Ad Code

Abokin Mijina Hausa Novel


 Ammar Hassan Ibrahim:

Abokin mijina PAGE 1 📒

"Hmm naga sai wani Dauki kake kamar wanda yau aka kai maka matar. "Abokina bazaka gane bane Wallahi tunda na auri Husna ban ta6a kusan tantaba kai baka tunanin zan shiga hakkinta?" Ya karasa 😠 maganar fuska dauke da damuwa. Wani dadi ne ya lullu6e Yusuf sannan yace "To ai sai kayi hak'uri tunda kasan tsoro take ji kuma idan kayi bata cire wannan tsoron ba Wallahi ciwo zaka ji mata kaca-kaca. 😠Gaban Farooq ne yayi mummunar fad'uwa sannan yace "To Abokina menene mafita?" Ya tambaye shi. "To mafita dai d'aya ce kawai ka hak'ura har sai ranan da Husna ta bude baki tace ka kusanceta. Bude ido yayi yace" 😠Kai Wallahi Husna bazata iya cewa na kusanceta ba koda kowa zamu shekara ne sai dai kawai na cire tausayinta nayi abinda yake raina dan kuwa Wallahi yana damuna kasan dai abinda Doctor yace mun. 😠 Wani kallon tsana Yusuf yayiwa Farooq sannan yace "Kenan kayarda ka kashe 'yar mutane ko? Dan kuwa nasan kai bazaka sausauta mata ba. "No Yusuf yanzu nazo wajen kane dan kabani shawara saboda kai ka dade da mata kuma kaine aminina dan haka nazo gunka please Abokina ka taimaka mun. 😠 "Murmushi mugunta Yusuf yayi sannan yace "To shawara ta daya ce kajira ta nan da sati d'aya idan kaga babu halamun bukata a tattare da sai kawai kayi abinda kayi niya."Hmm to Allah yakaimu nan da satin amman Wallahi nikam a matse nake.Haka dai suka tayi a tsakanin su sannan suka yanke akan sai nan da sati. Yusuf ne ya rak'oshi har gida a lokacin da suka shigo gidan wani wawan k'amshi ne ya daki hancin su Wanda sai da gaba d'ayan su suka shiga wani hali. Zaune take akan d'aya daga cikin kujerun da suka zagaye parlour. Swiss lace ne a jikin ta Wanda ya amsheta kamar dan ita akayi.


Abokin mijina PAGE 2 📒

Farooq ne yayi sallama wanda Yusuf ya kasayin Sa. Amsa musu tayi cikin zazzak'ar muryan ta sannan ta tashi tana musu sannu da zuwa. Yusuf sake rikicewa yayi da ya kalli😠 halitattar Husna Wanda bai ta6a tsammanin tana da shi ba. Farooq ne ya d'an bigeshi yace "Kai kuwa sai kace Wanda baka Santa ba sai wani kallon ta kake" ya k'arasa maganar cikin zolaya. D'auke idon shi yayi a kanta sannan yace "Wallahi abokina sai naga kamar Yau ta chanza mu😠 "Sannun Ku da zuwa" Yusuf yayi saurin amsawa da cewa "Yauwa sannu amarya ya kike?" Murmushi tayi tace "Lafiya k'alau Ya Yusuf, ya Anty Hafsat?" Ta tambaye shi. "Lafiya ta k'alau gobe insha Allahu zan kawota ku wuni saboda Ku fara sabawa tun yanzu." "Kai amman naji dad'i Wallahi ya Yusuf Allah yakaimu. Shikuwa Farooq yana zaune yana kallon amaryar Sa wacce duk kallon da zai mata sai yaji wani abu a jikin shi. Juyowa tayi tace "Sannu da zuwa ya Farooq." "Yauwa sannu uwar gidana uwar 'ya 'ya na ya kike? Ya kuma kad'aici." "Alhamdulillah Ya office?" "Alhamdulillah My Angle. 😠 Wannan kalamai na Farooq ne ya fara 6atawa Yusuf rai hakan ne yasa shi katseshi da cewa "Abokina nifa yunwa nake ji muci na gudu nima gida na."Murmushi Farooq yayi yace "To ai ga abinci a dining muje mana."Haka kuwa suka tashi suka nufi dining dan cin abinci amman ina Husna Sam ta kasa sakewa dan wani kallo Yusuf yake mata hakan ne yasata tashi tabar abinci. Bayan sun kammala sun koma parlour in zauna 😠 yace da Farooq "To Abokina ni zan gudu amman dan Allah kar ka kusanci yarinyar nan Wallahi yanda na fahimceta har yanzu tsoro ne a ranta kagani dai ko abinci ta kasa ci.


Abokin mijina PAGE 3 📒

Eh nima dai hakan nagani amman kasan bazai yu na zuba mata ido ina kallon ta ba, dole sai nayi abinda yake rai na." Mugun kallo ya masa sannan yace "To naji ka k'irata kuzo Ku rakani zan wuce." Haka kuwa ya tashi yaje ya kirata suka rakashi bakin motar shi sannan suka dawo cikin gida. Bai tsaya a ko inaba sai gidan shi, ba laifi yau tayi wanka tayi kwalliya har da turare ta saka a gidan ta abinda rabonta da shi har ya manta. Sallama yayi ya shiga kamar yanda yayi tsammanin a parlour ya sameta kwance akan three siter.


Amsa mishi tayi ya shiga "Sannu uwar 'yan jin dad'i ai daman nasan kina nan kwance." Turo mishi baki tayi tace "Sai yanzu kadawo kasan inajin yunwa."Kallon ta yayi yace "Wai ni bawan kine da zan dinga dafa miki kina ci to Wallahi Yau bazan dafa ba sai dai ki kwana da yunwa. Mik'ewa tayi da k'yar ta zauna tace "Haba ya Yusuf kaima kasan bazan iya fad'awa ba kuma ko na daga bazan iya ci ba ko naci ma amarwa nake. "To Allah yasa kar ki iya ki zauna nikam bazan dafa ba" ya k'arasa maganar yana hayewa sama d'akin shi. Ita kuwa cewa tayi "Oho dai idan baka dafa ba zan iya badawa a siyomun." Haka kuwa tabawa Isyaku mai wanki da guga kud'i ya siyo mata tsire kasan cewar tanada yogurt a friez. B'angaren Farooq kuwa hankalin shi gaba d'aya baya jikin shi yanda yau yaga Husna... Yanda yaga Husna tana mishi wasu irin salo Wanda bai ta6a tsammanin ta iya irin su ba haka kuwa shima ya biye mata suka ci gaba da jin dad'in su. Ringing d'in wayan shine ya dawo da su daga duniyar da suka tafi. Ganin Number Yusuf ne yasashi d'auka da sauri ya kara a kunnen Sa. "Hello Abokina bakayi barci ba" Yusuf ne ya tambaye Farooq. "Eh Wallahi banyi ba amman dai lafiya ka k'irani cikin wannan daren? "Lafiya k'alau kawai dai na kiraka muyi hira idan amarya tayi barci. "Hira kuma nida inada mata kaima kanada me zaisa muyi hira bayan ga matan mu.


