Carar Zakaran dake harabar gidan ne ya katse min dogon bachin da nake. A hankali na matsa fuskata dauke da murmushi domin ko kadan hakan be bata min rai ba, na daga hannuna a sama ina mika tare da kara watsakewa, kamar kullum yau ma bachin ya min dadi, ba dan gurin da nake kwanciyar ba, sai dan farinciki da kwanciyar hankali da natsuwa irin ta masu wadatar zuci data cika min zuciyata nake kwanciya da ita a kowane dare.
Kamar wacce akai wa dole haka na bude manyan kuma lussasun idanuwana da suka rine suka sauya kala sakamakon dadewar da nai ina bachin. Akan farinciki na sauke idonuwana wato mahaifiyata wacce ke sanye da wani jan yade kodadden irin na talakawa kuma na gadonmu.
"Wainar ki ce take ci tun dazun aka aje miki"
Da yaren buzanci mahaifiyata take muna min kyanwar dake kusada ni tana cin waina.
Murmushi nai na kai hannuna na shafa kyanwar kana na shiga mata magana da yaren buranci.
"Kin cinye min waina ko?"
"Ataa yau ba za ki je baranki ba ne?"
Kanane ya tambaya, hakan yasa ni saurin tashi daga kwancen da nake, na fito daga cikin bunkar ina hamma ba tare dana rufe bakina ba, ba dan kuma ban san babu kyau ba, sai dan rashin kula da watsi da addini irin na mu na... Da hanzari na nufi wani dan guri da muka killace da kwano domin yin wanka ko kuma ba haya. Ba wanka nai ba domin wanka be dame ni ba duk kuwa da kasancewar na fi kowa tsabta a cikin gidan mu amman a hakan sai na kwana uku ban yi wanka ba.
Fitsari kawai nai na fito da sauri na wanke fuskata da fassashiyar butarmu marar murfi, sai da na gama wanke fuskar sannan na nufi gurin da muke girki na dauki gawayin kara na saka a bakina na tauna na saka yatsana na wanke bakin na kuskure sannan na wanke kafafuwana na nufo bukkarmu da sauri tuna ban yi sallah ba yasa na dawo na dauki butar nai alwala na sake kowa bukkar wanda zan iya kiransa da dakinmu.
Zanen dake daure a kirjina na cire na dauki riga da wando na wani shudin yadi mai kamar laile na saka na dauki hijab na saka nai sallah mai kamar asha ruwan tsuntsaye, wato da sauri domin cikin kannanen lokaci na yi na gama. Bakin dankwali na dauka na cire hijab din kaina na saka bakin dankwalin mai kama da karamin gyale na rufe kaina kamar yadda na saba ko kuma na ce muka saba.
Na kai hannu na dauko madubi tare da gawayin dana daka na kwaba tare da man shafi a guri daya, tsayawa nai kallon kaina a madubin ina murmushin daya kara bayyanar da kyauwona har dimple dina suka bayyana, sai faman lumshen manyan idanuwana nake ina budewa. Abu ne da ya ke bayyane, bana bukatar kowa ya kalleni ya fada min cewar ina da kyau, kyau na hali ko na halitta kyau na jiki ko na fuska, ni kaina idan na kalli madubi kyawona tsorata ni yake, idan ba a kirani balaraba ba to ba za a cireni a jinsin india ba indiyawan ma sai an tona, hakika ni kaina na san ina da kyau na wuce misali, kyan dake hana ni shakaf a cikin al'umma, gashin kaina kadai idan na sake ya sauko mutune har mamakin yadda nake da yawan da tsohon gashin dake saukona har mazaunaina suke.
Ba sai na fada ba, duk wanda yasan jajayen buzaye yasan su da kyau da gashi sai dai a cikinsu ni din ma ta dabam ce a bangaren kyau. Man dake gabana na gawayi na dauka na shafa a fuskata a take farin fuskarta da kyau ya gushe na koma kamar ba ni ba, dogon hancina kawai zaka gani ka iya gane ni shima kuma sai idan ka sanni farin sani sosai.
Sannan na mike tsaye na dauki kwagirin dana saba ratayawa a koguna (kwankwaso) idan zanje yawon bara na daura. Gurin da mahaifiyata take zaune naje ina mata sallama da yaren buzanci.
"Na tafi Nana"
Haka nake kiranta da sunan dana tashi naji mutane na kiranta da shi duk kuwa da kasancewar ba shine aihanin sunanta na gaske ba.
