sanarmin wai tayi b'arin juna biyu. Koda ta farfado take bani labarin cewa marainiya ce,marikinta yayi mata ciki. Kaji silar haduwarmu da Manal. Dalal da Hibba a club muka hadu dasu, anan kuma kawancennu ya d'ore kafin daga baya nace subar gidan hayar da suke zaune su dawo nawa. Ni na hadasu da Momy,kaji yanda alakarmu tayi tafiya. Wannan shine labarina Haris."
Haris ya numfasa kafin yace
"Kin tafka kura kurai da yawa a rayuwarki Tasleem,ciki kuwa babban shine fitowa da kikayi kika fada harkar bariki maimakon ki kame kanki da mutuncinki,a'a saima zuciya data kwasheki kika maida kanki karuwar gaske. Kinyi ganganci kin manta da dokokin addininki daya hanemu aikata zina. Kuskurenki na gaba kuma,daukar fansa da kikayi akan wadannan bayin Allah inda kika manta cewar Allah baya kyale wadanda suka zalunci bawanSa,kika manta da kalmar hakuri har kika ji a zuciyarki cewar lallai ke da kanki kin isa sakawa kanki batare da kinyi hakurin ganin Sakayyar Ubangijinki ba. Rayuwar da kikeyi Tasleem,rayuwa ce ta wofi wanda karshensa nadama. Na hakikance ba kwadayin abun duniya ne ya kawoki bariki ba illah kawai kuncin rayuwa. Haba Tasleem,a rayuwa akwai wadanda suka fiki shiga kunci da wahalar rayuwa. Ki godewa Allah ma a gefe kina da iyayenki da yan uwa, wasu fa basu da ko daya,wasu rayuwarsu har su mutu cikin kunci da bakin ciki sukayita amma basu fada karuwanci ba,basu nemi daukar fansa ba illah dai sun kasance masu tawakkali da mik'a zuciyoyinsu ga Allah."
Baby babu alamar jin haushin Haris a fuskarta saima kallo da take binsa dashi tana murmushi kafin daga bisani hawayenta su zubo. Ganin hawayen ya sanyashi tsayawa da maganarsa
"Ina fatan ban b'ata ranki ba Tasleem?"
Ta girgiza kai tana 'yar dariya
"Wallahi baka b'atamin ba Haris. Asalima burgeni kayi,dadi nakeji a kasan zuciyata. Tunda na soma harkar barikanci,babu wanda ya taba yunkurin gayamin gaskiya saikai. Tun farko haduwarmu saida na fahimci kai din daban kake. Ban kara sakankancewa da lamuranka ba saida na hadu dakai a karo na biyu. Tabbas Haris kai mutumin kirki ne wannan ne yasa nayi mamakin yanda ustaz ya iya aminta da mutum irin Kb."
Murmushi Haris yayi ya numfasa ya gyara zama kafin ya dubeta
"Muna iya tafiya gaida Mamma?"
Ta lumshe ido tana murmushi
"Da gudu ma."
Sukayi dariya kafin Haris ya mika mata ruwan roba daya siya zai sha
"Oya,ga wannan sauka ki wanke fuskar nan taki, ki d'anyi kwalliyar nan taki bebinsu."
Harararsa tayi a wasance,kafin ta narkar da fuska
"Au ba taka bace?"
Ya dubeta kafin ya basar da zancen ta hanyar fitowa ya bud'e b'angarenta ya amshi robar ruwan,yana kokarin budewa yace
"Juyo ki wanke fuskarki."
Ba musu ta gyara ta mika hannunta na hagu,yana zuba mata tana wankewa har fuskarnan tayi fayau,Baby ta gasken ta bayyana sannan ya zagayo ya bude boot ya dauko mata handbag dinta ya shigo motar kafin ya dire mata a cinya yana murmushi
"Ayi make up please."
Murmushin tayi kafin yayi addu'a ya daga gilasan ya kunna Ac,ya sanyamusu karatun al-kur'ani don kara nutsar da zuciyar Tasleem daga bisani yaja motar suka dauki hanyar Kazaure. Ita kuwa ta hau fente kyakkyawar fuskarta da kwalliya saidai bamai yawa ba. Bayan ta kammala ta dubeshi
"Baka sanar dani abunda zai kaika garinmu ba?"
Dam! Gaban Haris ya buga. Shaf ya mance da ainahin silar zuwansa Kazaure sai yanzu da Tasleem tayi tambayar. Ashe fa wai matar aure zaije zab'a.
"Kayu shiru??"
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(42)
Ya dan dubeta,ya rigaya ya gama tabbatarwa kansa cewar baby kyakkyawa ce ta gani a fada,tabbas baiga laifi ga KB dake makale mata ba domin kuwa idan zaka biyewa kyawun halitta da surarta,bakasan sadda zaka fada tarkonta ba. Yayi murmushi kafin yace "Garin iyayena ne."
Ta fiddo ido kadan fuskarta ta washe "Haba? Ashe kaima dan garinmu ne? No wonder na ganka da kyau kamar aljani."
Kallonta kawai yayi ya sakar mata murmushin da saida ta jishi har tsakar kanta. Tasan tun haduwarsu ta farko,tana jin wani al'amari bak'o game da Haris,saidai ita kanta tasan Haris yafi karfinta. Me zaiyi da 'YAR BARIKI? Ta maida kanta ta kwantar tana sauraron karatun Al-Kur'ani mai girma. Shi din ma kogin tunanin ya fad'a. Anya bai fada tarkon son 'YAR BARIKI ba? "A'a ban fada ba,just ina girmamata ne a matsayinta na wacce ke bukatar taimako. Ina kuma tausayawa rayuwarta."
Ya fadi a ransa.
*******
Hankalinsa a tashe,nutsuwa tak'i samun mazauni a kwakwalwarsa da jikinsa. Yana zaune sai afkin kiraye kirayen waya yake. Daga ya kira Manal,sai ya koma Dalal kafin a karshe yaji ta bakin Hibba. Momy ma ya kirata sau d'aya saidai ita kanta bata da labarin duniyar da Baby ta shiga. Zuciyarsa tayi bak'i har hasko Baby yakeyi kwance a kirjin wani da namijin. Kishi matsananci wanda har ya janyo sauyawar kalar kwayar idonsa.
Tun tsawon daren jiya take lura da mijin nata, hakanan ko lokacin daya fidda kunya ko shayi yake waya a gabanta duk tana sauraronsa,hankalinta ya tashi jin cewar mace ce ta rikita Kabir har haka. Ta soma sharar kwallah saidai gogan baisan tana yi ba,kwata kwata ma baisan da wanzuwarta ba sai sambatu yakeyi a fili
"Ina kikaje? Wane dan iskan kika samu har kika kashe wayoyinki Babyna?"
Ire iren abunda yake fadi kenan. Maganarta ta katseshi
"Wacece haka prince?"
Ya dubeta,gaba daya baisan da ita ba a falon. Tsaki yaja ya mike ya dauki wayoyinsa zai shiga d'aki
"Yanzu akan wata 'yar iska kake..."
Fisgota da yayi ne a fusace ya sanya sauran maganar makalewa a fatar bakinta. Ya hau jijjigata cikin tsawa yace
"Koda wasa kika kuskura kika k'ara kiran Babyna yar iska wallahi Yasmeen saikin raina kanki."
Ta fisge jikinta tana hawaye itama a fusace tace
"An fad'a d'in! Yar iska! Yar bariki..."
Tass! Ya kwasheta da mari,kafin ya hankadata ta bugi bango ya nunota da yatsa
"Wannan kadan kika gani! Wallahi akan Baby zan iya rabuwa dake Yasmeen! Sannan ki ajiye a ranki! Baby saita shigo gidan nan matsayin matata!"
Ya kwashi wayoyinsa da suka tarwatse a k'asa yayi daki ya buga kofar a fusace. Yasmeen ta tsorata ainun,mikewa tayi ta nufi dakinta. Mayafinta da fos na kudadenta ta dauka,ta sab'i diyarta Nasreen dake bacci tayi waje. Ta rantse yau bazata kwana Abuja ba kuma ma a gidan mutum irin Kb. Maigadi yana tambayarta ko lafiya ta dakamishi tsawa "Budemin kawai!" Yayi mamaki don baisan Hajiyar tasu da haka ba,akwai ta da girmama na gaba da ita komin kankantar matsayinsa. Mace mai hankali da tunani,ga fara'a da hakuri. Ba musu ya bude a hanzarce ta sanya kai ta fita tana zubar hawaye. Yau kam sai KANO......!
****
Karfe uku da mintuna na rana sai gasu a Kazaure. Gaba daya garin ya chanjawa Baby harma ta kasa sanin ta yanda zata soma kwatantawa Haris gidansu. Ga mamakinta taga yana ta shiga wurare bai tsaya ko'ina ba sai kofar gidan Liman. Tabbas gidan kakan nata ma yaso ya sauya mata sakamakon fenti da shukoki da aka k'ara mishi. Ta tsaya cak tana kallon tsohon dake zaune akan tabarma tare da makwaftansa suna hira,saidai suma hankalinsu ya dawo kan motar. Fitowar wata yarinya karama ce ta basu mamaki,tamkar an tsaga kara an karya ita da Baby saboda tsananin kamar da sukayi,tana wani yanga irin ta kananun yara masu iyayi ta isa ga tsoffinan ta zauna saman cinyar tsohon nan. Haris da Baby suka dubi juna,ganin hawaye a fuskar Baby da kuma murmushi yasa ya girgiza mata kai. Ta kwashesu da hannunta
"Haris kayimin abunda har abada bazan mance dakai ba. Ka samu babban gurbi cikin zuciyata. Ina jinka sosai a jinin jikina kana yawo akowane sassa na jikina. Wallahi banajin zan taba mancewa da abunda kayimin. Nagode sosai."
Yaji maganganunta har cikin k'ok'on ransa,ya kasa dauke idanunsa daga kanta. Ya rasa me yakeji game da ita,ji yakeyi tamkar kada su rabu. Inama zasu shekara a haka bayajin zai damu. Murmushin nan nata wanda yake tayar mishi da tsikar jiki ta k'ara yi mishi.
"Fito muje,gaskiya ka bari ka huta saika karasa gida."
Ya girgiza mata kai ya saki lallausan murmushi idanunsa a kanta
"No,ki bari zan shigo anjima kinsan gobe fa zan tafi. Zanzo mu gaisa sai na kaiki ku gaisa da Kakannina."
Ta marairaice fuska,kwalla ta ciko idonta
"Gobe zaka tafi ka barni Haris?"
Maganar ta shigeshi,yana kara jin zuciyarsa na shiga wani yanayi. Kwankwansa gilashin da akayi ne ya maido hankulansu ga wajen,Haris ya sauke gilas kasancewar gilasan daga wajenm akwai duhu. Dan saurayi ne,yana murmushi yace
"Malam tambaya kukeyi ne?"
Haris ya girgiza kai,baby ta sanya dariya
"Baharu." Ta fada kafin ta fito,da gudu gudu ta isa ga Kakanta wanda da alama shi kam ya ganeta. Domin gaba daya ya mike yana farin cikin ganinta sosai,ta rungumeshi kafin kuma su zauna ta saki kukan farin ciki. Zuciyar Haris tayi babu dadi,ba abunda ya tsana sama da kukan nan. Dolensa ya bude motar ya fito suka gaisa da wanda ta kira da Baharu.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(44)
"Tasleem,kukan na menene kuma? Me ya samu hannun naki?"
Ta share fuskarta ganin yanayin Haris shima kamar baiji dadin ganin hawayen nata ba,ta dubi hannun kafin tace
"Buguwa ce nayi Malam,amma yanzu da sauki sosai ma."
Tsohon ya kurawa Haris ido da murmushi wanda haka halittarsa take,da wuya kaga gushewarsa akan fuskarsa.
"Yaro kana yimin yanayi da aminina Hussein."
Furucin Malam yasa Baby zubawa Haris ido kasancewar tasan Baffa Hussein sosai jefi jefi takan lek'a gidansu a baya idan tazo domin har baffa Hussein ya santa yana nuna kauna agareta har takanyi mamakin irin soyayya da shakuwar dake tsakanin wadannan bayin Allah biyu. Haris cikin murmushi yace
"Lallai ma tsohon nan,tabbas idan na koma zan fadawa Baffa ka mance da autan jikansa,Haris."
Mamaki karara ya sauka akan fuskar Baby hade da dariyar nan nata mai burgewa,haris ya daga mata gira yana murmushi. Malam kuwa hakora ya washe ya rungumo kafadar Haris yana dariya sauran tsoffi uku suna tayashi.
"Allahu,daman kaine Harisu? Haka ka girma? Lallai Harisu baku da zumunci,da ace kun yo halin iyayenku da ba haka ba. Ina d'an wajen dan auta?(Alhaji idris)"
"Yana can Abuja da zama. Kayi hakuri dan tsoho ba rashin zumunci bane,ayyuka suke rikemu acan."
Malam ya jinjina kai,baby kam murmushi takeyi,yayinda ta kasa dauke fararen idanunta akan kyakkyawar fuskar Haris wanda samun namijin daya hada komai irinsa a fannin kyau na sura da halayya abune mai matukar wuya a zamanin nan. Ya kallota,tayi azamar mikewa tsaye tana basarwa da cewa
"Bari naga kishiyoyina,don Allah dan tsoho kada ku bari yayana ya gudu tun yanzu,kunga fa ko abinci bamu ci ba."
Haris ya hararota yana murmushi,tayi mishi gwalo kadan. Malam yayi dariya
"Ai babu inda zai tafi yanzu,Baharu shigar da yayan naka dakinku yayi alwala yazo muyi sallah sai yaci abinci ko?"
Suka mike,tuni Baby tayi gaba tana fadin zata turo yaro ya shigar mata da akwatin kayanta.
*****
Tun a hanyarta take ta kiran wayoyin yayan nata amma yana ringing bai dauka ba. Taci kuka har ta koshi,ganin baya kusa yasa tayimishi dogon text inda ta gutsura mishi halin da suke ciki da KB da kuma tahowarta Kano da tayi. Daga karshe ta kashe wayarta gaba daya.
Yasmeen kenan!!
*****
Murna da hira ta karade bayan tsakanin mutanen gidan bayan da Baby tayi wanka da sallah. Tana sanye da doguwar rigar kanti. Alokacin tana zaune tana cin abinci anata hira. Makwafta sai shigowa sukeyi,Gwaggo Hajara ma nan tazo da kwanonta. Kowa yaga bandejin hannun Baby sai ya tanka,tana rufesu da fadin buguwa ce tayi. Wayoyinta kuwa har lokacin a kashe suke ta jonasu a chaji. Sallamar da akayi ta maido hankulansu,Haris ne a gaba sai Yaya musty a baya. Ganin Yaya musty yasa Baby sakin ihu ta mike ta rukunkumeshi suna dariyar farin cikin ganin juna. Gaban Haris ya shiga dukan uku uku,haka kawai ya tsinci kansa da jin haushin wannan rungumar da Baby ta yiwa wani.
"Yaya mustyna,ashe da rabon rai ya k'ara ganin rai tsakaninmu?"
Sai kuma ta soma hawayen farin ciki.
"Yaya mustyna??" Ya maimaita a zuciyarsa,ashe har yanzu Yasmeen bata mance dashi ba?
Har lokacin hannuwansu harde cikin juna,Haris ya kauda kansa ya wucesu zuwa ga mutanen gidan suna gaisawa. Kasancewar gwaggo Hajara ta samu labarin kowanene a wajen Baharu wanda yakai mata tsegumin zuwan Tasleem yasa ta ganar dasu. Nan fa murna ta k'aru,suka shiga tambayarsa mutanen Kano yana amsawa. A karshe yayi musu sallama bayan ya dire musu rafar kudi 'yan dari dari guda biyu ya mike suna fadin ya barshi amma da azama ya nufi waje. Ganin haka tasleem tabar hirar bayan rabuwa da Musty tabi bayansa a da sauri. Ganin yana shirin wuce zaurensu ne yasa tayi azamar riko hannunsa wannan yasa shi juyowa ya watsa mata kallon da yayi kama dana farkon ganinta dashi. Ta saki hannun dayake kanta a waye yake ta nuna kamar bata gane yanayin fuskarsa ba ta hanyar marairaicewa da langabar da kanta
"Yanzu tafiya zakayi shine babu ko sallama?"
Ya dan tabe baki yana mai zura hannunsa cikin aljihun wandon jeans dinsa,ya daga kafada
"Gani nayi kina hira da yan uwanki banson katseki ne."
Murmushi tayi kawai,ta soma fahimtar wani abu kadan akan fuskar Haris, mai yiwuwa yana dauke da ciwon da itama take dauke dashi. Ya katse tunaninta
"Zan wuce."
Ga mamakinsa yaga ta durkusa har k'asa tana dubanshi
"Har na rasa manyan kalmomin da zanyi amfani dasu kuma wajen yin godiya agareka yayana,kayi jihadi babba wajen ceto rayuwata daga halaka. Daga yau na baka matsayi babba gareni. Zuwa yanzu bani da wanda yafimin.."
Ya katseta shima ta hanyar yin durkuson a gabanta,yana kafeta da wannan idanuwan nasa masu kara fama mata ciwon dake ranta. Saidai ita kanta tana raina kanta a gaban Haris,duk wani haduwarta ganinta takeyi tsumma a gabansa. Ita kanta ta riga tasan Babban Goro sai magogin karfe,me namiji irinsa zaiyi da 'YAR BARIKI? Ta kauda kanta daga dubansa ganin bashi da niyyar kauda nasa akanta. Wai daman akwai abunda take ko kuma zata tabajin kunya acikin mutane? Bata taba kawowa ba kuwa ko a kanta,ya katseta a karo na biyu ta hanyar mikewa
"Tashi Tasleem."
Ta mike tsaye,bai kara dubanta ba yace "Kina iya rubutamin lambar wayarki,watakil na leko gobe kafin na wuce."
Har ya soma tafiya sai kuma ya juyo dauke da murmushi saman fuskarsa wanda bata taba ganin irinsa ba a tattarr dashi. "Sannan ki sani,matsayin kanwata kike Tasleem. Bana bukatar ki yawaita godiya gareni. Ki cigaba da godewa Ubangijinki. Hakanan ya dace kiyi istibra'i. Sai Allah Ya kaddara saduwarmu Tasleem."
Ya soma tafiya da baya da baya, hawaye taji sun taho mata yayinda ya juya ya fita da sauri saurinsa. Ta tsaya cak tana binshi da kallo zuwa lokacin hawaye sun sauka saman fuskarta. A gaban idanunta yaja motarsa bai k'ara ko kallon kofar gidan nasu ba.
"Small."
Taji muryar Yaya Musty ya fadi ta bayanta,wannan ya fargar da ita a inda take tsaye.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(45)
Ta dubeshi tana murmushi,yayinda damuwa ta sauka saman fuskarsa shi kuma.
"Kin tsaya anan? Ko bakiso ya tafi bane?"
Abunka da wacce bata iya boye damuwarta ba tace
"Banso ba,ya tafi ya barni da damuwa marar misaltuwa saidai yace watakil kafin ya wuce ya biyomin muyi sallama."