Abokin mijina PAGE 4 📒

"To sarkin iyayi ai cewa nayi idan sunyi barci ko kai naka har yanzu batayi ba? "Eh batayi ba sai nan gaba. Kai dai kawai bakason muyi amman me zaisa Husna zama har yanzu batayi barci ba. "To shikenan tunda baka yarda ba to gatanan kaji muryan ta" ya k'arasa maganar yana mik'a mata wayar. Wani dad'i ne ya lullu6e Yusuf daman abinda yake nema kenan gashi kuma ya samu. Kar6an wayar tayi ta saka a kunnen ta badan ta so ba. "Hello Yaya Yusuf baka yarda cewa banyi barci ba?" Ta tambaye shi. Murmushi jin dad'i yayi yace "Ina kuwa zan yarda bakiyi barci ba dan nasan wannan lokacin ba abinda zakiyi. "To shikenan sai da safe." Ta kashe wayan. Ba dan yasoba saboda yanzu a rayuwar shi ba abinda yake so kamar yaji muryan Husna. Shi kuwa Farooq tsaki yaja yace "Wallahi Yusuf ya cika matsala war yanzu zai kira mutum a waya kawai ya katsemun jin dad'i na" ya k'arasa maganar yana rungumo Husna. "Husna dan Allah inason na miki tambaya ina fatan zaki bani amsa." Gyara kanta tayi wanda yake k'irjin Farooq sannan tace "Ina jinka ya Farooq. "Husna meyesa kike tsoro na? Kike tsoron bani hakk'ina?" Juyowa tayi ta kalli fuskan shi sannan tace "Wanne irin tsoro Yaya? "Husna nasan tunda aka kawoki gidan nan kike tsoron had'a shinfid'a da ni shiyasa nima na barki har sai wannan tsoron ya fita amman kuma naga har yanzu banga kina buk'ata naba. Rufe fuskan ta tayi Alamun jin kunya sannan tace "Aa Yaya kar kasa mala'ikun Allah su tsine mun. "Amman har yanzu baki bani amsa na ba. "Yaya Wallahi ba wani tsoron ka da nakeji ba, sai dai kasan duk wata mace dole sai tayi far gaban first night d'in ta. Murmushi yayi sannan yace "To yanzu kin yarda da nayi abinda naga dama?" Wani irin kunya ne ya lullu6e ta wanda ya sata tusa kanta tsakanin pilo.


Abokin mijina PAGE 5 📒

To yanzu tashi muje muyi alwala mu gabatar da sallah raka'a biyu. Bata amsa mishi ba sai ma kara danna kanta take ganin zata 6ata mishi lokaci ne ya d'auke ta zuwa bathroom. Alwala sukayi sukazo suka gabatar da sallah sannan ya musu addu'a sosai tukun suka nufi gado. Sai Yau Farooq yasan cewa yayi Aure sun faran tawa junan su sosai sai misalin k'arfe d'aya na dare Farooq ya barta. Farooq ji yake kamar zai mayar da Husna ciki tsabar yanda yake jin k'aunarta yana k'ara shiga cikin zuciyar shi. Yau Husna ta shayar da shi madarar soyayyar ta. Ita kuwa Husna taji maza Wanda haka yasata narkewa sai faman kuke-kuke take na shagwa6a. Toilet ya shiga ya had'a mata ruwa mai d'umi sannan ya dawo yace mata "Heartbeat tashi na d'aukeki muje na miki wanka." Turo bikin ta tayi gaba tace "Aa Yaya nima zan iya kabar shi kawai nayi." "Aa Heartbeat nasan kin wahala bazaki iyayi ba kibari kawai na miki.


Kuka tasa mishi tace "Yaya nace zan iya Wallahi zan iya kayi hak'uri nayi" Aa Baby kar kiyi kuka dan Allah tashi ki shiga ina jiranki." Tashi tayi ta shiga Tana shiga shi kuwa ya cire beshit d'in ya chanza wani sannan ya cire mata wasu sleeping dress masu d'an nauyi. Fitowa tayi d'aure da towel da sauri ya k'araso inda take yana mata sannu yace mata "Sannu Babyna zo muje na saka miki sleeping dress. Sake narkewa tayi tace mishi "Ya Farooq jikina yana mun ciwo. "Ayya sorry Heartbeat ko zan kaiki hospital ne? "Aa basai munje hospital ba. "To ko nasake had'a miki ruwan zafin ne? Shiyasa nace ni zan miki amman kika k'i. Bata mishi magana ba ta wuce. A hankalin ta k'arasa bakin gadon ta zauna. Dauko kayan yayi yasa mata ya kwantar da ita sai da ya tabbatar tayi barci sannan shima ya shiga toilet.


Abokin mijina PAGE 6 📒

Bangaren Yusuf kuwa dad'i yake ji sosai dan kuwa ya tsorata Farooq ko ba komai burin shi zai cika. Tashi yayi yaje d'akin Hafsat a zaune ya sameta tana chart hakan ne yabashi daman karasawa. "Bakiyi barci bane?" Eh amman yanzu zan kwanta. "Daman in son na fad'a miki gobe insha Allah zamu tafi gidan Farooq zamuje mu wuni. "Gaskiya kuma fa ya kamata mu tafi gidan shi. "To sai ki shirya gobe 8:30 zamu tafi. "To Allah yakaimu goben. Washe gari Farroq shida kanshi ya shiga kitchen dan had'a musu breakfast. Dankali ya soya musu da eggs sai kuma tea. Bayan ya gama da yadawo d'akin se ya same zaune tasha kwalliya sai k'amshi take sha ga kuma kayan da ta saka sun bayyana suranta. Karasowa wajan ta yayi yana murmushi yace "Heartbeat har kin warke kinsha irin wannan kwallayar gaskiya ya miki kyau." Wani irin fari da ido tayi wanda yake k'ara mata kyau sannan tace "Na warke mana ya Farooq ko bakason na warke ne?" Ta tambaye shi. "Aa na isa ai ni nafiki damuwa, Yanzu ba wannan BA tashi muje dining muyi breakfast." Tashi sukayi suka nufi dining amman suna zama sukaji... Sallaman su Yusuf sukaji daga k'ofar parlour dan su ko bude k'ofa basuyi ba. Farooq ne yaje ya bud'e musu, ganin abokin shi da matar shine yasashi yin murmushi sannan yace "Aa Abokina kaine da sassafan nan? "Eh nine ko bakason zuwan mu ne?" "Aa bai kai ga haka Ku shigo sannun ku da zuwa." Ya k'arasa maganar yana nuna musu hanya. Hafsat ce ta kalli Farooq sannan tace "Abokinka kad'ai Ka sani ko?" "Aa k'anwata kiyi hak'uri ai dole na gaida ki." Gaba d'ayan su a parlour suka zaune itadai Husna badan ranta yaso ba saboda kwana biyun nan ta kasa gane me Yusuf yake nufi. Farooq da Hafsat ne suka gaisa cikin mutun ci da girmama juna saboda


