Ad Code

Yanda Zaki gyara Gashin ki


 GYARAN GASHI

Kafin ki fara gyaran gashi akwai buqatar sanin kalan gashin ki ina nufin type dinsa ba wai fari ne ko baqi ba


DRY HAIR

Zaki ganshi ko da yaushe a bushe daga kin shafa mai nan da kwana daya ya bushe fatar kanki fari tas sometimes yana sa dandruff mai gari idan rashin kulawar tayi yawa sanna gashin baya tsawo yana saurin kakkaryewa. Wannan gashin yafi kowane buqatar gwata sai kinyi da gaske in har ba sou kike ki zama kwakwido ba at least koda gashin bazai karu ba dai tou ba'a so ya ragu


OILY HAIR

Zaki ganshi ko da yaushe cikin maiqo sannan yana saurin jiqewa idan kin shiga rana irin wannan gashin wari yake yi idan ba'a yawan kula dashi especially idan akwai amosari ko kuraje akan... Domin idan ciwo ya shiga cikin gashin nan ruwa yake yi wanda hakan ke sanya wa gashin wari


NORMAL HAIR

Wannan bashi da wani matsala zaki ganshi ba a bushe ba kuma ba'a jiqe ba yana da kyau sosai very fresh


COMBINATION HAIR

Wannan gashin yawanci zaki same sana qasan (wato daga keyan ki xua kasa) yana da maiqo ta saman kuma abushe ko kuma normal shima wannan gawhin sosai yake buqatar gyara.


SENSITIVE HAIR

Wannan gashin bashi da kyau sam... Kuma rashin gyara ne yake kawo shi tare da too much iyayi komai kika samo ki laftawa gashin ki sai yazo ya lalace kullum yay ta karyewa ga yawan kuraje da amosari wani lokacin ma gashin zai zama dai dai dai dai kamar dai mutum ya zauna ya irgasu. Hakan yana faruwa a kowame launin relaxer na lissafa a sama.

Wadannan suna kalolin gashin da muke dasu gaba daya wanda akwai hanyoyi da yawa da zaki gane irin su gareki da kuma yanda zaki magance sa cikin sauki amma fa zai dauki lokaci sannan kafin ki fara akwai buqatar ki san wannan


BANBANCIN SHAMPOO DA RELAXER

Mutane da yawa sun san banbancin su kazalika mutane da yawa basu sani ba dan haka akwai buqatar ayi masu uzuri. .



SHAMPOO

 kamar sabulu ne na ruwa wanda ake wanke kai da shi baya qara komai baya rage komai sai dai idan anyi shi mussamman dan yayi din. Wanda idan hakan ya kasance zaki ga an rubta a jiki. 


RELAXER

 wannan kuma wani mai ne mussaman da aka kirkire sa don gyaran kai musamman ga baqaqen fata mai gashi a cushe idan suna buqatar gashin su ta kwanta tayi kyau kamar na fararen fata sai suyi amfani da ita.


NATURAL HAIR

Idan akace natural hair ana nufun wadanda basa sa relaxer (famin ko kumfar los.. Mama jugu jugu da sauran su). Sabida rashin lokaci yau zanyi bayanin yadda mai natural hair zata kula da gashin ta idan Allah ya kaimu next week sai muyi na masu sanya relaxer. 


Da farko dai shin gashin mu na baqaqen Africa gashi ne wanda yafi na ko wane ginsi kyau lisabab... yana buqatar gyara sosai sabda adunkule yake wanda hakan ke hana asalin maiqon dake fatar kanki (natural sebum) wazuwa har bakin gashin ki rashin faruwan hakan kuma yana taimakawa wajen kakkarye gashin wato sabo na fitowa tsoho na karyewa.