Musty ya k'ura mata ido yana kallon kwayar idanunta. Akwai wani kwantaccen sirri game da Haris a cikinsu.
"Kanwata are you in love?"
Tayi tsai domin batayi mamakin jin wannan tambayar ba,inda takeson Yaya mustin nata kenan,nan da nan ya dago damuwarta ko wace iri ce. Ta basar ta hanyar dariya ta soma tafiya tana fadin
"Yaya mustyna kenan,ina Haris ina mace irina?"
Ya riko hannunta wanda yayi silar tsayuwarta,ya jawota baya kadan yana dubanta da idanunsa da suka bayyana bacin rai da damuwa karara a cikinsu,mamaki ya hana baby magana sai ya rigata da cewa
"Ya kike irin wannan maganar sisna,wa zaik'i mace kamarki? Ko kina da wani aibu ne?"
Ya karashe bayan ya saketa yana murmushi a sanyaye,bata yardarwa kanta hakan yayi niyyar fada ba sakamakon zafin da ya nuna a farko. Batace komai ba banda murmushi da "Uhm" daga haka tayi ciki.
Ya bita da kallo rai a bace,wai daman Tasleem ba sonshi takeyi ba kamar yanda ya jima yana yaudarar kansa? Yaya mustyna! Yaya mustyna! Me hakan ke nufi?!! Tsaki yaja bazai kuma iya komawa cikin gidan ba kawai sai yayi gaba zuwa gidansa rai babu dadi domin ya gama lura Haris ya samu gurbi a zuciyarta.
*****
Mutanen gidan sunyi farin cikin ganinsa sosai. Nan aka shiga hidima dashi,sai abinci ake ajiyewa agabansa. Hankalin Haris ko kusa baya kan yan matan da suka had'e cikin kwalliya sunata shawagi a falon wajen kawo mishi abinci,ya tabbata an riga an basu labarin abunda ya kawoshi. Sai hirarsu sukeyi da kakarsa,Hajja. Koda ya kammala mikewa yayi ya nufi sashen kishiyoyinta suka gaisa kafin ya nufi bangaren kakansa,Malam Hussein.
Nan ma suna hira yake sanar dashi tare sukazo da Tasleem diyar gwaggo maryama 'yar amininsa Liman. Ai sai Malam Hussein ya tashi zaune fuskarsa a sake sosai. "Jikar Abdulmalik ce? Ikon Allah,daman kunsan juna ne acan Kano?"
Haris ya rasa amsar da zai bashi a karshe yace "Eh munsan juna,tare mukayi makaranta saidai banma san 'yar gwaggo maryama bace saida muka hadu itama zata zo nan take bani labari." Kakan nasa yayi dariya,cike da mamaki yace
"Wai kuwa d'an tsoho wane irin aminta ke tsakaninka da Liman? Na lura kuna kaunar junanku fiye da tsammani."
Jin tambayar ya k'ara sanya Malam dariyar farin ciki
"Bazaka gane ba Harisu,kaunar da muke yiwa junanmu ta samo asali tun daga iyayenmu da suka rasu,saboda karfin zumuncin ne,yasa mahaifina sanyamin sunan mahaifin liman din,wato Hussein yayinda shima yaci sunan nawa mahaifin Abdulmalik. Bayan haka,Allah Ya riga ya sanya mana kaunar junanmu fin tsammani Harisu. Wanda muke burin wataran mu kulla zumuncin da zai d'orar. Saidai kasan a zamanin nan ba'a yiwa yara dole,amma har gobe bamu bar burin wasu cikin jikokinmu ba su share mana wannan hawayen."
Haris yayi murmushi,baffa ya katse tunaninsa
"Ina fatan kayi abunda akace ya kawoka?"
Haris ya hade fuska
"Na rasa wacce zan zab'a domin na lura jikokin naka akwai yanga. Duk kama sukeyimin da juna ma."
Sukayi dariya,Baffa yace
"Ja'iri,ko kanawan dabo ba zasu nunawa mutanen Kazaure kyawawan yan mata ba shiyasa har zuwa yau ka kasa zab'en matar aure. Kada ka damu ka nutsu ka zab'a bazan bari Aliyu yayi maka dole ba."
Daga haka suka tab'a hirarsu ta zumunci kafin Haris yayi mishi sallama ya fice zuwa d'akinsa. Hankalinsa yakai ga wayoyinsa wanda ya barsu suna chaji,ya dauko yana dubawa. Missedcalls har fin goma,shida kuwa na kanwarsa ne. Yayinda daya na Abba sai kuma daddy daya kira sau uku. Hankalinsa yafi raja'a ga na kanwarsa. Yana shirin kira ya hangi sak'onta. Tun soma karantawarsa ransa yayi mummunan b'aci,jikinsa har rawa yakeyi. Wai Kb wane irin d'an akuya ne? Meyasa baya shakkar b'ata ran mutane? Ya lalubi layin Yasmeen ta daga tana kuka alokacin tana kwance a gadon mami(Maman kb wacce ta gama fusata).
Cikin kuka tace "Yayana kaga text dina? Yayana ka ceci rayuwata bazan iya yinta ba saida Kabir. Na shiga uku."
Ya runtse ido yanajin bakin ciki har ransa
"Wacece yarinyar?" Shine kawai abunda ya nemi sani.
"Baby yake yawan ambato."
Tuni idanun Haris suka bud'e,Baby?!! Akanta Kb yake cin zarafin kanwarsa? Kawai sai ya kashe wayar a fili ya furta
"Na rantse da Allah Kabir bazaka tab'a aurar Tasleem ba. Daga kai har ita zan nuna maku ni Haris na isa."
A fusace yasa kai,bai zarce ko'ina sai d'akin BAFFA......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(46)
"Ya wajen yayan naki? Ai farko mun damu da rashin samunki a waya. Wancan zuwan da sukayi na karshe yace min kin koma makaranta da zama anan Kano kuma ya hanaki yawan amfani da waya a dalilinsa nason ganin kin mayarda hankali ga karatu, har ina fad'a ina cewa me zaisa a wannan zamanin baligar mace tabar gaban mahaifanta ta koma jami'a da zama. Haba Tasleem,shi Khalid(Abba waziri,mahaifinta) din baiga kuskuren yin hakan ma? Koda dai na yarda da tarbiyyar da kika samu wajen maryamu amma hankalina bai kwanta ba Tasleem,nafison ganinki a d'akin mijinki."
Baby dake sauraron dogon bayanin kakarta,a gefe idanunta yana kan wannan 'yar budurwar mai matukar kama da ita tunaninta kuwa ya raja'a akan zuk'i tamallen da Yaya Abdullah ya shararo ya gaya musu. Kenan cewa yayi tana makaranta? Ikon Allah kenan. Ta numfasa ta kauda maganar
"A ko'ina Allah kan tsare bayinSa inna,kubar damuwa. Wai wacece wannan duplicate din tawa?"
Inna ta dubi yarinyar duk da bata gane turancin ba saidai ta fahimci baby bata ganeta ba.
"Lallai ma 'yar nan,keda har aike kikayi na sutura a kawowa kanwar taki tana jaririya? Aisha humaira ce fa,taci sunan aminiyar uwar taki. Lallai baki kyauta ba tasleem."
Tasleem idonta ya cika da kwalla,inna ta katseta da cewa
"Ai kusan sa'annine da takwararki,ko wannan zuwan nasu na karshe karkiso kiga har tasleem karama ta kusa kamota a tsayi."
"Wacece mai sunana?"
Anan kuma inna ta tsaya cak tana dubanta,wannan karon mamakinta da shakku sunfi na koyaushe domin kuwa tun zuwan Tasleem take lura da yanda ta chanja duk da tasan yanga da nuna aji halinta ne saidai zuwa yanzu ta soma zargin kodai Tasleem bata wani zumunci da yayan nata.
"Kinga abunda yasa banason makarantar kwana ko? Kada dai kicemin bayan mu da kika daina zumunci damu,yayan naki ma bakya zuwar mishi hutu kamar yanda ya fadamana ne? Nayi mamakin jin cewar kin manta da d'iyarsa."
Sai lokacin Baby ta farga da kuskurenta,ta wayance ta hanyar dariya duk da har lokacin tana fushi da yayan nata hakan baisa ta karyatashi ba.
"Kai inna,karatu fa yayi zafi duka duka munkai wata bamu hadu ba,inada matsalar yawan mantuwa ni ki gayawa liman ma ya nemar mini maganinsa."
Inna tace "Assha,naga alamun hakan kuwa. Tabbas dole ki nemi magani da kuruciyarki da komai wannan cuta ce babba. Saiki bar yin fitsari a inda kike wanka,domin shima yakan jawo larurar yawan mantuwa. Zan kuwa gayamishi."
Tasleem ta janyo hannun humaira wacce ta kammala cin tuwon dare,ta rungumeta kafin ta sumbaci goshinta.
"Ni yayarki ce, kina sona?"
Humaira tana dariya tace "Eh."
Ta kara rungumeta tana kokarin danne hawayenta,burinta gari ya waye taje ga mahaifiyarta.
Daren bata iya bacci ba,sai kuka da taci k'asa k'asa tunanowa da gurb'atacciyar rayuwar datayi a baya, gashi tana kunyar yan uwanta su samu labarin. Batasan yayanta yana mugun sonta ba sai a lokacin,tunda har ya iya sanyawa 'yarsa sunanta ayanzu kam bata da burin daya wuce ta sanya yarinyar a idonta. Har zuwa lokacin bata da niyyar bud'e wayarta domin batason amsa wayar mutanenta agaban mutan gidan.
******
Baffa ya dubeshi ya ajiye littafin karatunsa
"Lafiyarka kuwa Harisu?"
Harisu ya zauna kansa a kasa
"NA SAMU MATAR AURE BAFFA.....!"
"Alhamdulillah! Wacece?"
Ya gyara zama har lokacin ransa a matukar b'ace yake.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(47)
Yayi kokari sosai wajen danne mugun tsanarta dake taso mishi aduk sadda ya tuna cewar ita ke haddasa rashin zaman lafiya a gidan kanwarsa.
"TASLEEM."
Ya karashe cikin d'acin zuciya,yayinda idanunsa suka kara kad'awa.
Ji yayi Baffan ya rungumoshi cikin matsanancin farin ciki wanda sanin amintar bayin Allahn a yanzu yasa ko kusa baiyi wani mamaki ba yanzun.
"Allah Ya albarkaceka a gaba daya rayuwarka Harisu,kamar kasan addu'ar dana gama yi kenan akan Allah Yasa kace kanason jikar aminina. Allah Yayi ni Husseini ban mutu ba zanga aure ya kullu tsakanin zuri'ata dana Abdulmalik? Allah na gode maKa daka amsamin addu'ata nan take. Saidai kuma harisu bazan baka auren jikata ba har sai ta amince zata aureka don haka ka tashi ka tafi zuwa gobe sai na tuntub'eta. Allah Ya tashemu lafiya."
Haris ya mike jiki babu kwari ya fice zuwa d'akin da aka tanadar masa. Kwanciya yayi akan makekan katifar sakamakon kansa da yaji yana sarawa. Anya bai kwari kansa ba kuwa?!! No! Bazai yiwu kuma yabar rayuwar Yasmeem cikin garari ba. Tabbas rayuwarta da farin cikinta sun dogara ne da Kb,burinta a duniya bai wuce Kb ba. A yau aka wayi gari Kb ya auri Tasleem,wulakanci da bakin ciki sune abunda zai biyo bayan auren ga Yasmeen. Shikam ya gwammace yayi wannan jihadin,alhalin ma a yanzu koda kud'i yana da yak'inin Baby bazata k'ara waiwayar karuwanci ba. Yana jin tsanarta a wani sashen zuciyarsa yayinda wani sashen kuma yakejin sassauci game da ita. Ya rantse sai ya rabata da Kb hanyar data dace,kb bai isa ya nemeta ba idan ta zama matarsa. Bai isa koda wasa ma ya tunkareta ba,ba wai don kishinta yakeyi ba(a fad'arsa kenan!!),sai don samawa kanwarsa 'yanci da kuma farin cikin gidan aure. Wanda bazai tabbata ba sai yayi nasarar raba wad'annan shaid'anun biyu..!
*****
Da sassafe ya kammala komai ko karyawa baiyi ba ya fito da shirinsa na komawa garin Kano domin bashi da bukatar k'ara yin tozali da Baby hakazalika hankalinsa ya tafi gaba d'aya ga kanwartasa.
Ya shiga ya samu Baffansa yana lazumi,ganinsa cikin shiri yasa Baffa watso mishi tambaya
"Harisu tafiyar ce?"
Haris ya danyi murmushi kai da ganin idanunsa kasan bai samu wadataccen bacci ba
"Tafiyarce Baffa,akwai ayyuka masu yawa da zanyi a yau in sha Allah."
"Toh madallah,game da zancen da kazo dashi kuma fa?"
Yaji ransa ya b'aci tunawa da batun aurensa da Baby wanda ya k'ak'abawa kansa,
"Baffa na baku nan da karshen sati,duk abunda kuka yanke in sha Allah zan dawo sai naji."
Ya jinjina kansa
"Ai shikenan,lallai kuma ka gayawa iyayenka maza ina bukatar ganinsu idan zaku dawo ku dawo tare. Allah Ya tsare hanya. Ka shiga kuyi sallama da aminin nawa ko?"
"Amin." Daga haka Haris ya fice batare da yayi na'am da zancen baffa na karshe ba,bayan ya yiwa mutan gidan sallama ya fita,yan matan da bai zab'a ba kenan!
Yana sane ya share batun zuwa gidan liman,ya tayar da motarsa wacce tun jiya da yamma yasa aka wanke mishi tayi k'al. Ya zauna kenan yana kokarin daura seat belt ya hango wata sark'a a k'asan mazaunin kusa da direba. Hannu yasa ya dauka,ba shakka sark'a ce da baby ke ado da ita a k'afarta. Zuciyarsa ta d'an sosu,ji yayi kuma yana kewar rashin abokiyar hira a kusa dashi. Saidai tunawa da yayi da kanwarsa da halin da take ciki yasa yayi azamar ajiye sark'ar a saman kujera ya kunna karatun kur'ani mai girma yayi ribas ya d'auki hanya...sai Kanon Dabo.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(49)
"Ya akayi Kabir?"
Ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya cikin jin dadin muryar daya jima yana kewarta.
"Idan da abunda yafi tashin hankali da matsanancin damuwa tsanani,toh kin sanyani a ciki Babyna. Nayi mugun kewarki har na zama tamkar zararre wanda hakan ke nema ta shafi mu'amalata da kowa da kuma aikina. Where have you been for so long? Kinsan irin halin da na shiga?"
Ta numfasa cike da takaicinsa,ita kam yanzu haushi ma yake bata,ta dan ja karamin tsaki
"Banson takura ne Kabir,na d'anyi tafiya bana zaton dawowata nan kusa ma."
"What?!!"
Ya fad'a da k'arfi yana mikewa zaune daga kishingid'ar da yayi a daya daga cikin kujerun na babban airport dake birnin tarayyar Abuja,alokacin yana shirin zuwa Kano ne domin amsa kiran iyayensa duk akan matar da sai daga baya ya gane rashin kyautatawarsa gareta. Yayi kokarin saita kansa ganin yanda mutanen wajen suka zubomishi ido gaba daya. Cikin tattausar murya yace
"Meyasa kikeson tayarmin da hankali babyna? Jikina ya bani kina tare da wani shegen shiyasa kika chanjamin. Wai me yake baki? Me kuma yake maki da bana iya kokarina wajen yi maki?"
Hawaye suka surnano daga idanuwan Baby,ba wai na wani abu bane sai jin tsanar kanta da kanta. Wai har itace yau ake gayawa haka? Karuwa ta gaske ake daukarta. A fusace tace
"Nabar wannan rayuwar kabir! Bana tunanin daga yau zaka kara ganina ballantana akai ga kaji muryata! Bakai ba,kowanene nabarshi har abada na gane wannan rayuwar ba rayuwa ce..."
Dariyar daya sanya kamar wani zautacce yasa Baby tsayawa cak, hakazalika mutanen dake zaune tare dashi suka zubamishi ido domin zuwa lokacin baiko damu dasu ba.
"Karya kikeyi?! You can never live without me baby! Ke d'in tawa ce, baki isa kiyimin YANKAR KAUNA ba! Dani dake babu mai rabamu,kuma ki sani, ina nan ina jiranki. Ki ajiye a ranki baki da miji sai ni! Saina aureki kota halin k'ak'a sai na cigaba da gabatar da rayuwa dake!"
Ta katse wayar gaba daya a fusace ta fiddo sim ta tauneshi ta furzar. Kawai sai ta durkushe ta fashe da kuka.
"Adda menene?"
Maganar Humaira ya ankarar da ita a inda suke, ta share hawayenta ta mike tana kokarun kakalo murmurshi
"Bakomai kanwata,muje."
Tafiya takeyi saidai komai na kalaman kabir yana dawo mata,taji ta tsani kanta. Inama za'a maido hannun agogo baya,inama inama zai zamana wannan kaddarar zata shafe a tarihin rayuwarta. Kai inama ace Abbanta bai auri Raliya ba har ma hakan yayi sanadin fad'awarsu ha'ula'i. Haka tayi ta tunane tunane jikinta babu laka har suka iso gidan auren Mamma. Baki ta saki ganin makeken gidan wanda bata taba zaton anan Kazaure za'a samu gida mai kyawun fasali kamar na turawa ba. Humaira ta katseta tana jan hannunta
"Nan ne gidan fa Adda."
Wata yarinya suka soma cin karo da ita tasha d'amara,ta cika eyeshadow a saman idonta,ga kuma jan baki data maka. Lukuta ce ta gaske,tana tsallenta kamar ba budurwa ba tana b'alla rake. Ganinsu yasa tayi d'if tana bazo ido. Kafin ta washe baki ganin Humaira
":Yar Humeme,wacece wannan kamar baturiya?"
Baby murmushi kawai takeyi ganin yarinyar,kamar dai tana da matsalar yarinta amma irin wannan kwalliyar ai an bar yayinsu.
"Addana ce, daga birni."
Yarinyar ta cuno baki. Wani saurayi mai shekaru sha takwas ya iso wajensu yace
"Kedai kam Safiya bazaki bar shiririta ba,inace anti tace ki tafi gidanku kibar fitowa idan kaka tana bacci? Wannan yar birni ce,kinga ma yanda ake kwalliya ba irin naki ba."
Ya karashe suna dariya har baby wacce abun ya bata dariya,wacce aka kira da Safiya ta murguda baki ta k'ara b'antalar rake
"Oho dai,Ali nuhu ma kansa yace mata suna kauye."
"Yauwa d'an k'arasa mana."
Ta harareshi tayi gaba tana tsalle tsallenta tace
"Akwai wanka."
Ta fice, saurayin ya dubi baby sukayi dariya. Ya dan russuna ya gaisheta gami da tambayar wanda take nema. Kafin ta bashi amsa humaira ta cafe
"Yaya Nura,addana ce ta Kano."
