BA’A SHAN
ZUMA… 01
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Kwance take tsakiyar wani dan
karamin daki mai mugun bakin
duhu, babu komai a cikin dakin
sai yar tabarmar kabar da take
kwance akai, ga wani irin sanyi
ana yi, mai masifar buji, ta
takure wuri guda, ta lullube
kafafuwan ta da dankwalin ta,
hannuwan ta ko ta hada su ta
cusa tsakanin cinyoyin ta,
domin kuwa ko arzikin zanin
da zata rufa bata dashi. Bata
da banbanci da prisonern da
aka yankewa hukuncin daurin
rai da rai! Wasu irin hawaye
masu zafi ne suke sintiri akan
kyakkaywar fuskar ta, tunani
take ena rayuwarta ta dosa?
Tun tana karama take shan
azaba a hannun goggo wadda
ta kasance kanwar mahaifi a
gare ta. Cikin muryar kuka take
cewa "anya kuwa goggo ta
hada jini da mahaifina kamar
yadda aka sanar dani?" Bata
karasa rufe bakin ta ba, taji an
banko kofar dakin tun karfi, ba
tare da bata lokaci ba matar
data shigo ta daga robar ruwan
dake hannun ta, ta juye ta tass
akan yarinyar, cikin tashin
hankali tayi zumbur ta mike,
tace "goggo dan Allah kiyi
hakuri, wlh ban san asuba tayi
ba" matar da aka kira da goggo
ta karaso gaban ta, ta jawo
gashin kanta tayi wurgi da ita
zuwa tsakar gida, tace "uban
mi kike nufi da baki san asuba
tayi ba?" tsinanniyar yarinya
kawai, mai hali irin na uwar ta,
wuce ga bargunan fitsarin
shehu can ki wanke su tass ki
shanya, sannan ki wuce ki dibo
mun ruwa tun kafin layi ya
cika" tana kai wa nan ta
hanbare ta da kafa, taja tsaki
sannan ta wuce.
Mikewa tayi jiki ba kwari, ga
wata irin rawar sanyi da take
yi, bargunan ta tattara, ta wuce
ta zuba su a ruwa, ta wanke ta
shanya, sannan tayi alwala,
taje ta gabatar da sallar asuba.
Tana sallamewa goggo ta dawo
dakin tace "sannu yar milki,
wato dan uban ki rainin da
kikai mun har ya kai na in maki
magana kiyi banza dani ko, yau
zaki gayawa yan garin ku" ba
tare da ta bar ta tace komai
ba, ta fara jibgar ta, ga kayan
jikin ta dama a jike, ga wani
irin muku mukun sanyi da ake
sararawa, amma babu tausayi,
ba imani goggo taci gaba da
kwalfarta har saida taji ta gaji,
sannan ta kyale ta, ta fito daga
dakin ta dauko wani Katon
baho, ta wurga mata, tace
"saura kuma in kin tafi ki
kwana a can, kizo kiga yadda
zan lallasa ki a gidan nan"
cikin kuka ta mike ta dauki
bahon ta wuce ta bar gidan…
Borehole ta nufa a lokacin
babu kowa saboda tsabar
sanyin da ake yi, ta tara bahon,
sannan ta fara buga famfon,
cikin yanayi na damuwa da
mugun tashin hankali, ga wata
irin kyarma da take yi, hakoran
ta sai gamewa suke suna wani
irin kara.
Ta cika bahon dam, dakyar ta
dauka, ta dora a kanta, sannan
ta dauko hanyar gida tana ta
uban sauri.
BA’A SHAN
ZUMA…. 02
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
A hanya ta fara ganin mutane
kadan kadan kasancewar, gari
ya fara haske. Gidan ta karasa,
taje ta aje ruwan, sannan ta
tattara wanke wanke, taje tayi,
ta gama ta share tsakar gidan,
duk su goggo ana daki ita da
ya'yan ta, ta leka dakin goggon
ta durkusa tace "na gama
goggo" ba tare da ta kalle ta
ba, ta dungura mata roba mai
kosai a ciki, ta mika mata kofin
kunu, ta ansa tayi godia,
sannan ta wuce dakin ta, ta
zauna ta cinye, ta jawo wasu
kodaddun uniform, ta burma ta
dauki jakan ta, ta wuce
makaranta. One thing da zai
birge ka a tare da Deedo shine
kokarin ta wurin karatu, bata
wasa dashi duk kuwa da
wahalar da take sha a gidan
goggo, domin kuwa babban
burin ta a rayuwa bayan ta
hardace Qur'ani, to shine ta
zama medical Dr. haka rayuwar
ta take tafia, bata da wani
'yanci balle kuma ayi maganar
gata.
WACECE DEEDO?
Asalin sunan ta Nana
Firdausi Kabeer Sani, yarinya
ce mai shekara 12 a dunia,
tana js2 a wata private skool,
wadda scholarship ne ta samu
daga Gov. Bauchi anan cikin
garin Ningi. Mahaifinta
haifaffen garin Ningi ne, ta
jihar Bauchi. Su biyu iyayen su
suka haifa daga shi sai qanwar
shi Batula wadda ake kira da
goggo. Goggo irin izgilallun
matan nan ne, masifaffu masu
ji da bala'i, irin mutanen nan
da idan suka dauki karan tsana
suka dora maka, sai kaji kamar
ka bar dunia saboda masifar
su. Tana da yara guda biyu,
Hadiza da Shehu, mijin ta
malam ilu, bata dauke shi
bakin komai ba, domin komai
ita take yiwa kanta, wannan
yasa suma yaran suka raina
uban nasu. Mahaifiyar Deedo
mai suna Rukayya,yar asalin
garin kafanchan ta jihar kaduna
ce. Yanayin aiki yasa
mahaifinta dawowa cikin garin
kaduna da zama, inda ya tare a
unguwar hayin banki. Su biyar
ne iyayen su suka haifa, kuma
duka mata. Akwai babbar yayar
su Fatima, sai Labeeba sai
umman deedo, sai Halima mai
no mata, sai kuma Aminatu yar
autar su wadda suke kira da
baby.
Riqon Deedo ya dawo hannun
goggo ta sanadiyyar hadarin
mota da iyayen ta suka yi, a
hanyar su ta zuwa Kd, inda ita
kuma Deedo a lokacin sun
barta wurin inna mahaifiyar
baban ta, saboda zuwa
makaranta, wanda a lokacin
duka duka bata fi shekara 5 ba
a dunia!!
Wannan tashin hankali shi ya
haifar wa yar tsohuwar da
ciwon zuciya, ga kuma
tausayin yar marainiyar
yarinyar da suka bari, hakan
yasa ta kwanta ciwo sosai,
inda daga bisani itama tace ga
garin Ku nan dan dama malam
mijin ta, ya dade da rasuwa.
Tun asalin auren umma da
Abban su Deedo, goggo take
fama da baqin ciki da takaicin
dalilin da yasa dan uwan nata
ya rakito umma, kwata kwata
bata son ta bata kaunar ta,
kasancewar kafin yayi auren
akwai kawar ta Badiyya data so
ya aura, sai dai kuma shi bai
yaba da halayen ta ba, hakan
ya haifar da rikici a tsakanin
su, inda daga karshe ta yanke
shawarar fita harkar shi tare da
matar shi, sanadiyyar tsanar da
take yima mahaifiyar Deedo
kuma ita ce ta shafe ta har ya
kai ga ko ganin yarinyar bata
son yi kamar ba jinin ta.
Bayan inna ta rasu, yan
tsiraran yan uwan da suka rage
masu, suka yanke shawarar
goggo ta dauki Deedo ta riqe,
amma fur matar nan ta rufe ido
tace babu dalilin da zai sa ta
hada kanta da mugun iri, tace
"wani a cikin ku ya rike ta
mana, in kuma baku iyawa sai
ku kaita gidan marayu" ta mike
tayi tafiyar ta. Haka akai ta
fama da goggo, inda daga
bisani dai aka samu aka
lallaba ta, ta dauke ta, a cikin
zuciyar ta tace "ko bakomai na
samu yar bauta" haka ta tusa
keyar Deedo gaba, ta mayar da
ita gidan ta. Tun daga wannan
rana kuma Deedo tayi sallama
da duk wani farin ciki na dunia,
daga nan ta fara fuskantar
tsananin rayuwa, dan tun tana
karama take kwana a wannan
dan daki mai kama da keji, Dan
kuwa bata da ikon da zata
matsa kusa da Hadiza, wadda
suke kusan sa'anni, balle har
ta samu damar hada shimfida
da ita.
BA’A SHAN
ZUMA… 03
NA
LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Tsakanin ta da shehu kuwa
banda kyara da hantara tare da
wanke mai kayan fitsari babu
abinda ke hada su, duk da
lokacin ya kai shekara 9,
amma haka yake miqewa ya
sharta fitsarin shi a gado, ba
ruwan goggo, balle tayi qoqarin
hana shi.
Bayan Deedo ta cigaba da
zama a gidan goggo cikin
kuncin rayuwa da ukuba,
dangin mahaifiyar ta suka
samu labari, Dan haka Fatima
babbar yayar umman ta, tazo
da niyyar tafia da ita, amma
goggo ta rufe ido ta furza mata
ruwan rashin mutunci, ta qara
da cewa ita ce dolen Deedo,
tunda mahaifin ta bashi da
kowa wanda ya wuce ta, dan
haka kuma babu wanda ya isa
ya karbe wannan yarinya daga
hannun ta. Haka Ummi
kasancewar haka yaran ta suke
kiran ta, ta tattara ta koma kd
cike da tunanin halin da Deedo
take ciki..
* ***
Ana tashi daga makaranta ta
sabo jakar ta, ta fara bunguza
sauri, dan ta San halin goggo
sarai, ta riga ta mata warning
muddin Hadiza ta riga ta
dawowa gida, sai ta yabawa
aya zakin ta. Hally kawar ta,
tana ta kwada mata kira, amma
ina ta riga tayi nisa, da gudu ta
karaso gaban ta, tana cewa
"wai ke Deedo goggon nan taki
sai kace mala'ika, baki so ki
bata mata rai ko kadan" ta
murmusa tace "Hally kenan, kin
fa san komai, amma sai kina yi
kaman baki sani ba, ina zan
tsaya in sha na jaki, yau ma
tunda asuba da shi na karya"
suna haka suka kawo kwanar
gidan su Deedo, hally kuma tai
mata sallama ta mike hanyar
gidan su.
Tana shiga ta tarar da goggo a
kofar dakin ta, ta karasa ta
gaishe ta, bata ko kalli inda
take ba, balle ta ansa, tace "sai
yanzu kika ga damar dawowa
dan uban ki? Wlh in kika yi
wasa sai kin daina zuwa
makarantar banzar nan, ke
dama kwakwalwa irin ta uwa,
babu komai ciki sai majina" ta
saddar da kanta, tace "kiyi
hakuri goggo, in sha Allah
bazan qara ba" tace "munafuka
wadda tayi gadon munafunci,
tashi wuce ki bani wuri kin
mun tsuru da idanuwa kaman
na mujiya" simi simi Deedo ta
miqe tana matse yar kwalla, ta
shige dan akurkin dakin ta, ta
cire uniform dinta, ta canja
kaya sannan ta fito tayi alwala,
goggo sai hararar ta take, ta
koma ta fara sallah, sai a
sannan Hadiza ta dawo. Goggo
ta washe baki tana "Dijangala
ta mai gari, ita kuma tana wani
yatsina, ta isa gaban goggo ta
zauna, tace "ena abinci na" ba
gaisuwa ba komai, abin ka ga
ba tarbiyya, goggo tace "jeki
kitchen indomie tana nan dana
dafa muku keda shehu ki
dauko" tana mikewa, shima ya
shigo ya dawo daga
makarantar, nan suka zauna
suka kwashi indomien su, suka
cire uniform din su, goggo ta
kwada ma Deedo kira, ta fito
da gudu gudu, ta duka gaban
ta, tace "gani goggo" kafin
goggo tace wani abu, Hadiza
tace "ke kwashe kayan nan ki
wanke su tas, kuma wlh kika
mun wankin da bai fita ba sai
naci uban yarinya" shehu yace
"niko kinsan hali na, dan in
zubarwa yarinya da hakora ba
wani aiki bane a wuri na
muddin kikai mun wankin da
bai fita ba" bata ce komai ba,
ta tattara kayan ta wuce wurin
wankin, ta jawo roba zata diba
ruwa, Goggo tace "dakata
munafuka, in baza kije ki debo
ruwan wankin ba, to ki kwashi
kayan ki wuce can wurin
famfon ki wanke su, ke ga yar
iko ko? Har zaki diban mun
ruwa kiyi wanki da shi" bata ce
komai ba, ta koma daki ta
dauko hijabin ta, tazo ta dauki
katon bahon nan, ta wuce
borehole.
A hanya ta hade da hally zata
tafi islamiya, kasancewar tahfiz
take yi, hally na ganin ta, tace
"ke Deedo ina zaki da wannan
katon bahon kamar yar ga
ruwa" kwallan da take boyewa
suka gangaro mata, tace "Hally
na gaji da wannan rayuwar da
nake ciki, kullun cikin bauta
kamar baiwar da aka ciyo a
yaki" Hally ta kalle ta, tace "kiyi
hakuri Deedo wata rana sai
labari" ta goge hawayen tace
"haka ne hally, bari naje kar na
kuma yin wani laifin" hally tace
"in tambaye ki mana" tace "ina
ji" tace "wai ina dangin umman
ki? Ki gudu wurin su mana"
Deedo ta zaro ido, tace "suna
kaduna fa, kuma saida suka zo
tafiya dani goggo ta hana,
kuma ni kinga ko bauchi ban
taba zuwa ba balle kaduna"
hally tace "shikenan, Allah ya
saka maki cin zalin da ake
maki" tace "amen" sukai
sallama, ta wuce ta fara buga
famfo, kasancewar babu kowa
a wurin, ta cika bahon, ta
kinkima ta dora akai, ta cigaba
da sauri zuwa gida.
BA’A SHAN
ZUMA… 04
NA
LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Ta na isa ta tarar ba kowa a
tsakar gidan, can ta jiyo waka
tana tashi daga palon, hakan
ya tabbatar mata kallo suke yi,
ta wuce ta sauke ruwan,
sannan ta fara wanke kayan, ta
gama ta shanya, sauran ruwan
da ta gama wanke masu ta
dauko nata uniform din ta cuda
a ciki, ta gama ta gyara wurin
ta share, sannan tayi alwallar
la'sar.
Palon goggon ta shiga tayi
sallama, ta rakube a bakin
kofa, tace "na gama goggo" ta
juyo a qufule tace "to uban mi
kuma zan miki? Iyii?" Tace
"bakomai" har ta miqe, goggo
tace "ni wlh wannan bala'in ya
fara isata, ace wannan
shegiyar yarinyar kullun ni zan
rinka cida ki, bazan iya wannan
abu ba, ke ba uban komai kike
mun ba, sai dai kizo ki
tsugunna mun kice in baki
abinci, na gano ki munafuka,
mai mugun hali irin na uwar ta,
wuce ga sauran kosai can na
safe da shehu ya kasa ci ki
dauka, dan ni dai ba abinda
zan baki gare ni ba" ta mike
tana tunanin wai wane irin hali
ne uwar ta take dashi, wanda
kullun goggo ta tashi sai tace
mata mai mugun hali irin na
uwar ta, kwalla suka kawo wa
kuncin ta ziyara, tasa hannu ta
share, tace "ya Allah kayi
gafara ga iyaye na" ta shige
kitchen din ta dauko sauran
kosan dan wata muguwar
yunwa take ji, ta tuttura shi, ta
bi da ruwa, sannan ta mike ta
bada sallar la'asar, ta dauko
Qur'anin ta, ta fito.
Palon ta kara komawa, tace
"Hadiza zaki je islamiya ne?"
Tayi banza da ita ta qyale, bata
yi kasa a gwiwa ba ta kara
nanata tambayar, ta mike daga
shingidar da tayi, tace "yau
naga bala'i, wai ke ko dai
mayya ce? Shin in ma zanje
islamiyar tare dake nake
jerawa? Ko ni tsarar ki ce da
zaki zo da wani guntun
munafuncin ki kina tambaya ta"
Tace "Allah ya baki hakuri,
naga kamar baki san lokaci
yayi bane" ta mike ta fita,
goggo ko da yake itama ba
ilimin addinin ya wadace ta ba
ko kala bata ce ba, haka suka
maida hankalin su ga kallon
su, babu wanda yayi kokarin
motsawa bare yayi sallah, daga
gani ma babu wanda yayi ko
da azzahar a cikin su.
Sauri take tayi dan ta riga ta
makara, tasan kuma dole ne ta
anshi hukunci, tana isa Allah
ya taimaka ta an gama taran
yan makara, ta silale ta shige
ajin su, nan ma malam bai
shiga ba, nan fa yan ajin suka
yo mata caa akan ta biya masu
karatun da akayi jiya, domin
yau za a anshi harda, kuma da
yawan su basu iya ba. Ba tare
da bata lokaci ba ta fara
kwararo qira'a cikin muryar ta
mai zakin sauraro, duka ajin
aka yi tsit ana sauraren ta,
haka ta gama biyawa, sannan
kowa ya cigaba da nanatawa
cikin ran shi, har malam ya
shigo aka fara gabatar da
darasi.
Ana tashi daga Islamiyar bata
tsaya bata lokaci ba ta kamo
hanyar gida. Tana dab da
shiga layin su, wasu yan
samari suka tarye ta, suna tai
mata magana amma ko kallon
su bata yi ba, daga bayan ta
taji ana cewa "ke Deedo dan
kin samu ana kula ki shine har
wulakanci kike wa samari ko,
wlh bara naje gida sai na hada
ki da goggo" juyowar da zata yi
taga ashe shehu ne yake binta
a baya ya dawo daga kwallo,
kafar shi tayi budu budu kamar
an tono shi daga rami. Ta
tsaya tace "in ka fasa fada din,
wadannan tsamayen mei zasu
bani da zan tsaya in bata ma
kaina lokaci a wurin su" ta juya
ta cigaba da tafiyar ta. Aiko
shehu ya daga kwallon dake
hannun shi ya daddage ya seta
keyar ta, ya halba kwallon, tayi
tangal tangal ta zube a kasa,
da samarin da sauran yaran da
suke wurin suka dau ihu suna
mata daria, wasu na cewa
"katuwa ta sha kasa" wasu
zafafan hawaye suka zubo
mata, ta mike tace "wlh yau sai
na rama, sai dai duk abinda
zai faru ya faru, shiru shiru ai
ba tsoro bane" ta samu wani
dan dakali ta dora Qur'anin ta,
sannan ta rugo ta cafki shehu,
suka fara dambe, nan dai
dakyar wasu dattijai suka raba
su, ana rike shi yana cewa
"shegiya mai mugun hali irin
na uwar ta, yar tsintuwa kawai"
ita kuma tace "na ji din, dadin
abun dai ni bani fitsarin
kwance, kuma in ka Kara ce
mun mai mugun hali saina
fasa maka baki wlh" wani
dattijo yace "ke Deedo kyale
shi da Allah, shehu ai ba sa'an
ki bane" da yake Allah yasa ita
yarinya ce mai girmama na
gaba da ita, haka ta juya ta dau
Qur'anin ta, ta wuce ta bar
shi…
BA’A SHAN
ZUMA… 05
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Kafin ta isa gida ashe rahoto
har ya isan wa goggo, tana
shiga da sallamar ta, taje
gaban ta ta duka tace "sannu
da gida goggo" bata ansa ta
ba, dan haka ta mike ta shiga
daki ta cire hijab dinta, ta aje
Qur'anin ta sannan ta fito zata
fara aiki, Hadiza ta gani ta fito
da dorinar malam Ilu
kasancewar shi tsohon kurtun
dan sanda, ta mika wa goggo,
amma goggo tace bari shehun
ya shigo da kan shi zai rama
abinda tai mashi, bata ida rufe
bakin ta ba, shehu ya shigo
yana ta gurnanin kuka, goggo
ta fara lallashin shi, tace "anshi
bulalar nan ka dake ta yadda
ranka yai maka" aiko shehu ya
ansa ya fara tsula mata, tana
ihu amma goggo ko motsi bata
yi ba daga inda take, saida yai
mata mai isar shi, sannan ta
taso tace su debo mata ruwa a
kofi, suka dibo suka miqa
mata, ta juye shi a kan Deedo,
sannan ta fara kwalfar ta, sai
da tai wa yarinyar nan lilis
kamar bata san hanyar da
imani ya biyo ba, sannan tace
"ke dan baki da mutunci, kin
riga kinyi gadon butulci wurin
uwar ki, har kin isa ki taba
mun da, har kina ce mishi mai
fitsarin kwance, to uwar mai
fitsarin kwance ita take rufa
miki asiri take cida ki, kuma
daga yau baki da abincin dare
a gidan nan, tsinanniyar
yarinya kawai" tayi kwallo da ita
da kafa, sannan ta wuce ta bar
ta tana ta rera kukan da sautin
shi ko fita baya yi…
Haka ta qaraci kukan ta babu
mai lallashin ta, daqyar ta
lallaba ta mike tayi alwalla ta
shige dan akurkin ta, a zaune
ma take sallar saboda tsabar
dukan da tasha, tana gamawa
ta dan shingida akan tabarmar
kabar ta, addu'a take a cikin
zuciyar ta, ya Allah ya kawo
mata karshen wahalar nan,
shawarar da hally ta bata ita ta
fado mata a rai, ta fara tunanin
ko dai ta gudu din? Wata
zuciyar tace "karatun naki fa
Deedo, in kin gudu wa zai sa ki
a wata makarantar har ki zama
hematologist" a fili ta furta
"duk runtsi duk wuya zan daure
har inga na cimma burina, ya
Allah ka taimake ni" tana nan
har aka kira isha'i, ta mike tayi
ta a zaune, sannan ta koma ta
kwanta, a haka bacci ya sace
ta duk da matsananciyar
yunwar da take ji. Ba ita ta
farka ba, saida taji saukar
robar ruwan goggo tunda bakar
asuba…
BA’A SHAN
ZUMA… 06
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tamike a firgice, tana kokarin
shafe baccin dayaci fuskanta
sannan tamike,goggo tace
cikin bacin rai "tsinanniyar ya,
baki iya komi ba sai yada baki
kiyi bacci saikace gidan
uwarki!,, ni da Allah fice ki
debo min ruwa,"
Tafito tana dirin sanyi tadauko
bahon ta ijiye agefe ganin
goggo tashige yasa ta yi sauri
tadauro alwala sannan tashige
dakin don tayi sallah, tana
ruku'un karshe taji saukan
zuban ruwan sanyi akanta, a
shide tatashi tazauna don tayi
tahiyya, goggo kuwa tasa kafa
ta tokareta sannan tace
"munafukar yarinya , ni zaki
rainawa hankali? Awan ki nawa
kina sujjada?, wawiyar ya!,"
bata yanke sallahn ba saidata
yi sallama alokacin takafayin
wani tari wanda yasata
gigicewa, goggon ta kamota
sannan tajefo waje inda tazfadi
agefen bahon, abunka da
tsohon bahon daya tsufa, jira
yake yaji nauyi yafashe tuni ya
tsage, habawa kamar goggo
jira takeyi ta fasa, tadubo
gefen gadon shehu tadauko
belt takafa zugeta, inda take
shiganta deedo ihu take tana
ambaton Allahnta, makwabta
dasuke shirin zuwa masallaci
hankalinsu duk ya tashi anma
bawanda yashigo balle yakawo
agaji don sunsan halin goggo
sarai,
Bayan tagama shiganta da
duka kwakwaran motsi deedo
batayi, tafice tabarta agun,
kanta nawani matsanancin
ciwo, tadauki dayan katon
bahon wanda shi goggon tace
tadauka kuma tacikoshi akanta,
tafito tana tafiya dakyar haka
ta dingisa har borehole , sanyi
na shiga jikinta gashi tagagara
motsawa, haka ta ajiye bahon
tacigaba da zama jiratake taji
dadin jikin tamike donta tuko
ruwan, akanta taji taku, bata
dago ba balle tagane waye,
sallama yayi bata amsa ba,
ganin haka yasa yaja bahon
yaci sannan yacika jarkarsa
daya dauka, sannan yace
"baiwar Allah ko zaki taimaka
kitashi,yayi safiya dayawa ace
mace ta zo tazauna anan, bata
kulashi ba, donhaka shima yaja
yazauna, saidata fara jinta
daidai sannan tadago kanta,
alokacin yaganeta, deedon
gydan goggo, uhm yagane
komi kobata mishi bayani ba,
donhaka kawai sai ya ce "tashi
muje na taimaka miki " yadauki
bahon akansa dakyar nauyin
har kirjinsa yaji , toh shi namiji
kenan ballatana kuma mace,
tana biye dashi har suka isa
kofar zaure googo tagani a
kofar gun takama kunkumi
gabanta yakara fadi rassssss
BA’A SHAN
ZUMA… 07
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Wani mugun salati goggo ta
kwasa, tace "lallai yarinyar nan,
abinda kika koma yi kenan?
Meye hadin ki da wannan
katon? Wato kullun na aike ki
dama shi yake dauko miki
ruwan ko? Yau zaki sani" Tana
kokarin warto ta, Ado ya shige
tsakiyar su, yace "goggo wlh
ba laifin ta bane, naga ne bata
da lafia, shine na taimako mata
da ruwan, kiyi hakuri hakan ba
zai kuma faruwa ba dama yau
aka fara" tace "habawa
munafukai, yau duk sai kun ci
uwaku" tayi cikin gida da sauri,
Ado ya lallaba ya sauke ruwan,
dagowar da zaiyi yaga goggo
da wani dan icce ta nufo kan
shi, da gudu suka runtuma
waje daga shi har Deedo, ta
leko tana cewa "shegu, yau da
kun tsaya da kunga karyar
munafunci, ke kuma kya zo ki
same ni ina nan ina jiran ki" ta
juya ta koma ciki. Deedo dai
banda kuka babu abinda take
yi, Ado yace "kiyi hakuri Deedo,
muje ciki in yi mata bayani, na
san zata fahimta" suka juya
suka shiga cikin gidan a tare,
goggo ta kare masu kallo, tace
"wai Ado dama kaine?" Yace
"eh wlh goggo, kiyi hakuri baza
a kuma ba" tace "ka ci
albarkacin kai ne, amma wlh
kar in kuma gani ka taimakawa
waccen tambadaddar" Ado
yace "baza a kuma ba goggo"
ya juya zai fita sai ga Hadiza
ta fito daga daki sanye da
uniform, tana wani karairaya,
tace "Ado ne yau a gidan
namu" ya watsa mata wani
kallo, sannan ya juya, ya fice.
Goggo tace "Dijangala wai ba
dai wannan Adon bane dama
kike fada mun?" Tayi narai
narai da ido tace "shine goggo,
kinga ma ko magana baya
mun" goggo tace "aihoo, shi
yasa waccen tsinanniyar ta
fara shige mai kenan, to wlh ki
shiga taitayin ki, Ado ba irin
mazan ku bane kucakai" ta
juya wurin Hadiza tace "ki bar
komai a hannu na dije na, zo ki
karya kumallo ki wuce kar kiyi
latti" ta zauna ta fara cin
abincin tana galla wa Deedo
harara, ita dai bata ce uffan ba,
ta koma zaure ta dauko bahon
ruwan ta, ta kawo ta aje.
Da sauri ta wuce daki ta cire
hijabin ta, sannan tazo ta fara
wanke wanke, ta gama ta share
ko ina duk tayi aiyukan data
saba, sannan ta shige ta
burmo uniform dinta ta fito ta
leka dakin goggo bata nan, ta
koma Palo a can ta ganta ta
cake dauri, ta dora daya kan
daya tana sakacen hakori, a
gefe guda kuma tana sauraren
radio…
BA’A SHAN
ZUMA… 08
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Da sallama ta rakube a kofar
palon tace "goggo na gama zan
tafi" a harzuke ta dago tace "ki
gaida su, ko kuma wata tsiyar
kike so in miki, iyiii?" Tace "a'a
bakomai" ta mike ta fito, har ta
kusa zuwa kofar zaure goggo
ta kwala mata kira ta dawo, ta
duka tace "gani goggo" ta
watsa mata harara tace
"munafuka, sai kace mutuniyar
arziki, mtseww wuce ga
dumame can ki dauka, nasan
abinda kika tsugunnawa kenan"
tace "nagode" ita kuma ta
cigaba da banbami tana ta
faman soka mata zagi kamar
wata mahaukaciya sabon
kamu.
Ita dai Deedo dumamen ta
kawai take kwasa dan ta riga ta
Saba da wadannan munanan
halaye na goggo. Tana
gamawa ta wanke hannun ta,
tasha ruwa, tayi sadaf sadaf
zata fita goggo ta kwada mata
kira, ta juyo a firgice, goggo ta
kara hankado dankwalin ta
gaban goshi tace "an shi nan
tsinanniya" tayi mata dakuwa,
Deedo ta dukar da kanta kasa,
ta matso ta bata rankwashi
tace "Allah yasa in kinje
gwamnati tace ta daina biya
miki wannan kudin makarantar
dan banga uwar da kike
koyowa ba, ke ni da ina da iko
ma da da kaina zanje wurin
gwamnan in sa a kore ki wlh,"
taja tsaki, ta ce "nasan
maganin ki shegia, mai hali irin
na uwa, wuce ki ban wuri" ta
juya sum sum ta wuce, tana
zuwa zaure ta arta da gudu,
dan kar goggo ta biyo ta, gashi
dama ta riga ta makara.
* ***
Tana tasowa daga
makaranta kamar yadda ta
saba ta fara bunguza sauri
kamar zata tashi sama. Hally
ta fallo da gudu tazo ta sha
gaban ta, tace "ni anshi nan
uwar yan tsoron goggo" ta
mika mata bakar leda. Deedo ta
dan murmusa tace "menene
wannan kuma" hally tace "man
shafawa ne da sabulun wanki
da na wanka, dan na lura ko
wanka bakiyi Deedo, ga sanyi
duba kiga yadda kika yi furtutu,
shi yasa na roki mama nace ta
siyo in kawo miki, saura kuma
kije ki kai wa wannan mala'ikar
mutuwar" ta fada tana murguda
baki. Deedo ta rungume ta,
tace "nagode hally, in sha Allah
idan na zama likita ke zan ba
albashi na na farko" suka sa
daria duka, sannan hally ta
anshi ledar ta sa mata cikin
jaka, suka juya suka cigaba da
tafia suna firar exams da zasu
fara next week…
BA’A SHAN
ZUMA… 09
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Deedo ce ita kadai tsaye
gaban borehole tana ta faman
buga famfo tun karfin ta, ga
kiraye kirayen sallar maghriba
ana ta kwadawa, amma bata da
yadda zata yi, dole ta debi
ruwan nan, in ba so take taci
na jaki a wurin goggo ba. Daga
gefe taji ana cewa "shine kika
zo kina ba kanki wahala bayan
nace ki daina buga famfon nan
zai iya yi miki illa a matsayin ki
na diya mace mai karancin
shekaru" ta juyo da dan
murmushin ta, tace "bana son
kullun ina sanya ka cikin
matsalolin rayuwa ta, nagode
da kulawar ka" Ado ya karaso
gaban ta yace "wuce ki zauna,
bara na ida cika miki" ganin
fuskan shi ba alaman wasa
yasa Deedo ta koma baya, ya
ida cika bahon ya dauko, yana
gaba tana bin shi a baya, dan
yanzu kullun shi yake dauko
mata ruwa, da sun zo zauren
gidan goggo, sai ya dora mata
ta shige. Haka nan kuma yaji
Allah ya dora mashi masifar
tausayin yarinyar, wani lokacin
har kudi yake bata amma bata
ansa, haka zai gaji ya maida
yan kudin shi cikin aljihu. Suna
karasowa zauren yace "to
matso ki ansa" ta matso ta
miko kanta, shi ma ya matso
zai dora mata, basu tantance
ba suka ji muryar goggo ta
fasa wani mugun ihu, Ado da
ya daga bahon ruwa zai
dorawa Deedo bai san lokacin
da bahon ya subuce ya fadi
kasa ba, goggo wani irin ihun
munafunci take kurmawa tana
salati tana cewa "Deedo daman
abinda kike yi kenan? Jama'a
ku taimaka mun na shiga ukku
na lalace, wayyo Allah na yan
iska har cikin zauren gida na"
kafin wani cikin su ya ce wani
abu, tuni wurin ya cika dam da
mutane masu zuwa masallaci,
yara da manya..
BA’A SHAN
ZUMA… 10-11
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Shidai Ado tsayawa yayi yana
mamaki, ikon Allah bata
karewa, gwaggo ta tara musu
jama'a sannan takiyin shiru
balle su fahimci me ake ciki,
cikin sanyin murya yace "ba
abunda kike tunani bane,
taimaka mata kawai nayi"
Ta katse shi da karfi tareda
cewa "kaidin banza kaidin wofi,
meya hadaka da ita? Lalata ka
zatayi don yanzu idonta a bude
yake gwara kadena bata
lokacinka"
Wata makwabciyarsu tace
"Kaga kai ado duk da taimako
kakeyi, amma kaga wa ita kake
jawa balai, donhaka ka kiyaye
kawai"
Kansa akasa ya amsa, nan
akadan fara watsewa gwaggo
kuwa tariko kunnen deedo
sannan tayi cikin gida da ita,
rufeta tayi adaki tasa shehu ya
tsinko bulali, ta sa ta kwanta,
ta zuba mata ruwan sanyi
tashiga zuba mata bulalinnan,
tas suka karye ajikinta, deedo
bata iya tashiba don
mazaunanta kumbura sukayi
tum, nan da nan jikinta yayi
jajur, sai hadiye numfashi
takeyi, domin kuwa kukanma
guduwa yayi yabarta ahaka,
Da ja jiki ta isa daki, tayi kuka
tagode Allah, takuma roki Allah
daya gaggauta fitar da ita cikin
wannan kangin datake ciki,
sallama taji tundaga tsakar
gida, muryar haly donhaka taji
gabanta yafadi, don zuwa
gidansu ba aladan haly bane,
gashi dare yarufa sosai,
gwaggo ce ta tareta tareda
cewa "mekuma kikazo yimata?"
"Assighnment fa aka bamu, toh
tabat nata shine nakawo mata
tana sauri zataxo gyda"
"Kokuma tana sauri taje gydan
saurayinta ba, dake a ke hada
baki ai"
"A a wlh gida fa kawai take
zuwa, bata tsayawa"
"Toh koma dai meye, ki tattara
kiyi kibar gydannan, minti biyu
nabaki"
Itadai haly jikinta narawa
tashigo , da tocinta ahannu
ganin halin da deedo take ciki
tasaka kara…
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Gwaggo tashigo tareda cewa
"meye kuma?"
" naganta kamar ta mutu ne,
gwaggo kitaimaka akaita asibiti
wlh zata mutu"
Ganin haly zata bata mata rai
yasa tajanyeta ta wullata waje
tarufo kofan, dakinta tawuce
batare tadamu da halin da
deedo take ciki ba
Haly akofar gidan hankalinta a
tashe tarasa wazatayiwa
magana, kuka nabin idonta
donhaka gida takoma tana
addua wa kawar tata,
Haka deedo takwana da asuba
kuwa gwaggo tashigo da
ruwan sanyinta, ta kwara mata
anma bata motsa ba, hakan
yasa taji jikinta yayi sanyi
tafara jijjiga deedo,harsai da ta
juyo fuskanta, jini tagani
naxuba, bashiri tamike tace
"shehu jeka kiramin malam
audu(likitam gargajiya),
shegiya tsinanniyar yarinya
zata tonsmin asiri, ta Allah
bataki ba "
Da gudu yafita, mituna kadan
saigashi yashigo
"Malam tayar min da yarinyyan"
"Anma dai kinsan cewa yaune
na hudu dana ke xuwa don
ceto rayuwarta, idan har bazaki
iya riketaba kikaita gidan
marayu mana"
"Kai tsaya banson raini!, kana
abu ba lissafi, ni meruwana da
mutuwarta ko ranta,ai inta
mutu zanfi kowa jin dadi,
damuwana kawai karta mutu
ahannuna"
Girgiza kai yayi donganin
jahilci a filin Allah
Ya dubata yaga dogon suma
ne, nan da nan yayi dabarunsa
sannan tafara tari, saidai jikin
baya motsawa, yajuyo yakalleta
sannan yace "tafarka saidai
dole kibari tayi jinyan jikin"
"Badamuwa naji" ficewa yayi
don bazai iya kallon wannan
bakim cikiba,
Yana ficewa tariko kunnen
deedo
"Bari ingayamiki ba mutuwa ko
hadiye ranki kikayi bazaki
mutuba, don wlh bazanje
prison akan yar mage ba.
Shegiya tsintacciya,
laananniyar ya, ido kamam na
mayu," hawaye ne kawai
yakebin idon deedo,
"Sannan kitashi kisan yadda
zakiyi kidebo ruwa yarana
zasuyi wanka!"
Tafice tanata guna guni, deedo
tayi godiya wa Allah kamar
yadda musulunci ta bukaci
kowani dan adam yake godewa
Allah bayana tir da halin
dayake ciki ba, musamman in
kashiga wani Hali, kamata yayi
kasa hakuri dangana kasaka
cewa Allah kadai zai taimakeka
yarufa maka asiri, shikadai
keda iko akanka , shike baka
jarabawa, kowani hali kake ciki
akwai wanda yafika wahala, sai
ka godemishi daya barka da
ranka. Wani yanemi rai
baisamuba , hakan nakara
karfin imani, donkuwa koda tayi
godiyan tariko bango, tabi
bango har jikin ginin sannan
tariko bahon tana bi da bango
harta isa bakin zauren jitayi
anhakadata dakarfi ta tsinci
kanta akasa
BA’A SHAN
ZUMA… 12
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tayi baya luu zata zube, Allah
ya taimaka tana dab da bango
ta dafa shi tun karfi har saida
hannun ta yayi kara, cikin
bacin rai goggo tace
"tsinanniya, ni zaki ja wa
sharri? Iyii? Zaki fita kina wani
bin bango kamar kadangaruwa,
wlh ko ki mike ki dauka bahon
nan ko na kwada miki wannan
iccen a gadon baya" ta nuna
mata wani katon icce da yake
rike a hannun ta. Bata jira taji
mai zata Kara cewa ba, ta
warci bahon, tayi waje cikin
sauri. Saida ta danyi nesa da
gidan sannan ta samu wuri ta
zauna ta dan huta, sannan ta
dau bahon ta karasa gaban
famfon ta fara tukawa, ta cika
shi, ta kinkimo ta dora a
kanta, ta fara zabga sauri zuwa
gaban goggo. Tana isa ta tarar
da tulin bargunan fitsarin
shehu, tana aje ruwan goggo
tace ta kama su ta wanke ta
shanya. Duk mai imani idan
yaga halin da Deedo take ciki a
wannan lokacin dole ya
tausaya mata, amma goggo da
yake ta kwashe kayan ta daga
gaban manzo, ko kallon ta bata
yi balle taji tausayin ta. Haka
yarinyar nan ta wanke kayan
nan, ta shanya, ga wata rawar
sanyi tana yi, Jikin ta yayi zafi
rau, haka ta cigaba da bauta a
cikin gidan nan, tana gamawa
ta lallaba ta shige dan akurkin
dakin ta, yau bata ma jin zata
iya zuwa makaranta, dan haka
ta dan shingida a saman
tabarmar kabar ta, tasa
hannuwan ta ta tallabe kanta,
saboda azabar ciwo da yake
mata. Muryar hally taji tana
kwada sallama, goggo tayi
caraf ta fito tace "ke ko
almunayar yarinyar nan, ba jiya
na kore ki ba, shine kika
lallabo kika dawo" ta dan galla
mata harara, sannan tace "nazo
ganin jikin Deedo ne, kuma ma
in kika yi hakuri ni ba nan zan
kwana ba" muryar Hadiza suka
jiyo tana cewa "ke wlh kar ki
wa mutane rashin kunya anan
kisha shegen duka" bata tanka
ta ba, ta bi ta gefen goggo zata
shiga dakin Deedon, ta ko jawo
kunnen ta, tace "wannan ya
zama shine zuwan ki na karshe
gidan nan, dan na kula ke kike
koya wa waccen shegiyar
iskanci, in ba haka ba wlh kika
kara zuwa sai na karya wannan
shegun kafafuwan naki masu
kama da na sauro" tasa kara,
tace "ni dai sake mun kunne
gaskia" goggo ta hankada ta,
tayi gaba, tana yi mata Allah ya
isa cikin zuciyar ta.
