1, Abinci da mace zata ci kamin jima'i- Bako wani irin abinci mace ya kamata taci ba kamin tayi kwanciyar jima'i da mijinta, domin da akwai wasu abincin da basu dace mace ta cisu ba daf da lokacin da zata soma jima'i. Domin wasu abincin suna iya ragewa mace ni'imarta ko kuma su kwantar mata da sha'awarta na jima'i, don hake ne ya zama dole mace ta san irin abinci da ya kamata taci kamin gudanar da jima'i.
Abinci mai nauyi bai kamci mace ba a awanni hudu ko uku kamin ta soma jima'i a cewar Anna Robensun wata mai illimin girke-girke. A nazarinta abinci mai nauyi yakan jawo kasala ga mace kuma ya hanata kuzari a lokacin jima'i, inda ta bada shawarar cewa duk matar data san da akwai aikin kwanciya na jima'i a gabanta to dole ne ya kasance awanni 6 kamin lokacin bata ci abinci mai nauyi ba.
Dukkannin masana illimin girke-girke da kayan makulashe sun nuna cewa, mace kamin jima'i abincinta kada ya wuce abinci mara nauyi, kuma su kasance masu ruwa-ruwa ba busassu ba.
Abinci irinsu taliya mai ruwa-ruwa, fatai-fatai da ire irensu sune abinci da mace zata ci kamin jima'i. Haka kuma kifi ko soyayyen kwai mai ruwa-ruwan wanda bai soyu sosai ba yafi dafaffe amfani a jikin mace kamin jima'i. Haka shima ferfesu da naman da aka gasa mai ruwa-ruwa a jiki yafi tsirai ko balangu amfani a jikin mace kamin jima'i.
Abubuwan sha irinsu madara da zuma su lemun zaki ko mai tsami ko jucy amfani a jikin mace kamin jima'i. Haka kuma abarba, kankana, ayaba da lemun bawo sunada amfani mace ta cisu kamin kusantar miji. Amma kuma mata su sani cewa, kada ki cika cikinki sosai da abinci awa daya da rabi kamin soma jima'i, shi yasa ake bukata cin abinci ya kasance shine abu na farko da mace zata fara yi a shirinta na tinkaran jima'i, domin abinci ya narke kamin lokacin. Muddin mace ta tinkari jima'i bayan ta cika ciki sosai, da akwai yiwuwan tana iya yin amai, haka kuma tana iya gajiya da wuri watakila tun kamin mijin nata ya samu gamsuwa wanda hakan kuma illa ne babba.
Wadannan abincin dana sha da muka ambata a sama dukkaninsu suna da matukar alfanu da mahimmanci a jikin mace, dayake da ruwa-ruw. shiyasa dukkannin abincin da muka ambata suna karawa mace ruwane da kuma miniyi a jikinta, wanda hakan zai karamata jindadi jima'in ita kanta da mijin nata. Kuma mata suna iya fahimtar haka ne idan suna lura da dukkannin abincin da mace taci kota sha muddin dai mai ruwaruwane tana iya jin yanayinsa kamshinsa a cikin ruwan gabanta. Idan kuma ta ci wani abu mai wari irinsu albasa zai fito a gabanta.
2, Gyara dakin jima'i- Abu na gaba a cikin jerin abubuwan da zata yi kamin jima'i shine ta gyara dakin da zasu kwanta da mijinta domin jima'i bayan ta smun abincin da muka ambata ko masu kama dasu taci.
Dole ne mace tayiwa dakin kwanciyar jima'insu gyara na musamman ba irin gyran dakin da take tsamanin zuwan kawaye ko 'yan uwa ko abokan miji ba. Dakin kwanciyar jima'i yana bukatar tsafta kamar kowani bangare na gida, haka kuma yana bukatar a kauda duk wani dauda mai wari, doyi, zarni ko tsami daga cikin dakin.