Ya kalli humaira ya kalleta,tabbaa yaga kama ya kara washe baki
"Yaya tasleem,right?"
Ta lumshe ido hadi da jinjina mishi kai lokaci daya. Ai sai ya sheka da gudu
"Kai ka kai,amma yau ni zan soma kaiwa antinmu albishir."
Jin haka Humaira ma tabi bayansa a guje. Dariya baby tayi ta mara musu baya tana mai zumudin yin tozali da mahaifiyarta....
******
Haris cike da mamaki ya dubi Yasmeen bayan sun keb'e a farfajiyar gidan inda tayo mishi rakiya zai koma ofis lokacin karfe ukun rana.
"Ashe kina da hankali har haka little? Kwarai banyi tsammanin zaki iya b'oyewa iyayenmu ainahin abunda ya had'aku da KB ba."
Yasmeen tayi murmushi mai ciwo
"Bari kawai yayana,wallahi inason Yaya kabir kai kanka shaida ne. Gani nayi a yanda kawai Daddy ya dauki zafi jin cewar yace na dawo ba tare da wani dalili ba(kamar yanda ta fad'a musu kenan don kare mijinta),kar kaso kaga yanda ya fusata sai faman bud'e wuta yakeyi. Ya kake tunanin idan sunji har marina yayi akan karuwarsa? Ba yanda za'ayi nayi gangancin da za'a rabani dashi. Kaima ina rok'onka don Allah kada ka nunamishi kasan zancen."
Ya kara tsintar kansa da kauna da matsanancin tausayin kanwar tasa, shi kuwa ya za'ayi yayi gangancin barin Tasleem ta ruguza farincikinta? Bazai yiwu ba. Ya numfasa
"Baki da matsala dani little,saidai ina rok'onki da ki rage son d'a namiji har haka kada ya zame maki babbar matsala fiye da yanzu. Ki cigaba da addu'a Allah Yayi mana magani. Bari na tafi, Abba yana jirana."
Ta tareshi
"Af,baka sanarmin wacce ka zab'o mana matsayin antin tawa ba? Kodai zatona ya zama gaskiya,Zahra ce?"
Yayi murmushin dole
"No.. Baki canka ba."
Ta dan nuna damuwarta,ganin ta bude baki zata k'ara magana ya bude motarsa ya fad'a
"Ke kyaleni kinji ko? Sai mun dawo da yamma."
Daga haka ya fice, taso taji kowace mai sa'ar ce tayi nasarar samun namiji irin Haris? Da ace KB yana da kyawawan halaye irin na Haris da ta bugi kirji ta kira kanta mai sa'a. Saidai abun takaici ya zamana bashi da hali.....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(48)
Fuskarta ta bayyana tsananin damuwa da mamakin jin cewar wai
Haris da take zaman jira su karb'i lambar juna ya koma Kano.
Menene haka Haris yayi mata kodai mantuwa ce yayi? Inna dake
lura da ita tace
"Kin shirya zuwa gaida malam husseini daga can ki wuce gidan
mahaifiyarki,kuma kin cire mayafi kinyi zaman dirshan daga samun
labarin tafiyar Harisu. Kina nufin bazaki ba saboda shi?"
Baby ta kalli kanwarta humaira wacce duk ta shanye janbakin data
shafa mata a lebba kafin a sanyaye kuma ta janyo mayafi
wadatacce wanda ta dauka cikin kayan mamma data barsu a dakin.
"Banji dadi bane daya wuce batare da munyi sallama dashi ba.
Amma ba hakan na nufin bazanje ba. Taso muje Humaira."
Ta dauki wayoyinta fuskarnan ta baby babu walwala ta zura
takalminta mai tsini wanda sanyasu har sun zame mata jiki. Inna
dai takalmin take kallo cike da mamaki kodayake ta lura duk
takalma uku data zo dasu haka suke da tsinin dunduniya. Ta kasa
dai hakuri ta tofa
"Wai Tasleem baki tsoron wadannan takalman su karya maki
k'afa?"(Kamar dai yanda kawata Ummu Abdool ta sanya ta fad'i
cikin taron mutane koda yake farkon zuwanta birni ne👌)
Baby tayi murmushi
"Inna ai na rigaya na saba,inajin dadinsu sosai."
Inna ta tabe baki
"Oh,duk wannan tsawon naki neman k'ari kikeyi. Toh Allah Ya
tsare,sai kun dawo."
Ta amsa kafin ta fita rike da hannun Humaira wacce ta rigaya ta
mamaye zuciyarta.
Tayi mamakin samun Malam Hussein din tare da Liman a falonsa.
Ashe ma yana gidan? Suna ganinta fara'arsu ta k'aru inda Liman
yace "Ga jikar taka ai."
Cike da ladabi ta gaishesu suka amsa,Malam Hussein ya sanya
mata albarka kafin ta mike tayi musu sallama ta fita.
Duk da hakan saida ta nufi gidan ko Allah zaisa ta hadu da wanda
zai bata lambar Haris.
******
Alhaji Aliyu Hussein(mahaifin Haris, su shida iyayensu suka haifa.
Shine d'a na farko namiji,sai mace mai bi masa ta rasu, sannan
Kawu Usman,Kawu Bilal da autarsu Hajiya Barira dake aure a garin
Maradi,jamhuriyar Nijar da kuma Hajiya Mariya(mami,mahaifiyar
Kb)
Gaba dayansu mazan idan an cire Abba dake kano,suna zaune ne
anan gidan kowanne da bangarensa.
Fa'iza,Habiba 'ya'ya mata ne ga Kawu Usman,manyan mazan su
uku ne. Yasir,Abdulmalik(Babban yaya) da Faisal
Rahina,Badiyya da Atika 'ya'ya matane ga Kawu Bilal,rahina tayi
aure sauran Badiyya da atika wadanda sukayi candy. Bashi da d'a
namiji.
Sai kuma babbar diyar Hajiya barira ta fari kafin tayi aure na biyu ta
koma Nijar da zama,Zahra. Wacce ke a hannun kakarsu uwargida
kuma amaryar Malam husseini,Hajja Kubra.
Kyawawan yan mata saidai na wata tafi na wata,hakan bai hanasu
sakin baki wajen kallon wacce suka tabbatar ta ketaresu a komai
ba,wacce kamshinta mai sanyi ya soma ziyartar hancinsu kafin
kyakkyawar surarta ta bayyana a gabansu gami da zazzak'ar
muryarta wacce tayi musu sallama da ita.
Gaba daya kuwa yan matan sun had'u suna masu jimamin tafiyar
Haris wanda bai zab'i d'ayansu ba. Kada ma Zahra taji
labari,yarinya mai tsananin kunya da kawaici saidai a k'asan ranta
ba k'aramin so take yiwa Haris ba. Abunda batasani ba,daman Haris
a farko kafin yazo ya kudurtawa ransa matukar anyimishi dole ya
fito da mata cikinsu toh hakika yafi ganin dacewar zab'ar Zahra. Ya
lura akwai nutsuwa da tarbiyya tattare da ita duk da dai sauran ma
akwai saidai basu da kawaici kamarta. Ko jiya da suke shawagin
nan bai ganta ba saida yasa aka kirata suka gaisa. Wannan ba
karamin dadi ya yiwa Hajja Kubra ba ganin matukar dacen data
hanga tsakanin Haris da Zahra. Hakan yasa ta kudurta yiwa Malam
zancen.
Bayan gaisuwa ta sanar dasu itace tasleem. Zahra ta tareta da
murmushi
"Wow,kece d'iyar gwaggo maryama ta Kano ko? Duk sadda naje
gidanta bamu da hira sai taki. Tabbas kinyi kama sosai da
Humeme."
Kasancewar haka take kiranta,sukayi dariya gaba daya. Bayan
gama gaisuwarsu ta nemi gaisawa da Hajja Kubra,har cikin dakinta
Zahra ta jagorance ta,itama ta nuna murnar ganin Tasleem a karshe
sukayi sallama. Ta sanya Zahra yi mata rakiya sauran sashen kafin
ta dubeta har lokacin tana murmushi haka kawai taji Zahra ta
burgeta.
"Nagode 'yar uwata,bari na karasa gidan Mamma."
"Lah bazaki shiga gidan Malam Ibrahim ba?"
Cikin rashin sani tace "Waye hakan?"
Zahra tayi dariya "Mahaifin amininin Kawu Abba ne dake garin
Kano. Kawu Abba kuma mahaifin Yaya Haris ne."
Jin wannan bayanin,Tasleem ta jinjina kanta,ta hakikance gidan
kakannin KB kenan. Gidan yana kallon juna dana kakannin Haris
suka shiga.
*****
Matansa biyu,Hajja Badi'atu da Hajja Atine. Yaransa tara cif. Hajja
badi'atu tana da biyar yayinda Hajja Atine keda hudu.
Alhaji Idris(Babangida),mahaifin Kb shine babba. Sai Safinatu,
Aisha(mahaifiyar Haris),Bello,Abdulmalik(Baba karami). Ya'yan
Hajja Badi'atu kenan. Matan duka suna gidan mazajensu. Mazan
kuwa idan an cire Daddy suna nan agidan da matansu da yaransu.
Hajja Atine kuwa,Garba,Fatima,Hafsa da Zakari. Suma duk sunyi
aure sun hayayyafa.
******
Babu inda Zahra bata shigar da tasleem ba,a inda Tasleem ta rasa
ma da wanda Kb ke kama tsakanin iyayensa. Idan ta hangi
kamanninsa da Hajja badi'atu saita hango da Malam ibrahim.
Karshe Tasleem ta yiwa Zahra godiya suka kama hanya da
kanwarta wacce tayi wayon sanin gidan mahaifiyarta."
Sai lokacin ta kunna wayarta,da kamar mintuna biyar kiran Kb ya
shigo. Wannan yasa dole ta dakata a gefen wata bishiya domin
amsa kiran nasa....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(50)
Hankalinsa idan yayi dubu ya tashi,Allah Allah yakeyi jirginsu ya tashi yaje ya nemi inda baby take ya dauketa koda ta halin k'ak'a ne. Shaf ya manta da dalilin zuwansa Kano akan matarsa ce,ana kiran masu tafiya Kano yayi zumbur ya mike yayi gaba.
Baby tana neman rainamishi hankali,shi kam bayajin zai iya rabuwa da ita a yanzu. Ko me za'ayi saidai iyayensa su amince su aura masa ita koda na watanni ukun ne yanda kungiyarsu tace idan yaso daga baya zai san yanda zai fiddata cikin shaid'anin kungiyar nan.
******
Da gudu ta isa ga Mamma wacce ke tsaye tana sauraron maganar Nura da humaira duk bata gama yarda dasu ba. Jin tasleem a jikinta tana kuka yasa ta tsaya cak,itama hawayen ne suka cika idanunta. Sallamar dattijon ta katsesu,duk suka waiga suna amsawa. Yayi tsai ganin bakuwar fuska,kafin ya jefo tambaya,nura ya amsata
"Adda tasleem ce fa Dad,'yar anti ta birni."
Fara'arsa ta k'aru,fari fari ne da silkin bak'i,dogo ne yana da jiki. Ganin Mamma ta nufeshi gami da amsar ledar hannunsa a ladabce ya fahimtar da baby lallai shine mijin Mammanta. Murmushinta ya fad'ad'u itama had'e da hawayen farin cikin ganin irin sauyin da Allah ya yiwa mammanta. Tun kafin yakai ga k'araso kusa da ita ta zube gwuiwoyinta k'asa ta gaisheshi
"Ina kwana Kawu."
Ya mikar da ita ta hanyar riko hannunta yana 'yar dariya
"Ashe bazaki bani matsayin uba ba tasleem? Toh ni kuma na daukeki matsayin d'iyata tun kafin na sakaki a kwayar idona. Kiyi kirana da Dad kema amma banjin dadin uncle dinnan."
Mamaki ya kamata tana dariyar farin ciki,kawai saita fashe da kuka,ashe wataran zata samu wannan soyayya irinta uba? Alhamdulillah.
Dad ya katseta ta hanyar duban Mamma fuskarsa ta cika da farin ciki
"Yau duk abunda za'ayi a gidan nan na fannin girke girke da shaye shaye ya zamana yazo daidai da ra'ayin d'iyata kada ayi abunda bataso."
Daga haka ya dubeni
"Menene abun kuka my daughter? Sai kisa naji kamar bakyayin uban dani."
Tayi azamar share hawayenta ta dubi mamma wacce murmushi kawai takeyi tana kallonta kafin ta maida dubanta ga Dad
"Ba haka bane Dad,kukan murna nakeyi."
Ya dafe kanta cikin murmushin yace
"Ya isa hakanan kada yayi yawa kuma. Bari na shiga ciki."
Ya mike ya nufi sama. Baby ta zauna saman kujera tana dariya tace
"Mamma nayi maki murna."
Ta harareta kadan,nura yaja hannun humaira yana fad'in
"Yar kanwata zo mu amso alawa wajen Dad."
Suka haye saman tare,Mamma da Baby suma saman suka nufa d'akin Mamma.
Ta dubi hannun diyarta
"Ya naga kamar hannun naki a kumbure?"
Ta d'an dubi hannun,ashe fa dazu da zatayi wanka ta fidda bandage din,ta dan tabe baki kadan
"Buguwa nayi kuma har yanzu yanamin zafi kadan kadan. Amma da sauki,mamma ya sunan dad din nawa? Ke daya ce a wajensa ne? Waye wannan nuran shima d'anki ne?"
Mamma tayi dariya
"Tambaya uku lokaci d'aya?"
Baby tayi dariya itama
"Allah kuwa mamma ke d'ince duk kin chanja kin k'ara kyau kamar baki da kishiya."
Ta fada don a zatonta wannan katon gidan bazai yiwu ace mata daya ciki ba. Kuma daman a baya gwaggo Hajara ta fadamata yana da iyali.
"Kema kinyi chanjawar data bani mamaki tasleem,kamar ba 'yar makaranta ba anya kina karatun ma?"
Mamma ta fada tana binta da kallon zargi. Tasleem ta diririce sai kuma ta basar da sakin 'yar dariya,mamma tayi tagumi ganin d'iyartata harda b'ulin hanci haka kawai jikinta yayi sanyi duk da tasan kwalliya ce.
"Kai mamma,muda muke karatu. Kuma fa shekara nawa rabonmu da juna kinga dole fa na chanja maki. Don Allah gayamin mamma."
Mamma ta sauke ajiyar zuciya
"Alhaji Kamal Hassan sunansa,kafin ya aureni yana da mace guda daya,Hajiya Aisha. Tana da yaranta manyan maza biyu,suna karatu a turai,sai budurwa d'aya,tana aure a Minna. Sai kuma nura wanda a wajen haihuwarsa Allah Ya dauki ranta. Tun bayan rasuwarta Alhaji yak'i aure har Allah Ya kawo mutuwar aurena ya amince zai aureni bayan da yazo gaida Liman ya ganni yace yana so. Humaira sunan matarsa taci muke kiranta hakan. Kinji tambayarki. Inaso kema ki amsamin tawa tambayar. Menene ainahin abunda ke faruwa? Jikina yana bani akwai abunda keda Abdullah kuke b'oyemin,hakanan nayi mamaki don ko d'azu munyi waya dashi bai bani labarin zuwanki Kazaure ba. Ya cemin mahaifinki na kwance tsawon watanni biyu baijin dadi shine ke d'awainiya dashi,duk sadda na tambayeshi ko kinzo dubashi daga makaranta sai ya hau yimin kame kame. Tasleem ko bakwa jituwa da yayan naki ne?"
Zufa ta karyowa Tasleem,gabanta ya hau dukan uku uku. Shigowar Nura da sallama itace ta ceceta
"Anti kizo inji dad."
Mamma tayi azamar mikewa
"Ina zuwa."
Tayi gaba wanda hakan yasa tasleem sauke ajiyar zuciya. Amma rashin gaskiya ma baiyi ba.
Hawayenta suka kwaranyo,wannan wane irin bala'i ne haka? Ita kam ko za'a kasheta bazata fadi komai ba ko don gargadin yayan nata ala barshi shi da bakinsa ya fad'a d'in. Waya ce ta soma k'ara,ta duba taga mai kiran. "Abdullah1"
Bata d'aga ma ta ajiye. Har yayi ya katse. Haka ya jera kira har uku shiru sannan ya hakura. Tana nan zaune tana tunane tunane har Mamma ta k'ara shigowa tare da Humaira. Ganin wayarta na blinking ya fahimtar da ita anyi kiranta ne. Ta dauka ta duba,murmushi tayi mai ma'anoni tana duban Tasleem wacce ganinta yasa ta d'agowa daga kwanciyar da tayi idanunta bai bar fidda ruwan hawayen ba.
"Ko yanzu kadai maganata ta fito."
Ta zauna tana mai daure fuskarta tamau ta zauna kan gadon
"Humaira tafi wajen gwaggo kuyi hira."
Ba musu yarinyar ta fice a guje,tasleem kallo daya ta yiwa mahaifiyarta tasan babu wasa a tattare da ita
"Baki da wacce ta fini duk duniyar nan,baki da wacce zaki kaiwa kukanta a duniya ta baki shawara wacce ni bazan iya baki ba. Tun rabuwata daku bana bacci mai dadi tasleem. Ga yawan mafarkai da nakeyi da lamuranki,haka kawai hankalina bai kwanta ba akan irin rufeni da Abdullah ke yawan yi idan na tambayeki. Ki fito ki gayamin hakikanin halin da rayuwarki ke ciki,naso na dauko ki alokacin da RALIYA ta rasu saidai kuma hakan bai samu ba sakamakon Abdullah daya cemin karatu kikeyi nima kuma alokacin Allah baiyi zanje gaisuwar ba. Wai menene ainahin abunda ke tafiya dangane dake?"
"Raliya ta rasu?!! Ta maimaita a fili cike da tsananin mamaki. Tuni hawaye sun wanke fuskar Mamma
"Baki kyautamin ba keda yayanki Tasleem,tambayarki ta kara fad'armin da gabana. Mutuwar Raliya baki da masaniya akai,rashin lafiyar abbanki baki sani ba,haihuwar yayanki da takwarar daya samar maki nan ba baki da labarinsa. Wannan wane irin al'amari ne mai d'aure kai? Tasleem ko guduwa kikayi daga gidan mahaifinki kika kasa hakuri har komai ya wuce??"
Kawai sai baby ta fashe da kuka,toh ya ta iya? Mahaifiyarta ce fa.
"Bazakiji komai daga bakina ba wallahi sai kinyi kiran yaya abdullah garin nan. Sai mun hadu mu uku sannan zanyi maganar dake bakina."
Mamma tayi shiru tana kallonta har na tsawon mintuna kafin tayi azamar daukar wayarta tayi kiran Abdullah. Ya dauka ya soma gaisheta gami da tambayar ko lafiya ya kira ba'a d'aga ba?
"Bana dakin,kanwarka ce a ciki."
Bai taba kawo tasleem take nufi ba,a zatonsa ma Humaira ce. Mamma ta katseshi
"Duk abunda kakeyi inaso ka ajiyeshi abdullah,gobe kazo kazaure inason ganinka."