BA’A SHAN
ZUMA… 13
NA LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Yadda taga Deedo ta takure
wuri daya tana wata irin
kyarmar sanyi, abin ya bala'in
bata tausayi, nan take taji wata
muguwar tsanar goggo ta kara
shiga ranta, wasu kwalla masu
zafi suka zubo mata, ta karasa
gaban ta, tana yi mata sannu,
Deedo kasa magana tayi,
hawaye ne kawai yake anbaliya
a fuskan ta. Hally ta ciro rigar
sanyin jikin ta, ta sanya mata
sannan ta tayar da ita zaune, ta
bude skool bag dinta ta fito da
biredi da shayi a cikin roban
coke, ta mika mata, kamar
tasan abinda yake damun ta,
ba tare da bata lokaci ba
Deedo ta ansa ta fara yagar
bread din nan, bata saurara ba
saida ta gama cinye shi tas,
sannan ta kora da ruwan
shayin tayi gyatsa, hally da
hawaye suka cika idon ta, ta
share ta fito da paracetamol ta
mika mata tasha. Sannan tace
"ki kwanta ki huta, zan fada ma
form master baki da lafia,
anshi sauran maganin nan ki
boye in anjima ki kara shan
guda biyu, kiyi hakuri Deedo ki
dauka wannan bakomai bane,
wata rana sai dai ki bada labari
in sha Allah,kinsan ita rayuwa
daman ta gaji haka, kuma BA'A
SHAN ZUMA SAI AN SHA
HARBI, ina ji a jikina akwai
ranar da goggo zata bukace ki,
ranar da bata da wani
mataimaki bayan ke, Allah ya
sauwake kinji" ta dago
idanuwan ta cike da kwalla,
bakin ta na kyarma tace
"nagode hally, Allah ya saka
maki da alkairi, ke kadai kike
sona duk fadin duniyar nan,
Allah ya biya ki da gidan
aljanna" ta rufe mata baki da
hannun ta, sannan ta share
mata hawayen, ta dau jakan ta
tayi mata sallama, ta fito ko
kallon inda goggo da ya'yan ta
suke bata yi ba, ta wuce ta bar
gidan.
Deedo na nan kwance kamar
gawa, dan ko motsin kirki bata
iyawa, goggo ta leka dakin,
tana kiran sunan ta amma
shiru, ta karasa gaban ta tasa
kafa ta hankada ta, cikin gigin
bacci tayi firgigit ta mike tana
zara idanu…
BA’A SHAN
ZUMA… 14
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Kafin ta karasa washewa taji
goggo ta damko gashin kanta
tayi waje da ita. Cikin kuka tace
"Dan Allah goggo kiyi hakuri,
wlh ban san mai nai miki ba"
ta watsar da ita a kasa tace
"yanzu zaki sani dan uban ki"
dakin ta ta wuce ta fito da
almakashi tace "bara na aske
wannan shegen kan, sai inga
ta karyar iskanci. Har ni zaki
bazawa wani banzan gashin ki
kina ji ina kira amma kika yi
shiru" ta fara ihu ta tashi ta
runtuma da gudu tayi hanyar
zaure, goggo ma ko bata yi
kasa a gwiwa ba ta daddage ta
cafko ta, Deedo tasa hannuwan
ta ta lullube gashin ta dasu,
amma ena goggo ta riga ta
damko wani gefe na gashin
mai uban yawa, bata yi wata
wata ba tasa almakashin ta
datse. Deedo ganin gashin ta
mai uban yawa a kasa yasa ta
kurma wani gagarumin ihu,
wanda hatta goggo saida ta
razana. Malam Ilu ne ya shigo
gidan da sauri, ganin abinda
goggo ta aikata yasa ya karasa
shigowa da gudu, sai da ya
daddage sannan ya hankadar
da goggo ta fadi kasa warwas!
Cikin daga murya yace "Ke
Batula kiji tsoron Allah, wlh ina
jiye miki ranar da alhakin
wannan yarinyar zai tambaye
ki, ke yanzu duk uban dukan
da kikai mata jiya bai ishe ki
ba, dan bakin ciki shine yau
har da aske mata gashi, ke
baki tunanin wata rana zaki
mutu ki bar abinda kika haifa?
Ya zaki ji idan wani ya rinka
cuzkuna musu irin yadda kike
wa wannan marainiyar Allahn,
in baki iya rike ta ki kai ta
gidan marayu mana.." kafin
mallam Ilu ya rufe bakin shi
goggo ta daddage ta cilla mai
almakashin da yake hannun ta,
bai tsaya a ko ina ba sai a
saman goshin shi, kafin yayi
wani motsi jini ya riga ya
wanke mashi fuska tasss!
BA’A SHAN
ZUMA… 15
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Ihu Deedo ta saka ganin jini ya
wanke wa mal. Ilu fuska, da
gudu ta ruga ta warto wani
kallabi na goggo da yake
shanye akan igiya tana kokarin
daure mai wurin, cikin gadara
da rashin nadamar abinda
goggo ta aikata ta taso da
sauri ta warce kallabin, tace
"wato iskanci naki har da irin
wannan kucakan kike yi? Mei
zaki samu a jikin wannan
tsohon? Lallai Deedo, daman
na dade ina zargin ku, sai
gashi zato na ya tabbata" ta
juya ta kalli mal. Ilu da yake
raba idanuwa tace "to wlh baku
isa ba daga kai har ita, kuma
idan ma kashe ta nake tana
farkowa akwai abinda ya
shalleh ka ne? Ince zama na
take yi a gidan ko? Ko ko
daman dan kuna labewa kuna
iskancin ku shine har zaka zo
ka tare mata, to ni Batula ba
kanwar lasa bace, duk wanda
yace zai ja dani wlh sai jikin
shi ya gaya mishi, wannan ma
da na maka kadan ne, dan a
ciki na so in caka maka
almakashin ka mutu kowa ma
ya huta dan banga amfanin da
kake tsinanawa wani ba a cikin
gidan nan" tana kaiwa nan, ta
bi ta gefen su, tasa kafa ta
hanbare Deedo ta kara gaba
abin ta..
Deedo wadda tausayin mal.
Ilu yasa ta manta da tata
larurar, tace "kayi hakuri baba,
ka lallaba kaje chemist a gyara
maka wurin kar wata cutar ta
shiga" yace "kar ki damu
Firdausi, dunia ce, ta ishi
Batula riga da wando har ma
da mayafi" ya mike dakyar yana
ganin jiri, ya wuce ya fita ya
bar gidan.
Allah mai iko, ashe wannan fita
ita ce fitar mal. Ilu ta karshe,
yaje zai tsallaka titi ba tare da
ya kula ba wani mai mota ya
banje shi, nan take ya ce ga
garin Ku nan.. Kulli nafsi
za'katul maut! Allah ya jikan
mal. Ilu da rahma amen!
BA’A SHAN
ZUMA… 16
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Hakika deedo taji rasuwan mal.
Ilu , tana tuna kalmominsa na
karshe akanta,gwaggo batayi
nadama ko kadan ba, don
taaziya ma sau daya ta leka,
Deedo kuwa harta rame, tafada
takara baki, asatin tafara zuwa
makaranta, cikin ikon Allah
saigashi wani malami yashigo
ajin, yadebi masu kokari uku,
ciki harda deedo sukaje ofishin
principal, nan ya sanar dasu
cewa gasa zasuyi wanda akwai
baki daga kaduna zasuxo don
su ga wannan gasa, akwai
kyaututtuka masu tsoka dazaa
raba, deedo tayi farin ciki
sosai, nan da nan akabasu
topic na debate
FEMALE EDUCATION IS MORE
USEFUL THAN MALE
EDUCATION IN THE SOCIETY,
inda ita zatayi supporting,
zuwa tayi tasami malamin
turancinn su tabashi don
yarubuto mata hujja dazata
kare kanta, yakuwa karba,
Ranan da tadawo gida duk
bakin cikin da gwaggo ke son
tusa mata, deedo taki bata rai
sai faraa take abun harya
damu gwaggo, washegari
dawurwuri tadebo ruwanta. Duk
da bayanta baigama warkewa
ba tanufi makaranta tanajira,
hally tayi mamakin ganinta
dawuri haka, malamin na isowa
takarba, tafara haddacewa, har
ajiye haly tayi tana koya
agabanta, dahaka tahaddace
komi akanta takuma yi
murajaan yadda zata fita
tabada tsokacinta
Ran jumaa aka taru a hall na
makaranta duk dalibai suntaru
don ganin wannan ranan da
zaaraba kyaututtuka, karfe
takwas na safe aka bukaci
suje, agyda kuwa tunda shehu
yazo yasanar da gwaggo
abunda zai faru , gwaggo ta
tsiri aiki ranan, harda sa deedo
wankin bango, deedo tanayi
zata fita tadauko ruwan kayan
miya tabata wai tafitar, tsabar
nauyinsa saidaya bata mata
kaya gashi batada wani
uniform din sawa, dawuri tafice
agydan don isa makaranta
BA’A SHAN
ZUMA… 17
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Hakika deedo taji rasuwan mal.
Ilu , tana tuna kalmominsa na
karshe akanta,gwaggo batayi
nadama ko kadan ba, don
taaziya ma sau daya ta leka,
Deedo kuwa harta rame, tafada
takara baki, asatin tafara zuwa
makaranta, cikin ikon Allah
saigashi wani malami yashigo
ajin, yadebi masu kokari uku,
ciki harda deedo sukaje ofishin
principal, nan ya sanar dasu
cewa gasa zasuyi wanda akwai
baki daga kaduna zasuxo don
su ga wannan gasa, akwai
kyaututtuka masu tsoka dazaa
raba, deedo tayi farin ciki
sosai, nan da nan akabasu
topic na debate
FEMALE EDUCATION IS MORE
USEFUL THAN MALE
EDUCATION IN THE SOCIETY,
inda ita zatayi supporting,
zuwa tayi tasami malamin
turancinn su tabashi don
yarubuto mata hujja dazata
kare kanta, yakuwa karba,
Ranan da tadawo gida duk
bakin cikin da gwaggo ke son
tusa mata, deedo taki bata rai
sai faraa take abun harya
damu gwaggo, washegari
dawurwuri tadebo ruwanta. Duk
da bayanta baigama warkewa
ba tanufi makaranta tanajira,
hally tayi mamakin ganinta
dawuri haka, malamin na isowa
takarba, tafara haddacewa, har
ajiye haly tayi tana koya
agabanta, dahaka tahaddace
komi akanta takuma yi
murajaan yadda zata fita
tabada tsokacinta
Ran jumaa aka taru a hall na
makaranta duk dalibai suntaru
don ganin wannan ranan da
zaaraba kyaututtuka, karfe
takwas na safe aka bukaci
suje, agyda kuwa tunda shehu
yazo yasanar da gwaggo
abunda zai faru , gwaggo ta
tsiri aiki ranan, harda sa deedo
wankin bango, deedo tanayi
zata fita tadauko ruwan kayan
miya tabata wai tafitar, tsabar
nauyinsa saidaya bata mata
kaya gashi batada wani
uniform din sawa, dawuri tafice
agydan don isa makaranta
BA’A SHAN
ZUMA… 18
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Angaji da jiranta hakan yasa
aka fara kawai, dasauri tashigo
tazauna, ruwan tumatur agefen
riganta tana kokarin
kakkabewa, kanta a kasa
yayinda wacce tafarayi
agefensu takeyi, kasancewar
sune yan supporting, tana
gamawa daga yan opposing ,
first speakernsu yafito yayi
sannan yakoma anan aka kira
sunanta
Firdausi kabir sani, tafito a
sanyaye ta tsaya, sannan
takalli high table din tafara
bayaninta
"Mr.principal sir, honourable
panel of judges, accurate
timekeeper, co-debators, my
collegue,ladies and
gentlemen…….." Kanshi na
kasa daga kan high table
yadago dob ganinta, fararen
idanunta yagani, yayinda take
bayaninta, yadda take furta
haruffanta bawanda zaiyi
tunanin daga kauye take,
tashin birni kawai, don tana
fitar da kowanni kowanii hakki
na kalamunta, yadda take
Haka yata kallonta harta idar
da batunta, wani tafi hall din
yadauka kowa na tofa
albarkacin bakinsa, yayinda
alkalai suketa zuba mata mark,
haka kowa yazo yayi nasa.
Shikam hankalinsa yayi kanta,
idonsa zur akanta har abokinsa
nagefensa yadan sunkuyo
sannan yace
"Yadai lafiya naganka haka?"
Yadan gyra murya don muryan
takame ta ciki yace
"Wacan yarinyan, second
speaker"
[10/12 01:16] Lubieee: BA'A
SHAN ZUMA.. NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Murmushi Faroukh ya saki,
yace "kai ko meye hadin ka da
ita? Ko ka santa ne?" Ya
girgiza kai, yace "voice dinta
ne exactly irin na ummi na,
look at ha, hatta yanayin ta
wlh" yace "haba abokina, ni
kam banga kaman ba, ko dai
ko dai?" Ya fada yana daria.
Suna haka, aka fara kiran
daliban don su anshi
kyaututtukan da aka tanadar
masu, aka kira 3rd position,
sannan 2nd, sai daga karshe,
principal ya anshi mic ya fara
jawabi, wanda duk yawancin
bayanan nashi yayi su ne akan
namijin kokarin da deedo tayi,
ya yaba mata, sannan daga
karshe yace "I'll like to call on
stage Dr. NAWAF KHAMIS!" Ya
mike cikin takun shi na kasaita,
kowa a wurin hankalin shi yayi
kan shi, the most honourable
nd young academic Dr. Ya
karasa gaban principal ya mika
mashi hannu, bayan sun gaisa
ne principal din ya bashi mic,
tare da wata yar paper ya koma
wurin shi ya zauna. Ya buda
papern cikin voice din shi mai
wani irin zaki da girma, irin ta
cikakken namijin da ya ansa
sunan shi, ya kuma san abinda
yake yi, ya fara jera tsararran
turancin shi wanda ya tafi da
imanin mutanen da suke wurin,
most especially Deedo, wadda
a duniya ba abinda take so irin
taga hadadden namiji dan boko
wanda ya iya tsara turanci. Ya
gama jawabin shi, sannan ya
kira FIRDAUSI KABIR SANI a
matsayin dalibar da ta zo 1st a
cikin daliban, nan da nan wuri
ya kaure da tafi, ita kuma a
natse ta mike, kanta a kasa ta
karasa saman stage din. Nawaf
wanda tunda ta taso ya zuba
mata idanun shi, har ta karaso
gaban shi, nan ya dauko gifts
dinta, ya bata, haka duk abinda
ake ya kasa dauke idon shi a
kanta.
BA’A SHAN
ZUMA… 19
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
A haka aka gama gabatar da
duk abinda ya dace, sannan
aka rufe taro da addu'a, kowa
ya kama gaban shi.
Ana fitowa Deedo tare da hally
suka rungume juna,suna
murna, nan da nan wasu
hawayen farin ciki suka saukan
mata, ta kalli hally tace "ina ma
ina da wani wanda zaiyi proud
dani a irin wannan ranar, ina
ma iyayena suna raye suga
wannan abin farin cikin da ya
same ni" hally tace "kar ki
damu Deedo, Allah yana tare
dake, haka nima ina tare da ke
100%, iyayen ki kam ki dage
da yi masu addu'a, shine
babban abin da suke bukata
daga gare ki" ta share
hawayen, tace "in sha Allah
hally, nagode miki da duk wani
abun alkairi da kikai mun a
rayuwa, bazan manta dake ba
har abada" suka jero da niyyar
tafiya gida, sun zo ta wurin
staff room zasu wuce wani
yaro yazo yace "Deedo ana
neman ki a office din principal"
bata tsaya bata lokacin komai
ba, ta mika wa hally gifts din
da suke hannun ta, sannan ta
wuce zuwa kiran da ake mata.
Tana shiga ya dago dara daran
idanun shi masu matukar
haske da sheki, bai aje su a ko
ina ba sai saman kyakkaywar
fuskar ta. Dam taji gaban ta ya
buga, ta karasa da sallamar ta,
ta samu gefe ta duka. Principal
ya maida kallon shi ga Nawaf
yace "Wannan kake nufi?" Ya
girgiza kan shi alaman ita fa,
principal din yace "no problem,
ga ka ga ta ai" kafin Nawap ya
buda bakin shi, wani teacher
ya leko, yayi ma principal
magana, haka ya mike ya fita,
ya bar su a office din daga shi
sai ita. Kallon ta yake, yana
son ya karanci wani abu da ya
gani tattare da ita, ba komai
bane illa damuwa da rashin
samun natsuwa tare da
kwanciyar hankali. A hankali ya
fara magana "Firdausi ko?"
Kanta na kasa, dan ta kasa
hada ido dashi, wani irin
Kwarjini yake mata, cikin siriyar
murya tace "yes sir" yace "yu
did a good job today, kin fita
kunyar makarantar ki, malaman
ki tare da dalibai yan uwanki, I
know they 're proud of yu" har
cikin zuciyan ta abin yai mata
dadi, dan har sai da wani
murmushi ya bayyana akan
fuskar ta!
BA’A SHAN
ZUMA… 20
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Ya cigaba da cewa "well,
dalilin kiran ki ba komai bane
illa ina son na san ko ke
wacece, ba don komai ba sai
don mugun kama da kike yi da
ummi na, maganan ki, nd a lot
of things" cikin tashin hankali
ta dago fuskar ta, caraf suka
hada ido, dan dama ita din
yake kallo, sai da ta tattara
natsuwar ta, sannan ta fara
magana "ni kam ba kowa bace,
ba kuma komai bace, asali ma,
marainiya ce ni, ina zaune da
goggo na, wadda ta kasance
kanwar mahaifina, iyayena sun
rasu tun ina shekara 5 a
dunia" tana kai wa nan, taja
bakin ta tayi shiru. Shiru na
yan dakiku ya ratsa wurin,
sannan ya saki ajiyar zuciya,
yace "ehnn ina sauraren ki" ba
tare da ta kalle shi ba, tace
"shikenan ai" ya kura wa
kyakkaywar fuskar ta ido,
tabbas ya ga damuwa a tattare
da yarinyar, amma ya rasa
dalilin da yasa a lokaci daya
yaji ta shiga ran shi, ya rasa
dalilin da yasa yaji yana son ya
san wani abu dangane da
damuwar da ya gani bayyane a
saman fuskar ta. Ya dan gyara
zaman shi, sannan yace "a
matsayina na psychologist, na
karanci wani abu a tare da ke,
wanda baki son ki sanar dani"
ta dan firgita, sannan tace
"bakomai fa" ya shafi tarin
sumar da take saman kanshi,
sannan yace "alright then, zaki
iya tafia" bata kai ga mikewa
ba principal ya dawo office din,
a haka tayi musu sallama, tasa
kai ta fita ta bar office din.
Hally ta gani zaune a gefe ta
karasa kusa da ita, tace "muje
ko" ta mike suka jera,ta fara
tambayar "me ya faru ne
Deedo?" Ba tare da ta boye
mata komai ba, ta fada mata
abinda ya faru tsakanin ta da
wanda taji an kira da Dr.
NAWAP KHAMIS..
BA’A SHAN
ZUMA… 21, 22
& 23
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
A haka suka kawo layin su
Deedo, inda suka yi sallama
kowa ya kama gaban shi. Tana
shiga gidan da murnar ta,
sallama tayi, a lokacin goggo
tana kofar daki, ta dago ta
watsa mata wani kallo mai
tattare da tsana da tsangwama,
da sauri ta karasa gaban ta,
tana "sannu goggo" ta dago
fuskar ta a murtuke tace "uban
mi zanyi da sannunki? Shine
sai yanzu zaki dawo mun gidan
nan ko? Kina can kina yawon
naki na iskanci da kika saba"
tayi kasa da kanta, tace "kiyi
hakuri goggo, wlh a makaranta
ne aka tsaida mu" tayi kwafa,
sannan tace "uban miyye nan a
hannun ki?" Tace "kyautar da
aka bamu ce" goggo ta warce,
ta farka wrapping sheet din,
sannan ta fara fito da text
books da math set, da note
books da sabbin uniform gal,
da sauran tarkace dai na
students, ta kwashi uniform
din tare da text books ta watsa
mata, tace "wannan kadai zaki
samu shegiya, wannan sauran
kuma duk su shehu zan ba su"
ta tattara ta tura su bayan ta, ta
kara da cewar "wai ke nan a
wannan shegen kan naki har
wani kallon mai kokari suke
maki, tashi wuce ki bani wuri,
kin zura mun ido kamar na
mujiya, kuma ga kayana nan, ki
tattare su ki wanke tass" ta
kwashe yan kayan da ta bata,
ta shige daki, ita murna ma
take yi, dan bata yi zaton zata
samu wani abu daga cikin
kyautar da aka bata ba.
Dr. NAWAP KHAMIS, matashi
ne mai kimanin shekarun da
basu wuce 28 ba a dunia.
Dogo ne sosai dan har ya dan
rankwafa saboda tsabar
tsawon shi, yana da kirji mai
fadi wanda a kallo daya zaka
ga bayyanannun 6-packs din
shi. Yana da muscles a
damtsen hannun shi,
kasancewar shi masoyin gym
ne na bala'i, yana da doguwar
fuska wadda ke dauke da dara
daran idanu tare da dogon
hancin da ya dace da
kyawawan lips din shi. In fact,
Nawap namiji ne wanda ya
ansa sunan shi namiji, yayi
degree din shi na daya dana
biyu a jami'ar Bayero da ke
garin kano, inda daga bisani ya
wuce England inda ya hada
PhD din shi akan psychology.
Shine da na farko a wurin
mahaifiyar shi haj. Fatima
wadda yake kira da ummi,
mahaifin shi Alh. Khamis
shaharraren dan kasuwa ne a
garin kaduna, wanda Allah yai
mashi rasuwa shekara biyu da
suka gabata, kanwar shi kwaya
daya Hafsat wadda take aure a
garin Abuja. Yanzu haka yana
aiki da federal ministry of
education, wannan ne dalilin
da ya bashi damar zuwa
kauyen su Deedo, kasancewar
su masu inganta ilimin matasa
yan secondary skool.
BA'A
SHAN ZUMA… 2⃣2⃣
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tun ranan da Nawap ya bar
kauyen su Deedo bashi da abin
tunani wanda ya wuce ta,
babban tashin hankalin shi
shine damuwar da ya gani
shimfIda saman fuskar ta,
gashi ya rasa gane menene
ainahin dalilin damuwar ta a
matsayin ta na yarinyar da
duka duka bata wuce shekara
15 ba a dunia, idan zai iya
tunawa principal din su yace
suna 3rd term ne yanzu a ss2.
Babu abinda ke mashi yawo a
kan shi irin kalaman principal
na karshe da yace "Deedo ta
kasance yarinya hazika wadda
zan iya cewa babu kamar ta
kaf cikin makarantar nan, sai
dai kuma yarinya ce wadda
take bukatar taimako cikin
gaggawa!" Dam! Gaban shi ya
Kara bugawa, to wane irin
taimako ne take bukata? Shine
abinda bai tsaya ya samu
cikakken labari ba. Mikewa
yayi daga kan kujeran da yake
zaune, ya tattara laptop din
dake saman cinyan shi ya dora
kan center table, sannan ya
fara zagaya palon a hankali.
Tunani ya fara yi shin me yasa
ya damu da yarinyar bayan
kuma ya kan hadu da cases
sosai irin nata a yawancin
makarantun da suke zuwa, a
fili ya furta "nata is different! I
saw the sorrow in ha, she's
desperately in need of my
help!" Ya sa hannu ya ciro
wayan shi da ke ta faman
ringing cikin aljihu, ya zaro
wayan ya kaima screen din
kallo, lokaci daya yayi wurgi da
ita saman kujera har ta katse
bai daga ba. Aka sake kiran
wayan, a karo na biyu shima
kaman ba zai dauka ba, can
dai ya daga cikin muryar nan
tashi mai kwantar da hankali,
yace "Aysha ya akayi ne?" Ba
tare da mun jiyo ansar da aka
bashi ba, yace "I'm kinda busy
yanzu gaskia, May be I'll call
back later" bai jira ansar ta ba
ya katse wayar yaja tsaki, tare
da komawa kan kujeran ya
lumshe idon shi, Deedo ya
gani cikin kodaddun uniform
dinta, fuskar nan ta ta cikin
yanayi na damuwa da bukatar
tallafin gaggawa, firgit ya bude
idon, amma bai ganta ba,
hakan ya sa ya cika bakin shi
da iska sannan ya fitar, yace
"I'll come 4 yu Deedo nd I
promise I'll help yu" ya mike ya
shige bathroom ya sakan ma
kanshi shower…
Katon bahon ruwan ta, ta
doro a kai tana ta bunguza
sauri kasancewar maghriba ta
gabato, kayan jikin ta duk sun
jike sai rawar sanyi take yi,
kafar nan ta ta firi firi kaman
tayi birgima cikin kasa, shehu
ne tare da wasu yara suke
binta a baya suna mata daria,
bata ko damu da su ba, dan ta
san idan ta tsaya yau kashin ta
ya bushe wurin goggo. Hango
shi tayi rungume da hannayen
shi, ya zuba mata idanu kamar
mai nazarin wani abu a tattare
da ita. Kanshin turaren shi da
ta shako daga inda take shi ya
tabbatar mata da abin da take
tunani! Cikin jin kunyar yanayin
da take ciki tazo, ta raba ta
gefen shi zata wuce ba tare da
ta sake kallon inda yake ba,
bai tanka mata ba, ta shige
cikin gidan da saurin ta dan
har an kwalla kiran sallah.
Shehu ne ya shigo da sauri
yana kwala wa goggo kira, ta
fito daga daki zanin ta a
hannu, tace "Shehu na Allah,
yau kuma da waccen ka
shigo?" Yace "wani mai mota
ne wai a kira mai Deedo" ta
zaro ido tace "mai mota da
neman Deedo? Kai shehu ko
dai dijangala yace?" Yace "wlh
Deedo yace, har ma yace wai
wadda ta shigo yanzu" goggo
ta rafka salati tace "na shiga
ukku, ubanwa kuma kika jawo?
Wlh in masifa ce yau a kanki
zata kare, dan ni dai ina zaman
zama na baki isa ki jawo mun
bala'i ba" ta dafe kanta tace
"oh ni Batula! Wannan
tsintacciyar mage na neman
jefa ni cikin masifun ta" ta
damko kunnen ta, ta wurga ta,
tace "wuce kije ki san yadda
zakiyi da bala'in da kika
tattago, idan ma tafiya zasuyi
dake wlh ko kofar zaure bazan
je ba, tunda ban san sadda
kika je yawon iskancin ki ba
har kika jawo bala'in" Deedo
tasa kara, tace "wlh goggo
banje wani yawon iskanci ba,
wlh ban ja kowa ba" goggo ta
hankada ta, tace "ki wuce ki
fita wlh jar ki ja tsinannun su
shigo mun cikin gida, dan wlh
duk wanda ya shigo sai na
fasa mai kai da tabarya" Deedo
ta share yan hawayen ta, taja
lamusassun silifas dinta da
suka ji wahalar dunia ta bi
hanyar zauren zata fita, shehu
kuma ya sa ihu yace "bari muje
muga irin dukan da za a
nakadawa shegiya, dama su
tafi da ita mu huta" goggo tace
"ka tsaya daga bakin zaure dai,
dan kar su hada mun da dakai"
bai bi ta kanta ba ya juya da
gudu ya fita kofar gidan.
BA’A SHAN
ZUMA… 24, 25
& 26
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Koda ta fita baya kofar gidan,
sai dai motan shi kawai, har ta
juya zata koma ciki ta jiyo ana
kwala mata kira, waigowa tayi,
ta hango shi yana tahowa, da
alama daga masallaci ya fito.
Da sallama ya iso, ita kuma
tana tsaye tana matse kwallan
da suka taran mata, kallon ta
yake cike da tausayin rawar
sanyin da take yi, gata dai
yarinya karama amma alamun
damuwar da take tattare dasu
sun bayyana karara akan
fuskar ta, ba tare da yace
komai ba. Dukawa tayi har
kasa sannan tace "ina wuni" ya
ansa a taqaice, sannan yace
"kin gane ni kuwa?" Ta daga
kai alaman eh, ya gyara
tsayuwar shi, sannan yace "na
tambaye ki labarin ki, amma
baki fada mun komai, a yanzu
kam, ba sai kince dani komai
ba, domin yanayi da kike ciki
ya sanar dani irin matsalar da
kike fuskan ta a gidan nan" ta
dago jajayen idanun ta da suka
rine da kuka, tace "ni bana tare
da matsalan komai" kallon ta
yake yana nazarin yadda tayi
maganar, murmushi yayi, ya
juyar da kanshi ya ce "well,
tunda baza ki fada mun
matsalar ki ba, bara na shiga
gidan sai inji dalilin da yasa
kike daukan wannan katon
bahon na ruwa a kanki, a
matsayin ki na yarinya mai
karancin shekaru" ya sa kanshi
alamar zai shiga zauren, shehu
na ganin ya nufo inda yake ya
tashi ya runtuma da gudu cikin
gidan, itama tayi sauri tasha
gaban shi tace "kayi mun rai
dan Allah, ba dan ni ba, yau
muddin kaje ma goggo da
maganar nan wlh sai ta kusan
kashe ni" murmusawa yayi,
sannan yace "zaki fada man ko
ke wacece ko kuwa?" Ta
girgiza kanta, "zan fada maka"
ya ja da baya ya jingine jikin
kofan zauren, yace "ina
sauraren ki" ba tare da bata
lokaci ba Deedo ta warware
mashi komai, ta fada mashi
duk halin da take ciki a gidan
goggo, hatta da mutuwar mal.
Ilu bata boye ma Nawap ba, ji
yayi kafafun shi na neman
kasa daukar shi, bai taba
tunanin mutane marassa imani
irin goggo suna rayuwa ba har
yanzu a doron kasa, ya zata
irin su sun gama karewa tun
zamanin jahiliyya. Tausayin
yarinyar ya kara shigar shi, ga
wani irin kuka da take yi marar
sauti, kallon ta yake a matsayin
tilon kanwar shi Hafsat, har
yana imagining idan ita ce
wane irin mataki zai dauka.
Kallon ta yayi, yace "kukan nan
ya isa, ki shiga gida kinji, zan
karasa cikin bauchi na kwana,
zuwa gobe zan dawo in sha
Allah" ta mike jiki ba kwari ta
shige ciki, shi kuma ya shiga
motan shi yai mata key ya
kama gaban shi.
Tana shiga ta tarar goggo da
Hadiza da shehu sun jera sun
zuba ma kofar ido suna jiran
suga mei zai faru, damko ta
goggo tayi tace "uban wanene
wancan?" Deedo tasa kara tace
"wani ne" goggo tace "wani
wa?" Ta fara kame kame dan
bata san ya za tai ma goggo
bayani ba, ta daka mata tsawa
tace "baza ki fada ba?" Tace
"daga makarantan mu ne"
goggo tace "naga alamar yau
yan iskan ne a kanki, yanzu
zanyi maganin ki idan baza kiyi
magana ba" cikin tsoro da
fargaba ta fada ma goggo
yadda ta san Nawap, ta kara da
cewar "yazo garin ne shine ya
biyo ta nan" goggo ta sa salati,
tace "ke Deedo ki fita a ido na
wlh, yanzu ke yawon iskancin
naki ya kai har da yan birni
kike yi? Yau zaki gaya wa yan
garin ku" ta damki yarinyar nan
ta fara bugu, Hadiza ma ta
mike ta debo ruwa a randa ta
watsa mata, suka ci gaba da
jibgar ta, shehu kam sai tsalleh
yake yana jin dadi, dan duk
dunia ba abinda ya ke so irin
yaga goggo na kwalfar Deedo,
saida sukai mata liiis,sannan
suka shige daki suka barta a
wurin. Dakyar ta lallaba ta
shige dan akurkin dakin ta,
kuka take yi sosai, ita kanta
tausayin kanta take yi, wannan
azaba ta ishe ta, neman hanyar
da zata kubutar da kanta kawai
take yi, ta lallaba tayi alwala
tazo ta fara sallah ta gama, ta
jawo littafin ta Geography
tasha karatu sosai, abinka da
mai sharp brain, dandanan ta
kwashe komai da take bukata,
ga yunwa ta addabe ta, ga
kuma wani mugun bacci da
yake figan ta, nan inda take ta
dan shingida, kafin kace wani
abu tuni bacci yayi gaba da ita,
abin ka da ansha bauta da
rana an gaji.
Yau Allah ya taimaka ta kiran
sallar farko a kan kunnen ta
dan haka tayi zumbur ta mike,
tashin ta keda wuya, goggo ta
shigo da robar ruwan ta, tana
haska fitila ta ganta a tsaye,
tace "la'ananniya, da kar ki
tashi mana" tayi kwafa tace,
"kin wuce kin wanke kayan
fitsarin can na shehu ko sai
nasa kafa na hanbare ki?" Sum
sum Deedo ta fito tana rawar
sanyi, kayan fitsarin ta kwashe
ta wanke, sannan ta doro
alwala tazo ta gabatar da sallar
asuba, sannan ta dauki bahon
nan, ta wuce borehole.
Bayan ta dawo tayi duk wani
aiki da tasan nata ne, ta gama
ta jawo uniform dinta, ta saka
sannan ta fito ta karasa kofar
dakin goggo. Ita daya ce zaune
a bakin gado, dan su Hadiza
sun dade da tafia makaranta.
Tace "goggo zan tafi" ta watsa
mata harara tace "na rike miki
kafa ne? Ko wata tsiyar zan
miki ne? Eyee?" Ta girgiza
kanta, sannan ta mike ta fito
daga dakin ta nufi makarantar.
Tana isa har an fara exam,
malamin ya kalle ta kaman
wadda aka koro, yace "Firdausi
Kabeer" dam taji gaban ta ya
fadi, ta tsaya cak a inda take,
yace "mei sa tunda aka fara
exam kullun sai kinzo late?" Ta
rasa abin cewa, sai can ta tuna
da goggo ta fasa mata baki
jiya wurin dukan ta har ma ya
kunbura, tayi saurin cewa "I'm
sorry sir, na taho ne na fadi a
hanya saida na tsaya chemist
na ansa magani" ya kare mata
kallo, tabbas ga alama nan a
tattare da ita, dan haka ya bata
question paper yace ta wuce ta
zauna, ta ansa da sauri ta
wuce seat dinta ta zauna.
Nawap kasa bacci yayi a daren
jiya, yana tunanin ta ena zai
biyo ma mace mai mugun hali
da rashin imani irin goggo; shi
dai yayi alkawarin taimakon
yarinyar nan no matter what;
amma ya rasa ta wane hanya
zai bi dan ya kubutar da ita
daga hannun azzalumar matar
nan. Tunani ya fara yi ko court
zai mika ta, sai kuma wata
zuciyar tace "a matsayin ka na
wa? In kaje gaban alkali kace
me?" Yaja tsaki, ya watsar da
wannan tunanin can kuma
wata dabarar ta fado mashi,
murmushi ya saki wanda ya
kara mashi kwarjini, da sauri
ya canja akalar motar shi yabi
wani titi, ba tare da yasan ko
ina cikin garin Bauchi ba, haka
ya bi main road na cikin garin,
nan ya samu wani katon mall,
ya karasa yayi parking ya fito
ya shige ciki. Duk wani abu da
dan adam zai bukata akwai shi,
haka ya zage yayi kyakkyawan
shopping na dangin kayan
abinci masu uban yawa,
tarkacen man shafawa,
sabulun wanka dana wanki, ya
koma bangaren kayan sawa
nan ma ya kwasa son ran shi,
har da kayan yara maza ya
kwaso, akai mashi total kudi
wurin 150, 000, credit card din
shi ya ciro ya basu suka cire,
sannan aka kwashi kayan aka
sa mashi a pickup ta shopping
mall din, dan motar shi baza ta
iya daukar lodin ba, ya shiga
yana gaba masu motan na bin
shi har cikin garin Ningi.
A kofar gidan Hajia goggo
suka tsaya, ya kira wasu
almajirai suka taimaka ma
masu motan suka shiga da
kayan ciki. Goggo dake kofar
daki tana sakacen hakori taga
mutane da kaya niki niki, ta yi
zumbur ta mike tace "kai
malam daga ina wannan
kayan?" Wani cikin su yace
"wani ne yace mu shigo dasu
yana nan waje" tana tambayar
wanene amma bai bi ta kanta
ba, suka juya suka fita. Saida
aka gama shigo da kayan tsab,
sannan Nawap ya shigo ya
tsaya bakin zaure yayi sallama,
goggo data kagara taga wanda
ya kawo wannan kantin guda
(inji ta tace wannan ai kanti ne
guda ya kwaso) tayi saurin
cewa "shigo mana" ganin
tsayayyen namiji, jarumi,
matashi, dan boko, wanda ya ji
hutu, ya kuma ji bugun A.C,
mai asalin zati da kwar jini!
Yasa goggo tayi saurin ja da
baya kamar wadda tayi karya,
ta samu gefe ta rakube, bakin
ta na rawa tace "yaro daga
ena?" Yanayin da goggo ta
shiga ya bala'in bama Nawap
daria; haka dai ya gintse, yace
"bari mu gaisa mana goggo
ta"..
BA’A SHAN
ZUMA… 27, 28
& 29
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Goggo tana zara idanu ta mike
da sauri ta dauko sabuwar
tabarma daga daki ta shimfida
mashi, ya zauna, ya gaishe da
ita cikin ladabi, ta ansa bakin
ta na kyarma, tace "ni fa har
yanzu ban dau haske ba, daga
ina kazo ne samari?" Ya saki
lallausan murmushi, sannan
yace "Sunana Nawap, dan
asalin garin kaduna ne ni,
yanayin aiki na ne ya kawo ni
Bauchi state, daga nan kuma
aka turo ni wannan gari" goggo
tace "Ayyya, to wannan tulin
kayan fa na menene?" Ya kara
murmusawa, yace "naki ne Haj.
Goggo" goggo ta zaro ido ta
dafe kirji, tace "wannan uban
kaya haka? To wai kai a ena ka
sanni ma?" Nawap cikin
zuciyar shi daria kawai yake,
ya san hakon shi ya kusan
cimma ruwa kasancewar
yanayin da goggo ta shiga, ya
san dama baza ta rasa son
abin dunia ba. Yace "ina zaune
da mahaifiya ta, ina kuma da
kanwa kwaya daya, amma tayi
aure, to mu kan samu masu
aiki da dama, sai dai da yawan
su basu zama sai su gudu,
saboda aikin gidan yana da
yawa. To jiya sai naga wata
yarinya da katon baho na ruwa
ta shigo gidan nan, hakan ya
tabbatar mun da zata iya ko
wane irin aikin wahala, shi
yasa nace bara nazo naji ta
bakin ki, ko zaki taimaka ki
bani ita? Ke kuma ina turo miki
da kudin aikin nata a ko wane
karshen wata" goggo ta gyara
zaman dankwalin ta, tace "ba
dai wannan tambadaddiyar
yarinyar kake nufi ba?" Yace
"wa kenan?" Tace "Deedo
mana, tsintacciyar mage,
shegia mai mugun hali" har
cikin zuciyan Nawap baya jin
dadin zagin da goggo take ma
marainiyar yarinyar nan, haka
dai ya daure yace "ina ga ita
din ce, ban dai san sunan ta
ba" goggo ta dan matso da
kanta dab dashi, kamar wani
zaiji abinda zata ce, a hankali
tace "nawa zaka na biya na duk
wata idan na baka ita?" A
takaice, yace "naira dubu
hamsin" dan tsabar tsorata har
sai da goggo ta hantsila baya
daga kan yar kujerar tsugunnin
da take kai, tace "dubu
hansin?" Ya gintse dariyar shi
yace "ko sunyi kadan ne
goggo?" Tace "haba ina fa, ai
ban taba kama ko rabin su ba,
bari tsinanniyar tazo, ko zata
mutu sai ta bika, kuma ko
wahala zata kashe ta, kar ta
sake ta dawo mun gidan nan,
kai ni in ka tafi da ita ma ko
ganin gida kar ta sake tazo"
Nawap kallon ikon Allah kawai
yake, tare da tsantsarar rashin
imani na matar nan, ya
muskuta, yace "ena yarinyar
take ne?" Tace "ta tafi
makaranta, ai tana dawowa ba
abinda za a jira wucewa kawai
zakuyi, daman ba wata kwalwar
fahimtar karatun ne da ita ba,
haka nan dai take zuwa
makarantar" Nawap yace "bari
dai muji ta bakin ta ko goggo"
goggo tace "in dai ta bakin
wannan shegiyar zamu tsaya ji
ai ba yarda zata yi ta bika ba,
dan haka kawai ba sai an mata
wani bayani ba" Nawap wani
irin kallo mai tattare da tsana
yake watsa ma goggo, yanzu
shi inda ace ba manufar alkairi
gare shi akan yarinyar ba, da
haka zata dauke ta ta bashi, ba
tare da tunanin shi din ko
wanene ba. A zuciyar shi yayi
Allah wadaran hali irin na
wannan matar, ya kuma yi mata
addu'ar Allah ya sa ta
dandanin kuncin rayuwa koda
rabin wanda Deedo ta dandana
ne.