Dakin kwanciyar jima'i baya bukatar fitila mai haske haka kuma yana bukatar mace ta bulbule shi da turare mai kamshi musamman wanda tasan maigidanta yana sha'awar kamshinsa. Haka kuma amfison mace tayi amfani da zanin shinfida mai dauke da zanen fulawa ko kuma mai wani alami na motsa sha'awa. Shima wannan shinfidan dolene abishi da turare ko ina hade da matashin kai na shinfidar.
Wasu masana jima'i suna ganin yanada kyau mace ta samu wani waka mai ratsa zuciyar masoya ta saka yana tashi kamin wannan lokacin, hakan a cewarsu shima wani tsimine dake ratsa zuciyar ma'aurata tare kuma da zaburar da sha'awarsu. Haka kuma dakin jima'i ana bukatar jinsa da sanyi mara cutarwa musamman ga mazajen da basu bukatar sanyi, dole mata su tabbatar da dakin da za suyi kwanciyar jima'i da mazajensu baya dauke da zafi, domin akasarin maza basa bukatar yin jima'i a yanayi mai zafi ganin jima'i yana haifar da jin zufa koda kuwa dakin nada sanyi.
3, Wanka Kamin Jima'i- Dole ne mace tayi wanka na musamman kamin lokacinta na jima'i, domin shi wanka na jima'i ya babbanta da sauran wankan da mata kanyi na zuwan kasuwa, unguwa wajen aiki ko sana'a, domin shi wanka na jima'i da akwai wasu muhimman wuraren da sune akafi la'akarin dasu a lokacin wanka, don haka da zaran an tsaftacesu wanke jima'i ya samu.
A lokacinda mace zata shiga wanka jima'i, dole ta tambatar da cewa sabulun da zata yi wanka dashi yanada kamshin da mijita yake so, kada ta sake tayi amfani da wani sabulun datasan cewa mijinta baya bukatar jin kamshisa, domin hakan yana iya kauda masa sha'awar jima'i ma gaba daya. Don haka dolene mata su fahimci irin sabulun da mazansu keso domin yin amfani dashi. Namiji yana iya kawowa matarsa sabunlun wanka ba domin shi yana son kamshinsa ba saidon ya fahimci matarsa nada sha'awar yin amfani dashi.
Ki tabbatar da cewa kin wanke bakinki tsaf babu wani wari dake fitowa daga cikin bakin naki a lokacin da kika shiga wanka jima'i, hamatanki, lungunan kunenki, matsaimatsinki, farjinki da kuma duburanki, kasan nonuwanki, kunnuwanki sune manyan abubuwa kulawa a lokacinda kike wankan jima'i. domin dukkanin wadannan wuraren sunada matukar mahimmanci a jima'i, (za ayi bayanin amfaninsu a gaba) don haka warin guda daga cikinsu yana iya hana mijinki kusantarki. Don haka mata su danadi kayan tsaftace wadannan wuraren na zamani domin yanzu haka ana samunsu.
4, Kwalliya Kamin Jima'i- Bayan mace ta fito daga wankanta na jima'i, abu na gaba dake gabanta a shirye shiryenta na kwanciyar jima'i shine kwalliya kamin jima'i. Domin muddin mace bata san yadda zatayi kwalliyarta na jima'i ba, yanada matukar wahala ta iya shawo kan mijinta a wannan daren domin ya sadu da ita.
Mafiya yawan mata suna dauka cewa da zaran mace tayi wanka ta wanke wadannan wuraren da muka ambata a baya shi kenen tayi mai wuyan a kokarinta na jawo da kuma motso sha'awar mijinta sunyi jima'i, ba tare da sanin cewa wanka babu kwalliya maigida ba zai sanma anyi ba.
Kwalliya na jima'i shima yana da babbanci da sauran kwalliyar da mata kanyi, domin shi wannan kwalliyar akasarinsa anayinsa ne da kayan kwalliyan da suke da kamshi na motsa sha'awa. Kwalliya ne da baya bukatan gazal, ja gira, fankeke bare kuma foda a fuska. Kawai abunda wannan kwaliyar yake bukata shine ki tabbatar da cewa kinada man sanya baki kamshi, tare kuma da samu wata alawa ko cingam mai kamshi ki sanya a baki. Haka kuma ki tabbatar da cewa, idan mijinki baya bukatan gashi a gaba ki kin aske a lokacin wanka, idan kuma yana bukata sai ki shafa masa man gashi mai sheke da kuma kamshi. Haka kuma ki tabbatar da cewa kin fesawa farjinki turareni saboda shine yake soma yin wari da zaran kin soma yin gumi.