Yayi tsai kamar mai tunani sai kuma a sanyaye yace
"Lafiya dai mamma?"
"Lafiya lau,kazo dai nace."
"Shikenan,in sha Allah ina nan tafe goben."
Sukayi sallama. Mamma ta mike bata kara cewa komai ba ta fita. Ranar basuyi wata hirar arziki da diyarta ba kamar a farko ba itace ke d'okin ganinta ba......
*****
Gaba daya sun hadu a babban falon Daddy ciki kuwa harda Kb.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(51)
Abba ne ya soma magana cikin nutsuwa
"Kabir."
Cikin sussunne kai ya amsa
"Na'am Abba."
"Jiya yarinyar nan muka ganta kwatsam ta dawo a motar kasuwa,koda muka tambayeta tace kaine kace ta dawo ba tare da ita kanta tasan dalilinka ba,gashi mun taru munason jin hakikanin matsalar data had'aku. Me tayi maka da zafi har haka?"
Kabir ya saci kallon Yasmeen wacce akaci sa'a ita d'inma kallonsa takeyi. Kauda kai tayi gefe,jikinsa ya k'ara sanyi, ga kunya data dabaibayeshi. Toh me zaice? Lallai Yasmeen ta barshi a tsaka.
"Wai bakaji ne ana magana sakaran banza da wofi!"
Cewar Daddy cikin fusata. Yasmeen cikin kuka ta tare
"Wallahi Daddy laifina ne,fad'a yayimin ni kuma nayi fushi nayi tahowa wata. Don Allah kayi hakuri Yaya kabir,ka gafarceni bazan k'ara ba don Allah."
Haris ya runtse ido kansa a k'asa idanunsa sunyi jazur kirjinsa har d'agawa yakeyi saboda bacin rai. Ya saci kallon Kabir,duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a fuskarsa.
"Daman nasan kece marar gaskiya Yasmeen. Ni nasan d'ana bazai wulakantaki ba.." Cewar Abba.
"Kada kayi saurin shaidar mutum mana Aliyu,idan anbi ta b'arawo abi ta mabi sahu. Alamun wannan shashashan sun nuna bashi da gaskiya. Idan ba haka ba kayi magana mana."
Kabir ya daure kansa a k'asa yace
"Gaskiyane Daddy,laifi tayimin nayi mata fad'a saidai banyi tsammanin zai mata ciwo har haka ba ta taho Kano bada sanina ba. Na yafemaki kema kuma ina fatan komai daya faru ya wuce,kuskure ne."
Haris ya wurga mishi kallon raini,saidai baice komai ba.
Abba yace komai ya wuce,nan ya k'ara yi musu fad'a akan hakuri da juna daga karshe yace su bari zuwa gobe su juya Abuja.
"Na dawo kanka kai kuma,ya zancenka ya kwana?" Cewar Daddy.
Haris ya k'ara russunar da kansa
"Kamar yanda na fad'awa Daddy ne,Malam yace muje daku karshem sati yanason ganinmu ne."
Daddy da Abba suka dubi juna,kafin Abba ya jinjina kai
"Shikenan,Allah Ya kaimu asabar d'in."
Aka amsa da amin kafin su sallamesu.
Da sassarfa ya nufi wajen motarsa
"Haris!!"
Muryar KB ta dakatar dashi. Kamar bazai tsaya ba sai kuma ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Ya karaso ya jingina da motar yana fuskantar Haris.
"Nasan koda yasmeen ta boyewa kowa abunda ya had'amu,toh bazata boyemaka ba. Nayi laifi,please ka tayani bata hakuri."
Haris yayi mai wani irin duba yana d'aga girarsa kadan
"Ka kwantar da hankalinka dan uwana,yanda kaima ka shaidi Yasmeen da nuna maka soyayya tsantsa wacce ba algus hakika bazaka samu wata mishkila ba daga gareta..."
Jin taku a d'an nesa dasu ya sanya Haris juyawa kafin ya dubi Kabir yana murmushi wanda tuni KB ya fahimci can k'asan nurmushin nan bacin rai da haushinsa ne tsantsa.
"As i said,bazatayi fushi dakai ba koda kuwa zata kamaku turmi da tab'arya,ita d'in mai rufa asirinka ce. Sai kayi hattara KB,ba'a cutar irin wadannan matan a zauna lafiya."
Daga haka ya kama handle na motarsa zai bud'e,KB fuska daure ya matsa,daidai lokacin Yasmeen ta k'araso.
"Yayana tafiyarce?"
Haris wanda ke kokarin sanya key ya dubeta yana murmushi cike yake da tausayinta
"Tafiyarce kanwata,kada ki damu zan b'ullo kafin ku wuce. Hope bada wuri zaku tafi ba?"
Ya maida akalar tambayar zuwa ga KB,KB ya d'an tab'e baki
"Banajin da wuri zamu tafi, watakil ma sai zuwa jibi.."
"Meyasa? Kaga fa ban taho da wasu kaya ba sosai,kuma Abba yace lallai gobe mu wuce."
Ya watsa mata kallo kamar yayi magana sai kuma ya fasa, shi fa so yake ya nemi inda baby take. Ganin kallon da yayi mata yasa ta tsoraci fad'ansa tayi azamar cewa
"Yayana saida safen."
Tayi gaba da sauri saurinta,Haris ya dubeta kafin ya watsawa Kb kallo a wulakance,tuni idanunsa sun sauya
"Baby ce ke neman shiga rayuwar aurenka kb,right?"
Kb ya dubeshi a sanyaye,ya numfasa
"Hakane Haris, saidai wallahi bansan meyasa na tsinci kaina da mugun kaunar yarinyar nan ba ni kaina bazance maka ga...."
Figar motar da Haris yayi ne ya sanya Kb ja baya da sauri hakanan hon ya shigayi da karfinsa har Maigadi ya kammala bud'ewa ya fita. Yayi daidai da zuwan Abba da daddy. Abba ne zai shiga gidansa.
Ganin yanda Haris ya fita,Abba yace
"Kai Kabiru,menene ya faru?"
Kb wanda tunani da mamakin yanda akan yasmeen amintarsa da dan uwansa ke neman samun mishkila duk ta hanashi motsi,jin maganar Abba ne yasa ya juyo.
"Bansani ba Abba."
"Allah Ya tsare hanya toh. Matarka nace ta shirya kuje can gidanka idan yaso zuwa gobe saiku wuce Abujan."
Baiji dadin wannan hukuncin ba,saidai yasmeen ta biyashi data boye sirrinsa,tabbas idan yayi mata wani rashin adalcin bai kyauta ba. Ya amsa da toh kawai. Jimawa kadan ta fito suka wuce a mota sai janta yakeyi da hira ta basar dashi bisa hud'ubar mami da ta nuna mata ya dace ta d'an ja ajinta.
****
Da sallama ya shigo gidan,humaira aguje ta rukunkumeshi tana ihu
"Ga yaya! Ga Yaya!!"
Wannan yayi sanadin tashin tasleem dake bacci a falon sakamakon damuwa ta haneta bacci daren jiya da kuma shariyar da Mamma tayi mata tabar wani d'okin ganinta gaba daya ma ta chanja mata fuska.
Cak ya tsaya ita kuwa ta daure fuskarta tamau tayi azamar mikewa zata nufi falon sama,a guje yasha gabanta. Bakinsa na rawa,ya kasa gaskata cewar ita d'ince tsaye a gaban idonsa. Dakyar ya iya tab'a hannunta jin cewar ita d'ince yasa ya riko hannun hawaye sun wanke fuskarsa. Kawai sai ta soma kukan itama kafin ta warce hannunta tayi sama a guje har zuwa d'akin mamma da batanan tana dakin mijinta. Gadonta ta fad'a tana kukan tunowa da yanda yayan nata yayi mata korar kare daga gidansa. Muryarsa taji cikin kuka a kusa da ita
"Na rasa kalar godiyar da zan yiwa Ubangiji,da ace kin kara shekara baki dawo ba wallahi mutuwa zanyi ko nima a nemeni a rasa. Tasleem kin jefa yayanki cikin tashin hankali,nayi magana cikin fushi na zartar da hukunci ban tab'a zaton zakiyimin haka ba. Tasleem ina kika shiga? Ya za'ayi ni Abdullah na yankewa kanwata abar kaunata wannan hukunci mai tsauri. Ina sunan 'yan uwantakanmu? Wallahi kusan zaucewa nayi dana wayi gari naga da gaske kin gujeni...."
Mamma ya gani tsaye ta harde hannuwanta a saman kirjinta,hakanan ta zuba musu ido. Jin da tasleem tayi Abdullah yayi shiru yasa ta dago kai,taji k'arar rufe k'ofa wannan yasa itama ta dubi k'ofar. Mukulli mamma ta saka daman mijinta ya fita zuwa aiki,humaira tayi umarni ga gwaggo mai aikinta ta mik'ata gidan liman. Nura kuwa makaranta yake zuwa baya dawowa sai yamma sakamakon shirin jarabawar karshe na sakandire da yakeyi.
Gidan ya zamana daga Mamma sai yaranta mafi soyuwa azuciyarta. Fuska a daure ta zauna yayin data dubesu
"Ku zauna sosai."
Tasleem ta mike zaune daga kwanciyar da tayi,shima abdullah ya zauna gefenta a saman gadon,yayinda mamma taja kujerar gaban madubinta ta zauna idanunta a kansu. Ta dubi tasleem
"Kince sai yayanki yazo zaki fadamin abunda ya afku a rayuwarki ko? Yau kuma gani gaki,gashi muna sauraronki duka."
''YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(52)
Yau ba ranar boye boye bace, ita kam koda zata boyewa kowa matsalarta toh banda mahaifiyarta. Don haka ta russunar da kanta ta labartawa mamma halin data tsinci kanta tun rabuwarsu. Da kuma fyaden da Usman yayi mata wanda ya sanya mamma fashewa da kuka,Yaya Abdullah kuwa tsananin mamakin yanda akayi kanwarsa bata sanar dashi bane ya cikashi.
"Haba Tasleem,meyasa kiks boyemin magana har haka?"
Tayi murmushi duk da ruwan hawayen da take fitarwa
"Yaya baka nemi hakan daga gareni ba. A karshe ma saika kama maganar su Raliya ka yarda cewa na bawa wani budurcina. Haba yaya, wane talauci ne zaisa nayi haka?"
Ta ja majina kafin ta dora,haka har ta gangaro kan rayuwarta a hannun yayanta da kuma rud'in shaidan da yasa ta bawa rilwan jikinta da cikin data samu yayanta ya koreta. Haduwarta da Momi harma da barikancin data fad'a har zuwa taimakon da haris yayi mata bayan tayi hatsari da zuwansu nan. Hakanan bata b'oyemusu ko wanene haris ba saidai bata tonawa kb asiri ba.
Salatin da Mamma ta doka ne ya maido hankalinsu gareta,tuni kuma ta kife a k'asa sumammiya. Ihu tasleem ta fasa,Yaya abdullah kuwa yayi yunkurin fadawa bandaki ya debo ruwa. Baiyi wani jinkiri ba ya yayyafawa mamma amma ina bata motsa ba. Tasleem tana ihun kiran sunanta tana fadin "Mamma kimin aikin gafara,wallahi mamma ni ba 'YAR BARIKI bace yanzu. Mamma mutuwarki mutuwata ce..."
"B'udemin kofar nan da sauri."
Yaya abdullah ya fada lokacin da yake kokarin daukar mamma. Da gudu tasleem ta bude kofar,tuni yayo waje yana fadin
"Ki biyoni da hijabin mamma."
Ta wulk'a idonta,ta kasa gane hijabin ma kawai saita janyo farin abu dake rataye jikin hanger. Yaya abdullah ya ajiye mamma a baya jikinsa a sake yana kuka.
Ganin haka tasleem tayi azamar zagayawa ta shiga mazaunin direba ta tada motar. Da gudu maigadin dake kallonsu ya bude kofar ta fita shaf batajin radadin hannunta tama manta tana da ciwo saboda tsabar Firgicin da take ciki.
"Yaya ina ne asibitin,ka gayamin kada ka janyo mu rasa mamma."
Yayi ta maza ya dunga gwada mata hanya har suka iso. Da gaggawa aka amshesu akayi ciki da mamma. Tasleem kawai ta zube a bakin kofar ta hada kai da gwuiwa tana kuka sosai. Yayanta ya iso ya zauna kujerar dake gefanta,hakan ya bata damar kwantar da kai a cinyarsa
"Yayana na halaka!"
Ya dafa kanta ya shiga girgiza kai saidai ya kasa magana. Ta dago ta dubeshi
"Idan mamma ta mutu wallahi nima mutuwa zanyi. Rayuwata bata da amfani,dana sani da nadama sun dabaibayeni fin tsammaninka yayana,meya rud'eni da bariki? Menene shi? Mena d'and'ana cikinsa? Wallahi yaya abdullah rayuwata bata da amfani,wani wanda baida uwa da uban ya fini. Amma yayana kaima kasan bani da laifi ko? Khalid Ma'aruf waziri shine ya watsar dani. Bayasona,bai damu da sauke hakkin daya rataya a wuyansa a kaina ba. Wallahi bana sonshi,na tsaneshi nima. Bayamin fad'a,bayamin nasiha,ya kasa aurar dani. Na tsaneshi!!!"
Sai ta mike tana ihu kafin ta hau buga kanta da bango,yaya abdullah ya damk'eta a gigice,mutanen wajen ma sai salati sukeyi suna kiran lafiya kuwa? Kawai saita suma jikin yayan nata......!
''YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(53)
"Tasleem!!" Yaya abdullah ya fadi da k'arfi sannan ya dubi mutanen wajen gumi duk ya gama wankeshi hadi da hawaye kwance saman fuskarsa.
"Ku taimakamin don Allah."
Sai ga wata nos, tayi azamar kama tasleem ita da wata mace dake a layin ganin likita suka shiga ta kwantar da ita saman gado sannan ta kirayi likita. Nan suka soma kokarin ganin ta farfad'o.
Yana nan tsaye likitan dake tsaye kan mamma ya fito
"Alhamdulillah,ta farfado har ma tana nemanku. Kuna iya shiga,ina ita kanwartaka?"
Yaya abdullah ya numfasa yana hamdala kafin ya nunamishi d'akin da aka sanyata
"Ta suma ne amma likita yana tsaye a kanta."
Cikin damuwa likitan ya nufi dakin da baby take bayan ya damkawa abdullah takardar magungunan da za'a siyo ya kuma tabbatar mishi hawan jininta ne ya tashi amma da sauki,shi kuwa abdullah yayi azamar fad'awa d'akin da mamma take. Tana kwance ta kurawa silin ido,jin shigowar mutum yasa ta duban kofa kafin ta yunkura ta mike zaune,gaba daya tayi mugun sanyi ga hawaye na zubo mata. Abdullah ya zauna yana mai rike hannunta
"Sannu mamma."
Ta gyadamishi kanta kawai,kafin ta hau duban hanya, cikin rawar murya ta tambayeshi
"Ina tasleem?"
Ganin halin da take ciki yayi nufin rufeta,ta girgiza mishi kai
"Banda yau Abdullah,kabar k'ara b'oyemin komai ga rayuwarku. Idan ka boyemin taka,kada ka kara cutata da karemin damuwar diyata mace."
Hankalin abdullah ya tashi
"Ki gafarceni mamma,wallahi ban tab'a rufeki domin cutar rayuwar kanwata ba. Asalima bacin raine yasa na kori tasleem daga gidana wanda daga baya nayi muguwar dana sani bayan kuma da komai ya fito. Mahaifin rilwan ya sameni ya sanar dani batun wasikar,harma ya nemi a daura aurensu anan ne hankalinmu ya tashi."
Ya zame ya durkusa gwuiwoyinsa a k'asa yana hawaye jikinsa kuwa har kakkarwa yakeyi
"Ki gafarceni Mamma,bansan zan cuci rayuwar kanwata ba da ban aikata wannan mummunan laifin ba. Saidai ganinta da ciki ya rud'amin kwakwalwa har ma na kasa wani kwakkwaran tunani. Na tsoraci kada ta rusa aurenki ne,ganin da nazo nayi maki kina cikin kwanciyar hankali da walwalar dana jima ban riskeki cikinta ba mamma.
Bayan haka kuma ina...."
"Kiyi a hankali mana."
Jin muryar nos duk suka mayarda hankulansu ga kofar shigowar. Tasleem ce gaba dayanta a hargitse gashin kanta na usuli wanda bana k'ari ba duk ya barbazu a kafad'arta ko dankwalin babu. Ga bandaji da aka zagaye goshinta dashi sakamakon jinin dake fita daga goshin nata.Ta ja burki wanda ya janyo nos dinma tsayawa kafin kuma ta fita ta rufe musu kofa ganin kamar ba'a bukatarta a wajen. Kunya da nadama tsantsa suka kasa barin Tasleem k'arasawa ga mahaifiyarta. Meyasa alokacin data tashi yin wannan aika aikar na zina duk basu fad'omata ba? Babban tashin hankalin ma,mantawa da tayi da Mahaliccinta kuma alhamdulillah kullum cikin tuba take hakanan yanzu hakan ma haila takeyi. Zubewa tayi anan tana mai sanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana kuka kamar ranta zai fita.
"Astagfirullah! Astagfirullah."
Tayi ta maimaitawa har babu adadi,mamma kallo daya tayi gareta bata k'ara ba. Koda taji tausayin diyarta da kaddararran rayuwar da tayi a baya batajin zata iya saukowa a daidai wannan lokacin da bacin rai da tsoron tambayar da Allah zaiyi gareta akan amanar daya damk'a mata na d'iya babu abunda ke yawo a kwanyarta. Ta saki hannun abdullah bayan data dubeshi
"Maidani gidan mijina."
Wannan ya tsayar da tasle daga kukanta,a gaban idonta mamma ta kunce dankwalinta ta d'an rufawa jikinta tayi waje. Abdullah ya dauki takardar maganin ganin mamma na shirin fita tayi saurin rike kafarta
"Don Allah mamma ki yafemin. Nayi kuskure bazan kara maimaita irinsa ba."
Bata ko saurareta na ta janye kafarta tayi hanyar fita,da sauri abdullah ya ciro takalman kafarsa ya ajiye kusa da kafafunta
"Ki sanya Mamma,kada ki fita haka."
Ta sanya tana mai k'ara jin kaunar yaran nata a zuciyarta. Saidai kuma sunyi laifi gareta. Tabbas ta k'ara hakikancewa Dr. Khalid bashi da amana.
Suka fita, abdullah saida ya bari mamma tayi gaba ya bude mata motar ta shiga kafin yazo ya rarrashi baby itama ta mike tayi gaba sannan yaje ya share bill nasu,likitan yana kara jaddada mishi cewar a kula da abunda zai k'ara tab'a zuciyar mamma saboda blood pressure dinta kada yayi high.
A mota shiru,ba wanda ya cewa wani uffan tsakanin mamma da baby domin mamma zaune take a gidan gaba. Abdullah ya dawo
"Ki gafarceni mamma,na tsaya karb'o magani ne."
Batace uffan ba yaja sukayi gaba.