Sai da ya tattaro natsuwar shi,
sannan ya saki murmushin
yake, yace "to shikenan goggo,
bara na dan zaga cikin gari zan
dawo zuwa anjima" yasa hannu
a aljihu ya ciro bandir na yan
500 ya mika mata, goggo
hannu na bari, tayi saurin
warcewa, sai da ta adana su
cikin zanin ta, sannan tace
"bayan wannan kantin guda
daka kwaso, abin kuma har da
wahala" yana tsaye yana kallon
karfin hali da munafurci irin na
goggo, ya girgiza kanshi, yayi
murmushi, yace "wannan ai
kadan ne goggo, kar ki damu"
ta wangale bakin ta, tace "to
shikenan Nawab, sai ka dawo
din" yadda ta kira sunan nashi
yasa ya kasa gintse dariyar
shi, dan haka ya dan dara,
sannan ya wuce ya fita.
Yana fita skool din su Deedo
ya zarce, direct office din
principal ya nufa, bayan sun
gaisa yake tambayar "Dr. Kaine
a garin namu" Nawap ya shafi
kyakkyawan sajen shi da ya
kwanta luf saman fuskar shi,
yace "wlh fa, ya students?"
Yace "Lafia fa" nan suka cigaba
da fira, inda yawancin firan
nasu duk akan tabarbarewar
ilimin yaran karkara ne, nan ya
samu labarin su Deedo suna
zana waec ne, wadda zasu
gama sati mai zuwa, sannan
kuma su fara neco. A haka yai
ma principal din sallama,
sannan ya fito.
A kofar gidan goggo ya tarar
da Deedo tare da hally, tana
mika mata magani da ta ciro
daga jakar ta, tace "wlh Deedo
ki natsu, yanzu kinyi girman da
za ace kin wuce duka, har ana
kumbura miki baki, wlh idan
nice ke tuni zan ture goggon
gefe, sai dai ko mai zai faru ya
faru" Deedo ta murmusa tace
"hally ke dai ki gode ma Allah
da yasa iyayen ki suna raye,
amma baki san menene
maraici ba, ni ina naga karfin
halin da zan iya taba koda
yatsan goggo ballantana kuma
in samu halin ture ta, ke dai ki
taya ni da addu'a kawai har
Allah ya kawo karshen zamana
a gidan nan" hally tace "Allah
ya taimaka, bara na wuce" suka
juyo a tare, nan suka ga Nawap
jingine jikin mota, fuskan ba
yabo ba fallasa, duk suka duka
suka gaishe shi, sannan suka
yi gaba ta dan taka ma hally,
nan take fada mata yadda suka
yi jiya, hally tace "Allah yasa ya
zamo silar fitar ki daga kangin
da kike ciki" Deedo tace
"kaman ya? Ke ni ko ganin shi
bana son yi wlh" hally tace "Ke
dai yanzu je kiji da wacce yazo
tukunna" sukai sallama ta wuce
ita kuma ta dawo, amma bata
ganshi ba dan haka tayi saurin
shigewa cikin gidan, nan ta jiyo
muryar goggo tana cewa "kaga
gantalalliyar yarinyar nan har
yanzu bata iso ba" jiki ba kwari
tayi sallama cikin gidan ta
shiga, ganin shi tayi zaune
saman tabarma, dan da nan ta
shiga tashin hankali, tasan yau
karyar ta ta kare, Allah ne
kawai zai raba ta da goggo da
bala'in ta..
Dakyar ta karaso cikin gidan, a
dai dai lokacin kuma goggo ta
fito daga daki inda suke shiga
da kayan da Nawap ya kawo
masu. Harara ta watsa mata,
sannan tace "ke dai Allah
wadaran hali irin naki, shegiyar
'ya gantalalliya, ina kika je kika
zauna kuma" ta karaso gaban
ta, ta duka tace "kiyi hakuri
goggo wlh ban tsaya ko ina ba"
tasa kafa ta wurgar da ita, tace
"daga yau dai gantalin ki ya
kare, naga gidan uban da zaki
kara yawon iskancin ki, dubi
nan" ta nuna mata Nawap da
yake zaune yana kallon goggo,
Deedo ta dago ta kalle shi,
sannan goggo taci gaba "to da
shi zaku tafi, zaki je can kina
masu aikatau, sauran kuma inji
abinda ba shikenan ba, wlh na
lahira sai ya fiki jin dadi" wani
irin kuka ta saki, duk wanda ya
kalle ta sai ya tausaya mata,
kafar goggo ta rike tana "kiyi
mun rai goggo, ki taimaki
rayuwa ta dan Allah, wlh ban
san shi ba, bazan bi shi ba,
kila ma dan yankan kai ne, wlh
zan yi miki ko mai kike so,
amma kiyi mun rai kada ki
kaini wurin yan yankan kai"
saida goggo ta tattaro karfin ta
gaba daya, sannan ta wancakar
da Deedo, har saida ta bige da
dogon karfe na baranda,
sannan tace "kinsan Allah ko
gawar ki ce sai bawan Allahn
nan ya tafi da ita, kinji dai na
rantse, baki isa ki sani kaffara
ba kuma" tayi hanyar dakin
Deedo da niyyar watso mata
tsummokaran ta, Nawap dake
gefe yana kallon abinda ke
faruwa, cikin kunan zuciya
wanda bai bari goggo ta gane
ba, yace "ehnmm goggo" tayi
saurin dawowa ta duka gaban
shi tace "ya akayi ne Nawabu?"
Saida yaja dogon numfashi,
sannan ya tuna principal din
su Deedo ya fada mashi suna
exams, sannan ya tuno da
ummin shi, at least ya kamata
ya sanar da ita kafin ya kai
mata Deedo, wata dabara ta
fado mashi, ya dan gyara
zama, sannan yace "naga
alamar yarinyar nan tana da
yan matsaloli, ga kuma yanayin
jikin ta ba wani gyaran kirki,
dan haka ina son a aje mun ita
a nan zuwa nan da kamar wata
guda, amma ina so duk wata
wahala da take yi a da ta daina
yin ta, ba don komai ba sai
don idan na kaita can ta samu
karfin yin aiyukan da muke
dasu, irin dibar ruwan nan da
sauran su, in yaso ko kofar
gida kada a rinka barin ta tana
fita, makaranta kawai na
amince taje, wannan shima
wani aiki ne, wanda zan biya
kudin shi yanzu yanzun nan"
goggo da taji maganar kudi,
tayi sauri tace "to ai shikenan
tunda dai kai ka bukaci hakan,
amma dai naso ka tafi da ita
yau din" yace "bakomai, zan
dawo nan da wata 1" yasa
hannun shi aljihu ya kara
kwaso wasu kudin ya mika wa
goggo, sannan ya mike yayi
hanyar zaure, sai da ya kare
ma Deedo kallo tsab, sannan
ya sa kai ya wuce abin shi.
Shehu ne ya rugo daga daki da
sabbin kaya jikin shi, sai da
yasa kafa ya hanbari Deedo
sannan yabi Nawap har kofar
gida yana cewa "Allah ya
kiyaye hanya" Nawap wanda
yake jin haushin su shi da
uwar su, ko kallon shi bai ba,
ya shige motar shi ya tada.
BA’A SHAN
ZUMA… 30, 31&
32
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Acikin Gida kuwa goggo takalli
deedo sannan tace "kinji
abunda yace!, tsintacciyar
mage wacce bata gaji arziki ba,
albarkacinki daya karna miki
dukan tsiya kisamu illa yafasa
daukanki, donhaka kije kina
hutawa," takamo kunnenta
sannan tace "saura kuma da
gigin wasa kice bazakijeba,
kokuma inkinje su koroki, wlh
saina hallakaki" deedo dai
shiru tayi, tana ganin goggo ta
shige daki, itama ta mike ta
shige akurkin ta, ta cire
uniform dinta sannan ta fito
tayi alwala ta koma ciki.
Zuwan nawap gidan goggo ba
karamin alkhairi bane yajawo a
rayuwar kuncin da Deedo take
ciki, domin kuwa tadenaa
aiki,harta kai ko tsintsiya ta
dauka, goggo ta fara zagin ta
tana cewa zata janyo musu
asaran arziki, hakan yabata
daman yin karatu, hatta a
makaranta sukansu sun lura da
zuwa dawuri datakeyi, hally har
zolayen ta takeyi, tana cewa "
Allah ya yi abin, inji mafadin
aure. kekuma aidole kidawo
shalele, kudi saan kowa,
mutuncin kowa, mu dai muna
godewa Allah daya taimakemu
yakawo karshen wahala duk da
bauta zakijeyi" itadai Deedo ta
kan rasa abin cewa, duk da
tana son ta rabu da azabar
goggo, amma kuma bata son
bin mutumen da bata san daga
ina yake ba.
* **Nawap kuwa koda ya fito
gidan goggo, gudu ya rinka yi
sosai, har ya isa garin kaduna.
Ta Alkali road ya bi, sannan ya
shiga cikin Isah Kaita road,
gida mai No. 55 ya danna horn
mai gadin cikin uniform ya
rugo da gudu ya bude mashi,
bai jira komai ba ya kunna kan
motar ciki. Parking yayi ya
shiga gidan a gajiye, saida yayi
wanka yayi sallah sannan
yafito. Mahaifiyar tasa na
zaune a falo yazauna yana
sosa kai, kallon shi tayi, ta dan
yi murmushi sannan tace
"meya faru?" Ya dan gyara
zama, ya dukarda kanshi kasa
yace "Wlh ummi wata nasamu
a wani kauye da aka taba kaini
aiki, taban tausauyi sosai,
yarinyar tana cikin wani hali,
inason nataimaka mata, don
Allah inason kawota nan, ko
aiki tana dan tabawa" ummi
tayi murmushi ganin cewan
halin nan nashi na taimakon
mutane da tausayi, bai canja
ba, tace "bakomi, ai shi da' ai
na kowa ne, kakawota mana"
yasan daman ba zai taba
samun matsala da ummin shi
ba, kasancewar ita ta dora shi
akan wannan kyakkaywar
tarbiyya ta tausayi da jin kai.
Dan haka cikin farin ciki ya
wuce dinning ya ci abincin shi
yayi kat, sannan ya koma side
din shi dan ya dan huta..
BAYAN GAMA WAEC ND
NECO….. Ranana da Deedo
tagama exams dayamma tana
zaune, wani murna takeyi
tamkar zata shiga aljanna, ta
godewa Allah sannan tanemi
albarkan karatun agunsa,
sallama taji saiga shehu ya
rugo da gudu yana kiran
goggo, da sauri tafito tana
cewa "mei kuma ka samo mana
yau?" Ya wangale baki yana
cewa "Goggo nawabu ne yazo"
Idonta ta zaro sannan tace
"yana ina?" Yace"yana waje," da
gudu gudu goggo ta koma
tacanja zanin jikinta, ta jawo
wani sabon mayafi ta buga
sannan ta fito, yara ta gani
sunata shigowa da carton
carton da buhhuna da manyan
ledoji, ta washe baki tana cewa
"Nawabu sarkin kokari, baya
gajiya da hidima, ku aje nan"
tace da yaran, sannan dasauri
goggo ta shige daki taciro wata
atamfa sabuwa kal, dakin
Deedo ta shiga tabata tare da
cewa "ungo wannan, yi sauri
kisa, yaganki fes fes abunki,
kozamu samu da tsoka" ita dai
ansa kawai tayi tasa ba tare da
ta fahimci abinda goggo ke
nufi ba. Da sallama ya shigo
cikin gidan, goggo na jin shi
tayi saurin fita suka gaysa, sai
a sannan Deedo ta fahimci
abinda ke faruwa, Dam taji
gaban ta ya fadi lokacin data
jiyo shi yana cewa yazo tafiya
da ita ne. Goggota gyara
zaman mayafin ta, tace "Ah
itakam dasauki ai, kaga kuma
yau tagama jarabawa sai farin
ciki take" bai ce komai ba, dan
bai yadda da goggo ba, burin
shi dai yaga Deedo sannan ya
tabbatar da abinda take fada,
jin da tayi yayi shiru yasa ta
kwala mata kira, Deedo ta fito
jiki ba kwari, fuskan ta ba yabo
ba fallasa, gashi kuma ta dan
yi kumari, ga wani dan haske
da tayi abin ta. Juyawa yayi ya
kalla goggo, sannan yace "ai
babu wata matsala ko?" Goggo
ta wangale baki, tace "babu
komai Nawabu, tafiya kawai ya
rage muku" yasa hannun shi
aljihu ya fito da kudi masu
yawa ya mika mata, sannan ya
mike tsaye yace "idan ta gama
ta same ni a mota" yasa kai ya
fice kofar gidan
Goggo na ganin fitar shi, ta
kwashe kudin da ya bata, ta
kama bakin zanin ta ta daure
su tam, sannan ta juyo inda
Deedo take tsugunne bata da
niyyar tashi. Kunnen ta ta
damka, tayi daki da ita, tace
"kinsan Allah, idan kika yi
abinda mutumen nan yasa
yace ya fasa tafiya dake, sai
dai uwar ki ta dawo daga lahira
ta haifa wata, dan wlh sai na
hallaka ki, shegia wadda bata
gaji arziki ba" ta wurga ta, ta
ce "maza hada inaki inaki ki
wuce ku tafi, kuma ko da ganin
gida kar ki sake ki dawo mun
nan" Deedo ta dan matse
kwalla, ta shiga tattara yan
kayan ta, ta daure a dankwali,
ta matse a hammata, sannan ta
fito. Shehu da goggo suna
kofan dakin suna jiran ta,
Hadiza kuwa tunda Nawap ya
fita ta bi bayan shi tana
karairaya wai ita dole don ya
ganta ya kyasa, wanda shi bai
ma taba tunanin Allah yayi
halittan ta ba a wurin. Shehu
ya buga ihu yace "yau zamu
yar da dajar mangwaro mu
huta da kuda" goggo tace "kai
dai bari mana kar ya jiyo ka"
haka suka tasa keyar Deedo
gaba suna binta a baya, shehu
har dan jawo mata kullin kayan
ta yake yana cewa "tsintacciyar
mage bata mage" sai ya
kyalkyale da daria, a haka har
suka iso gaban motar. Deedo
ta bude gidan baya ta shiga,
goggo kuma ta koma ta side
din Nawap tana cewa "Allah ya
tsare Nawabu, sai na ji sako
na" wani kallo mai tattare da
tsana ya watsa mata, sannan a
zuciyan shi yace "zaki ga sako
ganin idon ki" a fili kuma ya
dan daga mata kai, alaman sai
ta ji shi din, sannan yai ma
motar key suka dau hanya.
Suna fitowa layin gidan goggo,
Deedo dake matse yan kwalla
daga bayan mota, tace "dan
Allah ina son in yima hally
sallama" ba tare da ya kalle ta
ba yace "ina me gidan?"
Kwanar ta gwada mashi ya
shiga, suka so har kofar gidan,
sannan ta fita ta shige gidan
su hally. Ta gaishe da maman
su, sannan ta wuce dakin hally,
ta same ta zaune ta gama
sallan la'asar, ta zauna a gefen
gado tace "nazo yi maki
sallama ne, yanzu zan tafi"
hally ta mike suka rungume
juna suna dan kuka, a haka
suka fito har bakin motan,
suka yi sallama, tare da
alkawarin baza su taba manta
juna ba har abada. Tana shiga
ko, ya ja motan sai garin
kaduna..
BA’A SHAN
ZUMA… 33, 34
& 35
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Gudu ya cigaba da yi, babu
wanda ya ke ma wani magana,
Deedo dai adduo'in matafiya
take ta faman nanatawa cikin
zuciyar ta. Shirun ya ji yayi
yawa dan haka ya danna
Suratul Room cikin qira'ar
Sheikh Ahmad Sulaiman, ita
kuma ta tattara hankalin ta baki
daya, banda kallon titi ba
abinda take yi, dan yau ne rana
ta farko data fara barin kauyen
Ningi. A sannu a hankali har
suka shigo garin kaduna,
Deedo idon ta kyar, ko alamar
bacci babu, gashi lokacin
kusan karfe 8 na dare, idanuwa
ta baje ta fara kallon street
light da yawan hold up, da
kyawawan motocin da suke ta
rafsa uban gudu a manyan
titinan garin. Wani dadi taji ya
ratsa mata zuciya, a hankali
kuma ta fara samun natsuwa,
dan tunda suka taho hankalin
ta a tashe yake, hamdala ta
yima Allah, sannan cikin
zuciyar ta tace "ko bakomai
ganin wannan kyawawan
abubuwan ma wani abu ne a
rayuwa" daga karshe tayi
addu'ar Allah ya sada ta da
dangin mahaifiyar ta, tunda dai
ta san a garin nan suke. A
haka taga sun shigo wata
hadaddiyar unguwa wadda
babu kowa sai kukan karnuka
da yan tsiraran motoci da suke
wucewa jefi jefi. A bakin wani
makeken gida taga yayi horn,
mai gadin ya fito da sauri ya
bude tafkeken gate din, Nawap
kuma ya tura kan motar shi
hankali kwance. Ido ta cigaba
da zarawa tana kallon flowers
din da suka kayatar da
tsararren ginin gidan. Wuri ya
samu kusa da wasu jerin
motoci ya parka, sannan yace
mata ta fito suje ciki. Haka ta
fito tana ta kalle kalle, yana
gaba tana bin shi a baya, har
suka iso kofar palon, ya tura
kanshi da sallamar shi, babu
kowa sai karan T.V an kunno
tashar BBC WORLD. Deedo ma
bata yi kasa a gwiwa ba ta
biyo shi a baya ta shigo,
sanyin A.C ne ya dake ta,
sannan ta taka wani lafiyayyen
carpet mai asalin taushi, gefe
guda ta samu ta rakube ta
zuba ma screen din tafkekiyar
LED plasma idanuwan ta, yayin
da shi kuma ya haura sama, ba
tare da ta san abinda zai yi
ba…
* **Wata kyakkawar dattijuwa
mai cikar kamala da kwarjini, ta
gani tana saukowa a hankali
daga stairs din yayin da shi
kuma yake biye da ita a baya.
Ido Deedo ta tsura masu, ganin
asalin kamar da suke ne ya
tabbatar mata da cewa matar
jinin shi ce. A tare suka zauna
a kujerun da suka yima palon
ado, sannan matar ta gyara
muryar ta, tace "ta so ki dawo
nan mana yan mata" a hankali
deedo ta mike, tana matse da
dan kullin ta kamar wani zai
kwace mata ta karasa tsakiyar
palon ta zauna kasan carpet, ta
dago domin ta gaishe da matar
sai taga ashe tun da ta taso
idon matar a kanta yake! Nuna
ta matar ta fara yi da hannun
ta, kamar zata ce wani abu, sai
kuma ta fasa tace "ki saki jikin
ki, kinji" ta dukar da kanta, ta
gaishe ta, ita kuma ta ansa
cikin fara'a da jin dadi, sannan
kuma a hankali ta fara
tambayar ta labarin ta, dana
garin su da labarin karatun ta,
da duk wani abu da ya shafi
rayuwar ta. Hankali kwance
Deedo ta rattaba mata tarihin
ta, dana goggon ta, da irin
rayuwar kaskancin da ta yi a
kauyen Ningi! Dam gaban
ummi ya fadi, mikewa tayi ta
karasa gaban Deedo ta mikar
da ita tsaye, kallon ta take
kamar ta samu T.V daga bisani
kuma ta rungume ta, wasu
kwalla masu zafi suka gangaro
mata, Deedo da bata fahimci
komai ba, ta fara zara idanu,
Nawap ma da yake gefe a
zaune mikewa yayi, yazo gaban
su yana cewa "ummi lafia?"
Kuka sosai ummi ke yi, tace
"Nawap ita ce wlh, yarinyar da
nake kwana da tunanin ta nake
tashi da shi a ko wace rana"
tasa hannu ta kara rungume
Deedo, tace "Firdausi dama
kina raye? Ashe da rabon zamu
gana dake" Nawap yace "ummi
ban fahimce ki ba fa" sakin
Deedo ta yi, sannan ta kamo
hannun ta suka zauna a kan 3
seater, ta juya tana facing
Nawap, tace "ita ce yarinyar da
kanwa ta Rukayya ta rasu ta
bari, wadda har naje dauko ta
amma goggon ta ta hana, ashe
dama don ta azabtar da
marainiyar Allah ne" ta karasa
maganar tana matse kwalla,
Nawap kan shi sai da kafafun
shi suka kasa daukan shi,
karasawa yayi ya zauna sannan
ya fara tunanin ashe dama
yarinyar nan jinin shi ce, no
wonder ya ji tausayin da yake
mata ya banbanta da na sauran
mutanen da yake taimakawa,
Allah mai iko! Shine kawai
abinda Nawap ya iya fada a
bayyane..
* *Ummi ta kama hannun Deedo
ta rike gam, kallon ta take
tamkar marigayiyar yar uwar ta
Rukayya, yarinya tubarkallah
amma wahala ta kashe ta, cikin
zuciyan ta take cewa zan kula
dake Deedo, in maki gatan da
banyi ma diyar dana Haifa ba,
zan mayar da ke abin
kwatance, in inganta rayuwar
ki, sannan in tallafa maki har
sai kin cika burin ki na zama
kwararriyar likita. Deedo banda
kuka babu abinda take yi, yau
itace ta samu matar da ke
consoling din ta, har ta yarda
ta zauna kusa da ita! Ashe
dangi ma wata rahama ce a
rayuwar dan adam, Nawap ya
katse su ta hanyar saukar da
ajiyar zuciya, sannan yace
"well, faduwa tazo dai dai da
zama kenan, tunda dai yau ga
diyar ki ta dawo hannun ki ai
shikenan, ita kuma goggo
akwai Allah, zai yi ma Deedo
sakayya" ya mike, ya kara da
cewar "bara na shiga ciki, ko
sallan maghriba ba mu yi ba"
ummi kai kawai ta daga mashi,
dan yau wani farin ciki take ji,
gata ga diyar ta. Kallon ta tayi,
sannan tace "da izinin Allah,
wahalar ki tazo karshe Deedo,
ki saki jikin ki, dan baki da
mahaifiyar da ta wuce ni, idan
kin kwana biyu kin huta, zan
kaiki kiga dangi su ma su
ganki, zan baki duk wani farin
ciki wanda ya kamata uwa ta
bai wa diyar ta, kinji? Tashi
muje in kaiki dakin ki, kiyi
wanka kiyi sallah, sannan ki
sauko muci abinci" dagowa tayi
da jajayen idanun ta, tace
"nagode ma Allah da ya nuna
mun wannan rana a rayuwa ta,
nagode ma Yaa Nawap wanda
yayi silar sada ni da ku ummi,
Allah ya yi maku sakayya da
mafificin alkairi" hannu ummi
tasa ta rufe bakin ta, tace
"kyautata maki ya zama dole a
gare mu, saboda mune dolen
ki a rayuwar nan, kar na kara
ganin hawaye a idanun nan
kina jina?" Ta daga mata kai,
sannan ta mike ta dauko kullin
kayan ta, ummi na gaba tana
binta a baya har suka haye
sama, dakin da ke opposit na
ummin ta bude mata, anyi
painting dakin da pink nd
purple, yayin da komai da yake
cikin dakin ma pink nd purple
ne, baki Deedo ta sake tana
kallon haduwar wurin, hannun
ta ummi ta ja ta gwada mata
komai, haka ma toilet ta gwada
mata, da yadda za tayi amfani
da komai, ta dauko towel mai
mugun taushi ta bata, tace ta
daura ta shiga tayi wanka.
Yayin da ita kuma ta juya ta
fita, ta rufe mata kofan dakin.
A bakin gado Deedo ta zauna
tana kare ma dakin kallo, bata
taba tunanin akwai irin jin
dadin nan a wannan duniyar
ba, hawaye suka yayyafo mata,
tasa hannu ta share, sannan ta
mike ta cire kayan ta, ta daura
towel din ta shige wanka…
BA’A SHAN
ZUMA… 36, 37
& 38
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tana shiga wankan takurawa
bandakin kallo shima kansa
wani duniya aka zuba, tadauko
shampoo da sabulu ta ajiye
akasa tazauna dirsham akan
tiles din don yanda taganshi
tsaftsaf tasan zata iyacin
abinci aciki, takaranta jiki
sannan tadauko soso tanufi
cikin shower, murdawa
taringayi harya kunnu taji
ruwan sanyi dasauri takashe,
takara kunna dayan saitaji
ruwan zafi, murmishi yafito
mata, tasanya tafara wanka,
tafi awa biyu tana dirje jikinta,
kafin ta wanke kanta ma, duk
da Allah ya hore mata gashinta
daidai gwargwado baya samun
gyra, tafito tana goge kanta,
itakanta wani iska takeji yana
buso mata, tazauna gaban
dressing mirror. Shafa wancan
mulka wancan, dakarshe
tashafa powder sannan ta leka
wardrobe taga kaya azube ,
lalle yanzu duk wannan kayan
ita zatasa?, set 4 takedashi a
kauye, nan kuwa tanaga yafi
dari, ga gun gyale daban, hijab
daban, atamfa daban less da
shadda ma haka, gefe kuma
dogayen rigunane a tsaye.
Taciro riga daya, ta maida ta
rufe, sannan ta bude ta kasa
nan taga inners, ta ciro shima
tasaka sannan tadaure kanta ta
tattara kayan da ta cire, ta zuba
su aciki sannan tadauki sallaya
tabiya sallahn dake kanta, tana
nannadewa wata ta shigo tana
murmushi daga gani saar
Deedo ce, tace "inji ummi
kisauko abincinki is ready"
itama murmushin tayi sannan
tabita suka sauka, Nawap na
zaune yana mikawa cikinsa
abinci takaraso, itama zama
tayi sannan tafara kallon
coolers din gabanta, Nawap
yayi murmushi sannan ya
kwala kiran saude, wacce
takirata a sama sannan yace
"zo ki diba mata abincin ko" ta
amsa da "toh" Nan tafara zuba
mata, ferfesun kayan cikin,
agefe kuma jollof din shinkafa
ne yaji busheshen kifi, tun
tana kunyan ci anma tazage
taci abunta, Nawap kuwa ganin
zai takura mata yasa yamike
yabar mata gun, itakuwa taci
tayi nak, sunadan tadi sama
sama da saude wacce take
kimtsa gun, suna gamawa tai
masu saida safe, ta haye
sama, saboda wani bacci da
yake figan ta.
Haka Deedo ta kwana cikin
farin ciki da jin dadin sauyin
rayuwan data samu cikin dan
kankanin lokaci. Da safe bayan
ta tashi tayi wanka ta shirya
tsab cikin wata royal blue din
abaya, palon ta sauko domin
taimaka ma Saude da aiyukan
gida, amma abin mamaki har
ta gama komai ta jera abinci a
dining, suna cikin magana
Ummi ce tashigo palon
fuskarta kaman gonan auduga,
Deedo ta karasa gaban ta da
sauri, ta duka har kasa ta
gaisheta. Cikin jin dadi ta
ansa, sannan tace "Masha
Allah, kinga yadda kikayi
kuwa?, kuyi ku gama cin
abincin nan na aike ku da
Nawap ko kema zakiga gari,"
Jikinta narawa tamike don
yanzu gani take kamar a
aljanna take, Allah sa dai ba
mafarki takeyi ba balle ta tashi,
da sauri ta tuttura abincin,
sannan ta koma sama, gyalen
abayan ta dauko sannan ta
fito, yana jingine ajikin mota,
yasha brown shadda da hular
zanna, kullum kwarjini yake
kara mata, ta isa gareshi
sannan tashiga.
A hankali ta gaishe da shi, ya
ansa ba tare da ya kalla inda
take ba, ya cigaba da tukin shi
har suka bar unguwan. Ido ta
ware sosai ganin yadda
mutane ke shawaginsu ba
ruwan wani da wani, babban
abinda ke kara sanya ta
nishadi shine yadda take ganin
kyawawan motoci suna rafsa
gudu a titi hankali kwance. Ta
cikin Malali suka shiga, sannan
suka bi wani layi inda taga an
rubuta Raba Road, ita dai bin
ko ina take da kallo, ba tare da
wata damuwa ba. Ba suyi wata
tafiya mai nisa ba taga sun
kawo gaban wata katuwar
supermarket, wuri ya samu yayi
parking mai kyau, sannan ya
juyo yace mata "muje ko?"
Fitowa tayi har tana dan
tuntube, ta daga kanta sama
wani tafkeken sign board ta
gani mai dauke da manyan
haruffa, an sa STOP AND
SHOP! Jinjina kanta tayi, ganin
haduwar wurin, ba tare da bata
lokaci ba Nawap ya ja basket
suka wuce ciki. Shopping ya
cigaba da yi ba tare da ya bi ta
kanta ba, kuma most of
abubuwan da yake kwasa duk
na mata ne, dangin cosmetics,
native wears, handbags,
takalma, jewelries da dai
sauran su, sai da ya cika
basket din dam, sannan ya tura
zuwa inda zaiyi payment, ya
biya kudin aka kwashi kayan
aka sanya a boot din shi,
sannan suka shige suka dau
hanya. A tunanin ta hanyar da
suka bi zasu koma, amma sai
taga ya dau wata sabuwar
hanyar. Emirate plaza ya nufa,
inda ya shige ciki kai tsaye;
sannan yayi parking a wurin da
aka tanadarwa motoci. Ya fito
yana bada fadi, a tunanin shi
tana biye dashi, amma sai da
ya juyo ya ganta zaune cikin
motan sai kalle kalle take.
Girgiza kan shi yayi, ya kara
gaba inda ya shige wani katon
shop mai kofa hudu, kuma
babu komai a ciki dai zallan
electronics. Gefen wayoyi yayi,
inda ya zabo mata Samsung
Galaxy s3, ya karasa ya biya
kudin, sannan ya fito, yadda ya
hango ta kura ma wasu
kyawawan yan mata da suke ta
kilbibi ido, sai abin ya bashi
daria, inda cikin zuciyan shi
yake cewa "kema very soon
zaki zama abin kallo Deedo" da
sauri ya karasa ya shige
motan, yana shirin tadawa ne
wayan shi dake aje a tsakanin
seat din shi da na Deedo tayi
ringing, ita ta dawo da Deedo
daga duniyar da take, inda a
tare suka kai kallon su kan
screen din wayar…
BA’A SHAN
ZUMA… 39, 40
& 41
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Aysha shine sunan dake
rubuce a saman screen din,
sai da ya ja dan siririn tsaki,
sannan ya maida hankalinshi
ga tukinshi. Reverse yayi, ya
fita daga wurin, yayin da wayar
ta cigaba da rera waka alamar
kira yana kara shigowa. Deedo
ganin bashi da niyyar dauka,
tace "Yaa Nawap ana kiran ka"
cikin halin ko in kula yace "ina
ji ai" ganin bai damu da kiran
ba yasa itama ta juya ta cigaba
da kalle kallen ta har suka iso
gida.
Direct ya shige yayi parking
kanshi tsaye, a gefe suka ga
wata sabuwar Audi V10 baka,
ba tare da tunanin komai ba ya
fito, ya bude boot din ya
cigaba da ciro kayan da suka
siyo, yayin da Saude wadda ta
fito tun lokacin da taji shigowa
su ta cigaba da kwasa tana
kaiwa ciki.
Sauran da suka rage Deedo ta
kwasa ta yi gaba yana binta a
baya, da sallama suka shiga
palon, inda suka tarar da Ummi
da wata bakuwa a zaune. Sai
da Deedo ta gaishe da su,
sannan ta haye upstairs da
kayan hannunta.
Karasawa Nawap yayi ya zube
a kujera yana kiran wash.
Ummi tace
"ya dai? Ko ka gaji ne?" Yace
"Wlh yarinyar ki din can ta bani
wahala Ummi"
Ummi ta murmusa, sannan ta
kara da
"Ai sai hakuri dama, tunda dai
ka riga ka zama babban yaya"
ba tare da yace komai ba ya
mike da niyyar barin palon,
Ummi ta dakatar dashi ta
hanyar cewa "wai baka kula da
bakuwar mu bane?" Sai a
sannan ya kai duban shi ga
kyakkaywar budurwar da ke
zaune, wadda tunda ya shigo
ta tattara duk wata natsuwa,
tare da hankalin ta, ta mika
mashi.
A kasalance ya juyo ya kare
mata kallo, sannan ya shafi
sumar shi mai tarin yawa, yace
"Yaushe a gari?"
Wani lallausan murmushi ta
saki, sannan tace "inji maki'
bako kenan" cikin halin ko in
kula, yace "sorry naga call
dinki, I was driving" ta gyara
zaman ta, tace "no p" a dai dai
nan, ta ja handbag dinta,
sannan tayi ma Ummi sallama,
ta mike da niyyar barin palon.
Ita ma Ummi mikewa tayi, ta
nufin wurin Deedo wadda
hankalin ta ke wurin ta tunda
suka shigo gidan.
Shima juyawa yayi, ya bi
hanyar da zata sada shi da
part din shi, ba tare da ya kara
bi ta kanta ba. Aysha ta juya ta
bi bayanshi da kallo, tace
"Nawap"
Ya juyo hankali kwance, yana
mata kallon fadi matsalarki.. Ta
gyara tsayunwanta, tace "amma
kasan saboda kai nazo gidan
nan ko?"
"Ban fahimce ki ba" ya fada,
sannan ya jingine da bango ya
nade hannayen shi yana
kallonta. Takowa tayi a hankali
zuwa gaban shi; tace "har
yaushe ne ranar da zaka
fahimci yadda zuciyata ke
tafarfasa saboda sonka?
Nawap yaushe ne ranar da zan
samu farin ciki daga gare ka?
Shin wai mei yasa baka
tausaya ma zuciyar da ta dade
tana azabtuwa da so da
kaunarka ba? Plz Nawap kaji
tausayi na mana" ta karasa
maganar tana mai marairaice
fuska kaman zata yi kuka.
Kayataccen murmushinsa ya
saki, sannan yace "look Aysha,
ya kamata ace maganar nan ta
wuce tsakanin mu, ya kamata
ace a matsayin ki na mace
kinyi facing reality yanzu, ki
gane abinda kike so ba zai
taba kasancewa tsakanin mu
ba, in fact, kiyi hakuri ki bama
masoyanki dama har a cikin su
Allah yasa ki samu wanda zai
kwanta maki, I'm sorry" yana
gama fadin haka ya juya, ya
cigaba da tafiyar shi..
Hawaye ne kawai Aysha bata yi
ba, sai kukan zuci da take ta
faman yi, zuciyanta yayi baki,
ta rasa menene yake mata
dadi. Juyawa tayi zata fita, a
dai dai lokacin Deedo ta sauko
daga sama, kujeran da Aysha
ta tashi Deedo ta kaiwa kallo,
nan taga iPhone6 dinta a
yashe, da alama ta manta da
ita ne, dan haka tayi saurin
karasawa ta dauka wayan,
sannan ta bi bayanta…
Har ta shiga motan ta zauna, ta
hada kanta da steering, wani
irin zugi take ji a zuciyanta.
Deedo ta karasa tayi knocking
glass din, ta dago ta kare mata
kallo, sannan ta zuge glass din
ta watsa mata kallon raini, tace
"ya akayi ne?" wayan Deedo ta
mika mata, sannan tace "kin
manta wayan ki ne" fisgan
wayan tayi, sannan ta maida
glass dinta ta zuge, ta fara
kokarin tada motan. Ita kam
Deedo da bata fahimci halin da
take ciki ba, ta juya ta shige
ciki abinta.
WACECE AYSHA?
Aysha Sabe Musa, 'ya kwaya
daya tal a wurin iyayenta
wanda suka kasance yan asalin
garin Katsina, amma yanayin
aiki ya dawo dasu garin kaduna
da zama. Suna zaune a
Galadima road inda ya kasance
basu da nisa tsakanin su da su
Nawap. Sunyi karatu tare da
kanwar shi Hafsat a A.B.U
zaria, inda daga bisani ta wuce
Jordan inda ta kammala
masters dinta, ta dawo gida
yanzu.
A kalla Aysha tayi shekara
biyar tana dakon soyayyar
Nawap, wanda son da take
mashi ne ya kara kusancinsu
da Hafsat har zuwa lokacin da
tayi aure, amma saboda shi ta
kan wanke kafa taje gidan su
duk don ta ganshi, sai ta fake
da cewar taje gaishe da Ummi
ne. Sai dai tayi rashin sa'a, har
inda yau take, Aysha bata
samu karbuwa ba a zuciyar
Nawap, asali ma bata jerin
matan da Nawap zai iya so a
rayuwanshi!
BA’A SHAN
ZUMA… 42, 43
& 44
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cigaban Labari
Cikin gida Deedo ta koma inda
ta tarar da Saude tana jera
abinci a dinning, taimaka mata
tayi har suka gama, sannan ta
wuce tayi sallah, ta gama ta
shiga dakin Ummi ta sameta
zaune saman sallaya, gefe
guda ta samu ta zauna har ta
gama, sannan ta juyo da
murmushin ta, tace "auta ta ya
aka yi ne?" Ta murmusa tace
"lafia lau Ummi, abinci ne ya
zama ready" ta kara fadada
murmushinta, tace "kuma autar
Ummi na jin yunwa ko?" Ta
dukar da kanta tana 'yar daria,
sannan tace "a'a nazo na fada
maki ne kawai" daria Ummi
tayi, tace "to tashi muje kasan"
a tare suka mike, inda Deedo
ta tattara hijab da sallayan da
Ummi ta gama sallah ta ninke,
ta mayar da su wurin su,
sannan ta bi bayan ta suka
sauka kasan.
Nawap suka gani zaune da
jallabiya a dinning area yana ta
kwasan girki ba ji ba gani,
Ummi ce tayi gyaran murya, sai
a sannan ya lura da zuwan su.
Daria suka sanya shi da
Ummin, inda ita kuma Deedo ta
dukar da kanta tana tata
dariyar a boye.
Karasawa sukai suka zauna,
Ummi ce ta umarci Deedo da
tayi serving dinsu, dan ta lura
akwai abubuwa da dama da ya
kamata ace Deedon ta iya, dan
haka ma ta kalleta, ta kara da
cewar "yau fa da girkinki zamu
yi dinner, dan haka sai ki
shirya" murmushi tayi, yayin da
ta cigaba da zuba abincin, tace
"to shikenan Ummi"
Kallon ta Ummi ta cigaba da yi,
tana mai tunano 'yaruwarta,
wani so da tausayin yarinyar
taji ya kara tsirga zuciyarta,
wasu yan kwalla suka feso
mata, inda tasa hannu ta share
ba tare da ta bari sun lura da
ita ba.