Abokin mijina PAGE 7 📒

ita Hafsat ta dauki Farooq tamkar yayan ta. Shikuwa Yusuf sai faman zuba ido yake nason yaga Husna amman ina bai ganta ba hakan ne yasa yace da Farooq "Wai kai ina Amaryan ne ko har yanzu bata tashi a barci ba?" "Aa ta tashi tana dining ko breakfast bamuyi ba." Ita kuwa Husna yanayin kayan jikin ta ne yahanata tashi hakan yasa ta koma gefe ta zauna. Yusuf ne yace "Yauwa nima haka yunwa nake ji kutashi muje mu karya." Haka kuwa suka tashi suka nufi dining. Tsayawa yayi cak ko motsawa ya kasa sai faman lashe le6e yake kamar sabon maye ya zuba mata ido musamman yanda yaga na shanun ta sun kunburo a cikin k'aramin riganda ta saka. Farooq ne yace "Ya katsaya ne bazaka zauna ba." Sai a lokacin ya d'an motsa sannan yace "Zan zauna Amarya me ta girka mana? "kai yau ba nata girkin bane nawa ne. "Kana nufin kaine kayi girki?" "Eh nine wani abune? "Aa ba komai kawai dai naga ga Amarya ne. "Kai kabari kawai yau Heartbeat d'ina batajin dad'i." Wani wawan juyowa yayi ya kalli Farooq sannan tace "Me yake damunta. Zan fad'a maka amman ba yanzu ba muci abincin mu kawai. Ita dai Husna batada bakin magana saboda duk wani iri take jinta. "Ya Farooq" ta furta a hankali. Matsowa yayi kusa da ita yace "Na'am my Angle.""Dan Allah kabani hijabi na a d'aki." Sai a lokacin shima ya gane abinda yasa taki sakin jiki bare tayi magana. Da sauri ya mik'e ya shiga d'aki ya d'auko mata k'aton hijabi har kasa ya bata ta saka.


Sai a.lokacin tace "Sannun ku da zuwa Anty Hafsat." "Yauwa sannu Amarya ya kike?Ya Amarci?" Cikin jin kunya tace "Lafiya k'alau Alhamdulillah. "To ni kuma baza'a gaidani ba?"Yusuf ne yayi magana. Murmushi tayi tace "Aa wallahi Ya Yusuf zan gaida Ka Ina kwana. "Sai da na rok'a za'a gaidani banaso."


Abokin mijina PAGE 8📒

Farooq ne yace "to yanzu dai muci abinci ba wai surutu ba. Haka kuwa sukaci abincin su duk da Husna ba dad'in cin abincin take ba saboda Yusuf ya zuba mata ido duk motsin da zatayi. Bayan sun kammala parlour suka koma suka zauna shi kuwa Farooq zan Husna yayi tace suje ya chanza mata kaya. Kusan 30 minutes sukayi wajen chanza kaya wanda duk ya dami Yusuf ji yake kamar ya bisu yaga me sukeyi. Sanye take da wata atamfa me d'an green a jiki Wanda ya mata kyau sosai duk da ba wani kwalliya tayi ba, Rike suke da hannun junan su kana ganin su sai sun baka sha'awa. Farooq kenan da matar shi Husna. Wani bak'in kishi ne ya bige Yusuf wanda yasa zuciyar shi bugawa da k'arfi amman sai ya danne yace "Wai kai Farooq bakajin kunya ne dan Allah? Kana gani a gaban mu zaka rik'e mata hannu kuna tafiya." Cikin mamaki Farooq yace "Haba Abokina wannan fa Matata ce ko kamanta lokacin da Ka auri Hafsat a gabana kake d'aukanta dan ni na rik'e hannun ta shine rashin kunya." "To naji kayi hak'uri kazo Ka zauna muyi hira. "To tashi muje parlour na yau akwai labari." Wani kallo ya mishi sannan yace "Dan meye sa bakason mu zauna anan tare da matan mu? "Kai dalla cewa nayi zan baka labari kuma banson suji. "To shikenan muje."Haka kuwa suka tashi suka wuce parlour Farooq. "To inajin Ka menene labarin? "Abokina jiya na kusanci Husna nasan wacece ita kuma nima na samu lafiya Alhamdulillah." Tunda Farooq ya fara magana YusufYa shiga cikin wani hali wanda shi kanshi baisan dalili ba. Sai kuma yace "Haba Farooq dan meyesa Ka kusanci yarinyar nan a yanzu?" Cikin mamaki Farooq yace "kamar yah ban gane ba? "Ina nufin ai dakabari sai zuwa wani lokaci. "Kamar ya Yusuf? Dan meyesa kake mun haka ne? Yau fa aure na wata d'aya amman sai jiya nasamu. Katseshi yayi da cewa " to naji


Abokin mijina PAGE 9📒

nataya Ka murna amman ina baka shawarar kar kabari tayi ciki yanzu dan wallahi nima na Hafsat ba so nake ba dan zai hanaku jin dad'i. "Hmm kai wallahi kacika matsala naji kuma nagode shikenan."To yanzu tashi muje nifa inason na zauna kusa da mata na ina kallon ta. "Kai wallahi maye ne kaida kullum kuna tare shine yanzu zakace kanason kallon ta" ya k'arasa maganar yana kallon shi yana dariya. "Naji dai tashi mutafi wallahi inason kallon mata ta. "To tashi muje." Bangaren su Husna kuwa hiran su suke sosai da Hafsat, itama Hafsat ta sake jiki da Husna dan taji tanason ta. Husna ce tace "Anty Hafsat me kike son kici zan shiga kitchen na d'aura abinci. "Aa Husna komai kika dafa zanci dan bana sha'awan komai." Ta tashi zata shiga kitchen kenan sai gasunan sun shigo Farooq ya bud'e baki zaiyi magana amman Yusuf ya rigashi da cewa "Aa Husna ina zaki naga kin tashi?" Juyowa tayi ta kalleshi sannan tace "Kitchen zan shiga d'aura girki.Farooq ne yace "Yauwa yayi dai-dai muje muyi girki kai kuma sai Ka zauna wajen matar ka kafin mu gama" yana k'arasa maganar ya ja hannun Husna sukayi kitchen. Shikuwa Yusuf wani bakin ciki ne ya lullu6eshi daman shi yazone dan Husna kuma gashi ta tashi wanne hanya zaibi dan ya dawo da su. Ai kuwa a take wani abu ya fad'o masa da sauri ya mik'e shima ya shiga kitchen d'in. "Haba dan Allah ya munzo gidan ku zaku shiga kitchen Ku barmu a parlour." Husna kam har ta tsorata dan batayi tsammanin mutum ba. Farooq ne yace "To Idan bamu girka muku abinci ba ya zamuyi kenan?" Ya tambaye shi. "Abu mai sauki anjima kaje kasiyo mana. Da k'arfi Farooq yace "Abincin siya! Sanin kanka ne kasan bana cin abincin siyarwa Yusuf dan Allah kaje Ka zauna yanzu zamu gama mu dawo." Zuciyar shi cike da Kuna ya dawo ya zauna yana kullah abinda zai shirya.