SHAMPOO

Zai dace ki bar amfani da ko wane irin shampoo musamman wandanda suke dauke da sinadarin SULFUR.. PETROLEUM DA SODIUM domin suna dauke da sinadarin busarwa irim wanda ake amfani da su a sabulan wanki omo da sauransu don haka duk lokacin da zaki saya sai ki duba ingredients din idan kuma yq zama dole sai kinyi amfani dashi tou sai ki surka shi da ruwa daidai adadin sa. 50-50 kenan ko kuma ki nemi 


MILD SHAMPOO

 wannan bashi da chemicals masu zafi sosai. Amma organics is the best option


ORGANICS

abun da ake nufi da organic shine natural abu wanda ba'a yi amfani da wani harsh chemicals (kemikal masu qarfi) wurin sarrafa su ba kamar dai wasu nau'ika da nau'in abinci da ake sarrafawa acire wani abu daga cikin sa

Yafi dacewa abun da ya kama daga man shampoo conditioner man kitso da duk wani abun da zakiyi amfani dashi a kanki ya zama natural ko kuma organic Domin duk man da kika shafa a fatan kanki yana shanyewa sannan jini ya tafi dashi zuwa hantar ki daga nan kuma ya cigaba da wanzuwa ko ta ko ina don haka yake da matuqar mahimmanci kisan irin abubuan da zaki na sawa a kanki saboda tsaro.


CONDITIONER

Shi conditioner ana amfani dashi ne dan a dawo da taushin da aka rasa na gashi. Yanda ake amfani dashi kuwa shine bayan kin gama shampoo kin dauraye tas! Sai ki shafa conditioner tun daga qasan gashinki zuwa bakin sannan ki samu leda ki rufe gashinki ki daura dankwali ki barshi na tsawon lokacin da suka rubta a roban. Bayan nan sai ki wanke ki tabbatar baki barko kadan a cikin gashin ki ba don kar yayi maki illa. 

Amma sau daya ake yin hakan a wata daga nan du ranar da zaki wanke kanki baza ki sha shi a fatar kanki ba gashin kawai musamman karshen gashin (ina nufi. Inda kike kamawa da ribon)

Ga wadanda suke wanke gashim su kusan kullum yana da kyau ya kasance duk lokacin da zaki sa ruwa a kanki to kiyi amfani da conditioner ki dauraye hakan zai sa gashin yayi maintaining moisture dinsa sannan idan ya bushe sai kiyi oiling (oiling yana nufin shafa mai lungu da saqo)


COMB

ki riqa amfani da qaton kum mai manyan haqora ko kina da gashi ko baki dashi domin karamin kumb yana tuge gashi

Sannan ki sayi daya safaya ki ajiye wajen sa da ban saboda baki idan ba haka ba kullum aikin ki baya xai riqa dawowa duk wani abun fa kike amfani dashi a gashi ya zama naki ke kadai ko ke da yaran ki. (Idan kina kula da gashin kansu kenan)


OILING

Yanda zaki fiqa shafa mai akan ki shine ki riqa sagawa kanana kina shafa mai daga fatar kanki zuwa qarshen gashin har ki gama sannan ki zauna kiyi ta massaging gashin kamar kina susa kaikayi amma a hankali dan man ya natsu a ciki idan na tsawon minti 30 ko awa daya ma idan kin gama ki tace sannan ki qara shafawa bakin gashin mai sosai. 

Rashin shafa mai a bakin gashi shi yake kawo karyewan gashi sabo na fitowa tsoho na karyewa gashi baxai taba yin tsawo ba kenan.


PROTIEN TREATMENT

Yana da kyau ko wani wata ki riqawanke kanki da kwai misali bayan kin wanke kai kin tsane ruwan tas ya fara alaman bushewa sai ki fasa kwai wasu suna amfani da farin ne kawai wasu kwaiduwan (york) wasu kuma both duk dai wqnda kika zaba sai ki shafa bayan awa daya ki wanke ki dauraye da conditioner zai sa gashinki shining (kyalli) da kyau . zaki iya hada kwan da ayaba da madara wannan ma yana da kyau sosai ya kuma qara bakin

Gashi. Amma fa kar kiga ya qarbe ki kije kiyi tayi toh ba ruwana idan ya kakkabe gashin..... Sau daya tak! A wata


SALOON 

Ki dainq yawan zua saloon ana kona maki gashin ki abanza yana karyewa gara kina gama wanke kanki kiyi kalaba ki barshi yabushe washe gari ki tsefe ki shafa masa mai

Idan kuma ya zama miki jiki amfani da kayan wuta a gashi don warware gashi tou gara ki shiga dryer (draya) yafi sauqi da rqwhin karya gashi sannan kuma ki siya HEAT PROTECTION SHAMPOO, MOISTURIZER, SPRAY KO KUMA SERUM ki fara sawa a gashinki kafin a fara qonawa.

Close Menu