"Allah ya tsare a samo da yawa"
Ta fada min tana dariya ni kuma na kada kai na fice ina murmushin domin bata san gaskiyar abun ba, a duk tsawon kwanakin da nai ina aikin.
Sai da nai nisa da bukkarmu ta yadda babu wanda zai iya hango ni sannan na ra6a ta cikin kangon gidan da muke gaban bukkar mu wanda wani shahararren mai kudi yake ginawa na shiga ta gurin da aka fasa domin yin windows na fada cikin wani gurin da ban san me za ayi da shi ba, daki ko falo, na dauki kayan aikina na bi ta kofar gaba na fice, na saba ba tun yau ba, idan nai nisa da gidan mu da sunan zuwa bara kamar yadda mahaifiyata take saka ni sai na biyo ta window kangon gidan na dauki kayan wankin motana, na bi ta kofar fita na fito, har yau mahaifiyata bata ta6a sanin cewar ina wannan aikin ba, ni kuma ban ta6a ganganci fada mata ba, domin na san zata hana ni idan ta gano ba bara na ke ba, kamar yadda take son nai, ni kuma bana son barar domin tana ci min rai, kamar yadda take kankantar ni ga duk wanda na mikewa hannu na ce ya bani.
Ya zame mana kamar al'adar yin bara a titi ko manyan gidaje ko ma'aikatu domin samun abunda zamu ci, wasun mu suna da shi wasunmu suna da rufin asirin da zasu iya rike kansu ba tare da sunyi bara ba, tsabanin mu da kullum sai mun yi bara muke samun abunda zamu ci. Na sha ganin irin wulakancin da ake ma mahaifiyata kala kala idan muje bara musamman akan titin manyan motoci wanda hakan yake bakanta min rai, sai dai ita ko a jikinta duk kuwa da irin kyamar da ake nuna mana.
Wannan dalilin ne yasa na daukar mata alkawarin cewar zan rika yin bara da kaina ina kawo mata kudi ita ba sai taje ba, da wannan ta dogara ni kuma na sauya hanyar bara zuwa neman na kai, duk kuwa da kasancewar wasu na min dariya ganin kamar aikin be dace da ni ba, wai ace mace kamar ni ina tsayawa a inda motoci ke tsayawa saboda traffic ina wanke gilashin mota ana biyana, aikin da akasan maza ne suke yi. Nikam hakan be taba damuna ba, domin na san yafiye min bara kuma ina samun sosai fiye da baran ma, ganin ni macece yasa wasu mazan ba hansin suke ba ni ko ashirin ba, har dubu daya na kanyi dacen wani ya bani.
Ba dan kuma an san ni din wacece ba, domin kullum fuskata shafe take da fantin gawayi wanda hakan kan jama min kyama a gurin wasu, sai dai ni yafi min kwanciyar hankali na boye kyauna na, gudun abunda zai iya biyowa baya, za a iya kawo min hari kamar yadda aka sha min lokacin da muke wacan gidan da ba a tashe mu ba, duk wanda ya kalle ni a aihinin yadda Allah ya hallicce ni ba za a min kallo daya a dauke ido ba, ba kuma za a ki fadar cewar ina da kyau mai jan hankali ba, mata ma sukan fada balle mazan da babu adadi.
Ko a unguwar da muke zaune a yanzu wato Clapperto babu wanda ya san iya ainahin yadda fuskata take, domin kullum ina tare da bakin gawayi a fuskata, wanda hakan kan sa a kara kiranmu da kazamai, ganin irin gurin da muke zaune mai kama da juji, wani kangon fili ne kato wanda aka ware wani bangare na filin aka fara ginin gida kuma aka bari, lokacin da aka tayar da mu daga wacan kangon gidan da muke rabe sai muka dawo wannan muka zauna ba tare da tambayar izinin mai shi ba, muka kafa yar bukkarmu muka zauna a nan muke rayuwarmu ta yau da kullum.
Na saba tafiyar kasa, dan haka komai nisan guri ni baya damuna, ina tafe ina rare wakar mu ta buzanci wance mahaifiyarmu take yawan rarewa a gida, idan na dora alkalamina a ko wane kalar littafi zan cika shine da kalmar kaunar iyalina kamin na bayyana komai na rayuwata, ina son yan uwana kuma ina son yarena da al'adata fiye da komai a duniyar nan.