Hamantanki da kuma matsaimakinki suma ki tabbatar da cewa sun samu turare mai kamshi gaske. Gyara gashinkanki a wannan lokacin ya zamemaki dole, domin mace da gashin kanta kawai tana iya demauta namiji idan har tasan yadda zata sarrafashi, don haka yana da kyau mace ta gyara kanta sosai ta hanyar wankeshi da kuma sanya masa man gashi mai kamshi irin wanda tasan mijinta yana bukata jin kamshinsa ba irin mai warinnan da wasu mata kesanyawa wanda kuma akasarin maza basu bukatar kanshinsa.
Manda zaki shafa a lokacin kwalliyarki na jima'i shima abun la'akarine, dole ne ki tabbatar da cewa man mai sa taushin jikine ba mai busar da jiki bane, domin namiji bayan bukatar jin jikin mace a bushe. Haka kuma ki tabbatar da cewa hannunki ki shafeshi da man shafawa mai laushi domin hannun shine sarki aiki.
5, Ado Kamin Jima;i- Bayan mace ta kammala adonta na jima'i, abu na gaba shine ado, domin shima jima'i yana da tasa irin adon daya kamata mata suyi masa amma akasarin mata basuda fahimtar hakan. Don haka nema wasu matan bayan sunyi wanka suyi kwalliya sai kuma suga mazan basu kula ba, wannan kuwa na faruwane saboda rashin karasa wannan kwalliyar da akayi da ado mai kyau.
Adon kwanciyar jima'i ba a samasa zobe, sarka ko awarwaro. Haka kuma ba a daura masa atamfa ko sanya masa wandon mai tauri irin jens, abunda adon jima'i yake bukata shine kaya masu nuna tsiraici, kaya masu shara-shara, kayan da zasu fito da nunuwanki a filin, kayan da mijinki zai rika hango kan nunuwanki, kayan da zasu rika fito da kuma nuna motsin duwaiwukanki a duk lokacin da kika motsa.
Ado na jima'i yana son mace ta sanya kayan da baza su danne hakkin duwaiwukanki ba idan kina bukatar son juyawa mijinkisu. Kayane da babu damuwa idan sun fito da shashin gabanki a fili, ko kuma suna baiwa mijinki sararin hada idanuwa da tsiraicinki. Akwai rigan nono da kuma fant na mata wanda da zaran mace taci adon jima'i dasu kamin mijin natama ya matsota yayi zuwan farko, sune irin shiga na ado dayakamat mata surika yiwa mazajensu. Haka kuma da akwai riguna na barci masu kyau da kuma sauki ga mata domin amfani dasu a lokacin adonsu.
6, Yanayin Lokacin Jima'i- Abu na karshi a wanna babin kamin soma jima'i shine na zama dole mace tayi la'akari da lokacin daya kamata ta shiryawa jima'i ganin shi lamari na jima'i lamarine dake bukatar lokacin da babu wani da zai shiga rayuwar ma'aurata.
Kashi 80 cikin 100 na ma'aurata sun gwammace yin jima'i a tsakiyar dare ne domin ganin shine lokacin da babu wani da zai shiga rayuwarsu, don haka mace ta tabbatar da cewa kamin ta shirya yin jima'i babu wani da zai raba mata hankali. Ta tabbatar da cewa idan ita maishayar wace ta shayar da danta har lokacin da take tunanin bazai sake tashi ba. Haka kuma idan tanada kananan yara sunyi barcin da baza su sake neman kulawarta ba. Idan tana da baki ko kawayen da suka kawomata ziyara na kwana ta tabbatar ta kamala dasu. Haka kuma babu barin waya a kunne ko kuma duk wani abunda tasan cewa yana iya dauke hankalinsu a lokacinda suka soma jima'i.