Suna zuwa gidan sukayi kicibus da Dad yayi ribas zai fito,ganinsu yasa shi komawa. Suka fito ya nufosu a gigice yana kama kafadun mamma.
"Maman nura lafiya dai? Maigadi ke sanarmin kuna asibiti dawowata kenan."
Ya dubi abdullah sannan Tasleem yayi mamakin halin da suke ciki.
"Ita kuwa d'iyata menene ya sami goshinta?"
Da sauri Mamma ta tare
"Lafiya,hawan jinina ne ya d'an motsa shiyasa suka kaini asibiti ba'a hayyacina ba. Bakaga yanda yaran naka suka rud'e ba?"
Baby ta amshe
"Dad buguwa nayi wajen sauko da mamma daga steps."
Ya danyi murmushi ya amince da hakan
"Wayyo sannunki diyata." Ya maida dubansa ga matarsa wacce kallonta ke mantar dashi komai
"Nagode Allah da ya ceci ran abar kaunata."
Daga haka yaja hannunta zuwa ciki yana sannu sannu ba iyaka. Baby ta daskare tana dubansa cike da sha'awa.
"Tell me now my sister,ta yaya zan bari matsala ta b'ullo tsakanin dad da mamma?'
Ta dubi yayan nata wanda ke magana cike da matsanancin damuwa hannunsa rike da ledar magunguna. Hawayenta suka cigaba da kwaranya tayi murmushi mai ciwo
"Babu."
Ya numfasa kafin yaja hannunta
"Inason mu zauna mu tattauna dake sosai."
Daga haka yaja hannunta suka mara musu baya.
Sam mamma tak'i bawa tasleem damar yin magana da ita a keb'ance. Tun magrib tayi sashen mijinta domin yace ta huta bayason ganinta a kicin. Shima can ya tare a wajenta. Abdullah yace mishi sai zuwa gobe zai koma.
Tana zaune ta idar da salla ta zubawa talabijin ido inda humaira ke kallon tashar Disney na cartoons zallah. Ta lula cikin tunanin wannan shariyar da mamma keyi mata,Abdullah ya zauna kusa da ita saman kujera yayinda take zaune kan darduma ta takure.
"Biyoni." Ta bishi babu musu har zuwa d'ayan falon dake jikin wanda suke. Bayan sun zauna ya dubeta......!
YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(54)
Saidai ya soma da bata hakuri laifin daya aikata gareta na korarta daga gida da kuma gargadinta da zuwa wajen mahaifiyarsu kafin yayi mata nasiha ya kuma nuna mata kurenta na rashin dacewar jefa kanta a karuwanci da tayi. Koda suka gangaro kan Mamma,ya shawarceta data koma gidan liman ta bari har zuwa sadda mamma zata sauko hakanan jininta ya daidaitu. Tasleem tayi na'am da wannan,saida ya kammala da wannan babin kafin ya kirayi sunanta wanda hakan ya sanyata dago kai ta dubeshi tana mai amsawa.
"Ya dace ki sassauta kiyayya ga mahaifinki."
Nan da nan ta daure fuska tamau,ya share kamar bai gani ba ya cigaba da magana.
"Mahaifinki a yanzu idan kika ganshi,kikaga yanda yake fama da ciwon sugar da hawan jini,zaki tausaya mishi saboda ramar da yayi tayi yawa,aikinsa tuni ya ajiyeshi gefe. Zakiyi mamaki idan nace maki kullum cikin zubar hawaye yake duk a dalilin rashin sanin takamaiman inda kike. Ban boyemishi dukkan abunda ya faru ba ya nunamin kurena,yace idan shi ya koreki ba'a hayyacinsa na meyasa zanyi wannan ta'asar? A karshe yace laifin nashi ne. Da ace bai koreki ba babu yanda za'ayi ki shiga wata rayuwa ta daban."
"Yaya bani labari mana game da abunda ya kawo chanjin Abba."
"Tun bayan tafiyarki da watanni uku, mummunan iftila'i ya fad'awa Usman na konewar babban shagon da baiyi ko wata biyar da bud'ewa ba,hakanan wasu b'arayin sun tareshi a hanya sun mishi duka har suka nakastashi suka kwace wayoyi da kudadensa. Abun mamaki kuma sati ba'a rufa na itama marigayi raliya akayi hada mata jini da majina a karshe aka watsar da ita a kofar gida. Jinyar da tayi kamar bazata tashi ba,gashi kuma wata kaddarar komai na Abba ya soma ja da baya Tasleem. Kamar wanda aka sanyawa hannu fitar ma da yake zuwa asibitinsa ya gaza. Hakanan raliya ta matsa mishi akan sai an fidda d'anta waje anyi mishi aiki saboda tuni matarsa tace bazata iya zama da nakasashshe ba ta ajiye mishi 'yar sa ta tafi. Akan dole Abba ya kashe makudan kudade wajen aikin kafar Usman ta hanyar fitar dashi waje saidai aiki baiyi ba wai a niyyarsu a sanyamishi kafafun roba saidai garin haka mutuwa ta riskeshi acan. Nan raliya ta hau ihu da zage zage,abun ne ya zame mata wajen goma ba. A gefe ga d'iyarta ta tsunduma kanta a harkar bin maza itama. Can kuwa nura ne ya kara lalacewa da bin mata. Matarsa ma ta gujeshi,hamza kuwa ya zamo mijin tace a wajen matarsa. Ke rayuwa fa tayi mata zafi ga mutuwar Usman,haka ta dawo ta rungumi jikokinta da suke a wajenta. Bata isa ta sanya Hamida da Hamid aiki ba suyi,kamar wata sa'arsu haka zakiga sunayi mata tsawa. Duk cikinsu,hindatu kadai ta fita daban,babu ruwanta ke sai kice ma ba daga jikin raliya ta fito ba. Nazo jana'izar Usman sannan na tattara na koma Abuja ina mai cike da dumbin mamakin ramar da Abba yayi sannan gaba daya duk yayi sanyi kamar bashi ba.
Wata biyu rabona dashi saidai nakan kokarta kiranshi na gaisheshi,wataranar juma'a ina zaune na dawo daga masallaci na amsa kiransa inda ya nemi nazo na sameshi da sauri. Ba shiri washegari na tafi a mota. Kuka sosai na samu Abba yana yi,cike da fargaba nikam na karasa wajenshi don gani nakeyi kamar zai yimin magana cikin fada fada kamar yanda ya saba. Ga mamakina naga ya rungumeni yana neman gafarata,yace a baya yakan damu idan yayimana wani abun ashe ba'a son ransa yakeyi ba Tasleem. Yace min ya iske raliya tana waya da bokanta inda takeso tazo ayi mata aikin da za'a kasheshi suci ragowar kudinsa saboda ta fahimci ya soma talaucewa ita kam bata tab'a ganin jinin sarauta mai bak'in jini kamar Khalid ba. Kowa gudunsa yakeyi yan uwan duk sun juyamishi baya saboda ganin shi kadai ne ba uwa ba uba.(Ta manta itace ta janyomishi tsanar,don akwai randa yayansa waziri yana son ganinsa yace bai zuwa. Kusan sati shiru har da kanshi wazirin yazo gidan,ganin babban mutum yasa maigadin budemishi dakin bak'i,yayita zaman jira amma raliya ta rike abba ta hanashi fitowa a karshe waziri ya fusata yabar gidan da alkawarin bazai kara shiga harkar Khalid na tunda bashi da bukatarsu hakanan ya gargadi dukkam zuri'arsu kada wanda ya k'ara lek'awa gidansa. Wannan labarin nima baba Maigadi ke bani,hankalina ya tashi don har gidan waziri naje na bashi hakuri ya sakarmin fuska sosai ya nunamin ai mu d'in nasu ne. Yace kuma zai sanya ayi addu'a sosai gareshi don bai amince da yanayinsa ba. Shima ya d'agawa mahaifinmu kafa ne har zuwa wani lokacin.
Abba ya cigaba da labartamin,yace tun sadda yaji wannan zancen yaji kamar bashi ba,komai na rayuwarsa ya daidaita,kirjinsa yabar nauyi. A ranar kuwa ya yiwa raliya abunda bai tab'a yinsa ba sakamakon tsanarta da yaji,duka yayi mata sosai sannan ya saketa. Tace wallahi bazata bar gidan ba,saida ya hado da jami'an tsaro har jikokinta yace duk ta tattara ta tafi dasu shi kam baisan menene ya kwasheshi ya auro wannan kaddarar ba. Hakanan ya kori nura wanda har ya nemi ya zageshi. Hindatu kam tasha kuka,ta hau rokonsa ya barta a wajensa itama ta tsani uwarta. Haka dai ya hakura yabar yaransa. Washegarin faruwar al'amarin ne yayi kirana yake sanar dani. Nayi godiya ga Allah da baisa zan mutu kafin wannan rana ba. Nan Abba ya tambayeni game da mamma,na bashi labarin komai har zuwa gidana da kikayi da sauransu. Anan ne nadama tsantsa ya kamashi. Tun dai daga lokacin ya kamu da rashin lafiya,karshe yasa na kaishi wajen waziri. Muna shiga waziri yana zaune a fada,yana ganin Abba cikin yanayin zubar hawaye yana nufoshi,tsam ya mike har na tsoraci ko marinsa zaiyi kawai sai ya rungumeshi wanda hakan ya bawa abba kuka sosai a jikinsa. Ya jashi inda fadawan suka mike suna zuba kirari,sukayi ciki. Kinji yanda aka sasanta,Abba ya tsanantawa su Hamid ya hanasu fita ko'ina ya santa ido sosai a kansu,ganin batanci da rashin maida hankalin Hamid a karatu zaiyi yawa yasa shi turashi makarantar horo. Hamida kuwa kasancewar tana tsoron abba alokacin ganin irin korar da yayiwa mamanta sannan taje taga muhallin da raliya take babu wani kayan morewa rayuwa dolenta ta nutsu,Abba yace ya bata sari ta fiddo miji ko kuma ya aurar da ita ga wanda yaso. Har nan kazaure na rakoshi ya roki gafararsu kafin ya koma kuma rashin lafiya ta hau shi. Yayimin fadan dalilina na boyewa iyayen mamma inda kike karshe abba ya hau yawaita addua da tsayuwar dare da kuma zubar hawaye duk saboda rashinki da alhakin daya dauka namu. Raliya kuwa gobara sukayi a gidan babu wanda ya tsira daidai da nura,sakamakon jonin wuta direct da Nura yayo musu acewarsa bazai iya rayuwa ba wutar lantarki ba ya gama zage mahaifiyarsu tas akan bakin cikin data janyomusu suna cikin daula. Karshensu kenan. Yanzu haka hamida tayi aure ga wani alhaji mai mata biyu har ta haihu,duk da wulakancin da take sha hakanan take zaman hakuri. Hindatu kuwa tana nan tare dani a Abuja ta soma karatunta a jami'a, hakanan Abba da nake jinyarsa saidai yanzun jikinsa da sauki sosai. Waziri ma ya matsamin na maidoshi gabansa inajin hakan zaiyi tunda shima Abban yace ya gaji da zama gidana saboda kunyar hasina. Duk da dai yanzu gidane na kashin kaina."
Tasleem tayi shiru,tabbas rayuwa abar tsoro ce. A sanyaye ta kara tambayarsa
"Ina labarin Ridwan kuma?"
Murmushi Abdullah yayi
"Allah Sarki,abbansa fa ya jima yana fushi dashi har korarsa yaso yi na hana. Amma yanzu yayi aure yana zaune acan London wajen uncle dinsa da matarsa Jidda. Yaransu biyu ma,daya taci sunanki dayar kuwa sunan mamansa."
Tayi murmushi kawai.
*****
Washegari yaya abdullah yana tafiya,itama ta shirya koda ta yiwa mamma sallamar komawa wajensu inna bata ko kalleta ba. Haka nan ta wuce a sanyaye.
Da la'asar Liman ya tura ayi kiranta.....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar
(55)
Bata kawo komai ba ta mike ta yafa mayafinta ta nufi dakin Liman jikinta akwai yanayin sanyi wanda tun dawowarta daga gidan mamma take cikinsa. Koda inna ta tambayeta ta amsa da babu komai.
Yana zaune yana duba wani littafi na hadisai yaji sallamarta wanda hakan yasa shi ajiye littafin a gefe yana mai amsawa fuska a sake. Ta shigo tana yamutsa fuska kadan kafin ta soma kokarin zama tana fad'in
"Nidai wannan tsohon kana neman matsamin fa,yanzu kuma menayi aka d'agoni bama a tarbeni da 'yar shila ba."
Yayi dariya
"Shak'iyiya,wanda kika ci bai isheki bane a k'aro maki gobe? Nutsu don magana zamuyi."
Ya soma da yi mata doguwar nasiha akan muhimmancin aure wanda tun daga haka tasha jinin jikinta,kirjinta kuma bai bar bugu da sauri da sauri ba. Saida ya kammala sannan ya bijiro mata da bukatarsa na neman amincewarta kan batun aurenta da Haris.
Cikin tsananin mamaki da fargaba ta dubeshi
"Shi Haris dinne yace yana sona baffa?"
Jin dadi game da amsar da zai bata yasa Liman yin wata 'yar dariya
"Shakka babu,harisu ne yazo da batun kamar yasan fatanmu kenan ni da aminina. Kuma munyi na'am da batunsa nasan bazaki watsa mana k'asa a ido ba kasancewarki yarinya mai biyayya."
Tayi k'asa da kanta,nan da nan abokan hirarta suka ziyarci fuskarta(hawaye). Ina ita ina Haris wai? Haris yasan abunda yake kuwa? Me zaiyi da sauran maza? Sam bazata bari ta cuci mai niyyar taimakonta ba,kai ta kasa gaskata da gasken shine yayi tayin auren nata.
"Kuyi hakuri bafamfa,bazan iya aurensa ba!"
Nan take annurin dake saman fuskarsa ya dauke,tamkar bai taba dariya ba ya koma Abdulmaleek Hussein dinsa sak!
"Nufinki zaki bani kunya ne Tasleem? Toh bari na fadamaki wallahi tunda nake da Aminina tun zamanin kuruciyarmu dayanmu bai taba zuwar wa dayanmu da bukata ba munyi watsi da ita. Baki isa ba Tasleem! Ko uwarki k'arya takeyi na nemi bukata awajenta tak'iyi,na takaice maki ma aminina shine ya wuce gaba wajen aurenta da Ubanki tun a farko domin a baya banso tayi nesa har haka ba. Ki tashi ki barmin d'akina,aure kuwa keda Harisu saidai idan anyishi ki mutu."
Daga haka ya maida fuskarsa gefe babu wata walwala a samanta.
A sanyaye tasleem ta mike tana k'ara mannewa da abokin hirarta harda sheshshek'a.
Kallo daya tayi mata kafin tabar murza robb a hancinta
"Lafiya kuwa?"
Cikin kukan dai ta labarta mata yanda sukayi da Liman,inna taja tsaki gami da fadin
"Allah Ya kyauta,ina goyon bayan Liman,wannan hukuncin yayi. Domin kuwa samun yaron mutunci irin Harisu a zamanin nan akwai wuya. Nikam dari bisa dari na amince kuma banga aibu da aurenku ba. Budurwa sharab dake,ai wallahi sai yanda kikayi dashi ta hanyar biyayya da kissar d'iya mace."
Ji tayi tamkar magana take yab'a mata,da sauri ta mike ra shuri takalmanta batayi wata wata ba ta fada gidan gwaggo Hajara bazata kwana a gidan ba. Meyasa Haris zaiyiwa rayuwarsa haka? Duk a zatonta jihadi yake niyyar yi don tausayinta batasan kudurin da Haris ke shirin yi ba. Gwaggo Hajara ma yabo da hamdala ta shiga yi,ai ita kam tun farkon ganinta da Haris takeso aure ya kullu tsakaninsu sai gashi Allah Ya amsa. Nan tayita lallashin tasleem gami dayi mata nuni akan illar bijirewa umarnin babba.
******
"Nayi zaton ai da Zahra za'a hadashi?"
Murmushi Malam yayi kafin ya bata amsa
"Ya kike wata magana kubra? Da Zahra da Tasleem basu da wani bambanci a wajena. Tunda yaro ya nuna yanason Tasleem sai a bisu da addu'a inajin hakan zaifi."
Ba haka taso ba sanin da tayi Zahra ita kadai take iya gayawa sirrinta,kuma ta tabbatar mata cewar tana son Haris. Bata hakura na dai ta k'ara muskutawa
"Malam fadamaka ne banyi ba amma hakikanin gaskiya Zahra banda alkunya ya hanata magana tana son Haris kwarai dagaske,mezai hana a had'a mishi su biyu duka a aura mishi na tabbata Harisu bazai watsa mana k'asa a ido ba."
Malam ya dubi hajja kubra a mamakince
"Harisun ya gayamaki yana da ra'ayin mata biyu da wurwuri haka ne?"
Ta girgiza kai,zatayi magana ya dakatar da ita
"Bazan hanaki abunda kikaga zaifi ba,saidai ni da kaina bazan tunkari Harisu da zancen ba. Ki tuntub'eshi da kanki idan yaga zai iya toh nawa bai wuce daura aure ba."
Ranta ya d'anyi sanyi jin hakan. Tana matukar kaunar Zahra,bata tab'a tsayawa kula samari ba sai gashi rana tsaka ta kamu da son Haris wanda har ta kasa b'oye mata ita kuwa mezaisa ta kasa yin wannan kokarin gareta?
"Shikenan Malam,Allah Ya zab'a abunda yafi alheri. Zan gwada hakan."
"Ameen." Kawai yace mata kafin ya nemi ta kawomishi furarsa.
******
Momi tayi wani murmushi kafin ta rausaya idanuwa
"Ka kwantar da hankalinka Kb,na tabbatar maka baby zata dawo. Bata komai saida shawarata. Koda ya tabbata auren zatayi na tabbatar maka da cewar zata nemeni bada jimawa ba. Nima ban sameta a waya ba,saidai nasan wacece baby tunda har ta furta maka tabar wannan harkar tabbas da gaske takeyi. Mu kuwa a sharuddan kungiyar,lallai idan mace zata bar harka sai ta tattaro mana dukkan kadarar data mallaka cikin harka idan kuwa ba haka ba zamu hanata auren gaba daya muyi sanadiyyar gurb'acewar dukkanin rayuwarta wanda nake da yak'inin Baby bazata iya ba. Yanzu kawai mu jirayi dawowarta."
Kabir ya jefa hannu aljihu ya zaro bandiran kudi 'yan dari bibbiyu har uku ya dire a kusa da Momy yana murmushi
"Ga wannan asha ruwa,burina ta dawo na ganta."
Tana taunar cingam gami da wani irin murmushi na duniyanci ta dauki kudin a wulakance tana juyawa kafin ta watsa mishi kallo tana fari da ido
"Bukatarka zata biya da zarar Baby ta dawo. Zanbi kowacce hanya don ganin ta amince da aurenka."
Ya shafi suma yana dariya kafin ya jinjinawa Momy
"Dakyau momynmu,anjima zanbi jirgi zuwa Abuja,sai naji wayarki."