Abokin mijina PAGE 10📒

Gyaran murya yayi sai a lokacin Hafsat ta d'aga ido ta kalleshi. "Hafsat inason nayi mana gyaran gida kuma bansan ina zamu komaba inason kafin ki haihu an gyara mana gidan mu." Cikin mamaki Hafsat take kallon shi sannan tace "Gyaran gida fa kace? naga gidan namu ba abinda ya sameshi duduma yaushe aka ginashi auren mune fa." "Eh nasani Sweetheart bakyason idan anzo suna aga sabon gida?"ya tambaye ta. Sai a lokacin Tayi murmushi tace "Gaskiya ne kuma fa wallahi sai yanzu na fahimmace ka. "To shine bansan ina zamu zauna a mana gyaran gidan ba, kinga ai bazai yu mu zauna ana gyara ba ko?" "Ai kuwa haka ne to ai ko gidan haya zaka iya kamawa kafin a gama gyaran." Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yace "Haba wanne irin gidan haya?Ki bari kawai zan samu zuwa gobe ko anjima." Ita dai kallon shi kawai take dan tasan akwai dalilin wannan maganar nashi. Su Farooq kuwa suna girki suna zuba soyayyar su haka sukayi har suka kammala. Rice and stew sai kuma salat da kunun aya wanda yasha kayan had'i A dining suka jera komai da komai hatta plate da cups sai da Farooq ya d'auko ya ajiye sannan ya bar wajen. Kasan cewar suna gamawa aka kira sallan azahar Farooq yaja Yusuf suka wuce masallaci su kuma sukayi sallahn su. Gaba d'ayan su suna zaune suna ci Yusuf kam baya magana sai kwasan na gara yake. Bayan sun kammala cin abincin parlour suka koma suka zauna Yusuf ne yace "Abokina daman akwai maganar da nake so na fad'a maka. "Owhk ina jinka. "Inason zanyi gyaran gida amman kuma banida wajenta zama da mata ta zuwa lokacin da za'a gama mana. "Gyaran Gida kuma Yusuf? Me yasamu gidan naka da zaka gyara?


Abokin mijina PAGE 11📒

Kana gani dai Hafsat ta kunsan haihuwa to banason ayi suna ban gyara mana gidan ba. "Owhk na fahimceka kana so ka fara gyara kenan. "Yauwa ashe ka gane, to amman banida inda zamu koma da zama kafin a gama gyaran. "Owhk wannan ba matsala bane zan bud'e muku wancan part d'in sai Ku zauna. Wani mugun murmushi yayi sannan yace.. Ido cike da k'wallar muna furci yace "Nagode Abokina Allah yasaka maka da alkhairi bansan me zance maka ba banida bak'in yi maka go" Katseshi yayi da cewa" Haba Yusuf menene a ciki idan ni ban maka ba waye zai maka a duniyar nan dan Allah ka daina gode mun, ka godewa Allah kawai. "Ya k'arasa maganar ya rumgumarshi. Husna kuwa gabanta ne yashiga fad'uwa dan kuwa tasan akwai wani abinda Yusuf yake shiryawa. Hafsat ce tace" mun gode Ya Farooq nima naji dad'i haka wallahi dan kuwa kullum muna tare da Husna. Yusuf kuwa a zuciyar shi cewa yake "Wallahi Farooq sai kabarmum Husna nafika sonta saboda kai bakasan menene so ba dan haka sai na shiga tsakanin ku na rabaku." Maganar Farooq ya katseshi da cewa" ai kar kidamu Hafsat yanzu kam ga Husna sai Kuna wuni tare kunga ko wanne a cikin Ku zaiji dad'i. Yusuf ne yace "To yanzu Hafsat ki tashi mu tafi gida mu fara shirye-shirye kinga gobe zamu dawo nan da zama." Farooq ne yace "Kai wallahi kacika gaggawa kabari mana Isyaku ya share muku gidan. "Eh haka ne amman yanzu ka sashi ya share dan Allah. "To shikenan ba matsala Allah yakaimu goben." Gaba d'aya suka amsa da "Ameen Thumma Ameen." Suna gama maganar Yusuf ya d'auki matar shi cikin farin ciki sukayi gida. Suna fità Farooq ma ya fita.


Abokin mijina PAGE 12 📒

Suna tafiya Husna ta shiga gyaran gida tayi shara tayi moping duk da ba wani kurane da gidan ba. Kitchen ta shiga ta d'aura abinci nan da nan ta gama kasan cewar tuwon semo da miyar ku6ewa d'anya sai kuma banana juice. Burner ta kunna nan da nan gidan ya d'auke da k'amshi. Wanka tashiga bata wani dade ba ta fito d'aure da towel akwatin k'anan kayanta ta bude. Wani riga da wando ta fidda ta saka Wanda ba k'aramin kyau ya mata ba. Rigar pink sai kuma wando white sai ribom d'inta shima pink zama tayi a gabàn mirror ta fara tsara kwalliya. Farooq kuwa da yafita gidan Hajiyar shi ya nufa dan sanar da Ita dawowar Yusuf gidan sa. A parlour ya sameta zaune akan sallaya da halamun ta idar da sallah ne. Sallama yayi ta amsa masa ya shigo. Gaidata yayi cikin ladabi da biyayya Ita ta amsa cikin so da k'aunar d'an ta.


"Umar lafiya kazo da yamman nan? "Eh mummy lafiya k'alau daman Yusuf ne yace zaiyi gyaran gida to shine yace bashida wajen zama. "To shi kuma wanne irin gyara zaiyi bayan gidan nashi sabo ne. "Eh Mummy saboda Hafsat takusan haihuwa shiyasa yake son ya d'an kinkintsa. "To ya zakuyi kenan? "Eh Mummy nace yazo ya zauna a d'aya part d'in shiyasa nazo na fad'a miki. "Hmm Umar ba wai na hanaka ba kasan rayuwar yanzu ba tabbas kar ka ajiye abokin ka a gidan daga baya wani abu yabiyo baya. "Aa Mummy insha Allah ba abinda zai biyo baya kimana addu'a kawai. "To shikenan Allah ya had'a kawun nan Ku. "Ameen Thumma Ameen Mummy."

"Ya Husna tana lafiya ko?"

"Lafiyan ta k'alau Mummy tace na gaida ki."

"To ina amsawa."

"Mummy inasu Khadijat da maryam ne banjisu ba?"

"Eh basu dawo a islamiya ba."

Haka dai sukayi ta hiran su sai da magriba ya tafi.