Kallonta, ta mayar kan Nawap
wanda ya tada plate din fried
couscous yana korawa da
kunun aya mai gardi, tace "wai
kai yaushe zaka koma office
ne? Ko har yanzu hutun bai
kare ba?" Yayi gyatsa tare da
hamdala, sannan ya dan shafi
sumarshi yace "Jibi zan wuce
in sha Allah" tace "ai gara kazo
ka tafi dan ka kusa cinye mana
abincin gida" yace "kin dai gaji
da ni tunda kin samu diya
yanzu" tace "har ma da hakan"
yace "yawwa yanzu naji batu
Ummi" haka suka cigaba da
firan su cikin jin dadi, Deedo
da bata cika saka baki a firan
ba, sai dai tayi dan murmushi
kawai. Jin ta take a wata
duniya ta daban, yay ita ce ta
samu 'yanci. Hamdala tayi
sannan ta yima Allah godia da
ya nuna mata wannan
kyakkaywar rana…
A tare suka mike bayan sun
kammala con abincin, inda
Deedo ta tattara wurin ta
kimtsa komai, sannan ta wuce
da kwanukan kitchen.
Tana kokarin shigowa palon
taji Ummi na cewa "yanzu
Nawap kana ganin rayuwa zata
yi a haka? Ka tuna kai fa ba
yaro bane, ya kamata ace
yanzu ka aje iyali fa, kuma ni
ita yarinyar can Aysha ban ga
abinda ta rasa ba da baza ka
so ta ba, ko dai kana da wata
matsala ne?"
A hankali ya fara magana, "wlh
bata da komai Ummi, kawai dai
ba zan iya rayuwa tare da ita
bane, amma kar ki damu in
sha Allah zan nemo mata in
dai hakan zai faranta maki rai"
tace "shikenan, Allah ya
taimaka" ya ansa da amen,
sannan ya mike ya bar palon.
Karasawa Deedo tayi, ta zauna
a kasan carpet tana dan matsa
kafan Ummi.
Kanta Ummi ta dafa tace "auta
ya akayi ne?" "Lafia lau" ta fada
tana dan murmushi, ita ma
Ummi murmushin tayi, tace
"gobe dai in sha Allah zamu je
kiga danginki, kiga yar
tsohuwar kakarki da kowa da
kowa" dadi ne ya ratsa ta, ta
rasa abinda zata ce ma Ummi,
nan da nan hawaye suka fara
bin fuskarta, a hankali ta fara
magana "Ummi kinyi mun
komai a rayuwa, kin mayar da
ni mutum a lokacin da kowa ya
ke kyamata, bani da bakin yi
maki godia, sai dai ina addu'ar
Allah yayi maki sakayya da
mafificin alkairi, ya sa ki gama
da dunia lafia"
Nan take itama Ummi hawayen
suka gangaro mata, mikar da
ita tayi ta rungume ta sosai,
tana shafa bayanta alaman
rarrashi. A sannu a hankali ta
daina kukan, mikewa duk suka
yi zuwa sama domin gabatar
da sallan la'asar.
Suna gamawa suka wuce
kitchen, inda Ummi tare da
Saude suka cigaba da taimaka
ma Deedo har ta gane yadda
zata yi amfani da abubuwan
kitchen din, cikin raha da
annashuwa suka gama komai
suka jera a dinning, sannan
suka wuce domin bada farali..
Misalin karfe sha daya na safe
Deedo ta fito daure da towel a
jikinta, a hannunta dan karamin
towel ne tana tsane
yalwataccen gashinta. Gaban
mirror ta zauna, ta shafa mai
tare da Dan simple makeup. Ta
gyara gashinta sannan ta mike
zuwa wardrobe domin ta samu
kayan sakawa.
Daya bayan daya take bin lodin
kayan da kallo har ta rasa
wanne zata saka a ciki. A
karshe ta jawo wata super
peach nd coffee brown dinkin
skirt and blouse ta saka, ta
buda kallabin tayi mashi wani
mugun dauri kamar ta kifa
turmi. Kallon kanta tayi a
mirrorn dake jikin wardrobe din
taga kaman ba ita ba, a fili ta
furta "lallai sutura ita ce
mutum" murmushi tayi, sannan
ta jawo bakin gyale ta buga
abinta.
Wurin takalma ta matsa taga
duk high hill ne, ita kam ta san
ko za a sa mata wuka ba zata
iya tafia da su ba. Wani
maroon ta gani shine mai dan
tudu kuma bai cika tsawo ba
dan haka ta jawo abinta, ta
dora ta sauka zuwa palo inda
Ummi ke jiranta.
Nawap ne ya fara kallonta,
daria taso kwace mashi, amma
ya fuske yace "Ummi ga fa
autar ki ta faso"
Juyawa Ummi tayi ta kare mata
kallo, gata dai tubarkallah, kaya
sun ansheta sai dai wani
bahagon daurin kallabi da tayi
da kuma color riot din da ta
buga. Murmushi tayi sannan ta
mike tace "eyyeh! Lallai auta ta
tayi kyau, sai dai matsala daya"
taja hannun ta suka koma
sama.
Wardrobe din ta bude ta dauko
mata peach din gyale, ta bata
peach din takalmi, sannan ta
dauko mata handbag coffee
brown, ta zaunar da ita ta
gyara mata daurin kallabin
sannan tace "tashi ki gan ki"
mikewa tayi ta kare ma kanta
kallo, lallai gyara shine mace,
ta dan rufe fuskanta alaman
kunya, Ummi tace "tashi muje
kar muyi rana" ta mike ta bi
bayanta, a hankali take takawa
kasancewar bata iya tafia da
high hill ba, amma abin sai ya
bada wani style na daban…
Dagowan da Nawap zaiyi, tsab
suka hada ido, da sauri ta
dukar da kanta, inda shi kuma
ya kasa dauke idonshi a kanta,
Tubarakallah Masha Allah ya
dinga furtawa a zuciyanshi,
lallai yarinyar mai kyau ce.
Ummi ce ta katseshi da cewa
"muje mana" cikin jin kunya ya
dan sosa kai, sannan ya mike
suka wuce, amma hankalin shi
kaf yana gun yadda Deedo ke
takawa a kasaitance..
BA’A SHAN
ZUMA… 45&46
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Da dan sauri ya karasa wurin
ajiyar motocin, inda ya darzo
wata dark blue din Audi R8,
reverse yayi, sannan ya gyara
tsayuwar motar, inda su kuma
a lokaci daya suka bude suka
shiga. Deedo ce a gaba, yayin
da Ummi ta kame a owner's
corner. Wuta ya ba motar,
sannan suka lula saman titi
hankali kwance.
Tafiya suka yi mai dan nisa,
Deedo har ta fara tunanin ko
garin zasu bari. Daga karshe
dai ta ware idanunta ta cigaba
da yan kalle kalle, cikin hikima
Nawap ke satar kallonta yana
ganin yadda farin ciki ke
bayyane a fuskanta, yanayinta
kawai, zai sanar da kai cewar
bata da sauran damuwa.
Murmushi ya saki wanda bai
san lokacin da ya sufce mashi
ba, a haka suka iso main
house din su Ummi da yake
Hayin Banki. Ba tare da bata
lokaci ba ya samu wuri yayi
parking, sannan duk suka fito
suka shige ciki.
Zaune suka tarar da mai gidan
a cikin wata yar baranda, idon
shi sanye da medical glass
yana duba jaridar Daily Trust.
Inda yake zaune suka karasa
duk suka kwashi gaisuwa,
sannan suka mike gaba
dayansu zuwa cikin gidan.
Kallon Deedo yake kaman ya
taba sanin mai irin fuskarta,
sai dai bai ce komai ba har
suka shige ciki. Ita ma tunda
suka shiga take kallon dattijon
mai cikar kamala da kwarjini,
kamar shi sosai ta gani da
Nawap, sai dai yanayin tsufa
kawai da yake tattare dashi.
A palon suka samu Inna zaune
da yar casbaharta tana lazumi.
Kallo daya tai wa Deedo taji
gabanta ya fadi, a take kuma ta
yardar wa kanta cewar duk
yadda akai wannan yarinyar
jininta ce. A daddafe suka
gaisa, yau ko tsokanar da ta
saba yiwa Nawap ba ta mai ba,
cikin zakuwa ta kalli Ummi tace
"ke kam ina kika samo mai
kama da ke?" Murmushi Ummi
tayi, ba tare da bata lokaci ba
kuma ta warware masu komai
dangane da Deedo, ta kara da
cewar "amma yanzu ta dawo
nan da zama kenan in sha
Allah"
Salati Inna ta kwasa, sannan ta
saki kuka, tana cewa "yaki nan
Firdausi, ashe dama kina
wannan duniyar?" Matsawa
Deedo tayi, suka rungume juna,
inda Malam ya kallesu
fuskarshi dauke da murmushin
dattako yace "to ke banda
abinki wannan ai abun farin
ciki ne, menene abun kukan?"
Nawap kallon Inna yake yana
daria, Ummi kam itama sai da
ta dan matse kwalla, nan fa
wuri ya kaure da murna, yan
tsofaffin sai nan nan suke da
Deedo, gani suke kaman
Rukayyar su ce ta dawo.
Hamdala suka yi, suka yima
Allah godia da ya dawo da
yarinyar cikin danginta. Itama
Deedo taga gata, banda
hamdala babu abinda take yi.
Godia tayi ma Allah daya sada
ta da dangin mahaifiyar ta,
jinta take tamkar yau ce ranar
da aka haifeta..
Nawap tsintar kanshi yayi a
yanayi na mugun farin ciki,
ganin Deedo cikin walwala da
jin dadin rayuwa. Sai da suka
yi sallan azahar sannan suka yi
haramar tafia, daga nan ma
gidajen kannen Ummi suka je,
duk wani dangi na nesa da na
kusa babu inda basu kai
Deedo ba, a nan ta tabbatar ma
kanta lallai ita mai gata ce,
sannan ta kara tantancewa dan
uwa rahma ne, ko ba komai
wannan soyayyar da zai nuna
maka ma wani abu ce a
rayuwa.
Wurin karfe shidda na yamma,
sannan suka dau hanyar gida,
a nan Ummi ke ce ma Nawap
"ya kamata ace Deedo tayi
jamb fa, don bana so ta bata
lokaci, so nake da result din su
ya fito ta wuce makaranta"
Sai da ya saci kallon Deedo
wadda tsananin farin cikin da
take ciki yasa sai faman
murmushi take, murmushin
yayi shima, sannan yace "nima
nayi wannan tunanin sai dai
kaman an gama jamb yanzu fa"
Ummi tace "ba naga sun bullo
da wani sabon system na
computer base ba?" Yace "haka
ne, zan bincika gobe kafin na
wuce in sha Allah" ta ansa da
"amen" inda a dai dai lokacin
kuma suka kawo gida.
The next day kamar yadda
Nawap yayi alkawari haka ya
gudanar da duk wani bincike,
inda bai bar Kaduna ba sai da
ya tabbatar ya gama mata duk
wani abu da ya kamata.
Misalin karfe biyu na rana suka
dawo gida, wanka kawai yayi,
yayi sallah ya ci abinci, sannan
ya dau hanyar Abuja, yana mai
cike da tunani da maraicin
Deedo da Umminshi..
*****
Haka rayuwa ta cigaba da
tafiyan ma Deedo cikin jin dadi
da walwala, weather garin ta
anshe ta sosai, tayi fresh tayi
das das abinta, gashi Ummi
tana kokarin koya mata
abubuwa, in ka ganta baza ka
taba gane ta ba, balle har kayi
zaton ita ce Deedon Goggo ta
kauyen Ningi..
BA’A SHAN
ZUMA…
47,48,49 &50
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Ranan wata Juma'a da misalin
karfe biyar da rabi na yamma
Deedo ta fara takowa a hankali
zuwa babban palon gidan,
sanye take da wani blue skinny
jeans, tare da wata armless
tshirt yellow mai dan fadi, an
rubuta LISTEN TO YOUR MUSIC
& SONGS. kunnenta makale da
earpiece, ta tattara yalwataccen
gashinta tayi parking dinshi a
tsakiyar kai.
A hankali take bada step, tana
dan latsa wayanta yayin da
take saukowa zuwa kasa. Duk
wanda ya kalleta sai ya kara,
saboda asalin kyaun da tayi,
tayi fes fes abinta, kaman irin
tashin birnin nan tun asali.
Karasawa tayi inda ta samu
Ummi zaune, a gefenta kuma
matar nan ce ta ranan nan,
wadda ta tabbatar da cewar
itace taji Ummi ta kira da
Aysha.
Karasawa tayi ta zauna a kasan
carpet dai dai inda Ummi take,
dagowa tayi da niyyar ta gaishe
da bakuwar amma taga idonta
kyam a kanta har lokacin da ta
zauna. Cikin siririyar muryanta,
ta kara duban Aysha tace
"aunty ina wuni"
Kallonta Ayshan ta kara yi,
sannan ta saki wani dan
murmushi yayin da tace "kina
lafia?" "Lafia lau" ta bata ansa
a takaice, inda ta maida
hankalinta akan game dinta da
take yi na candy crush. Kanta
Ummi ta shafa, sannan tace
"auta ya akayi ne?" Sai da ta
murmusa sannan tace "lafia
lau Ummi na" "Masha Allah"
Ummi ta fada, inda ta maida
hankalinta kan wayanta da take
ringing a gefenta.
Wayan ta daga da sallamarta,
tace "ai mun zata laifi muka yi,
yau kusan kwana ukku kenan
babu kai babu labarin ka"
Daga dayan gefen Nawap ya
dan yi daria, sannan ya gaishe
da ita, ya kara da "Ummi ai kin
yaye ni yanzu tunda kinyi
sabuwar 'ya" tace "to kai banda
abinka, ina zan tuna da kai ina
busy kula da autata" ta kara da
cewar "idan ka ganta baza ka
gane ta ba yanzu"
cikin raha da jin dadi suka
cigaba da firan su ta da' da
mahaifi, inda daga karshe ya
shaida mata cewar principal
din su Deedo ya mashi waya
cewar result din su ya fito, dan
haka zuwa Monday zai je ya an
so mata, daga nan zai biyo ta
kadunan. Hamdala Ummi tayi,
sannan tace "to Allah ya sa
muga alkairi" "amen" ya fada,
sannan ya kara da "a gaishe da
kowa" tace "ga autata nan, bara
ta gaishe ka" Ummi ta mika
mata wayar, ta ansa ba don
ranta ya so ba, a kunnenta ta
kara wayan, tace "Yaa Nawap
ina wuni"
Sai da ya ja wani gauron
numfashi, sannan ya ansa da
"kina lafia Autan Ummi?" Tace
"lafia lau, ya aiki?" Yace"Lafia,
Ummi ta fada maki result dinku
ya fito ko?" Tace "a'a, tana da
bakuwa ne yanzu, nasan
anjima zata fada man" yace
"ok, zanje Ningi on monday, ko
zaki je ne?" Ya fada cikin sigar
wasa, murmushi ta dan yi,
sannan tace "ka manta goggo
tace kada na koma koda ganin
gida ne?" Daria yayi sosai,
sannan yace "to shikenan,
zanje in ce kina gaishe da ita"
tace "to shikenan, amma ina da
sako dan Allah" yace "ki kira ni
idan na fita office sai ki fada
man"
A haka suka yi sallama ta mika
ma Ummi wayan, sannan ta
mike tace "Ummi bara na taya
Saude girki" yayin da take tafia
zuwa hanyar kitchen din.
Wani kallon tsana Aysha ta bita
da shi, har saida ta daina
ganinta sannan ta kyaleta,
juyon da zata yi karaf, suka
hada ido da Ummi wadda take
kallon duk abinda ke faruwa.
Murmushin yake tayi, sannan
ta dan fara kame kame, tace
"Ummi wai dama Hafsat na da
sister ne?" Murmushi Ummin
tayi itama, sannan tace "mai
kika gani?" Tace "naji kina
kiran yarinyar can da autarki,
kuma ni ban taba saninta a
gidan nan ba, ko ba nan take
zaune bane?" Ummi ta dan
muskuta, tace "owh wai Deedo
kike nufi? 'Ya ta ce 'yar
kanwata, amma Allah yayi wa
maman nata rasuwa, shine ta
dawo hannuna da zama"
Wani malalacin murmushi ta
saki, sannan tace "Allah sarki,
Allah ya jikan musulmi" Ummi
ta ansa da "amen" yayin da
Aysha ta kimtsa inata inata ta
kara ma bujenta iska.
Tana fita gidan, wayan Nawap
ta kira ya kai sau biyar amma
bai ansa ko daya daga cikin
calls din ba, haka ta hakura, ta
shilla kan motarta saman titi, ta
bata wuta..
Deedo na gama sallan
maghriba, tana zaune saman
sallaya taji wayanta ya fara
ringing, hannu tasa ta zaro
wayan, sannan ta kalla number
da take kiranta, Yaa Nawap ta
gani a rubuce dan haka tayi
saurin dagawa ta gaishe da
shi, cikin baby voice dinta mai
dadin sauraro.
Kwance yake saman 3seater,
bai san lokacin da idonshi ya
lumshe ba, a hankali ya bude
su, sanna yace "ya muka yi
dake? Ko kin fasa bada sakon
ne?" Yadda yayi maganan duk
sai ya daburtar da ita, ta fara
magana tana in'ina, "ehmm,
wlh, I'm sorry Yaa Nawap, na
shiga kitchen ne ban dade da
fitowa ba shi yasa" yadda tayi
maganan ya bala'in birge shi,
nan take idanuwan suka kara
lumshewa, ba tare da ya bude
su ba yace "idan kin gama
abinda kike zaki kwanta, ki kira
sai ki fada mun, sauran kuma
ki kara mantawa, kiga yadda
zanyi dake"
Da sauri tace, "ba zan manta
ba in sha Allah" ba tare da ta
jira abinda zai ce ba ta kashe
wayan, sannan ta mike tayi
sallan isha'i wadda taji an kira
a masallacin kofar gidan..
Rungume wayan yayi a
kirjinshi, wani irin abu ne ke
mashi yawo gaba daya jikinshi,
ya rasa tantance wane irin
yanayi yake ciki, a hankali
fuskantan ya fara yi mashi
gizo, muryanta yake ji cikin
tsararren turancinta ranan da
suke debate, a hankali ya
hango fuskanta mai cike da
damuwa a ranan da ya fara
magana da ita, sannan ya
hangota ranan da ta buga
daurin kallabin nan mai kama
da turmi, sannu a hankali
kyakkaywar fuskanta tai mashi
walkiya a ranan da suke
dawowa daga unguwa, yanayin
farin cikin da take ciki, da
yanayi na gushewar duk wata
damuwa da take tattare da ita,
shi ya bashi damar sakin wani
yalwataccen murmushi.
A hankali ya furta,
"Alhamdulillah Allah daka cika
mani burina, Allah nagode
maka daka bani damar cika
alkawarin dana dauka na
samowa marainiyar ka farin
cikinta… "
Kira ne ya shigo wayanshi,
wanda yayi sanadiyyar
katsewar tunaninshi. Da sauri
ya jawo wayan dan a tunanin
shi Deedo ce, ganin sunan
Aysha a rubuce yasa gwiwoyin
shi sakewa, inda ya daga
wayan a kasalance.
"Kina lafia?" Ya tambaya, inda
daga bangarenta, ta fashe da
wani irin matsanancin kuka
mai tsuma zuciya. Mikewa yayi
daga kishingidar da yayi,
sannan ya fara tambayar
"Aysha lafia? Ya akayi ne?"
Tambayoyi ya dinga jera mata,
amma ta ki ta bashi ansar ko
daya, kuka kawai take yi kaman
wadda aka fada ma sakon
mutuwar uwa ko ta uba! Jin
kanshi yayi ya mashi nauyi,
duk da ba son Aysha yake ba
amma yana jin kukanta har
cikin zuciyarshi, kasancewar
shi mutum mai tsananin
tausayin mace, wanda ko
kadan baya son yaga mace a
cikin wani hali.
Haske wayan ta fara yi call
waiting na shigowa, dago
wayan yayi daga saman
kunnenshi inda yaga sunan
Deedo a rubuce saman screen
din…
BA’A SHAN
ZUMA… 51, 52
& 53
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Da sauri ya katse wayan Aysha,
inda ya daga kiran na Deedo
kai tsaye, a hankali kwance ta
fara magana, inda ya nemi
tunaninshi gaba daya ya rasa,
jin muryanta yake har cikin
bargonshi, lumshe
idanuwanshi yayi inda a lokaci
guda ya nemi damuwar da take
tare dashi ya rasa, cikin
kunnenshi ya tsinkayi muryanta
tana cewa "kaji Yaa Nawap?"
Firgigit, ya dawo daga duniyar
da yake, yace "mei kika ce ne?"
Tace "zan bada sako wurin
Hally ne" "go ahead ina jinki"
ya fada, ita kuma ta cigaba da
cewa "kace ina gaisheta, kuma
dan Allah ka bata number ta
kace ta kira ni" duk a tsorace
take maganan, gani take
kaman zai ce ta raina shi ne,
dan haka take maganan cikin
wani salo na yarinta da neman
afuwa.
Wani numfashi ya ja, sannan
yace "shikenan sakon naki?"
Kai ta girgiza kaman yana
kallonta, sannan ta ansa mashi
da "eh shikenan, sai da safe"
da sauri ta katse wayan, inda
shi kuma ta barshi da tsananin
tunani da muradin sauraren
muryanta mai dadi. Yana cikin
wannan hali wayan Ayshan ta
kara shigowa, wanda dama
kiran take ta faman yi tun yana
cikin magana da Deedo.
Daga wayan yayi, ba tare da
yace komai ba, a tunaninshi
kukan zata cigaba da yi, sai
yaji ta buda murya tace
"Nawap na gano dalilinka na
wulakantani, yanzu nasan
menene dalilinka na kin ansar
soyayyata, abinda nake so ka
gane shine, bazan taba rayuwa
ba tare da kai ba, sannan kuma
wata yar ficiciyar yarinya bata
isa tazo ta wargaza mun plans
din da na dade ina shiryawa
shekara da shekaru ba
Wata tsawa ya daka mata,
wadda tasa ta shiga taitayinta
lokaci guda, cikin wata
kakkausar murya ya fara
magana "who do yu think yu
re? Nd where all this ur
nonsense are heading to?"
Kasa ansa shi tayi, inda shi
kuma ya cigaba da cewar
"thou, ban san ina maganan ki
ya dosa ba, amma ina so ki
gane ba wanda ya isa ya juya
ni, ni nake da ikon kaina kuma
ba wanda ya isa ya sani yin
abinda ba shi nake so ba, shin
wai ke yaushe ne ranar da zaki
farka daga dogon mafarkin da
kike yi? Yaushe ne zaki gane
abinda kikeyi is so old
fashion? Ya kamata ki neman
ma kanki Mafita Aysha, me nd
yu ain't belong to each other,
plz ki barni naji da rayuwata, ki
fita harka ta plz.. "
Bata bari ya karasa fadar
abinda yake son fada ba, ta
katse shi da cewar "lallai kana
da aiki Nawap, idan har kana
tunanin akwai ranar da zan
daina sonka, ina mai tabbatar
maka da cewar na bar dunia a
wannan ranan, sannan kuma
duk wulakancin da kake ganin
ka iya, bazan hana ka yi mun
ba, amma ka sani, wannan
fitsararriyar yarinyar daka baro
a gida, a kanta abin zai kare,
so yu better becareful.." tana
gama fadin haka ta katse
wayan tayi wurgi da ita, a
lokaci guda kuma ta fashe da
wani matsanancin kuka, ta
rasa wane irin so take ma
Nawap wanda ta kasa cire shi
daga cikin ranta shekara kusan
biyar kenan!
Sai a lokacin ya gane inda
maganan Aysha ya dosa,
amma babban abinda ke bashi
mamaki baya wuce yadda take
neman kulla wata alaka ta
daban tsakanin shi da Deedo,
yarinyar da tausayinta yasa
yake bata duk wani
muhimmanci da yake bata,
yarinyar da ya dauka a
matsayin kanwarshi, shin wai
menene dalilinta na yin wannan
exaggerating din? Amsar da ya
rasa inda zai samo ta, mikewa
yayi jiki ba kwari ya karasa
cikin bedroom, a lokaci guda
ya cire jallabiyan jikinshi yaja
towel ya daura sannan ya wuce
bathroom…
Ranan Monday da misalin karfe
5 na asuba Nawap ya mike,
bayan ya dawo masallaci bai
jira komai ba ya fara shiri, duk
wani abu da zai bukata ya
gama tattarawa. Karfe 7 dai dai
ya isa office din su, anan ya
samu yayi breakfast inda daga
bisani ya karasa nashi office
din, anan ya tadda reply na
letter da yayi na son yin tafiya
ta sati daya.
P.A dinshi ne ya shigo ya
gaishe da shi, sannan ya ke
fada mashi cewar dazu aka
kawo lettern daga office din
director. Godia yai mashi, inda
ya koma kan wata 2seater da
ke aje a tsakiyan office din ya
zauna. Zaro lettern yayi, ya fara
dubawa, nan da nan murmushi
ya bayyana a kan fuskanshi,
cikin hanzari ya mike yayi kiran
P.A din yai mashi bayanin duk
abinda ya kamata, sannan ya
tattara laptop dinshi da sauran
documents din da zai bukata
yai mashi sallama ya fito ..
Inda yayi parking mota ya nufa,
ya zuba tarkacen a baya,
sannan ya shiga ya tada motan
ya fito.
Gudu sosai ya rinka yi
hankalinshi kwance, jin
zuciyanshi yake fari tass
kaman anyi mashi albishir da
wani babban abun alkairi. Cikin
ikon Allah ya shigo garin Ningi,
bai jira komai ba ya wuce
skool din su Deedo, cikin
kankanin lokaci yayi duk wani
abu da ya kamata, sannan ya
anshi result din yai masu
sallama ya fito.
A hankali ya fara shiga cikin
garin yana tunanin ta ina zai
gano gidan su Hally, hanyar
gidan Goggo ya dosa, dan ya
san ta can ne kawai zai iya
samun damar da zai gane
gidan su yarinyar…
BA’A SHAN
ZUMA… 54, 55
& 56
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tun daga nesa ya fara hango
taron mutane, wuri ya samu
yayi parking, sannan ya fito
daga motan, a kafa ya karasa,
nan ya tarar da yan sanda har
guda ukku, biyu mata da namiji
guda. Hannuwan Goggo matan
suka kama suka rike ta gam
kamar wadda tayi kisan kai,
tirjewa take tana kuka kaman
ranta zai fita, amma matan nan
kokarin tura ta suke cikin
motarsu.
Da sauri Nawap ya karasa
gabansu yana tambayar abinda
ke faruwa amma babu wanda
ya tanka shi. Namijin dan
sandan ne ma ya juyo yace
"idan kana bukatar jin ba'asi
zaka iya biyo mu station
malam" a dai dai lokacin su
kuma suka yi nasarar tura kan
Goggo cikin motar suka shige
suka bata wuta.
Ba tare da bata lokaci ba
shima ya shige ta shi motar ya
bi bayan su har zuwa police
station din. Suna isa suka fito
da ita hannunta sagale da
handcuffs suka tusa keyarta
gaba, tana kuka tana komai,
amma ko tausayin tsufanta
basa yi, haka suka tura ta cikin
cell suka jawo shi suka rufe.
Da saurinshi ya karasa wurin
dan sandan yana tambayar
abinda ke faruwa, sai da
officern ya gama wasu 'yan
rubuce rubuce sannan ya dago
yace "malam ya kuke da matar
nan ne?" Nawap ya gyara
tsayuwarshi, yace "kanwar
mahaifi na ce, plz ka fada mun
abinda tayi" dan sandan ya
cigaba da jawabi kamar haka
"ita kam babu abinda tayi,
amma kasan dan kuka ya kan
ja ma uwarshi jifa, dan haka
shafin danta ne ya shafeta.."
"Ban fahimce ka ba" Nawap ya
fada yana kallonshi. Dan
sandan ya cigaba "yaronta
Shehu ne ya karya kafar wani
yaro, sannan kuma ya caka
mashi wuka a ciki, kuma an
nemeshi sama da kasa a cikin
garin nan an rasa, gashi kuma
iyayen wanda aka yi ma raunin
sunce baza su taba hakura ba,
saboda yaro yana can a asibiti
tsakanin rayuwa da mutuwa,
yau kuma kusan kwana hudu
kenan muna neman Shehu
amma babu wani labari, dan
haka muka yanke shawaran
kama uwashi, idan yana sonta
ya bayyana kanshi, sai mu
saketa"
Wani irin gumi ne ya yayyafo
ma Nawap, a lokaci guda kuma
ya fara karanto innalillahi wa
inna ilaihir raji'un…
Komawa yayi da baya, ya samu
wani dan benci ya zauna,
hannuwan shi duk biyun ya sa
ya tallabi kanshi, yana mai
cigaba da karanta innalillahi wa
inna ilaihir raji'un. Tunanin
abinda Goggo tai ma Deedo ya
fara yi, har wata zuciyar tace
ya tafi ya barta anan, amma
tunowan da yayi da ko
bakomai kanwar mahaifin
Deedonshi ce, shi ya bashi
damar mikewa ya koma gaban
dan sandan yace "abokina
yanzu menene abin yi?"
Officer yace "abin yi anan
shine kaje kaga dangin yaron a
asibiti, duk yadda kuka yi sai
ka dawo kai mana bayani"
Nawap yace "ka taimaka muje
tare mana" sai da yayi jim,
kaman ba zai je ba, sai kuma
yace "ok muje mana."
A tare suka fito suka shiga
motan Nawap din, sannan suka
doshi asibitin kai tsaye. Dakin
da akayi admitting yaron suka
nufa, nan suka tarar da baban
yaro yana matse kwalla.
Bayanin abinda ke tafe da su
dan sandan yai mashi, baban
ya dago yace "Allah dai ya
tsinewa yaron nan, Ian zaman
zamana ya jawo mun masifa,
yanzu gashi nan ance sai an
mishi aiki a ciki, kuma wai sai
na bada kudi naira dubu
saba'in, ni yanzu ina na
gansu?" Ya karasa maganan
yana matse hawayen da suka
taran mashi.
Dukawa gaban shi Nawap yayi,
yace "Baba kayi hakuri ka
daina kukan nan, alfarma zan
roke ka, kasa a saki mahaifiyar
Shehu da aka kama, ni kuma
zan biyawa yaronka kudin aiki
har ma dana magani, su kuma
yan sanda zasu cigaba da
neman Shehu har zuwa ranan
da za'a ganshi" dan tsohon ya
dago yace "in dai kayi wannan
alkawarin to zan sa a sake ta,
amma fa bazan taba yafewa
Shehu ba, dole ne alkali ya
raba mu"
Nawap yace "na maka alkawari
baba, muje in biya maku kudin
aikin, daga nan mu wuce
police station kasa a saki
Goggon" mikewa duk sukayi,
saida suka biya ATM Nawap ya
cire 100, 000 yaba dan tsoho,
sannan suka karasa station
aka gama rubuta statements,
daga nan aka fito da Goggo
ido yai mata gwale gwale
kaman danyen nama saboda
kukan da tasha, Nawap bai bari
ta ganshi ba, ya shige motarshi
ya kara gaba.
Unguwan ya koma, dakyar da
tambaya ya samu wani dan
matashi ya kai shi gidansu
Hally, a hanya ne yake
tambayar yaron abinda ya faru
da su Goggo, yaro da yaji
sanyin A.C, nan da nan ya baje
baki ya fara bashi labari yana
cewa "shi ai Shehun ne kasan
yanzu wasu mutane ne yake bi,
ni a yadda naji ma haka ake
cewa wai kashe yaron suka so
suyi, Allah ne bai basu sa'a ba,
sai dai suka caka mai wuka a
ciki kuma suka karya mashi
kafa saboda wata kungiya ce
garesu, shi kuma yaron ya fita
daga cikin su shine fa sukai
mai wannan danyen aiki."
"Allah ya kyauta" Nawap ya
fada, yaro ya cigaba da cewa
"amin fa, amma al'amarin
Shehu sai addu'a, gashi nan
yanzu ya ja ma uwar tashi ai" a
haka suka karaso kofar gidan,
ba tare da Nawap ya kara tanka
mashi ba, 1k ya zaro ya mika
mashi, sannan yace "shiga ciki
kace ana sallama da Hallyn"
yana kyarma ya anshe dubun
ya fara rafka godia, sannan ya
wuce cikin gidan yana ta
murna.
A tare suka fito, yana tsaye
jikin motan ya nade
hannayenshi yana dan kalle
kalle. Tana ganinshi ta gane,
dan haka ta karaso da dan
sauri ta gaishe shi, ya ansa
fuskanshi sake, cikin zakuwa
ta fara tambayar "ya wajen su
Deedo? Tana lafia?" Murmushin
shi mai tsada ya saki, yace
"tana nan lafia lau, nazo ansan
mata result dinta nema, tace na
biyo nace tana gaishe ki, kuma
na baki number ta" a dai dai
lokacin ya duka cikin motan ya
samo wata yar paper ya rubuta
mata number, ya dago ya mika
mata.
Hannu biyu tasa ta ansa tana
ta washe baki, ta san ko
bakomai, Deedo tana cikin jin
dadi tunda gashi har waya gare
ta. Godia tai mashi, sannan ta
juya zata koma ciki, kudi ya
ciro ya bata, amma taki ansa,
dakyar ya samu ta ansa, yai
mata sallama ya shige motan
ya bar kofan gidan.
Sai da ya hau titi sosai, ya fara
tafia, sannan ya jawo wayanshi
da niyyar kiran Ummi don ya
shaida mata ya taho, missed
calls din Aysha ya gani kusan
guda 5. Wani mugun tsaki ya
jaa, inda a lokaci guda kuma
yayi wurgi da wayan a seat din
dake kusa dashi..
BA’A SHAN
ZUMA…
57,58,59&60
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Gudu sosai ya cigaba da yi
kaman wanda zai tashi sama,
ya rasa abinda ke mashi dadi,
gurin shi daya, ya saita
idanunshi kan yar kanwarshi
wadda yake ta faman tunani da
son jin muryanta.
Ba shi ya shiga Kaduna ba sai
wurin karfe biyar da rabi na
yamma, dan haka bai tsaya
bata lokaci ba, gida straight ya
wuce ko dan ya samu natsuwar
zuciyanshi.
Da sauri mai gadi ya bude
mashi bakin gate din, inda a
lokaci guda ya tura kan
motarshi ciki, mikewa yayi
sosai da niyyar ya samu wurin
parking, amma numfashinsa ne
ke shirin daukewa lokacin da
ya hango ta zaune saman
wasu fararen kujeru. A gabanta
wani dan table ne fari, tana
sanye da bakin skinny jeans da
wata red din t-shirt mai dan
tsawo, saman kanta wani royal
blue din veil ne, tayi daurin
torchlight..
Kunnuwanta makale da
earpiece, ta dora kafanta
saman table din dake gabanta,
idanuwanta a lumshe, da alama
wakar da take sauraro tana
shigarta yadda ya kamata.
Wani gwauron numfashi
Nawap ya ja, a lokaci guda
kuma ya fara yan kalle kalle,
daga gefe ya hango Idi dake ta
faman gyaran flowers din shi,
can gefe kuma Mal. Habu
driver ne zaune yana sauraron
radio.
Wani mugun abune ya ji ya
cakan mashi zuciya cikin dan
kankanin lokaci, yaji
numfashinshi na shirin
daukewa, tunani ya fara yi ko
Deedo ta samu tabin hankali
ne, tana ganin gardawan
mazan nan amma take zaune a
haka, lallai yau zata yaba ma
aya zakinta!
Da sauri ya balla murfin motan
ya fito, har yanzu tana nan
yadda take. Wurin da take
zaune ya dosa, bai yi wata
wata ba ya fincike earpiece din
dake kunnenta, cikin kaduwa
da razana tayi saurin bude
idonta, tana shirin artawa a
guje, ganin mutum tayi kamar
wanda aka jefo daga sama
yana ta faman huci kamar
mayunwacin zaki..
Idanuwan nan sun canja launi
zuwa jaa, yanayin data ganshi
ya bala'in firgitar da ita, dan
haka ta mike da gudu tayi
hanyar cikin gidan, mikewan da
ta yi, yaji kaman an caka
mashi kibiya a kahon
zuciyarshi, ashe da tana zaune
bakomai ya gani ba kenan,
lallai yarinyar nan zata gane
kurenta. Bai yi kasa a gwiwa
ba shima ya bi bayanta da
gudunshi. A palo ya cimmata,
kunnenta ya damka ya murda
tun karfinshi, ihu ta saka
wanda yasa Ummi karasowa
cikin palon da sauri.
Ganin halin da suke ciki yasa
tayi saurin matsawa ta warce
Deedo daga rikon da Nawap
yai mata, kallonshi take cikin
fushi, tace "malam lafiya daga
zuwan ka zaka hau dukan mun
yarinya?" Idonshi sunyi zuru
zuru sai huci yake, yace "watau
Ummi ke baki ma ga laifin da
tayi ba kenan?" Tace "me tayi
fa, ince a zaune ka sameta a
waje, ko wani abun tayi?" Kara
kallonta yayi, gyalen da ta
daura ya sabule, gashinta ya
bazo saman fuskanta, gani
yayi tayi wani mugun kyau
kamar aljanna, yadda ta rakube
a bayan Ummi tana raba ido
abin sai ya birge shi, nan da
nan yaji kunyar abinda yai
mata, Ummi ce ta katse mai
tunani da cewa "ina saurarenka
inji laifin da tayi"
Cikin borin kunya ya dan shafi
sumarshi da ta kwanta luf luf,
kallonta ya kara yi, sannan ya
dan tsuke fuska yace "kar na
kara ganin kin fita haka ba tare
da kinsa hijab ba, baki ganin
akwai gardawa a cikin gidan
ne?" Kara kallon kanta tayi, ita
dai bata ga matsalan shigan ta
ba, asali ma lokacin da ta fita
babu kowa a wajen, ba tare da
ta kara kallonshi ba tace "kayi
hakuri, ba zan kara ba" wani
murmushi ne ya kwace mashi,
bai san lokacin da yace "that's
my lil sis" Ummi kam tabe baki
tayi, tayi gaba tana banbami
"mutum daga dawowa ko
hutawa bai yi ba amma ya fara
takura mana" a haka ta shige
kitchen ta bar su nan tsaye
kaman bishiyar da aka dasa..
Dukar da kanta tayi, ta rasa
menene abinda ya kamata tayi,
shin ta tafi ko ta tsaya? Bata
yanke shawaran abinyi ba, taji
ya tako zuwa inda take, a
hankali ya fara magana yana
kallonta, har yanzu dai kanta a
kasa yake, "I'm sorry lil sis,
nayi laifi ko?" Bata ce komai
ba, sai kanta da ta girgiza
alaman a'a, murmushi ya saki
kaman tana kallonshi, yace
"kece ai baki ji, wato tunda na
tafi haka kike fita gaban masu
gadi ko?" Da sauri ta girgiza
kanta, "wlh yau ne kawai, kuma
lokacin da na fita ba kowa a
wajen.."
Yace "issokay to, kada ki kara
kinji?" Dagowa tayi, da niyyar
bashi hakuri, idanuwanshi
kyam akanta, da sauri ta juyar
da fuskanta, tace "I'm sorry,
bazan kara ba" "kalle ni" yace
da ita, ta juyo idanuwanta
masu tafiyar da imaninshi ta
dora su kan nashi, wani abu
yaji ya tsirga saman kanshi, ya
sauka har zuwa babban
yatsanshi na kafa, sai da ya
tattara natsuwar shi, sannan
yace "promise?" Wani dan
murmushi ta saki tace "promise
Yaa Nawap…"
Murmushin ya saki shima yace
"that's my dearest sis" da sauri
tana yar dariya ta juya ta ansa
foodflasks din da suke hannun
Ummi ta jera su a dinning, shi
kuma ya karasa gaban Ummin
yana dariya, yace "na sameku
lafiya Ummi?" "Lafiya lau" ta
fada a takaice, sannan ta
karasa cikin palon ta zauna
saman 3seater, nan ma kara
biyo ta yayi ya zauna a
gefenta, yace "Ummi duk
gajiyan da nasha na kula baki
murnan zuwana ma" juyowa
tayi ta kalle shi tace "ina fa
zanyi murnan zuwanka, kazo
ka hau mun 'ya da jibga"
"Ayi hakuri Ummi, bazan kara
ba, kuma ma har mun shirya
da 'yar taki fa" kallon Deedo
tayi wadda take jera plates,
tace "wai haka auta?"