Daga haka yasa kai ya fice yayinda Momy ta bishi da murmushi na musamman.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(56)
Kwance yake akan restingchair a farfajiyar gidansa daga can poolside. Idanunsa a lumshe fuskarsa ma'abociyar kyau da kwarjini sai shek'i takeyi. Yammacin juma'a ne,garin yayi luf luf sai wani ni'imantaccen iska ke busowa da kamshin k'asa kasancewar da safiyar yau din anyi ruwa sosai. Sanye yake da jar t-shirt,da wando wanda da kad'an ya rufe gwuiwoyinsa.
Sallamar isah mai gadinsa ne ya sanyashi bude idanunsa yana mai amsawa bayan yayi kokarin danne damuwar dake shimfide kasan ransa.
"Yallabai kayi bak'o yace a sanar dakai cewa Deen Bukar ne."
Jin sunan wanda ya jima baiji daga gareshi ba ya dago yana murmushi
"Kayi mishi iznin shigowa isah."
Matsakaicin saurayi ne,mai d'an kiba. Yana sanye da kananun kaya shima,kallo d'aya zakayiwa bak'ar fatarsa ka fahimci yana hutawa sakamakon lukui lukui da tayi. Ganinsa yasa Haris mikewa tsaye yana bayyana hakoransa a waje cike da farin cikin ganin oldclassmate dinsa na Malaysia. Deen Bukar. Rungume juna sukayi suna masu dariya kafin su cafke.
"Shegen sama,deen kana hutawarka,irin wannan k'iba kamar ba soja ba?"
Deen yayi dariya yana nunoshi da yatsa
"Zaka fara ko Gent? Toh ai kaine za'ace baka aikin komai. Ka ganka kuwa?"
Sukayi dariya kafin Haris ya dauki wayoyinsa da tab
"Bismillah."
Suna tafe suna hira har suka shiga falon Haris wanda ya k'ayatu iya k'ayatuwa. Haris yayi kiran kuku dinsa,Henry. Ya sanyashi ya kawowa bak'onshi abun motsa baki. Bayan tafiyar henry ya dubi deen
"Sai fa hakuri kasan abunka da gwauro."
Deen yayi dariya
"Kai ka sowa kanka,ya dace ka nemo mana mata musha biki. Gashi dai twins dinka(yaran deen) suna k'ara girma. Kb fa,ya labarinsa?"
Haris yayi dariyar yak'e
"Yana nan da bebinsa d'aya,Nasreen."
Deen ya jinjina kai lokacin Henry ya iso ya soma zuba mishi juice a kofi.
"Banji dadin rashin aurenka Gent,ko still now tsoron matan kakeyi?"
Haris yayi murmushi
"Aure lokaci ne Deen, sannan idan nace ma ina tsoron matan na yanzu ai ba laifi bane."
"Magana ta fito,kacemin kawai tsoronsu kakeyi."
Murmushin dai Haris ya k'ara yi kawai,shi kadai yasan matsalarsa. Duk sadda ya tunano da tafiyarsu kazaure a gobe damuwa kadai ke dabaibaye zuciyarsa.
"Last two months ai,inajin 5th of may ne,na hadu da wani kamar KB naka a Ni'ima hotel da wata baby. Naso nayi mishi magana duk da dai ina kokwanton ko shi d'inne tunda kaga bazan kawo har yanzu KB yana yayin wasu bebs din ba tunda he's married. Kafin ma nakai wajensu sunyi gaba,na rako oganmu ne wajen wani abokinsa. Saidai yanzu kace yana ina ma?"
Haris ya kara zuciya da lamuran KB, yana kara jin kwarin gwuiwar auren Baby don ya fahimci ita kadai ce yake tarayya da ita yanzu. A zahiri ya murmusa
"Hum, bana zaton shi ka gani dai,mutumin dake zaune a Abuja ba."
Deen ya tabe baki yana mai daga kafada kadan
"Zai iya yiwuwa."
Daga nan suka share zancen,zuwan Deen shi ya mantar da Haris damuwarsa sukayita hira yana bashi labarin yanda wasu rundunarsu ke fama da matsalar boko haram,bai bar gidan ba saida sukaci girkin henry. Bayan magriba ya wuce.
*****
Abdullah kuwa,koda ya koma Abuja bai rufewa Abbansa komai dangane da halin da Tasleem ta shiga ba. Abba yayi kuka kamar me a karshe yayi nadamar watsi da rayuwar yaransa da yayi wanda sanadin hakan gashi har karuwanci diyarsa wacce ta samu kyakkyawar tarbiyya tayi. Abdullah kuma ya sanarmishi da zancen aurenta da za'ayi da Haris din kamar dai yanda Baffa ya sanarmishi kafin barinsa Kazaure. Abba yaji dadi matuka musamman jin cewar Haris din da kansa ya amince zai rufawa diyarsa asiri yana sonta ba tare da kowa ya tilasta mishi ba. Sannan kuma ya d'okantu da ganin tasleem ko don ya nemi gafararta,amma Abdullah yace mishi ya saurara dai tunda can gidan basu san komai ba. Ya hadashi a waya da baffa ya nuna amincewarsa dari bisa dari ya kuma nunawa Baffa ai tasleem ikonsa ce. Baffa yaji dadi matuka,bayan hakan ne ma ya nemi tasleem yayi maganar gareta.
Wannan kenan!!
*****
RANAR ASABAR!!!!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(57)
Kabir yana zaune a falonshi bayan ya kirayi wayar
Momy har zuwa lokacin babu kwakkwarar
magana ta inda Baby take. Ya damu kwarai,har
abun yana neman shafar walwalarsa. Daidai
lokacin Yasmewn ta zauna tana amsa waya cikin
dariya ta karashe maganar data soma tun kafin
shigowarta da cewa
"Aa yayana,mudai kam kada a tsawaita mana
lokaci munason shan biki da wuri."
Ta danyi shiru a nishadance tana sauraron amsar
da Haris ke bata,yayinda KB ya mike zaune yana
zuba mata ido cike da dumbin mamaki.
"Toh Allah Ya tsare hanya,agaishemana dasu
Malam."
Daganan ta katse wayar ta ajiye.
"Sorry prince,abinci saura kad'an."
"Wane yayan naki ne zaiyi aure?"
Tayi mamakin tambayarsa,bata dauka koda wasa
baisan da zancen ba kuma ganin agabansa aka
danyi maganar tafiya kazauren a kano duk da dai
ba'a fadada zancen yanda zai fahimta
"Baka da labarin sanya ranar auren Yayana
za'aje yi Kazaure?"
Ransa ya baci jin tambayt daya kalleta matsayin
rainin hankali
"Da ina da labarin zan tambayeki ne?"
Ganin ransa ya baci yasa ta sanyaya murya
domin yanzu batason batamishi ko kusa
"Kayi hakuri,ganin yanda kuke dashi shiyasa nayi
zaton bazaka rasa sanin komai ba. Ni kaina
bansan cikakken zancen ba. Amma Daddy ne ya
turashi Kazaure zab'ar matar aure cikin yan
uwanmu. Kuma yanzu ya zab'a shiyasa Malam
ya nemi ganinsu gaba daya harma dasu Daddy
din."
Kb jikinsa yayi sanyi, me ya yiwa Haris da zafi
har haka? Duk irin shakuwarsa amma ya kasa
sanar dashi labarin aurensa? Ya jinjina kai kawai
baice uffan ba.
"Hadomin Coffee."
Ta mike ta fita itama din dai ta lura yayan nata
saboda abunda KB yayi gareta ne ya kullaceshi
wanda ba halinsa bane(wato kullata).
Shi kuwa KB wayarsa ya dauka ya kira Haris
dake shirin tayarda mota zuwa gidansu Daddy
don tafiya. Kamar bazai dauka ba sai kuma ya
dauka da sallama.
Kb ya amsa yana yar fara'a kafin yace
"Wani tsastsauran laifi nayi da har dan uwana
kuma aminina ya kasa sanarmin da batun
aurensa har haka? Inda aminci kamata yayi ma
ace a bakina Princess(yasmeen) zata soma ji ba
bakinka ba. Haba Haris,abun har yakai haka?
Allah ma munayin laifi gareShi ya gafarta mana
ballantana dan adam?"
Ya karashe a sanyaye gwanin tausayi domin
hakikanin gaskiya KB yana kaunar Haris kwarai
dagaske,kauna ce mai tsafta tun suna yara suke
yiwa juna. Jin yanda ya narke murya yasa Haris
sauka daga fushinsa,shima cikin sanyin murya
yace
"Dan uwan nawa ne ya kasa saita rayuwarsa,ya
kasa fahimtar hatsarurrukan dake cikin sab'awa
Ubangiji. Banda wannan babu wani abu dake
had'ani dashi."
"Oh come on my friend,tuni na watsar da wannan
hanyar wallahi. Just ita ke wahaldani ga kuma
fama da rashin sanin inda take amma daman
banda ita komai na watsar. Ka tayani addu'a."
Murmushi Haris yayi na mugunta
"Bakomai,itama zaka mantata har abada in sha
Allah. Zan tayaka addu'a. Barni hakanan,Daddy
suna jirana."
"Toh ango,yaya sunan matar.."
Kafin ya karasa Haris ya katse kiran yana
murmushi
"Da sauran lokaci Kb,bazan amince ka rusamin
komai ba."
Daganan yayi ribas ya fita kasancewar tun
shigarsa mota isah ya wangale gate din.
*****
Rashin samun wadataccen bacci da kuma
matsanancin kukan da baby tasha a daren ya
janyo mata ciwon kai matsananci da zazzabi
wanda ya sanyata lafkewa saman darduma tun
bayan sallatar Asubahi da tayi. Gwaggo Hajara
tayi shigowa dakin wajen sau biyar amma bata
tashi na gashi har rana tayi sosai domin lokacin
wajejan karfe sha daya na rana. Ganin bata da
niyyar motsawa ne,yasa Gwaggo tashinta
"Wai lafiyarki kuwa 'yar nan? Wane irin bacci
kikeyi hakane?"
Jin muryar Gwaggo yasa baby bude ido kadan,
ganin yanayin baby yasa ta taba wuyanta
"Ikon Allah wannan bandejin kuma fa na kanki?
Jiya dankwalin kanki bai barni na lura ba,ga
jikinki da zafi ashe masassara kikeyi baki fada an
nema maki magani ba? Bari na aika kemis din
Abdulaziz a amso maki magani. Kokarta ki tashi
ki sanya ko kunu a cikin naki."
Ta karashe tana kokarin mik'ar da Tasleem
zaune,dakyar ta mike tayi azamar rike kanta
sakamakon sarawar da yakeyi.
Ta daure ta wanko bakinta ta dawo tasha kunun
kadan,saidai fa tuni cikinta ya hau murd'awa
saida ta ruga bandaki ta amayar dashi tas!
Gwaggo na mata sannu. Bayan ta kamota sun
fito take fadin
"Haba jama'a,ana kokarin yi maki gata amma
kina facali da damarki? Harisu yaron arziki ai ba
abun gudu bane."
Ita dai tasleem batace uffan ba,da gwaggo zata ji
labarinta da bata amince da aurawa namiji irin
Haris 'Yar Bariki ba. Dakyae ta iya hadiyar
magungunan ta sha ruwa sai kuma bacci ya
dauketa a saman gadon bayan ta ja bargo ta
kudundune jikinta saboda sanyin da takeji yana
damunta duk da kasancewar rana ake kwalawa.
******
"Kace ashe harisun sun iso kenan?"
Tambayar da taji Gwaggo na yiwa wanda batasan
ko wanene ba. Tashinta daga bacci kenan,ba laifi
zazzabin ya d'an sauka saidai ciwon kan.
Batasam takamaiman karfe nawa ba saida taji
muryar Baharu na fadin
"Ya iso gwaggo,shiyasa Baffa yace nazo nayi
kiranta su gaisa."
"Toh ai shikenan,bari na gani ko jikin nata yayi
sauki."
Jin gwaggo na kokarin shigowa tayi saurin
mayarda idanunta ta rufe gabanta na bugu fat
fat......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(58)
Ta taba goshinta taji sanyi radau wanda ya
tabbatar mata da saukar zazzab'in. A nutse
gwaggo ta hau bubbuga kafarta
"Tasleem,tasleem."
Ta bude ido sannu sannu kamar mai baccin
gaske.
"Na'am gwaggo."
"Sannu ko? Ya jikin naki?"
"Alhamdulillah."
"Haka nakeson ji,maza daure ki tashi,Baffa ya
aiko kiranki ku gaisa da bak'i."
Kamar zatayi kuka tace
"Banjin dadi fa gwaggo."
Gwaggo ta hau lallab'ata
"Haba d'iyata,meyasa bazaki kasance mai hakuri
a rayuwa ba? Babu amfanin bijirewa maganar
manya. Ki tashi kije ai ba auren kikaga anyi ba.
Mu dage da addu'ar zab'in Allah."
Haka tayita kashe mata jiki da maganganu,Baby
ta mike ba don taso ba.
"Toh nidai ki sanya a daukomin akwatina sai nayi
wanka."
Gwaggo tayi dariya
"Ai shikenan babu komai d'iyata ta kaina. Shiga
kiyi abinki don ma kayana bazasuyi maki ba ai da
shi zan baki."
Murmushi baby tayi kafin ta soma kwab'e kayan
jikinta.
****
Ta fito wanka sai kuma ta rasa suturar sanyawa.
Manyan kayan daman kala biyar ne. Uku
atamfa,biyu kuma shaddoji suma kyautarsu akayi
mata. A karshe dole ta dauki daya cikin shaddojin
nan ta sanya ba don taso ba. Shaddar brown
ce,tasha surfani anyi mata riga fitet hakanan skirt
din yayi d'as a jikinta saidai hakan bai boye 'yar
ramar da tayi ba. Ta sanya dankwalinta tayi
dauri wanda ya rufe bandejin kanta,ta kudurta
suna tafiya zataje kemis a fidda mata.
Kai kuzo kuga baby acikin hadaddiyar shaddar
nan. Batayi kwalliya ba kwata kwata,toh auren da
bata murna da yinsa kuma ma me zata nunawa
Haris bayan shi d'in daban ne a komai. Ta fesa
turaruka masu fisgar hankali wanda har gwaggo
dake waje saida tayi mata magana
"Kai tasleem,turaren nan kodai na maza ne? Kibar
amfani da turare mai k'arfi haka kina mace."
Batace komai ba ta maida ta ajiye,ita kam anya
zata iya daina shafa turare? Da kamar wuya don
ma'abociyar son kamshi ce. Ta zura takalminta
sai kuma ta rasa mayafi. Kawai saita janyo na
mamma da tun zuwanta take yafawa ta yafashi.
Gwaggo Hajara ta dubeta tana zabga murmushi
sadda ta fito
"Ko babu kwalliya kina da kyawunki diyata ta
kaina saidai muje na baki wani mayafi ki sanya
wannan ya tsufa da yawa."
Murmushi kawai baby tayi gabanta bai bar bugu
ba,taji kwallah ta taho mata saidai tayi azamar
maidasu. Baharu ya shigo karo na biyu yana
sallama ta amsa. Baki ya washe
"Antina wallahi kamar bake ba. Kullum k'ara kyau
kike."
Ta d'an harareshi ya kyalkyale da dariya
"Kamar kinsan kuwa surukan naki ne ya
tambayeki shine nace bari na turo masa ke."
Surukanta? Ta nanata a ranta,ita fa jikinta yana
k'ara yin sanyi. Mamaki takeyi ace wai Haris ke
sonta,haka kawai tsoronsa yayi mata dirar
mikiya. Tunaninta ya katse sa'ilin da gwaggo ta
fito rike da wani mayafi kalar ruwan madara(wato
surfanin dake jikin shaddar)
"Fiddo wannan ki yafa wannan."
"Kai gwaggo ashe kinsan kalar gayu." Cewar
Baharu. Baby dai kamar kurma ko don bata fiye
son yawan magana bane? Oho. Amma batace
musu uffan sai murmushi na dole.
Suka jera Baharu yana bata labarin yanda
surukan suka yaba da wannan auren ji sukeyi
tamkar a daura auren ma a yau.
"Wallahi anti angon nan naki burgeni yakeyi kana
ganinsa kaga dan boko kuma wayayye amma ko
kusa bashi da wulakanci ko girman kai. Kunyi
bala'in dacewa dashi wallahi."
Ta dubi Baharu zatayi magana ta fasa
sakamakon ido hudu da sukayi da Haris ya fito
yana amsa waya. Sanye da manyan kaya amma
babu babbar riga, kansa sanye da hula. Sai taga
yayi mata kyau da kwarjini sosai,shi kansa
Baharu saida yaga yayi mishi kwarjinin. Ya daure
fuska yana mai kauda kansa yana mai juya musu
baya ya cigaba da wayarsa da alama dai da
kanwarsa yakeyi. Ta sunkuyar da kanta yayinda
kwallah suka cika mata idanuwa. Daman tasan
ba sonta yakeyi ba. Har suka is a daf dashi bai
bar wayar ba hakan yasa tayi cikin gidan,zata
karasa can wajensu inna,Baharu ya dakatar da ita
da cewa
"Ki soma shiga suna nan d'akin fa anti."
Ta gyada kai kawai,gabanta na faduwa tayi
sallama. Dukkansu suka amsa kafin ta shiga
kanta yana k'asa. Su kuwa su Abba ganin
surukar tasu nan da nan fara'arsu ta k'aru bare
ma Malam Hussein wanda yaji tamkar diyarsa ce.
Ta gaishesu a ladabce,suka amsa kafin ta
tambayesu hanya. A karshe Malam Hussein ya
kara jin ta bakinta sannan yazo mata da batun
cewar ba ita kadai Harisu zai aura ba(kamar
yanda suka zauna sukayi zancen da yaransa
abba da daddy da hajja kubra,Haris ya amince da
hakan ga mamakinsu. Itama Zahra tayi na'am
tana mai farinciki saboda son da takeyiwa Haris
mai girma ne.),hankalinta ya tashi jin wannan
zancen. Saidai ta daure tunawa da nasihar
gwaggo tace ta amince da bakinta. A karshe suka
sanya mata albarka ta mike ta fito kanta na
k'asa suna zubar hawaye. Jikinta kuwa rawa
yakeyi gabanta na dukan tara tara sakamakon
tunanin daya darsu a zuciyarta na cewar lallai
d'osanawa Haris ita akayi,daman Zahra yakeso.
Tana kokarin sanya takalminta amma jikinta rawa
yakeyi,ta dunguro zata fad'i tayi azamar kai
hannu da niyyar dafe bango saidai taji ta dafa
hannun mutum. Da sauri ta dago idanunta ya
sauka akan kyakkyawar fuskarsa,taja baya bayan
ta sakeshi.
"Sorry." Ta furta murya na rawa,ya matso saitin
kunnenta ya soma magana
"Kina tsammanin sonki yasa na amince zan
aureki ne Tasleem? No! Lik'amin ke akayi,ni
kuma babu yanda na iya na kaucewa maganar
magabatana. Zahra itace zab'ina! Abar kaunata!
Zan aureki bisa kaddara kawai!"