Abokin mijina PAGE 13📒

Bangaren Yusuf kuwa suna zuwa gida ya fara had'a musu kaya nan da nan ya had'a kayan su gabaki d'aya ya saka a bayan motar sa sannan ya koma yace da Hafsat zai kai kayan su gidan yana zuwa. Haka kuwa akayi akan hanya magriba tayi mishi sai da ya tsaya a masallaci yayi sallah sannan ya wuce.Bayan Farooq yayi sallah ya dawo gida tun kafin ya shiga gidan yaji wani sanyayan k'amshi ya bige mishi hanci. A parlour ya sameta zauna tana kallon Arewa24 hakan yasa yak'i yin sallama ya lalla6a ta baya yaje ya rumgume ta. Wani irin tsorata Husna tayi dan batayi tsammanin mutum ba murya yana rawa tace "Dan Allah waye kayi hak'uri ka barni." Dariya ne ya kama Farooq ganin yanda tayi hakan ne yasa shi juyata ta kalli fuskan shi. Ajiyar zuci tayi sannan tace "Kai Ya Farooq dan Allah wallahi ka tsoratani. "Kai My Angle kinga yanda kikayi kyau kuwa. Murmushi tayi sannan tace

"Thank you" Budewar kofa sukaji sai da yashigo sannan ya musu sallah. Farooq ne ya amsa mishi amman ina Yusuf ya tafi wata duniyar ganin Husna cikin wannan kayan. Farooq ne yace mishi "Aa Yusuf lafiya ko kamanta wani abu ne?" Sai a wannan lokacin ya dan matsa yace "Aa nazo ne karbi key d'in parlour. "Owhk bari na shiga na dauko maka. "Owhk ina jiranka nakawo kayan mu ne." Farooq bai kulashi ba ya shiga ya barsu a parlour."Amarya amman kinyi kyau irin wannan kwalliyar duk Farooq kikayiwa?" Wani kallo ta watsa mishi sannan tace "Idan banyiwa mijina ba wa zanyiwa?" Murmushi yayi yace "To mukuma meye amfanin mu?" Kin kulashi tayi Tayi kamar ba da Ita yake ba.


Abokin mijina PAGE 14 📒

Sake matsowa yayi yana leka ta sai faman kallon kirjinta yake Ita kuwa duk ta damo Farooq ya dawo dan idan ta tashi wando ya matse ta abin zaifi haka. Shi kuwa mayen yana nan yana ta faman kalle-kallen shi sai ga Farooq...

Farooq ya fito da sauri ya matsa gefe d'aya kamar mutu min kirki. "Yauwa gashi nan sai yanzu na samu." Kar6a yayi bai kulashi ba ya fita ya bar musu parlour."Ya Farooq meyesa Yusuf yake shiga mana cikin gida kamar nasa gidan? "Husna kenan, ai Yusuf a matsayin d'an uwa na yake gidan shi da wannan duk d'aya ne dan yashigo ai ba wani abu bane." Ya k'arasa maganar yana rungumota. Itadai duk abin ya dameta amman tunda yace haka batada bak'in magana.

*​TUSHEN LABARI​*

Marigayi Alhaji Ibrahim shine mahaifin Farooq wanda yarasu a wani hatsari da yayi. Alhaji Ibrahim mai kud'i ne sosai wanda ya rasu yabarwa yaran sa. Farooq su uku ne a wajen iyayen sa. Shine Babba sai Khadija sai kuma maryam Hajiya Aisha itace mahaifiyar su. Hajiya Aisha macece mai hak'uri da mutunta juna kasancewarta ba mai rikici hakan yasa mutane suke k'aunarta. Farooq yayi karatu sosai shima yanzu haka yana aiki a bank ba da dukiyar da mahaifinsu ya bar musu ya dogara ba.

​*WANENE YUSUF?​*

Yusuf dan kawar Hajiya Aisha ne wanda mak'oftaka ya had'asu har suka zama 'yan uwan juna. Yusuf da Farooq jinin su ya had'u sosai hakan yasa farooq d'aukan Yusuf ya dawo dashi gidan su. Tare suke komai har Wanda basu Sani ba suna cewa uban su daya. Shi kuwa mahaifin Yusuf ba wani k'arfi yak'e da shiba, yanada wani k'aramin shago a bakin layin su yana sai da kayan tireda. Haka rayuwar su yakasan ce komai tare har Allah yakawowa Yusuf mata wato Hafsat ya aura.


Abokin mijina PAGE 15 📒

Hajiya Aisha ce tayima Yusuf aure hatta sadaki itace ta biya hakan ba k'aramin dad'i yayiwa mahaifiyar Yusuf wato Habiba ba dan batayi tsammanin hakan daga garesu ba. Bayan Yusuf yayi aure ne Farooq ya samu budurwa wacce ya gani yake so. Husna 'ya ce ga Alhaji Aliyu da kasuwa ne cikakke Wanda kowa ya sanshi. A lokacin da Farooq ya bayyanawa Yusuf Husna ya nuna kar ya aureta amman yanda yaga Farooq ya nace sai ya barshi ya aure ta. Ranar auren Farooq Yusuf ya sake rikicewa yanda yaga Husna ba hijabi a jikin ta, kasan cewar bata cire hijabi a jikinta. Ranar dinner ne Yusuf ya gama haukacewa yanda yaga shigar Husna a wannan lokacin yayi alwashin raba Farooq da matar shi. Ranar da suka raka Farooq har sunbaro gidan Yusuf ya kira shi a waya yace kar yasake ya kwanta da Husna saboda zai iya ji mata ciwo har ta kwanta a hospital hakan ne yasa Farooq tsorata ya yarda da maganar Yusuf. Ko wanne rana sai Yusuf ya kawowa Farooq wani karya har tsawon wata d'aya.

​​​

WANNE SHINE TA K'AITACCEN LABARI SU.​​​

*​CIGABAN LABARIN​*

Washe gari da sassafe Yusuf ya d'auko Hafsat suka dawo gidan su Farooq ko a barci basu tashi ba. A cikin barci Farooq yaji ana kwankwasa musu kofa wanda hakan ba k'aramin tsorata shi yayi ba dan baiyi tsammanin mutum war yanzu ba.Tashi yayi ya fito ganin Yusuf tsaye ne abin ya bashi mamaki tambayan shi yayi da cewa "Yusuf lafiya ko jikin Hafsat ne?" Murmushi yayi mishi yace "Aa ba jikin ta bane mun dawo ne so munaso muyi breakfast a gidan ka. "Kai wallahi ka cika matsala yanzu fa 6:30 ne shine zaka damu breakfast? To wallahi ko a barci bamu tashi ba. "Kana nufin bazamu shiga gidan ka ba kenan? "Aa nifa ba haka nake nufi ba,


Abokin mijina PAGE 16 📒

kawai dai nace bamu tashi a barci bane amman dan shiga gida ne bismillah, ina Hafsat din take?" "Owhk bari na kirata tana mota jirani nazo." Shi kuwa Farooq mamakin abotarsu yake da Farooq yanda suka saba da wasu abubuwa. Gaba d'ayan su a parlour suka zauna Hafsat ce tace "Nifa wallahi yunwa nake ji a taimaka mun da abinci." Wayyo hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Yusuf ba dan daman Allah Allah yake yaga Husna. Farooq ne yace "Gaskiya yanzu Husna barci take saboda jiya daddare bata samu tayi barci ba, sai dai kishiga kitchen ki girka ko Indomic and egg" ya k'arasa maganar yana kallon ta. Yusuf ne Wanda maganar ba k'aramin 6ata mishi rai yayi ba yace "Wai dan meyesa kake mana haka ne? Dan Allah Farooq ka tasheta tayi mana gaba d'aya mu nima yunwan nake ji. "Haba dan Allah Yusuf na fad'a maka yanzu tasamu tayi barci please kayi hak'uri mana." "Owhk Hafsat tashi mu bar mishi gidan sa" yana fad'an haka ya mik'e zai fita Farooq yayi saurin shan gaban shi yana cewa "Haba kai kuma daga fad'an haka shine har kayi fishi bari na tashe ta yanzu." Wani shu'umin murmushi yayi sannan ya dawo ya zauna. Ita kuwa tana k'ance sai faman shan barcin ta take hankalin ta kwance ba abinda yake damun ta. Zuwa yayi ya zauna a bak'in gadon ya zuba mata ido sai da yayi kusan 5mins sannan ya d'an shafa bayan ta yana wasa da gashinta jin hakan ne yasata tashi ba shiri. "Sorry My Angle na tashi ki ko?"Murmushi tayi mishi sannan tace "A'a. "Owhk ki tashi ga su Yusuf sunzo kuma wai yunwa suke ji please tashi mu shiga kitchen kunsan yau zan tafi office."