A sannu nake tafiyata har na iso babbar flyover din Alu inda na saba wanke motoci ana biyana, kamar kullum mutane suna ta kai kawo a gurin kama daga masu babura da masu napep da kuma masu motoci manya da kanana. A cikin a kusa na soma sana'ata idan naga babu motoci sai na koma inda muke zama ni da abokanin sana'ata yara maza mu zauna sai idan an sake hada motoci sai muje da gudu mu wanke wasu kuma suna siyar da popcorn wasu kuma pure water, wasu air freshener da turare dai sauransu.
Sai da yamma lis na nufo gida gani a gajiye amman ba zan iya cire kudi na hau abun hawa ba, a ganina idan na hau kudin zasu ragu, kamar yadda mahaifiyata ta koya tun a lokacin da muke bara.
A hanya na siye pure water da gyada ina tafiya ina ci can ta tsallaken titi nake hangon wasu buzayen irina a jikin wata motar suna mika masa hannu ya basu, ni dai ban da kallonsu babu abunda na ke, ban ankara ba naji an watso min ruwan saman da akai kwana biyu da suka wuce, wadanda suke kwance a gefen titin sakamakon wucewar da wata motar tai da gudu kamar zata tashi sama.
Wani bakin haushi naji domin ba kadan ruwan da motar ta taka suka bata min tufafi ba da kuma kayan aikina, dan brush da man wanke mota da kuma kyalena na gogewa idan na wanke.
Bance komai ba naja tsaki na cigaba da tafiyata, yo daman wa zance wa wani abu tunda ni kadai nake ta tafiya ta. A natse nake tafiya ta har na karyo kwanar dana saba bi idan zanzo gida, ina yanke hanya ne domin abun ya zo min da sauki, sai dai duk da haka ana kiran magariba na soma dosowa unguwarmu ta Clapperto road, a dai dai bakin gate din gidan dan Uti idanuwana sukai arba da kalar motar da wuce ta gabana dazun ta bata min tufafi, kuma wani abun dadi babu mutane a titi sai karar motocin dake kai da kawo.
Sai da naje gaban motar na leka gaba babu kowa a ciki, sannan na kara matsawa ina kara tabbatarwa idan ita dince ko aa, kalar dai daya ce sabuntar ma daya ce sai dai wannan anyi mata hoton ZAKI a jikin number motar kuma an rubuta mata ZAKI 001 da manyan haruffa tsabanin wacan da ban kula da number motar ba ma balle ma na san me aka rubuta.
Komawa nai ta inda na fito ina ta kalle kalle har na hango wani katon dutse da be fi karfina ba, na dauko na zo na jefawa motar ta gurin gilashinta, a take ta fara kuka, ni kuma na ranta cikin na kare, ai daman dai burina na dauki fansa, ko ba shine ya bata min tufafi ba be dame ni ba dan dan'uwansa ne mai kudi sai suji yadda ake ji...
Abunka da marar jiki nan da nan na karya kwana kwana ina ta sauri kamar an biyoni, tsoro ya saka na kasa mikewa kai tsaye na bi titi na isa gida, sai na shiga ta hanyar gidan taba (Gidan azaba) na bulla ta can kwantagora road na karyo ta wata hanyar, domin kawai wahala sannan na bullo da gidajen yan sanda da yake nan na biyo ta bayan gidan Alkali Abu dange wato gidansu Khadeeja Candy na fito titi Clapperto road na doshi gidanmu.
A inda na saba aje kayana na nufa na aje sannan na fito ina kirga kudin dake jakata, kamar ance na waigo ko da na juyo sai na hango wata halitta mai kyau da daukar hankali da kuma ban tsoro tana kallona. Mutum nake hange amman a siffa da fuskarsa, sai dai kwarjininsa da aibarsa kamar wani zaki. Nesa yake da ni amman fuskarsa zooming take min tana kawo min shi kusa kamar yana tsaye a gabana. Annuri ne shimfide a fuskarsa, sai dai ba irin na masu dariya da sakin fuska ba, irin wanda annurin ya zame masa jiki yake bayyana kansa a duk lokacin da mai shi ya kalleka, kwarjinsa ya cika min ido har kure ganina nake ganin kamar daga ni sai ainahin Zakin ne a jeji, wani abu mai zafi naji yana bin kafafunawa, ashe fitsari nake a tsaye ban sani ba, tsabar tsoro ya cika min ciki sai na fadi zaune a gurin na rufe idona kunya ce ta kamani budurwa kamar ni ace tai fitsari sai kuma naji ashe ba kunya ba ce tsoro ne.....