Ta juyo da sauri, ganin numfashinsu na gogar
juna tayi azamar ja da baya tana kallon
fuskarsa,murmushin mugunta kawai yakeyi mata
a zahirin gaskiya kuwa daurewa kawai yayi domin
cin zarafin dan adam baya daga d'abi'arsa. Ya
daga mata gira yana murmushi
"Idan kinga zaki iya,muje zuwa toh..."
Daga haka ya wuceta ya fita ya fasa shiga dakin
ma. Kawai tayi ciki a guje takalmin da bata
sanyaba kenan...!!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(60)
Takai mintuna biyar kafin ta kammala saidai kuma jin yanda hayaniya da shewar murna ta cika dakin inna ya hana Tasleem fitowa yayin data kifa goshinta jikin kofar bandakin tana rusar kuka. Ta tabbata an daura aurenta da Haris akan sadaki dubu hamsin. Shikenan Haris ya samu damar wulakantata da cin zarafinta. Yan uwanta sun kasa fahimtar Haris ba kaunarta yakeyi ba. Ta bandakin tana jiyo muryar Baharu yana labarta musu cewar ai Haris ne ya nemi a daura auren a yanzu,Abba(alhaji Aliyu,mahaifinsa) yana fadan wane irin gaggawa ne haka? Liman yace hakan shine daidai tunda gashi an hadu domin har mijin Mamma,Dad yana wajen wanda shine ya zama wakilin tasleem aka daura auren kawai. Zahra ma an daura saidai an bar tarewar sai nan da wata daya bayan an kammala shirye shirye. Nan dakin ya dauki kabbara cike da sowar farin cikin jin wannan labari. Tana jin sadda d'iyar Dada(dada matar kanin Liman daya rasu take zaune gidan) wacce take zawarci sakamakon mijinta daya rasu da jimawa,wato Hafsa ta tahowa tana buga kofar tana fadin
"Fito kin kunshe kanki a bandaki,komin abunki fa sai mun murjeki da lalle." Aka kwashe da dariya kafin dai kowa ya tattara ya fice. Saida taji shiru sannan ta fito, ji tayi an rukunkumeta ana dariya
"Ja'ira,ai daman nace sai na ga fuskarki." Cewar Hafsat. Tasleem tana kuka tace
"Anti Hafsa kina kallo aka auramin wanda baya kaunata baya sona? Anya ba'a kwareni ba?"
Jikin Hafsa yayi sanyi,ta ja hannunta suka zauna bakin gado
"Haba Tasleem,kinga yanda yake rawar kafa da wasa da dariya kuwa? Anya zan amince baya sonki? Kodai kece bakya sonshi ne?"
Tasleem tayi shiru da kukan,toh tana da bakin cewa batason mutumin da tun zuwanta Kazaure dashi take kwana take tashi a zuciyarta? Tabbas tana son Haris. Banda Rilwan bata taba son wani d'a namiji ba da zuciya daya sai shi.
"Kinyi shiru?"
Inna dake jinsu tace
"Ki rabu da wannan sakaryar wacce batasan abunda ya dace gareta ba. Nikam takaicinta ma yana sanyani jin kamar na kwasheta da mari."
Hafsa taja hannun Tasleem sukayi hanyar fita zuwa dakinta tana fadin
"Ayi hakuri innarmu,kinsan sabon shiga."
Inna ta tabe baki suka nufi dakin Hafsat. Ita dinma rarrashi da ban baki gami da gwada mata hanyoyin kissosi da zata bi domin mallakar zuciyar Haris cikin sauki. Tasleem dai sauraronta kawai takeyi,wannan ba matsalarta bace,babu wani abu na fannin kissa da bata kware dashi ba saidai Hafsa ta gaza fahimtar matsalarta. Ita fa kalaman da Haris keyi mata ne yake daukar hankalinta.
"Nan zuwa sati biyu za'a kawo lefenku. Aurensa dake aka soma d'aurawa sannan kuma da Zahra. Kinga kenan matsayinki ta babba dole saikinyi hakuri kin rike girmanki koda dai Zahra bata da raini yarinyar akwai hankali da nutsuwa ba kamar su Atika ba. Duk da haka sai kin dage."
Haka dai sukayita hirarsu har Hafsat take bata labarin zaman hakurin da tayi da facalolinta wanda yasa Tasleem sakewa sosai. Sallamar Musty ta katsesu. Ya shigo suka hada ido da Tasleem yayi mata murmushi a sanyaye
"Babana ya akayi?" Cewar anti Hafsa kasancewar sunan kanin Liman yaci kuma mahaifi gareta. Hakanan mustapha jikan Dada ne mahaifiyarta sannan shi din maraya ne gaba da baya a hannun Dada ya girma har zuwa aurensa da Farida.
Ya zauna saman hannun kujera yana yamutsa fuska
"Ina fa lafiya kuna ji kuna gani an kwacemin matata." Duk suka dubeshi Tasleem kuwa saita dauki abun wasa ashe Antin ma wasa ta dauka jin tayi dariya tace
"Me zatayi dakai yarinya yar birni.?"
Ta fice daga dakin,Tasleem ta gaidashi yak'i amsawa
"Small ashe zaki iya auren wani ba ni ba?"
A mamakince ta yamutsa fuska kadan kamar bazatayi magana ba sai kuma tayita tamkar bataso
"Wai daman kana sona ne yaya?"
Musty ya ciji lebbansa cike da takaici
"Tun kina secondary nake dawainiya da sonki. Allah bai kaddaro ke zam fara aure ba sai Farida. Yanzu kuma gashi ina murnar dama tazo min sai kawai na tsinci labarin aurenki da wannan gayen."
Ya danyi shiru itama tausayinsa takeji,
"Haka Allah Ya kaddaromin. Allah Ya baki zaman lafiya da mijinki. Saidai ina fushi har yau gashi satinki daya cif a garin nan baki tako kinga matata ba shiyasa nima duk da dokin ganinki da takeyi domin ina yawan bata labarin sister dita mai sona amma na hanata zuwa."
Ya karashe a wasance,itama ta share wancan zancen watakila dai ya tuna a yanzun matar aure ce,
"Kayi hakuri dai yaya mustyna,zan shigo."
"Ai na mantaa yanzun saida iznin oganki ko?"
Gabanta ya fadi,ashe yanzu komai zatayi saida iznin Haris? Tab ai kuwa ta gwammace tayi ta zaman gidan gashi tana matukar son komawa wajen mahaifiyarta domin ta kara neman afuwarta.
"Bari na wuce."
Ya maidota daga kogin tunanin data shiga,ta dubeshi har yakai kofa
"Toh yaya saida safe." Itama ta mike ta koma dakin inna. Sallar isha'i kawai tayi kafin tayi zaman hira da inna. Sai ga Liman ya aiko kiranta. Ta iskeshi babu kowa a dakin sai shi. Nan yayi mata doguwar nasiha akan aure da nuna mata ita din yanzu fa karkashin ikon Haris take sannan ya gargadeta data dunga mutunta shigarta. A karshe ya damka mata sadakinta tace ita yanzu bata da abunda zatayi dashi,ya adana mata. Yace shikenan. Ta mike ta fita, zatayi ciki taji muryar Baharu a bayanta yana kiranta dole ta tsaya ta dubeshi ta lura dai d'asawa yakeyi da Haris sosai. Leda ya mik'omata yana dariya
"Gashi inji maigidanki."
Ita kam duk sadda aka dangantata da Haris sai gabanta ya fadi,tasa hannu ta karba babu ko godiya tayi ciki.
Waya ce da chajinta da komai,sai kwalinta da alama harda sim. Blackberry ce. Sai kayan ciye ciye, nan inna ta hau duddubasu tana fadin oh,abun dadi basu karewa a duniya. Wayar tayi k'arar shigowar sak'o. Ta bude ganin lamba.
"Ga waya nan,ban amince ki bawa kowane namiji damar mallakarta ba ke daidai da dan uwanki banda Abdullah banason ganin lambar kowaye!
"Harith"
Ta tabe baki ai shi d'inma bazaici darajar saving number nasa ba a wayar. Ta ajiye wayar ta mike domin watsawa kanta ruwa haka dai inna ta dauka tayita kalle kallenta tana fadin yanda wayar ta burgeta kwarai.
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(59)
Cikin fushi inna ta ture tasleem daga jikinta
"Ke ni matsamin kibani wuri shashashar banza kawai! Aure hauka ne? Don za'ayi maki gata ke kuma kin kasa fahimta? Toh wallahi ba baki zanyi maki ba Tasleem,amma matukar kika bari batun auren nan naku ya rushe da yaron nan zaiyi wuya ki samu madadinsa. Ke kamar wata yarinya karama,a hakan ake cewa kinyi degree? Amma tabbas bakiyi kama da matan jami'a ba sam sam baki da wayewa. Mts. (Hhhh kuji fa! Baby ake fadawa duniya..cewar Rufaidarh)
Ta dago ta dubi inna dake faman zazzaga masifa
"Shi da bakinsa fa yace baya sona lik'a mi.."
"Kina nufin Liman k'arya yayi maki?"
Ita dai batace uffan ba,ai sai fadan inna ya k'aru karshe tace bazata iya ba saita had'ata da mamma. Sai kuma tayi shiru kafin ta kara cewa
"Allah Ya kyauta,namanta ashe ita dinma daren jiya tazo tana surutanta wai don me za'a yiwa Harisu haka? Saida na zageta tsaf na nuna mata kurenta sannan tace shikenan. Haka kawai kunbi kun tsani yaro na arziki ma."
Haka dai inna ta mike ta fice bayan ta dauki furar data kammala damunsa zata bayar a mik'awa bak'i.
Baby ringingine ta kwanta ta lumshe ido yayinda kwakwalwarta ke k'ara tunano mata bakaken maganganun Haris daya jefa mata. Zarginta ya tabbata kenan ba sonta yakeyi ba? Zahra,Zahra? Wacece ma hakan?
'Yar farar yarinyar nan dai siririya mai siririyar fuska. Kallo daya zakayi musu ita da Haris ka tabbatar da cewar jini d'aya suke saboda matukar d'ibar kamar da sukeyi da juna. Bata da mazauna sosai hakanan kirjinta baida cika sosai.
Tabbas ta tuno Zahra, itace dai wacce tayi mata rakiya gidansu KB. Murmushi kawai tasleem tayi tunawa da sanyin halinta. Babu ruwanta watakila shine dalilin da yasa Haris ke sonta. Kaico da rayuwarta,ita kam ba abun ta samu su Baffa ba tace bata kaunar auren nan.
"Taso kije Harisu ya aiko kiranki."
Ta bude idanuwanta sosai jin muryar inna. A sanyaye ta mike,ita fa batasan dalilin da yasa take shakkar Haris ba,kai bata taba kawowa bama zataji tsoron wani d'a namiji ba sai Haris.
"Don Allah ki mutuntashi babu kyau wulakanta mutum."
Murmushi tayi mai ciwo,ta mike ta dauki mayafinta ta fita bayan ta zura silifas. Ta nufi zauren saidai bayanan,ta karasa waje gabanta na dukan tara tara. Hon da taji ya tabbatar mata cikin motarsa yake, hakan yasa ta karasa kafin ta bude ta shiga. Bazata mance motar nan ba a tarihin rayuwarta,motar data fayyacewa Haris komai na sirrin rayuwarta?
"Baki iya gaisuwa bane ko kuwa dai rashin tarbiyya zaki gwadamin?"
Ta kalleshi
"Haris wai menayi maka hakane? Haris ka chanja ba haka...."
Kallon daya watsa mata shi ya sanyata yin shiru.
"Ba wannan na tambayeki malama."
"Barka da yamma."
Ya tabe baki kadan
"Rike abinki tunda rok'a nayi. Abunda nakeson sani shine,kinga period naki?"
Ta kauda kanta ga barin kallonsa
"Da asuba nayi wanka."
"Kina iya tafiya."
Shiru na mintuna,ganin bata da niyyar motsawa yasa shi saurin fita ya rabu da ita a motar. Tana kallonsa ya koma ciki,hawayenta suka kara kwaranyowa karo na ba adadi,toh zaman me takeyi kuma? Kawai saita bude ta fito itama.
*****
"Ayyiriri yiriri! Kai Alhamdulillah. Harda na Zahra?"
Batasan lokacin da cikinta ya murd'a ba,me kunnuwanta ke shirin ji mata ne? Innalillahi wa inna ilaihiraaji'un!
Da azama ta nufi bandaki domin rage cikinta......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar
(61)
Washegari wajejan uku na rana,mutan gidan basunan sunje gaisuwa acan k'asa gidan wani almajirin Liman wanda ya rasu sakamakon hatsari. Tasleem ce zaune a tsakar gidan cike da tunanin kawayenta. Tunani takeyi ko Manal tayi aure? Toh Dalal da Hibba fa ya suke? Tunanin neman layin Hibba ya fadomata. Bata mantawa saboda saukin lambar wayar Hibba ta haddaceta a kwanyarta har akwai ranar data taba karantowa sukayita mamaki har hibbar domin ko ita bata da haddar lambarta aka. Da azama ta mike tayi daki,wayar dai data tsana ita ta dauko ta dawo ta zauna. Ta duba akwai kud'i har dubu daya a ciki. Baki ta tab'e wannan kam a wurinta karamin kudi ne bazai burgeta ba. Batason wulakanci a rayuwa. A nutse ta jera lambar ta kira. Akayi sa'a ta hau ringing.
Hibba alokacin tana zaune a gefan ruwan Tiga Dam ita fa sabon saurayinya,HAYAT. Tunda ta soma bariki bata taba tsintar kanta dumu dumu cikin soyayyar wani d'a namiji ba illah Hayat. Matashi mai ji da naira da hutu. Ganin unknown number yasa ta jan tsaki ta ajiye wayar. Hayat ya dafa cinyarta yana kasheta da kallon kauna
"Lafiya dai my beb."
"Wata number ce da bansan da zamanta ba."
Acan kuwa baby tsaki taja sai lokacin ta tuna ko ita akayi kira da unknown no.a wayarta bata fiye dauka ba. Ta yanke shawarar tura sak'o.
"Hibba,it's me Baby. Pick d call."
Tana shirin turawa yayi sallama ya sanyo kai. Ta amsa bayan tayi saurin ajiye wayar a gefe. Hankalinsa yayi kan wayar cike da zargi kafin ya basar ta hanyar fad'in
"Ina mutan gidan?"
Itama fuskarta ba yabo ba fallasa saidai kirjinta sai bugu yakeyi.
"Basunan sunje gidan gaisuwa."
Bata ankara ba taga yasa hannu ya dauki wayar yayi tsai yana karanta sak'on....
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(62)
Fuskarta a tamke baisan sadda ya daga wayar ya bugata da bango ba kafin ya fisgo Tasleem wacce ta mike tsaye ganin yanda ya yiwa wayar. Murde hannunta tayi ya komar dashi ta bayanta,har suna shakar numfashin juna ita kam na tsoro ne. Tayi ta murza hannun saidai fa iyaka yatsunta ne don kuwa ba rikon wasa ta samu daga wajen maza ba.
Cikin kakkausar muryar da batasan Haris da ita ba yace
"Menene gaminki da ita a karo na biyu?! Me kike shirin yimin? Daga yau ki sani cewa banason mu'amalarki da kowace abokiyar shaidancinki ta baya! Wannan shine gargadina a gareki na karshe."
Daga haka ya saki hannunta,tayi saurin ja baya tana zubar hawaye. Ta dubeshi ido cikin ido kallon nan na alamar tambaya(Kaine kuwa?..lol). Ya kauda fuskarsa,har ya juya zai fita kuma ya dawo baya ya dauki wayar wacce tuni screenface dinta ya tsage,sim d'in ya fidda kafin ya cilla wayar jikinta daga haka yayi gaba cikin takunsa kamar wani basarake.
Ta dubi hannunta wanda har yatsun Haris sun bayyana jikinsa,kafin ta lumshe ido ta zauna d'abas akan sumintin tsakar gidan tana kuka. Karshe dai mikewa tayi ta dauki wayar tayi daki. Jimawa kadan taji sallamar Baharu,bata ko fito ba har ya shigo ya miko mata simcard sabo.
"Gashi inji angonki,yanzun nan suka wuce. Yace ki sanya a wayarki zai kiraki."
Bata ko kalleshi ba ballantana yasa ran zata karb'a,ganin shiru ya ajiye ya fita yana mai jin haushin yanda antin nan tasa ta kasa gano kaunar da Haris keyi mata.
*****
Tsaye yake a farfajiyar hotel din na Nicon dake birnin tarayyar Abuja yayinda yake cike da farin ciki da walwala na ganin wacce bai taba tsammatar ganinta ba a wannan lokacin. Ta karaso bayan ta cewa wacce suke tare tayi jiranta minti biyu. Ta wulka ido irin na kwararrun 'YAR BARIKI kafin ta sakar mishi murmushi wanda ya kara fiddo zahirin kyawunta na asalinta na buzuwa.
"KB manya daman ana ganinku?"
Kb yayi yar dariya
"Gaisheki DALAL,kun b'ata b'at a garin ta dabo. Ashe kina nan kina holewarki."
Dalal tayi dariya
"Kai haba,mu a suwa? Kaine dai gakanan sai fresh kakeyi,nikam tunda mun hadu yau bazan bari ka gudu ba saika kaini na gaisa da k'awarmu. Wallahi just one week kenan da bamu ganta ba amma kewarta ta cikamu."
Cikin rashin fahimta yace
"Wai Dalal kuna zaton Baby tana tare dani ne?"
Tayi k'as k'as da cingam tana kallonsa shek'ek'e
"Bangane manufarka ba KB? Wai bakwa tare da Baby? Toh ina take?"
Yayi wani d'an malalacin murmushi kafin ya zura hannu aljihun wandon jeans nasa. 'Yan dubu dubu ne da baisan ko nawa bane ya zaro da d'an kaurinsu ya mik'a mata
"Idan basu isheki ba kiyi magana na k'ara maki Dalal,fatana da burina bai wuce ki taimaka wajen lalubomin inda kawarku take ba. Ko kuma idan kinsan wani labari game da rayuwarta please ki sanarmin sauran binciken zanyi da kaina."
Ta shinshina kud'in,ita kam ai kud'i koyaushe basu tsufa awajenta sabbi ne. Ta tura a jakarta bayan ta tuno da Manal data tab'a tabbatar mata cewar ita kadai tasan wacece baby da kuma garinsu saidai bisa amana ta gayamata ita kam bazata fadawa kowa ba.
"Aikinka zai cika muddin zaka saki kud'i Hajy KB."
Shima kallo yakeyi mata na kwararren 'Dan Bariki,kafin ya shafi sumarsa yana dariya
"Ba abune mai wuya ba,kina iya bani acc.no dinki hade da phone.no."
Ya amsa kafin suyi sallama ya shige don gabatar da abunda ya kawoshi cike da matsanancin farin ciki....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(63)
A gajiye ta k'arasa kujerar tangameman falon wanda yaji kayan alatu ta zauna tana fadin wash! Manal ta zube gefanta suna dariya
"Shegiya Dalal,kina cin karenki babu babbaka nikam ina nan kamar kullin kayan wanki. Ke a yanda na lura anya kuwa Alhaji Ubalen nan idan munyi aure zai barni na fita wani wajen? Mahaukacin kishi gareshi,ji fa dai daga maganar aure har ya killaceni gidansa,babu wata harka wai yana bukatar nayi istibra'i,mts."