Abokin mijina PAGE 17 📒

Gaban ta ne yayi mummunar fad'uwa dan Ita yanzu batason Yusuf yazo gidan nan amman ba yanda ta iya. "Ya naga kinyi shiru lafiya dai ko." Murmushi tayi tace "Ba komai tashi muje." Haka ta mik'e ta saka k'atuwar hijabi har k'asa sannan suka fita. Suna fitowa sukayi arba da Yusuf daman idon shi yana gurin wani murmushi ya sakar mata Wanda yasa gabanta ya fad'i amman kuma sai ta basar ta watsa mishi nata hararar. Zama tayi a gefe d'aya tace "Ina kwanan ku. "Lafiya k'alau amarya ya kike? "Lafiya k'alau, Anty Hafsat ya jiki. "Jiki Alhamdulillah wallahi yunwa nake ji." "Ayya bari nayi sauri na had'a miki.


Yusuf yayi wuf yace "Ai nima haka yunwan nake ji a taimaka mana mu biyu yanzu."Kallon shi tayi sannan tace "Hmm kajira na gama."Allah sarki bawan Allah Farooq yana gefe yana kallon su sai da yaga Husna ta wuce kitchen sannan ya bita. Yusuf ma mik'ewa yayi ya bisu Yusuf mik'ewa yayi ya bisu kitchen d'in lokacin da yashiga samu yayi Farooq yana kissing d'in Husna wani abu yaji ya daki k'irjinsa amman kuma sai ya daure ya shiga yana cewa "Yauwa bari nima na tayaku dan mu gama da wuri." Farooq ne yace "Haba kai kuwa kabari mana yanzu ai zamu gama kagani fa doya ne" ya k'arasa maganar yana nuna doyar. Yusuf kuwa wuk'a ya d'auka yana cewa "A'a wallahi kabari na tayaku muyi mu gama mu tafi aikin mu." Husna wacce tunda ya shigo ya fara maganar bak'in ciki ya lullu6e ta, ko kallon sa batayi dan kuwa yanzu ta fara gane shi. Kallon Farooq tayi Wanda sai faman washe hak'wara yake tace "To ni zan koma parlour wajen Anty Hafsat kuyi girkin tare." Da sauri Yusuf yace "Haba amarya ya zaki bar mana girki ai kinsan bazamu iya ba idan ba ke.


Abokin mijina PAGE 18 📒

Farooq yace "Haba sweetheart idan kika tafi ai kinsan bazamu iya ba please ki tsaya mu k'arasa." Bata kulasu ba ta fere doyanta ta d'aura sannan tazo tayi egg sos. Bata wani d'auki lokaci ba ta kammala amman kuma ko wanne motsi idan Husna tayi a idon Yusuf dan ko kad'an baya d'auke idon sa akan ta. Farooq ne ya jera komai a dining sannan shima yaje ya shiga wanka. Hankalin Yusuf gaba d'aya yana kan d'akin da Husna ta shiga dan kuwa yasan wanka taje yi. Bata wuce 30mins ba ta fito cikin wani atamfa mai ratsin pink a jiki Wanda ya amshi jikin ta ba wani kwalliya a fuskan ta. Gaba d'aya sune suka zauna a dining Yusuf ne ya zauna a kujeran da yake kallon na Husna dan ko me tayi yana kallon ta, hakan ne yasa Husna mik'ewa ta zauna akan cinyar Farooq tana cewa "Honey ni a baki nakeso kabani bazan iya ci ba" tana maganar cikin shagwa6a. Kara tallafota Farooq yayi yace "An gama my angle." Wani bak'in kishi ne ya ziyarci zuciyar Yusuf yanda ya sashi ya mik'ewa yana shirin barin parlour ne Farooq yace mishi "Yusuf lafiya kuma zaka fita bakayi breakfast d'in ba?" Wani kallo Yusuf yayiwa Farooq sannan yace "Bazan zauna kuyi wannan rashin kunyar a gaba na ba." Husna ce tayi wuf tace "Wayyo Allah Honey yunwa nakeji kabani naci mana." Da sauri Yusuf ya fita dan idan ya tsaya kallo ta idan baiyiwa Farooq suka ba to zuciyar shi zata buga. Bayan ya fita sauka tayi a kanshi tace yaci dawuri ya tafi wajen aiki kar yayi lett. Shi kuwa Yusuf yana fita mota ya hau yabar gidan gaba d'aya dan shi bazai iya zama ba amman wallahi Yau sai ya dawo ya bayyana mata abinda yake ran shi.


Abokin mijina PAGE 19 📒

Ita kuwa suna gamawa Farooq ta raka mota ya tafi dawowa tayi wajen Hafsat wacce da halamun barci ne yake damun ta. Tambayan ta tayi da cewa "Anty Hafsat barci kike ji ne?" "Eh wallahi Husna barci nakeji sosai." "To ki kwanta mana." Ai kuwa tana ajiye kanta barci yayi gaba da ita. Husna tana ganin haka ta d'auki wayan ta ta kira Hajara mai lalle dan tazo yanzu tayi mata. Ai kuwa tayi sa'a Hajara bata aikin komai nan da nan tazo ta fesa mata lalle. Bayan an gama mata tashin Hafsat tayi tace ta tashi itama a mata, amman sai tace A'a ita zata shiga part d'in ta. Tana shiga Hajara tayiwa Husna shara da moping duk ta goge mata gidan ta fess. Sallaman ta tayi ta tafi sannan ita kuma ta d'aura girkin dare. Shima bata d'auki lokaci ba ta gama tuwon shinkafa da miyar ya kuwa Wanda yasha kayan k'amshi da nama. Ciki ta shiga dan yin wanka. Tana Barin parlour Yusuf ya shigo dan yasan Farooq yanzu bai dawo ba. Ganin bata parlour ne ya tabbatar da cewa tana cikin d'aki. Hanyar d'akin ya kama dan kuwa yau komai zai faru sai dai ya faru. Ita kuwa tana toilet tana wanka dan bata son Farooq ya dawo bata shirya ba. Cikin d'akin ya shiga yana du6e-du6e amman ina 6e ganta ba har zai fita sai yaji motsi a toilet. Wani shu'umin murmushi yayi sannan yayi hanyar.. Wani shu'umin murmushi yayi sannan ya kama hanyar toilet d'in da take.