Murmushi tayi, tace "haka ne
Ummi" sai a sannan Ummi ta
sake, suka cigaba da firansu,
inda daga bisani ya mike ya
wuce side din shi, dan ya
samu yayi wanka, ya sauke
sallolin da suke kanshi..
Shiryawa yayi tsab cikin
kananun kaya, black jeans nd
white t-shirt, kirarshi ta fito
sosai, hannunshi daure da
makekiyar agogo mai tambarin
GUESS anyi mata ado da
stones din diamond, kafarshi
daure da bakaken sneakers.
Sumar nan tayi kwance luf sai
sheki take, a haka ya karaso
cikin palon, hannunshi rike da
doguwar envelope kalar ruwan
kasa.
Saman dinning ya karasa, nan
ya ja kujera ya zauna, sannan
ya dubi Deedo yace "taimaka
mun da abinci" ba tare da tace
komai ba, ta mike tayi serving
dinshi, ta mika mashi, duk
abinda take idonshi a kanta ko
kyaftawa baya yi, murmushi ya
sakan mata yace "thanks my lil
sis" itama murmushin tayi, ta
koma ta zauna ta cigaba da cin
abincinta. Envelope din da ya
shigo da shi ya mika ma
Ummi, yace "kinga rashin
kokarin da autarki tayi" ya
fuske ya ci gaba da kwasar
abincinshi. Ummi bata ce
komai ba ta ansa ta aje a
gefenta, saida suka gama cin
abincin sannan ta buda, ga
mamakin ta, taga ko C babu a
result din Deedo, daga A sai B,
da murmushinta ta mika mata,
ta kalli Nawap tace "ai dama
nasan auta ta ba daga nan ba"
inda ta kai dubanta kan Deedo
tace "you deserve to be a
Doctor my dear, Allah yi maki
albarka ya sanya alkairi a
rayuwanki"
Wani mugun farin ciki ne ya
lullube Deedo wanda yasa ta
fara hawayen jin dadi, ta dade
tana neman wanda zai na
appreciating dinta a duk
lokacin da tayi wani abun
kwarai, Allah mai iko yau itace
ake sama albarka saboda ta
samu sakamako mai kyau, bata
ma san da bakin da zatai ma
Ummi godiya ba. Mikewa tayi
ta fada jikinta, tana kukan farin
ciki, Ummi ma kwalla ne suka
yayyafo mata, tasa hannu ta
share, tace "ya isa haka, bana
son kukan nan kina jina"
murmushi ta saki ga kuma
hawaye na bin fuskanta,
sannan ta fara daga kanta
alaman baza ta kara kukan ba.
Nawap dake gefe kallon su
yake yana mai jin wani farin
ciki na yawo a jikinshi, dan
haka ya tako zuwa inda suke,
Deedo ya kalla yace "lil sis
shirya ki raka ni unguwa" cikin
zakuwa ta mike ta haye sama,
inda Ummi ta kalleshi tace "ina
zaka kai mun ita kuma muna
tsaka da jin dadin mu?"
Murmushi yayi, yace "zamuje
duba jamb dinta ne Ummi" tace
"aiho, na zata yawo zaka kai
mun ita ai" a haka Deedo ta
sauko sanye da bakar abaya
yar Dubai, ta tattara gashinta a
tsakiyar kanta ta daure, sannan
tayi rolling gyalen abayan,
kafanta sanye da bakin plat
shoe na Gucci, sai wani kanshi
mai dadi yake tashi a jikinta.
Ido Nawap ya kura mata kamar
zai cinye ta, ya rasa mai yasa
yake ganin kyaun yarinyar
yanzu, wanda shi a da bai taba
sanin tana da shi ba, gashi ta
wani goge ta waye kaman
wadda ta shekara goma a
birni. Karasowa tayi cikin palon
tace "Ummi zamu tafi" "sai kun
dawo auta" Ummi ta fada, ta
juyo tana "Yaa Nawap na
shirya fa" nan taga yadda ya
ware idanunshi yana kallonta
kaman bai santa ba. Basarwa
yayi, yace "muje mana" inda
yayi gaba tana bin shi a baya.
Zaune take a gefenshi, shi
kuma yana seat din driver,
sunyi bala'in kyau abin ba'a
cewa komai. Dai dai lokacin
da yake kokarin fita gate din
gidan, motar Aysha ta kunno
kai, ganin Nawap tare da wata,
yasa ta saki wani uban full
light wanda ya kashe masu
idanu gaba dayansu..
BA’A SHAN
ZUMA… 61, 62
&63
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cikin kankanin lokaci idanuwan
nan suka juya, suka sauya
launi daga fari zuwa jaa, da
sauri zuciyarshi take harbawa,
Deedo da take zaune a gefe
hankalinta yayi kololuwa wurin
tashi, a tunaninta wani mugun
abun ne ya faru ganin mood
din Nawap ya canja lokaci
guda.
A zuciye ya balla murfin motan
ya fita, inda a hankali Aysha ta
fara rage full light din da tayi,
cikin isa da gadara itama ta
buda murfin tata motan ta fito,
sannu a hankali ta fara takowa
zuwa inda yake.
Kallonta yayi cikin tsananin
bakin ciki yace "so it's yu?"
Murmushi ta saki mai tattare
da rainin hankali, ta nade
hannuwanta, ta jingine jikin
motarshi, sannan ta kalleshi
tace "yup, it's me" wata
muguwar harara ya watsa mata,
sannan ya juyar da kanshi
yace "dame kike son a kira
sunan abinda kika yi?"
Murmushi ta kara saki, tace
"duk abinda ka kira shi" sai da
ya dai dai ta tsayuwanshi, yayi
facing dinta yadda ya kamata,
sannan yace "Aysha abinda
kike shirme ne, kauyanci ne,
kuma rashin wayewa ne! I told
yu ki fita hanya ta, otherwise
zaki gane kurenki, dan na lura
abin naki na neman ya zama
raini, ni bana ciki da rainin
hankalinki.. "
Wata kibiyar bakin ciki ce tayi
suka ta caki zuciyar Aysha,
kallonshi kawai take don ta
rasa ta cewa, babban bakin
cikinta shine Deedo tana
sauraren duk abinda sukeyi,
kasancewar a bude ya bar
motan, wasu yan kwalla suka
yayyafo mata, juyawa tayi cikin
salo na gogaggun yan mata ta
dan share, a lokaci guda kuma
ta cigabada kallon Nawap tana
dan murmushi, sannu a hankali
ta taka zuwa gabanshi tace
"Nawap sonka a cikin jinina
yake, dashi nake rayuwa, idan
har kana tunanin akwai ranar
da zan daina sonka, to ka tafka
babban kuskure, domin da
sonka nake numfashi, da shi
nake kwana da shi kuma nake
tashi a ko wacce safiya,
harkanka kuma da kake
magana, yanzu na fara
shigarta, dan haka mu zuba
nida kai.. "
Juyawa tayi da sauri da niyyar
ta shige motan ta, hannunta ya
finciko tun karfi, ta dawo da
baya, kallonta yayi ido cikin ido
yace "idan mafarki kike gara ki
farka Aysha, domin bakya jerin
kalar matan da zan iya so a
rayuwata, baki da quality kwara
daya da zan iya so a wurin
mace, sannan kuma rashin
kunya na daya daga cikin
abubuwan da nafi komai tsana
a tsarin rayuwata, dan haka ki
natsu, ki gane cewa ruwa ba
sa'an kwando bane!" Yayi
wurgi da hannun sannan ya
koma ya shige motan, yayi
reverse ya koma cikin gidan.
Wani tiririn bakin ciki ne ya
cigaba da fita daga zuciyan
Aysha, kallon motan tayi, inda
wasu hawayen bakin ciki suka
gangaro saman fuskanta, a
hankali ta furta "zaka san ka
wulakanta ni Nawap, ba dai
akan wannan tsinanniyar
yarinyar bane kake yi mun
abinda kaga dama, wallahi sai
tayi dana sanin shigowa
gonata da tayi" dakyar ta ja
kafanta ta koma cikin motan,
gidan da bata shiga ba kenan,
domin jin zuciyanta take
kaman ana tafasa ruwan zafi a
ciki.
Parking Nawap yayi, ya juyo ya
kalla Deedo wadda itama shi
din take kallo, ji yayi tamkar an
zuba mashi ruwan sanyi,
kyawawan idanunta kadai, sun
tafiyar da kunci da bakin cikin
da yake ciki, murmushi ya
sakan mata, wanda na tabbata
bai san lokacin da ya subuce
mashi ba, a hankali yace "ki
shiga ciki, da safe zan je na
duba maki jamb din kinji?" Ba
tare da tace wani abu ba, ta
buda motan ta fita, shi kuma
ya bita da idanu har sai da ta
shige ciki.
Ummi ta samu zaune tana
kallon Sunnah T.V da
murnarta, tace "ba dai har kun
dawo ba?" Sai da ta zauna,
sannan tace "bamu je bama,
yace da safe zai je ya duba
mun, wai dare yayi" tace "ba
laifi ai, Allah yasa dai muga
alkairi " "amin" ta fada, sannan
ta mike ta haye sama, zuciyarta
fal da tunanin wannan bala'i
irin na Aysha. Namiji yace
baya son ki amma ke kin nane
mashi sai kace mayya! A fili ta
furta "Allah dai ya kyauta
wannan rayuwar wahalar."
Alwala tayi sannan ta gabatar
da sallan isha'i, tana gamawa
ta cire kayan ta da niyyar shiga
wanka, wayanta ne ya fara ruri,
karasawa tayi inda wayan take
taga bakuwan number, da
sallama ta daga wayan ta kara
a kunnenta, daga dayan
bangaren taji ance "dan Allah
ina neman Deedo ne" wani
mugun dadi ne ya ziyarci
zuciyanta, domin ko a mafarki,
baza ta taba manta mai
wannan muryan ba.
Nan da nan suka barke da fira
ita da Hally, ba tare da bata
lokaci ba ta zayyana mata
dangantakar dake tsakaninta
da Ummin Nawap, ta kuma
bata labarin result dinta da
yadda rayuwa ke tafiyan mata
cikin jin dadi.
Murna sosai Hally tayi, ta kara
da cewar "mahakurci mawadaci
Deedo, dama ai haka rayuwa
take, idan wani ya kika wani
zai so ka" da haka suka yi
sallama, inda Deedo tai mata
alkawarin kiran ta da safe in
sha Allah
Nawap ya dade zaune cikin
motan yana tunanin abinda ya
faru kaman a mafarki, daga
karshe dai ya fito ya shiga
palon bai ga Deedo ba sai
Ummi kawai a zaune, kunnuwa
ya baza yana sauraren yaji
abinda zata ce game da abinda
ya faru tsakaninsu da Aysha
amma yaji tsit, don a
tunaninshi ko Deedo ta fada
mata. Haka ya karaci zaman
shi, inda daga bisani ya mike
yayi mata sai da safe ya wuce
side dinshi.
Da safe kamar yadda yayi
alkawari, haka ya fita around
10, cafe din da yayi mata
registration ya nufa ya siya
scratch card ya duba mata, yaji
dadi sosai ganin ta ci kusan
250, bai bata lokaci ba yayi
printing result din ya fito,
straight KASU (Kaduna State
University) ya wuce, gaban
faculty of medicine yayi
parking, sannan ya ciro
wayanshi ya kira wata number.
Cikin yan mintuna wani
matashi wanda shekarunshi
basu wuce 30 ba ya fito ya
karaso gaban motan Nawap.
Fitowa yayi, ya mika mashi
hannu suka gaisa, sannan
suka jera zuwa cikin faculty
din. Office din mutamin da naji
ya kira da Kashim Yarima suka
nufa, bayan sun gaisa ne
Kashim ke ce mashi "wlh baka
da kirki Nawap, zumuncinka
yayi karanci ko?" Nawap yace
"kasan abubuwa sai a hankali,
yanzu ma wata sis dita ce
nazo yima follow-up, ta cika
nan skool din ban sani ba ko
zaku dauketa"
Dariya Kashim yayi, yace "me
zai hana indai nan din ta cika,
kuma tana da abubuwan da
muke bukata, zuwa end of this
month ma zamu fitar da 1st
list na admission in sha Allah"
Nawap yace "plz kayi mun
kokari, komai tana dashi,
medicine take son karantawa,
dan Allah kar ku bata course
din da ba shi take so ba" ya
kara da "bara na baka sunanta
idan kun fitar da admission din
sai ka duba mun please" wata
paper ya mika mashi ya rubuta
details din Deedo ya bashi,
sannan sukai sallama, inda yai
mashi alkawarin kiran shi da
zaran sun fitar da list din..
BA’A SHAN
ZUMA… 64, 65
&66
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Yana karasawa gida wanka
yayi yanufi masallaci, bayan ya
fito ne yashigo cikin gida anan
ya ga feedo kwance akan
doguwan kujera, sanye take da
riga da wando, kanta ba
dankwali ta tattare gashin ta
baya ta daure, sai da ya kare
mata kallo kafin yayi sallama,
da sauri ta mike ta zauna tana
kokarin nemo hulanta wanda
dama ya fadi ne ta baya, "ina
wuni"tace dashi, ya ansa, ya
kauda kansa sannan yace "ki
shirya gobe muje in kaiki
saloon" ta ce "toh, dama dazu
ummi ta gama maganan" ruwa
ya dauka a fridge sannan ya
fice.
Washegari karfe goma ta
shirya tsaf tana jiransa, yazo
suka gaysa da ummi inda ya
mata bayanin cewa yaje
maganan admission din Deedo,
taji dadi sosai sannan yace
Deedo ta fito su wuce, ta shiga
motan sannan ta rufo, yajasu
suka fice, bai tambayeta inda
zai kaita ba kawai taga ya nufi
wani saloon da ita, Tripple D
Beauty and Care saloon taga
an rubuta, saloon din ya hadu
sosai domin babu abinda basa
yi ajikin board din takaranta,
nan ya ciro dubu biyar ya mika
mata tare da cewa "inkin gama
ki kirani"
shigewa saloon din tayi,
tasamu mutane biyu agabanta
don haka tazauna jira, har
akazo kanta, anwanke mata kai
ana kokarin sata a dryer saiga
Aysha da kawarta sunshigo, da
farko murmushi take tana
dariya, ganin Deedo yasa ta
dauke annurin fuskanta tamkar
taga malaikan mutuwa, taja
wani mummunan tsaki sannan
tanemi gu tazauna, hankalin
mutane ya nufi kanta jin tsakin
da tayi, Deedo ma ganinta yasa
tagane da itane, anma
kasancewar tasan ta girmeta,
sai bata nuna alaman ta ji
bama, nan ta ce "ina wuni?"
Bata amsa ta ba, hakan yasa
itama ta kauda kanta, kawarta
ce take kokarin cemata ana
mata magana, nan cikin fadin
rai da iko tace "itace
munafukan danake miki
bayani" habawa tuni kawar ma
ta daure fuska "awh! Ai sai kice
min ga snatcher, lallaima ina
zaki kai wannan abun?"
"Tayani ji dai inbanda namiji
da ruwan ido da rashin sanin
daidai, Allah wadaran tsiya inji
arziki" Deedo duk tana jinsu
bata tanka ba, hatta yan saloon
din ma kowa dai yayi shiru ne
don yadda suke maganan zai
tabbatar dacewa da dayansu
akeyi
Aysha takalli kawar ta sannan
tace "kinsan wani abu ma
kuwa?"
"A a saikin fada"
"Ita fa take binshi, sai
shishigewa take, matsiyaciya
tazo tashiga arziki, ta kainane,
a zatonta yatsu tsayinsu daya,
dontaga ita yar uwa ce"
Kawar ta tabe baki sannan tace
"ji munafukar kamar ba da ita
ake ba" kafin Aysha ta amsa
tanufi kan Deedo taja gashinta
, matan ta fara bada hakuri
yayin da Deedo tamike tare da
cewa "kuyi hakuri, anma duk
abunda kuke fada bahaka
bane" bata idar ba taji anwanke
ta da mari, hannu tasa tarike
fuskan alokacin yan saloon din
suka mimmike don kawowa
mata agaji, tuni Aysha da
kawaarta suka hau dukan
Deedo har sai da suka yaga
mata riga.
Wayanta taciro da kyar takira
Nawap, batayi magana ba yana
kokarin cewa hello yaji
hayaniya yayi yawa, dama baiyi
nisa ba nan da nan yajuyo
yataho, yana isowa ya bude
kofan motan ya manta baima
kulle ba yashiga saloon din
ganin Aysha da Deedo ko baa
fada masa ba yasan abunda
suka aikata mata tunda ga
riganta ayage tana kokarin rufe
jikinta, idonshi tuni ya canja
kala yayi jajur ya kalli mai
saloon din tare da cewa "meya
faru?" Ta mayar masa da komi
kamar yadda ya faru, alokacin
yaji kamar ya shako Aysha ya
kashe don bakin ciki, ya ruko
Deedo ya sanyata a mota bai
ce komi wa Aysha ba wacce
jikinta sai bari yake,
Rufo motan yayi yabawa mai
saloon kudinta sannan ya tuka
suka fice, kuka take tayi anma
yarasa ta yadda zai fara bata
hakuri, danne zuciyansa yayi
tareda cewa "kiyi hakuri duk
abunda ke faruwa saboda ni
ne, Aysha tadauka nemanki
nakeyi, kiyi hakuri ahankali
zata gane gaskiya" bata ce
komi ba har suka isa, tuni
tabude motan tashige gida,
daki tanufa saboda ta canja
kaya, Nawap kuma yana
tunanin abunda zaifada idan
Ummi ta tambayeshi meya faru,
duk da yasan Deedo zata fada.
Bai shiga gidan ba sai dare
inda yaga Deedo sai dariya
take suna tadi da Ummi, kuma
da ya zauna baiga sauyi ba
don anhada dashi ana tadin,
nan ya tabbatar da cewa Deedo
bata sanar da ummi abunda
yafaru ba. Cikin zuciyanshi
mamaki yake ita wace irin
yarinya ce, bai ce komai ba,
haka ya daure ana dan tadi
dashi, daga bisani ya mike ya
wuce part dinshi inda ya
cigaba da tunanin abun da zai
yi ma Aysha ko dan ta fita
hanyarsa..
Ranan da zai koma Abuja ya
gama shirinsa tsab, ya saka
kayanshi a mota, ya shiga cikin
gidan yayi ma Ummi sallama,
amma bai ga Deedo ba, fitowa
yayi zai wuce, a dai dai nan ya
hade da ita zata shiga kofan
palon, hannunta ya jawo suka
bar wurin zuwa bakin
motanshi, yana kallon kwayan
idonta yace "ni zan wuce lil
sis, ba lallai ina nan admission
dinku ya fito ba, amma zan
hada ki da Dr. Kashim phrnd
dina ne, nasan zai maki komai
in sha Allah, dan haka abinda
nake so dake shine ko kinje
skool ba ruwanki da samarin
banza bata gari, wanda basu
da aikin yi sai hure ma yara
kunne, ki natsu, kiyi abinda ya
kaiki, kina jina? Nd ina mai
kara baki hakuri akan abinda
Aysha ta miki, I promise yu
hakan ba zai sake faruwa ba
kinji?"
Murmushi ta saki, tace "in sha
Allah zan cika umarninka Ya
Nawap, Allah ya tsare hanya"
ta juya zata wuce, sai ya ji
kamar kada ya tafi ya barta, da
sauri yace "baza ki jira kiga
tafiyana bama" bata ce komai
ba, sai murmushin data saki,
hannayenta ta harde, ta tsaya
tana kallonshi, hakan da tayi ya
bala'in yi mashi kyau, ba tare
da bata lokaci ba ya zaro
wayanshi, ya kyalla mata hoto,
dariya tayi, ta rufe fuskanta,
haka ya cigaba da daukanta
har sai da yaga yana niyyan
makara, sannan yace tazo, ta
matso kusa dashi, dan haka ya
daukesu tare, sunyi bala'in
kyau, sai a lokacin yaga ashe
har kama suke yi.
Ba don ya gaji da ganin Deedo
ba, yai mata sallama ya shige
mota, inda ya cigaba da
jaddadada mata cewar ta kula
da kanta, tana murmushi ta
daga mashi hannu har sai da
ya fita gate din gidan, sannan
ta shige ciki.
Yana fita, gidansu Aysha ya
zarce, a bakin gate ya hade da
ita, da alama office zata fita,
parking yayi ya fito daga motan
ya karaso gabanta. Yanayin da
ta ganshi ta san ba mutunci,
kuma dama ta dade tana jiran
wannan ranan, dan haka ta
kama kanta, ta fara raba idanu,
kaman shege a rabon gado.
Nuna ta yayi da hannunshi,
yace "this shud be last
warning, ki fita hanyar yarinyar
mutane, idan ba kina so fita
daga cikin gidanku ya gagareki
ba, na fada maki bana son ki,
to menene na yi mun
shishshigi a rayuwa, ki tsaya
matsayinki, if not, zaki ga
abinda zai biyo baya" ya juya a
fusace, yana fadin "maran
zuciya kawai" ya shige
motanshi ya bata wuta.
Aysha saboda bakin ciki bata
ce komai ba sai mazurai da
take, nan take hawaye suka
cika mata ido, kuka ta cigaba
da yi kaman an bude famfo,
cikin kunan zuciya tace "baza
a rabu da kai din ba, sai an
soka din, kuma in dai wannan
shegiyar yarinyar ce yanzu na
fara takura mata har sai wahala
tasa baza ta taba sonka ba,
wanda bai son abinda ya dace
dashi ba kawai, wannan har
wani abun so ce" ta ja tsaki ta
share hawayen, tace "bari dai
kawata ta dawo daga tafiyan
da tayi, wallahi sai mun koya
ma yarinyar can hankali" ta
jawo mirror cikin jakanta ta
gyara fuskanta, sannan ta yi
ma motar key ta bar gun..
BA’A SHAN
ZUMA… 67-69
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Haka rayuwa ta cigaba da
tafiyan ma Deedo hankalinta
kwance, bata da sauran
matsala, gashi kuma ta kan
kira Hally su sha labarin
duniya amma ko ta tambayi ya
su Goggo, Hally zata
shashantar da maganar bata
ma son ko kadan Deedo na
tunawa da Goggo, yau ma
kwance take a daki suna waya
da Hally take ce mata ta samu
admission a ATBU, har ma ta
fara registration, Deedo ta mata
murna sosai, inda take
tambayar "ya maganan naku
admission din?" "Muna kan jira
muma, in sha Allah" "Allah ya
taimaka" ta fada, haka suka
cigaba da tadinsu cikin jin
dadi, daga karshe tai mata
sallama ta mike, domin gabatar
da sallahn azahar.
Bayan ta gama sallah tana
zaune kan sallaya taji wayanta
yayi kara, ta dauko ta duba,
email ne ya shigo daga KASU,
sun bata admission a faculty
of Medicine and Surgery.
Murna sosai take yi, da gudu
ta mike da niyyar zuwa dakin
Ummi, wayan Yaa Nawap ce ta
katse mata hanzari, cikin sauri
ta daga wayan tare da gaishe
shi cikin zakuwa, shiru yayi
yana imagining farin cikin da
take ciki, nan da nan ya ji
inama yana da iko da sai dai
su ganshi a gida kawai.
Murmushi yayi yayin da ta
katse mashi tunani ta hanyar
cewa "Yaa Nawap dama yanzu
zamu kira ka" "ni da na fi
damuwa daku ai gashi na riga
ku kira, kuma da babban
albishir na zo"
Cikin zakuwa tace "nima
albishir ne zan maka, amma ka
fara fada mun naka 1st"
murmusawa yayi, yadda take
maganar duk ta tafi mashi da
wata kasala da yake tare da ita,
idonshi a lumshe, yana juyawa
a kujerar office dinshi, yace
"yanzu Dr. Kashim yai mun text
sun baki admission" murmushi
ta saki mai taushi, kaman yana
gabanta, tace "shine albishir
din da zan maka nima, yanzu
email ya shigo mun"
"congratulations, sai ki shirya
on monday, kuje tare da driver,
zan hada ki da Dr. Kashim ki
fara registration ko" "nagode
Yaa Nawap Allah ya saka da
alkairi" "issokay" ya fada, inda
a lokaci guda yai mata sallama
ya koma bakin aikinshi.
Dakin Ummi ta wuce da
murnarta ta shaida mata yadda
sukai da Nawap, Ummi ta
rungume ta suna ta jin
dadinsu, tace "tashi mu wuce
kasuwa, ai zama bai ganni ba
auta zata tafi jami'a" murmushi
tare da hawayen farin ciki ne
suka gangaro a fuskar Deedo,
ta share, sannan ta mike ta
wuce daki ta fara shiri.
Siyayya sosai Ummi tayi ma
Deedo, dangin kayan sawa,
takalma, jakunkuna da sauran
tarkace na 'yan matan jami'a. A
gajiye liss suka dawo gidan
wurin karfe biyar na yamma,
wanka tayi, tayi sallah, sannan
ta gangaro palon don ta samu
damar hutawa, Ummi ta tadda
tana bude kayan da suka siyo,
inda ta zauna itama suka
cigaba da budawa tare, daga
karshe Ummi tayi ma tailansu
waya, domin yazo ya anshi
kayan dinki.
* **
A daddafe Nawap yake rayuwa
a garin Abuja don wani
matsanancin kewar Deedo da
ke damunshi, wadda ya rasa
tantance ko menene dalilin.
Pictures dinta kawai yake kallo
ya samu natsuwa cikin ranshi.
Ga aiki ya sakashi gaba sosai,
bashi da wani lokaci balle yayi
tunanin samun damar zuwa ya
ganta.
Da misalin karfe biyar na
asubar ranar litinin, wadda tayi
dai dai da daya ga watan
February, 2016 (1st Feb, 2016)
Deedo ta tashi, wanka tayi,
sannan ta doro alwala ta fito.
Sallah tayi, ta zauna a wurin ta
cigaba da azkar har wurin karfe
bakwai na safe, daga bisani
tayi addu'ar neman sa'a a
karatunta, da kuma rayuwarta,
ta kara da neman tsari daga
dukkan wani sharri na rayuwa.
Daga karshe tai ma Ummi
addu'ar da ta saba, sannan ta
nema ma iyayenta gafara a
wurin mai kowa mai komai.
Gaban dressing mirror ta isa ta
shafa mai tare da designers
din turarukan da suke zube a
wurin, simple make up tayi,
sannan ta matsa gaban
wardrobe din ta buda tana
tunanin wane kaya ya dace ta
saka a wannan farar rana.
Wata super java ta dauko, mai
kalar light orange nd purple,
dinkin skirt nd blouse ta saka,
wasu round dankunnen ta
sanya masu kalar gold, ta
daure hannunta da agogon
Vintage, itama dai kalar gold
din ce, bracelets ta sanya a
dayan hannunta na hagu,
sannan ta dora zobuna na
isassun yan mata, wanda duk a
cikin siyayyar da Ummi tayi
mata suka siyo da su.
Lafiyayyan daurin yan zamani
tayi, sannan ta jawo gyalenta
purple, takalmanta da handbag
dinta kirar Jimmy Choo wanda
suka kasance reddish brown,
ta sanya, ta dauko handbag
din, ta kara feshe jikinta da
turaruka na alfarma, sannan ta
fito. Karfe tara lokacin har da
minti biyar, dakin Ummi ta
shige, inda ta same ta tana
breakfast. Dukawa tayi har
kasa ta gaisheta, Ummi kam
binta tayi da kallon mamaki,
anya wannan autarta ce? Da
murmushinta ta ansa, tace
"wannan duk kyau ne Deedo?"
Kanta a kasa tana dan
murmushi, ta zauna kusa da
Ummi ta fara hada tea.
A gurguje tayi breakfast din ta
gama, Ummi dai sai yaba kyau
da gayun Deedo take, bayan ta
gama fitar da kwanukan, ta
dawo tayi ma Ummi sallama,
inda tayi mata nasiha mai ratsa
jiki kan ta kula da mutuncinta,
ta kuma tsare martabar
gidansu. A haka suka sauko
palon tare da Ummi, ta dauka
kudi ta bata, sannan tayi kiran
driver, tace ya kaita skool, idan
ta gama sai tayi waya, yaje ya
daukota. Cikin zakuwa ta
rungume Ummi, tayi mata bye,
ta wuce ta shige motan.
Tana shiga wayan Nawap ya
shigo, da murnarta ta daga ta
gaishe da shi, sai da yaja
numfashi, sannan ya ansa,
tambayarta ya fara "kin shirya
ne?" Tace "gamu zamu tafi
ma" yace "ina fatan dai bakiyi
wani kwalliya ba, dan karatu
zakije ba fashion parade ba"
murmusawa tayi, sannan ta
kalla mirrorn gaban motan,
tace "ban yi ba fa Yaa Nawap"
yace "idan kina son na yadda
ki mun snapping kanki, ki tura
mun ta whatsapp yanzu" "to"
kawai ta fada, yai mata bayanin
yadda zata ga Dr. Kashim, dan
shine zai mata komai ya kuma
hada ta da wannan zai taimaka
mata wurin registration. Daga
karshe cikin wata irin murya
mai sanyi yace "I wish ina tare
dake a irin wannan ranar lil
sis" kasa magana tayi, saboda
yanayin da yayi maganan bata
san ya zata fassara shi ba,
murmushi kawai tayi, tace
"thanks for everything Yaa
Nawap, sai na kira idan naje
skool din" ta kashe wayan
lokaci guda, sannan ta dauka
selfie ta kunna datan ta tura
mashi, tayi bala'in kyau kamar
aljana, ta kashe datan ta jefa
wayan cikin jaka.
Suna shiga office din Dr
Kashim ta nufa direct, ko da
bata fada mashi ba ya san ita
ce sister Dr. Nawap, saboda
asalin kamar da yaga suna yi.
Gaishe dashi tayi, sannan ta
samu wuri ta zauna, bayan ya
ansa, yace "Firdausi, ryt?" "Yes
Sir" ta fada, yace "ina fatan
kinzo da credentials dinki baki
daya?" "Eh na zo da komai" "ok,
lemme call someone who will
assist yu" "Ok Sir" ta fada,
yayin da ta dukar da kanta, ta
cigaba da wasa da 'yan yatsun
hannunta.
Wayanshi ya dauka ya kira
wani, yace ya sameshi a office
yanzu. Cikin mintunan da basu
wuce sha biyar ba, aka turo
kofar office din aka shigo,
kanshin wani lafiyayyan turare
ya daki hancin Deedo inda a
lokaci guda taji zuciyarta ta
buga da karfi, kafarshi ta fara
kallo ta ganta lullube cikin
lafiyayyun sneakers black nd
white kirar Tommy Takkies, a
hankali take dago kanta, sanye
yake da bakin pencil jeans, da
white t-shirt ta Ralph Lauren,
hannunshi daure da agogon
fata baka kirar Orlando, kasa
dauke idonta tayi lokacin da ta
yi arba da kyakkyawar
fuskarshi, gashin kanshi ya
kwanta luf, sai kyalli yake
kaman na jarirai, kallonshi take
kaman yau ne rana ta farko da
ta fara ganin bil adama.
Kallonta yake shima, inda cikin
zuciyarshi yake nanata "tsarki
ya tabbata ga Allah, ubangijin
da ya tsara wannan kyakkyawar
halitta!" Murmushi ne ya
subuce mashi, inda itama a
lokaci guda ta sakan mashi
nata kayataccen murmushin…
BA’A SHAN
ZUMA… 70-72
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Dr. Kashim ne ya katse su da
cewa "yawwa Affan ka zo ne?
Karaso ciki mana" cikin jin
kunya ya dan shafi sumarshi
ya karasa cikin office din ya
mika gaisuwarshi ga Dr.
Kashim, inda shi kuma a
hankali kwance ya ansa, ba
tare da ya dago ba, ya cigaba
da typing din da yake akan
laptop dinshi.
Kujeran da ke kallon ta Deedo
ya zauna, kura mata ido yayi,
inda a bangarenta itama ta
kasa tantance dalilin da yasa
take jin dadin kallon da yake
mata.
Dr. Kashim ya dago daga
kallon laptop din gabanshi,
yace "yawwa, Affan plz, wani
taimako za kai mun dan Allah"
ya maida dubanshi ga Dr. Yace
"na me fa? Hope dai ba aike
bane, cuz ina da class karfe
sha biyu" ya fada yana duban
kayataccen agogon hannunshi.
Dr. Yace "kai fa problem dina
da kai kenan, ka cika laziness
kaman, mace" murmushi Affan
yayi, ba tare da yace komai ba,
inda Dr. ya cigaba da magana..
"Wannan sister phrnd dina ce,
tazo registration ne, nd as yu
can see bani da time da zanyi
guiding dinta, kuma ba zai
yiwu na hada ta da Secretary
dina ba, plz ka taimaka mata
komai da za'a bukata tana
dashi, zaku je kuyi clearance
ku ansa admission, then sai ku
fara reg, plz my Lil bro" ya fada
yana kallonshi, inda shi kuma
ya dan dage giranshi tare da
kafada irin na big boys, yace
"alright then, I'll try my best"
sannan ya mike, ya cigaba da
kallon Deedo, yace "let's go
beautiful" murmushi tayi kawai,
ta mike ta yi wa Dr. godiya,
sannan ta fita.
Dr. Kashim ne ya kwala ma
Affan kira a yayin da yake
kokarin bin bayan Deedo, yace
"plz, ka kula da yarinyar nan,
amanan Dr. Nawap ne kana ji
na?" Juyawa yayi yana dan
bouncing yace "have no probz
bro.." yana dariya ya bar office
din, Dr. Ya girgiza kanshi,
sannan cikin zuciyarshi yace
"Affan the trouble maker"
Tare da taimakon Affan Deedo
ta kammala clearance dinta
tsab, ta anshi admission letter
dinta. Bayan sun fito ne tayi
deciding kiran Nawap ta fada
mashi, nan ta ci karo da 3
missed calls dinshi, sai da ta
duba taga ashe wayan silent ta
shiga lokacin da ta jefa ta cikin
jaka. Da sauri ta fara kiran
number har kuma ta katse bai
dauka ba, ta kara kira a karo na
biyu, nan ma shiru kake ji. Ba
tare da wata damuwa ba ta
maida wayan cikin jaka,
sannan ta cigaba da yan kalle
kallen yadda students suke
shawaginsu hankali kwance.
"Hey beautiful" taji an fada
cikin muryar nan tashi mai
dadin sauraro. Juyowa tayi
dauke da murmushi ba tare da
tace komai ba. Ya karaso ya
zuba mata idanu, sannan yace
"zamu je inyi lecture, idan na
fito sai muyi wani abun, zuwa
gobe kuma sai mu karasa ko?"
Ya fada yana mai cigaba da
kallon kyakkyawar fuskarta.
Bata iya yi mashi gardama ba,
dan haka suka mika zuwa
wurin da yayi parking suka
shige motan, sannan ya fara
k'ok'arin tadawa.
Bayan sun shiga motan sun
zauna ne, har ya tada, amma
sai bai tafi ba, kallonshi tayi
tare da alamar tambaya, nan ta
ci karo da shanyayyun
idanuwanshi na aiko mata wani
sako wanda har sai da
zuciyarta ta buga lokaci guda.
Dakyar ta daure tace "muje
mana" cikin wata irin murya ya
langab'ar da kanshi yace
"Feedo I can't hold it, to be
honest, you're beautiful nd
you've a beautiful smile too"
murmushi ne ya kwace mata,
inda tasa gyalenta ta dan rufe
fuskanta, a hankali ya furta
"OMG look at ha dimples, I love
them" ya dan ciji leb'enshi,
sannan ya daure yayi ma
motan key suka bar wurin.
Zaune take a gefenshi, inda ya
tattara hankalinshi gaba daya
yana kallonta ba tare da sanin
ta ba, kasancewar hankalinta
na kan game din da take yi a
wayanta. Wasu phrnds dinshi
ke ta tambayar inda ya samo
ta, amma yana ta basarwa, shi
a dole kada su samu fuskan yi
mata magana.
WANENE AFFAN?
Affan Taufiq, matashi ne mai
shekaru ashirin da biyar a
duniya, namiji dan gayu wanda
ya saba da hutu mai asalin zati
da kwarjini a wurin jama'a.
Kyakkyawa ne dai dai misali,
sai dai yana da wasu idanuwa
masu haske da walk'iya wanda
sune suke rikita duk wata
mace da tayi arba da kallonshi.
Iyayenshi Alh. Taufiq, da Haj.
Maryam yan asalin garin
mak'arfi ne ta jihar Kaduna,
amma Allah yayi masu rasuwa
tun Affan yana shekara goma a
duniya, wannan yasa rik'onshi
ya dawo hannun yayan
mahaifinshi, wato Daddyn su
Dr. Kashim.
Affan ya kasance masoyin
karatun likitanci kamar Deedo
tun daga k'uruciyarshi, wannan
yasa ya zama zakaran gwajin
dafi a gaba daya department
dinsu, tun ranar da ya fara har
izuwa yanzu da yake a final
year dinshi.
* *
Misalin karfe biyar na yamma a
gajiye liss Deedo ta koma gida,
a palo ta zube inda ta tarar da
Ummi, nan ta gaisheta, cikin
yanayi na tausayawa Ummi ta
ansa, sannan tace "makaranta
ba dadi ko auta?" Murmushi
Deedo tayi tace "a hankali zan
saba Ummi" ta mike saman 2
seater, can kuma tace "Ummi
ko Yaa Nawap ya kiraki?" "A'a
bai kira ba, ya akayi ne?"
"Munyi magana kafin na isa
skool, to na manta waya na
silent ashe ya kira, na kira
kuma bai dauka ba"
Ummi tace "may be aiki yake,
idan ya gani zai kira" bata kara
cewa komai ba, ta koma ta
kwanta luf, fuskan Affan ce ke
dawo mata, yadda yake
tsokananta da yadda yake
magana, abin na bala'in birgeta
murmushi ta saki, a dai dai
lokacin kuma wayanta ya fara
ruri,hakan yayi sanadiyyar
yankewar tunaninta.
Yaa Nawap ta gani, dan haka
tayi saurin dagawa, tana
kokarin gaishe da shi, taji yace
"haka muka yi dake? Wane irin
abu ne ban fada maki ba kafin
na tafi? Haka nace ki rink'a
dressing idan zaki je skool?
Wato kin raina ni ko? Ni ban
isa ince ga yadda zakiyi ba, kin
tashi kinyi uban kwalliya kin
tafi skool, a haka zaki
karatun?"
Kyarma hannunta ya fara yi, a
karon farko kuma ta saci kallon
kujeran da Ummi ke zaune
amma bata ganta ba, cikin
murya mai alaman ta kuka tace
"I'm sorry Yaa Nawap, wallahi
banyi dan na b'ata maka ba,
bazan sake ba in sha Allah"
wata muguwar tsawa ya daka
mata wadda ta sa yan hanjinta
motsawa lokaci guda, nan da
nan hawayen da suka mak'ale
suka gangaro saman fuskarta,
ba tare da ya jira me zata ce
ba ya datse wayan, sannan
yayi wurgi da ita saman kujerar
dake gefenshi..
BA’A SHAN
ZUMA… 73-75
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Zubewa shima yayi a kujeran,
ya rasa dalilin rasa
natsuwarshi tun lokacin da ya
ci karo da pic d'in da Deedo ta
tura mashi ta whatsapp.
Zuciyarshi da take wani
tuk'uk'i yake dan bugawa a
hankali yana fadin, "why! Why
this for my lil sis?" Ya dad'e
yana k'aryata zuciyarshi akan
abinda take fada mashi, amma
ina, ya riga ya gama yardan ma
kanshi cewa yana cikin yanayi
na soyayya! Soyayyar ma mai
mugun tsanani, wadda take
tattare da wani mugun kishi
wanda har ya kan rasa inda zai
tsoma ranshi a duk lokacin da
ta taso mashi.
Cikin k'unar zuciya ya furta "I
love yu Deedo, why can't yu
understand? Me sa baza ki
kulan mun da kanki ba? Me sa
kike neman halaka ni da
soyayyarki" ba tare da ya
tantance ba ya ji wata zufa ta
karyo mashi duk kuwa da A.C
dake palon, babu abinda yake
tunani sai hanyar da zai je
Kaduna, tunanin Deedo tare da
son ganinta yana bala'in
azabtar da shi da rayuwarshi.