Dalal ta mike zaune tana dubanta bayan ta kyalkyale da dariya
"Kefa baki fahimci wannan d'an fulanin naki ba,toh wallahi dagaske yakeyi sonki yakeyi da gasken gaske."
Ta tabe baki
"Barshi dai yayita haukansa,wani sa'in ni kaina ina jin kauna da tausayinsa wallahi ya iya lallab'a mace ne. Ke nasa fa an bincikamin asalin aurensa da matarsa,ashe dole yabi umarnin mahaifinsa ya aureta har yanzu da suke da yara biyar bai taba sonta ba. Kinsan fa ba wani shekaru ne dashi ba,arba'in da wani abu yake."
"Yara biyar? Kuma ace ba soyayya? A ruwa tasha?"
Manal ta harareta da alama maganar ta bata ranta,Dalal kam murmushi tayi gami da jin tsoron auren wata uku ya koma na har abada....
"Wai kuwa kina samun Baby a waya? Nasha nemanta naji switched off."
Jin an ambaci Baby ya tunasar da Dalal abunda ya kawota. Ta zabura ta matso kusa da Manal har tana firgitata.
"Ke nima bansan inda ta lulluk'a ba,anya ba garinsu ta koma ba?"
Manal tayi shiru tana tunani,daman tun sadda baby ta fito da shigar hausawa jikinta ya bata cewar Kazaure zataje.
"Gayamin sunan garinsu mana,kinga sai na gano mana ko lafiya?"
Cewar Dalal,Manal ta numfasa
"Banason karya alk'awarin dana daukarwa baby na cewar bazan sanarwa kowa ba game da garinta ko asalinta,wannan shine..."
"Haba Manal, bamusan halin da take ciki ba,idan ance ma tana bukatar taimako babu k'arya a ciki. Idan kin fadamin wa zan gayawa,just give me full address ni kuma zan binciko mana lafiyarta koda a b'oye ne. Kinga idan bata garin sai mu sanya cigiyarta ko kuma mu bi abokan harkarta gaba daya tunda ba wani yawa garesu ba muji ko suna tare."
Manal tace "KB fa?"
"Basu tare da KB,domin kuwa Momy tace min yazo nemanta wajenta amma bai sameta ba."
Dalal tayita siyasance Manal har saida ta samu ta shawo kanta tayi na'am da hakan batare data bata ko sisin naira biyar ba. Duk da dai Manal bata da tabbacin baby can tayi amma bata zaton zata je gidan yayanta da mahaifinta domin a yanda ta nunawa Manal ba karamin tsana tayi musu ba,mammanta ce ma take son sanyata ido wataran.
Ta gayamata ta rubuta.
"Idan kinje Kazaure ki nemi gidan babban limamin garin, nan ne gidan da nasan watakila ki samu labarin Baby."
Bayan ta gama rubutawa,Dalal ta tuntsire da dariya
"Amma Baby anyi shegiyar yarinya. Don ubanta ita daman d'iyar Liman ce take bura uba haka?"
Manal ma dariyar tayi,saidai tsoron kada Baby ta kamata da cin amanarta yasa bata gayawa Dalal cewar gidan kakannin baby ne ba ta wajen mahaifiyarta. Da zataji waye uban baby,zata fahimci cewar lallai Baby ta ketaresu kota ina tunda ba kudi ne ya fiddota bariki ba.
******
Kishingide yake a kujera mai zaman mutum uku,Yasmeen tana gefe tana mammatsa mishi kafafuwa yayinda ya maida hankalinsa ga kallon Ball. Wayarsa tayi k'arar shigowar sak'o
"Mikomin wayata."
Ya fada ba tare daya dauke idanunsa daga kallon ba. Ta dauki wayar ta mik'a masa. Ganin sak'on daga Dalal ne,ya sanyashi mikewa zaune.
"Kazaure gidan babban Liman,duk wanda ka tambaya za'a kaika. Idan kaje babu nasara zan k'ara bincika mana."
"Wuuu!"
Shine ihun murnar da KB ya saki. Yasmeen ta iso gareshi
"Lafiya prince?"
Ya mike ya dagata sama yana juyi da ita suna dariya. Babu kamar Yasmeen wacce take jin mamakinsa da kuma farin ciki. Yaushr rabon daya kula da lamarinta haka? Kai a ranar dai ya faranta mata fiye da tsammaninta. Shi kuwa Allah Allah yakeyi weekend yayi yaje ga Baby shi koda bai ganta bama ya samu shiga wajen liman. Domin kuwa yasan kwarai wanene Liman saidai bai taba kawowa shine uban tasleem ba. Har ya soma mamakin abunda zaisa Tasleem wacce ta fito gidan manya haka ta b'ata rayuwarta da barikanci. Meyayi zafi haka toh?
******
Karshen sati nayi,ya yiwa matarsa sallama da sunan zaije Kazaure gaida kakanninsu. Taso ya tafi da ita saidai koda ta matsa da magiya ya bata rai a dolenta ta hakura tana ji tana gani yayi mata sallama ya wuce airport domin hawa jirgin zuwa Kano.
Tunawa da tayi cewar tun angoncewar yayanta bai nemeta a waya ba yasa tayi kiransa. Yana dauka ta soma shagwaba murya
"Haba yayana ashe daman akwai sadda zaka share lamurana? Nikam har na soma fushi da yayyuna nasan waya dasu ya janyo ka shareni."
Haris dake kwance akan gado kawai yana hutawa domin ya jima da tashi daga bacci,darem jiya sun sha waya da Zahra wacce babu laifi ta samu gurbi sosai a zuciyarsa duk da dai karfin hirar itace shi kam yakan rasa abun cewa saidai ta jefo mishi tambaya.
"Kiyi hakuri small,ban manta dake ba. Ai babu matar da zata mantar dani ke. Ya kuke? Ya dotana?"
Yasmeen tayi dariya
"Gatanan tana tsalle tsallenta,babanta ma yanzu ya tafi Airport zai wuce Kazaure idan ya sauka anan Kano. Wallahi naso ya taho dani naga amare amma yak'i."
Tunda Haris yaji wai KB ya taho Kano zaije Kazaure yaji bacin rai matuka ya dirar masa. Bazai fa amince da wannan sakarcin ba,ya dace tun yanzu ya sanyawa lamarin burki.
"Hello." Cewar Yasmeen jin yayi shiru.
"Small,bani mintuna." Ya katse kiran ya mike zaune yana mai zuro kafafunsa k'asa. Dabara ce ta fadomishi na kiran Mamma. Matar da tunda ta ganshi ta nuna mishi kauna hakanan sun jima a falonta su biyu suna tattaunawa game da Tasleem sannan ya nuna mata komai dangane da lamarinta ya sani. Har kwallah tayi don farin cikin jin cewar yaji ya gani yana son diyarta zai iya aura. Bayan sun gaisa yace yanason Nura yaje ya dauko Tasleem a mota harda kayanta ta zauna a wajenta. Mamma ta tambaya ko lafiya. Bai sanar mata ba saidai yace akwai 'yar matsala ne. Tace bakomai zatayi hakan.
Tasleem tayi mamakin ganin Nura yazo wai Mamma da kanta ta nemi komawarta gidanta. Har inna tana fada wai Mamma babu ko kara,bata tambayi ko da iznin Haris ba ko Aa saboda taji Nura yace shine yayi kira. Hakanan ta hau mota,Nura yaja suka nufi gidan Mamma sai tambaya takeyi Mamma da fara'a tayi maganar zuwanta ko a'a shidai Nura tun yana amsawa har tambayoyin sukayita bashi dariya ma.
******
KB yana dira a Kano,direbansa ya kaishi gida. A gaggauce yaci abinci yayi wanka sannan ya saka kananun kaya. Jakar kayansa ya dauka ya saka a mota. Jeep dinsa ya dauki yayi hon Maigadi ya bude.. Sai Kazaure......!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(64)
Hankalin Haris bai kwanta ba har saidai ya lalubi layin baby saidai baiyi mamakin jinsa a kashe ba yasan tayi fushi tak'i sanyawa ne. Wannan yasa ya k'ara nemanta ta hanyar layin Mamma. Ya sanarwa Mamma yanason magana da baby. Ta mik'awa Tasleem lokacin tana zaune anan gefen Mamma suna 'yar hira don babu laifi ta sakarmata.
"Sai ki tashi ki shiga daga ciki mijinki ne."
Ta mike ba don taso ba wayar na hannunta. Saida ta zauna gefen gado sannan tayi mishi sallama. Ya amsa ciki ciki
"Kina jina ko? Kb yana hanyarsa ta Kazaure."
Tabe baki tayi,ai daman tasan ko ba dade ko ba jima sai KB ya samu labarin inda take tunda har yasha alwashin nemanta ruwa a jallo.
"Ya akayi yasan da zamanki a Kazaure?"
(Ya fadi hakan da niyyar bugar cikinta duk da bashi da tabbacin saboda ita Kb zaije Kzu.)
Cikin rashin fahimta tace
"Kana zargina ne da gayawa KB inda nake Haris? Ko ka mance garinsu ne?"
Ya lumshe ido ya kara gyara zaman towel din dake daure a kugunsa,fitowarsa kenan daga wanka. Zak'in muryarta daban ce,hakika zai iya rantsewa bai taba sauraron muryar mace a fili ko waya ba, da yayi mishi dadi irin na Tasleem.
"Nidai ina mai gargadinki,stay away from him. Kada koda wasa na samu labarin kun hadu har maganar fatar baki ta shiga tsakaninku. OK?"
Ta rausayar da ido tana tsuke baki cikin jin haushin Haris. Banda abunsa ma,kare ne ya cijeta da zata k'ara waiwayar BARIKI. Don KB barikin ne ma gaba daya a rayuwarta.
"Kin rasa baki ne?"
"Naji zan kiyaye."
"Good,had'ani da Mammana."
"Ko a ina ta zama taka?" Ta fadi a zuci,a fili kuwa da toh ta amsa kafin ta mike ta fita zuwa falon.
Mamma ta karbi wayar,sunyi magana wacce Tasleem batasan abunda yace mata ba saidai ta lura da hararar da Mamma ta dafko mata kafin ta amsawa Haris da cewa
"Kada ka damu d'ana,baza'a samu wata matsala ba."
Daga haka ta kashe wayar ta mike tayi dakinta a fusace. Wannan ya sanyayarwa da Taslewm da jiki ta mike ta rufa mata baya. Kuka sosai ta tarar Mamma nayi. Ganin ta shigo ta zauna Mamma ta ja majina
"Kin cuceni Tasleem. Idan na tuno kinyi karuwanci raina baci yakeyi naji ke kanki ina jin haushinki. Wallahi koda wasa naji kin sab'awa mijinki babu ni babu ke. Ba don Liman ne da kansa yazomin da batun aurenki da yaron mutuncin nan ba wallahi ban yarda a cuci rayuwarsa a aura mishi ke."
Jin haka itama Baby ta fashe da kuka sosai ta durkusa gaban Mamma
"Wannan ya nuna har wannan lokacin baki yafemin ba Mamma. Ya kikeso nayi,Mamma idan bada sanya albarkarki gareni ba komai na rayuwata bazata tafi a daidai ba. Please Mamma kada kiyimin bakin da zan kasa zaman aure."
Jin wannan furucin ne ya tashi hankalin Mamma,ta rungumo diyarta tana fadin
"Na yafemaki Tasleem,bazaki fi haka lalacewa ba. Har abada in sha Allah kin shiryu kenan,bana fiddaki a addu'ata."
Farin ciki yasa Tasleem dariya. Mamma ta kara dubanta bayan ta saketa
"Kabiru da Harisu sun taba ganinki cikin waccan rayuwar,hakan yasa Harisu rokona akan kada na bari ki hadu dashi."
Ranta idan yayi dubu ya baci,Haris yafison kare sirrin abokinsa akan nata??
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(65)
Bata cewa Mamma komai ba banda toh.
******
Yaran gida sai ihun murna sukeyi da ganin Kabir. Hajiya Atine ce a
tsakar gidan zaune kan tabarma suna hira da mai musu hidimar
girki yayinda take kwasar tuwo. Ganin dagaske jikan nasu ne ta
hangame baki tana dariya
"Ashe da gaskiyar yaran nan. Lale marhabin da mijin."
Kabir yayi dariya suka gaisa suka taba barkwanci kafin ya shige
wajen kakarsa Hajiya Badi'at. Itama karatun Kur'ani takeyi,sanye da
gilashinta na ciwon ido,ganin Kabir ta karashe aya tayi addu'a kafin
ta shafa.
"Ashe zakazo nan kusa? Ai da bamu ganka tare dasu Harisu ba nayi
zaton kaida zuwa nan sai biki kuma?"
Ya kai hannu ya bude firij ya dauki robar ruwan Faro,yana kokarin
budewa yayi dariya
"Haba dai? Ai dole nazo ganin amaren namu. Ko Haris din baisan da
zuwana ba so nakeyi dai na bashi mamaki. Wai ma naga kokarin
Haris,naji don karfin hali mata biyu ya aura? Yayi kokari."
Ya karashe yana mai daga robar ruwan ya soma kwankwada. Hajiya
badi'at tayi dariya
"Kai don bakaga zuk'ak'an matan da ya zab'a ba. Zahra da
Tasleem,....."
Tuni ya maido ruwan bakinsa ya fesar har yana b'ata jikin Hajiya
Badi'at. Ya cigana da tari saboda ba karamin kwarewa yayi ba.
"Baka da hankali ne? Kana shan ruwa kamar wani karamin yaro? Ji
yanda ka b'atamu?"
Hankalinsa baya tattare da ita,gabansa na bugu da sauri da sauri.
Ganin yanda gaba daya ya chanja yasa Hajiya Badi'at dakatawa
tana k'ara cillaro mishi idanuwanta wadanda tsufa ya soma
tab'awa.
"Kai Kabiru lafiya kake?"
"Hajiya wacece Tasleem da Haris ya aure ne?"
Ta d'an tabe baki
"Kai amma Allah Ya kyauta,ai na dauka wani abun ne wallahi. 'Yar
wajen maryama ce ta gidan Liman."
"What?!!"
Ya fada cikin tsawa wanda ya tsorata 'yar tsohuwa Hajiya. Ya mike
tsaye,duk jikinsa rawa yake. Nan da nan idanunsa suka kad'a wai
kodai wata ce daban?
Da sauri ya fito daga dakin ya zura takalmansa,yana ji Hajiya na
kwala mishi kira amma baijin yana cikin hayyacin da zai samu ya
tsaya. Bai dire ko'ina ba sai gidan Liman. Tsayawa yayi ya rasa ya
zaiyi,gashi ba wani sabo yayi da mutanen gidan ba saidai ko ta halin
k'ak'a yau sai yaga Tasleem matar Haris. Yana nan tsaye yana
shawarar shiga ko tsayawa anan,saiga Baharu ya sauka saman
mashin dinsa yana kokarin tsayar dashi. Kb ya karasa wajenshi
sukayi musabaha,cikin sakin fuska kasancewar Baharu yasan Kb.
"Yaya kabir saukar yaushe?"
Kabir yayi murmushi wanda iyakarsa lebbansa
"Dazun nan na sauka. Ina amaryarmu?"
Baharu ya washe baki yana dariya
"Anti Tasleem tana nan mun b'oye maku ita har sai ranar."
Kb ya share wannan don ba shine a gabansa ba.
"Kana iya yimin magana da ita? Sak'o angon nata ya bani."
"Kash,ai kuwa tana gidan Mammanta."
"Ko zan samu rakiyarka gidan?"
Ba musu suka hau mashin din Baharu suka tafi. KB burinsa yaga
wacece Tasleem matar Haris,baya fatan ta kasance bebinsa.
Haka har suka iso kofar tangameman gidan. Kb yabi gidan da kallo
kafin ya tabe baki
"Not bad." Ya fadi a zuci.
"Bismillah shigo."
Ya bi bayan Baharu suka shiga. A nan tsakar gidan suka iske
Humaira gwaggo mai aikin Mamma tana turata a saman kekenta.
Kuri KB yayi mata da ido yana karajin gaskiyar zatonsa tana
bayyana. Wannan inda ace Baby bata wuce sa'arta ba sai yace itace
saboda matukar kamar da sukayi da juna.
"No Haris! Kada kayimin haka."
Ya fadi a fili kasa kasa,zuciyarsa na tafasa sosai. Suka shige ciki ba
tare daya amsa koda gaisuwar da gwaggo keyi mishi ba. Sukaci
karo da Mamma ta fito daga kicin. Ta amsa sallamarsu cikin jin
dadin rashin ganin Tasleem a falon kamar yanda ta haneta fitowa
daga daki har zuwa sadda Kabir zai ba Kzu.
"Mahaifiyar Baby kenan." Ya fada a ransa.
"A'a yau kuma wa muka samu haka kamar ma ba bakuwar fuska ba
a wajena?"
Ta fara maganar da duban KB,yayin data karashe tana kallon
Baharu.
Baharu yayi dariya
"Yaya Kabiru ne da,jikan Hajiya kuma aminin surukinki."
Magana ta fito! Tasleem da Haris! Wai wanene maci amanata a
cikinsu ne?
Dakyar suka gaisa da Mamma,baharu ya tambayi Tasleem Mamma
kuwa tace bacci takeyi. Kabir murmushi kawai yayi kafin a karshe
ya mike yace zai wuce.
"Haba dai ko ruwa baka sha ba?"
"Bama wannan ba,yace sak'o aka bashi ya bata fa."
Cewar Mamma da Baharu. Kabir tuni yayi kofa,ganin haka Baharu
ya mara mishi baya. Tuni yakai gate wajen mashin din. Baharu yana
zuwa yayi azamar fiddo wayarsa ya bud'o bangaren hotunan
tasleem wadanda ma'adanarsu daban ce a wayarsa,dakyar ya
lalubo wanda take zaune a falo sanye da doguwar rigar abaya tana
dariya ya dauketa domin shi kadai ne mai mutuncin a ciki.
Kafadar Baharu ya rike cikin dusashshiyar murya yace
"Duba dakyau,itace wannan?"
Baharu wanda ya tsorata da yanayin KB yayi saurin duba hoton.
"Itace ai amaryar taku."
Ya watsawa Baharu mahaukacin kallo kafin ya maida jajayen
idanunsa ga gidan. Ashe Tasleem da Haris zasu iya cin amanarsa?
Bar maganar Tasleem,yafi mamakin yanda Haris ya munafunceshi
ya auri wacce yafi so cikin mata. Ya rantse sai ya dauki mataki koda
hakan zaikai ga rabuwarsa da Yasmeen,rabuwar zumuncin iyayensu
hakanan da rabuwar wannan amintar tasu da Haris na shekara da
shekaru,duk akan 'YAR BARIKI.......!!!!!
KARSHEN NA DAYA....!