Bud'ewa yayi a lokacin ita kuma ta d'aura towel a jikin ta kenan sai gashi nan ya shiga toilet. Ita bata kula da shiba dan ita sauri take, shi kuwa duk ya haukace a kallon ta. Juyowan da zatayi sai kawai taga Yusuf a toilet tsaye yana kallon ta. Wani irin ihu ta saka sannan ta fashe da kuka tana rok'on shi akan dan Allah ya fita. Kin fita yayi sai ma


Abokin mijina PAGE 20 📒

kara matsowa inda take yake ita kuwa duk tsoro ya mamaye ta gashi ba hanyar gudu. Sai da ya matso daf da ita yana lashe harshe sannan yace "Daman nazo ne nafad'a miki abinda yake zuciya na Husna, Husna ina sonki wallahi idan ban sameki ba mutuwa zanyi please ki taimaka mun ki taimakawa rayuwa na." Wani kallo ta mishi sannan tace "ban gane na taimaka maka ba Yusuf me kake shirin yi?" Kara matsowa yayi sannan yace "Yauwa dan Allah inason kibani had'in kai ina yin six da ke ko kuma ki raba auren ki na aure ki sai ki zabi d'aya a cikin biyun dan Allah Husna." Ita dai Husna ba abinda yake fita a jikin ta ni ba zufa ba, zuciyar ta tana zugawa Amman kuma sai ta daure tace "To sai mu fita a toilet mu k'arasa maganar dan naga mai muhimmanci ne." Haba wa tana fad'an haka yaji wani dad'i a rain shi dan gani yake tarkon shi ya kamata. Daki suka koma, shi kuwa har da zama a bak'in bed ban ji yake shine angon. Hijabin ta ta d'auka da sauri ta saka, Yusuf ne yace "Haba Husna ta d'an meyesa zaki rufe mun jikin ki baki san inajin dad'in ganin shi hakan ba?" Wani kallon tsana ta watsa mishi sannan tace mishi cikin d'aga murya tace "Tunda jikin na uban ka ne ba, To wallahi Yusuf ka fita a ido wallahi zan d'au mataki a kanka banza alade kawai mai bin matar a abokin shi" ta k'arasa maganar tana wani irin huci.

Wani kallo ya mata sannan yace

"Wallahi idan baki bani had'in kai ba wallahi sai na kashe Farooq idan yaso sai naga da wa zakiyi tunkaho." Husna da jin haka ta rikice idanun ta sukayi bak'i bata ganin komai hakan ne yasa ta d'aukan kwalba ta kwad'awa Yusuf a goshi. Ai kuwa nan da nan Yusuf jini ya wanke mishi fuska,


Abokin mijina PAGE 21 📒

Da gudu ya fita yabar gidan dan yaga alamun idan ya zauna Husna zata kashe shi. Yana fita ya hau mota ya wuce hospital d'an kuwa ba k'aramin ciwo ya ji ba. Ita kuwa Husna yana fita ta fad'a kan gado tana kuka sosai dan batasan ya zatayi ba. Waya ta d'auka ta kira Mummyn ta amman ina har 3 missed call bata d'auka ba hakan ne yasa ta sake kwanciya wani sabon kuka. B'angaren Farooq kuwa hankalin shi duk ya tashi kasan cewar Yusuf yak'i d'aga masa waya dan yasan fishi yake da shi. Har magriba Husna tana nan tana aikin kuka tana tunanin ta ina zata lullowa al-amarin Yusuf dan yaga ba da wasa yazo mata ba. Tana cikin tunani wayan ta ya fara ringing da sauri ta d'auka ganin Mummy. "Hello mummy nashiga uku Yusuf zai kashe ni wayyo Allah mummyna ki taimaka mun dan Allah" ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka. Mummy wacce bata san me Husna take nufi ba tambayan ta tayi da cewa

"Husna lafiyan ki kuwa?

Me aka miki?

Me Yusuf ya miki?"

Duk wannan tambayan tayi mata a lokaci d'aya. Ai kuwa nan da nan Husna tabawa Mummyn ta labarin abinda Yusuf yake mata tun randa aka kawo ta. Shiru na d'an lokaci tayi sannan tace

"Mijin ki yasan da wannan abinda yake faruwa?"


"A'a Mummy bai sani ba,

kuma wallahi ko na fad'a masa bazai yarda ba saboda ya yarda da Yusuf fiye da tunanin mu, Mummy kuma cewa yayi sai ya kashe shi fa. "Husna wannan al'amarin ba na waya bane, ki tashi kishirya ki saka kayan ki kar kibari mijin ki ya gane kina cikin damuwa, kuma kar kiyi kurkuren fad'a masa dan ba yarda zaiyi ba, kiyi hak'uri zuwa gobe zamuyi abu d'aya."


Abokin mijina PAGE 22 📒

To Mummy nagode. "Yauwa 'yar albarka kar kibari yagane kina cikin damuwa kinji." Haka dai sukayi sallama sannan ta tashi ta shirya tayi kwalliya. Bayan Yusuf ya tashi daga hospital gida ga dawo, part d'in shi ya shiga ko sallama babu. Hafsat ganin ya shigo ba sallama gashi goshi a fashe yasata mik'ewa tana tambaya lafiya? Amman ina kin kualta yayi yashiga d'akin shi ya rufe. Farooq yana dawowa gida part d'in Yusuf ya shiga d'an yasan yadawo gida kuma ga motar shi a ajiye.


Bayan ya shiga sun gaisa da Hafsat yake tambayan ta ina Yusuf, cemishi tayi yana cikin d'aki. Kwankwasa k'ofar yayi sai da ya dad'e sannan ya bud'e mishi yana shiga yagan shi goshi a fashe da sauri ya k'araso wajen shi yana tambayan shi me yasa me shi. Ko kallon shi baiyi Ba yace mishi "Acceded nayi." Cikin zaro ido Farooq yace "??Haba Yusuf yanzu har zaka mun fishin da zakiyi acceded baka fad'a mun ba." "No Farooq ba wani ciwo naji ba shiyasa ban fad'a maka ba." "To naji tashi muje hospital yanzu." "Naje gashi nan an bani magani." "Kaci abinci ne?" "A'a ban ci ba." "To tashi muje muci tare." "A'a kaje kawai bazan iya ganin wasu abubuwan da ya haramta ba." "Kaga dan Allah tashi muje kaifa bakada lafiya." "Kayi mum alk'awarin bazakayi komai a gaba na ba." "Eh naji dan Allah tashi muje." Haka suka tashi suka fita suka zo part d'in shi. Suna sallama gaban Husna ya fad'i amman sai ta d'aure ta amsa musu cikin sakin fuska.