Kuka sosai Deedo ta cigaba da
yi, ta rasa wannan wace irin
rayuwa ce, ace a matsayinta na
mace kuma 'yar jami'a amma
bata da wani 'yanci nata na
kanta? Tana tunanin tun da ta
bar gidan Goggo tayi
bankwana da bak'in ciki, ashe
ba haka abun yake ba, mutum
baya nan ma amma ya sama
rayuwarta ido, shin wai ya yake
so tayi ne? Jin alamar mutum
na tunkaro palon daga hanyar
kitchen yasa tayi saurin
mikewa ta haye sama, Jan
gado ta fada ta cigaba da rera
kukanta inda a zuciyarta tana
fadin baza ta k'ara bashi
hak'uri ba, tunda dai ba wani
abu tayi ba.
Ta k'ara da cewar "kuma
abinda nake in ba mai kyau
bane ai Ummi baza ta barni
nayi ba, dan haka taje can ta
matse mashi mutum sai fad'an
tsiya" a haka har aka kira
maghriba, sannan ta mik'e ta
shige toilet ta d'oro alwala.
Tana gama sallan taji text ya
shigo wayanta, sai da ta gama
duk abinda take sannan ta
dauko wayan, ga mamakinta
taga ashe Yaa Nawap ne,
gwiwa sake ta bud'a text din
"text me the registration fees"
taga ya turo, shiru tayi tana
k'ara kallon wayan, inda take
tambayar kanta "wai shi wane
irin mutum ne?"
Wurgar da wayan tayi ta mik'e
ta sauka k'asa ba tare da ta
mashi text din kud'in
registration din ba, nan suka ci
abinci, sannan suka cigaba da
firarsu da Ummi. Jin shirun da
Nawap yayi yasa ya kira
number ta har sau biyu amma
shiru, dan haka ya kira Ummi
yana tambayar ko ina Deedon
take. Bayan sun gama gaisawa
da Ummi ta mik'a mata wayan,
sannan ta wuce sama domin
gabatar da sallan isha'i.
Gaisheshi tayi ciki-ciki, haka
shima ya ansa mata yace "baki
ga text dina bane"
"Ban gani ba na bar wayan a
daki"
"Oya kije ki duba, ki mun reply
yanzu, ok?"
"Ok zan duba"
Ba tare da ya kara cewa komai
ba ya kashe wayan, inda
zuciyarshi ta cigaba da jin
haushi da kuma son yarinyar
da bata san ma yana yi ba.
Mik'ewa tayi ta koma d'akin, ta
d'auko wayan, nan tayi arba da
missed calls dinshi, shiru tayi
tana tunanin rashin kyautawar
da tayi wa yayanta mai burin
faranta mata a koda yaushe.
Admission letter dinta ta
d'auko ta duba kud'in
registration din, ta rubuta,
sannan daga k'arshe ta sa "I'm
so sorry big bro, bazan k'ara
ba" ta tura mashi.
Yana kwance ya ji alamar text,
da sauri ya duba wayan, nan
ya ci karo da text din Deedo,
wani lausassan murmushi ya
saki, nan da nan kuma ya nemi
damuwar da yake tare da ita ya
rasa. Bai b'ata lokaci ba yayi
mata mobile transfer ta kud'in
registration din, sannan ya
k'ara mata da 20k, yayi mata
text cewar "in case idan kina
da buk'atar wani abu"
Washe gari ma da wuri ta
shirya cikin turquoise blue din
abaya ta yafa gyalen abayar ya
zauna mata d'as, ta zaro
handbag dinta mai tarkacen
takardunta, ta sanya takalminta
sannan ta k'arasa dakin Ummi.
Ta zauna a gefe ta gaishe da
ita, ta ansa tana mai sanya
mata albarka, tayi mata
sallama, suka wuce tare da
driver.
Ko da suka shiga skool
tunanin abinda zata yi ta fara,
bata san kowa ba bata san ko
ina ba kuma, gashi bata da
number Affan, dan haka ta
wuce office din Dr. Kashim ba
tare da wata damuwa ba. Abin
mamaki tana isa kofan office
din ta jiyo k'anshin turaren nan
da ta ji jiya, ba tare da saninta
ba ta lumshe idanu ta, sannan
ta saki wani kyakkyawan
murmushi, a dai dai lokacin
shi kuma ya bude kofan ya
fito.
Kallonta yayi, ya tabbatar tana
cikin nishadi, dan haka yayi
saurin fadin "Hey beautiful"
kaman daga sama taji
muryanshi, hakan yasa ta kara
sakin wadataccen murmushi,
sannan ta gaisheshi, sai da ya
k'are mata kallo sannan ya
ansa yace "me kika zo yi nan?"
"Neman wanda zai raka ni
registration" ta fada kanta
tsaye. Murmushi yayi, yace "ga
wani kin samu, muje ko?" Ba
tare da tace komai ba, tabi
bayanshi suka fara tafiya. Suna
yi suna dan fira jefi-jefi.
A haka dai da taimakon Affan
da kuma sanayyarshi da
mutane ta samu ta kammala
registration dinta, sai dai 'yan
abubuwan da baza a rasa ba,
wanda koda tana cikin lectures
ne zata iya k'arasa su. Affan
ne yayi mata rakiya zuwa bakin
mota lokacin da driver ya zo
d'aukanta, sai a sannan kuma
ya anshi wayanta, yayi dialling
number shi, sai da ya tabbatar
ta shiga sannan ya mik'a mata,
cikin wani salo yace "I'll miss
you for a while" ba tare da tace
komai ba, ta d'an saki
murmushi, dan ta san itama
har zuciyarta zata missing
dinshi, saboda yan kwanakin
nan da suke yawan kasancewa
tare ta shak'u dashi da yawan
zolayarshi.
BA’A SHAN
ZUMA… 76-78
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Kwanakin da tayi tana fita
zuwa makaranta registration
yasa tafara jin kad'aici da bata
fita yau ba, zaune take tana
karyawa da dankali soyayye da
k'wai, wanda ta lafta ketchup
akai, wayanta a hannunta tana
game d'in candy crush,
message ne ya shigo mata,
cikin hanzari ta fita sannan ta
duba, Affan ne ya turo mata
"hey, ya gajiya?, sannan ya
shirin fara lectures?" Tayi
murmushi sannan ta ajiye fork
d'in ta masa reply da "ga
munan, munata shiri"
Message taji ya k'ara shigowa,
da sauri ta d'auka zata duba a
zatonta Affan ne sai kuma taga
sunan Ya Nawap, cikin sanyin
jiki ta bud'e ta karanta "kin
gama registration d'in ko da
saura?" Ta mayar masa da
"nagama Yaya, Allah bada lada"
Murna yake ji da walwala idan
yana musayar txt da ita, don
haka sai yafara tunanin me zai
kara ce mata, don yanzu so
yake ya jata ajiki kasancewar
yasan inda zata je, jami"a ba
gidan wasa da dama bane, kar
wani yaje ya hure mata kunne
duk shukan da yayi wani k'ato
ya girbe, ita kuwa tattara
abincin tayi sannan takai
kitchen ta nufi d'aki ta fara
gyran wardrope d'inta wanda
bata samu tayi ba saboda fita
data keyi kwana biyu.
Affan na k'ok'arin jan
hankalinta wanda itama ta
tattara hankalinta ta mayar
gunsa, k'arshe yaga message
d'in bazai yiwu ba don haka
kawai ya kirata, murmushi tayi
ta jawo earpiece ta saka
sannan ta saka wayan a
aljihun riganta ta cigaba da
gyaran yayin da suke magana.
Shikuwa Nawap ya mata text
yana jira ta mayar masa da
martani yaji shiru, ya fara
tunani me yarinyan nan take yi
tana gida yau kuma babu wani
aiki da takeyi, baya son kiranta
akan message d'in don haka
ya kira Ummi ya fake da
gaisheta yake yi sannan ya
tambaya ina Deedo?, tace "tana
d'aki"
Sallama yai ma Ummi, sannan
ya kira numbanta, sai kuma ya
kashe, sai da ya samo abin
cewa sannan ya kirata, number
busy yaji, domin bata sa
wayanta a call waiting ba balle
ta san yana kira, tuni yaji
gabanshi ya fad'i ganin sai kira
yake yi amma bai shiga ba, har
lokacin wayan take yi, tuni yaji
zuciyarsa ta tokare,
numfashinsa na neman
guduwa gagara zama yayi yana
jan tsaki, a kalla yakai minti
talatin yana kira yana jin busy,
bai san Affan da Deedo sunyi
nisa a tad'insu na duniya ba.
Wanda muka rasa gane shin
soyayya ce ko kuma tsabar
shak'uwa ce?
Deedo da Affan suna cikin
nishad'i domin kuwa wayan da
sukeyi kowanne acikinsu najin
kamar kada su rabu, sai taji
tana Allah Alah afara lectures
ko zasu na had'uwa da Affan
sosai, siffarsa na mata gizo,
tana tunanin halittarsa, duk da
cewa bai manyanta sosai ba,
anma namiji ne wanda ko
wacce mace zata so ya kulata,
don haka har ta gama aikinta,
ta wanke toilet duk suna
wayan, ta kunna ruwan wanka,
sannan ta zauna akan gado,
tanason cemasa zata shiga
wanka tanajin kunya, don haka
kawai sukayi ta tad'in
makaranta yana bata labarin
abubuwan dariya da al'ajabi
dake faruwa acikin makarantan,
Can dai ya dan nisa, yace "bari
naje na karb'i aiki, zan kiraki
anjima" suna sallama ta ajiye
wayan, bata lura da text din
daya shigo ba kai tsaye toilet
ta shiga tafara wanka, tana
shiga taji wayan na kara,
Nawap ne yake kira akalla awa
daya da minti sha biyar suna
waya, jin wayan ta shiga yasa
shi jan numfashi yana jira ta
d'auka ya sauke mata kwandon
masifa, sai kuma ikon Allah
yana ta kira shiru, feedo kuwa
jin kukan wayan ya tsananta
tafara tunanin waye, don dai
ita tasan Affan bazai kira yanzu
ba, toh ko ma waye ya jira ta
ta gama kammalawa.
Sai da ta gama wankanta tafito,
har lokacin wayan na kara, ta
duba kawai ta d'auka gabanta
na fad'i ganin sunan Yaa
Nawap, a hankali ta saka a
kunnenta sannan tace "ina
wuni Yaya?" "Dawa kike waya
for more than one hour?" Shiru
tayi bata bashi amsa ba, wanda
hakan ya kara kular dashi "Me
kike so ki mayar da kanki?,
daga fara makaranta tun kafin
muje ko ina har kin fara tara
maza?, ba na hanaki ba?, ko so
kike na kwace wayan?, ki
kiyayeni fa!, ki gaya mun da wa
kike waya kuma!" Duk fad'an
da yake yi bata bashi amsa ba,
sai ma kukan da ta saka, a
duniya babu abunda ya tsana ji
kaman kukanta, a take ya rud'e
sannan yace "Ji fa, fisabililah
daga miki magana kin fara min
kuka ke kinfi kowa yawan
ruwan hawaye ne?"
Bata amsa shi ba sannan ba ta
daina kukan ba, zuciyanta na
kunci, ta rasa meke mata dad'i,
kashe wayan tayi alokacin ta
ga missed call 42, ga
messages guda hudu, duk
nashi ne, sai taji wani iri ta
tabbata yayi ta kirane yaji shiru
yasa yake fad'a, batason taji
yana mita ko fad'a , don haka
saida ta ida hawayenta a
lokacin text d'in affan ya shigo
"Yh, how far r u done?" Saitayi
shiru tana tunani, ta tabbata ita
bata ce masa zata yi wani abu
ba, shi yace bari yayi abu
anma sai gashi yana
tambayanta, murmushi tayi
ganin cewa ya gane akwai
uzuri agabanta har ya saurara
mata, tuni ta manta da batun
Nawap, yayinda shikuwa gogan
yana zaune yana jira yaga text
d'in ban hakuri,
Ba tare da bata lokaci ba ta yi
reply wa Affan da "ae am
done" Aikuwa sai gashi ya kira,
aka cigaba daga inda aka
tsaya, Nawap ganin bata turo
masa komai ba yasa yayi
tunanin ko kuka take har
lokacin don haka sai ya kara
kiran numban don yaji ko
lafiya, number busy da ya ji
yasa ya daki teburin dake
gabanshi, sannan yaja wani
mugun tsaki! Wanda muma sai
da muka tsorata..
Wayansu suke hankalinsu
kwance, domin kuwa yadda
Affan ke fada mata kalamai
masu kwantar da hankalin mai
sauraro yasa ta manta da
batun fad'an da Nawap ke
mata kwata kwata, cikin wani
irin salo na karya murya yace
"Feedo na yaushe zan ganki
dan Allah?" Wani irin abu taji
har cikin zuciyarta, dak'yar ta
gyara murya tace "ni ba sunana
Feedo ba, ka kira ni Deedo
yadda kowa ke kira na" kaman
yana gabanta ya mak'ale
kafad'anshi yace "no, ni ba
kowa bane so zan na kiranki
Feedo cuz ya fi mun dadi"
Bata k'ara cewa komai ba sai
wani farin ciki da take ji yana
ziyartanta, haka suka yini suna
wayan nan inda ta b'angaren
Nawap kuwa, fashewa ne
kawai bai yi ba saboda bak'in
ciki. Ana gab da kiran azahar
sannan Affan yayi mata
sallama, ba wai dan sun gaji
da juna ba, kawai dan ya bata
daman aiwatar da abubuwan
da suke gabanta hankali
kwance. Suna gama wayan ta
d'an mik'e rigingine a gado
sannan ta rungume wayan a
k'irjinta, ta rasa me sa take
jinshi har cikin jininta, saboda
ita dai bata tab'a shiga irin
yanayin nan ba.
Mik'ewa tayi da niyyar ta d'oro
alwalla, amma taga wayanta
yana blinking alaman tana da
sak'o murmushi ta saki, inda
cikin zuciyarta tace "Affan baya
gajiya shi kam" toilet din ta
zarce tayi alwalanta ta fito ta
tada sallah ta gama, ta shirya
tsab, sannan ta dauka wayan
ta sauka k'asa. Dinning ta
wuce ta zuba abinci, sai da ta
fara cin abincin sannan ta
duba wayan, gabanta ne ya
fad'i dam! Kasancewar karo da
tayi da text din Ya Nawap
kamar haka "are yu insane? Kin
maida ni k'aramin yaro ko? Shi
yasa ina maki magana kika
share kika cigaba da wayanki.
Ki shiga hankalinki tun kafin
na iso garin nan"
Ture plate din tayi a gefe ta
dafe kanta, "wai shi meye
nashi da yake neman matsa
ma rayuwata?"
BA’A SHAN
ZUMA… 79&80
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Wani fanni na zuciyarta ne
yake fada mata "ya damu da ke
ne da kuma al'amurranki, kuma
ko bakomai Yayanki ne wanda
ya cancanci kiyi mashi biyayya
a kowane irin hali" girgiza
kanta tayi, alaman ta gamsu, a
karo guda kuma ta fara kiran
numbershi amma shiru. Saida
ta kira har sau hudu, amma bai
dauka ba, hakan ya tabbatar
mata cewar lallai Nawap yayi
fushi da ita, daga k'arshe da
taga zaman ba zai kaita ba,
dan haka ta yanke hukuncin
tura mashi text na ban hak'uri,
inda take bayyana mashi cewar
ba wai abinda yake tunani
bane.
* ****
Wasa wasa har ta suka fara
lectures, amma Nawap bai
k'ara bi ta kan Deedo ba, dan
ko waya suke da Ummi da ta
bata wayar yake kashewa. Bata
damu da irin abinda yake yi ba,
dan a tunanin ta ko ya bata
freedom dinta ne, dan haka ta
ba Affan dama suka fara
shimfid'a nagartacciyar
soyayya mai asalin dad'i da
kuma tsafta, hakan yasa har
aka fara sheda su a cikin
makaranta, dimin ko da yaushe
suna manne da juna, idan
bashi da lecture haka yake
rakata har sai ta gama
lectures, yayin da itama hakan
yake a wurinta, basa iya
rabuwa ko kadan sai abinda ya
zama dole.
Yau ma kamar kullun zaune
suke gaban faculty suna
tad'insu na masoyan da suka
zurfafa a cikin son junansu,
wata bak'ar mota k'irar Corolla
S ce tayi parking daga gefen
da suke. Kamar ance ma
Deedo ta kalla wurin, cikin
firgici tayi arba da fuskar
k'awar nan ta Aysha wadda
suka nad'a mata duka a
saloon. Cikin yanayi na
mamaki matar take kallon
Deedo, bata gaskata abinda
take gani ba saida tayo tattaki
har zuwa inda suje, a dai dai
lokacin ita kuma Deedo tace
ma Affan ya tashi su bar
wurin.
Mik'ewar da zasuyi taji caraf
matar ta damk'e hannunta gam,
cikin fargaba ta zare ido tana
kallonta, can murya dashe tace
"ina wuni aunty" wani
malalacin murmushi matar ta
saki, sannan ta matso daf da
kunneta tace "hey you lil bitch!
Nan kika dawo kenan? Kin bar
mu muna shan wuyan
nemanki. Ina mai yi maki
albishir da ki shirya taranmu
nida k'awata, domin muna nan
zuwan miki, domin ke baki kai
matsayin fa za'a ci mana
mutunci saboda ke ba" tayi
wurgi da hannun sannan ta
dafa kafadarta tana murmushi
tace "see you 'yan mata" ta
juya ta cigaba da tafiyan ta.
Sai a lokacin Affan ya kula shi
kadai yake tafiya, bai wani
b'ata lokaci ba ya dawo, yace
"meke faruwa ne? Kin bar ni
ina tafiya ni daya"
Murmushin yak'e ta k'ak'alo,
tace "I'm sorry, ina gaisawa da
mutane ne, muje mu tafi" a dai
dai nan drivernta ya iso, dan
haka sukai sallama ta wuce
gida, zuciyanta fal da tsoro da
tunanin abinda zai biyo baya.
Lokaci na tafiya, yayin da
abubuwa da dama suke
shud'ewa, rayuwar Deedo ta
zama sabuwa, ta inda in ba
wanda yayi mata cikakken sani
ba, ba lallai ya gane ta ba, ta
zama cikakkiyar budurwa mai
madaidaitan shekaru kusan
goma sha bakwai, (17) kenan,
ta waye ta goge, tayi clean
abin sai dai wanda ya gani. Da
sauri take ta shiri dan tana da
exams k'arfe biyun rana,
kasancewar sun fara exams
d'in first semester, gashi kuma
tana son ganin burin ziciyarta
kafin ta shiga exams din.
Duk wannan abu da ake, har
yau Nawap bai shigo Kd ba, ta
inda ya daina kiran ta kwata
kwata, ya kuma daina chatting
da ita ta ko ina. Wannan ya
bata damar sakankancewa ta
cigaba da b'arje gumin
soyayyarta, ita da Affan.
Hakan bai k'ara komai ba, sai
asalin so da kuma k'aunar
Deedo wanda suka cigaba da
wanzuwa a cikin zuciyarshi,
suke kuma azabtar dashi.
Kasancewar yau Juma'a, da
wuri ya tashi ya fara shiri,
jakunkunanshi guda biyu
babba da k'arama ya jawo ya
cika su dam, da kayanshi, ya
tattara takalmanshi, da duk
wani abu mai muhimmanci,
sannan ya wuce toilet yayi
wanka, ya fito. Fuskarshi babu
yabo, babu fallasa, haka ya
fara shiri, ya gama tsab, ya fito
cikin shaddar Gezna fara k'al,
ya d'ora hularshi zanna mai
kwalliya bak'i da ash, ya sanya
bak'in takalmin ALDO, sannan
ya d'aure hannunshi da
lafiyayyar b'akar agogon fata,
ta Promado Royal.
Dan da nan ya fito tass dashi
kamar sabon ango, ya feshe
jikinshi da turaruka, sannan ya
fara kwasar kayan shi yana
sanyawa a boot din motarshi.
Gudu yake yi sosai, domin
baya son ya tsaya ko ina sai a
cikin garin Kaduna.
BA’A SHAN
ZUMA… 81&82
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cikin ikon Allah Nawap ya iso
Kaduna k'arfe d'aya da yan
mintuna, bai b'ata lokaci ba ya
wuce massallacin Juma'a yabi
jam'i, sannan ya wuce gida.
Ummi tana zaune ta ganshi
kamar wanda aka jefo daga
sama, da murnanarta, ta tarbe
shi tana mashi lale marhabun
da mutanen Abuja. Cikin jin
dad'i ya zauna suka gaisa,
sannan suka cigaba da
tad"insu na d'a da mahaifiyar
da suka dad'e basu ga juna ba.
Ido ya ware yana ta jiran
saukowar Deedo, amma shiru
kake ji, Ummi ce ta so ta
fahimci halin da yake ciki,
kasancewar yadda yake yawan
kallon stairs din benen, dan
haka tace "wai baka ce ina
auta ta ba"
Yace "ina niyyan tambayarta
inda take ai Ummi" "tana skool,
kasan har sun fara exams"
nunawa yayi kaman bai sani
ba, yace "eyya, abin ba wuya
kenan, to Allah ya taimaka"
Ummi tace "amin." Har ya mik'e
zai wuce side dinshi, ya juyo
yace "k'arfe nawa zata gama
exams din na yau?" "K'arfe
biyar" Ummi ta bashi ansa, bai
k'ara cewa komai ba, ya wuce
domin ya samu damar hutawa.
* **
K'arfe hud'u da kamar minti
ashirin, Aysha tare da k'awarta
mai suna Baby Labo, suka yi
parking motarsu gaban faculty
of medicine & surgery. Baby ce
ta fara fitowa kasancewar ita ta
san kan makarantar, saboda
anan take masters dinta, itace
kuma ta binciko cewar Deedo
tana da exams yau, da misalin
k'arfe biyu zuwa biyar na
yamma.
Bayan Nawap ya dan huta, ya
tashi yayi sallan la'asar,
sannan ya shirya, ya zari key
din motarshi, ya fito. Wurin
Ummi ya k'arasa yace zai je ya
d'auko Deedo ba sai driver ya
je ba. Allah ya kiyaye Ummi tai
mashi, sannan ya sa kai ya
wuce, zuciyarshi duk a dagule,
ya rasa abinda yake mashi
dadi..
Kasancewar basu da nisa
sosai yasa ya isa wurin da
misalin k'arfe biyar saura
kwata. Gefe guda yayi parking
ta inda zai iya hango duk wani
mai shiga da mai fita a harabar
wurin.
Cikin jin dad'i Deedo ta fito
daga exam hall tana ta faman
fara'a, kasancewar ta rubuta
komai da aka tambayeta,
murmushi ta saki a lokacin da
ta hango abar k'aunarta
rungume da hannayen shi, a
gaban hall din yana jiran
k'arasowanta.
Wayarta dake cikin jakar
hannunta ta fara ruri, ta fito da
ita ta duba, Hally ce ta kira ta,
da sauri ta d'auka suka fara
gaisawa, tayi mata ya exams,
ta ansa da "lafia lau 'yan mata,
ya skool" "ina gida ma wlh,
kinsan an sa ranan bikina"
"amma baki da kirki, shine baki
fadi mun ba" "jiya ne fa aka sa,
kuma naga kina da exam yau,
shi yasa nace idan kin fito zan
kira na fada miki" murmushin
jin dadi Deedo tayi, tace
"Bauchi dai ta aureki kenan, ai
nasan dama baza ki bar
Mubarak din nan ya wuce ki
ba" duk suka sa dariya, tayi
mata fatan alkairi, sannan tace
"say hi to my boo" ta mik'awa
Affan wayar, ya ansa suka
gaisa, kasancewar ya san
labarinta tsab a bakin Deedo.
Ansar wayar tayi bayan sun
gama gaisawar, tace "zamuyi
waya anjima" "ke ban gane ba,
ina Ya Nawap din?" Hally ta
tambaya, "ke ki share, bakomai
fa tsakanin mu" "ni dai nafi son
ki da shi Deedo, wannan daga
ji ma dan yaro ne, irin chewing
gum guys din nan wallahi"
murmushi tayi, tace "zamuyi
waya anjima" ta kashe wayar ta
jefa a jaka, suka jera da Romeo
dinta, suna tafe suna firansu
abin gwanin ban sha'awa, sai
dai wanda ya gani.
Gaban faculty suka isa, saman
wasu kujeru suka zauna suna
ta zabga soyayyarsu, su Aysha
da suke gefe suna jiran
fitowarta ne suka hango kamar
ita, dan haka duk suka fito a
motar, a dai dai lokacin wani
abu yazo zai fada idon Deedo,
Affan yace ta rufe idonta ya
cire mata, hannunshi da ya sa
zai cire abun, yayi dai dai da
d'agowar Dr. Nawap ya kawo
kallonshi kan kujerun da suke.
Daaaaaaam! Yaji zuciyarshi ta
buga a lokaci guda, wani
bak'in kishi ne ya ya kai mashi
ziyara, yayin da a karon farko
yaji k'wanyarshi na shirin
d'inkewa! Da sauri ya fito, a
dai dai lokacin kuma su Aysha
suka k'arasa wurin inda Baby
tasa hannu ta finciko gashin
kan Deedo wanda ta daureshi a
baya, gyalen kanta ta fara
k'ok'arin warewa, amma Allah
ya bata sa'a ta rik'e shi gamda
hannunta. Affan yayi saurin
mik'awa yana fadin "what the
hell are you doing? Ke
wacece?" Isowar Nawap yayi
dai dai da shiga hankalin kowa
da yake wurin in banda Affan
wanda bai taba ganinshi ba,
bai kuma san daga ina yake
ba.
Deedo dake lab'e bayan Affan
tana raba idanuwa tuni tayi
saurin fitowa, ganin Idanun
Nawap sun sauya kala daga
fari zuwa jaa, ta san cewar yau
k'aryarta ta gama k'arewa.
Hannunta ya finciko tun
k'arfinshi ba tare da ya cewa
kowa komai ba, shima Affan
bai yi k'asa a gwiwa ba yasa
hannu cikin izza yana jawota
daga hannun Dr. Nawap!…
BA’A SHAN
ZUMA… 83&84
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Nan da nan hankalin mutanen
da suke wurin ya dawo kansu,
kafin kace wani abu wuri ya
cika mak'il da mutane iyayen
son jin k'wak'waf. Juyowa
Nawap yayi idon shi ya
k'ank'ance, kallon Deedo yayi
cikin wani irin yanayi yace "I'm
disappointed in you, abinda
kika koma yi kenan? Irin
tarbiyyar da aka baki kenan?
Who's this guy?" Ya fada da
wata irin tsawa, wadda tasa
'yan cikin Deedo kadawa a
lokaci guda. Cikin muguwar
tsawar da tafi ta dazu yace
"I'm talking to you, kin tsaya
kina mun shirme, me sa kika
zubar da k'ima da darajarki ta
'ya mace? Me sa kika yi watsi
da hudubar da na dade ina yi
miki? Me sa baki fahimci
abinda nake ji game dake ba?
Me sa baki kulan mun da kanki
ba? Me sa kika kasa gane
cewar duk abin da nake ina yin
shi ne sabo da SO da
K'AUNAR da nake miki? I LOVE
YOU DEEDO y can't you
understand!?"
Numfashin Deedo ne ya fara
k'ok'arin sark'ewa, cikin tashin
hankali ta d'aga kai ta kalle
shi, sai a sannan abinda ya
fad'a ya fara yawo a kanshi,
"damn it" ya fad'a tun
k'arfinshi, sai kuma a lokacin
Affan ya samu bakin magana,
ya k'araso gabanshi, ya kalle
shi ido cikin ido, yace "malam
kai kuma daga ina? Me
hadinka da matar da zan aura?"
Wani mugun kallo Nawap ya
watsa mashi, a yayin da ya
dunk'ule hannunshi yana shirin
kai wa bakinshi naushi, ko me
kuma ya tuna, kawai ya saki
hannun ya juya, a fusace ya
fara tafiya.
Aysha da kuka ya k'wace mata,
ta bi bayan shi, da sauri ta tari
gabanshi tace "Nawap nice mai
sonka, wadda take k'aunarka,
zan iya jure ko wane irin cin
fuska in dai daga gare ka ne,
me sa baza ka bani dama na
nuna maka irin yadda nake son
ka ba? Ka taimaki rayuwa ta
Nawap!" Gefenta ya bi, ba tare
da yace mata uffan ba, ya
shige motarshiya tada da wani
irin k'arfi, ya wuce ya bar
wurin..
Kuka sosai Deedo ta saki
ganin Nawap ya ja motarshi ya
tafi, Affan ya matsa gabanta ya
fara lallashinta, yana fad'a
mata kalamai masu dad'i
wanda suke tafiya da ita da
imaninta. A sannu a hankali ta
samu natsuwarta, ta kalleshi
tace "ka fitar dani bakin gate
na samu abin hawa, nasan
driver ba zai zo ba" "no, bazan
iya barinki ki tafi ke daya ba,
muje na kaiki gida" dak'yar ya
lallabata, ta tashi, inda yayi
parking motar shi suka isa, ya
bude mata gaba ta shiga,
sannan ya maida murfin ya
rufe, ya zagaya ta mazaunin
driver ya shiga ya tada suka
tafi.
Baby Labo da akaje da niyyar
dambe, can na hange ta, taja
k'afafun nan nata masu kama
da na sauro ta k'arasa gaban
k'awarta, tana bata baki,
dak'yar Aysha ta mik'e saboda
kukan da take, haka dai ta
kamata suka shige motarsu
suma suka kama gabansu, ta
inda suka fara tunanin canja
shiri akan na dukan Deedo da
suka zo dashi.
Har sai da Nawap ya kawo
gida, sannan ya fara tunanin
halin da ya baro Deedo, amma
dakewa yayi, ta inda yake
ganin koma me yayi mata,
itace ta ja wa kanta, dan haka
bai shiga gidan ba, yayi
parking nesa kadan da
gidansu, yana jiran yaga yadda
za ai ta dawo gida.
Kusan mintuna ashirin ya
share yana jiran zuwanta
amma shiru, dan haka ya tada
motar da niyyar ya shige gida,
sai kuma ya hango wata ash
din Toyota Supra na k'ok'arin
danna kanta a gate din gidan
su.
Dakatawa yayi, har motar ta
shige, sannan ya bi bayan ta
shima ya shigar da tashi, nan
ya ci karo da Affan ya fito, ya
bude wa Deedo k'ofa yana aika
mata da wani sak'on kallo mai
tattare da so da kuma k'aunar
juna..
BA’A SHAN
ZUMA… 85&86
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Fitowa yayi zai shige kaman
bai san da halittar mutane
agun ba, a zahiri kuma
zuciyarsa tafasa takeyi, tana
ingizashi da yaje ya kama
Affan da duka, can kuma har
zai shiga daga ciki wanda
Affan jikinsa yayi sanyi ganin
cewa cikin d'aya ko yayanta ko
dan'uwanta bai ankara ba yaji
Nawap na cewa maigadi
"yaushe ka fara barin samari
suna shigo mana cikin gida?"
Dasauri mai gadin ya nufi inda
Affan yake tare da cewa "mai
gida don Allah kad'anyi hakuri"
Wani k'ullutun bak'in ciki yaji a
zuciyarsa yana kallon Nawap
anma rashin sanin wayeshi yafi
komi 6ata mishi rai, ya kalli
Deedo wacce duk ta rikice tana
neman madafa yace "ki shiga
zamuyi waya" tayi shiru kaman
zatayi magana saikuma ta
shige, motarsa yaja yafice
yayinda shikuma Nawap
yashige palo ya zauna, yana
ajiyar zuciyar kamar wanda
yafito daga filin daga.
A hankali take tafiya zata wuce
yace "zo nan" jikinta na bari ta
zo ta tsuguna kanta a kasa,
cikin mugun gushi yace
"Inaso kigayamun wanda
yabaki izini kiyi saurayi" shiru
bata amsa ba illa hawaye da
yake kokarin zubowa, ganin
hawayenta yafi komi cimasa rai
anma haka yarufe ido ya fara
zuba mata yayyafin masifa ta
inda yake shiga ba ta nan yake
fita.
Muryarsa Ummi tajiyo tafito, a
yadda yake masifan kaman uba
ya kama 'yarsa tana zina, abin
ya matuk'ar bata mamaki sanin
cewa bata taba ganinshi
awannan yanayin ba, idonsa
yayi jajur ya cicciko, ya kalli
Ummi sannan yace "Ummi da
wani fa na ganta"
Sai da ta nemi wuri ta zauna
sannan tace "toh daka ganta
da wani shi ne yazama laifin
me? Wayeshi kekuma?"
Kuka take sosai yayinda ta
goge hawayenta tace "wanda
ya tayani registration ne"
Nawap ya katseta da cewa
"ohhhh shine kuka hau
soyayya, Ummi can u imagine
har yana ce mun ni waye meya
had'ani da matar da zai aura"
Abun yabawa Umma dariya
ganin yadda Nawap karara
yake nuna kishinsa.
Anan tace wa Deedo ta tashi ta
shiga ciki, shikuma tace "
kamata yayi in sonta kakeyi ka
fad'a mata, baka fito kana
takura mata ba, zata tsaneka,
mu mata bama son takuri
munfi gane lallab'i inka bincika
lallab'ata yakeyi shima wancen
din" fuskarshi cike yace "Ummi
yaro ne fa, irin chewing gum
boys din jami'a"
Dariya tayi sannan tace "ahaka
kuma ya take ka agun nema
ba, dole ka koyi sassauci ka
koyi danne zuciyarka idan
mace kakeso, kacire maganan
dizgi da takuri karka kara yiwa
y'ata tsawa haka, ji yadda ka
sata zubar da hawaye" tana
gama fad'in haka ta mike ta bi
sawun Deedo wacce ko da taje
d'akin ma fad'awa tayi akan
gado tana kuka, har ranta
bataji dadin yadda Nawap ya
mata ba, sai dai ta wani fannin
kuma ji tayi kaman ansauke
mata dutse a ranta ganin yau
ya furta mata da kanshi cewa
yana sonta..
BA’A SHAN
ZUMA… 87, 88
& 89
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Da murmushi Ummi ta shiga
d'akin, wuri ta samu a bakin
gado ta zauna, sannan ta kai
dubanta ga Deedo wadda take
kuka bil hak'k'i da gaskiya. A
hankali ta furta "oh, auta ba
dai abinda wancen yayi miki
bane kike kuka?" Sai a sannan
Deedo ta san da shigowarta,
kasancewar kanta na kasa tayi
ruf da ciki. Ba tare da ta jira
ansarta ba ta cigaba "ke manta
mun da shi auta, babu wanda
zai miki dole kinji 'yar albarka,
dan haka tashi maza, ki wanke
fuskar nan taki bana son ganin
bacin ranki 'yar auta ta" cikin
jin kunya, Deedo tana sum
sum da kai ta mik'e ta shige
toilet, wanka tayi sosai, sannan
ta fito, amma bata tarar da
Ummi ba.
Shiryawa ta cigaba da yi dan
lokacin maghriba ta gabato,
kasancewar tana hutun sallah,
ga wani yunwa da yake
addabar cikinta yasa tayi
gaggawan sauka kasa domin
ta samu abinda zata ci. Zaune
ta tarar dashi a kujerar da ta
barsa ya k'ura wa halittar t.v
ido, amma daga dukkan alamu,
bai san abinda ke faruwa cikin
t.v din ba. Sad'af-sad'af tayi ta
shige kitchen, shi kam jin
kanshin turarenta yasa yayi
zumbur, ya dawo daga dogon
tunanin da yake.
Mik'ewa yayi yabi hanyar
kitchen din, can ya hango ta
tana faman daga manya
manyan food flask din da su
kan zuba abinci. A kofan
kitchen din ya harde
hannayrnsa, ya zuba mata
idanu wanda bata ma san
Allah yayi ajiyarsa a wurin ba.
Ta gama dibar abincinta, tana
k'ok'arin fitowa, amma ya kare
hanyar ta yadda baza ta iya
wucewa ba matuk'ar bai bata
hanya ba.
Ido ya k'ura mata sosai ta
yadda ba wani motsi da zata
iya yi. Take ta daburce, ta
nema natsuwarta ta rasa, bata
ta6a tunanin Nawap na da
kyau haka ba, ga wasu irin
idanunshi masu kamar yana jin
bacci, dak'yar ta sauke idonta
a kansa, cikin k'arfin hali tace
"zan wuce Yaa Nawap" bai ce
komai ba, sai ma gyara
tsayuwarsa da yayi, ya
fuskance ta sosai. Har ya daga
baki zai fara masifa, sai kuma
ya tuno da kalaman Ummi
wanda tace "mu mata mun fi
son lallami" sumarsa ya shafa,
cikin boron kunya ya daure
yace "Lil sis, yanzu haka kike
ganin ya dace ace munyi
dake?"
Bata ansashi ba, dan haka ya
cigaba "ban son yadda akai na
kamu da soyayyarki ba, haka
na tashi na tsinci kaina a
cikinta, amma a tunanina, baza
ki ta6a gujewa duk wani abu
da ya shafe ni ba, matuk'ar ba
sa6on Allah bane." Ya ja
gauron numfashi sannan ya
cigaba "soyayyarki ta riga ta yi
mani mugun kamu, wanda in
har ban samu goyon bayanki
ba, komai zai iya faruwa,
amma idan kina ganin zan
takura ki, fine, kina da 'yancin
da zaki zabar ma kanki dukkan
abinda kike so, amma kafin
kiyi saurin yanke hukunci, ina
son kiyi nazari, duk shawarar
da kika yanke, zan aminta da
ita, matuk'ar abin zai zama
farin ciki a gare ki."
Ya gyara mata hanya, yace
"zaki iya wucewa" bata ce
uffan ba, ta bi gefensa ta wuce
palon, yayin da shi kuma ya
fito ya kwashe wayoyinsa,
sannan ya wuce part dinshi.
Juyawa spoon din hannunta
kawai ta cigaba da yi, ita dai ta
san bata k'in Yaa Nawap, dan
shine mutun na farko da ya
daga darajarta a lokacin da
bata da wani gata balle kuma
'yanci, shine wanda ya inganta
rayuwarta da farin cikin da ta
dade tana mafarkin samu. To
amma ya zata yi da Affan
wanda ko wane bugun
zuciyarta yake fita da son shi
da k'aunarshi? Ya za ta yi da
shak'uwa da karamcin da ya
nuna mata a cikin dan
k'ank'anin lokacin da ta san
shi? "Ya Allah ga ni gare ka"
shine abinda ta furta, tare da
ture plate din da yake gabanta
zuwa gefe.
Wayanta ne ya fara ruri alamar
text yana shigo mata, hannu ta
sa ta ciro shi a aljihun dake
jikin rigarta, text din ta fara
dubawa kamar haka "Hope
you're fine Feedo na?"
Murmushin k'arfin hali ta saki,
sannan ta fara typing mashi
ansa "I'm good, kayi hak'uri da
abinda ya faru dazu fa"
Take ta ji ansar shi ta dawo
mata, "never mind dear, but
wanene shi a wurin ki?"
"Cousin dina ne" ta maida
mashi ansa itama.
Dam! Zuciyar Affan ta buga, ba
don komai ba sai don jin
dangantakar dake tsakanin
Nawap da Deedo, shi dai yana
son ta, har cikin ransa, amma
ya san aure tsakanin su abu ne
mai matuk'ar wahala, domin ko
ga Dr. Kashim nan har yanzu
bai yi aure ba, ya san da kunya
ya kai batun nashi auren daga
gama skool dinshi, sannan
yanayin da Nawap ya shiga a
yau, ya tabbatar mashi da
cewar yana k'aunar Feedo fiye
da yadda yake son ta, kuma ko
bakomai zai so mata abinda
yake mafi alkairi ne a gare ta,
dan haka yana jin zai iya
sadaukarwa Nawap da
soyayyar da yake wa Feedo ba
don komai ba sai dan
cancantar shi da ya gani.
Jin shiru bai dawo mata da
ansa ba yasa ta k'ara tura
mashi "are you there?"
Shigowar message din ne ya
katse tunanin shi, a hankali ya
share zufanda ta karyo mashi,
sannan ya fara rubuta mata
ansa "ki fada mun gaskia kina
son shi ko?"
Kamar daga sama ta ji
tambayar, haka dai ta daure
tace "I can't say Affan, but,
shine mutumin da ya 'yanta ni,
ya mayar da ni abinda nake a
yau"
"Ok, na fahimce ki, ki kwantar
da hankalinki, zamu yi magana
anjima kinji?"
"Alright, take care" ta tura
masa, sannan ta mik'e a
3seater ta cigaba da tunanin
halin da take ciki.
Number Hally ta fara kira
amma har ta katse shiru bata
daga ba, dan haka ta shafa
mata lafia, don ta san indai ta
gani, to zata kira ta.
BA’A SHAN
ZUMA… 90&91
NALUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tunani kam tayishi harta gaji,
ta rasa me zatayi, don tasan ba
karamin butulci bane tace taki
jinin ummi,
Shikuwa acikin kwanakin
yakara daburcewa yadawo wani
iri har Ummi tagane saidai bata
ce masa komi yadawo baya ko
kulata ayayinda shikuma Affan
yariga da ya cire abun aransa
yasawa kansa cewa ya hakura
kawai, tunda tamishi bayanin
komi na rayuwanta da nawap,
randa taje makaranta lectures
ma sun zauna anan yace mata
"ina ga zan baki zabi ne, kije
kiduba kiga wa kika fi so,
zanzama mai farin ciki da
bayaninki, zan kuma yarda da
kaddara, saidai kisani cewa
inasonki ba kuma zan hadaki
da wata ba, niyyata na aureki"
Har ya idar da bayaninsa
batace komi ba, ita dai ta shiga
rudani gashi shareta da nawap
keyi yakara sata awani
damuwan.
Nawap a gida yasamu ummi ya
ce yana son magana da ita, ta
ce "toh" sannan ta zauna
yafara sosa keya sannan yace
"Ummi na zauna nayi tunani
ne, wlh inason Feedo ba kadan
ba, don Allah ummi ki mana
aure" tunda ya fadi kalmomin
sa tasan cewa tabbas dagaske
yanason feedo din tunda tasan
shi mutum ne mai balain
kunya, bai taba tunkararta da
magana shige irin wannan ba
tayi murmushi sannan tace
"Ai dole sai yar tawa ta
Amince, zan mata auren dole
ne aka gaya ma?"
Yayi shiru don bai tabbatar
tana sonshi ba yace " zata
cemiki tanason wani ne, wlh
ummi kar ki yarda, yaro ne
yaudaranta zaiyi" itadai ta zura
mishi ido aranta kuwa kaman
ta juye ruwa a kasa tasha don
murna, tadade tana adduan
Allah yanuna mata wannan
rana da zata hadasu aure,
shikenan tuwonta maiyanta,
Feedo kuwa bayan tagama
tunaninta duk ansa daya ta
kare dashi, wato nawap takeso,
takira Affan tace inta gama
lectures suhadu nan ya
amince, ko da yazo yazauna
akan kujera a dept dinsu
datake jiranshi, ta ce "ni dai
nasan randa nafara soyayya
dakai, bantaba yi don ranka
yabaci ba, banyi don na
yaudareka ko na rabu dakai
daga baya ba, ban yi da zuciya
biyu ba, anma kasan dan adam
ajizi yau an wayi gari bakai din
zancigaba da so ba, maganan
gaskiya yaa nawap nafara so
arayuwata, shi ya maidani
mutum har ka ganni kakeso,
shi ya taimakamin kuma yana
kai, mahaifiyarsa ita tarikeni da
zuciya daya, ban mata adalci
ba ace dan cikinta guda yace
yana sona naki yarda, ba zata
ji dadiba duk da zata nunamin
ba komi anma danka naka ne,
kayi hakuri ka gafarceni" tana
fada ta share hawayenta,
shima kallonta yake har ransa
tausayinta yake ji, yace
"bakomi wallahi, na fahimceki
sosai ubangiji Allah ya sa
hakan shiyafi alheri, nima Allah
hadani da wata" nan suka
danyi tadi sannan ta mike don
komawa aji
BA’A SHAN
ZUMA…
93,94&95
BA'A SHAN ZUMA… 93
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Gida ta dawo zuciyarta wasai,
tana jin tamkar ta sauke wani
gagarumin nauyin dake kanta.
Bayan sun gaisa da Ummi ta
wuce sama, don ta shirya ma
wannan rana, domin alkawari
ta yi yau zata fada ma Yaa
Nawap ta ansa tayin
soyayyarsa, don haka take son
tayi surprising dinshi ta hanyar
kawata mashi kanta da ado na
ban mamaki da daukar hankali.
Number sa ta laluba ta kira
amma a kashe, ba tare da wata
damuwa ba tai mashi text "I
need to see my big bro" ta tura,
amma bai yi delivery ba,
hankali kwance ta gama
shirinta tsab, ta sauko kasa
amma ba kowa a palon, ga
wani shaukin son Yaa Nawap
da yake fisgarta, bata da buri a
lokacin wanda ya wuce mata
ganin fuskar shi. Ko ina ta
dudduba amma babu kowa a
cikin gidan, ba tare da wata
fargaba ba ta zarce part dinshi,
a hankali ta tura kofar palon,
amma ga mamakinta ta jita a
datse gam.
Cikin natsuwa take
kwankwasa kofar amma shiru,
dukawa ta yi ta dan leka ta
inda ake sanya key, nan taga
jam lock, cikin rashin jin dadi
ta juyo ta dawo cikin gidan, a
palo tayi arba da Ummi, nan ta
fara kame-kame, amma Ummi
ta basar tace "ina kika shiga
ina ta kwala kiranki?" "Na dan
zagaya nan baya ne in sha iska
Ummi" tace "to, wuce ga abinci
can" dining area ta nufa ta
zuba abincin ta ci gaba da juya
spoon din tana tunanin inda
Yaa Nawap ya nufa, domin shi
dai yawo ba al'adarshi bace
matsawar yana gari to fa kullun
yana gida kaman mace.
Ummi tana hankalce da
yanayinta amma ta basar, don
bata son ta takura mata sai
taga kamar don ba ita ta
haifeta bane. Spoon biyu kawai
tayi a abincin ta taso ta dawo
gefen Ummi ta zauna ta kurawa
wayanta ido tana jiran taga
delivery na sakon da tayi wa
Yaa Nawap.
Can dai zuciyarta ta kasa
daurewa, tace "Ummi ni kam
ina Yaa Nawap ya shiga?
Rabon da na ganshi tun
shekaran jiya" murmushin jin
dadi Ummi tayi a fakaice, ta
san ko bakomai d'an nata ya
fara samun kar6uwa a zuciyar
Deedo. Ta kalleta tace "jiya tun
kafin ki tashi bacci ya koma
Abuja an mashi kiran gaggawa"
ta dan saci kallon ta taga
yadda hankalinta ya tashi
lokaci guda, sannan ta cigaba
da magana…
BA'A SHAN ZUMA… 94
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
"Bayan ya isa kuma wurin karfe
shidda na yamma ya kira ni
yake sheda mun cewar yau da
misalin karfe biyar na asuba
zasu tashi zuwa London, an
tura su yin wani course na
shekara ukku" tana kawowa
nan taja bakinta tayi shiru, tana
mai cigaba da kallon akwatin
t.v.
Mikewar da Deedo zata yi taji
wani mugun jiri ya kwashe ta,
kukan da take makalewa a take
ya subce mata tagal tagal tayi,
tana me kokarin faduwa, nan
Ummi ta kwashi salati tana
kwalawa Saude mai aiki kira,
cigaba da jijjigata tayi tana
fadin "lafiya Deedo? Menene
abin kukan?" Cikin rashin sani
Deedo take magana "Yaa
Nawap me sa kai mun haka,
bayan kasan kaine buri na,
kaine farin cikin rayuwa ta"
kuka ta kuma fashewa da shi
ta koma kaman zararriya, ta
kalli Ummi da tausayin Deedo
ya cika ta, tare da jin dadin
kalamanta, tace "Ummi da
gaske Yaya ya tafi ya barni?
Ummi ya zan yi da DAKON SO
(Na KAUSAR LUV) na Yaa
Nawap da nake fama dashi?"
Ta k'ara fashewa da wani
kukan mai ban tausayi..
Dak'yar Ummi ta lallaba
Deedo a wannan rana, banda
kuka ba abinda take yi, haka
dai Ummi ke kwantar mata da
hankali, yayin da wutar
soyayyar Nawap take faman
kara ruruwa cikin zuciyarta
tamkar ana watsa mata fetur.
* ***–******
Da sallama suka shigo palon
ba kowa sai Deedo da ta
kurawa wani makeken hoton
Yaa Nawap dake mak'ale a
palon ido, wanda ya kasance
sana'arta kullun da ta dawo
daga makaranta bata da sauran
aikin da ya wuce ta zauna
gaban wannan hoto tayi ta
kallonshi, wani lokacin har da
yan sambatun da baza a rasa
ba.
Aysha ta karasa ta dafa
kafadar Deedo, sai a sannan ta
dago a razane dan ko alama
bata ji shigowar mutun ba.
Kallonta tayi a tsorace, inda ita
kuma ta sakar mata murmushi
tace "Ina Ummi fa?" Murmushin
k'arfin hali ta mayar mata, tace
"ku zauna mana, taje unguwa
ta dawo" su Baby Labo aka ja
yan kafafuna aka karasa cikin
palon aka zauna a kujera ana
aika ma Deedo sakon
murmushi.
Ita kam abin ya bata
mamaki, mutanen da suke
neman ta su daketa sune suka
dawo kamar ba su ba, anya
babu wani kulli a kasa? Ta dai
daure ta kwala kiran Saude ta
kawo masu dan abin motsa
baki, yayin da Aysha ta fito da
I.V na guda ukku ta mik'awa
Deedo, tace "da naki, da na
Ummi, wannan kuma na daurin
aure ne ki bama Nawap"
[18/04 23:41] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 95
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Ansa tayi idonta waje ta duba
da kyau, tabbas bikin Aysha za
ayi, cikin zuciyarta tace "har ta
hakura da Nawap din kenan"
tunani ta fara itama ko hakura
za tayi dashi, tunda bai damu
da ita ba, gashi yau kusan wata
daya da tafiyarsa amma ko a
waya bata jishi ba, Ummi ma in
zai kira ta sai yayi hiding
number sannan, tasan kuma
duk don saboda ita yake
hakan. Aysha ce ta katse mata
tunani ta hanyar cewa "ya dai?
Naji kinyi shiru ko congrats
babu" murmushin dole tayi,
tace "I'm so happy 4 yu, sai
dai kuma Yaa Nawap baya nan,
yaje yin wani course London,
amma in sha Allah zaki ganmu
ni da Ummi" "Allah ya sa"ta
fada, sannan suka mike a tare,
ta d'an taka masu zuwa inda
sukai parking sannan ta dawo
ciki, tana me cike da mamakin
sauyawan da Aysha tayi lokaci
guda.
* *–****
Cikin yarda da hukunci irin
na ubangiji, aka yi bikin Aysha
da angonta Saifullahi, wanda
dak'yar Ummi ta lallaba Deedo
ta leka wurin dinner. Haka ma
aka sha bikin Hally, aka kaita
Bauchin Yuguda, amma Allah
bai ba Deedo ikon zuwa ba,
kasancewar rashin Yaa Nawap
wanda ya kasance wani jigo na
rayuwarta, tafiyarsa ta zama
wani gi6i a rayuwar Deedo,
domin tana jin tamkar ta rasa
shi ne har abada, ga wani irin
son shi da ya bi ya addabi
zuciyarta, gani take ashe son
da tayi wa Affan ba soyayya
bane shak'uwa ce kawai, amma
asalin so na zahiri Nawap take
yiwa shi, sai dai bata gane
hakan ba, sai yanzu.
Idan tana tunanin shi ta kan
zubar da hawaye domin shine
kawai abinda take yi ta samu
sassauci a cikin birnin
zuciyarta. Ummi ce ma take
dora ta akan yawan addu'oi
domin kuwa addu'a takobin
mumini ce kuma ta kan
taimaka ma bawa a kowane irin
yanayi.
Shawarar Ummin dai ta bi,
idan abun ya dameta ta kan yi
salloli tare da addu'oi, sannu a
hankali ta fara samun natsuwa,
ba wai don ta daina jin DAFIN
SO (coming soon) na harbin
zuciyarta ba, sai don
fawwalawa Allah dukkan
lamurranta da tayi, ta maida
hankalinta ga karatun ta,
wanda take ganin shine kawai
abinda zata yi ta farantawa Yaa
Nawap dinta.
BA’A SHAN
ZUMA…
96,97&98
BA'A SHAN ZUMA… 96
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
BAYAN SHEKARA UKKU
A hankali yake saukowa daga
matattakalar jirgin janye da dan
madaidaicin trolley, yana
shakar iskar da take busawa
mai cike da ni'ima tamkar za'a
saki ruwan sama a dai dai
lokacin. Waige-waige yake
alamar yana neman wanda ya
zo daukarshi, can ya hango ta
sanye da wata light purple d'in
abaya, ta yafa gyalen, ta nade
hannayenta duk biyun ta zuba
mashi idanu tana murmushi.
Sosai ya wara idonshi yana
kare mata kallo, tabbas
Deedonshi ce, ta canja sosai,
ta zama cikakkiyar budurwa,
fatar jikinta ta goge sosai, ga
wani annuri mai haske tattare
da ita. Wani mugun dadi ne ya
tsirga zuciyarsa, nan take
soyayyarta ta dawo masa
sabuwa fil, tayi masa famin
ciwon da yake fama da shi
shekara da shekaru, sai dai
kuma ya san ta riga ta mashi
nisa, ya san son da take ma
Affan ba irin wanda zata yi
fatali da shi ne ba, ya san ba
zai taba samun kar6uwa a
wurin zuciyar da ya hallakar da
tashi zuciyar domin ta ba, dan
haka dole ya kama mutuncinshi
tun kafin ya zube a idonta.
Gintsewa yayi, ya karasa gaban
ta, dariya take mai cike da
wani salo, tana kallonshi, a
lokaci guda tace "sannu da
zuwa Yaa Nawap"
Kaman ya nitse a wurin,
kasancewar muryarta da ya ji,
shekara ukku cif cif rabon da
ya ji wannan zakakkar muryar.
Dakyar ya dawo daga duniyar
da yake, yace "na sameku
lafiya lil sis?" "Lafia lau" ta
fada, yayin da ta anshi trolleyn
da ke hannunsa tayi gaba, shi
kuma ya bita a baya.
Inda tayi parking suka
k'arasa, fuskanta lullu6e da
wani farin ciki wanda ba zai
iya 6oyuwa ba, bayan motan ta
buda ta jefa jakan hannunta,
sannan ta zagaya driver seat ta
zauna ta daura seat belt, duk
idanun Nawap na kanta,
mamakin ta yake yi sosai,
yadda take abu komai a waye,
kanta ya gama fashewa kamar
ba Deedon Goggo ba, kallonshi
tayi ta saki murmushi wanda ya
rasa ko na menene sai dai ya
kawar da kanshi, ita kam ta yi
ma mota key suka kara gaba.
BA'A SHAN ZUMA… 97
NALUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Har suka je gida ba wanda ya
tanka ma wani, illa Deedo da
lokaci zuwa lokaci ta kan kai
dubanta gareshi sannan ta saki
murmushi, wanda ya rasa gane
ko na menene, daga k'arshe
tasa ya tsargu da kanshi, har
yana tunanin kodai wani abu
ne a jikinsa wanda yake sanya
ta dariya? Nan da nan ya hade
rai, ya juyar da kanshi yana ta
faman shan kanshi, har suka
isa.
Wucewa ciki yayi bayan tayi
parking, inda ita kuma ta fito
da jakarsa, ta ja zuwa cikin
gidan.
Da murna Ummi ta tare shi
tana mashi barka da zuwa,
cikin jin dadi da girmamawa ya
isa suka gaisa, sannan suka
mike gaba dayan su zuwa
dining table, kamar sun san da
yunwa ya iso.
A haka suka gama cin
abincinsu hankali kwance,
suna yi suna yar fira jefi-jefi ta
yaushe gamo.
* **—-******
Tun bayan da Nawap ya dawo
kwata-kwata Deedo ta rasa
gane kanshi, baya shiga
harkan ta ko kadan, haka zalika
ko shigowa yayi ya tarar da ita,
to fa baya zama zai bar wurin,
inda a bangarenta take fama
da so da kuma k'aunar shi
wanda su kan tunzura
zuciyarta. Hanyar da zata sanar
dashi yadda soyayyar shi ke
azabtar da ita take nema,
amma ina, babu fuska ta
bangarensa, domin kuwa ya
dade da sallamawa da ita, ya
shafa ma zuciyar sa ruwan
sanyi, ya daukan ma kanshi
alkawarin ba zai taba takurata
ta so shi ba.
Ganin halin ko in kula da
Nawap yake gwada ma Deedo,
yasa Ummi ta kira shi, tana
tambayar "ni kam Nawap ina
maganar ku ta kwana kai da
auta ta?" Ba tare da ya kalleta
ba yace "Ummi wannan
magana ai ta wuce, ita da take
da wanda take so" murmushi
Ummi tayi, ganin yadda yayi
kicin-kicin da ido, tace "me zai
hana ka kara jarraba sa'ar ka,
ka sani ko ka samu kar6uwa
yanzu" bai ce komai ba, sai ma
mikewa da yayi ya wuce part
dinsa…
BA'A SHAN ZUMA… 98
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Yana shiga ya mike a kujera
yana jin wani tiririn son Deedo
na tokarar zuciyar sa, anya zai
iya jure rashinta? Ko dai
shawarar da Ummi ta bashi zai
yi amfani da? Cikin azama ya
mike ya jawo wayarsa, ya cire
screen lock din, nan da nan
hotonsu shida ita da suka
dauka wata rana dazai koma
Abuja ya bayyana, sosai ya
kura ma hoton ido yana ganin
yadda take dariya, ga dukkan
alamu bata da wata damuwa a
wancan lokacin. A fili ya furta
"i can't let yu go Deedo, cuz yu
belongs to me" ya shafa
fuskan wayan, sannan ya
lalubo number ta a sabon layin
mtn din da yake amfani da shi.
Sai da ya kira har ta katse
bata daga ba, inda ya k'ara kira
a karo na biyu, nan ma shiru
kake ji. Text ya tura mata "Ina
fatan lokaci yayi da zan samu
ansar tambayar da na maki
shekaru ukku da suka wuce" ya
tura ba tare da ya sanar da ita
ko wanene ba.
Kwance take tana sana'ar
tata, wato tunanin halin da zata
shiga in ta rasa Nawap, tana
kallo aka kira har ta katse
amma bata ko motsa yatsanta
ba, shigowar text din ne yasa
ta gane mai kiran yana bukatar
wani abu daga gare ta. Hannu
tasa ta janyo wayan ta buda
text din, sai da ta gama
karantawa sannan ta duba
number, amma bata san mai
ita ba, tunani sosai ya cika
kwanyar ta, daga k'arshe
dabara ta fado mata, inda ta
sanya number a TrueCaller,
nan ta ci karo da sunan DR.
NAWAP KHAMIS har ma da pic
dinshi..
Yadda kasan an mata albishir
da gidan aljanna, haka Deedo
ta tsinci kanta cikin farin ciki.
Zumbur ta mike daga
kwanciyar da take ta kara
murza idonta, tabbas ba gizau
sunan yake mata ba, cikin
zazzodi ta fara rubuta mashi
ansa "I'm just waiting for this
day to come" can kuma wata
zuciyar ta bata shawaran ta
dan jaa class mana, tunda dai
har yanzu yana son ta.
Murmushi ta saki sannan ta
goge text din, ta rubuta wani
"nd who's this?" Ta tura masa
ba wai don zuciyarta ta so ba.
Jin shigowar text yasa yayi
saurin duba wayar, bayan ya
karanta, yayi murmushin
takaici, sannan ya rubuta
"someone who can't live
without yu" ya senda mata…
Ganin text din yasa ta taka
rawar disco, domin ta gama
sarewa Nawap ya guje mata,
ashe ba haka abin yake ba,
ashe kallon kitse ne su ke wa
rogo. Wasu hawayen jin dadi
suka gangaro ga bakinta
kunshe da murmushi, ta shafa
idonta taji tabbas hawaye ne,
nan ta kara fadada
murmushinta, domin duk
duniya ba yanayin da ya kai
wannan dadi, kana hawaye a
lokaci guda kuma kana
murmushi, wannan ya nuna
farin cikin ya kai k'arshe
BA’A SHAN
ZUMA… 99&100
BA'A SHAN ZUMA… 99
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Cikin sigar shagwaba kamar
wanda yake kallon ta ta turo
dan bakinta, sannan ta fara
rubuta ansar da zata bashi "if
yu really mean ur words, me
zai hana ka bayyana kanka?"
Ta tura, yayin da ta rungume
wayar tana jin sabon yanayi na
daban a cikin jikinta.
Murmushi yayi wanda har sai
da kyawawan hakoransa suka
bayyana, a lokacin da yayi arba
da sakonta, ba tare da wata
fargaba ba, ya mayar mata da
ansar "ok, ki shirya gani na da
misalin karfe bakwai na daren
yau."
Ihun murna ta saki, inda ta
fada da baya ta kwanta, ta
k'ank'ame wayan tana tunanin
abinda ya dace tayi kafin
lokacin haduwarsu. Da sauri ta
mike ta wangame wardrobe
dinta, sannu a hankali take bin
kayan ciki da kallo, amma bata
ga wanda ya dace da ita a rana
irin ta yau ba, rufewa tayi,
sannan ta bude dayan gefen
wanda yake dogayen riguna ne
zallah jere a cikin wardrobe
d'in, a hankali take duba su
daya bayan daya, inda a
k'arshe ta sauke idonta akan
wata English gown kalar lemon
green, murmushi ta saki
sannan ta zaro rigar, wuyanta
irin rufaffen nan ne (tuttle
neck) yayin da hannun rigar
yake dogo, sai dai ya matse
daga k'arshe, doguwa ce har
k'asa, in banda kyakkaywan
(shape) da aka yi mata daga
sama.
A samar gado ta aje rigar,
sannan ta bude inda
gyaluluwanta suke, ta samo
wani madaidaicin jan gyale
wanda ta san tabbas zai hau
da rigarta, haka ta gama hada
duk wani abu da zata sa,
sannan ta sauka kasa zuwa
kitchen.
Saude ta tarar tana aiki, ta
kalleta tace "je ki huta Saude,
bar ni da aikin kitchen din nan
yau" godiya Saude tayi ta
wuce, duk da ta fuskancin
yanayin farin cikin da uwar
dakin nata take ciki.
Tana tsaka da aiki, ta juya
bayan ta Nawap ya shigo
kitchen din, ya buda fridge ba
tare da ya san ita ke aiki wurin
ba. A hankali ta dago idanunta,
inda ta sauke su a kan nasa,
amma yayi kicin-kicin da fuska
shi dole ga big bro, baya son
ta gane da shi tayi musayar
text dazu.
Murmusawa tayi, sannan
tace "har ka tsorata ni wlh, me
zaka dauka na kawo maka?"
Basarwa yayi, yace "eyya, ban
san kina nan bama ai, ruwa ne,
na riga na dauka ma, kiyi aikin
ki kedai" tana kallonshi tana
dariyar yadda yake faman
bonewa, tace "ok, ehnmm" ya
juyo yace "ya dai?" "Daman zan
ce ne anjima ina da bako, yace
zai zo nan dan kada kace ban
fada maka ba" ta karashe
maganan tana mai karantar
yanayin da yake ciki. Cikin
borin kunya ya shafi kanshi,
"lokacin da kika fara
soyayyanki dama kin nema
izinina ne?" Ya fada yana fita a
kitchen din, biyo shi tayi tana
fad'an "ni fa ba wani soyayya
Yaa Nawap, aboki ne kawai" da
murmushi ya juyo, sai kuma ya
daure yace "naji, kije kiyi
aikinki"
"to bakon nawa fa? Baka ce
komai ba"
Ido ya kura mata, yana mata
kallon kece rayuwa ta, nan da
nan yake neman sanya ta a
wani hali, domin bugun zuciyar
ta taji ya karu, ba tare da tace
komai ba, ta juya ta koma
kitchen din zuciyarta fal da so
da k'aunar Yaa Nawap.
[20/04 20:56] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 100
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Lokacin da ta gama girkinta har
karfe shida saura kwata, a
gurguje ta jera komai a dining
table, lokacin Ummi na
saukowa ta kalleta sai zuwa
take tana dawowa tsakanin
kitchen da dining area, ga
fuskanta a sake da alama tana
cikin farin ciki sabanin
kwanakin baya da ko kasan ta
daina saukowa, kullun tana
daki kaman bokanya.
"Ba dai ke kika yi girkin yau
ba auta" Ummi ta fada dai dai
lokacin da ta karaso gabanta.
Da murmushi ta kalla Ummi
tace "yau special na hada
mana Ummi, har sai kunne yayi
motsi idan aka ci" bubbuda
coolers din Ummi take yi, inda
wani kanshi ya daki hancinta,
tace "lallai naga alama, amma
menene sirrin?" Ta fada da
sigar tsokana.
"Ba komai fa Ummi" Deedo ta
fada tana rufe fuskanta da
hannu, "sai dai ehnmmm"
"mene?" Ta tambaya tana
kallon ta. "Ina da babban bako
anjima Ummi, idan ya zo zai zo
ya gaishe ki ma" ta fada tana
dariya. "Bako Deedo?" Ummi ta
fada cikin karaji,
girgiza kai Deedo tayi, "zaki
ganshi Ummi, kuma in sha
Allah zaki yaba dashi" "Allah
yasa" ta fada yayin da take
wucewa zuwa palo ba tare da
ta ji dadin maganar Deedon ba.
"Yanzu shikenan yaron nan
yana gani zai yi rashin mace
kamar Deedo? Duk dan saboda
dan banzan kishi irin nasa,
kuma yana son ta ba wai baya
son ta ba." Sababin da Ummi
ke ta faman yi kenan a cikin
zuciyarta, har aka kira
maghriba, ta mike ta haye
sama domin bada farali.
A bangaren Deedo ko bayan
ta fito wanka ta bada sallar
maghriba, sannan ta cigaba da
yan shafe-shafenta, sassaukar
kwalliya tayi kasancewarta ba
ma'abociyar dam6are-dam6are
ba, sannan ta ja rigarta ta
sanya, ta gyara gashinta ta
faka shi a tsakiya, inda tayi
amfani da jajayen kananan yan
kunne, ta daura bracelet ja,
tana kokarin feshe jikin ta da
turare, taji alaman message ya
shigo mata, da sauri ta duba
"Ina cikin gidan ku, zaune a
palon baki, just waiting for my
princess" shine abinda ta gani
rubuce a message din.
BA’A SHAN
ZUMA…
101-103
BA'A SHAN ZUMA… 101
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Dariya mai sauti ta saki, a fili
ta furta "Yaa Nawap kenan"
sannan ta rubuta mashi ansa
"hmmmm, ina zuwa yanzu" ta
tura masa, sai da ta karasa duk
abinda zata yi, ta janyo wasu
red plat shoes ta saka, ta yafa
gyalenta sannan ta fita. Dakin
Ummi ta fada, ta tarar da ita
zaune tana jan casbaha, ta
zauna gefen gado tana wasa
da hannunta. Har sai da tayi
addu'a duk suka shafa a tare
sannan Ummi tace "har ya iso
ne?" Kanta a kasa ta girgiza
kai alaman "eh"
"To ki tashi kije, ki dai kula
da kanki da mutuncinki" "in sha
Allah Ummi" Deedo ta fada
lokacin da take mikewa, a
zuciyarta tana mai cewa "Ummi
da ta san ko waye da ba
wanda zai kaita jin dadi, shaaa,
zanyi surprising dinta ne" ta
wuce hankalinta kwance,
domin yadda take jin son
Nawap yasa ta rage fargaban
haduwa dashi.
Zaune yake ya bama kofa
baya, in banda kanshin
turarensa na Tom Ford Velvet
Orchid, babu komai da yake
tashi a wurin sai fa sautin T.V
inda ake nuna labaran kasa a
tashar TVC. Da sallama ta
shigo, kanta a kasa ba tare da
fargaba ko mamakin ganinsa
ba, haka ya dago kansa yana
kallon yanayinta, me sa bata yi
mamakin ganin shine ba? Anya
babu wani abu da ta sani
tuntuni? Kawar da tunanin da
yake yayi, sannan ya ansa
sallamar yayin da take
karasowa tsakiyar palon.
Kallonta yake tamkar yau
ce rana ta farko da ya fara
ganinta, tayi mashi kyau sosai
wanda bai taba tunanin tana
da shi ba. Nesa dashi ta
zauna, ta dago a hankali tace
"Ina wuni Yaa Nawap"
Cikin rashin kuzari ya ansa ta,
nan wani dogon shiru ya ratsa
tsakaninsu, muskutawa Nawap
ya yi, cikin k'arfin hali, sannan
yayi gyaran murya yace "ke
haka ake taran bako ko ruwan
sha babu?" Shiru tayi kaman
baza ta ansa ba, can dai ta
nisa tace "bakon nazo nema,
but unfortunately sai na ganka,
kunya ce ta hana ni tambayar
ko ka kasan inda yake?"
Ido ya tsare ta dashi har
saida ta gama maganarta, inda
ya cika bakinsa da iska, a karo
guda ya furzar dashi, ya rasa
ta ina zai fara mata bayani, ga
so da k'aunarta na matuk'ar
azabtar dashi, amma yana
tunanin halin da zai tsinci
kanshi matuk'ar bata ansa
tayin soyayyar shi a karo na
biyu ba.
Fuskantarta yayi, yayin da ya
dawo daga duniyar tunanin da
yake, cikin wata irin murya ya
kira sunanta "Firdausi" ta dago
a hankali ta yadda taga
fuskarsa ta san he's damn
ready nd serious. Domin tunda
take dashi sau daya ya taba
kiran ta da ainahin sunanta,
ranar da ta fara ganinsa a
duniya.
Kwantar da kai yayi, sannan
ya fara magana "Bazan so na
zama mai son kai ba, haka
zalika kada kiyi tunanin
dangantar dake tsakaninmu,
ina son ki dauka baki taba sani
na ba, ta yadda baza ki sha
wahala wurin yanke hukunci a
kaina ba. Shekaru ukku da
suka wuce na nemi sanin
takamaiman abinda ke
zuciyarki dangane da ni, amma
Allah bai nufa zan samu ansa
ta, ta inda tafiyar gaggawa ta
same ni, gashi kuma nayi
alkawarin bazan neme ki ba,
har sai ke da kanki kin neme ni
da ansar tambayar da na miki"
sai da ya dan tsagaita, yana
mai cigaba da kallon yadda ta
dukarda kanta, tana wasa da
yatsun hannunta, sannan ya
cigaba…
BA'A SHAN ZUMA… 102
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
"Ina mai rokon Allah yasa yau
ta kasance rana ta k'arshe da
zan san matsayina a wurin ki"
yayi shiru yana mai cigaba da
kallon ta yana kuma rokon
Allah yasa ya dace a wannan
rana.
Shirun da tayi har na tsawon
mintuna kusan bakwai yasa ya
cigaba da magana "idan har na
saka ki a rudani, ina son ki
gafarci zuciya ta wadda take
bugawa a ko wacce sa'a da so
da k'aunar ki, wadda take
azalzala ta, ta ke kuma hana ni
sukuni a duk tsawon shekarun
dana sanki, ba laifi na bane
Deedo, ba kuma ni na dorawa
kaina ba, Allah ne ya jarabce ni
da son ki, me sa baza ki
taimaki yayanki ba? Me sa
baza ki gane farin cikin da zan
samar maki ba, matuk'ar kika
yarda da ni a matsayin uban
ya'yanki, ina son ki sosai,
wanda bazan iya dainawa ba,
domin kuwa kece mace ta
farko da na fara so, haka kuma
kece ta karshen da zan tafi ga
mahaliccina da k'aunarta koda
baki yarda kin so ni ba."
Yana gama fadar haka ya
mike da niyyar fita, domin
zuciyarsa ta gama karyewa,
gashi Deedo ta ki tace komai,
asali ma ko kallon yanayin da
yake ciki bata yi.
Har sai da ya kai bakin kofa
sannan ta samu damar dago
da jajayen idanunta, wanda
suka rine da ruwan hawaye
tace "Yaa Nawap" juyowa yayi
da sauri jin raunanniyar
muryarta na kiran shi, ganin
hawaye na zuba daga
kyakkyawar fuskarta yasa yayi
saurin dawowa da baya yace
"no please lil sis, don't be like
this kinji, na fahimci kina son
Affan ko? Me sa zan shiga
rayuwarku, na hakura zan
danne son da nake maki,
amma bazan iya jurar ganin
hawayenki ba, it's ok kinji"
yayin da yasa hannu ya zaro
handkerchief ya mika mata.
Ansa tayi ta toshe bakinta
dashi, sannan ta saki kuka mai
sautin, wanda ya gigita Nawap,
har ma ya rasa ta ina zai
lallasheta, da ya san haka ne
da bai zo mata da maganar
nan ba.
Katse mashi tunani tayi ta
hanyar cewa "Yaa Nawap kaine
mutun na farko wanda ya kalle
ni a matsayin mutun kamar
kowa, kai ka daga darajata, ya
cika mani gurin rayuwa ta,
sannan kaine mutun na farko
wanda zuciya ta ta mace
saboda son shi, ban taba son
wani kwatankwacin son da
nake maka ba, amma na rasa
me sa baka fahimci hakan ba,
har kayi fushi da ni, tsawon
shekaru ka barni ina dakon
sonka ka manta da ni, me sa
Yaa Nawap? Kasan halin tashin
hankalin da na shiga?" Ta k'ara
fashewa da kuka mai tsuma
zuciyar masoyi, wanda yasa
Nawap dafe kanshi da duk
hannayensa biyu.
Ya ma rasa menene
yanayin da yake ciki, shin farin
ciki ne ko kuma haushin
kanshi yake ji yadda bai
fahimce ta ba tun asali. Kasan
carpet din ya zauna shima ya
dago fuskanta ya share mata
hawayen, sannan yace "I'm so
sorry lil sis, azaban kishi ne ya
hana ni fuskanta inda kika sa
gaba, I promise baza ki taba da
na sanin kasancewa tare da ni
ba, zan faranta maki dai dai
gwargwadon iko, zan kula
dake, in tarairaye ki fiye da
yadda ARCH. SADDIQ ya
tarairayi LAILA (Rabon ka ko
yana bakin kura na Chuchun
Gaye) zan shayar dake
madarar farin ciki fiye da
yadda FU'AD ya shayar da
MEELA (WATA RAYUWA) ki
yarda da ni my lil sis, ki bani
aron zuciyarki, ni kuma na
maki alkawarin I'll never ever
let yu down…."
BA'A SHAN ZUMA… 103
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Murmushi ta sakan mashi
yayin da hawayen suka cigaba
da zarya akan kuncinta,
"shhhh.." ta fada lokacin da
take dora dan yatsanta akan
bakinta, nan take yayi tsit, tare
da aika mata sakon kallo mai
alamar nayi missing dinki,
langabar da kai tayi, itama tana
kallonsa, sannan a tare suka
sa dariya kamar ba ita ce
wadda tasha kuka yanzu yanzu
ba.
Cikin dan k'ank'anin lokaci
suka dinga aika ma juna da
kalamai masu dadi da kwantar
da hankalin masoyi, har sai da
suka gama aminta da junansu,
inda daga k'arshe Nawap ke
tambayar ya akai bata yi
mamakin ganin shi yake aika
mata sakon text ba, nan ta fada
mashi tayi amfani da
TrueCaller ta gane shine.
Dariya yayi, sannan yace
"Ooops, na manta akwai
wannan fa" dariyan tayi itama,
gani take kaman ba Yaa Nawap
din da ta sani ba, ashe dama
ya iya soyayya?
"Tashi muje ka nema izini
wurin Ummi, dan idan ba kai
mata ba nima zan hakura da
kai" wara idanunsa yayi "da
zaki hakura ai da yanzu kin
mance dani, yarinya ko Ummi
bata yadda ba ni ba yadda za
ayi dani, dole a so ni,"
Sannan ya mike ya bi bayanta
tana dariya suka fito, suka
k'arasa cikin gidan.
Ummi zaune saman dining
table suka shigo fuskokinsu
dauke da murmushi, kallon
Nawap tayi tace "Kai kam ina
ka shige ina nemanka ka taya
ni cin abinci?" Sosa kai yayi,
yace "naje neman aure ne"
Ummi sake da baki tace "to fa!
Babbar magana"
Ganin Deedo na bin shi a
baya tace "ke kuma ina bakon?
Ko har ya tafi?" Dariya ta
kwace mata, ta karasa kujerar
da take kusa da ta Ummi ta
zauna, yayin da shi kuma ya
zauna a wadda take kallonsu,
tana kallon Ummi tace "ga
bakon na kawo ya gaisheki"
tana yi tana nuna Nawap da
yatsa.
Shiru Ummi tayi, yayin da
take k'are masu kallo duk
kowannensu da fara'a dauke a
fuskarsa, tace "kai ku dakata,
ban fa gane ba" duk suka sa
dariya, inda Nawap yace
"Ummi zaki bani autar taki ko
na nema wata?" Duk da kanta
ya kulle da sha'anin yaran
zamani, amma matuka tayi
farin ciki, taji dadi fiye da
misali, inda ta kai kallonta ga
Nawap tace "akwai sharudda
dai, wanda matuk'ar ka kiyaye
su to zan baka ita"
Ya buda ido yana kallon
Ummi, yace "tohm a jero su ina
ji" ya fada lokacin da yake sai
ta kunnensa garesu.
Dariya ya basu, dan haka suka
kyakyale gaba dayansu,
sannan Ummi tace "banda
yawan takuri, sannan bana son
yawan la6e, ana kiraye mun
auta, kuma idan ka shirya ka
turo da magabatanka dan dama
na gaji da ciyar da gauro a
gidan nan"
Sosai ya ji dadin
maganganunta, "zanyi yadda
kike so Ummin mu" ya fada
yana kallon Deedo da ta dukar
da kanta tana murmusawa…
BA’A SHAN
ZUMA…
104-106
BA'A SHAN ZUMA… 104
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Deedo wadda tunda aka fara
maganar kanta yake kasa, tana
jin wani sabon canji a jikinta,
domin yanayinta na yau, yasha
ban ban dana kullun. Mik'ewa
tayi ta zuzzuba masu abincin
cikin jin kunyar mugun kallon
da Nawap ya tsare ta dashi.
Bayan sun gama Ummi taga
abin nasu ba mai k'arewa
bane, dan haka ta wuce sama,
inda a zuciyarta take cewa "oh
ni Fatima, yaran zamani sai a
bar su, ko dan kunyar idona
ba'a ji, uhunmm" ta haura
sama, ta haye dan gadonta
tana tunanin yadda zata aurar
da ya'ya har biyu.
Deedo da Nawap wanda
soyayya tasa suka manta ko
sallar isha'i basuyi ba ne suka
ankare da lokaci, yayin da ta
sauke idanunta kan tafkekiyar
agogon bangon dake manne a
palon, k'arfe goma har da minti
ashirin da biyu (10:22pm).
Mik'ewa tayi ba wai dan ta so
ba, ta kalli Nawap wanda ya
marairaice fuska kaman zai
saki hawaye yana mata kallon
ban gaji da ganin ki ba. Alama
ta mashi da ido, abin nufin ya
kalla agogo. Wadda ke daure a
hannunsa ya duba, bai ma san
lokaci ya ja haka ba, dan haka
ya dan wara idanunsa, sannan
ya mike, hannuwansa duk
biyun cikin aljihu, ya kalli
Deedo yace "it's ok yan mata
na, ki shiga ciki, I'll call kafin ki
bacci"
Murmushin itama ta sakan
mashi, sannan ta juya tana
tafiya, sai da ta hau stairs din,
kafin ta juyo tace "don't keep
me waiting plz" cikin shagwaba
mai narkar da zuciya tayi
maganar, dan haka Nawap ya
sandare a wurin, ya kasa
motsa koda yatsan k'afarshi,
har ta haye tana mai dariya.