Abokin mijina PAGE 23📒

Tashi tayi tanayiwa Farooq sannu da zuwa, cikin sakin fuska ya amsa mata sannan yace mata "My angle muje dining kinga Yusuf yayi acceded bai fad'a mana ba kuma yunwa yake ji yaci abin ci yasha magani." Kallon shi tayi tace "Ayya Yusuf acceded kayi ? To Allah ya sawak'e" Tana maganar tana wani basarwa. Abin ci sukaci suka tashi sannan Farooq yabashi magani yasha. Suna zaune suna hira shi kuwa Yusuf yana kallon Husna yana tunanin ne ya kamata yayi mata wani shawara ya yanke Wanda da haka yakama ta ya fara. Suna cikin hira kawai ya rik'e kai yana ihu wai yana mishi ciwo. Farooq wanda hankalin shi gaba d'aya ya tashi ya rik'e shi yana addu'a a haka barci ya d'auke shi a wajen. Farooq ne yace da Husna "Alhamdulillah tunda munsamu yayi barci ki d'auko blacker na rufe shi kinga sai dai ya kwana ana." Badan ran ta yaso ba taje ta d'auko Farooq ne ya rufe shi suka kashe mishi wutan parlour suka shiga ciki. Suna shiga ya tashi ya zauna yana zuba wani uban murmushi..

TURKASHI!

Suna shiga d'aki Husna bata wani bata lokaci ba ta d'auki hijabin ta tasaka tana shirin fita, ??Farooq yace mata "Ina kuma zaki tafi Husna?" Kallon shi tayi sannan tace "Gidan mu zan tafi mana." "Kamar ya gidan Ku? Me aka miki da zaki tafi gida a Daren nan?" "Ya Farooq zan fad'a maka gaskiya, Bazan iya kwana tare da namijin da ba muharramina ba a cikin gida d'aya ba, Kai yanzu kana ganin abinda kayi ya dace ? To wallahi idan har Yusuf anan zai kwana wallahi bazan kwana ba." "Haba Husna mutumin nan fa Bashi da lafiya kina gani kulawan mu yake buk'ata dan Allah kiyi hak'uri mu kwana, Kuma ma naga kwana d'aya ne."


Abokin mijina PAGE 24 📒

"Hmmm Ya Farooq kenan! Wallahi kaji na rantse bazan kwana a nan ba Wallahi gidan mu zan tafi tunda naga Aboki yafi matar ka muhimmanci a gareka." "Wai Husna bakida hankali ne kike fad'a mun haka? Karfa ki manta Yusuf tamkar d'an uwana ne na jini dan meyesa bazamu taimaka masa ba?" "Tai mako fa kace! Wallahi sai dai kai ka taimaka masa bad'ai ni ba, Kuma kana cewa shi tamkar d'an uwa yake a gurinka, Eh naji amman kai kana tsammanin Yusuf zai kaika gidan shi yace ka kwana a parlour bayan ga matar shi a cikin gidan?" Sai da ya d'an yi jimm sannan yace "Kwarai kuwa Husna nafi k'arfin haka a wajen Yusuf." "Kaga ya Farooq yanzu bamuda lokacin kace nace kawai kayi abu d'aya ko ni ko Abokin ka kaza6a." "Wayyo Allah na Husna ya kike son nayi?" "Owhk hakan yana nufin kazabi abokin ka." "No Husna dan Allah kar ki tafi kibarni dan Allah na rok'eki." "To bari ma kagani mummy zan kira a waya ta turo mun driver dan wallahi bazan iya ba na kwana da k'ato a cikin gida" ta k'arasa maganar ta danna waya. Da sauri ya warce wayan yace naji zan tashesa ya tafi. Wani farin ciki ne ya lullu6e ta dan daman hakan take nema amman kuma bata nuna yanda Farooq zai gane ba. Bangaren Yusuf kuwa yana la6e yana jinsu dan kuwa duk abinda sukeyi a kunnen sa sukayi shi. Yana jin Farooq ya nufo k'ofa hakan ne yasa shi gudu Wanda har yana buguwa da gini baya ganin gaban shi. A daddafe ya zo ya kwanta dan kuwa kan shi ya bugu amman ba damar magana. Farooq shi kad'ai ya fito dan yau Husna da gaske take ba da wasa ba.


A kwance ya sameshi tamkar marar lafiyar gaske, Shi kuwa Farooq duk tausayin Yusuf ya mamaye mishi zuciya.


Abokin mijina PAGE 25 📒

Zuwa yayi ya zauna a bakin kujeran da yake kwance a hankali yake tashin sa tamkar wani Baby, Shi kuwa Yusuf yana jinshi amman yayi banza da shi. Sai da Farooq yayi da gaske sannan Yusuf ya tashi. Yana tashi yayi dai-dai da kwankwasa k'ofar parlour. Farooq yake tambaya waye?

"Ni ce Ku bud'e mun."

Jin muryan Hafsat ne yasa shi mik'ewa ya bud'e kofar."Wai yau kai a gidan su zaka kwana ne? Ya kabarni har yanzu ina zaune ina jiranka amman shiru?" Farooq ne yace "Ayya kiyi hak'uri yanzu ma da zan rakashi." "Owhk tashi mu tafi." Wani haushin su ne ya kamashi sannan yace "Wayyo Hafsat nifa banda lafiya kuma gaskiya ina tsoron gidan nan ni kad'ai kawai kizo mu kwana a parlour nan." Wani kallon tara bai cika goma ba tayi mishi sannan tace "Gaskiya naga alamun rashin lafiyar gaske a tattare da kai, Gaskiya kan ka ya bugu sosai Wanda har ya kawar maka da hankali." Wani kallo ya mata yace "Ke Hafsat banason zancen banza ni sa'anki ne kike fad'a mun haka?" "Eh ai naga hakan a tattare da kai ne, Dallah malam tashi mu koma namu gidan kujimun mutum fa" ta k'arasa maganar tana dariya dan ita abin gaba d'aya dariya ya bata. Ganin zai 6ata mata lokaci Bashi da niyar tashi, Hakan ne yasa ta rik'e mishi hannu ta fara Jan shi. "Wai ke Hafsat baki da hankali ne? Dallah sake mun hannu." "To naji kazo mu tafi." Haka ya tashi ya fita ba dan son ran shi ba. Washe gari da asuba Farooq yaje duba abokin shi. Yana tafe bayan sun gaisa yake tambayan shi ina Husna. "Husna tana barci bata tashi ba dan jiya bamu kwanta da guri ba." Wani bak'in ciki ne ya mamaye shi amman kuma ya daure yace "Gashi kuma yunqa nake ji." "To Hafsat bata tashi a barci bane? Ai da ko tea ta d'aura maka kafin gari ya gama waye wa."


Abokin mijina PAGE 26 📒

"Kayya Abokina kasan Hafsat ba wani abin kirki zatamun ba. "To shikenan bari na d'aura maka ai yanzu zaiyi. "No Abokina! Munada mata kuma zaka shiga kitchen? Wallahi ban yarda ba." "To ya zanyi kenan?" "Tashi muje ka tashi Husna ta d'aura mun." Kallon shi Farooq kawai yake dan shima yanzu abubuwan da Yusuf yake ya fara isan shi. "A'a gaskiya yanzu bazan tashi matata a barci ba gaskiya, haba Yusuf ga taka matar a gida amman sai tawa matar?" "Owhk kanason kamun gori ne ko me? Na rigaka aure fa Farooq." "Ai wannan ba maganar aure bane, No kawai nace matata Ba zata tashi yanzu ta d'aura maka breakfast ba wallahi"............



Close Menu