Girgiza kansa yayi, sannan
ya juya ya wuce side dinsa,
inda a zuciyarsa yake cewa
"tabbas ka so a so ka ma wani
babban abu ne mai tattare da
farin ciki a duniyar masoya"
* ***—-******
Soyayyar Nawap da Deedonsa
soyayya ce wadda suka
shimfid'a a kan gaskiya da
amana, soyayya mai cike da
so, tattali, da kuma kula da
junansu, wanda hakan ya basu
damar sanar da magabatansu
domin cika burin masoya.
A ranar yau, wadda tayi dai
dai da juma'a ishirin da ukku
ga watan ifirilu (23 Apr,) aka
sanya ranar auren Deedo da
Nawap dinta, wata ukku cif cif,
wanda ya kama sati daya dai
dai gama jarabawarta ta aji
hud'u (400L). Bayyana farin
cikin da masoyan suke ciki,
b'ata baki ne, domin ko suna
cikin tsananin farin cikin da ni
Lubiee ba zan iya fasalta shi
ba, lokaci kawai muke jira mu
sakata mu wala, sannan kuma
mu 6arje guminmu.
BA'A SHAN ZUMA… 105
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
BAYAN WANI LOKACI
A gajiye liss ta shigo gidan, ta
zube akan kujera tana kwala
kiran Saude wadda ta rugo da
dan saurinta tana cewa "sannu
da zuwa uwar dakina, ya
jarabawar?" Idonta a lumshe
tace "Alhamdulillah, taimaka
mun da abu mai sanyi, baki ji
ranar da na kwaso ba" "to, to
bari inzo" Saude ta fada,
sannan ta mik'e ta koma
kitchen din, ta dawo hannunta
dauke da dan tray, da jug, da
kuma cup a sama.
A gaban Deedo ta dire shi,
tace "kinyi sa'a ko, dazun nan
muka hada zo6on nan ni da
Hajiya, kinga har ya dau ra6a
kuwa" tsiyayawa Deedo tayi, ta
kai bakinta yayin da taji wata
nutsuwa ta sauko mata, ga
wani gard'i da dad'i da zo6on
ke da shi, sai da ta kara cika
wani cup din, ta sha kaman
rabi, sannan tace "lallai zo6on
nan yayi dad'i Saude, wai ina
Ummin take ma?"
"Tana ciki, ga dukkan alamu
sallah take"
"Ok, bara na shiga, nagode
Saude"
Yayin da ta mik'e ta haye
saman, ta wuce dakin Ummin
straight.
A zaune ta tarar da ita tana
duba wani littafi mai sunan
(You can be the Happiest
Woman in the world) na Dr.
A'id al-Qarni. Saida ta gama
karanta bayan littafin, sannan
tayi murmushi, ta zauna gefen
ta.
"Sannu da gida Ummi"
Da fara'arta ta dago, ta cire
medical glass din da yake
idonta, sannan ta kalle ta,
"Yawwa auta, ya exams din?"
"Alhamdulillah Ummi, amma fa
ta yau sai hamdala, ku dai taya
mu da addu'a"
"Ana ta yi ai, Allah dai ya baku
sa'a"
Tace "amin" sannan ta dukar
da kanta bakinta na motsi, da
alama akwai abinda take son
fada.
"Ya akayi ne amarya?" Ummi
ta tambaya, tana kallon ta da
alamar tsokana.
Rufe idonta tayi da duk
hannunta, tana dariya, sannan
tace "ehnmm, Ummi dama zan
ce ne dan Allah idan na gama
exams ina son zuwa ganin
Goggo, in masu bankwana"
Murmushin jin dadi Ummi tayi,
tace
"Ahaf, kin hutar da ni kenan,
dan ni ina nan na shirya irin
lallashin da zan maki akan kije
kuyi bankwana, dan ba dadi
haka kawai suji an miki aure,
ashe 'yar tawa mai hankali ce
da hakuri da kuma maida
komai ba komai ba, amma naji
dadin kasancewarki haka,
domin haka ake son dan Adam
ya kasance, duk wanda yayi
maka sharri, kai kuma ka saka
mashi da alkairi, sai kiga kai
kuma Allah yayi maka sakayya
ta wani 6angaren"
Hannunta ta rike, "Allah yayi
maki albarka Deedo, ya kuma
kare ki daga ko wane irin
sharri kinji"
Da murmushinta, ta ansa da
"amin Ummi, Allah yayi maku
sakayya da gidan aljanna
kuma"
"Amin, kinga next week zanyi
tafiya, kuma Hafsat (kanwar
Nawap) tace mun jibi zasu zo,
sai ku zauna dasu, ga Saude
kuma, idan kin gama exams, ke
kuma sai kuje da driver, nasan
kafin nan na dawo, zan zo sai
mu dawo tare, da su din ma,
tunda na san zasu zo bikin
suma"
"To shikenan, Ummi, duk
yadda kika ce haka za'ayi"
"yawwa autalle, tashi kije ki
danyi wanka ki huta kinji" ta
mik'e ta wuce dakin ta, sannan
Ummi ta maida tabaranta ta
cigaba da karatun ta.
BA'A SHAN ZUMA… 106
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Tana shiga, kiran Nawap ya
shigo mata, da murmushi ta
ansa wayar, suna firarsu ta
masoya, nan take shaida masa
zata je ganin su Goggo, yace
"yaushe kuma keda kike
exams"
"Sai na gama fa, kuma Ummi
ma tace naje ai" ta fada tana
tura bakinta gaba, kamar yana
kallon ta.
"To ke banda abinki, Ummi ce
mijinki ko ni? Idan nace a'a fa,
ya zakiyi?"
"Tafiya zanyi mana, tunda dai
Ummi ta barni, kai kuma sai ka
bari idan na zo gidanka ka juya
ni yadda ka so"
Dariya mai sauti ya saki, yace
"Yarinya kina da aiki, ai tun
yanzu zan fara ba sai kin zo
ba"
Ba tace komai ba, tayi shiru
tana saurarensa. Sai da ya
gama tsokanarta sannan yace
"I'm just kidding kinji, na san
by then na samu hutu, kinga
idan na zo sai muje tare kawai.
"Thanks hun" ta fada, bakinta
kunshe da murmushi, nan suka
cigaba da firan su har suka
gama, sannan ta mike ta fada
toilet.
* —****
Ranar da Ummi tare da
kanwarta zasu wuce Dubai,
domin hado lefen Deedo, da
kuma siyayyar wasu abubuwa
daga cikin kayan dakin ta, kiran
ta tayi, sukai sallama, inda ta
kara da cewar "duk in mun
dade, to sati guda ne, ke kam
ai jibi kike gama jarabawan
ko?"
Deedo ta girgiza kai, Ummi
tace "yawwa, kinga washegari
sai ku wuce da driver, idan na
dawo na dan huta, zan zo sai
mu dawo tare"
"Ya Nawap yace zai zo sai
muje tare wai"
"To ai shikenan ma, amma
abinda za ayi shine, to ku tafi
da Hafsat da yaranta, su sai su
dawo tare da shi, ke kuma su
baro ki can"
"To shikenan Ummi, Allah ya
tsare, ya kuma dawo daku
lafia"
Tace "amin" yayin da ta mika
mata kudi, tace "kya yi masu
tsaraba."
Gaba dayansu suka fito
domin yi masu rakiya, yayin da
driver ya dauki su Ummi zuwa
Abuja, kasancewar ta can zasu
tashi.
Bayan sun shiga Abuja,
waya sukai ma Nawap, yaje ya
samesu, nan sukai bankwana,
yayin da shi kuma ya dauko
hanyar Kd, tare da driver,
zuciyarsa fari kal yana ta
faman sharta gudu kaman zai
tashi sama.
Deedo wadda tuni suka saba
da Hafsat, tare suka shiga
kitchen suka cigaba da tanadar
mashi dad'ad'an abincin kala
kala.
BA’A SHAN
ZUMA..107&108
BA'A SHAN ZUMA… 107
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Bayan sun gama ta wuce ta
fesa wanka, ta dau gayu na
musamman domin taryar rabin
ran nata.
K'arfe biyu da kwata dai dai
suka iso gidan, da sallamarshi
ya shigo palon babu kowa sai
Mahmoud yaron Hafsat yana
kallon cartoon a MBC3. Da
gudu ya taso ya rungume
Nawap yana cewa
"ga Uncle ga Uncle."
D'aga shi sama Nawap yayi,
yana fadin "my boy, ka zama
babban mutum"
Dariya ya kyalkyale da shi,
"sosai ma, har na kai nursery 2
fa uncle"
"Smart boy" Nawap ya fada
yana dariya, sannan ya sauke
shi, ganin Deedo na saukowa
fuskarta kunshe da wani
murmushi na ban mamaki.
Karasawa yayi inda take tsaye
ta nannade hannayenta, ya
kalleta yace "yan mata na,
yakike?"
"Ina wuni" ta fada, yayin da ya
ansa a daburce, "na same ku
lafia?"
"Lafia lau, ya hanya?"
"Alhamdulillah, ina ta sauri na
zo nayi tozali da abin k'aunata
"
Rufe fuskarta tayi, alamar
kunya, tayi gaba tana cewa
"muje ka ci abinci, dan na san
yanzu haka ko breakfast baka
yi ba"
Bayanta ya biyo yana cewa
"banda abinki waye zai ba
gauro abinci"
Dariya tayi lokacin da suka iso
kan dining table din, sai da ta
rage muryanta, sannan tace
"just two weeks ya rage, ka
daina zama da yunwa in sha
Allah"
Ta juya ta cigaba da serving
dinshi, inda shi kuma yana
murmushi yace "I trust my
baby doll"
Ta kalle shi ta murmusa,
sannan ta mika mashi plate din
abincin, ta wuce kitchen domin
kwaso drinks.
A haka Hafsat ta tarar dasu
yana cin abincin, yayin da
Deedo ke zaune gefenshi suna
tadinsu cikin jin dadi.
Suka gaisa dashi, yana
tambayar
"ina mama small" tace
"dak'yar na lallabata, tana
sama tana bacci."
Sannan ta wuce cikin palon
inda Mahmoud yake a zaune.
Tunda Nawap yazo kullun
suna manne da Deedo, shi ke
kaita skool, sannan ya jirata
office din Dr. Kashim, har sai
ta fito exams, sannan ya dauko
ta su dawo gida kullun, har
zuwa yau da take gamawa.
A hanya take ce mashi
"Ummi ta fada maka da su Yaa
Hafsat zamu tafi?"
"Me zasuyi mana ne in mun
tafi dasu? Me sa Ummi take
mun haka, bata son ina
ke6ewa da matata" ya dan ja
tsaki, ya kara gudun da yake,
yace "ke kuma me kika ce
mata?"
Dariyar da take ta dan
tsagaita, tace "ni har na isa
ince wani abu ne bayan Ummi
ta gama yanke hukunci, lallai
ma"
"Duk ke kika ja mana ai da
kika fada mata"
"Zan bi wani ne ba tare da
sanin Ummi na ba aka fada
maka" tana yi tana kallon
yadda yayi kicin kicin shi dole
ga wanda aka shiga hakkinsa.
"Zaki maimaita ranar da kika
zo hannuna yarinya, dan sai
kinyi wata biyu baki ga Ummin
taki ba" ya fada a dai dai
lokacin da suka iso kofar gida,
ya fara danna horn kamar
wanda ya d'auko majinyaci.
Ita dai dariya kawai take,
yana yin parking ta fito zata
shige, yace "wa kika bar ma
wannan tilin books din naki?"
"Wa fa in ba mijin yar auta
ba" ta shige tana ta dariyar
mugunta.
Yayi kwafa, ya kwashi k'atin-
k'atin din text books din har
guda ukku, shi kanshi sai da
hannuwansa suka k'age, ya
zube mata su a palo, yana
banbami "koma ya ake tana
daukan books din nan, gata dai
abu kamar a karya ta"
Mahmoud yace "uncle kai da
wa kake fada?"
Yace "wannan yar siririyar
auntyn taka mana, ta sanya ni
daukar books masu nauyi"
Yayi dariya, yace "ai idan ta
dauka zasu fadar da ita ne shi
yasa, kai kuma kana da k'arfi
kaga"
Shafa kanshi yayi, ya wuce
kitchen ya dauka robar ruwa,
sannan ya wuce side dinsa.
[24/04 21:45] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA…
108
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
K'arfe goma dai dai na safe,
kowa ya gama shiryawa tsab,
suna zaune a palo suna jiran
fitowar oga Nawap wanda yake
ta faman cika yana batsewa
shi dole an takura masu, za'a
hana su sakewa shi da Deedo.
Karasowa yayi, ya dau wanka
cikin farar gezna, hularshi da
takalminshi har ma da agogo
duk bak'ak'e, yana ta kanshin
Tom Ford Velvet Orchid,
Mahmoud kawai yai ma dariya,
ya kama hannunsa suka fita.
Deedo da Hafsat da suke
kunshe dariya suka kyalkyale,
sannan Deedo ta sa6i mama
small suka fito, yayin da Saude
take kwaso kayan da zasu tafi
dasu tana lodawa a boot.
A gaba suka zauna ita dashi,
sai mama small a hannunta,
yayin da Mahmoud da Hafsat
suke a baya. Haka suka fara
tafiyar kamar kurame, in banda
Mahmoud da mamah da suke
yan surutansu na yara.
* ********
K'arfe d'aya na rana Nawap
yayi parking motarsa a kofar
wani kwarmad'ad'd'an gida
wanda yake da tabbacin tabbas
nan ne gidan Goggo, domin ko
ba zai taba manta gidan da ya
fara ganin mamallakiyar
zuciyarsa ba.
Kallon Deedo yayi, yace
"kamar munyi batan kai
ko?"
"Anya kuwa?" Bari dai in shiga
mu ga"
Ta 6alla murfin motar ta fito,
yayin da shi ma ya bude nashi
kofar ya bita a baya.
Cikin gidan wanda ga
dukkan alamu rabon da ya ga
shara akalla anyi shekara
hud'u, domin ko yadda kasan
kango, haka bola ta samu wuri
ta basar, suka kutsa kansu,
Nawap ya kalle ta
"Bana tunanin akwai dan
Adam din da yake rayuwa a irin
wannan wurin, fito mu shiga
makwabta mu tambaya ko sun
koma wani wuri ne"
Basu ankara ba suka tsinkayi
murya daga cikin dan akurkin
dakin da Deedo take da, wanda
shi kadai yayi saura a cikin
dakunan da suke gidan, domin
kuwa sauran duk sun rufta,
kana iya hango komai daga
inda suke a tsaye.
"Wane dan banzan ne nan?
Iyii? Ko bakwa ji na ne
la'anannu"
Ta fara laluben sandarta,
dakyar ta dafa bango ta mik'e
tsaye, tana bin bangon ba tare
da sanin ta ba ta taka wani
kwano, aiko ba tare da 6ata
lokaci ba ta fadi kasa, ji kake
wani rigijib!!!
Nawap da Deedo da suke
tsaye bakin dakin suka yi
saurin kutsa kai ciki, amma
wani mahaluk'in k'arni tare da
wani gagarumin wari ne suka
yi ma hancinsu sallama nan da
nan suna rige-rige suka yo
waje da gudun bala'i, Nawap
ya rik'e cikinshi wanda yake
murd'a mishi, nan take ya fara
shek'a amai ba k'akk'autawa…
"Allah dai ya tsine muku, wai
su uban waye a nan?" Ta
cigaba da laluben inda ta
wurga sandar, ko Allah zai
taimaketa ta fita ta warci daya
a cikin irin yan iskan yaran da
suke shigowa suna tsokanarta
ko wacce rana.
(Nayi iya kokarina na karasa
labarin nan yau, amma hakan
bai samu ba, I promise yu
zuwa gobe in sha Allah.
Thanks y'all for the love. I love
yu too)
BA’A SHAN
ZUMA…
109-111
BA'A SHAN ZUMA… 109
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Hawaye masu azabar zafi suka
gangaro a fuskar Deedo ganin
halin da kanwar mahaifinta ke
ciki. Hannu tasa ta share, ta
juya tana kallon Nawap wanda
yake goge bakinsa da
handkerchief, karasawa tayi,
gabanshi
"Sannu Yaa Nawap" ta fada
yayin da take waige waige ko
me take nema,
"Kaje waje, bari nayi magana
da ita"
Goggo wadda ta rarrafo ta turo
kanta kofar dakin, tace
"Wai muryar su waye nake
ji nan? Iyii? Ko baza kuyi
magana bane tambadaddu
ya'yan fata, Allah dai ya tsi… "
Nawap ya katseta ta hanyar
cewa,
"Goggo Nawap ne, wannan
kuma Deedo ce, dago ki ganta"
"Deedo? Nawabu? Ku ne? Ko
dai tsinannun ya'yan unguwa
ne suke tsokanata"
Ta fada yayin da ta dago kanta,
ko Allah zai sa ta hango
kyallin wani abu wanda zai
tabbatar mata da cewar su din
ne.
A tare suka toshe bakinsu da
hannu, suna fadin
"innalillahi wa inna ilaihir
raji'un!
Goggo!"
Ganin kwantsa mai kama
da mugunya, har da wasu yan
tsutsotsi suna fita daga idanun
Goggo, idon ya ca6e, ya
cakwale, Allah kadai ya san iya
shekarun da ta dauka tana tare
da wannan azabar.
Lalube ta cigaba da yi, inda
ta jawo 'yar k'afarta guda daya
da tayi mata saura, ta fito da
ita wajen dakin dak'yar,
"'Ya'yan nan ku fada mun
gaskia, Deedo ce wannan a
gaba na da gaske?"
Tasa hannu tana lalube ko
zata samu damar ta6a Deedon.
"Nice Goggo, wai me yake
faruwa da ke ne? Bakya gani
ne ko ya akayi?"
Kuka mai sauti Goggo ta
saki, sai dai kash, kukan babu
ko alamar hawaye, amma duk
wanda ya ganta zai tabbatar
kukan nadama Goggo take
rerawa.
"alhakinku ne yake bibiyata
Deedo, dake da malam Ilu,
wanda bakin cikina yayi
sanadiyyar barin shi duniya, na
shiga ukku ni Batula,"
Abinda Goggo take nanatawa
kenan, yayin da ta dauki
hamnuwanta ta dora bisa kai,
tana kurma ihu kamar
mahaukaciya.
Ihun da Goggo ta kurma,
shi ya jawo hankalin su Hafsat,
da Mal. Labarin makwabcin
Goggo wanda shi kadai ne
mutumen da ya rage wanda ke
taimaka mata a unguwar,
kasancewar kowa ya san bakin
hali da bala'i irin na Goggo,
shi yasa babu mai kallon inda
take, anan inda take a zaune
zata yi kashin ta da fitsari,
haka kuma idan malam
Labaran ya miko mata dan
abinci, anan din dai zata cinye
shi, ba tare da wanke hannu ko
kashin da yake jikinta ba.
Da azama suka yo cikin gidan,
ganin yanayin yadda wurin
yake yasa Hafsat dakatawa,
hannunta rik'e da na Mahmoud,
yayin da Mal. Labaran ya
karasa yana fadin
"Samari daga ina? Lafiya
kuwa?"
"Lafiya lau mal., ina wuni"
Cewar Deedo, inda shi kuma ya
cigaba da kare mata kallo
kamar ya santa.
"Deedo ce" ta fada tana kallon
goggo,
Nan ya fara salati yana
sallallami
"Deedo? Ina kika shiga?
Wanene wannan din shi
kuma?"
Anan suka gaisa da Nawap, yai
mashi bayanin kanshi, mal. Ya
kara da tambayar "kai kuma ina
ka santa?"
Nawap wanda baiyi kasa a
gwiwa ba ya labartawa mal.
Yadda akai ya san Deedo, har
ma da yadda akai ya tafi da ita.
Goggo wadda ta daskare tun
lokacin data tabbatar da Deedo
din dai ce a wurin, ta kara
kurma wani sabon ihun, a
yayin da Mal. Labaran ya
kwashi sabon salati yace
"Eh lallai dole kike shiga
wannan halin Batula, ka ganta
nan" ya fada yana kallon
Nawap tare da nuna Goggo da
yatsa, yace
"Wannan matar bayan tafiyar
Deedo, duk wanda ya
tambayeta ina yarinyar nan
take, ce mashi take ta tafi
yawan karuwanci, ashe ke da
hannunki kika dauki diya kika
bayar, chabdi! Lallai Allah yana
son ki Batula, tunda har ya
baki damar sake ganin Deedo
don neman gafararta"
Cigaba da jinjina kai yayi, ko
a film bai taba jin irin wannan
tsantsan rashin imanin na
Goggo Batula ba.
[26/04 01:21] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 110
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Deedo wadda take shar6ar
kuka domin jin bayanin mal.
Labaran nan da nan taji wata
sabuwar tsanar Goggo ta karyo
mata, ba don kanwar ubanta
bace, da babu wani abu da zai
kara hada su, duk uwar azabar
da ta gana mata bata isheta
ba, har sai da ta zubar mata da
duk wani mutuncinta daga idon
mutanen garin.
Nawap ne ya lallabata har tayi
shiru, sannan ya kai dubansa
ga mal. Labaran wanda har
yanzu bai daina mamakin
makirci da mugun hali irin na
Goggo ba,
"Mal. To ita menene
musabbabin dawowarta haka?
Ina yaranta suke ne basu kula
da ita?"
"Chabdi! Dogon labari
kenan,"
Cewar mal. Labaran, sannan ya
cigaba
"Abinda yayi sanadin
dawowarta haka baya rasa
nasaba da dan ta shehu,
wanda tun yana dan shekara
sha biyar ya zama tataccen
dan daba, inda ya shiga wata
kungiya ta wasu mutane masu
yanka mutun su gudu. Haka ta
faru da shi bayan ya soka ma
wani yaro wuka a ciki, ya gudu
ya bar garin, yan sanda suka
nemeshi suka rasa, har suka
kame ita Batular, inda wani
bawan Allah da bata san ko
wanene ba yayi belin dinta, to
bayan an sako ta daga caji ofis
din ne ta taho gida mota tayi
ciki da ita, wanda hakan yayi
sanadiyyar rasa kafarta guda ta
dama"
Mal. Labaran ya dan
tsagaita, sannan ya dora,
"To ita kuma waccen Hadizar,
babbar 'yar tata kenan, da tana
kula da ita, daga k'arshe sai
abin ya dawo kamar ta dan
samu ta6in hankali, kullun in
banda kuka da kiran shehu
bata da wani aiki, nan zata yi
kashi, tayi fitsari, bata iya
motsawa ko kadan, ana haka
duk Hadizar na taimaka mata,
kwastam, sai aka wayi gari aka
ga Hadiza da katon ciki wanda
babu wanda ya san inda ta yo
shi, kuma ita dai ba aure akai
mata ba, nan fa yaran unguwa
suka dinga jifarta, suna
zaginta, itama daga nan aka
nemeta aka rasa. To ni dai a
ganina kukan rashin ya'yanta,
da kuma iftila"in da ta jefa
mutane, shine yayi sanadiyyar
rasa ganinta, ana haka kowa ya
watse babu ko wanda yake
kallonta, sai fa ni din nan, nima
dan dai kawai in sauke hakkin
makwabtaka, amma in ba haka
ba, babu abinda zai sa na kalli
mai mummunan hali irin na
wannan matar"
Ya karasa maganar, yana
mai nuna ta da yatsarsa.
"Hasbunallahu wa ni'imal
wakil"
Shine abinda Nawap yake
maimaitawa, yayin da yayi
saurin dauke idonsa akan
Goggo, wadda yake jin kamar
ya shaketa ya hada da bango
ta mutu kowa ma ya huta.
"Sai ki nemi yafiyar yarinyar
nan, tunda Allah ya taimaka
miki gata a gabanki a karo na
biyu"
Cewar mal. Labaran kenan
yayin da yake kallon Goggo.
"Na yafe mata ni kam, mal.
Ko yadda Allah ya mayar da ita
ai ya isa ishara gareta, da duk
wani mai hali irin nata, fatan
dai Allah ya yafe mana baki
daya"
Deedo ce take wannan jawabin
a lokacin da take share kwallan
idanunta.
"Amen" duk jama'ar wurin
suka ansa da.
Goggo dai banda wasu
surutai, da wasu yan bige bige
kamar wadda sauro ke cizo
babu abinda takeyi, sai kuma
lokaci zuwa lokaci kaji ta
kurma wani gagarumin ihu,
babu Allah, bare kuma salatin
annabi a bakinta.
Kofar gidan suka fito gaba
dayan su, in banda ita da bata
iya takawa sai dai
rarrafe.
Gaban mota Nawap ya
bude, ya fito da kudi wanda
bansan adadinsu ba, mik'awa
mal. Labaran yayi,
"A taimaka a gyara mata
ginin nan da ya rufta, sannan a
dinga sai mata abinci, inda hali
a samu wanda zai rinka
tsabtacce mata wurin, ni zan
rinka biya in har an samu
wanda zaiyi hakan, mun gode
mal., Allah ya kara girma, ya
kuma baku ladar abinda kuka
yi"
"Amin" ya fada, sannan
sukayi musayar number shi da
Nawap, ya wuce zuwa cikin
gidan shi, inda shi kuma ya kai
kallonsa ga su Deedo da sukai
jugum,
"Sai ku shiga mu wuce"
Babu gardama, duk suka
shige suka dau hanyar
komawa.
Sai da suka shiga Bauchi
sannan suka tsaya, domin
neman abinda zasu ci, anan
Deedo ta kira hally, tai mata
kwatacen gidanta suka je, nan
ta tarar da ita har da dan
yaronta mai shekara daya da
rabi, suna cikin fira take shaida
mata halin da Goggo take ciki,
addu'a dai sukai mata, inda
daga bisani ta fada mata
bikinsu kwana goma masu
zuwa. Hally kuma tai mata
alkawarin zuwa in har Allah
mai kowa mai komai ya bata
iko, sukayi sallama, sannan
suka dau hanyar Kaduna.
[26/04 02:05] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 111
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Har suka iso gida firar da suke
ta irin mutane masu halayya
irinta Goggo ce, Hafsat wadda
abin ya zama sabo a wurinta
tace
"Allah kenan, buwayi gagara
misali, yanzu ji yadda matar
nan ta dawo, ko duniyar da
take ma hadama ta juya mata
baya, suma ya'yan da ta
musguna ma wasu saboda su
sun gudu sun barta, kai Allah
dai ya sa mu cika da kyau da
imani,"
"Amen" suka ansa da shi,
lokacin da suka iso kofar
gidan, ana ta faman kwalla
kiran sallar maghriba.
* *******
Kwana ukku da dawowarsu,
su Ummi suka dawo, inda tayo
siyayya ta ban mamaki, sun
hado mata lefe dai dai
gwargwado, babu karya, babu
kuma karanta a ciki, sai dai
san barka, haka kayayyakin
daki ma sun siyo dai dai
iyawarsu, inda suka karasa
siyen sauran anan gida
Nigeria.
Bayan Ummi ta natsu, ta
huta duk hankalin kowa ya
dawo jikinshi, anan take
tambayar Deedo yadda akai
bata je Ningin ba, ta kara da
cewar
"Ba dai mutumin can ne ya
hure maki kunne ba?"
Ta fada tana kallon Nawap,
Murmushi Deedo tayi, tace "ko
daya Ummi, munje ai"
Nan ta labarta duk abinda ya
faru, bata rage komai ba,
Salati Ummi tayi, sannan ta
kara da "Allah kasa my gama
da duniya lafia"
Suka ansa da amin gaba dayan
su, inda suka d'auko wata firar,
wadda yawanci duk labarin
yadda za'a tsara bikin ne suke.
Biki dai sai matsowa yake,
inda yau rage kwana hud'u a
fara. Kasancewar Deedo bata
da tarkacen kawaye, hakan ya
bata damar kammala duk wani
rabon invitation da zata yi,
wanda dama duk course mates
dinta ne ta gayyato, sai fa yan
mutanen da baza a rasa ba,
wanda suke gaisawa a
makaranta.
Hakan ya bata damar
natsuwa wuri guda, tana
daukar gyara a wurin matar da
Ummi ta dauko takanas, daga
Niger republic. Haka Hafsat ma
ba a barta a baya ba, itama da
nata sinadarin gyaran na
daban, wanda ya kasance
tsakanin ta da Deedo ne, sirrin
kissa da kisisina, da iya rik'e
miji kawai take dora mata,
yayin da Deedo take kwashe su
a kwakwalwarta kamar tana
rubutawa. Domin ko zamanin
nan dai sai da kissar, amma
sai kaga mace a harbutse, ko
magana bata iya ba, sai kuma
idan mijin ta ya kyallo wata
abun ya zama bala'i, a daure a
koyi sirrikan mazan aure
yanuwana.
Rana bata karya, wai sai dai
uwar diya taji kunya! Inji
Hausawa. Haka aka fara bikin
Deedo da Yaa Nawap dinta,
amarya sai kyalli take tasha
dilka, tayi kyau har ta koshi da
shi.
Daga su sai su suke bikin
nasu, dangin Maman ta ne, sai
kuma dangin baban su Nawap,
sai 'yan gayun kawayenta
wanda duka duka basu wuce
mutun sha biyar ba, biki ne
suke hankali kwance ba tare da
hayaniya ba, babu wata bidi"a,
illa kyakkyawar dinner da za
suyi a gobe, sai kuma daurin
aure.
Amarya ce ta fito cikin light
brown din gown mai asalin
kyau, wadda ta dace da kirar
jikinta, yayin da KHADY'S
MAQUILLAGE ta gwangwaje ta
tsararran make up mai daukar
hankali. Tayi kyau dai dai
misali, haka angon ya fito a
cikin danyar farar shaddar
Sheraton, wadda taji lafiyayyan
aiki da light brown din zare,
hularshi da takalmansa, gami
da agogonsa duk light brown
din, sunyi kyau kamar a sace.
Bayan sun shigo hall din Kabir
Gymnasium, inda ya kasance
can ne aka tanada domin
gabatar da dinner, nan fa aka
fara sakin flash, masu video
coverage suma suka cigaba da
dauka, yayin da zaka hango
farin cikin da yake kwance a
fuskar Ummi domin ganin
wannan kyakkyawar rana.
Haka aka cigaba da
rakashewa, ana gwangwajewa
yadda ya kamata, har aka gama
lafia, kowa ya kama gabansa.
Washe gari da misalin k'arfe
1 na rana aka Daura auren Dr.
NAWAP KHAMIS, & FIRDAUSI
KABIR SANI, akan sadaki mafi
daraja, wanda ya ta'allak'a
akan koyarwa ta ma'aiki
(S.A.W).
Bayan daura auren da
misalin karfe shidda na yamma
aka dauki amarya sai gidanta
dake Sultan Road. Komai ya ji,
babu abinda Ummi bata yi ba,
sai kuma fatan zuri'a mai
albarka.
Kwanansu biyu a Kd, sannan
suka tattara suka wuce Abuja,
kasancewar hutun da Nawap
ya dauka ya kare. Rayuwarsu
abin sha'awa, soyayya suke ta
ban mamaki, kowa kokari yake
yaga ya faranta ran dan
uwanshi, dan haka suke zama
na jin dadi da salama.
Satinsu biyu a Abuja su
deedo suka koma hutu, bata da
yadda zata yi, dole ta dawo Kd,
da sabuwar Mercedes-AMG
dinta wadda Nawap ya bata
tukwicin amarci.
BA’A SHAN
ZUMA…
K’ARSHE
BA'A SHAN ZUMA… 112
NA LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
®NWA
Shi da kanshi ya tuko su,
gidansu suka zarce ko da suka
shigo Kd, wanka sukai suka
gabatar da sallar maghriba
wadda tai musu a hanya,
Deedo ta fito cikin wani skinny
long skirt, da yar top dinta,
gashinta, ta tara shi wuri daya
ta daure, kitchen take k'ok'arin
shiga domin ta sama masu
abinci, a dai dai lokacin Nawap
ya fito palon shima cikin blue
din jeans da red din t-shirt,
gabanta ya karaso, ya mika
mata agogon dake hannunsa,
sannan ya miko hannun, yana
kallon ta.
Ansa tayi, tana tura baki tace
"Abinci fa zan girka mana,
kuma ka zo zaka tsaida ni"
Dariyar yadda tayi da bakinta
yayi,
"Gobe kaman haka baza ki
ganni ba, balle har na tsaida
ki"
Ya fada yana langabar da kai,
Itama fuskan tausayin tayi,
tunowar da tayi gobe fa ita
kadai ce; babu yayan ta.
"Yi sauri dauko hijab dinki
muje gaishe da Ummi, can sai
mu samu abinda zamu ci"
Ya fada yana kallon console
mirror din dake makale a palon,
yana gyara collar rigarsa.
"Da gaske Yaa Nawap?" Ta
fada cikin zumudi.
"Zan ce na fasa ko ki wuce
kizo mu tafi"
Da dan gudu ta shige daki tana
fadin "I'm sorry Mon amour",
Bata wani dade ba ta fito
sanye da dogon hijab har
gwiwanta, suka rufe gidan suka
shige mota sai gidan Ummi.
Taji dadin ganinsu sosai, sun
kuma yi sa'a tana zaune a
dining table tana cin abinci,
dan haka ba tare da bata lokaci
ba suka zauna suma, Deedo ta
zuba masu, suka cigaba da ci
suna fira.
Sai wurin goma da rabi,
sannan suka yi mata sallama
suka wuce gida.
A palo suka zauna, firar
yadda zasu yi missing juna
suke ta yi, a haka har sha daya
da rabi, inda Deedo ta fara
hamma, bata ankara ba ta
bingire a wurin ta cigaba da
bacci. Juyowar da Nawap zai
yi ya ganta sai bacci take,
murmushi yayi, don ya zata
baccin karya ne, saboda haka
take mashi, sai ya dauke ta ya
kaita daki sannan ta mik'e.
Shigewa yayi ya gama shirin
baccinsa, ko da ya fito dai a
haka ya tadda ta, dan haka ya
sa6i abinshi suka wuce dakin
baccinsu.
Tun karfe biyar na asuba
suka tashi, wanka suka yi, tare
da alwallah sannan ya ja su
sallah, bayan sun gama suka yi
adduoin da suka saba, Nawap
ya mike ya koma gado, inda ita
kuma ta wuce kitchen ta shirya
breakfast mai sauki, sannan ta
shirya jikinta da jeans wanda
ya matse ta tsaf, ta samo top
dinta mai fadi ta dora, tayi
kyau sosai, sannan ta matsa
inda yake a kwance, lokacin
karfe bakwai dai dai, fuskarsa
take shafawa har ya buda
idonsa,
"7:am har yayi kana bacci, ka
manta akwai aiki yau ne? Nd
flight din karfe takwas zaka bi"
Ya mike tare da salati,
"Ai duk lefinki ne"
Ya fada yana cire kayan jikinsa,
Ta mika masa towel, "je ka
shirya idan ka fito sai kayi
banbanmin" ta fada tana fita
daga dakin.
K'arfe takwas saura suka fito,
jikinta sanye da doguwar
abaya, ta yane kanta da gyalen,
ita ta kaishi har airport, sannan
ta dawo, tana mai cike da kewa
da maraicin mijin ta.
Daga nan ita ma skool ta
wuce domin sun fara lectures
tun satin da ya wuce.
BAYAN SHEKARA HUD'U
Deedo ce ta fito daga babban
asibitin gwamnati na garin
Kaduna, atamfar super wax ce
jikin ta dinkin riga da skirt, sai
dogon hijab dinta, hannunta na
dama sagale da farar riga ta
likitoci (lab coat), yayin da
dayan hannun yake dauke da
jaka, da kuma katon littafin
(text book) mai hoton
kwakwalwar dan Adam a jiki.
Gaban motar ta kirar BMW
M4 ta isa, ta juye tarkacen
hannunta a baya, sannan ta
bude bangaren driver ta shiga
ta bata wuta, ta wuce
hankalinta kwance.
Cikin unguwar rimi ta nufa
dai dai kan alkali road, naga
tayi parking gaban wani asibiti
wanda aka rubuta TAIMAKO
SPECIALIST CLINIC, lab coat
dinta ta buda bayan motar ta
dauka, yayin da ta shige cikin
asibitin kasancewar wayar da
aka mata kan tayi sauri tana da
marassa lafia. Cikin k'warewa
take bin gadajen marassa
lafiyar, a bayanta kuma nurse
ce tana dauke da file na
kowanne patient a wurin.
Gadon wani dan tsoho ta isa,
wanda yake fama da ciwon
zuciya, ta duba file dinshi, ta
juyo da kallonta gare shi
"Baba akwai gwaje gwaje da
zanyi maka, akwai kuma na jini,
sannan kuma zan duba bugun
zuciyarka, amma sai kayi
hakuri fa"
Cikin ciwo tsohon yace
"Kuma duk a nawa zakuyi
wannan aikin? Ni fa wlh ba
kudi ne da ni ba, sai da nace
su kaini na gwamnati, amma
suka kawo ni nan, ni ban san
ya zanyi ba 'yar nan"
Da murmushinta, ta kalle shi
"Kar ka damu Baba, domin
kuwa babban dalilina na bude
asibitin nan ba komai bane, sai
dan na taimakawa marassa hali
irin ka, in sha Allah za ayi
komai, ba kuma tare da ko
sisinka ba"
Ta mik'awa nurse din file
dinshi, sannan ta wuce zuwa
gado na gaba, haka har ta
gama round dinta, ba ita ta bar
asibitin ba sai misalin karfe
biyar na yamma.
[26/04 09:40] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 113
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Tana shiga gidan ta zube a
palo saboda tsabar gajiyar da
ta kwaso, hannuwanshi taji ya
ziro ta kafadarta yana danna
mata su a hankali, lumshe ido
ta fara yi, tana jin tamkar a
mafarki,
"Likita bokan turai" shine
abinda ta ji an fada, wanda
yasa tayi firgigit ta juyar da
kanta tana kallonsa.
"Yaushe a gari?"
Ta fada tana kare mashi kallo,
murmusawa yayi,
"Ko 30 mins banyi da
shigowa ba, na gaji da missing
matata bazan iya daurewa har
sai Friday kafin na ganta ba"
Ya zagayo inda take a zaune
ya zauna a gefenta,
hannuwansa cikin nata.
Bude bakinta zata yi magana
wata kyakkyawar yarinya mai
asalin kama da Nawap, ga dan
banzan wayo, duk da
shekarunta basu wuce biyu ba,
ta rugo da gudu ta fada kanta,
tana shashshekar dariya.
"Mammy sannu da zuwa" ta
fada cikin maganarsu ta yara,
lokacin da ta mik'e ta rungumo
wuyanta, tana mai nuna farin
cikin ganin Mammyn tata.
Sama Deedo ta daga ta,
tana fadin
"Thank you Ummina "
Nawap ya jawosu jikinshi
yace "Ummi har kin manta da
ni ko, dan kinga mammy ko?
Gobe ma zan koma bazan kara
wasa dake ba"
Suka kyalkyale da dariya ita
din da Deedo, yayin da ta
zaunar da ita a tsakaninsu, ta
mika hannu ta rungumo
Nawap, shima haka yasa
hannunsa ya k'ank'amesu yana
jin soyayyar matarshi, da tilon
'yar tasa, har cikin birnin
zuciyarsa.
ALHAMDULILLAH, anan na
kawo karshen wannan labari,
kuskuren da nayi Allah ya
gafarta mana, Allah kuma ya
amfani abinda na fada dai dai,
ya bamu ikon amfani da
darasin da yake ciki.
This is a dedication to a sis
from another mother (FEEDO-
DEEDO) thank you 4 been
there always.
Special thanks to Aysha
Chuchu, Jam33la & Ummu
Ahmad, 4 loving this story like
no one.
Nagode kwarai da hakurinku
akan jinkirin da aka samu kafin
kammaluwar wannan labari. Ku
cigaba da kasancewa tare dani
a labarina na gaba wanda ya
ansa sunan K'ADDARAR
AURENA!
Lubabatu Maitafsir & Benaxir
Omar muke yi maku fatan
alkairi a koda yaushe.